Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

fara.”

Cewar Abban su Shamsu, Umman su ta rausayar da kai tare da cewa,

“Amin ya Allah.”

“Toh ni zan tafi masallaci, sai Allah yayi mana dawowa.”

Sai da ta gyara masa mab'allin rigarsa, sannan ta mik'a masa sallayar da zai tafi da ita tana cewa,

“A dawo lafiya a samu cikin addu'a.” Sai da ya fito sannan yace da ita.

“Zanyi miki kuwa, har da ta samun 'yan biyu k'annan Shamsu.”

Cikin sauri tace,
“Ba amin ba wallahi, haba Abban su ya za kai wannan fatan da girmana, haihuwa sai dai in kaine kayi amarya sai taxo tayi ‘kannan amman banda ni.''

Dariya yayi ya fita, shi tunda yake a rayuwar sa bai tab'a ganin matar da take neman ayi mata kishiya ba sai matar sa, wani lokacin idan tana yi masa magiyar ya ‘karo aure sai yayi ta tunanin ko son shi ne ba tayi? take ta matsa masa akan yayi aure. Ita kuma tana ganin kamar yana san 'ya'ya da yawa ,ita kuma gashi tun guda biyu da Allah ya bata, bata kuma yin koda b'atan wata ba, hakan yasa take son ya kara aure saboda farin cikin sa. (Tab kunji true love).

Da 'yar waka Shamsu ya shigo gidan saboda yaga babu mashin d'in Abbansa yasan ya tafi masallaci, dubawa yayi yaga Umma ma ta shiga band'aki, sai ya koma ‘dakin su dake zaure shima yayo shirin wanka daga shi sai gajeran wando, ‘karasawa wajan raken sa yayi yana kuma k'irgawa, bakin nan nasa har kunne tamkar ya fara ciniki.

“Toh abar raken nan azo ayi sallah.”

“Umma ya kika ganni a wannan harkar?”

“Bafa tambayarka nayi ba kasan juma'a ce karkaxo ka rasa sallah, kazo ka wuce idan ka dawo mayi maganar.”

Murmushi yayi sannan ya wuce band'aki ya ‘dakko bucket, ruwa ya ‘diba ya koma band'akin yayo wanka, shaf-shaf saboda kar ya rasa jam'i, gashi sai jiyo huduba yake yi a babban masallaci.

Shiryawa yayi tsab cikin wani yadi ash colour d'inkin 'yar shara ne, domin yana matukar son irin d'inkin hakan yasa duk kusan kayan sa irin sune, guda biyu ne kawai yake da masu hannuwa suma kuma yaya Garzali ne yayo ya bashi, ba wani saka su yake yi ba, saboda sam basa burge shi yafi son 'yar sharar shi, duk tsadar yadi ko shadda haka yake kaiwa a d'inka masa.

Ko sallama beyi da Umma ba yayi tafiyar sa, Saboda yaji ana shirin tayarwa. Ana idarwa kuwa bai tsaya ko'ina ba ya dawo gida ya d'ibi raken sanda biyu yakai kofar gida ya jingine, sannan ya dawo ya dauki bencin injin taliyar Umma ya fita, zama yayi yana jiran masu siya. zuciyar sa cike da addu'ar Allah yasa a dinga siya.

“A'a Shamsu rake ka fara siyar wa?”

Cewar malam Rayya makocinsu da yazo shigewa gida. Shamsu yana murmushi wuk'ar yanka raken tana hannun sa yana jujjuya ta yace.

“Eh malam sannu da dawowa.”

“Yauwa Shamsu nagode, yanko min ta hamsin amman yankan 'yan goma-goma zaka yi min, Saboda yaran akwai yawa, Allah ya karo kasuwa.”

Da zumud'i Shamsu ya mik'e tare da zaro sandar rake guda d'aya ya shiga ferewa, yankar wa malamin Rayya yayi sannan yayi masa kamar yadda ya buk'ata, malam Rayya ya karb'a ya bashi kud'in, Shamsu ya tura cikin aljihu dan ba k'aramin dad'i yaji ba. Kamar bud'ewar hanya nan da nan mutane suka fara tururuwar zuwa siya, kafin zuwa yamma damin raken da ya saro ta kusan ‘karewa, aljihun sa kuwa cike yake da kud'i, haka ya shiga gida ya zauna a cikin ‘dakin su yana ‘kirga su.

Yana gama ‘kirgawa ya ware uwar kud'in sannan ya ware ribar sa, da gudu ya kwasa ya nufi wajan Umma dasu, wadda ta kammala miyar kub'ewar ta kenan.

“Umma taho-taho ki gani! Allah ya sanya wa sana'ar nan tawa albarka, taho kiga nawa na samu.”

Cikin farin ciki Umma ta k'arasa wajan sa, bayani yayi mata akan yadda ya saro raken, sannan ya nuna mata kud'in da kuma ribar ga kuma ragowar sanda biyu da ta rage masa, wadda idan aka idar da sallar magriba zai fitar dasu waje.

“Kai masha Allah Shamsu, haka dama sana'ar rake take da d'in bin riba a ciki?”

“Kin gani dai Umma, ai gobe dami biyu zan siyo tunda wannan ‘ya kare.

Shafa kanshi tayi, bakin ta yaki rufuwa tace.

“Toh Shamsu ai dole ne nima na ‘kara maka jari, Allah ubangiji ya kara bud'a maka.”

Ya amsa ta yana bata ribar dan ta ajiye masa, koda Abban su ya dawo shima fatan alkairi yayi masa, Yaya Garzali ne kawai bai ji dad'in wannan abun da Shamsu keyi ba, domin har form yace a kawo masa ta wata makaranta da ake koyan turanci zai siya masa amman ya tattago wani rake, cikin b'acin rai yace.

“Toh duk da wannan sana'ar da kake yi hakan ba zai hana ka shiga makarantar nan ba, da safe ake yin ta karfe takwas zuwa sha biyu an gama kuma Monday to Friday ne, idan yaso in ka dawo sai ka ci gaba da siyar da raken.”

Fuska ya b'ata kamar wanda aka yiwa bushara da cin k'aya sai faman hura hanci yake yi, Yaya Garzali yana kallon sa amman yaki ya tanka shi, cikin b'acin rai suka ji yace,

“Wai dan girman Allah karatun bokon nan shi za'a tambaye mu a kabarin mu? ahh! nace na gama neman ilimin boko dole sai nayi ne? gaskiya ni babu wata Dabo English academy d'in da zanje bare na b'atawa kaina lokaci, idan naje guri ban iya turanci ba dan Allah a zageni ko ayi min dariya, ba dai abinda mutum yake ji dashi zai yi amfani ba? Toh ayi min turanci sai nayi hausa dan shima yare ne.''

“Ni kake yiwa rashin kunya Shamsu? Umma kinji yaron nan ina cewa yayi abu yana cewa ba zai yi ba dan raini, to idan kayi wa zaka yi mawa? Kar Allah yasa kayi, kud’i na ma sun huta, kaje kayi duk uban da zaka yi sakarai kawai shashasha.”

Tashi yayi yabar gurin yana k'unk'uni, kawai yaya Garzali yazo ya b'ata masa rai saboda wani buri na shi can, yace baya so ba sai a kyale shi ba ko dole ne?, sai kace fita daga addini duk yabi sai yab'a masa magana yake yi harda cewa yayi masa rashin kunya dan sharri.

Kayan raken saya d'iba yayi k'ofar gida ransa duk a jagule, yana fita ya tarar dasu Auwal sunzo nan, suka zauna suka siyi raken suna sha suna hira a haka yaya Garzali ya wuce su, mamaki yake ganin irin rayuwar da Shamsu ya zab'arwa kanshi, bayan kuma Kabeer abokinsa yana zuwa computer school yanzu gashi nan dashi suke hirar tamkar bai je gurin koyarwar ba. Sosai yake cinikin rakensa hakan ya kuma sanya masa ‘kaunar yin kasuwanci gashi daman Umma ta ‘kara masa jari, idan ya tashi sai ya siyo damin rake guda biyar ko shida cikin kwanaki kad'an ya siyar.

Littattafan sa daya tara guri d'aya su ya kwaso yaje k'ofar gida dasu, duk yaran unguwar su wad'anda suke makaranta ya rarrabawa Umma ba ta da labari sai zuwa wani yaro yayi yana mata godiya, taso yiwa Shamsu magana amman ta share shi fatan alkairi kawai take yi masa, domin tasan duk abinda zata fad'a indai akan karatune to baji zai yi ba, tunda Abban su ya zuba masa ido itama zata zuba ma sa taga iya gudun ruwan sa.


••• ••• •••


Tsaye take hannunta rike da tab'arya jikinta kuwa d'aurin kirji ne tana surfen masara, kai daga ganin ta kasan cewar matar a gajiye take, saboda duk ta ‘kare banda ‘kasusuwa babu komai a jikin ta tamkar ka hure ta ta fad'i.

“Inna ga Aliya can suna fad'a da Jatau mai kayan miya.”

Inna na jin haka ta saki tab'arya tare da gyara d'ankwali ta fito, can ta hango su kuwa, Aliya anci d'amara kai kace zata iya kai naushi sai fitsara take yiwa Jatau. ‘Kwaf’! Aliya taji an sallare mata ‘keya tare da d'umama mata dundu a bayan ta, ta saki wani mugun ihu, had’e da juyowa dan ganin ko waye, Cikin rawar baki ganin Inna ce ta sallare mata kai tace,

“Inna shine fa ya fara y...”

“Rufe min baki shegiyar yarinya kawai, nidai kam wallahi ubanki ya haifo mana alak'ak'ai, toh wallahi tallahi dangin mahaifiyar ki zaki koma, ai munyi k'ok'ari da muka kula dake tun kina zanin goyo, wuce muje yau zaki tafi ba sai gobe ba, na gaji da janyo min surutun da kike yi.”

Aliya na jin haka tayi tsallan albarka ta dire, tare da kurma ihu. Inna ta watsa hannu baya, ta lailayo rantsuwa ta dire, tare da ‘doriyar cewa,

“Kiyi duk abinda zaki dan k'aniyar ki, wallahi sai kin bar ‘kauyen nan.”

Aliya ta zube a 'kasa tana shushshure 'kafafuwa, cikin tirjiya tace,

“Dan Allah inna kiyi hakuri, wallahi na dena.”

Inna ta yatsina fuska, had'e da buga yarkacaccen zanin ta. Kafin tace,

“Ai na rantse da Allah sai kin tafi, dama da yaya nake ciyar dake.”

Haka Aliya tana ji tana gani, inna ta shirya mata kayan ta cikin bakko, sannan tasa Amiru ya kai ta gidan kakanin ta, wato iyayen da suka haifi mahaifiyar ta, ai kuwa suna sauka a garin, Idanun Shamsu su kai kyakkyawan tozali(Love atfirst sight).akan Aliya, yana zaune a k'ofar gida, hannun sa rike da wukar yankan rake.

——
_Littafin KAI MIN HALACCI na kudi ne, yana d’aya daga cikin ZAFAFA BIYAR NOVELS da aka fara, idan Kina So ki biya kudi ki siya ta; _

Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank

*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*



_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO🧕🏼_
*............_KAI MIN HALACCI!_*
💕


_*NA_*


_*©NANA HAFSAT_*
_*(MISS XOXO)_*


®_*HASKE WRITERS ASSO💡_*


*_SHAFI NA HUDU(4)_*

_Littafin KAI MIN HALACCI na kudi ne_
_®ZAFAFA2020_

“Amma dai gaskiya kai d'an k'auye ne wallahi, ya zaka nacewa yarinya sai kace idanun ka sun rufe?okay! na gane saboda kyanta shine duk kabi ka damu har kake jure duk wannan iskancin da take yi maka ko?”

“Ba zaka gane ba khaleel, duk wani abun da zan gaya muku ba zaku tab'a ganewa ba, indai akan yadda nake jin Aliya a raina ne.”

“Kaji wawa, dalla can matsa kai nan gaba bamu san me mace zata mai da kai ba.”

Kabeer yayi maganar yana mik'ewa tsaye, sallama yayi musu ya tafi, saboda ya tabbatar idan ya zauna a wajan toh zasu iya samun sab'ani da abokin sa, yarinyar ta had'u, sai dai bata da kunya shi kuma zai iya zaneta tunda ba soyayya tsakanin su, wanda yake son ta kuma zasu iya samun sab'ani da shi duk kuma a kanta bayan sun jima cikin yin abota tsakanin su.

“Gaskiya Shamsu ka canza takun ka akan yarinyar nan, karka ja ta raina ka duk da kariga ka janyo tunda ka furta mata kalmar so.”

Cewar khaleel yana k'ok'arin ajiye kofin shayin da ya gama sha, shima Shamsu tashi yayi, sakamakon wani mutum da yazo siyan sabulun wanki yaje ya bashi daga nan be sake barin sunyi maganar Aliya da khaleel ba, Saboda baya son duk wani abu da zai sa a zagar masa ita. Ita kuwa Aliya haka tayi ta fitowa neman Kabeer wajan Shamsu baya nan, daga ‘karshe ce mata yayi ,ya tafi makaranta saboda yasan duk wannan neman da take yi masa wulak'anci zata mai, kuma yasan Kabeer ba kyaleta zai yi ba musamman da yasan baya ‘kaunar yarinyar. Cikin hukuncin Allah Abban su Shamsu yasamarwa Aliya makarantar junior secondary sch, js one tare da temakon gwaggo Talatuwa, Saboda bata san wannan zaman da Aliya keyi na janyo mata surutun da yafi ‘karfin ta.

Shi kuwa Shamsu kasuwar sa ce ta shahara wajan yin ciniki ga arha ga sauki, domin wani shago ya bud'e anan unguwar tasu daga d'aya b'angaran, dan gidan suma yana kallan shagon nashi k'ato dashi na provisions, babu abinda babu a cikin shagon hakama yana da yara masu kular masa da customers d'in shi, sai dai kawai shi ya zauna a gurin ko kuma yaje ya siyo wasu abubuwan, cikin k'ank'anin lokaci ya bunk'asa gashi duka befi shekaru Ashirin da biyu ba, ya kuma bud'e shagon sai da wayoyi da yin charge, ga kiwon kaji da tantabaru da Umma take kular masa dashi, sosai Allah ya sanya masa albarka a cikin kasuwancin, amman duk da haka Aliya bata son shi sai dai taci abin hannunsa, yayin da shi kuma befasa kyautata mata ba kamar yadda ya saba.

Cikin takun ta na cewa itama fa yanzu 'yan mata ce kuma budurwa, tazo wucewa ta gaban shagon sa, yana zaune akan kujera a k'ofar shagon nasa. Yayin da daga cikin shagon kuma wak'ar *alagidigo* ce take tashi, ta cikin speakers hannunsa rike da game yana ta faman yi.

Muryarta kawai ya jiyo kamar yadda ta saba duk lokacin da ta hango shi a guri, ko cikin mutane abokansa ne sai tayi masa waka, tun lokacin da tsautsayi yasa shi furta mata kalmar SO.

Satar kallan ta yayi yaga yau ma ta cokaro d'aurin d'ankwalin nan nata wato ture kaga tsiya, mayafin nan a kafad'arta ta tsaya dai-dai shagon, kusa da wata mai suyar awara ta rike kugu tana karkad'a jiki bakin nan yasha kanta kile, cunoshi take tana waka,

_”Allah ya tsine wa saurayin kusa da gida, shekaran jiya yazo.., jiya ma yazo..yauma kuma zaizo...!”_

Kamar yayi shiru ya kyaleta kamar kullum idan tayi, Amman yau zuciyar sa tana son ramawa dan bai ga dalilin da zai sa k'aramar yarinya dan yace yana sonta ta dinga gasa masa magana a fakaice ba, dan haka shima yana danna game d'in ba tare da ya kalleta ba yace,

_”Allah ya sakawa saurayin kusa da gida, shekaran jiya ya kai an k'arb'e.., jiya ma ya kai ta karb'e.., yauma kuma zai kai, indai da gaske ne ba'a son kyautar kullum idan ya kai, yau kar a karb'a...!”_

Da sauri ta kalle shi, domin ba tayi tsammanin martani ba daga bakinsa, murgud'a baki tayi tare da bugun cinya da hannunta ta kalle shi, shima dai-dai sannan ya d'ago suka had'a ido ta dank'ara masa harara, yayin da shi kuma ya mayar mata da lafiyayyan murmushi, mai awarar ta kalla tana cewa.

“Aikin banza, Sa'ade soya ki bani ta hamsin.”

Sa'ade dake zuba awara cikin mai tace,

“Toh.”

Shi kuma da yake gefe yana jinsu yace.

“Sa'ade dad'a mata ta wata hamsin d'in, ta d'ari kenan zan biya ki”

Tab'e baki tayi maimakon tayi masa, godiya amman cikin ranta fess domin ko sisi daman babu a gurinta, saboda tasan zai biya, shi yasa tace a bata ta hamsin dan ta kare yawa a gabansa, da mamaki ya bita lokacin da aka gama soyawa aka mik'a mata ta karb'e ta juya zata tafi tace,

“A duniya dai akwai wahalallu, Sa'ade Allah ya sa a rage kud'in waken suya(soy beans), kinga kuma kun huta masu saidawa kuma sun kwaso asara.”

“Kai Aliyah Shamsu mafa yana sai dawa kuma a gurinsa nake auna, so kike shima asarar ta same shi bayan kuma gashi ya siya miki awara har ta naira d'ari?”

Dariya Aliya tayi tana kuma sauyawa ledar awararta hannu, saboda zafin da d'ayan yayi, sai da ta kalli inda Shamsu yake zaune sannan tace,

“Oho ke wacce kike so a amsa miki a cikin addu'ar tawa? A kara kud'in waken suyar, ko kuma a rage kuma dole ku siya a haka wanne kika fi cewa amin?”

Da sauri Sa'ade tace,

'”A'a nafi son a rage amman ai su Shamsu ne zasu yi mugun asara fa Aliya.”

Cikin saurin baki Aliya tace,

“Haka nake so ai Sa'ade kinsan wasu a wahale suke duk abinda zaki musu toh ba ganewa zasu yi ba, ni na wuce sai anjima.”

Murmushi Shamsu yayi yana girgiza kai, sosai Aliya take bashi mamaki, gashi yayi-yayi soyayyar da yake yi mata ta fita daga ransa, amman abin ya faskara yarinyar duk tabi ta raina shi, yakan jure duk wani wulak'anci da zata yi masa, sannan yana lodar kayan ‘kwalam da makulashe ya bayar akai mata bata tab'a dawo masa dashi ba, amman duk lokacin da yaje tad'i gurinta bata fitowa haka kuma baya fasa komawa gobe.

•••• •••• •••

Fitowarsa daga cikin d'akin su ya shigo cikin gidan daga shi sai gajeran wando da singlet, wajan kajin sa ya nufa ya basu abinci kasan cewar yau Umma bata da lafiya tana fama da zazzab'i da ciwon kai, ‘kwayayen da kajin suka yi ya kwashe sannan ya koma wajan tantabarunsa, can saman soran d'akin tattabarun ne ya fashe suke bi ta gurin suna fita shine yau zai hau ya gyara gurin, sai da ya fito ya lek'a d'akin Umma yayi mata sannu sannan ya tambaye ta inda ta ajiye masa gudumar sa, cikin yanayin ciwo Umma tace,

“Kayi hakuri Shamsu tun jiya nake son sanar dakai, jiya ne dasu Ameer suka zo suna wasa da ita sai suka fara rigima shida khaleefa, shine fa Ameer kasan shi da mugunta kawai ya jefata saman gidan Talatuwa, ina taso ince kazo ka dakko na manta sai yanzu da kake tambaya ta.”

Tsaki Shamsu yaja cike dajin haushin yaran, fitowa yayi daga d'akin Umma yaje ya janyo tsohon tebur d'insa na sai da rake ya taka zai hau ya d'akko, dai-dai lokacin kuma Aliya na band'aki tana wanka kasan cewar babu rufi (roof/roofing) a band'akin, jin motsin langa-langan d'akin gwaggo Talatuwa taji kamar takawa ake yi, kamar ance ta d'aga kai kawai ta hango mutum a sama, shi Shamsu ma sam be kallo gurin ba saboda yama riga ya d'akko gudumar kawai yaji wani ihu wanda yasa shi saurin waigawa inda yake jiyowa. Aliya ce ya gano jikinta duk kumfa ga kuma soso a hannunta, kafin ya gama tunanin abinda yake faruwa har su Gwaggo da Fa'iza sun fito, karaf kuma idanunsu akan na Shamsu.

“Na shiga uku gwaggo zai shigo min, wayyo Allah na shiga uku ya kalle ni.”

Suka jiyo muryar Aliya daga cikin band'akin, fitowa tayi ko dauraye jikinta ba tayi ba sai zani kawai da ta d'auro taje da gudu ta fad'a jikin gwaggo, tana kuma sakin wani kukan mai tarttare da maganganu tana fad'in,

“Gwaggo dama na sanar dake Shamsu d'an iska ne amma kika karyata ni, d'azu fa ya aiko naje nace wanka ni zanyi shine sai da ya bari ya daidaici lokacin da na shiga shine zai biyo ni ta saman gida, wayyo Allah na ya kalle ni wallahi kuma sosai gwaggo.”

Cikin hanzari Shamsu ya sakko daga saman jikin sai duk a sanyaye, gabaki d'aya ya rasa abin yi sai kawai ya zauna akan bencin saboda jin kansa da yayi yana jujjuya wa, yana nan zaune a wajan ya rasa ma abinda zai yi kawai yaji muryar su Gwaggo Talatuwa sun shigo, Aliya sanye cikin hijab banda kuka babu abinda take yi, gwaggo ta hau faman kiran Umma yayin da Shamsu yayi saurin mik'ewa yana cewa,

“Talatuwa wallahi Allah bansan da mutum ba, kuma wallahi ban kalleta ba sai da naji tayi ihu na waiga dan naga a ina ne ake yi, kuyi hakuri amman ba da san raina na kalleta ba.”

Wani irin kallo Talatuwa tayi masa irin na kama raina min hankali, cikin fushi kasan cewar Aliya ta gama yiwa Shamsu sharri a wajanta tun a gida yasa tace,

“Kai tafi can ba dan na ganka da idona ba da tuni kace karya take maka, toh bari kaji na gaya maka daman duk wani abun da kake yi mata tana sanar dani, nayi tunanin iya kyautatawa ce kawai a tsakaninku, ashe kai da taka manufar to ahir d'inka akan jikata na rantse da Allah duk abinda ya sake samun ta kaine.”

Fitowar Umma daga cikin d'aki yayi matukar tayarwa da Shamsu hankali, dan baya so taji amman tunda ta fito yasan tama jiyo su kasan cewar da karfi Talatuwa ke magana,

“Dan Allah kiyi hakuri gwaggo Talatuwa, wallahi nice nan nasa Shamsu hawa sama ya d'akko gudumar da yara suka cilla masa jiya, kiyi hakuri anyi kuskure da ba'a aika an sanar daku za'a hau sama ba.'”

Tafa hannaye gwaggo Talatuwa ta shiga yi tana sallallami idanunta kyar akan na Umma tace,

“La'ilaha'illal ALLAHU! kai kaji min Amina, yanzu ke a gabana kike shedar d'anki ni kuma kike karyata ni?da idona fa na ganshi ba wai labari aka bani ba bare kice sharrin yara ne, kai Shamsu ko bamu had'a ido dakai ba?”

Mamaki ya sake kama Umma, tunda suke zaune da Talatuwa wani abun na rikici be tab'a had'a su ba, amman gashi yanzu kankanin abu ya gagara solving, Umma ta rantsewa Talatuwa cewar itace tasa Shamsu ya hau sama amman Talatuwa taki yadda itama ta rantse da Allah Shamsu yana sane ya lek'a Aliya, domin suna da hujjar cewa sai da yaji tace wanka zata shiga sannan ya tsiri d'akko gudumar tasa. Sosai rigima ta kasance tsakaninsu, hatta Asabe matar malam Rayya sai da ta jiyo abin yaki karewa ne yasa ta sako mayafi ta fito.

Koda da tazo shiga gidan su Shamsu, tararwa tayi har an cika k'ofar gidan yara da manya, da ‘kyar ta samu ta shiga ciki, a tsaitsaye ta tarar dasu, yayin da Aliyah ke kwance jikin gwaggo, nan Asabe da wasu samari manya da suka shiga gidan, suka fara bada hakuri har aka samu gwaggo ta fito suka koma gida bayan tace zata dawo idan mai gidan ya dawo dan sai an shiga tsakanin Shamsu da Aliya.

Asabe ce tayi ta bawa Umma hakuri, Saboda ta yadda da maganar da ta gaya mata kan cewar itace tace da Shamsu ya hau saman ya d'akko tunda shi bema san an cilla masa ita ba.

“Sai hakuri kawai Umman Shamsu, kinsan hallin Talatuwa bare kuma abin ya had'a da sharrin Aliya yarinyar nan marar kunya da ita.”

Numfashi Umma ta sauke tana rintsa ido saboda tsananin ciwon kai tace,

“Haka ne, ni wallahi banga dalilin da yasa Shamsu zai fara soyayya tun yanzu ba, ni duk wannan shirmen da naga yanayi akan yarinyar kawai na barshi a matsayin yarinta da kuma kuruciya, shi yasa ban tab'a hanashi abinda yake yiwa yarinyar ba, amman yanzu kinga ai dole ya rabu da ita tunda abin yazo da haka.”

Ta ‘karasa maganar tana k'ok'arin komawa d'aki saboda wani jiri da yake d'ibarta. Sallama Asabe tayi mata sannan itama ta fita, yayin da aka bar Shamsu zaune kan benci ya rik'e kansa wani irin tunani yana zuwar masa cikin zuciyarsa dan be tab'a zaton sharrin Aliya yakai wannan mizanin rashin mutuncin ba. Da kyar ya iya komawa d'akin su, dan yasan idan yaje gurin Ummansa a yanzu toh komai na iya faruwa, gara ya bari zuwa anjima yaje suyi maganar.

Ko fita kasa yi yayi har yaran shagonsa suka zo yace musu suje suci gaba da aikin su, ranar be fita ba tunda wannan abun ya faru har dare lokacin Abba ya dawo. Umma ce ta kwashe duk abinda ya faru ta sanar masa, abin ya daurewa Abba kai, dama tun a waje aka taresa ana gaya masa abinda ya faru, harda sharri ma aka had'a domin wani abokinsa cewa yayi wai an kama Shamsu yabi Aliya band'aki tana wanka yana shafarta, duk unguwar zancen ake yi sai yanzu da aka gaya masa gaskiya maganar ya gano sharri aka yiwa d'ansa.

Yana shirin kiran Shamsu, sai ga su Gwaggo sun shigo gidan nan ta zayyanewa Abban Shamsu cewar dama yana sonta yana aika mata da wasiku da alawoyi harma idan yaga zata siya abu yace shine zai biya duk tsadar abin indai Aliyah ce zata siya a gabansa. Shamsu Abba ya kira ya fito sanye cikin riga 'yar shara da wando na wasu korayen yadi, tsugunawa yayi can gefe nan Abba ya tambaye shi shin da gaske ne yayi yiwa Aliyah duk wad'annan abubuwan? Shamsu yace haka ne sannan yace.

“Amman Abba wallahi ban tab'a nufar wata 'ya mace da niyar yin wani abu makamancin wanda suke zargina akai ba, wannan d'in ma tsautsayi ne wallahi bansan tana ciki bama.”

Cikin mamakin jin kalamansa gwaggo tace,

“Kaji min yaro, wato dama haka kake ko Shamsu? Toh daman d'azu babarka ta karyatani yanzu kuma kaima ka karyata ni, babu abinda zance muku sai na gode kwarai, ke Aliyah tashi mu tafi gida”

Ganin yadda gwaggo ta dauki zafi yasa Abba saurin dakatar da ita.

“Gwaggo ki tsaya dan Allah ai kowa yaji abinda ya faru ko da Shamsu yace bada niya yayi ba
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment