Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

kai ya nanata,

“Ummah na tafi..”

“Toh Abban Mirha tashi zanyi na kai ka da kaina ne?.”

Umman tafada tana daria, Aliya tashiga make kafada tana cuno baki gaba, ganin haka yasanya Shamsudden ficewa yana hararar ta, Dan a matse yake ba kadan ba. Ummah ganin haka ta mike tai dakin ta Aliya ta bi bayanta har tana tuntube.
Kan gadon ummah Aliya ta malale tana sauke numfashi, wannan cikin nata yazo mata da laulayi kala kala ciki harda na kin kusantar Shamsudden tana bashi tough time kafin ta bashi had’in kai sai yayi naci sosai. Ummah ta debi kayan shimfidar ta tai dakin Abba

Shamsudden sai shawagi yake a tsakar gidah. Ta cikin window ya hangi Ummah’ tayi dakin Abba, cikin sauri ya nufi dakinta inda Aliya ke ciki, daga ita sai daurin gaba tana shan fura, tana ganin sa tafara hade rai, kusa da ita ya zauna yana zura hannun sa yana wasa da kirjin ta, sai ture shi take yi yayi biris cikin wata irin murya ya shiga ce mata,

“Thank you for making me feel like the luckiest man in the world every single day. You never cease to surprise me with all that you can do and all that you can achieve. Yet you never make the people you love feel like they need to compete for your time and attention. Thank you for making our married life all that I dreamed it would be. Thank you for filling our home with love and happiness. Thank you for giving me the most beautiful children. Yes saboda unborn dinmu. I love you with all my heart...”

Kalamansa sunyi matukar shiga ranta, kanta ta dora akan kafadar sa, hakan ba karamin dadi yaiwa Shamsudden ba, a hankali ya shiga wasa da albarkatun kirjin ta, daga nan yafara sumbatar koina na jikin ta, salo ya fara canzawa ya jata suka tafi nashi dakin na da, anan suka cigaba da k'ok'arin farantawa juna. Da asubah bayan sunyi sallah, Aliya na kishingid’e a kafadar Shamsudden ta lumshe ido bayan ta karanta anniversary reminder din da wayar ta turo mata, tai wa Shamsudden peck a kumatu kafin tace

“My beloved husband, in all these years by your side you have given me all the joy I could ever wish. Thank you for being always by my side, you are my soulmate and you will always be. I love you a lot, happy anniversary. My king, thank you for another year together. Knowing you and marrying you is my best achievement in life. I want that every year our anniversary becomes the most magical day ever. I love you and I adore you. When they ask me why I love my hubby I don’t even need to answer: my smile says everything. Thank you for making me happy year after year, you are my best finding. I love you!..My best moments are always with you. You are the love story of my life. I don’t know what I would do without you! Happy anniversary my dearest husband, you are my better half and always will!”

“Barkan mu da zagayowar ranar bikin mu habibty na, ♥️ My wife, you are my secret of happiness and success I will never confess. ♥️ You are the woman I dreamed of. The Woman who made our beautiful family a reality. The Woman that gave meaning into my life! ♥️ You can make the clouds go away and paint the sky with the brightest colors of our love! ...”

Haka dai suka shiga karantowa junan su kalamai na soyayya kowannen su yana son yafarantawa d’aya rai, Sosai suke bawa soyayya hakkin ta, Abun dai dai ace TubarkAllah Masha Allah kawai, domin suna baiwa ‘kauna *HALACCIN* ta tamkar cin ‘kwan makauniya.

*BAYAN WASU SHEKARU*

*ABUJA*

EL’ AIS.
(EL’ AMIN INTERNATIONAL SCHOOL)
Ss2b

Ana tashin su Sultan ya nufi kofar ajin su Mirha ya tsaya kamar koda yaushe. Duk sanda aka tashe su shi yake zuwa ajin su ya tasa ‘keyar ta suka shiga mota su tafi gidah. A bakin ‘kofa su kai kicib’is dashi ta zabga masa harara tana cuno baki gaba, Ta ci gaba da magana da Kamal tana ‘daga sautin muryar ta don Sultan yaji.

“Okay Love! Za muyi chat da wayar Mammy later, c...”

Wani tukukun bakin ciki ya sake tokare mak’ogaran Sultan, ransa a matuk’ar b’ace ya janyo hannun ta sukai gaba, batare data ‘karasa magana da sahibin ta Kamal ba. Suna shiga mota ta kwace hannun ta tana nuna shi da ‘danyatsan ta, cikin muryar bada umarni ta shiga kwarara masa bayani cike da tsiwa,

“Several times na maka warning akan ka dena shiga abubuwa na, Wai shin ina ruwan ka da rayuwata? Mai na tare maka ne? Babu damar nai magana da Kamal ko wani namijin sai ka fara yankamin wasu shara’do’di tamkar kai mijina ne, Haba! Shiysa na matsu ka gama makarantar nan ka tafi ko zan samu freedom..”

Tunda tafara masa masifa harta gama bai tanka ba, Sai ma cigaba da driving da yake yi, shi kansa yakan zauna yayi ta mamakin yadda yake tsintar kansa da b’acin ran duk sanda idanuwan sa suka sauka akan Mirha da wani ‘da namiji. Yanzu ma sai tarawa yake yana ‘dibewa akan yadda zai sa a hana ta chatting da Kamal. A k’ofar gidan su Mirha yai parking, dake suba Asokoro suke. Buga kofar motar tai tana jan tsaki akaro na ba adadi. Kallo d’aya za kai mata ka gano ‘y’ar Aliya da Shamsudden ce domin ta d’akko yanayin kowannen su, farar fatar su, hancin Aliya, idanuwan Shamsudden, hancin Aliya, leben Shamsudden, yalwar gashin Shamsudden da dimple dinsa har tsawon sa, yanayin jikin ta kuma da tsiwar ta duk na Aliya ne. Tana gaba yana biye da ita a baya. Girgiza kansa Sultan yayi, jiyo Mirha da yai tana wake waken ta, wanda a fakaice shi take zagewa, yarasa mai yasa wutar son ta take ruruwa a cikin zuciar sa kullum,

_”ALLAH ya tsinewa saurayin cikin dangi (family) kullum a tafe, shekaran jiya yazo, jiya yazo, yau ma yazo, nacacce marar zucia..”_

Sultan yai murmushi kawai, irin Murmushin da mahaifin sa Sahal yakan yi a duk lokacin da idanuwan sa suka sauka akan Fa’izah. Sak kamannin Sahal ya dakko kamar yayi kaki ya tofar, sai yanayin fatar Fa’izah da kuma irin leben Fa’izah. Hannuwan sa cikin aljihu, matashin saurayi ne ‘dan shekaru goma sha bakwai yana ajin k’arshe na makarantar sakandire. sunan Baba Sulaiman yaci suna kiran sa da Sultan. Tun yana yaro ALLAH ya dora masa son Mirha wadda taci sunan Gwaggo Talatuwa. Tun tana zanin goyo Sultan ke sonta, tamkar da soyayyar ta aka halicce shi. Gashi ko sau d’aya Mirha bata taba son sa ba. Kullun cikin gasa masa ba’ka’ken maganganu take. Shi kuwa ko ajikin sa mai yakwan son nata ya ragu’karuwa ma yake yi tamkar ana hura masa wutar son ta a zuciar sa. A bakin kofa suka tsaya tana gaba yana bayan ta, ta danna door bell ba’a bude ba, mutanen naku nacan na bawa soyayya hakkinta a d’aki ko jin karar k’ararrawar basa yi. Mirha ta kara sakin tsaki jin hucin numfashin Sultan a bayan ta. Tana danna door bell tana wak’ar data zamto mata wajibin yin ta a dik lokacin da su kai ido biyu da Sultan.

_”ALLAH ya tsinewa saurayin cikin dangi (family) kullum a tafe, shekaran jiya yazo, jiya yazo, yau ma yazo, nacacce marar zucia..”_

Hannuwan ta ya kamo ya sanya cikin nasa, ya zuba mata idanuwan sa da suka rikide da kallon soyayya, kasa jure kallon sa tayi, ta sunkuyar da kanta a ‘kasa, yai murmushin gefen baki kafin yace,

“Kalli cikin idanu na ki ‘kara maimaita abunda kikace..”

Mirha tai shiru tana kiciniyar kwace hannun ta, sakar mata hannun yayi ya juya ya tafi yana ce mata,

“Matsoraciya...”

Yana tafiya, Aka bude k’ofar. Haj Aliya ce ta bude kofar tana murmushi, Mirha ta yamutsa fuska tana cewa,

“Mami tun d’axu nake danna door bell ba’a bude ba..”

“Toh Mirha idan kana sama ai baka cika jiyo ‘karar bell ba..”

“Ina Baffa? (Shamsudden)”

“Yana sama ya akai..?!”

“Kara zan kai masa Mami.”

“Toh akan menene?”

“Akan Ya Sultan mana.”

Sama tayi, Aliya tabi bayanta. Su Aslam da Islam a parlorn suna kallon cartoon a tashar Nickelodeon. Baby Maheer kuma yana bacci. Kofar ‘dakin baban nata tai knocking yana tsaye a gaban mudubi yana bottling din rigar jikin sa ya dan daga murya jin ana knocking,

“Yes! come in..”

Shiga Mirha tayi Aliya na biye da ita, tana jijjiga Maheer a kafadar ta wanda ya tashi a lokacin da Mirha ke doka kofar dakin Shamsudden. Mirha ta zube a sofa din d’akin tana cuno baki gaba, Shamsudden ya yatsina fuska,

“Mirha menene kuma? Learn to grow up. Yadda kike tabara ko su Aslam ba sayi. Kece fa first born..”

“Baffa! Ko ba Ya Sultan bane..”

“Toh! What about him?”

“Ya takura min da yawa, daya ganni da classmates dina muna hira ta karfi da yaji sai yasa na bar wajen, so suffocating.”

Ajiyar zucia Alhaji Shamsudden ya sauke, cigaba yai da taje gashin kansa dake ‘dauke da furfura kadan ka’dan.

“Baffa baka ce komai ba..”

“Me kike so nace? Sultan first cousin din ki ne, shine babban wanki and again a school senior dinki ne...”

Cuno baki Mirha tayi, Alhaji Shamsudden yai murmushi kawai, ganin bai goyi bayan taba hakan yasa tafice ranta a matukar b’ace. Haj Aliya ta zauna a gefen gado ta kwantar da Maheer tana jijjiga shi dake bacci ya fara ‘daukar sa. Alhaji Shamsudden ya koma kusa da ita yana kamo hannuwan ta duka biyun a cikin nasa yace,

“Habibatee kinji abunda ‘yarki ke cewa..?!”

“Naji Habibee! Bansan abunda ke tsakanin su ba, Amman is like sultan yana son Mirha ko?”

“Babu tantama, soyayyar ta ke ‘dawainiya dashi tun tana zanin goyo.”

“Toh yanzu ya za’ai kenan Habibee?!”

“Taurin kanki ta’dau ka...”

Haj Aliya tayi rau rau da idanuwa tana cuno baki gaba,

“Taurin kai fa kace? Da nayi me to?”

“Tab ai bayan taurin kai harda tsiwar ki, kinsan rannan me na kamata tana cewa dashi?”

“A’a...”

“Wallahi yadda kikasan tasan wannan wa’kar da kike gasamin lokacin yarintar ki, ca take cewa, ALLAH ya tsinewa saurayin cikin dangi (family) kullum a tafe, shekaran jiya yazo, jiya yazo, yau ma yazo, nacacce marar zucia..”

Haj Aliya ta kama baki tana ware idanuwan ta, cikin tsantsar mamaki har tana rawar baki tace,

“Mirhan?!”

“Ita dai, kuma inde ina raye sai na cikawa yaronnan burin sa..”

“Habibee auren dole fa kenan..”

“Auren dole mukai dake?”

“Ka..A.. A’a..”

“Toh koma dai auren dole mu kai koma menene dai idan yabi irin tactics dina na sace zuciar yar muten bunkure, Nasan tabbas Sultan da sannu zai sace zuciar Mirha..”

Haj Aliya ta kyalkyale da daria tana rufe idanuwa,

“Madam a ‘dauramin necktie zan fita..”

“Okay Habibiee..”

Mikewa tayi tana gyara masa necktie din, ‘kasa ‘kasa ta shiga kallon sa, gaba d’aya kishi take ya fita yadda ya ‘kara had’ewa haka, kudi, kyau da wadatar zucia sun sake zama awajen Alhaji Shamsudden.

“Habibty kishin ya motsa ne?”

“Eh! Wanda kake so ai shi kake yiwa kishi. A day without you is like a day without air. I wouldn’t breathe if I ever lost you. Nothing else completes me like you do my love. I love you more than life itself miji na d’aya tamkar da dubu, uban ‘ya’yana, Masoyi na na gaban abadan...”

Peck ya bata a gefan kumatun ta, ya rungumo ta jikin sa yana shak’ar kamshin turaren kayan jikin ta, a hankali ya shiga rad’a mata kalamai masu ratsa zuciya da magudanar jini. Ya ‘kar’kare mata da.

“Habibty kenan, ki sani akan ki na son so, na san menene so, son ki ya koma ‘kauna, wallahi can’t even think about how life would be without you. It almost feels like a sun without rays, a river without water, ground without sand, and a body without a brain. I’m empty without you, my love. Pls karki dena so na, bansan wacce irin kauna nake miki b...”

Bai karasa ba yaji bakin Aliya cikin nasa, Sosai suka shiga kissing juna. Dak’yar ya zare bakin sa daga nata. A hankali tasa hannu ta goge jambakin bakin ta daya mamaye labban sa. Har mota ta rakashi driver yaja shi suka tafi presidency, Saboda shine acting head of service na Nigeria.

MAITAMA
Ganges Street.

Dr Fa’izah ce a hakimce a parlorn ta tana kallon news da ake nuna wa tashar Aljazeera. Sultan ya shiga parlorn bakin sa ‘dauke da sallama, amsa masa tayi tana duban agogon hannun ta,

“Ina yaran?!”

“Ummah wallahi da naje school din teacher dinsu wannan Mr Petter din ya hana a ‘dauke su wai sun fara mid term lessons sai 4:30 za’a ‘dakko su..”

“Wannan mutumin ya cika gadara wallahi, shiyasa nace wa Abban ku idan akai hutu ya canza musu school su koma tasu Aslam. Nagaji da ikon Mr Petter. Ko shi ya haifamin yaran nan sai haka..”

“Abba yana nan?”

“No yana office. Nima clinic zan koma yanzu dama jira nake ku dawo daga school..”

“Oh okay..”

“Ya akai?!”

“No babu komai, kawai tambaya nayi..”

“Okay!”

Mikewa tayi ta yafa mayafin ta dake gefe. Dama a shirye take jiran dawowar su take ta tafi asibitin ta mai suna ‘Faisah Clinic and maternity’.

“Ga abinci can a dinning..”

“Toh Ummah..”

“Yauwa sai na dawo..”

Ficewa tai da mukullin motar ta a hannu, sai jaka mai dauke da tarkacen ta. Zubewa Sultan yayi a kujera yana dafe kansa, gaba d’aya ji yake yi duniyar tana juya masa, son Mirha na dawainiya dashi. Abincin ya caccakuna yai wanka ya fara karatun SSCE/Waec/Neco da zasu fara nan kusa. Lokacin dakkowar su yanayi ya tafi school ya ‘dakko su. Yara ne guda biyu mace da namiji wanda d’aya yaci sunan Senator Sa’idu wanda suke kiran sa da suna Abeed sai macen da taci sunan Ummi mahaifiyar Sahal. Suna kiranta da Ahlam. Daga school din gidah suka dawo a gurguje suka ci abinci suka canza uniform zuwa na Islamiyya, nan suka rankaya suka tafi harda Sultan din.

••••<><>. ••••<><><><>. ••••<><>

Haka rayuwa ta cigaba da garawa. Dare ya zama safiya, safiya ta zama yammaci, Lalle ALLAH mubuwayi ne gagara misali. Cikin haka su Sultan suka kammala makarantar secondary, Mirha ta samu ‘yancin kanta a ganin ta tunda yagama makarantar yanzu babu sauran wata takura. Amma ina takura sai wadda ta’karu ma, kullum shi zaije ya kaita school ya ‘dakko ta, badama ta kula maza gaba d’aya ya hana, yayi kanai kanai a duk lamuranta sai kace mijinta ne yadda yake gurza mata iko san ransa. Kuka da ba’kin ciki suka taru sukai wa Mirha yawa tarasa meyasa babu wanda ke bin bayan ta.

Bangaren Sultan kuwa ya rasa yadda zaiyi ya sanar da mahaifin sa kan cewar bayasan yabar ‘kasar batare da Mirha ba ko da sa ranar aure a tsakaninsu. Sai jinjina yadda zai sanar da mahaifin sa yake, don haka mahaifin nasa na dawowa daga office yaje parlorn sa bayan sun gaisa ya fara zayyanawa mahaifin nasa zancen dake tafe dashi.

“Abba...!”

“Na’am! Me ke tafe da kai? Indai akan maganar zuwa Manchester ne don yin karatun ka kada ka damu, vissa dinka nake jira tafito. Soon zaka tafi..”

“Okay Nagode Allah ya saka da alkhairi. Amman Abba ba abunda ya kawo ni kenan ba”

“Toh Ina jinka..”

“Abbah da...D...d..”

“Idan shiririta ce ta kawo ka tashi ka fita.”

Kasa furta komai Sultan yayi. A daddafe ya mike ya fice saboda ba ‘karamin kwarjini mahaifin nasa yayi masa ba. Komawa dakin sa yayi ya shiga zagaye dakin yana magana shi kadai. Dr Fa’izah ta shiga parlorn Alhaji Sahal hannunta dauke da fruit salad jar. Ajiye masa tayi ta koma ta dakko bowl da spoon ta ajiye a gaban sa.

“Abban su..”

“Na’am Umman su..”

Fari tayi tana tab’e baki,

“Ni dai gaskia kadena cemin Umman su. “

“Nace miki idan kika dena cemin Abban su nima zan cigaba da kiran ki da My Queen kamar sanda muna amarya da ango..”

Murmushi Haj Fa’izah tayi tana ka’da kai,

“Toh My King! Na dena..”

“Yawwa Queen of my heart, ya kinga yaron ki ya fita ko?”

“Sultan ko Abeed?”

“Sultan dai...”

“Meya faru..”

“Shiriritace irin tasa, nasan so yake yai min maganar Mirha amma ya kasa...”

“Toh nace zanwa Sissy magana kace a’a, yanzu sai mu barshi yai ta azabtuwa kenan?”

“Babu ruwan mu kar ai irin ta shekarun baya. Let them settle their selves. Kar muyi using force. Su yiwa zuciyoyinsu HALACCI su dai-daita kan su....”

“Toh ALLAH ya zab’i abunda yafi alkhair..”

“Yawwa yanzu ki kai magana. Alkhairin ALLAH a kullum shi muke bukata. Allah ya zab’a musu abinda yafi mafificin alkhairi a rayuwar su..”

“Ameen ya hayyu ya qayyum...”

Haka rayuwa taci gaba da garawa, Sultan ya rasa mataimaki, ganin kwanakin tafiyar sa zuwa university of Manchester nata matsowa yasanya shi garzayawa gidan su Mirha, wajen Alhaji Shamsudden, Ya fede masa bindi harda wutsiya game da yadda zucia fa gangar jikin sa ke son Mirha. Alhaji Shamsudden ya murmusa kawai yana kara kurbar ruwan robar dake hannun sa. Sai da Sultan ya kai aya sannan Alh Shamsudden yai gyaren murya kafin yace dashi,

“Toh duk naji zancen ka Sultan na kuma san za’ai haka dama, karkayi mamakin kalamai na, abunda nake nufi shine tun ba yau ba nasan yadda kakejin Mirha a zuciar ka, Saboda haka kada ka damu Inn Shaa Allahu Mirha zata zamto mata a gareka, Shekarar ka nawa ne yanzu?!”

“Sha bakwai...”

“For real?”

Sultan ya gyad’a kansa yana murmushi kunya duk ta dubibiye shi, Alh Shamsudden ya gyada kai,

“Nima bana mantawa inaga bazan fi shekarun ka ba sanda nafara son aunty dinka. Kai love chronicles dai kala kala kowanne side son maso wani aka dinga yi/legacy of unrequited love. But Alas Alhamdulillah yanzu komai ya wuce....When zaka tafi Manchester?”

“Possibly next week.”

“Masha Allah! Toh duka duka dai kaga daga kai har Mirhan duk yara ne ku. Bana mantawa I clocked 29 sannan nai aure. So yanzu Inason ka nutsu ka bani hankalin ka nan. Kaje school kayi karatu kamar kowa. Mirha zan hanata kula kowa na maka alk’awarin baka auren ta ko bayan rai na banyadda wani ya aure taba fyace kai...”

Sultan ya sosa keyar sa. Da’di kashe shi za’a bashi auren Mirha. Alh Shamsudden yai murmushi kawai yana tariyo rayuwar sa a baya.

“Nagode Baffa. Allah ya saka da alkhairi..”

“You knw what? I think zamu daura auren ku kawai, Shekara nawa zakai acan? Cux Mirha dai anan nakeso tayi karatu ko kafi son ta a kusa da kai.”

“Petrochemical engineering ne Baffah! Amma Abba yace sai nayi har master kafin na dawo..”

“It shall be well In Shaa ALLAH! Kaga by then itama tagama first degree d’inta..”

“Toh Baffa..”

“Yauwa kada ka damu Sultan kayi concentrating akan karatun ka kawai. Insha Allah Mirha zata zamto mata agare ka..”

Godia Sultan ya shiga yiwa Alh Shamsudden sannan sukai sallama ya fito zai tafi gidah, sai cilla mukullin motar sa yake yana cab’ewa. School dinsu Mirha ya wuce ya dakko ta sai zumb’urar baki take yi, tana nacacciyar wakar da take zagin sa fakaice wannan karon harda ‘karin maganar,

_”ALLAH ya tsinewa saurayin cikin dangi (family) kullum a tafe, shekaran jia yazo, jiya yazo, yau ma yazo, nacacce marar zuciya. Allah ya raba mu da sharrin cousin mai raba soyayya yasa ayiwa mutum auren dole.._”

Banza yai da ita har suka karasa gida, tasa hannu zata bude kofar taji ta a kulle,

Harara ta galla masa cikeda tsiwa tace,

“Malam bude min kofa zan fita..”

“This should be the very last time da zaki ‘kara zagi na agaban idona, wallahi Idan kika kara sai na gayawa su Baffa.. So behave like a lady and stop those annoying childish behaviors. Fita zan wuce gidah...”

Mamaki ne ya mamaye ta dama sultan zai iya maida mata martani? Ta bude murfin motar zata fice yace,

“Oh daga yau ba zaki sake gani na ba, zan tafi karatu Manchester. Thanks for everything madam Mirha..”

Haka kawai Mirha taji abu ya soke ta a kahon zuciar ta. Sai taji gaba d’aya ba kuma tasan ya tafi. Harara ta galla masa,

“Daga can ka shallara can. Who cares..”

“Thanks..”

Tana ficewa ya taki motar a guje ya barta da ‘kura. Cikin sanyin jiki ta shiga gidah gaba d’aya bata da walwala. Tarasa mai yasa take jin wani al’amari na daban. Ni kuwa nace Mirha dama wani lokacin zazzafar k’iyayya ai tana komawa soyayya * I was once a victim😹*. Haka dai kwanaki nata shudewa har Sultan ya tafi school. Driver ya cigaba da kai Mirha school. Alh Shamsudden yasamu Alhaji Sahal da maganar yaran nasu. Sun tattauna cikin lumana suka tsaida lokaci kan Idan Mirha ta kara girma tunda yanzu tana cikin shekarun 14/15 Sultan kuma yana 17/18. Idan sun kara tasawa kowanne ya mallaki hankalin kansa sai ayi auren. Bayin Mirha tagama secondary anan Abujan tafara university tana karantar Banking and finance. Har ta gama karatun ta sultan bai dawo ba. Gashi kuma zazzafar soyayyar sa ta mamaye ta batai mata shigar sauki ba. Takan yi kuka mai tsuma zucia a duk lokacin data tuna irin yadda take yanka masa rashin mutunci sala sala. Bayan tayi bautar ‘kasa tadawo tafara serving anan central bank of Nigeria dake Abujan. mahaifin ta Alh Shamsudden ya tunkareta da maganar zai yi mata aure da ‘dan aminin sa tunda duk ta kore samarin ta. Mirha ta dire tsallen albarka tana ro’kon sa kan ya bata time zata fa’di wanda take so. Alh Shamsudden yace a’a. Ta tunkari kowa da maganar akai biris da ita. Ranar jumu’ah aka tsaida ranar da za’a daura auren ta da Sultan wanda a ranar ya dawo ya sami labarin ba karamin da’di yaji ba. Ya sake gogewa ya zama cikakken saurayi wanda keji da tashen samartakar sa. Gidan su Mirha ya nufa luckily babu kowa a parlorn sai Mirha dake rusgar kukan an mata auren dole da wanda bataso ba kuma tasan waye ba. Tana ganin sa ta shagala da kallon sa, ya wuce ta ya zauna akan kujera bayan yayi mata wakar da take zagin sa a lokacin yarinta ya kar’kare da,

“Congratulations Cousin! I heard za’a daura miki aure yau, ALLAH ya..”

Cikin rawar jiki da baki ta nufe shi ta tsugunna a gaban sa hannuwan ta biyu ta daga tana neman gafarar sa,

“Pls Ya Sultan ka taimake ni wallahi ALLAH babu wanda nakeso yansu sama da kai, pls ka samu su Baffa da Abba da Aunty kuyi magana wallahi tallahi yanzu kai nake muradin so na aura.. *KAI MIN HALACCI* ka temaka kasa a aura maka ni, wallahi Ya Sultan, this is my vow to you today. I’ll be your lover, I’ll be your friend, I’ll love you like no other till the very end, this heart belongs to you forever. I love you way too much. Pls *KAI MIN HALACCI* ka temaka ka karbi kokon barar soyayya ta..”

Sultan ya yamutsa fuska yana tab’e baki, hannuwan sa cikin aljihu ya fice ya barta a gurfane tamkar me neman gafara, Mirha taci kuka ta koshi rana d’aya jal aka cancada biki babu ango, Sosai Mirha ta rame ta kwanjale aka kaita gidan angon ta, taci kukan nadama da dana sanin abubuwan da ta aikawata Sultan a baya ganin yanzun an aura mata wani daban, sai wajen goman dare ya shjga gidan da ledojin gadon da kowanne ango ke kaiwa amaryar sa, Banda ango dan haru-haru na labarin *HAR ILA YAU NI CE TAKA* da yajefi amaryar sa da ledar awara guda hud’u. Cikin Sanyayyar muryar sa sultan ya shiga dakin yana kare masa kallo. Sautin kukan Mirha ya ‘karu na jin angon ta na sallama. A gabanta ya tsugunna yana yaye mayafin kanta,

“Sugar pie..”

“Ya..Ya sultan kai ne an... Kai ne mijin da aka daura mana aure dashi”

Sultan ya jaddada kai kafin ya janyota jikin sa cikin rada ya shiga labarta mata komai ya kar’kare da,

“Getting to know you felt like a class about how angels operate because, in the real sense, you are angelic in every aspect. Thank you for calling me yours and for accepting me for who I am, with all my imperfections. In you,
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment