Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

dake faman bankad’a kayan tace,

“Eh kuma fa hakane Ya Sahal, d’ayar sunan ta Fa’iza...”

Tana fad’a yaji wani shauk’in soyayya ya shiga memory card ‘din card din kansa, take yai rebooting ‘karshen haduwar su, ya wani lumshe idanu, Tare da gyara kwanciya akan kujerar da yake, zuciyar sa na haskalo masa ita, yana jin sonta na ‘kara shiga magudanar jinin sa.. Ummi dake gefe ta sa masa albarka ganin kayan, had’e da dakko na wajen ta da suka siyo itada Fa’iza, Nan suka had’a a babban Bucket kan da safe sai tafiya sumaila visiting din su Aliya...

*WASHE-GARI*

Da safe ahalin gidan Baba Sulaiman su ka nufi Sumaila Local Govt. Shi da matar sa, da Gwaggo Talatuwa, cike da kayan da za’a kai wa su Aliya, domin har soyayyar miya akai musu data ji kaji, an kuma yi musu shinkafa da miyar kifi harda coleslaw da zob’o, Gwaggo Talatuwa sai zuba magana take yi, Ita dai Umman su Fa’iza a kunyace take amsa surikar tata jefi-jefi, Saboda kunya...

A kuma lokacin ne su ma su Sahal suka ‘dau hanyar sumaila, shida Husnah da abokin sa Fareed, Ummi bata samu damar zuwa ba, saboda dawowar ba zata da mahaifin su Sahal yayi daga tafiyar dayayi daga birnin ikko (Lagos).

Su Baba Sulaiman sun riga zuwa, Ai kuwa ana sanar dasu Aliya suka tafi a guje suna kukan farin ciki. Aka baje ana hirar yaushe gamo? Tare suka ci abincin, Aliya nata zubar basu labarin yadda makarantar take, suna ta daria, sai ga su Sahal sun danno, tunda suka taho idanuwansa na kan na Fa’iza gaba d’aya ganganr jikin sa da ruhin sa ita suke muradi.

Dakyar ya iya gaydasu Gwaggo, Aliya sai zak’alk’ale masa take, shi dai duk kunya ta kamashi gefe d’aya kuma yana son kasancewa da Aliya domin gaya mata zuciyar sa, suna hada idanu Fa’iza ta zabga masa harara tana kallon gefe, daga nan kuma ta mike tace wa su Gwaggo zataje tadawo, murmushi Sahal yai ganin dan shi tai haka saboda ta tsane shi, Fareed ya kinkimo bucket din da suka kawo dake cike da kaya ya ajiye a gaban su Gwaggo.

Gwaggo Talatuwa ta shiga bud’ewa tana godia, cike da itama fa tasan zamin ta d’au kwalbar Nutella tana cewa,

“Harda Makilis din kwalba, Lalle Allah yayi albarka Sahalu angode, Ga kaya nan birjik harda ‘kanzon turai..”

Tafad’a tana mai nuni da cramp crackers, Shi dai Sahal mikewa yayi yana jan hannun Fareed, ganin haka yasanya Husnah cewa da Aliya,

“Kawata ki tashi kije, kinsan fa wajen ki yazo..”

Umman fa’iza tai murmushi kafin tace,

“Sirikin namu ne?”

“Eh..”

cewar Husnah cikin zak’uwa, mikewa Aliya tai ta tafi wajen sa, shi kuma alokacin ya tafi yana waya, hakan yasanya Aliya tsayawa da Fareed suna magana, shi kuwa Sahal inda Fa’iza tai yabi, can ya hangota gaban tuk’a tuk’a tana wanke fuskar ta, hannuwan sa zube cikin aljihun sa ya ‘karasa kusa da ita yana tafiya a hakimce, ‘dagowa tayi........

*SWITZERLAND🇨🇭*
*UNIVERSITY OF ZURICH*

Zaune Shamsudden yake, Shi da abokan sa Jeremy da Yazeed. ‘dan Nigeria ne shima, yana d’aya daga cikin wanda aka turo ta ‘bangaren scholarship, wato su Shamsudden kenan da honorable ya ‘dau nauyin karatun su.. Kamar ko yaushe suna zaune suna tutorials ne akan course din, ‘Oil Politics’. Afrah ta taho cikin takun ta na ‘kasaita, domin Afrah ‘yar sarkin Yola ce, kyakkyawa ce kamar ita tayi kanta, Samari ne suke tururuwa wajen zuwa ganin ta, domin ta karbi ‘kok’on barar su na soyayyar su, Sai dai kash! Afrah duk wani ‘da namiji baya gaban ta fyace Shamsudden. Shi take so, ta kuma ke muradin mallakar sa a amatsayin mijin ta, shi kuma baya sonta bayasan ganinta, a takaice dai ya tsaneta ma, domin mata basa gaban sa, Saboda abunda Aliya tayi masa, ya yi masa babban tabon da aganin sa wata ‘ya mace bata isa ta goge shi ba, shi yasa ya ‘dauki mata yayi musu kud’in goro. Ma’ana duk hali d’aya ya ‘dauke su...

Yazeed na hango ta ya zunguri Shamsudden dake daga hannuwa yana musu bayanin Oil in Middle East, siririn tsaki ya saki, kafin ya furta kalmar data zamto masa jiki wato,

“So intolerable...”


MX🧕🏼

_*K/11/S_*

*Tashi* tayi ta nufi hostel, kai tsaye d'akin Maman d'akinsu tayi, sai da suka gaisa har sun d'an fara hira kasancewar suna mutunci da juna Fa'iza ta d'akko ledar dake gefenta, Maman ta mik'awa sannan tace,

“Mama kayan nan zaki ajiye min sai ana gobe hutu sannan zanzo na karb'a.”

Mama ta karb'a ba tare da ta bud'e ba tace,

“Toh Fa'izinzin Allah ya kaimu lokacin.”

“Amin Mamah na gode, bari naje na zubo miki abinci.”

Fa'iza tayi maganar tana k'ok'arin tashi, har tasa takalmi taji Maman tana cewa,

“A'ah kinga 'yar uwarki Aliya ta kawo min, har nake tambayarta kina ina tace vice ya kiraki.”

Murmushi Fa'iza tayi sannan ta juya ta tafi, tana shiga ta tarar Aliya ta gama shirya musu kayan provision d'in cikin akwatunansu, zama tayi cikin nuna gajiya tana dafe kai Aliya ta kalleta tare da cewa,

“Sissy me akai, me vice d'in yayi miki?”

Gyara zama Fa'iza tayi tare da kallan Aliya, har zata gaya mata gaskiyar abinda yake faruwa, sai dai tayi had'iye tace mata,

“Cewa yayi wai muyi k'ok'ari mu sanar da Baba maganar jarabawar kwalifayin dinmu d'in mu, shine nace masa ai mun gayawa su Maman mu.”

“Ohh kaji vice da wani abun, toh idan mun gayawa Baba me zai yi? Hmmm kinga mutumin nan d'an nema ne shima Allah ya kyauta.”

Cewar Aliya, ganin yadda ta yarda da abinda ta gaya mata ne yasa Fa'iza sauke numfashi, bata son gaya mata cewar turaruka ne aka kawo mata daga wajan Muhamman S, tasan indai Aliya taji batun turare toh babu shakka sai an fito dasu ita kuma tayi alkawarin dena cin duk wani abun da Muhamman S ya kawo mata har sai ranar da ya bayyana kansa, yanzu abin tsoro yake bata, dan bata son yin abota ko soyayya da wanda zuciyarta bata amin cewa ba..

'”Sissy me, ya naga kin fad'a kogin tunani what's wrong?”

Kafin Fa'iza tayi magana wata classmate d'insu ta shigo corner d'insu, yarinyar kyakyawa ce a A class take tana mutuwar son Aliya, tana so suyi soyayya irin ta lover's da ake yi a boarding school, amman Aliya tak’i bata fuska. Saboda sam bata da sha'awar yin lover a rayuwarta, hasalima ita bata son abinda zai zo yasa ayi rigima da ita domin idan tana son abu toh bataji kuma bata gani dan haka taki yadda tayi, musamman ma da ita wannan d'in da take son suyi saboda yarinyar ana yawan kai mata hari kamar yadda ake yiwa Aliya da Fa'iza, garama Fa'iza tana da ita kuma suna mugun son juna da lover d'in ta ta, dan har Aliya mamaki take yi..

Nihla shine sunan yarinyar, guri ta samu a kusa da Aliya ta zauna wadda take ta faman shan k'amshi tana wani kawar da kai tamkar taga abin kyankyami. Cikin murya ta mai fad’in sauraro Nihla tace,

“Fa'iza ya gajiya?”

“Wallahi akwaita Nihla, anzo miki ne kema?”

“Yah! anzo min, ai har Aliya na kira dan tazo su gaisa da 'yan gidan mu amma wallahi tak’i zuwa, hmmm! Fa'iza ban san abinda na yiwa Aliya ba duk ta tsaneni.”

Dariya Fa'iza tayi tare da kallan Aliya taga sai faman d'aga uniform d'inta da ta cire takeyi, Nihla ma kallanta tayi, Amma duk cikin su babu wadda Aliya ta kalla. Fa'iza ta cillawa Nihla wata chocolate dake hannunta, karb'a tayi tare da cewa,

“Thanks Fa'iza, dan Allah ki tambayar min ita kiji me yasa taki accepting d'in? Bari na tafi nabar kayana a center.”

“Shikenan Nihla, kima kwantar da hankalinki tana sonki kawai shegen girman kai ne yasa ba zata nuna ba, amma idan muna tare da ita 'yar rainin hankalin sai tayi ta cewa dama ku hadu tana son ganinki.”

Duk cikin su babu wanda be waigo ya kalleta ba, Fa'iza ta maze sai faman murmushi take yi tace,

“Nihla da gaske nake miki naga kinyi saurin juyowa kina min kallan mamaki.”

“Dole na kalleki domin abinda kika fada ya cancanci na kumaji duk da cewar nasan kin dai fada ne kawai.”

Kai Fa'iza ta kad'a tare da cewa,

“Zamuyi magana dake gobe, kinga yau duk an gaji gashi ma dare yayi zamu gyara gurin.”

Tafiya Nihla tayi, Amma sam bata yadda da abinda Fa'iza ta gaya mata ba, musamman da taga Aliya na zaro ido lokacin da Fa'iza na yin maganar. Tana tafiya Aliya tace,

“Gasiya Fa'iza yanzu kin zama makaryaciya wallahi, a gidan uban waye nazo ina cewa nima na sonta?”

“Ban sani ba, idan na zama makaryaciya ai koya min akai, ke dalla wallahi garama ki rabu da wannan Sahal yake ko waye oho miki dan nasan bama auranki zeyi ba kawai kina wahalar da zuciyarki akan sa.”

Tashi Aliya tayi tare da sanya takalminta, kallan Fa'iza tayi sannan tace da ita,

“Dan Allah kiyi abinda ya dace wajan ganin gurin nan ya gyaru kafin su zo, kin tsaya sai zuba kike kamar kanyar da babu zak'i, aure na da Sahal kuma da sanin Allah domin shine ya had'a zuciyoyin mu dashi.”

Cikin sauri ganin tana niyar barin wajan Fa'iza tace,

“Hmmm wannan gayen 2face ne, wallahi gara ki tsaya ki gane mai sonki, kafin yazo yayi miki rashin mutunci kamar yadda kikaiwa yaya Shamsudden?”

Da baya ta dawo ta dafa wata locker wacce aka fitar da hanyar shiga da fita ta corner d'in, farrrr tayi da ido sannan tace,

“Karki sake cewa my Sahal mai fuska biyu zan iya yi miki rashin mutunci karkiga ke 'yar uwa tace kiyi tunanin zan kyaleki ki dinga yi min duk abinda kike so, sannan kuma wane yaya Shamsuddeen na tab'a yiwa rashin kunya?”

“Ke yanzu Aliya harkin manta Shamsu? Lallai aikuwa bai cancanci irin wannan mantuwar ba, Saboda yayi miki HALLACCI a rayuwarki, ya nuna muki so fiye da yadda zaki manta shi.”

Mtcew! Aliya taja tsaki tana hararar Fa'iza tare da yatsina fuska tace,

“Duk duniya babu wanda yake takura life d'ina irinki Fa'iza, kinga ni bana miki shisshigi a cikin duk abinda zaki yi, amman ke banda samin ido babu abinda kike yi, toh wallahi ya isheki idan ba haka ba kema zan takura miki.”

“And so? Ni dan kin takura min har wani haushin ki zanji ne yarinya, abu d'aya zaki min naji b'acin rai shine kik'i rabuwa da wannan Sahal d'in shifa ba sonki yake yi ba wallahi munafuki ne na tab'a ganin wadda yake son aura.”

Daram kirjin Aliya ya buga babu shiri sai gata a kusa da Fa'iza, dan tasan indai ta fadi magana toh tabbas ta shinshino kamshin gaskiya, jiki na rawa Aliya ta kamo hannunta tana rawar baki tace,

“Dan girman Allah da gaske kike yi Fa'iza? Please nasan ba zaki so ganina cikin damuwa ba, dan Allah ki gaya min da gaske kike yi yana da wadda zai aura?”

Ganin yadda duk Aliya ta rud'e sai ran Fa'iza ya kuma b'aci akan Sahal d'in, murmushi tayi bata son sanar da ita gaskiya a yanzu, Saboda karta kasa rubuta jarabawa gashi sun kusan farawa, dan haka cikin ‘kyalkyala dariya harda dukan cinyar Aliyan tace,

“Ke da wasa nake miki, ni a gidan wama nake wani ganinsa bare har nasan yana k'ok'arin auro wata? kawai dai ina son ki rage wannan soyayyar da kike masa dan wallahi namiji ba'a masa haka, sis dan Allah dan girman Allah ki rage son yaron can ba dan komai ba sai dan ki kare mutuncinki, WUTSIYAR RAK’UMI TAYI NESA DA ‘KASA)”

Murmushi taga Aliyan tayi tare da hayewa kan gadon sosai. Numfashi taja tana kallan yatsunta ta cikin hasken touch light d'in da suka kunna, ba tare da damuwa ba Aliya tace,

“Karki damu sis ni nasan Yaya Sahal ba zai yi min haka ba, sam ba zai yaudareni ba, kinji kuwa yadda yake shirya irin rayuwar da zamu yi idan munyi aure? Hmmm duk Husnah tana gaya min komai dan haka karki wani damu ki dinga ganin tamkar ya Sahal zai wulak'antani nan gaba.”

“Hmmmm! wanda yayi nisa baya jin kira, shikenan ina miki fatan alkairi, zan kuma taya ki da addu'a Allah ya sassauta miki sonsa da kike yi haka.”

Da sauri Aliya ta d'ago tare da janyo kafadun Fa'iza, kallan juna suka yi kafin Aliya ta dafe goshi tare da shafar fuskarta tana cewa,

“Dan girman Allah karki min wannan addu'ar, idan addu'a zaki min kice kawai Allah ya mallakawa Aliya Yaya Sahal, wannan addu'ar zaki min ba waccan ba, idan kika ce a rage ai sai naji bana sonshi, kodai kina ciki kema sis?gara ki sanar dani inji batu.”

Mtcew! Fa’iza taja tsaki ba tare da tace komai ba, saboda taga alamun 'yar uwar ta ba zata fahimci abinda take gaya mata ba.

“Ohh! Ashefa kina da wani saurayin, ko wanene wannan Muhamman S d'in? Dan Allah Fa'iza da gaske kike baki sanshi ba?”

Tab'e baki Fa'iza tayi tare da cewa,

“Ni wallahi idan ba Muhamman mai saida kifi ba, toh wallahi ban tab'a jin makamancin wannan sunan ba, bare shi wannan harda wani S a cikin sunan nashi. Na gaya miki ni ba kula samari nake yi ba bare na tsaya sanin sunansu, ki dena tunanin zan b'oye miki ko waye shi, nima addu'a ta kullum itace Allah ya bayyana shi na ganshi nima na huta da hasashen banza.”

“Karki damu idan anyi hutu zan taya ki har mu gano shi, irin wannan 'yan rainin hankalin wallahi idan suka bayyana sai kin raina su, kika bibiya ma kayan da ya kawo miki bashi yaje ya ciwo, motar kuma kila driver ne a wani gidan mai kud'in shine ya dakko ya taho wai shi zai yi miki fafa (karya).”

“Ahh sis dena min fatan d'an karya dan Allah, 'yar rainin hankali kina tunanin kece kawai zaki dinga samari masu aji?”

Aliya tayi dariya, tare da cewa,

“Toh banda d'an karya me yasa yaki fito da fuskarsa mu ganshi?”

“Hmmm kedai kawai ki taya ni addu'a Allah ya bayyana shi, Allah kuma yasa mutum ne dan abin ya fara bani tsoro

Amin Aliya tace daga nan sukaci gaba da hirarsu suna yi suna zuba abinci suna cewa a kaiwa ‘kawayensu suci abincin gidan su, idan an kai suma sai a kawo musu, haka dai suka dinga yi komai dai na 'yan makarantar kwana.
Shirye-shiryen exams suka fara yi, inda kowannen su ya maida hankali sosai, Aliya ‘bangaren Art class, ita kuma Fa’iza tana science class. Shiysa karatun nasu ya ‘dan banbanta ta wani ‘bangaren, amma sauran subjects din duk tare suke karatun su, su da ‘kawayen su. Su Na’ima gwaigwai ‘Saboda batada gashin kai’, Mannira dugwi ‘Dan batada tsawo’ haka suke kiranta, dasu Reema da A’ilo da sauran su, Sosai suke maida hankali wajen yin karatu, Sannu a hankali har aka fara jarabawar first term. Sun maida hankali sunyi komai cikin nutsuwa, shiyasa sosai jarabawar tazo masu da sauki, ranar Monday suka gama exams din, akai musu hutu Friday, Ai kuwa da sassafe Baba sulaiman yazo ya ‘dauke su, dadi kashe su zasu koma gidah, wani ‘bangare na zuciyar Fa’iza na adduar Allah yasa Muhamman S ya bayyana kansa, gaba d’aya yanzu zuciyar ta sai kawo mata take to ko shamsu ne shima ya kamu da son ta? ya ke aiko ‘dan aike ya kawo mata sak’o shiya sa ba’a ganin fuskar mai kawowar? Ai kuwa ‘kwa’kwalwar Fa’iza ta gama yadda da mai sunan Muhamman S, Shamsudden ne dake ‘kasar waje, yasa ake bibiyarta, yana bayyana mata zuciyar sa, wata nutsuwa taji tazo mata lokacin da suka shigo kano, ta kudiri aniyar washegari zata je ta gayda Umman su Shamsu. To hakama ‘bangaren Aliya, gaba d’aya ji take kamar tai tsuntsuwa ta tafi Abuja wajen Sahal, amma tasan da yaji tazo gari zai dawo,...
•••

*SWITZERLAND*
*UNIVERSITY OF ZURICH*

Kwance Shamsuddeen yake akan gadon sa madaidaici, yayi ruf da ciki yana ta faman yin rubutu, numfashi yaja tare da matsar da books d'in yayi rigingine yana kallan sama hannunsa rik'e da biro ya d'an sanya k'asan biron a bakinsa yana sa hakori yana d'an gatsawa. Murmushi yake yi jefi-jefi tare da lumshe idanunsa, ya dad'e cikin wannan yanayin kafin ya gyara yaci gaba da karatunsa yana kuma joting wasu words din dan ya samu time d'in warware su idan be gane su ba.

Wayarsa ce tayi ringing amman yaki d'auka, Saboda yanayin ringing tune d'in da yasa yasan ko waye mai kiran, sake kira aka yi bayan ta farko ta yanke, amman duk da haka yaki d'agawa har sai da yaji abin yaki karewa sannan ne ya juya ya d'auki wayar, Afrah! Shine sunan da na gani a jikin screen d'in, tamkar itace a gabansa haka ya daure fuska tare da karawa a kunnensa, daman saboda nacin kiran da take yi masa shine abinda yasa shi makala sunanta akan wayarsa amma da yaki yin saving, amfanin sanya mata ringtone daban dana kowa kuma, Saboda idan yaji yasan itace dan haka baya takurawa kansa wajan zuwa ya d'auka.

“Ya akai?”

Yayi tambayar murya a ciki, yana jinta tana faman sauke ajiyar zuciya yaja tsaki wanda ya tsaya masa iyakar makogwaransa. Sai da ta sake shake murya sannan ta fara yi masa magana tamkar wadda aka ragewa volume,

“Pulchritude kana ina ne yanzu? nazo department d'in ku ban ganka ba.”

“Kina bina bashi ne da kike nema na?”

Wani irin numfashi taja, wanda yasa Shamsuddeen janye wayar daga kunnansa saboda ji yayi tamkar da biyu tayi masa shi, jin bata yi magana ba ne yasa shi yin magana a takaice,

“Tunda babu bashinki a kaina, ina da abin yi, bye.”

Yana kaiwa nan ya mik'e tsaye tare da ‘karasawa wajan dispenser, ruwan sanyi ya tsiyayo tare da komawa bakin gadon ya zauna, sam ya rasa me yasa mata suke bibiyarsa shi kuma yana yakicewa dan ya kasa sabawa dasu tun abinda aka yi masa a Nigeria. A baya yakan tambayi Yazeed cewar menene yasa yawanci mata suke shige masa suna yi masa zancen Love?, budar bakin Yazeed cewa yayi saboda kanada halitta mai kyau wadda ba kowa ubangiji yake bawa ba, sai 'yan baiwa, ya k'ara da cewa, 'kaga wannan kyakyawar sumar da kake gyarawa har ta bada wani shu'umin style, itama tana daya daga cikin abinda yake jan ladies d'in cikin university d'in nan. Lokacin da Shamsu yaji haka daga bakin Yazeed suna rabuwa zuwa yayi gabaki daya ya aske duk wani gashi dake fuskarsa harda na kansa, ya Subhan’Allah yana fitowa tamkar yaje an sake gyaro shi, domin wani irin sihirtaccen kyau ne ya bayyana a gareshi, a lokacin da yayi asikin yayi nadama domin a ranar ne ya fara cin karo da nacin ‘Afrah’ akan sa.......

MX🧕
——
*L/M/12/13/S*

*UNIVERSITY OF ZURICH*

Tunda ya fito daga cikin hostel d'insu sanye cikin ‘kananun kaya farin wando dogo da farar riga polo takalmin kafarsa trainers kansa babu hula, sai scarf daya yafa a wuyansa, yayi masifar yin kyau duk a tunaninsa babu macen da zata kulashi a lokacin sai yaga abin kamar asiri, domin duk inda yayi ya d'aga ido zaiga tabbas shi suke kallo. Yana gaf da shiga department d'insu kawai yaji muryar mace tana kiran full name nasa cikin sassanyar muryar yaji tace,

“Hey! Shamsuddeen Al'amin Buhari, in bracket (SAB) or (Pulchritude).”

Tamkar karya juyo haka yake ji, sai kuma yayi tunanin ko tambayar sa zata yi duk da cewar besan me kiran nasa ba? dan yayi imani yau ba zai yi kasuwa a wajan ladies d'in school d'in ba, cikin nuna basarwa ya juya ya kalleta fuskarsa a ‘daure dan karma taga yayi fara'a ya burgeta.

“Pardon?”

Cewar Shamsuddeen yana kallan cikin idanun Afrah, ita kuma ganin yadda ya sanya kwayar idonsa cikin nata sai taji ya sake shiga cikin ranta, cikin yatsina fuska tana tsuke baki tamkar mai shan sweet tace dashi,

“Nothing much! ina son ka zama aboki na please”

Wani ‘kululun abune ya tsaya masa a wuya, hannu yasa ya shafa kansa tare da jan numfashi ya sauke da karfi yace,

“Matan cikin nan duk sun yi miki kad'an wajan yin kawaye shine har sai kin had'a da namiji? Idan na zama abokin ki me zan dinga yi miki ni da nake jinsin namiji kina mace?”

Turo masa baki tayi kamar zata yi kuka, kallanta ya sake yi tsab kafin ya d'auke kai. Sanye take cikin riga da wando ta d'ora jacket a saman karamar rigar dake cikin jikinta, k'afarta sanye cikin takalmi boots ta yane kanta da wani d'an siririn mayafi, tayi kyau sosai domin itama sai gwara kan samari take yi a hanya da kuma cikin makarantar,

“Uhmm! sorry Pulchritude ba karewa suka yi ba, kawai ina so na kulla alak'a mai aminci tare da kai.”

“Ohhh! Na fahimceki, amman nima ina son ki fahimce ni, ni a tsarina yanzu bana son mata su shiga cikinta, dan Allah ki barni kije ki sami wani kuyi abotar, count me out pls..dan girman Allah kiyi hakuri.”

Yana fada ya bar wajan, kallansa Afrah tayi har ya shige cikin hall d'in sannan ta fara k'ok'arin d'aga k'afarta ta bar gurin. Gurin k'awayenta ta koma suka tambayeta yadda suka yi, sam bata nuna musu cewar ya disgata ba nuna musu tayi ya amince da tayin da ta kai masa, Marassha dake gefenta ta kalleta tana murmushin mugunta tare da janyo wayarta tana dannawa tace,

“Afrah ‘karya kike yi wallahi kuma ba zanyi kaffara ba. Idan su kin raina musu hankali toh banda ni wallahi, hmmm! baki da labarin na tab'a nuna masa mu kulla alak’a dashi amman gayen nan sai cemin yayi shi yanzu bashi da lokacin yin wani abokantaka, yayi tafiyarsa ya barni a gurin dan ranin wayyo..”

Karkad'a kai kawai Afrah tayi, sam ba ta son su gane cewar Shamsuddeen ya wulak'antata dan haka tace,

“Toh ai kuwa Allah yayi miki ke kadai domin ni kinsan inada sa'a, kuma kila baki sanar dashi abinda ni na sanar masa ba, kinsan komai na duniya akwai mai sa'a da marar sa'a so ni ce mai sa'a akan Shamsuddeen d'in.”

Da haka duk 'yan gurin suka yi dariya suna jinjina mata da sa'ar siyo zuciyar Shamsuddeen da tayi, sai faman murmushi take yi sai kace abinda ta fada gaske ne, nan kuwa zuciyarta tunaninsa kawai take ta hanyar da zata bi wajan ganin sun kulla abota ta saurayi da budurwa tsakaninsu dan ganin da tayi masa kam ya sake tafiya da imaninta.

•••••••

Mai yakwan su ga Baba Sulaiman ya nufi hanyar jakara, sai gani sukai ya ‘dau hanyar hotoro, Aliya da Fa’iza suka kalli juna, kowa da abunda zuciyar sa take sakaya masa, Amman duk hasashen su bai wuce kawai irin zuwa zasuyi su huta gajia ba, da yamma ko da safe su koma jakara, domin kowannen su akwai abunda yakeson aiwatarwa, Gwaggo Talatuwa kuwa tuni tayi bacci, ba abunda kakeji sai sautin munsharin ta..kurr!

Tunda suka koma gida farin ciki ya wanzu cikin zuciyarsu, sai dai b'angare d'aya dukannansu basa farin ciki da zaman Hotoro. A b'angaren Fa'iza tasan ba zata sake jin koda labarin Shamsuddeen ba bare har ta shiga gidan su ta gaida Umman sa ko zataji wani daddad'an labarin akan mutumin nata, haka yake a sashen Aliya sam ta rasa yadda za'a bulluwa lamarin dan harga Allah an shiga hakkinta ba tasan yadda zata samu wani access najin Sahal ba, gashi ba waya garesu ba daga ita har Fa'iza bare sa samu hanyar jin maganganun abin kaunar su.

Aliya kwance a d'akin gwaggon Talatuwa bayan dawowarsa da sati d'aya taji babu wani labarin zasu koma can jakara,

“Wai Gwaggo dan Allah sai yaushe zamu koma gida ne?”

“Wane gidan kuma? Shi nan inda kike daji ne ko kuma kango?”

Gyara kwanciya tayi rana matsawa gwaggon k'afa, bakinta a zumbure tace,

“Gida ne mana kinji ki, amman ai can gidan ki na jakara yafi dad'i wallahi, gashi kinga yanzu an yanke mana zuwa islamiya.”

Dariya gwaggo tayi tana dukan bayan Aliya, cikin nuna ta da yatsa tace,

“Ja'ira ni zaki yiwa wayo ko? Toh ai duk wayonki kinsan baki kaini ba saboda wadda ta kawoki duniya ma nice na haifeta bare ke. Nasan so kike mu koma can saboda kije gidan su Sahalu ko?toh kisha kuruminki na bashi kwatancen nan gidan da muke ciki nasan zaizo, ai yaran nan nayi masa alkawari zan bashi ke koda babu sadaki, Saboda da yaron
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment