Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

bakinta na kyarma tace.

“Idan na yarda cewar baki san waye Muhamman S ba, amman na tabbatar kinsan Shamsu ko? No wonder idan mukaje gidan aunty Yagana kike guduwa can gidan su ashe ya dawo gurinsa ma kike zuwa. Kin bani mamaki Fa'iza ban tab'a tunanin zakici amanata ba sai kwanan nan, ashe zaki iya son wanda nake so?(Sahal) ashe zaki iya lallab'awa wajan wanda yace yana sona nace a'a har ya lekani a bayi?(Shamsuddeen), kije ku fara soyayya dashi. Kin bani mamaki Fa'iza, sai yanzu kika nuna min true color d'inki. Wallahi tallahi Fa'iza bazan iya auran wanda nasan akwai abu a tsakaninku ba Saboda zan dinga ganin tamkar ban miki HALACCI ba, ashe ke bazaki iya ba, na gode sannan karki sake kirana da Sissy d'inki kije can ki nemesu.”

Ba k'aramin mamaki Fa'iza ta shaba jin yadda Aliya taji labarinta da Shamsuddeen sai dai kafin ta tambayeta tuni ta fice. Umma ta tarar a kitchen ta fito d'auke da abinci zata kaiwa gwaggo ganin yamma tayi tana had'a mata kayan shan ruwa.

'”A'ah! Aliya kin dawo?”

“Uhmm..”

Tayi a shake saboda ma ba zata iya yi mata banza bane yasa tayin hakan amman gabaki d'aya gidan haushinsu take ji.

“Toh sannu, amman mai yasa kika fita d'azu baki yiwa kowa sallama ba Aliya? yanzu haka ake yi kibar gida tun asubar fari babu wanda ya sani?”

Batace komai ba tayi shiru kanta a kasa zuciyarta nayi mata zugi dan yanzu sam bata kaunar fad'a ji takeyi tamkar an tsaneta a duniyar komai yayi mata zafi, ganin tayi shiru yasa Umma girgiza kai tare da wucewa ita kuma ta d'auki bucket taje ta d'ibi ruwa ta shiga toilet. Tajima a ciki kafin ta fito ta wuce d'aki lokacin Fa'iza na zaune ta gama kiran Shamsuddeen amman bai d'aga ba da alama baya kusa da wayar gashi so take ta tambayesa ko sun had'u da Aliya amman bai d'aga ba har gashi ta fito daga wanka. Mai ta d'akko ta fara shafawa ba tare da ta kalli inda Fa'iza take ba dan yanzu duk duniya babu wanda Aliya ta tsani gani irin mutum uku (Fa'iza, Sahal, Shamsuddeen) gashi sun zame mata karfen k'afa da dole sai tayi mu'amula dasu koda babu kyakkautawan kalamai tsakaninsu, har gara Sahal shi ba zata dinga ganinsa ba sai dai idan zuwa yayi gidan.

“Sissy dan Allah kizo kici abincin nan rayuwa fa bazata tab'a yiyuwa babu cin abinci ba.”

Bata kulata ba har ta gama shafa man sai faman rintse ido take yi saboda wani irin azababban ciwon kai da yake sara mata ko sunkuyar da kan batason yi. Kaya tasa marasa nauyi sannan taje tabi lafiyar gado ta d'an huta wai kafin a kira sallar magariba.

“Sissy dan...”

“Dan Allah ki rabu dani kiji da rayuwarki kema please.”

“Amman Si...”

“Nace ki dena kirana da wata Sissy d'inki bana so, domin da ace ni d'in shak'ik'iyar 'yar uwarki ce da bazaki min wad'annan abubuwan ba. So ki kirana da sunana Aisha ko Aliya.”

“Bazan ce Aishan ba Sissy zance idan yaso idan na kiraki karki amsa, kuma sannan ni ban san cewar Muhamman S shine Sahal ba sai daga bayan nan, kuma bari kiji na gaya miki ni bama son shi nake yi ba shine yake faman takura min akan dole sai na soshi.”

Wani bakin ciki ne ya sake tokare wuyan Aliya ta runtse ido tare da cewa.

“Naji baki san Sahal shine Muhamman S, amman Shamsu kuma fa? Ko shima baki san abinda yake tsakanin mu a baya ba?”

Anan kam shiru Fa'iza tayi saboda sarai Aliya ta fita gaskiya amman soyayyar da take yiwa Shamsu bawai ta yanzu bace, jin yadda tayi shiru ne ya sake b'atawa Aliya rai wacce ke kwance jikinta har ya fara zafi ga tsananin ciwon uwa uba yadda damuyoyi suka taro suka yi mata yawa har ta rasa yadda zata yi dasu. Jikinta na tsuma irin na wanda zazzabi yake son ya rufe shi tace da Fa'iza.

“Idan har kinsan ba soyayya kuke yi da Shamsu ba, toh karki sake yi masa magana bare wani abun ya had'a ku, har yanzu bana son shi kuma abinda yayi min bazan yafe masa ba dan har wannan lokacin image d'in abin baya ya kasa goguwa a cikin kwakwalwata. Na sani ya soni a baya kuma ya hidimta min da kudinsa ta yadda ko had'uwa muka yi dashi a wani gurin indai abu na kud'i ne to shine yake biya. Ina so kidena kulashi domin hakan ma zai dinga janyo min wulak'anci a gurinsa.”

Tunda Aliya ta fara maganar cewar Fa'iza ta rabu da Shamsu, Fa'izan ta dinga jin zuciyarta tana wani irin tsalle saboda tsabar tashin hankali, ba zata iya rabuwa dashi ba koda kuwa zata rasa duk wani abu a duniya. Sam bata shirya rabuwa dashi ba dan a yanzu ne ma taji sabuwar kaunarsa tana kuma huda duk wani b'argo da yake cikin jikinta.

Jin Fa'iza tayi shiru yasa Aliya juya mata baya ta kuma curewa cikin bargonta tana zubar da hawaye, bawai son Shamsuddeen take yi ba tana son ne saboda ita Fa'iza tayi mata Halacci ta dena kula Shamsu amman taga alamar ba zata yi mata ba. Ana kiran sallah Aliya ta sani ta sakko daga kan gadon da kyar saboda tsananin ciwon kai, taje tayo alwala sannan ta wuce dakin gwaggo tayi sallah ta kuma hayewa gado tana kuka dan shine kawai take yi taji ranta yana sassautawa. Gwaggo da ta idar da sallah ta juya tana kallon Aliya wadda tana jiyo shashekar kukanta tace.

“Aliya lafiya kike kuka?”

“Gwaggo kaina.'”Ta fad'a da kyar cikin kuka,

“Toh Subhan’Allah!, kinsha magani?''

Tayi shiru saboda idan tayi maganar ma ji take tamkar zata mutu, abubuwa sunyi mata yawa zuciyarta gab take da bugawa ko ‘konewa dan abinda Fa'iza take shirin yi mata yafi komai d'aga mata hankali akan rabuwa da Sahal da su kayi. 'Mai yasa Fa'iza zata yi mata haka? Daman zaman amana zama na mutuntaka zama na 'yan uwantaka bayasa ka yiwa d'an uwanka HALACCI? wannan tsananin damuwarki da mamakin sune suka haddasawa Aliya shiga cikin wani yanayi wanda ya d'agawa gwaggo hankali ta fito tsakar gida tana kiran mutanan gidan cikin tashin hankali.

“Gwaggo lafiya?” Cewar Umma hankali a tashe.

“Kuzo..kuzo muje Aliya nacan zata mutu.”

“Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un mutuwa?!”

Suka had'a baki wajan yin furucin tare da d'unguma su nufi d'akin gwaggo hankali a tashe. Suna shiga Umma ta yaye bargon da Aliya ta rufa dashi nan suka tarar idanunta a kafe hannayenta a dunkule kamar wadda take b'oye wani muhimmin abun da bata son a gani. Suma tayi nan Umma ta janyo ruwa a gefenta ta shiga zubawa a jikin Aliya amman abu yaki yi sam taki dawowa normal, jikin Fa'iza banda rawa babu abinda yake yi, ita kanta hawaye take faman yi, ganin Umma ta rasa yadda zata yi shine yasa Fa'iza yin k'arfin hali wajan hawa gadon ta sunkuya saitin fuskar Aliya tare da rintsa ido ta had'e bakinta dana Aliyar a guri d'aya tana faman hura mata iska a ciki, hannu d'aya kuma ta toshe hancin Aliyar haka ta dinga tattaro numfashinta tana dureshi a bakin Aliya.

Tsawon lokaci ta d'auka tana yi amman shiru hakan yasa ta d'agowa tare da fashewa da wani irin kuka mai tada hankali. Ganin haka yasa Umma fita da sauri daga d'akin taje ta d'auki wayar ta tare da kiran Baba Suleiman, wanda yake can majalisa suna ta hira da abokinsa. Yana jin abinda matarsa ke fad'a yayi saurin tashi ya taho gida, can kuma suna ta fama sai da kyar dan harsun fitar da rai cewar Aliya ta mutu sai kuma sukaji ta sauke wata babbar numfashi tare da fashewa da kuka kai dakaji kasan cewar irin na marayun nan ne....

*MUHAMMAD SAHAL*

Janye yake da yar jakar sa, wadda ba ba zata ci kaya da yawa ba, Gaba d’aya ya zabge ya rame, farar fatar sa ce kawai takara haskawa hancin sa ya ‘kara fitowa, tamkar dai an canza masa halitta, Sanye yake cikin ‘kananun kaya. Samfarin jeans da long sleeve riga shud’iya, takalmin sa da agogon sa duk kalar kayan jikin sa ne, Sai tashin ‘kamshi yake yi. A parlor ya tarar da Ummi da itada Husnah suna kallon wani Indian drama series. A hannun kujera ya zauna yana kallon agogon sa, A hankali yace.

“Ummi zan tafi..”

“Har zaka tafi Sahal? Gashi baka gama watstsakewa ba”

“Eh Ummi gwara na tafi, Uncle yace idan naje zamuje embassy din da sukai magana da Baffa (Baban su)..”

“Okay toh shikenan! Allah ya temaka ya bada sa’ar abunda akaje nema.”

“Ameen Ummi..”

“Ka dai ‘ki ka fadamin abunda ke damun ka ko?”

‘Keyar sa ya shafa, yai murmushin gefen baki, ya mike ya rataya jakar sa yana cewa,

“Kakki damu Ummi! kawai addua zaku tayani da ita, Allah ya bani nasara akan abunda nake muradin samu!”

“Allahumma Ameen, In Shaa Allahu kuwa zamu tayaka da yi.”

Husnah dake gefe tayi murmushi kawai tana kallon Sahal. Har mota ta rakashi tana sake bashi baki akan maganar su Aliya da Fa’izah! Basu jima suna tattaunawa ba driver yaja shi su kai airport. A mota ya shiga tsarawa Fa’izah text message da,

“Assalamu alaikum Ya Rouh..💕
I have shown you what an idiot I can be by making that mistake. Now it is your turn to show me what a darling you can be by giving your anger a break. I am sorry. Just like the words I Love You, the value of the words I Am Sorry too does not decrease no matter how many times they are said or repeated. I am sorry. I know you’re angry but I want you to think about all the beautiful memories, that have made us believe that we’re meant to be. I am sorry. The homepage of our relationship cannot be currently displayed because of a server error. Can we please click on the refresh button and start over again? I am very sorry habibty😘KI MIN HALACCI! Ki karb’i ‘ko’kon barar gafara ta, har gaban abadan ba zan ‘kara kamanceceniyar hakan ba, Na tuba ki yafemin Fa’izahhh naaa🥺..”

Yana gama rubutawa ya tura mata, ya kwantar da kansa a kujera yana tunanin kuskuren daya aikata, kila da’ace baiyi toying da zuciar Aliya ba, watakila da tuni sun dad’e da yin aure shida Fa’izah, Har suka ‘karasa airport bai dena tunani ba..

*ABUJA*
(Apo)

*Senator Sa’idu Abubakhar Residence*

Muhammad Sahal bai jima da zuwa ba aka kira sallar isha’i a masallaci, A tare suka halarci sallar shi da kawun sa Uncle Sa’idu. Bayan an idar suka dawo gidah aka shantake hira, Kawu Sa’idu ya dubi Sahal yace dashi,

“Moha S (muhammad Sahal) yana ganka haka? Duk karame meke damun ka haka?”

Sahal ya shafe ‘keyar sa yana ‘karasa had’iye fruit Salad ‘din bakin sa,

“Na ‘danyi zazzabi ne kwana biyu shi yasa ma ban dawo last week ba.”

“Ayyah Allah ya ‘kara maka lapia, Nace maganar wajen aikin nan zuwa Monday In Shaa Allahu sai ka fara zuwa, Dan sunyi ta tambayata kai nace zaka zo ne cikin wannan watan.”

“Okay to Uncle! Nagode Allah ya saka da alkhairi..”

“Ameen Ya Rabbi, Nan ba nisa a Lokogoma yake embassy ‘din, zaka ga sabo nema, sunce Envoy ‘din su dake wakiltar su shima ‘dan nigeria ne someone in person of ko Shamsudden something dai nake jin bahaushe nema, kaga kuwa it shall be well In shaa Allah..”

“Okay Allah ya dafa mana, ya sunan embassy ‘din..?”

“SWITZERLAND EMBASSY.....”

_*KAI MIN HALACCI......!💕_*


_*NA_*


_*_MISS XOXO🧕🏼_*_


_*WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE, DOMIN SIYAN SHI KO ZAFAFA BIYAR DUKA KU TUNTUBI: +234 803 081 1300_*

_*44B_*

Tunda ta shiga d'akin Fa'iza tayi mata sannu da zuwa ta amsa sama-sama, jakar hannunta ta saqale sannan ta cire mayafin jikinta ta ninke tare da yin shirin wanka. Har yanzu jikinta kamshi yake amman tsabar cin mutuncin Shamsudden yace wari take yi, banda ma idan ta dena turara jikinta ita kanta ba zataji dad'i ba ai da dena sawa zata yi ta yadda zaiji warin jikin nata sosai. Gabaki d'aya taga alamun rashin mutunci kawai yaje ya koyo a can Switzerland d'in da kuma k'aryar banza amman banda wad'annan abubuwan bataga abinda yaje ya koyo ba. Kilama loan yaje ya karb'o yazo ya gina wannan uban wajan har yake wani yi mata fiffik'ala yana kiran kansa da CEO.

Kamar ta yiwa Fa'iza maganar yace zasu fara soyayya sai kuma ta share a ganinta bata cancanci zama a tsakaninsu ba kartaje tayi irin abinda Husnah tayi mata akan Sahal ta dinga cewa ai yana sonta kullum idan tazo ta tafi ya dinga maganar ta ko kuma idan an kawo abu sai yayi saurin d'aukar mata ashe shi duk ba soyayyar aure yake mata ba, sone kawai irinna mutuntaka. Shirin wanka tayi ta nufi band'aki tana wanka tana share hawaye, babu abinda take tunowa irin iyayenta, tana jin inama ace Allah ya bar mata guda d'aya a ciki uwa ko uban ta yadda itama zata gansu tasan yes sune silar zuwanta duniya. Har ta gama ta fito bata dena tunani ba, gashi har zuwa wannan lokacin ta kasa cire Sahal a cikin zuciyarta duk da kullum tana addu'ar Allah ya cire mata shi dan bata son ta auri mijin da ba ita yake tunani ba watace can daban.

A haka rayuwa taci gaba da garawa sam tsakaninta da Shamsuddeen a office hantara ce da wulak'anci tun abin yana damunta har ta fara jin gara ta nuna masa cewar itama fa zata iya dan haka yau data shirya kaya tasa riga da skirt na atamfa sun yi mata kyau kirjin nan ya matse dalilin pin da tasa kasan cewar Umma bata matse musu kaya sosai, yau kam da yake tana cikin son b'awata oganta shima rai sai tasa pin daga bayan rigar ta tattaro shi ta matso yadda shape d'in boobs d'inta ya fito. After dress dinta ta dora sannan ta yane kanta da mayafin rigar. Red d'in janbaki tasa kasan cewar akwai red a jikin atamfar sannan ta rangad'a kwalli a cikin idanunta ta d'auki jakarta Fa'iza na kallonta wacce ita kanta sai da gabanta ya fad'i dan ba karamin kyau Aliyar tayi ba. Tana kallonta ta fita ji take tamkar ta hanata zuwa dan tasan dole yau Shamsuddeen yaga Aliyan zata so a ce itace a matsayin sakatariyarsa amman ya zata yi? Sai hakuri dole.

Jikinta a rufe yake hakan yasa ba ta samu tsaiko ba a gurin Umma ta yadda za'a hanata fita da kayan, suka yi mata sallama mai napep d'in da Baba Suleiman ya samar mata tuni yazo yana jiranta a k'ofar gida, taje ta hau suka tafi. Yau kam ta riga shi zuwa kuma tana shiga ta fara shirya masa meeting wanda ta riga ta sanarwa da wad'anda suke son yin meeting d'in dashi cewar gobe suzo zai gansu shine kawai bata gayawa cewar yana da meeting yau ba, wanda tayi masa hakan ne cewa son nuna mata ya kaita makura abinda yake yawan yi mata sun isheta tunda ya hana a bata resignation letter. Duk abinda tasan yana buk'ata tayi masa hakan yasa ta koma b'angaren ta taci gaba da aikinta har Allah ya kawo shi. Daman tana zuwa ta yaye labulayen da suka yi shamaki tsakanin su ya zama zata iya ganinsa shima zai iya ganinta sannan.

Yana zuwa kuwa ya wuce office sam bai kula cewar ta bud'e labulayen ba kawai zuwa yayi ya zauna akan kujerarsa tare da fara duba documents d'in dake ajiye yana bubbudewa, mik'ewa tayi dan zuwa ta gaidashi kamar yadda ta saba amman sai da ta sake feshe jikinta da turare kafin ta bud'e gaban after dress din nata ta d'auki wani file wanda ta gama aikinsa yanzu ta shiga office d'insa bakinta dauke da sallama. Bai d'ago ba saboda idanunsa suna kan file d'in meeting d'in da bai san za'a yi ba, ransa a b'ace duk da kamshin turaranta da yake dukan hancinsa, ji yayi tana cewa.

“Good morning sir.”

A hankali ya d'ago file d'in tare da d'ago idanunsa yana watsa mata wata wahalalliyar harara, amman mai?sai idanunsa suka yi kuskuran sauka akan kirjinta wanda a lokacin ta sunkuyo tana mik'a masa file d'in dake hannunta tana motsa baki tamkar mai tsotsar candy milk.

Dire masa tayi tare da komawa tsaye tana kwararo masa bayani, shi kuma sai faman kallan file d'in yake yana mamakin yanayin shigarta yau. Wato tana cikin rufin asirin suturarta kullum tana zuwa a mutunce yau gashi ta nuna masa cewar itama fa ta iya irin shigar da yake tunanin itace wayewar. Wani koren miyau ya had'iye tare da tura hular kansa zuwa gaban goshinsa yayi baya ya jingina bayansa da kujerar ya cilla mata file d'in hannunsa tare da cewa.

“Wannan kuma?”

Tayi tamkar bataga file d'in ba tana ta faman yatsina fuska ta kuma jin ya bugi tebur d'insa yana cewa.

“Bakyaji ina miki magana?”

“Sorry sir, me kace?”

“Nace wannan wane meeting ne da tun jiya baki sanar min ba sai yau dan tsabar kin rainani ko?”

“Sir ba haka bane wallahi, tun jiya na harhad'a da wad'anda na kawo maka, ashe shi ban hado dashi ba sai yau dana zo na ganshi, gashi meeting d'in k'arfe goma ne na safiyar nan.”

Tana maganar ne tamkar zata saki kuka hakan yasa jikinsa yin sanyi ya d'auka da gaske take yi kukan zata yi, yaja tsaki tare da sauke numfashi yana rintsa ido, ba tare da ya bud'e idon ba taji yace mata.

“Ina my Faizaah? Hope tana lafiya?”

Aliya ta dauke kai ba tare da ta bashi amsa ba domin ba aikin da ya kawo ta ba kenan, cikin rashin ko inkula d'in maganarsa da yayi tace dashi.

“Sir, idan babu wani abun zan koma site dina saboda masu son ganina.''

Mai zai yi mata bayan gabaki d'aya ta bata masa tsari, so yayi yau da ya gama rage duba wasu files d'in yaje ya gano filin da yasa aka siya masa wanda nan gaba zai yi gidan mai a wajan, shine dan tsabar iskanci ashe akwai meeting d'in da dole sai ya halarta gurin amman bata sanar dashi ba. Dan haka yayi mata alamar ta tafi da hannu ba tare da yace mata komai ba, ita kuma ta tafi tana yin kamar mai ciwon k'afa harta fice. Office d'inta ta koma kafin ta zauna sai da ta cire after dress jikinta ta sagala jikin kujerar ta sannan taci gaba da aikinta, da yake suna iya hango juna hakan yasa Shamsuddeen juyowa zai harareta kawai ya hangota ta cire after d'in farar fatar hannunta ta bayyana, bai san lokacin da ya zabga tsaki ba shima yaci gaba da aikinsa.

Wajan karfe tara da rabi ya mik'e ya tattara abinda zai d'auka yasa a cikin brief case d'insa sannan ya fito daga office d'insa, har zai wuce sai kuma ya shiga wajan Aliya tana zaune gefenta lemon smoov chapman ne da alama sha take yi kawai ya shigo, nan d'in ma still idanunsa akan kyakyawan kirjinta suka sauka ya tab'e baki tare da cewa dan yaga kamar bataga shigowarsa ba yace.

“Ke! Nan fa ba club bane da zaki dinga yin duk irin shigar da kika ga dama ba, sannan kice zaki zauna yadda kike so. Malama ki d'auki rigarki kisa saboda karkija wani d'an iskan yazo ya danneki kice nine dan ni a yanzu baki kai matsayin da zan rab'eki ba”

Tunda ya fara harya dire bata d'ago ba sannan bata da niyar saka rigar, ganin haka da yayi ne yasa shi buga tsaki tare da furta.

“So intolerable.”

D'agowa tayi ta kallesa domin a duniya ta tsani taji ya fad'i wannan kalmar, sai taji tamkar dan ita yake fad'a hakan yasa cikin rashin damuwa tace masa.

“Bansan wace irin shiga kake son nayi ba sir, ina yin ta mutunci kace ina wari, kullum sai nasaka abubuwan kamshi na kaya dana jiki dana wanka dana wanki, amman still baya hanaka idan kazo kace min ina d'oyi, shi yasa daga yau zan fara yin irin wannan shigar har zuwa lokacin da zan bar maka office d'inka ba kuma zaka sake ganina ba daga lokaci. Dan Allah ka dena yi min fatan wani ya ganni har yazo ya cuce ni dan idan hakan ta faru toh kaine sila saboda baka tayani kare mutuncin kaina ba a matsayina na wacce take karkashin mulkinka”

A tunanin Aliya maganarta ta shigesa amman sai gani tayi ya juya yana tafiya yana cewa.

“Nidai na gaya miki karki sake yin irin wannan shigar kizo min office.”

Bayansa tabi da kallo kamar ta bishi da gudu ta kwad'a masa mari, amman babu dama dole tanaji tana gani yayi ficewarsa tabisa da harara ba tare da yasan tana yi ba. Shi kuwa Shamsuddeen gurin meeting d'in ya nufa ana gamawa ya dawo amman ya tarar bata nan sai wani ya gani, da ya tambaya sai aka shaida masa cewar ta tafi gida kakarta batada lafiya. Kafad'a ya d'aga alamar ko'ajikinsa saboda tsabar jin haushin gwaggo da yake yi bai san bama ita ake nufi ba inna tacan bunkure itace aka aiko tana neman Aliyar akan taje saboda batada lafiya gashi sai kiran sunan Aliyar take shine aka zo tafiya da ita.

Cike da tashin hankali Aliya ta shiga cikin gida anan ta tarar da Sabitu wanda yazo tafiya da ita, aikuwa hankalinta ya kuma tashi dan ba karamin kaunar kakannin nata take yi ba. Da ita da Humaira kanwar Fa'iza suka tafi, tun a mota gaban Aliya yake yawan bugawa ta dinga addu'a har suka karsa cikin kauyen nasu. A lokacin rai yayi halinsa domin inna Adama Allah yayi mata rasuwa, sanadiyar amai da gudawa a safiyar yau d'in nan.

Aliya taci kuka bata tab'a zaton zata yiwa tsufaffin nan kuka ba duk lokacin da aka ce mata ta rasa wani a ciki, sai gashi tana kuka tamkar yaune iyayenta suka rasu. Tasha kuka haka aka dinga rarrashinta, cikin lokaci k'ank'ani harta kuma zugewa sai uban idanuwa kamar ana sake janyo mata su. Toh su Baba Suleiman basu samu damar zuwa a ranar ba sai washe gari suka zo da Umma dasu uncle Bashir kanin Baba Suleiman da sauran 'yan uwan mahaifiyar Aliyan duk sun zo. Ranar uku Fa'iza ta samu damar zuwa lokacin Umma ta koma daman an barta ne saboda yara kar a tafi a barsu babu wani babba mai kula dasu. Anan ta zauna gurin Aliya dan ba karamin tausayi take bata ba saboda ta sake zama so silent sai hawaye da sukan zubo mata jefi-jefi, gashi ko abincin kirki bata iya ci sai dai fura da nono suma kad'an take samu tasha.

**** *****

Yazeed ne ya shiga office d'in Shamsuddeen hannunsa rik'e da waya ya kara a kunne yana magana fuskarsa na nuna alhini, zama yayi akan kujera yana cewa.

“Ayya sorry Aliya Allah yayi musu rahama, ke kuma ya baki hakurin rashin su, ga oga zan baki yayi miki gaisuwa.”

Yayi maganar yana mik'awa Shamsuddeen wayar ita kuma ji take kamar tace ya barshi sai ma ta jiyo Shamsun yana cewa.

“Wazan yiwa gaisuwa?”

'”Aliya ce ashe kakarta ce ta wajan uba ta rasu, ungo kayi mata gaisuwa.”

“Oh ai naji rasuwar tun a ranar na kuma ce Allah yaji k'an rai no need sai nayi a wayar ta.”

Wata harara Yazeed yake jifansa da ita amman hakan bai sanya shi karb'a ba, haushi da kunya suka sanya Yazeed d'in katse kiran yana mik'awa tsaye yace.

“Ka bani mamaki wallahi dude, ashe kai karamin yaro ne ban sani ba? Mutuwa tafi k'arfin duk wani wulak'anci da zaka yiwa Aliya duk abinda tayi maka kuwa, kuma zan yi mata alfarmar da ta nema a gurina na maida ita cafe idan yaso idan ka tashi kurarta saika had'a dani, na barka lafiya”

Yazeed yayi ficewarsa dan Shamsuddeen bai tab'a masa rai ba tunda suke sai yau, yaci ace duk abinda Aliya tayi masa ya hakura tunda shi namiji ne kuma namiji da hangen nesa aka sanshi amman ace wai common gaisuwa bazai mata ba saboda kawai tayi masa abu tun yarinta, gashi abun bai fito a goshinsa ba bare kowa ya gani shi kansa da suke tare tsawon lokaci har yau bai san abinda tayi masa ba saboda yaki sanar dashi amman shine ya zauna yana wani kullatar yarinya. Koda ya fita text message ya tura mata na ban hakuri akan abinda ta jiyo Shamsun na cewa, bata ce komai ba lokacin da ta karanta haka ma bata yi reply ba taci
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment