Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

zai yi kyau ba, bare wata a cikin su ta gano cewar yafi sonta a kan wata, tasan sai kishin yafi tsananta.

A wajan Aliya kuwa harta gaji da neman Mu'azzam ta zuba ido taga ta inda zai bullo mata, ta sanar da Umma ita kuma ta sanar da Baba Suleiman sai cewa yayi ai an shaida masa cewar yayi tafiya ne amman yana nan dawowa sai gabannin biki, hakan ne yasa hankalin Aliya ya samu nutsuwa taci gaba da karatunta hankali kwance.

•••••••√ •••••••√ •••••••√ •••••••√

*Bayan wasu lokuta; Saturday*

Akwatuna goma sha biyu masu tsananin kyau da tsada sai carpet da wata katuwar Ghana must go aka shigar cikin gidan Baba Suleiman, dama maza ne suka kai ba mata ba hakan yasa babu wani hayaniya aka fito musu da kayan motsa bakin da aka yi musu suma aka sanya musu a mota suka tafi. Kayan lefen Fa'iza ne aka kawo makota da suka shigo gidan da 'yan uwan Umma dana Baba Suleiman duk sunzo gani, haka aka dinga d'aga kayan masha Allah babu abinda babu a ciki. Aliya ce tayi video ta dinga turawa Fa'iza tana gani kasan cewar tana makaranta, kasan cewar Umma tasan daga gidan da aka kawo kayan hakan yasa bata shiga wani mamaki ba dan sati d'aya kenan da Baba Suleiman ya kirata ya karanta mata duk abinda yake faruwa.

Aliya kuwa tafi kowa murna kai kace ita aka kawowa sai taya Fa'iza murna take yi, wacce itama take ta nuna jin kunya, ta turawa Shamsuddeen text message din godiya tare da addu'ar karin budi a cikin lamarinsa. Yana gama karantawa yayi murmushi tare da jujjuyawa akan kujerarsa da yake yana zaune a office d'insa. Bayan ta gama ganin kayan ne ta gama tabbatarwa da zuciyarta cewar Shamsu yana sonta dan idan ba soyayya babu abinda zai sanya shi hado mata wad'annan uban kayan. Bayan sati biyu da kawo kayan auran Fa'iza aka kawo na Aliya wanda itama Baba Suleiman ya nemi alfarmar maza su kawo dan baya son gulmace-gulmace idan aka had'a mata, itama 'yan uwan babanta dake bunkure sunzo ganin kayan. Akwatuna ne set uku different colors masu tsananin kyau da tsada na designer din Victoria secret, da Louis Vuitton sai dolce and Gabbana, Gaba d’aya sai kallo ya koma kan na Aliya, fadar yawan kayan da tsadar suma ‘bata lokacine. Toh dama haka abun yake ko a yatsun hannu ma wani yafi wani tsawo da kauri, sai dai muce TubarkAllah kawai, domin duk kanin kayan babu na yarwa, Daga Fa’izah har Aliyan sunyi goshi. Sai fatan ALLAH yasanya alkhairi yasa kuma kowacce ta shiga gidan ta na sunnah a sa’a.

Toh mai karatu tunda aka kawo lefen nan daga Fa’izah har Aliya kowannen su zuciar sa babu dad’i. A ‘B’angaren Fa'iza tun sanda tafara istikhara domin neman zab’in ALLAH taji zuciar ta na cire mata son Shamsudden, Sosai yake raguwa har take jin tamkar tasamu Baba Sulaiman tagaya masa itafa ta fasa auren Shamsudden yazo ya karb’i kayan lefan sa. Gaba d’aya haushin Shamsudden din take ji, tarasa mai yasa? Lokuta da dama takan zauna tayi ta kuka ita ka’dai. Gashi koda wasa batason taji ana maganar yadda bikin su zai kasance sosai zuciar ta ke mata rad’ad’i, haka kayan ma bata gayawa kawayen ta ba sai da Aliya tafad’a musu suka zo suka gani ciki harda husnah data kasa b’oye farin cikin ta, Fa’izah tarasa meyasa tafarin wani sabon al’amari yafara bijiro mata akan soyayyar wanda yadena sonta yanzu....

‘B’angaren Aliya ma kusan hakanne, Ta kan zubda hawaye a duk lokacin data tuna Mu’azzam ne zai zamto miji agareta tunda yakawo lefe, Gashi ya ‘dauke kafa dif, Kiran dunia tai masa layikan sa duk a kashe. Shikenan yanzu wanda bayason ta zata aura? Ita kuma haka tata ‘kaddarar take? Gaba d’aya rayuwar ta ta baya ta shiga nazari, siraren hawayenta ta goge, tana mai cigaba da goge kayan da zata saka gobe taje school.

•••••¥•••••¥. .•••••¥••••¥••••¥

*LIBROS/CAFFE 24*
(SAB PENTHOUSE AND MORE)

Zaune yake a office yana faman jujjuya kujerar da yake akai, kansa a sama yana kallon p.o.p, tunaninta yake yi wanda ya zamto masa jazaman kullum sai ya yi shi. Tashi yayi ya nufi inda da take a matsayin Secretary dinsa. Tunda ta tafi shikenan kuma ya kasa ‘daukar wani secretary’ ‘din, lumshe idanu yayi yana shak’ar kamshin ta kujerar, zama yai akan kujerar yana shafawa, daga gefan desk ya idanuwan sa suka sauka akan wani dan karamin abu, sa hannu yai ya ‘dauka ya murda saman sa ashe jambaki ne kalar pusher pink, tabbas na Aliya ne domin yana yawan ganin sa a dan karamin bakin ta, murmushi yayi ya zura shi a cikin aljihun gaban rigar sa, Dake wando da riga ne a jikin sa, bakin wando farar riga da bakar Pcap. Car key dinsa ya dauka ya fice zuwa wani shagon sayarda kayan anything girly mai suna go gorgeous. Yar siyayya yai kadan ya kamo hanyar dawowa. Yana shawarar yadda zai je Buk yaga Aliya don ya jima baiyi

BUK

A lokacin kuma Aliya tashiga school, lecture d’aya zasu yi ta Ya Gazah, kammalawar su kenan Ya Gazah ya kira ta lokacin ya bude gaban motar sa ya ciro wasu takardu na filin Shamsudden daya siya wanda har an soma ginin sa a Nassarawa LG. Unguwar magaji rumfa, Alu Avenue. Mika mata takardun yai dake cikin wata zungureriyar envelop brown color an like ta.

“Aisha ungo dan Allah, Ina sauri ne zamu shiga meeting da senate board members akan strike dinnan da za’a tafi, ki kaiwa Shamsudden yanzu pls, kice masa lawyer din zai kira shi, idan na dawo zamuyi magana dashi.”

Aliya ta gyad’e kai, tasa hannu biyu ta karb’a da dan rissinawa, cike da girmamawa tace,

“Okay sir! In Sha Allahu zan kai masa.”

Godia ya mata sannan su kai sallama kowanne ya kama gaban sa. Wurin su Nour ta nufa, dama a lokacin labari Nour din ke basu akan yawan carryovers din da tasa mu. Da yadda su lamfat suka sanyata a watsattsiyar hanya. Cikin motar Nawal suka shiga duk kanin su domin dama sun gama lectures na ranar, Nour sai kuka take tana dana sanin rayuwar ta. Pinky ‘kawar su dake gabar motar ta dan bubbuga bayan Nour tana fadin,

“Bari na gaya miki wani wa’azi da ummah ke gaya mana kullum.. Matsayin mata da darajar su a addinin Musulunci. Mace itace mutun na farko da ta fara karban addinin musulunci wato Uwargidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi (Nana Khadija bint Khuwalid). Allah ya bayyana cewa ita mace abokiyar rayuwar namiji ce, ya kuma mutunta ta a cikin mutane. Har ila yau kamar yadda suke tarayya da maza wajen samun ladan aikata aiki nagari, haka kuma suke samun zunubi wajen aikata mummunan aiki. Kamar yadda yazo a fadin Allah (S.W.T) yana cewa: "Wanda ya aikata aiki nagari, namiji ne ko mace alhali yana mumini lallai za mu raya shi rayuwa mai dadi, kuma za mu saka musu ladansu da mafi kyawun abin da suka aikata,

“Wani gata da musulunci ya yi wa mace shi ne, haramta mayar da ita kayan gado da ya yi, sannan ya tabbatar da cewa a ba ta gado idan miji ko kuma wanda gadonsa ya wajaba a gare ta ya mutu. Bayan haka musulunci ya duba alfarmar mace ya martabar ta, ya darajar ta sannan kuma ya daukaka ta ya zaba mata yin hijabi (sutura) wadda za ta rufe jikinta domin kare mutuncinta, Allah (S.W.T) a cikin hikimominsa da ba za sa, ya halicci halittu guda biyu wato mace da namiji ya kuma sanya kowanne ya zama abokin rayuwar dayan, ko da rayuwar dayan za ta yiwu ba tare da dayan ba. To lallai dayan ba zai ji dadin rayuwar ba, kuma al'umma ba za ta yadu ba, saboda kasantuwar rashin dayan. Ubangiji bai bar mutum haka ba sai da ya ajiye sharadi akan cewa namiji ba zai kusanci mace ba har sai ya cika wasu sharadu wato ya biya sadakin ta, shaidu, sannan ta halatta a gare shi, Babu shakka zuwan addinin musulunci ya sauya duk wani kuncin rayuwa da mata ke fuskanta a baya kafin zuwan sa. Sannan ya daukaka martabar ta da suturtata har ta zamo abun takawa a duniya....”

“Wannan haka yake pinkilicious!Domin kwanaki brother na yana mana magana akan mu dinga darajta mu’amalar mu mu mata, yake cewa wai Wai Matakai 5 Don Zaben Mace Ta Gari A Wannan Zamanin! Yace, A duk lokacin da matasa suke kokarin shiga cikin rayuwar soyayya, to kada su manta da wasu abubuwa guda biyar 5, wadanda zasu taimaka musu wajen zaben mace da ta dace da su. Wasu masana halayyan dan a’dam sun bayyanar da wasu abubuwa biyar da, duk na miji ko mace suka dauke su, babu shakka baza suyi kunya ba. Kamin ka zurfafa cikin kogin soyayya da mace, yana da kyau kasan wane irin tarbiyya iyayen ta suka bata, musanman mahaifi, irin ‘yayan nan ne da ake shagwabawa? Ko kuwa irin yaran da basu da kamun kai ne suna iya tanbayar saurayi wani abu? A duk lokacin da kake kokarin kiran mace amma tana yawan yimaka kukan cewar ta gaji, koda kuwa bata yi wani aiki da ya kamata ace ta gaji ba, ko kuma ka fuskanci cewar bata son duk wani aikin motsa jiki, ta cika son kanta. To kaji tsoron irin su,

“Macece mai tausayi ko kuwa irin zubin matane da basu da damuwar halin da mutun ya shiga. A wasu lokaci yana da kyau ka gwada ta da wani abu don ganin yadda zata dubi abun, idan ta nuna tausayi da damuwa to lallai sai ka kara gyara dangantar ku. Hakama duk mace da ka lura tana da alamun rashin gaskiaya a tare da ita, dangane da tarayyar ku, to itama ba mace da ta dace mutun ya nema bace. Gaskiya da mutunta juna shine babban ginshiki a duk rayuwar wasu masoya. A karshe kuwa, yana da kyau mutun ya duba irin yadda mace take nuna kauna da damuwa ga ‘yan’uwan ka da abokan ka. Haka yana da kyau mutun ya duba yadda mu’amalarta take da wane irin kawaye gare ta. A duk lokacin da mutu ya samu mace da ta dauki wasu daga cikin hallayan nan na kirki, to sai mutun ya bada azama, samun akasin haka kuwa, yana bama mutun kwarin gwiwar neman mafita..”

Nawal ta karasa fada tana jaddada kai, Haka dai suka shiga fadakar da Nour akan irin banzar rayuwar data dora kanta akai gashi ankaita an barota, bada gangar jikinta da take a jamia a bata maki gashi nan dunia ta juya mata, har suka sauke Aliya a kamfanin Shamsudden zancen da suke kenan. Aliya ta wuce ciki su kuma suka dauki hanyar gidan su Nour.

LIBROS/CAFFE24
(SAB PENTHOUSE AND MORE)

Tana tura kofar office din Shamsudden bakin ta d’auke da sallama shi kuma yana Ko’karin futowa zaije Buk wajen ta. Atare suka koma ciki yana mamakin ganin ta, gaishe shi tayi ya amsa a fara’ance ya kasa danne farin cikin sa, mika masa envelop din tayi ya karba yana jujjuya ta,

“Malam GAB ne yace na kawo maka oga sir..”

K’arba yayi, hannuwan su ya hadu, wani electric shocking ya kama kowannen su, Shamsudden ya lumshe idanu yabude su akan kyakkywar fuskar ta, cikin kasalalliyar murya yace,

“Kada ki sake kira na da oga sir..... kinji?”

“Sir au me zance toh?”

“Shamsudden..”

Murmushi kawai Aliya tayi, ya mike tsaye ya dakko wani book acikin book shelves dinsa, mika mata yayi,

“Ungo fill it, da wannan takardar ta gaban ki, aiki ya min yawa, Temaka pls..”

“Haba! Ba sai ka roka ba.”

Ta k’arasa fada bayan ta karbi littafin daga hannun sa. Kan kujerar sa ya koma yana danna laptop, lokaci xuwa lokaci ya kan saci kallon ta, kanta yana kan littafin tana faman cika sheshi domin kamar questioner yake. Kawai tsinkayo muryar Shamsudden tayi yana waka shi kadai, sai faman lumshe idanu yake, ya dora kafafuwan sa akan table din gaban sa, ya sarqe hannuwa kansa a sama, cikin zazzakar muryar sa tamkar ana busa sarewa ya fara rera wakar perfect ta Ed Sheeran, wanda ko tantama babu daka ji kasan da ita yake, domin yanayin wakar yayi yanayi da rayuwar su shi da Aliyah, Amma Aliya tana fara jin yanayi takawo da Fa’izah yake, sanin wakar masoya ce gashi kuma Fa’izah yake so, wadda nan bada jimawa ba zata zamto matar sa tunda an kawo lefe. Har wani lumshe idanu yake, hannun sa d’aya akan saitin zuciar sa, babu tantama Shamsudden ya fada kogin soyayya,

“_I found a love for me, Darling just dive right in, And follow my lead! Well I found a girl beautiful and sweet I never knew you were the someone waiting for me... Cause we were just kids when we fell in love, Not knowing what it was
I will not give you up this time, But darling, just kiss me slow, your heart is all I own.. And in your eyes you're holding mine!...🎶🎵”

Aliya ta ‘daga idanu ta dube shi, karaf idanuwan su suka hadu, tai saurin dauke nata tana ci gaba da rubutu, ya cigaba da wakar sa, sai nanata waje d’aya yake yi yana cire wasu guraren kai da kaji kasan soyayya na ratsa shi,

“She shares my dreams, I hope that someday I'll share her home
I found a love, to carry more than just my secrets, To carry love, to carry children of our own! We are still kids, but we're so in love! Fighting against all odds! I know we'll be alright this time! Darling, just hold my hand
Be my girl, I'll be your man! I see my future in your eyes!,🎵

“Baby,I have faith in what I see
Now I know I have met an angel in person! And she looks perfect! don't deserve this! You look perfect....”🎵

Yana gama wakar Aliya na karasa aikin ta, sai jifanta yake da kallo, tayi masifar masa kyau, sanye take cikin atamfa blue mai zanen red, ta yafa mayafi red, harta jakar ta ma red ce, tayi daurin ture kaga tsiya, dama tun lokacin da take kwaila shi kuma yana gajan sa take irin wannan ‘daurin. Mika masa tayi da dan rissinawa, karba yayi yana mata wani kallo’kasa ‘kasa. Jiyo muryar sa tayi,

“Amarya ya shirin biki?!”

“Muna nan muna tayi..”

“Yayi kyau! Sai dai rowar mijin naki kike mana, har yau bamu taba gaisawa dashi ba..”

Aliya tayi shiru, idanuwan ta suka fara gaurewa zasu fara zubar hawaye, Shamsudden na hankalce da ita, ‘dan daurewa tayi kar ya gano tace,

“Baya ‘kasar ne..”

“Oh shysa kenan! Allah yasanya alkhairi yasa gidan zaman ki ne.”

Aliya tayi shiru bata ce Ameen ba, Hakan ba karamin dadi yayi wa Shamsudden ba, Haka dai suka zauna jigum jigum, Ta mike zata tafi ya dakatar da ita,

“Tsaya na sauke ki..”

“Kabasshi ai naga kana aiki”

“Ba damuwa muje kawai”

Sani ne batai ba, duk wani shige da ficen ta yasani, yanada balain kishi bayason wani ya ganta ko ta hau adaidaita sahu agama kalle masa ita, acikin lift ya mika mata jambakin ta data bari, ta karba tana masa godia, ya kuma sake mika mata yar ledar hannun sa mai dauke da original Kylie Nude lipsticks, godia sosai tayi masa, ko a mota jefi jefi suke hira har ya sauke ta a gidah...

•••
ANKON FA’iZAH: zai kasance MATERIAL PINK with a touch of BLACK a hada da BLACK RAW SILK VEIL...
Hashtag #FAISAH2020.

ANKON BIKIN AYSHA (ALIYA) DA SHAMSUDDEN na mother's eve da za'ai, su pinky da Myriam, Mom Heena da sauran yan team Aliya da Shamsudden sun fitar da kalar, JEALOUSLY GREEN mixed with a LITTLE ANGER RED, with a touch of E DEY PAIN YOU PURPLE, to match with PEPPER DEM GANG YELLOW SHOES, with a slight touch of OSI NDI PINK with a dash of HEART ATTACK BLACK...
DEM NEVER SHISHUNTIN🤪

HASHTAG #AISHAM2020...
__
*Wannan littafin na kuɗine, kiji/kaji/kuji tsoron ALLAH karki/karka/karku shiga haƙin wanda ya saya, kema idan kina buƙata ki nema wannan Numbers ɗin._👇🏻*

*08030811300*
*07067124863*


_*KAI MIN HALACCI......!💕_*


_*NA_*


_*_MISS XOXO🧕🏼_*_


_*NO: 47_*

Koda ta kammala komai Sani driver ta kirawo batasan suna tare da Shamsuddeen ba, Sani yace gashi nan zuwa, nan ya gayawa Shamsuddeen cewar Madam tace tana jiransa ya d'aga kai tare da cewa ya zauna shi bari yaje ya d'auke ta. Haka kuwa aka yi ya fito yaje gashi daman a ranar aka kawo masa dalleliyar motarsa Benz fara kal sai kyalli take yi ya murza kan motar yabar kamfanin nashi zuwa Buk. Yana shiga ya hangeta a tsakiyar kawaye da abokai sai murmushi take yi, duk da yaji haushi amman be nuna a fuska ba yaje gurin yana danna horn hakan yasa duk mutanan wajan suka waiga suna kallan motar, hatta Aliya baza ido tayi tana jiran taga wanda zai fito daga cikin amman anki fitowa sai uban horn da ake saki. Wane ne a cikin su ya ce bari yake yaji, yana zuwa Shamsuddeen ya zuge glass tare da kallon guy d'in yace.

“Please Aliya nake kira.”

“Okay bari ayi mata magana.”

“Liyaaah ana kiranki.”

Ta yatsina fuska tare da kallon Nawal wacce itama mamaki ya kusan daskararwa, kallon Yahaya tayi wanda yake bata sakon ana kiranta tace dashi.

“Kace ni matar aure ce.”

Kamar wani d'an aike haka ya koma ya sanar da shi nan da nan Shamsuddeen yaji wani dad'i ashe tana cewa ita matar aure ce? Ashe tana kare martabar auranta sai wani farin ciki ya shigesa ya kalli Yahaya tare da yin murmushi yace.

“Eh kace mata mijinta ne.”

Koda ya sanar mata d'auke kai tayi saboda bata yarda cewar shi bane, duk yana hangota Yahaya yaje ya sake gaya masa hakan yasa Shamsuddeen bud'e k'ofar motar ya fito ya tsaye yana rike da k'ofar yana kallon bayanta. Nawal ce ta ganshi kasan cewar tana facing motar tayi dariya tare da kamo hannun Aliya tana cewa.

“Ke kawata wallahi shine, gashi nan ya fito”

Da sauri ta juya karaf suka yi four eye's dashi tayi saurin d'auke kai tana turo baki kafin tayi sallama da su ta nufi wajen motar tana tunanin ko aro motar yayi dan ita bata san shi da ita ba. Wucewa tayi ta bud'e ta shiga ta zauna ta rufe k'ofar sannan shima ya shiga ya rufe, kallanta yayi ta wani kauda kai sai faman zumb'urar baki take yi, yasa hannunshi tare da buge bakin yana cewa.

“Daina turo min shi ko yanzu na sake kumbura miki shi.”

Mayar da lips d'in tayi tana ta faman kallon waje ta glass da haka yaja motar suka bar makarantar, kai tsaye gida suka wuce yayi parking a k'ofar gidan saboda sun fitar da k'ofa sai dai idan zai ajiye ne sai yabi ta gate. Hijabin ta cire ta shiga toilet wanka tayi ta fito ta tarar ya karb'o mata abinci a gurin Umma, sai da ta shirya sannan ta zauna taci shi kuma ashe ya koma kamfaninsa, ta gama komai sannan ta d'auki hijabi ta tafi gurin Umma har sai da ya dawo sannan suka tafi tare, baya kulata shima sai dai kowa yayi harkar gabansa, ko tayi chat ko tayi kallo shine kawai aikinta.

Bayan wasu kwanaki sai gashi ya dawo gida wajan la'asar sai da ya fara zuwa gurin Umma ya nuna mata sannan ya shiga gurin Aliya wacce ke kitchen tana wainar fulawa gefe wayarta ce tana jin kasidojin fadar bege ana yi tana bi sam bata san yazo ba sai da taji yayi gyaran murya. Waigowa tayi suka had'a ido tayi masa sannu da zuwa fuskarta a sake shi kuma tashi a d'aure, sai dai bata wani damu ba haka taci gaba da aikinta.

“Sako hijabinki ina son ganinki.”

Yayi maganar yana komawa daga gefe ta mike ta wuce d'aki yana binda da kallo dan sanye take cikin dogon skirt english wears da riga 'yar karama mai gajeran hannu tasa hula, harta fito bai dena kallon hanyar ba tazo gurinsa tare da cewa.

“Muje.”

Dam gabanta ya buga ta kura masa ido bakinta yana rawa tace dashi.

“Ina zamuje?”

Kasan cewar yana gabanta yasa shi waigowa yaga idanunta a waje da alama tsoro takeji ko tayi tunanin gida zai kaita? Ya dankara mata wata uwar harara tare da lasar lips d'insa ya lumshe idanunsa yana cewa.

“Sai na gaya miki inda zamuje sannan zaki bini muje?”

Kad'a kai tayi idanunta suka ciko da hawaye bata son a gayawa su Baba Suleiman domin bata san zame musu matsala bayan 'yarsu ta cikinsu bata basu matsala ba, dan haka ta dinga ziraro da hawaye tana cewa.

“Dan girman Allah kayi hakuri karka fadawa su Baba, wallahi na dena sannan zan yi maka duk abinda kake so, dan girman Allah karka gaya musu, na shiga uku.”

Kugu ya kama kamar wata mace yana kare mata kallo, ashe tana tsoran su Baba Suleiman be sani ba? Ai da ya gano wannan abun da wallahi yayi amfani dashi wajan shawo kanta yasan da tuni sun zama abu guda d'aya. Amman yana son ne ta soshi bawai yayi amfani da tsoranta ba wajan karb'ar ta a matsayin matarsa, yaje gurinta tare da figar hannunta suka yi kofar gida tana ta goge hawaye tasan yau karyarta ta kare, gashi da taje gida tace musu bata da wata matsala shima bashi da ita, yanzu in sukaje ya fad'a cewar har yanzu babu abinda ya had'a su ya zata yi? Amman me? Suna zuwa k'ofar gidan taga wata 'yar karamar mota BMW red color banda shek'i da walwali babu abinda take yi, ya zura mata car key d'in a tafin hannunta yana cewa.

“Kyauta ce nayi miki saboda kin kammala makarantarki lafiya kin kuma fito da kyakyawan sakamako. Congratulations once again, but ba yanzu zaki fara amfani da ita ba sai nan gaba kina jina?”

Gabaki d'aya Aliya ta rasa abinda zata yi sai faman motsa baki take amman ta kasa furta komai. Ita kanta tasan bata cancanci irin wannan babbar kyautar ba saboda bata yi masa wani abu ba wanda zai sanya shi gwangwajeta da wannan motar ba.

“Ki koma gida idan na dawo zan karb'i key d'in aje a adana motar kinji ko.?”

Aliya ta daga kai tare da sake kallansa sai kuma ta ruga d'aki, tab'e baki yayi sannan ya koma gidan Umma. Tunda ta koma ta kasa karasa wainar fulawar da take yi, sai faman kuka take yi wanda tama rasa kona menene, sai da ta jima tana yi kafin ta mike ta karasa wainar wacce sai bayar da ita tayi saboda ta kasa ci dan ba karamin kaduwa cikinta yayi ba. Anayin magariba kuwa yaxo ya karb'i mukullin aka dauke motar daga wajan yana dawowa ya mik'a mata, tana son yi masa godiya amman kunya ta hanata dan batamasan dame zata fara yi masa ba. Aikuwa har ta kwanta bata yi masa ba ransa ya b'aci sai dai bai nuna ba yaci gaba da harkokinsa.

••••√ ••••√ ••••√

Wednesday itace ranar da su Shamsuddeen zasu tare a sabon gidan su, su matar Yaya Shamsuddeen sune 'yan rakiya Aliya taje sukai sallama da Umma har da kuka saboda sun riga sun shaku, taba yi mata abinda ko Shamsuddeen bata yiwa ta d'auketa 'ya ta cikinta ba wai suruka ba. Tanaji tana gani suka shiga mota, a cikin motar ma su Nawal kasan cewar ta gaya musu shine suka zo yi mata rakiya dai tsiya suke yi mata, dama babu wanda yasan wani abun bai taba had'a ta da mijin nata ba, gashi wasu lafiyayun magunguna da aunty Afiya ta bata tace tasha da yamma suna da matuk'ar kyau ta dannasu cikin jakarta bata kulasu ba. Koda aka zo gidan Aliya bata yadda cewar ita za'a kai ciki ba tsaboda tsabar tsaruwarsa kanta har juyewa ya fara yi dan a film take ganin irin su.

“Kutmelesiiii.. Liyaaah! Uhmmmm lallai liyaah mun dena ganinki wannan gidan naki ne ke kadai ko akwai 'yan haya a saman ko a kasan?”

Cewar Nawal domin ita kanta sai da gidan ya girgiza ta, ko gidan 'yan uwa idan sunje a abuja batajin ta taba ganin irin tsarin gidan shi yasa ta girgiza. Yaya Garzali da Yazeed suka gani zaune a can nesa, driven daya kawo su yayi parking a wajan
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment