Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

b'ace. Faysal ne ya bugi gefen kafad'ar Salman tare da cewa,

“Toh kai abinda na kasa ganewa shine, shin kana sonta ne kokuwa dai kara yawa kake yi da ita?”

“Wallahi nima ban sani ba Faysal, ban san tak'amaimai wane iri nake ji akan Khadija ba, ina sonta ban sani ba, bana sonta shima ban sani ba kawai dai naji ina son kulata wani lokacin, gashi idan muna waya ko idan mun had'u a hanya wallahi bana jin wani abu akanta.”

“Kai dalla can baka sonta haka kawai zaka ce bawai ka tsaya rainawa mutane hankali ba, idan banda rainin hankali ai abu uku ne zaka zabi d'aya, kodai kana so ko baka so ko kuma kawance kake da ita, meye na tsayawa yi min kwana-kwana.”

Shafa kai Salman yayi tare da huro iska daga cikin bakinsa, kasa cewa komai yayi domin babu abinda zai fad'a dan haka ya mik'e yana gyara wuyan rigarsa tare da kallan Faysal yace.

“Abokina zan wuce, idan na samu amsar tambayoyinka zanzo na sanar dakai, amman yanzu bani da ta cewa, sai anjima mu hadu a gidan kallo ya za'a buga mai zafi.”

Faysal ya tab'e baki tare da mikewa shima ya shige cikin gida.

A can b'angaren su Umman Shamsu kuwa sun tattauna maganganu ita da aminiyarta wato mahaifiyar Khadija akan yadda suke son komai ya tafi ba tare da ko wanne b'angare yaga anyi masa rashin adalci ba. Umma ce zaune akan sallaya ta idar da sallar magriba taji kira, tana dubawa taga sunan auta, cikin murmushi ta d'aga tare da karawa a kunne tayi masa sallama cikin farin ciki,

'”Assalamu alaikum Ummah nah.”

“Wa'alaikas salam d'an auta yaron kirki, ya kake?'”

Shamsuddeen dake zaune kan teburin cikin abinci a wani katafaren restaurant gabansa drink ne kawai yana sha, bayansa ya jingina a jikin kujerar yana sauraran Ummansa wadda yake jin tamkar yayi tsintsuwa yaje ya ganta, ya shafa kwantaccen bakin gashin dake kwance a hab'arsa tare da cewa,

“Umma lafiya ta kalau, sai fama da rashinku a kusa dani, ina Abba ne? sai kiransa nake amman ana cewa a kashe take.”

“Aikuwa nima kaga sai kiransa nake bana samu da yake nazo nan gidan Maman Khadija.”

Cikin murmushi mai d'an sauti Shamsu yace mata,

'”Ahh yau ankai ziyara kenan? Umma a mika min gaisuwa wajan Maman.”

Dai-dai sannan Maman Khadija ta shigo dakin hannunta dauke da tray na abincin da ta kawowa aminiyar tata.

“Gata ma kawai ku gaisa.”

Cewar Umma tana mika mata wayar. A kunne ta kara cikin kulawa itama ta fara yi masa magana, cikin girmamawa ya gaida ita ta dinga sanya masa albarka sannan ta mik'awa Umman sa, hirar sukaci gaba da yi lokacin ne Khadija ta shigo hannunta d'auke da jug na ruwan sanyi ta kawowa Umma ta ajiye mata a kusa da tray din abincin, tana k'ok'arin fita Umma ta dakatar da ita ta hanyar cewa.

“Khadija zoku gaisa da Shamsuddeen.”

Khadija ta juyo tare da zuwa kusa da ita, ranta duk babu dad'i sai dai babu wanda zai fahimta sakamakon murmushin yak'en dake saman fuskarta.

“Shamsu ga Khadija ku gaisa.”

Cikin rashin damuwa Shamsu yace.

“Okay Umma bata”

Mik'a mata Umma tayi tare da juyawa tana kallon aminiyar tata, a hankali ita kuma Khadija ta fice daga d'akin ta koma nata sai faman tsuke fuska take tamkar yana kusa da ita tace.

“Ya karatu?”

“Lafiya lau khady ya naku karatun?”

Yadda taji muryarsa sai yasa ta fara tunanin anya wannan Shamsun da ta sani ne a baya kuwa? Wannan muryar bata san ma yadda zata fassara yadda taji taba domin jikinta ko'ina sai da ya amsa, amman da ta tuno waye Shamsu da wad'annan shegun d'inkunan nasa sai ta kuma had'e rai kai kace suna tare yana ganinta, sai da ta zauna a bakin katifarta kafin tace dashi.

“Normal wallahi ai na gama tuni.”

“Secondary school kika gama ko?”

“Eh amman ai zan cigaba dan har nayi jamb.”

Shiru taji yayi har tayi tunanin ko ya kashe hakan yasa ta tab'e baki tana kallan screen d'in, still taga yana nan bawai kashewa yayi ba, ta kuma maida wayar jikin kunnata sai taji yana cewa.

“Masha Allah ai hakan yana da kyau, nasan yanzu kin kara girma ko khady?”

Tsaki yaji tayi hakan yasa shi bud'e ido tamkar yana gabanta, cikin basarwa dan kar tayi tunanin ko da nufin iskanci ya fad'a yace mata.

“Ina Umma bata wayar.”

“Bari na kai mata tana d'akin Maman mu.”

“Su khady harda warewa wai Maman mu, toh mu kuma fa? Ko an cire mu daga ciki?”

Khadija ta harari wayar ji take tamkar ta shiga cikin wayar ta shako shi, sam Shamsun baya take tunani bata san yanzu ya kerewa saninta ba, dan haka da sauri taje ta mik'awa Umman sa wayar ita kuma ta baro d'akin hankalinta na kan wayarta tana jiran Salman ya bugo mata suyi hira. Shamsu kuwa basu dad'e da Umma ba ya katse ya kira Yaya Garzali har ya bawa matarsa aunty Afiya suka gaisa kafin yace dashi.

“Kanina bari naje na d'akko Umma na maida ita gida, idan na dawo zan kiraka sai mu k'arasa maganar.”

“Toh babban Yaya a dawo lafiya.”

Daga haka suka ajiye wayoyin, inda Yaya Garzali ya tafi d'akko Umma shi kuma Shamsu daga inda yake tashi yayi ya koma hostel daman yazo nan ne dan karsu Afrah su dameshi kasan cewar duk inda yake zama ta sani nan d'in ne dai bata gano ba kuma baya fatan ta gano sabida shi sam baya wani son suyi mu'amula ko wace iri ce da mace sabida abinda Aliya tayi masa ya kasa barin zuciyarsa, gani yake kamar duka mata masharranta ne dan haka yake kafa-kafa da rayuwarsa yake baya-baya da duk wata d'iya mace..

•••••. •••••. •••••.

Result din su Aliya ne ya fito na SSCE wato ‘senior secondary school certificate na waec da neco..’ kowannen su yaci dai-dai gwargwadon yadda ake buk’ata, Dan haka tuni Baba sulaiman ya cike musu komai na jamb, Fa’iza Mbbs aka sanya mata wato ‘medicine/harkar lapia, second option kuma ya sanya mata agricultural engineering. Ita kuma Aliya da ta karanci Art ya cike mata first option dinta da Law, second option kuma Library science duka kowannen su gurbin karatun jami’ar Bayero yacike musu. Sannu a hankali kowaccen su ta dage da karatun jamb dan guntun fad’uwa, domin baba Sulaiman yace idan suka fad’i tofah yi musu aure shine mataki na gaba, ‘ABU mai labule kenan..’

Ana’i gobe zasu zana jarabawar Aliya taje gidan su ‘kawar su dake nan baya dasu wato A’ilo ‘kwaila wadda sukai boarding school tare, A’ilo nada waya dake ita batada burin cigaba da karatu, dan haka suna ‘kare karatu form master ‘dinsu dake nemanta ya turo akai magana da kudin zancen su a hannu, aka tsaida ‘yan watanni masu zuwa za’ai bikin, wayar A’ilo da ita Aliya ke karba tana waya da Sahal, kamar Kullum tana shjga gidan kai tsaye da sallama ta shjga dakin A’ilo dake kwance tana waya da saurayin ta, wato class teacher ‘dinsu na da dake sumaila, Aliya ta zabga tagumi har A’ilo tagama wayar tata, nan sukai ‘yar hirar su kafin Aliya cikin sauri tace da A’ilo,

“Aikin dai kenan, Kullum cikin waya, tun baki tafasa ba zaki k’one, wannan dai gwara ai auren ku cinye junan ku”

Ta ‘karasa fad’a tana kara wayar a kunnen ta, da alama ta kira Sahal ‘din, A’ilo ta tuntsire da daria kafin ta mike tana mik’a, sai da tai mai isarta kafin tace,

“Lokaci na ne, Dan haka nafi gaban k’onewa ma ingaya miki, inde akan malam Sadeeq ne to fa na babbake wallahi, ba gwara ni bama akan ki, gama wayar dai, bara na shjga band’aki..”

Cewar A’ilo kafin ta shiga band’akin ta dake cikin ‘dakin, Aliya kuwa tuni ta nutse cikin kogin soyayya, Dan da alama batama ji abunda A’ilon ke fad’a ba, cikin sake shak’e muryar ta tace,

“Dan Allah Ya Sahal kazo goben mu had’u a school, wallahi nayi missing ‘dnka da yawa...”

Sahal dake zaune akan kujerar ‘dakin sa, sai faman yatsina fuska yake, wayar tasa na kare a kunnen sa yana amsa Aliya, cikin tab’e baki yace,

“Zan duba nagani...”

“Uhm, uhm Ya Sahal, ni..ni kawai kazo..”

Kamar tana gaban sa, ya had’e rai kafin yace,

“Zan kai Husnah ma, dunno ko wuri ‘daya zaku yi, A’ina zaku zana...?”

“Ya Sahal ni a new site ne fa..”

Cikin sub’ucewar baki yace,

“Fa’iza fa?”

Kamar tana gaban sa yai saurin rufe bakin sa yana danne dariar data taho mai, da alama mutuniyar taku bata gano shi ba, domin ca tai,

“Ya Sahal nasan duk dan saboda bakason ganin tane yasa ka tambayi haka, kasha kurumin ka domin Fa’iza a old site zatai tata..”

Hamdalah ya sauke, jin a tare suke da Husnah, bugu da ‘kari kuma yanason sake tozali da kyakkyawar fuskar ta, cikin waskewa yace,

“Okay glad.. Till then Liya, Taya zamu had’u kenan?”

Cike da jin dadi Aliya tace,

“Zan ari wayar Gwaggo! Sai anjima Ya Sahal I love and miss you...”

“Okay bye..”

Kawai Sahal yace, kafin ya katse kiran, cike da jin dadi ya ‘daga hannuwa sama yana mai-maita,

“Yes...Alhamdulillah!”

A’ilo dake gefen Aliya ta buga tsaki tana fad’in,

“Toh Romeo ta Juliet bani wayata tunda kun gama farantawa juna rai..”

Aliya tai murmushi, tana yin ‘kas ‘kas da yatsun hannayenta kafin cikin kad’a idanuwa tace,

“Ai soyayya akwai dadi, Allah dai ya barmu da masu son mu...”

“Toh Ameen...Kuyi aure kawai..”

“Hmm! Da za’ai hakan sai nafi kowa jin dadi, Sai dai kash Baba Sulaiman yanaso muyi karatu, Kuma burin Ya Sahal ma shine yanason ya auri cikakkiyar ‘yar boko..”

A’ilo ta tab’e baki, kafin cikin rashin damuwa tace,

“Ai se kuyi tayi, lokacin da zaku kammala boko nasan na haifi yara uku ko hudu..”

‘Mtcew! Aliya taja tsaki tana tura ‘daurin ‘dankwalinta gaba, wato ture kaga tsiya, sai da ta jera tsaki uku, tanayi tanaiwa A’ilo kallon Kin renawa kanki hankali kafin tace,

“Ke fa A’ilo gwara kowa dake, ai da bari kikai ki zama babbar mace ba ‘kwailar ki ba, zaki kama ki wani aure yanzu, auren ma da ba zamu wani gyagije muyi rawa ba, Kin kama kin wani tsayar da malam sadeeq a matsayin mijin aure, bayan kinsan yadda yakewa mutane kwarji ni, banza mai kan kwa-kwa...”

A’ilo tayi dariar ta mai isarta kafin tace,

“A kwailar dai aka ganni aka susuce har aka aiko da kudin aure, a kwailar kuma zanyi aure nabar masu shi fal kirji, a kuma ‘kwailar ne zan auri shalelen maza, kuma dole a zube a gaida miji na a wajen biki, sani ne baki ga wallahi da sunji lapiyayyun hannu zasu tashi kamar funkaso..”

Aliya ta mike tana zaro idanuwa kafin tace,

“Su waye zasu tashi kamar funkaso?”

A’ilo tasa tasa hannu tana nuni da kirjin ta, Aliya ta shjga daria ba ‘kakkautawa, sai datai mai isarta kafin tace,

“Kinfi ‘karfina A’ilon Form master. Ta Malam Sadeqeqe mai komai dozen, sai kinji ni, idan Inna tadawo ki gaisheta..”

Ta ‘karasa fad’a tana zura takalmanta, har ‘kofar gidah A’ilo ta rakata, tana musu fatan samun nasara a jarabawar da zasu zana..


*WASHEGARI*

Da wuri su Fa’iza suka shirya don tafiya zana jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire, Fa’iza ta shirya cikin doguwar riga baka ta yane kanta da bak’in mayafin rigar, batai wani kwalliya ba ta dai shafa jan jambaki, Aliya kuwa shigar doguwar riga tayi dinkin A shape, blue ce an mata kwalliyar pink, ta yafa mayafi pink komai pink hatta jambakin lebanta, karfe bakwai saura kwata Baba Sulaiman ya ‘debe su a motar sa, Fa’iza ya fara saukewa a old site, ya wuce da Aliya new site dake can gwarzo Road.

Tunda Baba Suleiman ya sauke ta a wajan venue d'in ta take ta faman d'aga kai ko zata hango ta inda Sahal zai bollo amman shiru, ko wacce mace idan tazo gurin takan yi k'ok'arin yiwa na kusa da ita magana amman Aliya tunda ta diro daga mota batama nufi inda suke ba bare tayi kawa, duk hankalinta yana wajan da duk tasan mota ko d'an Adam zai bollo amman shiru. Yayin da shi kuma Sahal yana zuwa yayi parking Husnah ta fito, shima fitowa yayi tare da kulle motar ya zura key d'in cikin aljihun jeans d'insa blue yasa yellow d'in riga armless gashin kasan sai sheki yake yi, da mamaki Husnah ta kallesa tare da tsayawa tace dashi.

“Yaya Sahal ina zaka kuma?”

“Rakaki venue d'in zanyi.”

“Ahhhh ka barshi ai nasan wajan kayi zamanka a mota.”

Kallanta yayi sai yaga tamkar ta gano abinda yasa shi biyo ta, amman dan ya tabbatar da ta gano ko bata gano ba sai ya yatsina fuska tare da kallan gefe yace......

——-
_Afuwan jia bakuga post dina ba, hakan ya faru ne abisa rashin ajiyayyen Page da bani dashi, dake 2 Pages din dana turo shekaran jia waccan da washegarin ta nayi su ne tun kafin rasuwar baba, Shiysa ku kaga banyi post jia ba, bugu da ‘kari kuma kunsan da glass nake amfani, sanyin nan idanun sai a slow wallahi, kuyi mana uzuri dan Allah.. wallahi abubuwanne sai a slow😢🤲🏻_

T/U21/22/S


*MISS XOXO🧕🏼*


“Ki wuce ki tafi, idan ma dani ne bakya son jerawa toh yi gaba.”

Dariya tayi tana juyawa ta fara tafiya tace,

“Kaji Yaya Sahal da wata magana, nidai nayi nan.”

Sai da tayi nisa sannan shi kuma ya fara tafiya a hankali yana kallan duk wani group da yaga mata sunyi, Saboda ya gano inda Fa'iza take, tun yana dubawa har ya fara hakura yana tunanin ko basu karaso ba, Amma dan ya tabbatar da suna ina sai ya kira layin da Aliya take kiransa, a kashe yaji amman duk da haka bai hakura ba sai da ya kira numbern Gwaggo Talatuwa, cikin sa'a yaji muryar Aliya kafin ta fara masa magana yayi saurin cewa,

“Liya, kun karaso school d'in kuwa?”

Cikin shagwab'a tace,

“Yaya Sahal tun d'azu nake nemanka mun karaso gashi mu har zamu shiga, ka tafi ne ko zaka tsaya Husnah ta kammala.?”

Yayi shiru yana shafar sajen fuskarsa, baya son su had'u da ita yau sam, Amma kuma baya so yayi mata karyar cewa tafiya zai yi ya zamto kuma ita tazo nan inda suke tayi wani tunanin akansa, dan haka cikin damuwa dan ba haka yaso ba yace da ita,

“Zan jirata, Amma da kyar idan zanzo nan side d'in.”

Sautin murmushinta yaji a cikin kunnansa wanda yasa gabansa fad'uwa, shi kansa yasan yanzu bashi da nutsuwa saboda b'oye abubuwan da yake yi sai yaga tamkar mutane sun gano shi, ji yayi tana cewa,

“Please Yaya Sahal da har zan roki alfarma nace ka taimaka ka kawo Fa'iza nan kawai saboda idan Baba yaxo d'aukar mu kawai yazo nan ba sai yayi wahala ba, dan Allah my love ka kawo ta ko kuma ni kazo ka daukeni ka kaini wajan ta.”

Wani shu'umin murmushi ne ya kubuce masa wanda shi kadai yasan ma'anarsa, cikin rashin damuwa yace da ita,

“Okay karki damu indai ta yadda zan kawo ta kinsan 'yar uwar taki ta tsaneni ke kuma har yanzu kinki ki cusa mata soyayya ta a cikin zuciyar ta.”

Daria Aliya tayi daga ‘bangaren ta, kafin tace dashi,

“Ya Sahal kenan...Kasa a ranka Fa’iza zata so ka, So irin wanda y’ar uwa takewa masoyin y’ar uwarta, zata so ka a matsayin mijina to be, kuma zata ‘kara son ka idan mukai aure, karka wani damu Ya Sahal, Nasan sissy ‘dina, batada matsala, kawai dai wani lokacin tanada wuyar sha’ani..”

Sahal ai daskarewa yai, tun lokacin da yajiyo ta tana sharara maganar idan sukai aure da sauran su, ya kasa tantance a mummunan yanayin da ya samu kansa, illa kawai yayi dakiya yaita maza, cikin murya a sanyaye yace da ita,

“Okay Liya.. Idan na ganta Insha Allah zamu taho tare, best of luck..”

“Okay Ya Sahal, Thank you, Bye..Love y...”

Bata ‘karasa ba Sahal ya katse kiran, yana mita ‘kasa-‘kasa, kamar ance ya juya, idanuwan sa suka mai kyakkyawan tozali da sahibar tasa Fa’iza, kamar ana kad’ashi da ruwan kanwa haka jikinsa yake ingizashi da yaje gare ta, cikin sauri ya ‘karasa gare ta, alokacin ita kuma tana saka littafin key point na physics a cikin madedeciyar side bag din jikin ta, ta gefan ido ta hange shi, cikin sauri ta juya zata tafi ya riko jakar ta, zata sakar masa yai saurin fara mata magana cikin marairaicewar murya,

“Fa’izahh! Dan Allah ki dakata ki saurare ni..”

Cikin zuciyar ta tace, ‘shege sai iya kalamin furta sunan mutane a baka, a zuci kuma mayaudari ne’ Dan karamin bakinta ta murgud’a masa kafin tace dashi,

“Ya akai?! Menene? Exams zan shiga pls, idanma wai kana dakatar dani ne, kar na fadawa sister na ganka to kasha kuruminka, ba wannan damuwar bace a gabana ba yanzu, itama Ina fatan ta farga tagano kai din mayaudari ne..”

‘Nanata kalmar mayaudarin yayi a zuci, Sosai kalmar ta dake shi, amma ya maze kawai yace da ita,

“Hmm! Kece kike ‘daukata haka, wallahi Allah yasani ba yaudarar y’ar uwarki nake yi ba, Dan Allah kidena gayamin wa’ennan kalaman dan Allah na roke ki, abu na biyu kuma idan kingama zan kaiki wajen Liya, munyi waya da ita tace na..”

Bai ‘karasaba Fa’izahh tai masa kallon tara saura kwata, kafin cikin tab’e baki tace

“Inada ‘kafafuwa, Sannan nasan hanyar da zan bi naje gare ta, akan wane dalilin za...”

“Dan Allah dan annabi kar mu tsaya muna ja’in ja dake Fa’izahh! Wallahi Liya ce tace na kaiki wajenta idan kungama.. Pls I beg of you, karki musu na hadaki da Allah.”

Ajiyar zucia ta sauke, kafin cikin sauri ta karasa wajen da ake tantace su kafin su shiga dakin zana jarabawar, Cikin sanyi jiki Sahal ya bi bayanta da kallo yana kissima abubuwa da yawa akanta....

Sai ‘karfe sha biyu saura kwata suka gama exams din, Husnah ya hanga tana tsaye ita da mardiyya y’ar makociyar su, a bakin exam hall din suna bayani akan questions papers din dake hannun su, Sahal yai baya da sauri yana kiran wayar Husnah, dagawa tayi tana cewa,

“Hello Yaya..!”

“Husnah! Yaya kungama exams din?”

“Eh wlh Yaya Sahal, Exams din was superb..”

“Masha Allah ! Nace kinga wani uzuri ne ya tasomin, zaki jira nagama nazo na dauke ki, ko zaki tafi a ‘Dan sahu?”

“Laa! Bakomi Ya Sahal, kaje kawai, kaga Mardis ma tare mukai exams din, driver dinsu yana nan, Zan bisu kawai”

Ajiyar zucia ya sauke, Wadda har Husnah ta jiyo ta, ya ‘dau sakanni kafin yace da ita,

“Okay Alhamdulillah! Sai na dawo.”

Sallama sukai da ita, yana hango lokacin da suka shiga motar gidan su Mardiyya suka tafi, ba a ‘dau lokaci ba Fa’izah tafito tana waige-waige, Sahal ya ‘dauka shi take nema, cikin sauri ya nufi inda take, Sai dai kash kafin ya ‘karasa ya hango wani matashin yaro kyakkyawa ya ‘karasa wajenta, nan ya hango suna magana, Fa’izahh na faman sakarwa yaran murmushi, wani tukukun bakin ciki ya taso ya tokare a makogaron Sahal, duk daukar sa sabon saurayi tayi, a lokacin kuma biron data ara ne awajen yaran ta mayar masa tana godia, shi kuma ya tsaya yana bakomai har suka shiga maganar yadda exams din sukai dadi..

Cike da ‘bacin rai ya ‘karasa wajen, Lokacin kuma matashin yaron mai suna sudeis, sallama yakewa Fa’izahh, cikin dakilewar murya Sahal yace da ita,

“Wuce muje malama..”

Da alama bai masan ya fad’a ba, Sudeis duk daukar sa yayantane jin yadda ya bata umarni, Don ita kanta Fa’izahh tayi mamaki, ganin wannan ‘karfi da yaji irin na Sahal, hannu sudeis ya mikawa Sahal yana fadin,

“Barkada rana yayanmu..”

Wata shegiyar harara Sahal ya cilla masa, kafin ya dubi Fa’izah yana bata tata rabon hararar, jiki na rawa ta rab’a ta wuce motar sa, ya bi bayanta yana k’ok’arin danne bacin ran sa, Sudeis dake tsaye sangangan shi kadai ca yai,

“Ikon Allah..”

Sahal na shiga mazaunin driver yasa key, Fa’izahh dake gefe sai raba idanuwa take yi, tarasa akan meyasa yake wannan bace-bacen ran, figar motar yai a dari, har yana bulawa Sudeis kasa, ko a mota shi da ita babu mai yiwa wani magana, Sai dai wakar ‘particula’ dake yi a hankali.

Har suka karasa new site, Kafin su k'arasa wajan da su Aliya suke yayi parking yana dukan steering cikin zafin rai wanda yake k'ok'arin had'iyewa. Da kyar ya iya saita kansa yayin da ita kuma taki kallansa saboda bama tasan cewar yana cikin b'acin rai ba.

“Waye wancan yaron?”

“Yana ina?”

Itama ta tambayesa tana kallan waje ta glass, d'an tsaki ya saki ba tare da taji ba ya sake cewa,

“Wanda kuka tsaya dashi.”

“Saurayi na ne

Daram! Zuciyar Sahal tayi wani mugun bugawa wanda har sai da yasa hannu ya dafe gurin, kafin yayi wani abun wayarsa ta fara ringing amman ya kasa koda kallon wayar bare ya d'auka. Kauda kai Fa'iza tayi tana d'an yatsina fuska yayin da Sahal ya d'ago da kyar ya kalleta murya na rawa yace mata.....

*SWITZERLAND*
*UNIVERSITY OF ZURICH*

Zaune Shamsudden yake a waiting area dake farfajiyar sashen chancellors office, wayar sa ce a hannun sa yana dannawa, sai ka ‘dauka chatting yake, ganin yadda yake ware idanuwa yana bin rubutun da kallo, sai da yai zooming ne na gano PDF ne na littafin Karl max, mai suna classical theory of Have and Have not, wayar ce tai kukan agaji, danna Bluetooth din kunnen sa yai, yana sake ware rubutun littafin da alama nazartar sa yake ta nutsuwa, a hankali yace,

“Speak..”

Yazeed yai daria kafin yace,

“Arrogant being kenan! You and your arrogant manners ehh! That aside! Wai har yanzu baka gama da shi ba?”

“Maza, mutanen nan ai basa ganewa, nayi rejecting abu several times sunki yadda..”

“Maza kila alkhairi ne wallahi.. Beside abune babba da zai kawo maka arziki, kasani ko ka zama second dangote?”

Murmushi Shamsudden yayi kawai wanda har saida Yazeed ya jiyo alama, cikin i don’t care tone yace,

“Rabu dasu, ai ka..”

Bai ‘karasa ba sectarian din office din chancellorn tafito tana cewa dashi,

“You may enter...”

Katse kiran yayi, ya shiga cikin office din, cikeda girmamawa suka gaysa da chancellor din mai suna, ‘Professor Nathaniel Peter Zion’, Nan suka shiga maganar, Duk cikin harshen turanci, Kallo d’aya zakai wa fuskar Shamsudden ka gano ransa bayaso, Mika masa envelop Chancellor din yayi, hannu biyu Shamsudden yasa ya karba, sukai sallama ya fito daga ciki, cikin sauri ya kira Yaya Garzali yana sake nanata masa,

“Yaya kagani ko? Yanzu gashi nan mutumin nan har yabani papers dinnan a hannu gasu, shysa yaya tun wuri nace maka zanyi rejecting kace a’ah.”

Garzali da zuwan sa gidan su Ummah kenan, ya zauna a hannun kujera yana waya da Shamsudden, sai da shamsu yagama tsab kafin yace,

“Tun ran gini tun ran zane Shamsudden, Allah ya rugada yayi sai hakan ta faru, kuma abunnan karuwar ka damu dukane, ciki harda al’umma baki d’aya, Saboda kayi sallah ka godewa Allah bisa ga wannan babbar kyauta da yayi maka, acikin mutane dubbai, amma Allah ya tsamo ka yasanya hakan a d’aya daga cikin hanyar arzikin ka, Sai ka godewa Allah domin shid’in mubuwayi ne gagara misali, addua ba wacce bamuyi ba, amma dake alkhairi ne gashi dai sai da ta tabbata, kana jina?”

“Inaji Yaya, kawai ni ina ganin kamar nayi ‘karami da wani zama shugaban consulate office na Switzerland a Abuja, baya da haka ma yaya sabuwar embassy din da sukeyi a anan kano ma ni zan zama representative dinsu, Yaya dan Allah ku bari nayi rejecting dinsu pls, tunda nanda wani lokaci zan kammala makaranta na bar musu ‘kasar su..”

Garzali ya shiga bashi baki yana mai nasiha mai ratsa jiki, dakyar Shamsudden ya yadda badan yaso ba, yana katse kiran kuwa ya shiga nanata kalmar,

“So intolerable..”

“Pulchritude!...”

Karaf Shamsudden yajiyo muryar Afrah a dodon kunnen sa, bacin ransa ya dadu akan na da, yarasa mai yasa yarinyarnan bata iya controlling kanta a gaban sa, cikeda bacin rai ya juya. Karaf.........

*23/24/S/A/F/S*

*MISS XOXO🧕🏼*

“Saurayin ki..?!”

Ya tambayeta cikin tsantsar mamaki, kanta na kallan window taki kula shi saboda bataga dalilin da zai sa ya d'akko magana, ya zauna yana yi mata wad'annan tambayoyin ba. Numfashi taji yaja mai matuk'ar karfi, kallanta yake ta baya ganin yadda ta d'auke masa kai, tabbas ya yarda soyayyar gaske yake mata ganin yadda take faman wahalar da zuciyarsa, ya mik'a hannunsa da nufin rik'o nata sai kuma yayi
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment