Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

da mahaifiyar ta, kullum fatan ta Allah yasa kar Shamsu yaki yadda da zab'in nan da take tattala masa, sannan ba ta son tayi masa dole saboda kar yaje ya cuci yarinyar mutane, har Allah ya kamashi da laifi.

B'angaran su Aliya kuwa, is cikin satin Baba Suleiman yai ciku-ciku ya samarwa Aliya da Fa’iza makarantar kwana a sumaila ta gwamnati, Wadda ke unguwar k'ofar gabas ‘yadi’ dake sumaila. (Government girls senior secondary school sumaila..), babu wanda yayi farin ciki kaf cikin su, dan da kuka da komai Gwaggo Talatuwa ta had’a 'yan kayayyakin da zasu buk'ata da wanda Baba Suleiman ya kawo, da wanda mahaifiyar Fa'iza ta kawo musu duk ta gark’ama musu a cikin akwatin k'arfe, Fa’iza sai zunduma kuka take yi, ga haushin Aliya da ya cika mata ciki domin duk itace taja musu zuwa makarantar kwana. Aliya kuwa ‘kwa’kwalarta ce ta dena aiki saboda tsabar takaici da bakin ciki, ganin dagaske dama Baba Suleiman yake yi? Gashi nan harda takardar transfer ta tsohuwar makarantar su ya karb’o, gashi ba zata iya rashin Sahal a kusa da ita ba, a sace ta fice tai waje, kai tsaye gidansu ta nufa, shi kuwa yana can a d'akin sa a kwance, duk gangar jikin sa da idanuwan sa, na muradin so da ganin Fa’iza suke.

Tun a gate ta tambayi mai gadi ko Sahal yana gida? yace mata yana nan, nufa cikin gidan tayi bayan ta gyara zaman hijjabin dake jikinta. A parlour taga mutanan gidan nan ta fara rarraba idanuwa tana tunanin ta inda zata ganshi, amma babu shi kome kama dashi babu.

“Ummi ina yini?”

Taje kusa da mahaifiyar Sahal tana gaida ita, cikin murmushi ta amsa tare da fad'in,

“Ina su gwaggo Talatuwa?”

“Tana gida Ummi, tama ce tana gaida ke.”

Sai da Ummi tayi murmushi kafin tace mata,

“Ina amsawa.”

Tashi tayi ta koma kusa da Husna ta d'ad'a mata duka a cinya tare da turo baki tana cewa,

“Ki taya ni jimami k'awas..”

“Na mefa?”

“Mtcew! Kinsan wannan Baba Suleiman d'in mahaifin Fa'iza boarding school zai kaimu?”

“Boaa what?!Aliya kina nufin kice boarding school zaki tafi?”

Maganar Husnah ta sake karya zuciyar Aliya nan da nan ta fara wulkita idanuwa, Alamar kuka take shirin yi tace da ita,

“Kinsan idan ka rasa iyaye to komai za'a yi maka na ‘kuntatawa ne, wai dan kar nayi magana shine harda had'awa da Fa'iza, wallahi tallahi bana san makarantar kwana saboda aljanu..”

Ummi dake gefe kamar ba zata tanka ba, zaune take hannuwan ta bibiyu akan waya tana latsawa, ‘dan ‘dagowa tayi tana kallon su, jin yadda Aliya ke shararo ‘karyar muguntar da kawu sulaiman ke mata, a hankali tace da Aliya,

“Ke kuwa Aliya meyasa bakyason boarding school? kinga ‘yan gidan mu, duk ita muka yi, nan Government Girls Senior Secondary School Shekara, dake yakasai. Mu lokacin ma iya primary ne..”

Aliya ta wani jujjuya manyan idanun ta alamun ita fa tana kan bakanta kafin ta dubi Ummi, cikin turo baki gaba tace,

“Ummi ku fa cikin gari ne, mu kuma can-can ‘kauyen sumaila ne”

Ummi ta jaddada kai, kafin cikin ‘karawa Aliya ‘kwarin gwiwa tace,

“Makarantar na da kyau, kuma Sumaila ba ‘kauye bane, Akwai ‘kanwata dake aure acan, Auntyn su Hajara, Chairman din garin take aure ma..”

Aliya tai ‘kwafa tana zabga tagumi, Husnah dake gefe ta ‘dan zunguri Aliya kafin tace,

“Kakki wani damu ‘kawata, Insha Allahu! Duk ranar visiting ‘dnku zamu zo da ya Sa...”

Dai-dai lokacin Sahal yafito daga ‘dakin sa, yatsan hannun sa na hagu yana cikin hancin sa, sai faman ‘kwak’ule-kwak’ulen hancin yake, idanuwan sa suka sauka akan Aliya dake dashare masa hakoranta, wani siririn tsaki ya saki, ya taka ‘kafar hagun sa kenan zai koma ‘dakin sa, muryar Aliya ta doki dodon kunnen sa, cikeda farin cikin ganin sa tace,

“Ya sahaaaaaaal...”


MX🧕🏼

——
*J/10/S*


Tana sharce ruwan fuskarta cikin rashin sanin akwai mutum a wajan kawai ta yarfa masa ruwan, tana bud'e ido suka yi 4 eye's dashi yana tsaye yana kallanta, gabanta ne yayi wani irin bugawa sai dai tayi ta maza tare da kawar da kai tace,

“Lahh! Yi hakuri dan Allah wallahi ban san da mutum a wajan ba.”

“Idan ban hakura bafa?”

Yayi maganar yana goge fuskar tasa, yawu ta had'iye mai kauri, sannan ta saci kallansa suka yi ido hudu tayi saurin kawar da nata tare da cewa,

“Ka dai yi hakuri kodan albarkaci sister liya.”

Murmushi taga yayi mai shegen kyau, ta kuma kawar da kai tana shirin barin wajan, sassanyar muryar sa taji yana cewa,

“Faizahhh ina son magana dake.”

Cak ta tsaya gabanta sai bugawa yake yi, wani abu yana tasowa tun daga k'asan zuciyarta zuwa wuyanta, shiru yayi yana tunanin ta inda zai faro maganar sai dai ya daure domin wannan shine damarsa ta farko da ya samu akanta, matsawa yayi daf da ita yace,

“Tunda nake tare da sister d'inki ban tab'a yi mata soyayya irinta aure ba, shin ya za'a yi na bayyana mata hakan? Abinda yasa na gaya miki ina son ne na samu shawara daga gurinki kinga ke 'yar uwar tace, gashi ni yanzu na samu wadda zuciyata ta nutsu akanta harma nake jin idan ban aure ta ba zan iya rasa wani abun na rayuwata.”

Wani irin kallo da tayi masa sai da Sahal yaji cikinsa yayi kuka, tsab ya gano manufar kallon wato kallo ne na bakada mutunci, ni zaka zo ka yiwa wannan maganar kace baka son 'yar uwata, Saboda kana son wata? Bata san lokacin da taja wani mugun tsaki ba ta gallara masa harara, tare da wucewa zata tafi yayi saurin saka hannu ya rik'o ta.

Cikin rashin sani taji hannunta a nashi, nan da nan jikinta ya hau rawa ya sake damkewa, duk mutanan dake wucewa sunyi zaton yaya da ‘kanwa ne hakan yasa babu wanda yace komai sai dai an zuba musu na mujiya (idanu), kallansa take yi cike da takaici tama rasa bakin magana saboda bakin ciki taji yana cewa,

“Please Faizaah ina son ki nuna mata cewar ba soyayyar aure nake mata ba, so ne kawai irin na kanwa kamar yadda nake da Husnah.”

Da kyar Fa'iza ta had'iye abinda ya tokare mata wuya tace masa,

“Sakar min hannu na, ko nayi kalar 'yan iska ne?”

Cikin sanyin jiki ya sakar mata hannun, ta gyara zaman hijabin jikinta tare da cizon leb'enta na sama tace,

“Babu abinda ya dameni da alak'arku da Aliya domin ban san lokacin da kuka farata ba, Amma duk kasan ba son aure kake yi mata ba me yasa baka sanar mata ba tuntuni? Hmmm! sai yanzu dan kaga ta damu dakai tana masifar sonka shine zaka ce ba sonta kake yi ba? wallahi kaji tsoran Allah domin baya barin hakkin wani akan wani, kuma duk ba soyayyar aure bace amman har da zuwa nan inda take? Me yasa kazo mata harda wannan uban kayan? Wallahi idan baka aureta ba sai Allah ya saka mata..”

Ta karasa maganar hawaye na zuba daga cikin idanuwanta, cikin sauri kuma ta juya zata bar wajan ya kuma rik'o hannunta jikinsa a sanyaye, k'ok'arin kwacewa take amman ta kasa haka taji yana cewa,

“Faizaah! Wallahi akwai wacce nake so, akwai wacce zuciyata ta amincewa shin ya zanyi?”

Fa'iza na kukan bakin cikin yace baya son Aliya a zuci, ga kuka na zahiri tana yi. tace masa,

“Ai hud'u Allah yace ku aura, toh ka aure su dukan su mana ba shikenan ba.., ni ka sakar min hannuna wallahi ko na fad'awa principal d'in mu.”

Ba dan ya soba haka ya sakar mata hannun ta tafi, yayi saurin bin bayanta yana son su jera saboda ya dinga mata magana amman taki yadda dan sai zabga uban sauri take yi har ta koma gurinsu Gwaggo Talatuwa. Wajan mota Sahal ya koma inda ya jingina bayansa, gabaki d'aya kwakwalwarsa ta cunkushe ya rasa yadda zai yi, maganar Fa'iza sai dawo masa take yi inda take cewa, 'toh ka aure su dukan su mana' it means ya auri Fa'izan da Aliyan? Kai ya fara girgizawa a haka abokinsa Fareed ya same shi, kafad'ar sa ya dafa yace dashi,

“Ya akai ne, kunyi maganar da ita?”

“Yahh! but na kasa gaya mata cewar itace wadda zuciyata ta amincewa ba wai Aliya ba, amma kasan menene?”

Fareed ya kad'a kai alamar be sani ba, Sahal ya rik'e goshi saboda ciwon kai da ya fara shirin kamashi, yace.

“Kuka ta saka min da nace ba soyayyar aure nake yiwa 'yar uwar taba, sai ma cewa tayi wai to na hada biyu na aura da wadda nace mata ina so da kuma liya.”(Aliya).

“Kut! Amman gaskiya yarinyar nan zamu sha wahala wajan karb'o zuciyarta, toh kai my friend me yasa baka son Aliya? Tana da duk wani qualities da namiji yake buk'ata wajan neman aure, me yasa kai baka ji sonta ba?”

Cikin rashin damuwa Sahal yace,

“Fari, saboda fara ce ni kuma bana son farar mace gaskiya, farin ma kuma irin na Aliya, saboda har wani ja-jaja-jaja take yi.”

Wani irin ihu Fareed ya saki tare da kaiwa Sahal naushi a bayansa yana fad'in,

“Gaskiya kai d'an bala'i ne, to yanzu ya zakai da ita?”

“Ya zanyi kuwa, kawai ci gaba zanyi da farautar zuciyar Faizaah tunda dai ita zuciya ta take so, wallahi yarinyar nan yau ta kuma sace min zuciyata, dana rik'e hannunta wallahi ni kad'ai nasan abinda naji Fareed.”

D'an yatsina fuska Fareed yayi tare da kallan Sahal dake tsaye yana kallan ‘kasa, numfashi yaja tare da cewa,

“Gaskiya kana cikin matsala my friend, saboda ita kanta Aliya tsayawar da muka yi da ita maganarka kawai take yi, maganar gaskiya tana sonka, so ina ganin me zai hana ka aure su duka, tunda naga yaran ma kansu a had'e yake?”

Wani wulakantaccen kallo Sahal ya yiwa Fareed, kasa furta abinda yayi niyar fad'a yayi kawai ya bud'e mota ya shiga yana k'ok'arin tayarwa, murmushi yaga Fareed d'in yana yi kafin daga bisani ya juya ya nufi hanyar gurin su Aliya kasancewar ba'a barinsu zuwa bakin gate, iyakarsu wajan male staff room. Shima a hankali ya kashe motar ya fito yabi bayansa badan komai ba sai dan yasan idanunsa zasu dinga nuna masa Fa'iza.

Yana k'arasawa wajan Aliya ta mik'e taje gurinsa ita da wasu kawayenta su biyu taja su wai suzo ga saurayinta wanda zata aura su gaisa, sai sakin murmushi take yi, shi kuma idanunsa suna kan Fa'iza da ta zuba abinci tana ci tana dariya wadda da alama Gwaggo ce take fad'ar wani abun mai sanya dariya.

“Yaya Sahal ka dawo?”

Kallanta yayi kad'an sannan ya kalli kawayen nata ya lumshe idanunsa tare da bud'e su yace,

“Yeah na dawo, ya school d'in da dad'i ko?”

Yayi maganar idanunsa suna kan Fa'iza ,wadda itama lokacin ta d'akko loma zata kai bakinta kamar ance ta kalla kawai suka hada ido, harara ta watsa masa ta maida idonta tare da cigaba da cin abincin ta. Can kuma kawayen Aliyan ne suka shiga gaida shi sai suka ga yana murmushi suma duk saka hau yi duk a tunaninsu su yake yiwa basu san na Fa'iza bane murmushin.

“Yaya Sahal boarding school akwai wahala wallahi, bakaga duk na rame bane?”

“Uhmmm! Kin d'an rame kad'an amman, wai sister d'inki ba zata zo ta gaida ni ba?”

Yayi maganar yana kallan cikin idanun Aliya, farfar tayi masa da idanunta wanda ya zame mata jiki sannan ta juya ta kalli inda Fa'iza take zaune, kallan Sahal tayi tace,

“Yaya Sahal kenan, kadai san halin mutuniyar taka ba zuwa zata yi ba.”

“Shikenan toh mu bari mu tafi, Saboda yau zan koma abuja akwai abinda zanyi.”

Zaro ido tayi tare da cewa,

“Wai daman ka koma can Abujan yaya Sahal?”

Sosai yake kallanta inda yaga tsantsar farin ciki a cikin idanunta tamkar ance ita za'a kai can d'in, ya zuba hannuwa cikin aljihun wandonsa tare da cewa,

“Na koma mana, ko kina da sako ne wanda zan tafi dashi?”

“A'ahh bani da kowa a abuja, ina tayaka murna wallahi.”

Dariya yayi domin yasan ji take yi kamar da ita yaje, ya fara matsawa kusa da Fareed wanda yake tsaye da wata student da alama yasanta ganin yadda yake yi mata dariya. Alamu yayi masa da cewar yazo su ware ita kuma Husnah waya yayi mata yace tazo su tafi, lokacin itama tana tare da wasu kawayen ta da ta gani a makarantar. Zuwa suka yi dukan su suka yiwa su gwaggo sallama ta dinga zabga musu addu'a tana sanya musu albarka tare da nanata cewar Aliya ta Sahal ce babu wanda zata yadda a bawa ita, gwaggo dai aka dinga jajjada irin yadda zata tsaya tsayin daka wajan ya auri Aliya, shi kuwa sai kallon-kallo suke yi shida Fa'iza wadda ke faman yatsina masa fuska tana harararsa. Kud'i ya zaro ya bawa gwaggo Talatuwa sannan suka mik'e suka nufi gate, tsayawa yayi ya d'akko wata leda 'yar madaidaiciya yaje ya bawa wani mai gadi yace dan Allah a nemi Fa'iza Sulaimain a bata, mai gadi ya karb'a tare da tabbatar da cewar za'a nemota a bata.

Haka suka tafi duk Sahal baya jin dad'i, Saboda ya kasa furta abinda yake cikin zuciyarsa, amman ya barshi zuwa nan gaba dan so yake itama Fa'izan taji duk duniya babu wanda take so sai. Su gwaggo kuwa sun jima kafin suka yiwa su Aliya sallama suka tafi cike da kewa da jimami.

Suna komawa d'aki aka aiko cewar ana kiran Fa'iza inji vice principal, tashi tayi duk da cewar a gajiye take ta d'auki hijabi ta tafi, tana zuwa ya mik'a mata yace gashi ance a bata, karb'a tayi ta mik'e tare da bud'e ledar, wata kyakyawar takarda ta gani cikin sauri ta ciro tare da bud'ewa tana karantawa gabanta na fad'uwa, abinda ke rubuce shine.

_''My soulmate Fa'iza, gashi nan babu yawa Allah ya bada sa'ar karatu, ki adana min zuciyarki, karki bari kowa ya shiga ciki sai ni kadai Muhamman S, love you.''_

Cikin sauri ta zazzage ledar, gabaki d'aya turaruka ne masu masifar tsada, ga kamshi sai kud'i ta d'auka ta duba, dubu biyar ne nan da nan jikinta ya fara rawa ta d'auka ta mayar da su leda tare da dafe kai tana tunanin wanene wannan yake bibiyar rayuwarta? sam bata son wannan abun domin ita zuciyarta tana wajan Shamsuddeen, shine wanda ta amincewa take kuma burin ya aure ta nan gaba, amman waye wannan Muhamman S d'in...?!

*SWITZERLAND🇨🇭*
*UNIVERSITY OF ZURICH*

*Siririn* tsaki Shamsudden ya saki, kafin ya furta kalmar data zamto masa jiki wato,

“So intolerable..”

‘Karasawa kusada su Afrah tayi, taja gefe kujera mai fuskantar Shamsudden ta zauna, kumbure-kumburen fuska ya shi ga yi yana tabe baki,

“pulchritude...”

Cewar Afrah, dake haka suke kiran Shamsudden a school din, Saboda kyawun sa da ‘k’ok’arin sa, kamar ba zai amsa ba sai kuma ya furta murya ciki-ciki da,

“Afrah..”

Yazeed da Jeremy suka gaysa da ita, shi dai mutumin naku yaki ‘bata fuskar da zata jashi da hira, Da alama ba tada zuciya dan sake cewa tayi dashi,

“pulchritude, pls ka bani ko minti biyar ne, I badly wanna talk with you, your attention matters me most..”

Biron dake hannun sa ya ajiye, yana jifan ta da wani banzan kallo, kafin yace.

“Dan Allah ki kyale ni.. Baki ga a student bulletin an sa yau za mu fara semester tests ba? So ina bukatar nutsuwa, dan Allah ki kyale ni..”

Mikewa tai jiki a sanyaye, idanuwan ta sun kawo ruwa tace dashi,

“Shikenan pulchritude! Duk sanda ka gama you lemme knw... Kaji?.”

Ba dan ya soba ya kalli gefe, ciki ciki yace,

“Naji..”

Jiki a sab’ule taja ‘kafafunta tai gaba, Yazeed yaja wani dogon tsaki, kafin yace,

“Haba dude! Ya zaka dinga yi wa a whole princess haka ne? Yadda kake da kyan hali pls kadena yiwa mata rashin kirki dude..”

Hararar wasa Shamsudden yaiwa Yazeed, kafin yace dashi,

“Dan ‘yar sarki ce ita hakan ya cireta a sahun sauran mata ne? Dude nayi warning ‘dinka akan kadena interrupting ‘dina da anything girly, haba! So intolerable..”

Yazeed ya ajiye timemen textbook ‘din ‘Origin of oil’ a akan bench ‘din kafin ya sake cewa,

“Several times na tambaye ka akan meyasa ka tsani mata kak’i sanarmin, da nayi magana sai kace Aliya ce sila, wacece Aliyan? Shin metayi maka da ka tsaneta haka? Har laipin ta ya shafi sauran matan da basu sukai maka ba?”

Yazeed ya ‘karasa fad’a yana kallon Shamsudden don jin ‘karin bayanin abunda Aliya tayi masa, daya ‘dau mummunan mataki haka akan sauran mata? Shamsudden ya bude baki zai kwararo zance wayar sa tayi ‘kara, ‘Bro Gee’! shine sunan da yai appearing akan screen din wayar sa. Mik’ewa yayi zai amsa wayar, Jeremy ya tashi yana musu sallama da sai sun had’u a hostel, shi kuma Yazeed ya janyo littafi yana dubawa, ‘Dan nesa da wajen zaman su ya koma yana sake kara wayar a kunnen sa,

“Hello Ya Garzali..! Na’am, Lapia lou Alhamdulillah Wlh, dama yanzu nake shirin kiran ka sai gashi ka riga ni, oh okay eh Allah sarki! Nace Yaya na sako mak.. Okay ka ga alert ko? Eh yaya so nake a sake sake siyamun fili da kudin ribar kaji na, eh eh, na waje na kuma a soma ginin wajen, nayiwa hamza magini waya yace zai kawo maka zanen wajen kagani, Eh yaya kawai zabi za’a zuba aciki da d’awisu, inda ragowar canji kuma anyi rijiya a masallacin na lado nan bayan layin mu... Haba Yaya? Kai Masha Allahu! Alhamdulillah Ina godia wallahi, Lalle Allah yasa albarka! ai banzaci kudin sun nunku haka ba, Eh yaya ku fara ginawa shid’in ma, Nagode k’warai, kuma mutanen nan sai magana suke sake min, Nace su dakata dai zanyi shawara, Eh Eh su! Toh Yawwa kuyi shawara dasu Ummah, duk yadda kuka yanke sai ka sanarmin, nima zan kirasu mu gaysa anjima, har yanzu Ummah dai bata gane kan video call ‘dinnan hahah, okay Yaya, Yawwa nace wata mai kamawa(next month) zamu ‘kare degree dinmu, kuma idan mun fito da sakamako mai kyau sunce zasu ‘daukemu muyi masters kyauta (scholarship), Eh zan tsaya kawai nayi Insha Allahu, Eh shekara daya zuwa biyu ne, Eh MBA(master of business administration) zanyi Yaya, Eh Tunda kaga degree dina akan Bsc. international relations nayi, Eh yayi yaya, zan ‘kara da professional diploma ma akan ‘International law’ .. Okay yaya, Ameeen ya Rabb..Agayda su Aunty Afiya! Nagode k’warai JazakAllah bil jannah.. okay sai anjima..”

Murmushi Shamsudden yayi bayan ya katse kiran, zuciyar sa cike da jin dadin wayar da sukai da Garzali wansa, na jin kasuwancin sa na can sai hab’aka yake yi, abun sai sam barka kawai.. Komawa yayi kusada Yazeed ya zauna, Yazeed da a matse yake yaji labarin Aliya yai saurin cewa,

“Ina jinka dude...”

Nan Shamsudden ya bashi labarin rayuwar su da Aliya, amma ba komai ya fad’a ba, ya k’ar’kare masa da,

“Kai a ganinka na cancanci tai min haka? Duk irin HALACCIN da nai mata a rayuwa, na nuna mata soyayya da kyautatawa?”

Yazeed ya girgiza kai, kafin yace,

“Gaskia bata kyauta ba, but dude ai ba duka aka taru aka zama d’aya ba, bai kamata kace ka yanke mu’alama gaba d’aya da mata ba sa...”

Bai karasa ba Shamsudden ya ja wani bahagon tsaki, ya mike ya tattara books dinsa. Ya dubi Yazeed yace,

“Idan kagama silly talks din, kasameni a cafeteria, so intolerable!”

MX🧕🏼
*I/9/S*

*G/G/S/S/S.... SUMAILA*

Tun lokacin da aka kai su kasancewar su kyawawan yara, yasa manyan makarantar wato 'yan aji shida suka fara rubibinsu da son yin school daughter's dasu, ss1b shine ajin da aka kai Fa'iza, ita kuma Aliya aka kaita ss1c, sunci sa'a aka kaisu hostel d'aya, inda aka kaisu corner d'in captain d'in hostel d'in. Kasancewar Aliya tafi Fa'iza rawar kai hakan ya sanya kowa yake janyota jikinsa, tun a ranar suka tabbatar da cewa lallai sunzo makarantar kwana domin suna zaune suka ga an fara gudu kowa yana ‘daukar kwanonsa, Aliya ce ta kasa yin shiru sai da ta tambayi ta kusa da ita wadda taji ana kira da sister Bakori tace,

“Sister Bakori ina za'aje ake gudu?”

Rumaisa'u shine asalin sunanta, kasan cewar 'yar Bakori ce shine sunan nata ya ‘boye kawai ake kiranta da hakan, ta kalli Aliya tana murmushi tace,

“Dining hall zasuje su karbi abincin rana, kuma ku shirya sai captain d'inku ta tafi daku ta zuba muku.”

Tashi suka yi ko wacce ta bud'e akwatin ta suka d'auki robobin su merry verry (irin ta almajirai),sunga abin mamaki ganin yadda kowa ya jeru gashi gurin yayi tsit bakajin komai su maganganun prefects suna ta shewa, jansu aka dinga yi, robobin su kuwa sai da aka cika musu su da taliya. Haka sukaci gaba da rayuwa suna jin dad'i domin Mommy's d'insu na can sun tsaya musu, head girl itace Mommyn Fa'iza, sannan labour prefect ta Aliya, an gatanta su na tsawon lokaci kafin su fara d'an-d'anar wahalar makaranta, dan sai da ya zamana wata ran basa samun ruwan wanka dan an dena basu kamar yadda ake musu a baya.

Duk abinda Aliya take yi hakan baya hanata maida hankali wajan yin karatu, tana daya daga cikin zafafan ajinsu, malamai da dama suna ji da irin fikirarta kamar yadda Fa'iza ma take a ajin su, sosai suke karatu kuma duk da haka baya hana Aliya yin wasu abubuwan. Ana gobe visiting suka samu damar yin wankin uniform dinsu, suna bushewa suka ninke ko wanne yasa nashi a ‘karkashin katifarsa saboda su samu suyi karin goga yadda za'a gansu fes.
•••
*A* can gida kuwa dama tunda suka baro gidan gwaggo sai Baba Suleiman yaje ya d'auke mahaifiyarsa daga gidan ta, ya maida ita gidan shi, da kyar gwaggo Talatuwa ta yadda saboda a cewar ta kartaje su dinga samun matsala da matarsa, amman yace mata babu komai, babu yadda zata yi haka ta bishi suka tafi, d'aki d'aya aka bata daga can baya harda band'aki a cikinsa yadda ba sai ta fito sun had'a toilet da surukarta ba.

“Gwaggo zakije visiting?”

Maman su Fa'iza ta tambaya bayan ta d'aga labulen d'akin gwaggon, Gwaggo Talatuwa dake gyara ‘dan tofin cikin zaninta tace,

“A wane garin yake shi zibitin d'in?”

Gwaggo ta tambaya tana kallanta cike da son jin karin bayani. Sai da Mama tayi murmushi kafin tace,

“Gwaggo ba gari bane, ina nufin zakije ziyarar su Aliya makaranta.”

D'an Jimm! Tayi kafin tace,

“Allah sarki 'yan jikokina, zanje mana na ga halin da suke ciki.”

“Toh shikenan gwaggo, gobe ne dama za'a yi shi yasa nace bari nazo na tambayeki ko zaki je?”

Fitowa tayi ta wuce tana ci gaba da harhad'a kayan da za'a tafi musu dashi goben, yayin da itama gwaggo ta fara yin nata, inda ta bayar aka siyo mata manja da man gyad'a ko wanne ta zuba mishi a jarkar lemo, ta siyo aya da sauran abubuwan da duk tasan jikokin nata suna so.

*SAHAL*

A can b'angarensa shima yana jin labarin visiting d'in ya fara shirye-shiryen tahowa kano, waya ya yiwa Husnah yace ta shirya idan ya dawo zasu je tare, wasu uban kayan provision ya had'o musu shi kansa besan abinda yake hankad'ashi ba har yake yin wannan hidimar, kawai dai yasan kaunar Fa'iza na d'aya daga cikin abinda yake sashi.

Jirgin yamma ya biyo ya zo kano, Dan Adaidaita sahu ya hau tun a airport ya dawo gidah, hannuwan sa rike da kayan shopping na Next dake Abuja, ‘yan gidan suka yo kansa suna murnar ganin sa, Husnah ta mak’al’kale shi tana tambayar sa da,

“Ya Sahal wannan kayan nawa ne ko?!”

Wani kallo ya mata na kin renawa ‘kwa’kwalwarki hankali’ kafin yace,

“No! Ke zan baki ki saya, wannan na ...”

Bai ‘karasa ba Husnah ta wafce zancen da,

“Na Aliya ne, kai yaya kanason Aliya dayawa wallahi, bari muga kayan..”

Ummi dake gefe ta zuba musu ido tana binsu da kallo kawai, Aliya ta shiga bubbud’e kayan, tana fad’ar sunayen wasu, wasu kuma ta ajiye kawai,

“Laa! Harda crackers, ga Pringle’s, kai Ya Sahal harda Maltesers ga Hershey’s, duk favorites chocolates dina, la harda su ‘Ready to chew English Tofu’ (Awara), Tab La ummi kinga harda kenturkey fried chicken, hum uhm, La Ya Sahal harda kaya kuma, a’a yanaga Kuma na mutum biyu?”

Sahal ya sosa ‘key’ar sa, cikin basarwa yace,

“Dallah ba itada sister ‘dinta bane? Ya za’ai mu kai mata ita ‘daya ai d’ayar zata ji haushi.. Ya ma sunan ‘d’ayar?”

Ya ‘karasa fad’a yana raba idanuwa, had’e da ‘daukar Nutella dake cikin kayan yana jujjuyata, wai duk dan kar su harbo jirgin sa, Husnah
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment