Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

gado na ɗauki wayata na fara kiran Hajiya Mai gilashi. Wayarta a kashe har yanzu lallai duk yadda za,ayi in Allah ya yadda sai naje gidanta idan Allah ya kaimu. Allah dai yasa ya barni inje , wani sashi na zuciyata yace kawai cewa zakiyi ya kaiki , wannan shine gaskiyar magana , saukowa nayi daga saman gadon na fita palo inda yake.

Ya toshe ɗayan kunnenshi da abun sauraron magana , ya ƙurawa waya ido yana murmushi. Duk maganar da nayi kwata² ma bayajina sam² , zagawa nayi ta baya da niyar in ɗan riƙeshin nan irin idan mata suka tashi labbatar namiji idan suna san wani abu daga gareshi. Amma kafin in riƙeshi sai me...? Wani irin ruɗaɗɗen ihu nayi tare da faɗar da wayar daga hannunshi. A firgice ya juyo ya kalleni sannan ya tashi da sauri zai ɗauki wayarshi a lokacin har na zagoyo na rigashi ɗauka , bani wayata yayi maganar ranshi a matuƙar ɓace , kyarma jikina ya farayi saboda na tsorata da irin kallon da yakemin. Dakewa nayi tare da cewa idan fa naƙi bayarwa ? Sai in kashe ki............ Ya faɗa yana nuna shaƙewa da hannunshi saman wuyanshi , cike da tsantsar ɓacin rai nace ai yau nice zan kashe ka. Nayi maganar idona yana kallon ƙasa. Wani irin wulaƙantaccen kallo yayi min tare da nuna kanshi nine zaki kashen ? Kafin inyi magana Papy ya shigo yana kuka , ihun da nayi ne ya tasoshi daga koma ina yake yana bacci , cike da ɓacin rai Dikko ya jinjina kanshi ya matsa yaja hannunshi suka fita.

Wuri na samu na zauna na shiga binciken waya. A raina kuma addu'a nakeyi Allah yasa Papy yaita kuka ya hanashi dawowa da wuri , dan abinda na fahimta baya so yanayin wani abu wanda bai kamata ba idan ɗan shi yana gidan. Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un , wata irin yamutsa kaina yayi da sauri na rufe idanuwana dan irin ƙazantar dana gani , tunda nake da Dikko duniya bai taɓa abinda naji na tsaneshi ba sai yau , wayyo Allahna ? Mayun mata wai ina ruwanku da mijina ne ? Kunzo kun daddaɓeshi sai kace ƙuda ya samu ruɓaɓɓen nama. Ga kira waya sai shigowa yake ba ƙaƙƙautawa , saƙonni sai kokawa sukeyi wurin shigowa , jikina na kyarma idona cike da hawaye na fara neman number Sharifa , dakel na gano ta ɗan iska wai "yar uwarshi ya rubuta a jikin numberta , kam bala'e wai duk ina , ina wannan iskanci ya faru ? Da wata ɓeranyar yarinya shegiya zata girmeni baifi da shekaru biyu zuwa 3 ba , ta ciko mishi saƙon nata itama da ɗanyayen kalamai daɗaɗa , sanyaya , Sharifa kuma ta rubuto mishi cewa ni na kirata na zageta , nayi mata gori wai ni injini ni Sultana wai nice nace wa Sharifa ita karuwan Dikkon ne , a taƙaice dai ita Yusra kaf a cikin kwaratan itace ta saman iska , kaf babu feƙaƙen ɗan tasha na sama a wayar nan sama da ita , guguwar "yar iska ce , dan kalamanta data faɗa tana tattaɓa wasu sansa na jikinta nida kunya ta haifa na rantse da girman Allah ba a baki ba a rubuce duniya ni bana iya rubutawa bare kuma azo fagen in furta. Karuwai.....?׳ hmmm karuwai na sha'aninsu idan suka samu mazajen ballagazanzun mata , a hayaƙe ya dawo saida ya wanwanka min mari ya anshi wayarshi. Cike da rashin tsoro nace kadaiji kunya kuma kayi asara daka kallar da idonka tsiranci haram , naji kunyar kuma naje na kalla haram ɗin naki ne ko nata ? Banyi magana ba na nufi hanyar fita , har na fita zuciyata ta hayaƙoni na dawo ,

Nima dai a daren nan nayi ɗan ƙaramin hauka , haka na rufe idona naci gaba da zage² ba shi nake zagi ba su Yusra nake ta ɓaɓɓarkawa zagi , keda ke gidanki idan kinsan halin da nake ciki Dikko yasan ina nan ko yanajin abinda nake cewa ya basar dani yaci gaba da cht inshi hankalinshi kwance , inda yake saman kujera naje na kamo ƙafarshi na jawo da ƙarfi ina cewa saina faɗar dakai na ƙarya maka kashin baya , da ɗayar ƙafarshi yayi min wani irin kyakkyawan harbi a fuska saida hancina ya fashe. Shi kuma yaci gaba da latse² a wayarshi da yanayin shauƙi , baya nayi inajin juwa ɗakin na gani yana juyamin duniyar tayi shiru banajin motsin komai watan saurarena ya ɗan ɗauke shima numfashin an riƙeshi. Ina dawowa jin sauti na sake tafiya inda yake ina faɗar saina kashe ka , janye wayarshi yayi daga fuskarshi yana kallona da wani irin jarabben kallo , a kasalance yace wai nine zaki kashe....? Ya nuna kanshi , ey , An mata dukana ? Ey , har wannan shima zaki ? Ya nuna daddatsewa da hannunshi , gemunshi kenan , dai² lokacin dana iso kusa dashi , riƙeni yayi da yanayin mayata yace muje saman gado mu kashe kanmu nima saina kashe ki...... Ni ka sakeni , anƙi a sakekin ya ƙarasa maganar yana rufe ƙofofin hancina da "yan yatsunshi biyu , da hayaniya nace wai ba nace ka ƙyaleni ba ne iye ? Shima da irin magana na yace wai bana ce bazan ƙyale ba iye ? Ya faɗa a gajiye yana sauke numfashin jaraba yana min wani irin kallo.

Kwacewa nayi , ya riƙoni da sauri yace ai ƙarya kikeyi yarinya , ina ne zakije ? Sai kin kashe ni..... Ya ƙarasa yana lumshe idanuwanshi tare fitar da numfashi cike da kissa , ƙiƙi² muka fara rigel². Ni ina so in ƙwace , shi kuma yana so ya riƙoni har ya sauko daga saman kujerar , saina tafi , bana sanka׳ na ƙarasa ina ƙara yawan kukana. Ai basai kinsha wahalar faɗa ba nasan wannan shekaru 3 zuwa huɗu da suka wuce. Jana ya farayi hanyar bedroom wai muje in kasheshi. Da Allah ka ƙyaleni kaji , ah ni bazan ƙyaleki ba aradu sai kin kasheni yayi maganar yana murmushi tare da kafe ni da mayataccen kallonshi.

Nanfa abun yaci tura naci gaba da ɓarin maganganu , tun yana kallona har ya fara rufe ido ya sake hannuna. Nan gori ya tashi tunda na lura yana da buƙatuwa dani , haka na warware kamar farfera na ci gaba da zazzaga ranshi mutunci ni matar da za'a sauke buƙata a kaina , ƙarshen film in nace tafiya zanyi , cike da ɓacin rai yace ina ne zaki iya zuwa ? Bayan baki da gidan da yafi wannan ya nuna ƙasa da ɗan yatsanshi na hannu dama , yana ci gaba da cewa kije mana ? Idan kin tafi zan mutu ne ? Ya nuna kanshi cikin tsatsanin fushi mai sa kaji cikinka ya juya na kasa kallonshi , dan kinga ina lallaɓaki ? Idan kinyi haƙuri baki je ba kin zama banza , ki tafi ya nuna hanyar fita , rage murya yayi da cewa ina da dubunki a waje sai me ? Ko an faɗa miki wai bana iya rabuwa dake ne ? Kullum² zakije sai na tafi gidanmu kaza² tou kije ko wani ne ya baki haƙuri ? Hmmm ke baki san iskanci na ba , nafi ki ƙaryar rashin kunya wallahi , inda duk kike zato na tuni na wuce wuri nayi gaba.... Idan kina nan wata zan kawo idan ma kin tafi haka dai zan sake kawo wata.

Kina iskanci ana baki haƙuri tou an daina cewa kiyi haƙuri ki tafi duk gidan da zakije , ba burin daya fi duk macen da bata da lissafi tanayin faɗa da miji tace gidanmu zanje , fuuuu tayi yaji ya nuna da hannu , tou idan baki sani ba babu babban kuskure da yafi wannan jakancin , ko shi mijin dake aurenki bai san kuna da gida ba ? Ai yasan ba a sama kika faɗo ba , ya nuna yana ci gaba da cewa ai ina ganin idan yaso zaice kije gidanku. Mahaukaciya ma dake da Allah , fitarmin daga ɗaki yanayin fushi ya fara hawa kaina kafin inji miki ciwo , kuma na rantse da girman Allah idan kika fita gidan nan ko ina kikaje har can zan biki saina lalata miki fata , kaca² zan miki. Fita nace........................ Ya faɗa yana nuna hanyar fita tare da rufe idanuwanshi cike rashin mutunci. Fashewa nayi da kuka nace yi haƙuri don Allah , zo nan , ya kirani da hannunshi , tafiya nayi ina kuka ina kallonshi. Riƙeni yayi a jikinshi yana sauke ajiyar zuciya bakiji An mata , wai ni miye matsalar ne ? Kullum sai kin ɓatamin rai wai me nayi ne ? Haba An matana ya ƙarasa mganar yanamin kyakkyawan riƙo , cikin shashshekar kuka nace kaine , nine kuma ? Tou wai meye nayi da zafi haka ? Ka daina so na ai , haba Yarinya ke ko wani ne ya faɗa miki ai zaki ce a , a , duk duniyar nan wai waye yake dani idan bake ba ? Haba ƙaramar yarinya.... Duk kin burkeni na zama wani lusari sai anfani kike da soyayarki kina murzamin zuciya san ranki ya ƙarasa yana min kyakkyawan murmushi , shiru nayi ban mishi magana ba , kefa yarinya ce ? Kalli Dikko fa ? Akwai tazarar tsayi shekaru da kuma tunani , cikin dariya yace wallahi kin maidani kamar wani zararre ke ko tsoron Allah ma bakyaji ? Haba An mata , ɗagoni yayi daga jikinshi yace ai nasan ma kin yafemin ko ? Ey tou zo muje. Yana riƙe dani har toilet da kanshi ya wankemin fuska yana cewa dan Allah An mata ki daina ɓatamin rai gaskiya banajin daɗin abinda kikemin.

Wai ke baki san ba'a ɗagawa miji harshe ba ? Baki san idan mijin yanayin zuciya yadda ake saukeshi ba ? Ba'a hawo namiji yayin da yakejin tuƙuikin ɓacin rai , komai yana iya faru a dai² lokacin da yakeyin fushi , Juyowa nayi na riƙeshi ina ci gaba da kuka , a wahalce yayi gajeriyar dariya cewa ai nasan baki iya tafiya ki barni wasa kike , ƙaramar yarinya. Wai miye ke damun kanki ne ? Meye nake miki wanda baya miki daɗi....? Ni kifaɗamin , faɗamin matsalata dake sai nima in faɗa miki matsalolinki kowa ya daina ɓatawa kowa sai a daina faɗan tunda kin gaji. Kinga ko a rigima kin fahimci ni nafi sangarta bana gajiya haka zakiyi ta hawoni ina baki kashi kullum kina fama da jinyar fata , kuma kinsan banayi zuciya in zaneki kuma in maƙalƙaleki anjima inyi ta warwarewa ya riƙeni yana nuna yadda yakeyi idan yana kwance dani , dariya nayi ina kallonshi. Shima dariyar yayi tare da ɗagamin gira yace wallahi kuwa , tou ni ina ruwana ? Gani ga "yar yarinta ina fa morewa , niɗin mai sa'ar rayuwa ne , duk da dai kince wai niɗin tsoho ne , amma a haka dai ai ina bada wuta a tsakiyar filin wasa ko ? Ya ƙarasa maganar yana ɗan taɓe bakishi tare dayin wasa da girarshi.

Murmushi nayi ba magana amma har yanzu ina kwance a jikinshi , ɗan wayancewa yayi dai yaci gaba da yabona wanda nidai nasan a zuciyarshi ba haka bane ba , yana dai yabo na ne dan inyi farin ciki ya kuma sauke buƙatuwarshi yayi bacci da natsuwa. Koma dai bada gaske yakeyi ba ni naji daɗi , yana da kyau maza su riƙa farfaɗawa matayensu kalaman da zasuyi farin ciki su girmama musu kansu sai suji su suma ashe dai wasu manyan shegu ne , ta hakan ne zaka riƙa zaliƙo mata matsalolinta a hankali idan mai hikima ce saita riƙa gyarawa , irin dai kana yabonta kana cewa ai idan kikayi kaza kinga yadda kike bada haske ? Ko kike ruɗani ? Ko bana tare dake sai inyi ta tunaninki , kaza². Nan zaka ga ta warware tace you ai kaza da kaza ma da nakeyi kaza. Ni nayi farin ciki da yacemin duk nafi su Yusra kyau , gani "yar gayu kuma ni "yar yarinya su duk sun tsufa ma , ai haɗuwa ta ta wuce duk inda bana zato , shi a ganinshi ma yafi ko wane namiji sa'ar aure , bayan ni nasan Dikko ƙarya yakeyi , kuma wai da nace masa ba wani cewa yayi in kalli kaina a madubi fa , An mata kalli idanuwanki , ji lallausar bakinki ya nunamin saman lips ina , kalli nan ji can uwa uba kuma saikin dafe uztaz D ' K a gado. Kalamanki suna da daɗin sauraro bayan ni nasan duk lokacin da zai kwanta dani sai ankai ruwa rana , yanzu nan ya gama min faɗa ina ɗaga mishi murya , amma da yayi dai nayi farin ciki ,

Wai ni ina da kyakkyawar fata idan kuma nayi mata ado da lalle zan ƙara haɗuwa wai kuma lallen na hausa amma a zuba turare a cikin lalle dan ya kashe ƙaurin lallen , warware kaina yayi yana shafa gashin kaina wai na iya gyaran gashi ya mishi kyau a haka. Shiko banyi kitso ba yafi ibar mishi lissafi , haka na saki baki naita dariya kamar sakara ina cewa ai idanma nayi kitson warwarewa yakeyi , ey ai dama nima bansan kitso , saidai ina san wannan kitson kin tunashi ? Wani mai kyau ? Kai yayi miki kyau An mata , nifa nasan bana kitso harma gara kalaba , amma da nace masa ni banyi kitson nan ba , cewa yayi na manta yana ta nunamin yadda kitson yake. Yadda yake nunamin irinshi ni nasan ban taɓayin irinshi ba a tarihin rayuwata. Amma Dikko ya kafe kai wai nayi shi in tuno mana , saida na natsu sosai na gane irin kitson dake kan Yusra ne , dakel dai nayi yaƙe mai ciwo , shima zanen lallen a wurinta ya gani ai na gani itama lallen hausa ne akayi mata wani irin ado mai ɗaukar hankali.

Wato duk duniya ita mace baka da abinda takeso sama da a yaba mata , suma mazan haka suke , haka kuke mana "yan rainin hankali , kuma so kuke a yaba ku kan nan naku yana muku wani girma kunajin ku wasu manyan "yan duniya , kuna wani ciccika fuska ku masu gida ana zugaku kuna wani karkace baki kuna dariyar ƙasaita kan׳ dariyar cikin izza da nuna isa. Yana da kyau mazaje ku riƙa gyarawa matayenku da irin yajuju wama jujun da ku kuke gani a waje. Kuma a hikimance , ba zagi ba duka ba gori wance ta fiki ko wane matar shi kaza² a , a , ba haka akeyi ba a hankali zakayi mata dan kune kaɗai kuka san a inda kuke shiga kuna gano irin wannan duniyanci. Bawai nace kuɗin "yan duniya ne , ina nufin irin matan da kuke huɗɗoɗi dasu. Ba kuma ina nufin tasha ko sakarci ba , kamar a kasuwa ko a ofisoshinku da dai sauran wuraren da kuke mu'amula dasu , tunda suna ɗauko wanka da gayu kamar zasu tashi duniya dan haɗuwa , su barbaɗo muku turare a ciko ido da kwalli ana firfira muku idanuwa. Ku saki baki ba aji kuyita gaggaɓa dariya irin wacce ko matanku bakuyi ma irinta. Tou karta burgeka kuma karta ruɗa maka lissafi da tunani , ka riƙe karka bari tayi wasa da tunaninka nata ƙarya ne zahirin tana gida , idan tayi nata sai yafi baka sha'awa akan na sharar bakin titi , wai su kun gane matsalarsu.....? Matsallar auren su ba a gabansu yake ba. Haka zasu shaƙe miki wuyan miji suyi ta ranfa dashi , idan kuma ta gaji da cin aljihunshi taci shi har babunshi saita tura wata itama taci gaba da gayar miki miji babu tausayi , itama idan ta gaji tayi gwanjonshi shi kuma zuwa wannan lokacin ya zama ɗan gari. Ma'ana ya gane hanyar yadda take , kafin ki ankara an firgita miki miji , wata macen ma su biyu ne a wurin miji amma dai lusaranci da hauka yasa sunyi sake sun barwa karnukan bisa titi suna ta mishi haushi , baki jin haushin ta waje wai ta gidan itace ta tsone miki idon tsabar hassada , kullum kika tashi da ita a zuciyarki baki da buri da kwanciyar hankali yadda zakiyi waje da ita , tou idan ta tafi ance miki shikenan bazai sake aurar wata ba ? Ba matan gida ya kamata kuyi hassada dasu ba yaƙi zakuyi da matayen dake matse mazanku a waje , ku kuma maza gaskiya kuma kuji tsoron ku tausayawa matayenku , ku kyautata musu , kuyi musu magana da sanyi² ku lallaɓa su , ku tarairayesu , ku ririta su ku jawo su jikinku da farin ciki. Kuyi kwanciyar aure dasu cike da soyayya da kuma nuna musu finsu buƙaturwa hakan , ku gode musu ku yaba ƙoƙarinsu ku basu ƙwarin guiwa ku jinjina musu ko bakuji daɗi ba , a hikimance zaku riƙa nuna musu yadda abun yake har su ƙware su anshewa ɗan tama doki. Wasu matayen sunfi wasu mazan gogewa ta wannan harkar da kuma gogewar rayuwa ta zamantakewar rayuwarmu tayau da kullum. Wasu kuma mazan sunfi matan , idanuwansu a tsaye yake tsakiyar kai , tou koma dai waye tafi gogewa ta gogar da abokin rayuwarta sai kuyi rayuwarku gidan aurenku da natsuwa.

Kuma bawai ina nufin kuna biyewa matan waje ko ku fahimci magana ta da wani yanayi. Ku fahimce ni da kyakkyawar fahimta amma aradu ku ƙyale gaibu ku kama zahiri , idan kuma ka nuna mata taƙi gyarawa kayi mata...... Ba cewa nayi ka ƙaro aure ba , nufi na a ƙaro miki kayan ado a ci gaba da baki kula ana ta kwantanci nuniya da gyara har ki gane ki gyara , dan kunsan mu mata ba kishi mukeyi ba hassada muka iya. Sanin sirrin kishi zahiri babu munafurci da yadda akeyin shi kanshi kishin aradu yana nan wurin maza. To kuyi kishi yayin da akafi matayenku ku tsaya tsaye da gaskiyarku kuyi gyara.

Tou lallai fa idan taƙi gyarawa ka lallaɓa kayi mata ƙarin...... Haske , dan inda kuke shiga mu bama shiga wurin , irin matayen da kuke gani mu bama ganinsu , kuke ganinsu kune kuma kuka san inda kuke ganosu har sukeyin abinda kuke ganin mu bamayi muku irinshi , wata matar daga gidan aurenta maƙotanta sai familynka da nata ahalin su kaɗai ta shiga kuma ta sani , sai abokan arziƙi , kuma kila su basu da wayayyun idanuwa bare ta waye da wayewarsu. Sanin da daka santa dashi tun tana budurwa kafin kuyi aure shine dai har yanzu babu wani ci gaba , wata macen kuma da wayewar ido take zuwa gidan auren amma sai ta zama wata aljihun gefen riga ta daƙiƙance ta zama wata sai addu'a kawai. Tou kai da kake shiga kana fita kana zuwa inda ita bata zuwa kuna ganosu suna labbatarku da irin abubuwan da suke jan hankaliku ka sanar da ita mana , ka koyar da ita , idan ka faɗa mata raguwa kayi ne ? Kaɗan faɗaɗa mata kwalwarta ka buɗar mata da idonta dai² irin yadda ka gano suka ɗauki hankalinka. Ka wadata matarka da sutura dai² ƙarfinka ka wadata ta da kayan ƙamshi mayuka masu kyau hoda sabulun wanka ka ciyar da ita karka riƙa maƙalewa wurin mai indomie ko mai tsire da wasu lafiyayen kaji kabar matarka taita kokowa da tuwo , wallahi kuji tsoron Allah kuci irin abinda kuke ba iyalinku irin abun nan da kukeyi kuci daɗi ku barsu da marmarin irin abinda ku ya gundireku dan nacin cinsa da kukeyi wallahi zalinci ne. Cuta ce , ku kuma matan kuma muji tsoron Allah masu siyar da shinkafar miji kuna zubin adashe Allah yana kallonku tom.....

Idan an gyara miki kema ki riƙa gyarawa mana , kar yace kije kiyi kisto two step , ki karkace baki ah ni wallahi bana san wannan kitson kaza² , to wane iri kike so ? "Yar rainin hankali. Ke harma sai ya faɗa miki kiyi irin style kaza ? Ashe ma baki san abinda kike ba. Idan akwai abinda yafi two step kiyi mishi mana , ke meye naki a ciki ? Ba shine yake so ba ? Tou ayi mishi mana a zauna lafiya ? Ko yace miki wallahi kaza na gani ya burgeni , kiyi irinshi , ke uwar tsiwa maimakon kice tou sai kice ah sai kaje can idon daya gano a wurinsu kaje kayi ta gani. Ƙalu balenki da bawa namiji wannan ansar idan ya fara gani tou fa lallai ƙaryaki ya ƙare , kenan kinma yadda yaje ya gano na wajen ko ? Shin wai mema kika tsaya yi har namiji yafi ki hikimar rayuwa ? Ke bakya kishin kanki ne eye ? Haba Hajiyata da Allah karki bani kunya mana. Ko ke baki so tou kiyi mishi idan dai shi zaiyi farin ciki mana , sai sunje sun kallo na wajen a ɗauke miki hankalin miji ayi yamma dashi a barki da ciwon tunani , idan shima ɗan rainin hankali ne kuna gari ɗaya fa da kinyi waya zaice yana abuja ko kaduna ina nan airport zan hau jirgi in tafi lagos , ke ya maida jirgin tana can ta ɗaukeshi an barki gadin gida , kar kuma mijinki yayi tafiya ki tuno cewa kila yana miki ƙarya ne baije ko ina ba , kulli inki ahir inji tsofi , ƙalubalen ki da zargi. Damuwa ta dameki daga nan sai neman shawarar abokai , idan kinyi sa'a da ƙawar kirki ta baki shawara ta gari , idan baki dace ba ta haska ki da malam tsibbu suma daga nan kasuwa ta buɗe , idan kuma kika hau layin maijin taushinki tasa ki , ki kakkaɓo auren , dama tana can tana ta yawon zawarci ita ɗaya ta rasa ƙawar cin titi tou ta samu abokiyar yawo , idan kuma ta ƙwarewa cin amana ta auren miji a barki da wallahi² , ke baki gane illar abun sai kin shiga makarantar , baza ki fahimci wuyar karatun ba sai an shiga second semester ku kula dai......

Gadai Dikko yana faɗawa Sultana , wanda ita a ranta tasan ba haka bane ba. Amma taji daɗin yadda ya yabeta tare da nuna mata tasha gaban mata da yawa. Tou kai idan ka tashi faɗar naka kalaman ka faɗa mata su da gaskiya cikin soyayya. Ku daina haɗe fuskoki wa matayenku haka babu kyau , wani namijin idan kika ganshi a majalisa yafi kowa harshe dariyarshi tafi ta kowa , duk mai tallar da tazo sai yajata da surutu , sai matarka zaka rainawa wayau idan ka tashi shigowa gida ka haɗe fuska kayi ta wani gadarar banza wai kar ta raina ? You bayan ka manta kun haɗu a tsakiyar filin wasa ? Allah wani namiji idan ya shigo gidanshi kamar "yan fashi sunyo samamen dare. Ba "ya "ya ba iyayen suma kansu gabansu harbawa yake kamar an ɗorawa mutum wuƙa a maƙoshi.....

Cike da soyayya mukayi wanka muka baro toilet in cike da tsantsar muradin san kasancewa da junanmu. Kuma har muka fito bai daina zugani ba sai dariya nakeyi ina watse baki kamar lefen wacce babu uwarta a gidan babanta , ina ta sakin layi , zuwa wannan lokaci gaba ɗaya na manta da wasu banzayen hotunan da na gani a wayarshi na fuskanci rayuwa mai daɗi da gusar da damuwa a wurinshi........

Bayan kwana huɗu.

Ni na rasa inda mai gilashi ta sake a cikin jahar katsina , na nemeta na rasa inda take , kuma har gidanta naje bata nan
DOWNLOAD
DOWNLOAD

2 Comments On KWARATA RETURN
avatar
fatima-kasim

4 months ago

Reply

Naji dadi sosai sosai Allah y kara basira

avatar
daiy

4 months ago

Reply

Replying to fatima-kasim

Ameen muma munji dadin kasancewarki anan.

Please Login or Register in order to submit comment