Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

Jiddah yace ya akayi ne ? Yaya D ' K yayi mata liƙi kuma aurenta zaiyi , kai tsaye Yazeed yace wallahi D ' K bazai aureta ba , ke kina wasa da Dikko ko ? Tou D ' K mashaune shi ɓadda musulmi , shi kanshi tsoron kanshi yakeyi kuma bai yadda da kanshi ba , ita wannan yarinya da kike magana yanzu haka tana wurinshi Abuja taje mishi rakiya zaiyi tafiya. Jiddah tace zai aureta , Yazeed yace bazai aureta ba , haka sukayi ta maimaitawa kusan sau goma , shi Yazeed yace Dikko bazai auri Sharifa ba , Jiddah tace zai aureta , daga ƙarshe dai suka rabu a haka kowa yana cewa zaka gani , shima yace mata zaki gani.....

A wahalce ta ajiye kwalbar cikin maye tace wallahi saina auri D ' K , wata irin dariya Amisty tayi tare da cewa Dikkon ne zai auri "yar shaye² ? Cikin maye tayi magana cewa tsaya kisha kallo...... Dariya Amisty ta sakeyi tare da cewa me kuwa zan kalla saidai inga yadda zakici ubaki , murya a lalace da maye Hafsa ta nuna Amisty da ɗan yatsa tana rufe ido da yanayin buguwa murmushi ɗauke a fuskarta tace kema kina layin "yan hassada ko......? Tayi dariya. Tou dama malam ya faɗamin "yan hassada zasu fito ɗaya bayan ɗaya ngode ma Malam daya nunamin ke Kaka , ashe haka kike hassadata ban sani ba ? Gaki nan Malam ya zaƙulomin , buɗe tafin hannunta tayi tare da nuna ma Amisty tace me kika gani ne ? Wata irin ƙatuwar ƙuna ce a tafin hannunta , bayan ta tabbatar Amisty ta kalla ta naɗe hannun da tsumma kamar yadda yake farko cewa malam yace wannan ƙunar sai a gidan D ' K zai warke , ta ƙarasa maganar tana dariya irin ta mashaya......

Da massara ya isa Abuja shi yasa tunda ya shiga ciki bai fito ba yana kwance a gado jikinshi har ƙyarma yakeyi , saida yayi sallah isha'e yasha magani ya koma bargo. Ba tare daya juya bayanshi ba yace Papi tashi ka kawomin wayata ana kirana , sauka yayi ya ɗauko wayar ya kawo mishi , samin a kunne na yayi maganar yana kallon Papi , yadda yaga anayi idan za'a ɗauki wayar yayi tare da ɗorawa a saman kunnen Dikko shi kuma ya fara magana , bayan gaisuwa yace wallahi banajin daɗi ne Momy , magana tayi sannan yace a , a , shiru ya sakeyi bayan wani lokaci yace gaskiya ban sani ba. Ey Papi Momy zatayi magana dakai , cire wayar yayi daga wurin Dikko ya kara a kunenshi yana magana da tsantsamar muryarshi , kusa da Dikko ya ajiye wayar bayan ya gama ya koma ya kwanta gabanshi , yana mishi sannu , cikin yanayin damuwa yace Papi kaga Momy bata kirani ba ko ? Ta kiyaka Yaya , a , a Momyn goruba , ɗaukar wayar yayi yana cewa bari a kirawota Yaya ,

Tsareshi da ido Dikko yayi , saida ya yagaji da shirmenshi ya ajiye wayar ya fara bacci tunda bai iya kira ba , saida ya tabbatar Papi yayi bacci yayi mishi addu'a tare da gyara mishi kwanciyarshi shi kuma ya fara kiran Sultana , amma tsabar iskanci taƙi ta ɗauki wayar , ya kira harya gaji ya haƙura wanda bai ɗauki waya ba taya zaiyi lokacin duba wani saƙon banza can....

Tunani daban² a ranshi na sabon iskancin da An mata ta koyo , amma yayi alƙawari bazai sake kiranta ba taje can ta ƙari rashin wayanta. Yau sai 12:23am ya cire wayarshi daga jirgi , yana buɗewa kiran Yusra yana shigowa da bazai ɗauka ba amma sai yaji tausayinta har wane tsawon lokaci ta ɗauka tana ta kiranshi sai yanzu ta samu kuma bata gaji ta daina kiranshi ba haka batayi bacci ba. Yasan dan dai kawai tayi mishi sannu da hanya ne wacce ma baa matarshi ba ta damu dashi da san sanin halin da yake ciki , shidai bai faɗa mata ba amma yasan kila taje g r a ance mata yayi tafiya ne , ɗauka yayi tare da kara wayar a kunnenshi yayi sallama.

Ajiyar zuciya Yusra ta sauke cikin kissa sannan ta amsa sallammar da mairainiyar murya , ya gda ? Ya tambayeta , bata ansashi ba taci gaba da watso kalamai na matan waje cikin rashin kunya tana kambamashi da zugashi tare da turashi wata madakatar da bai isa zuwa ba , murmushi yayi kaɗan kuma mara sauti ya kalli Papi dake bacci ya riƙe mishi wuya da hannu ɗaya , shiru yayi yaƙi magana ita kuma taci gaba tunda ai tasan yana jinta , duk kiran dake shigowa bai ɗauka ba kuma bai tsinke kiran Yusra ba haka kuma baiyi magana ba yana dai kallon Papi , itace ta gaji ta sauka a layi.

Kiran Hafsa shima ya ansa saidai ita bata doguwar tafiya dan bata da irin kalaman da yake so , duk da yanajin haushin Jiddah yana ɗaukar kiranta , itama Mardiyya tayi nata kuma duk sun hura mishi kanshi yanajin yakai wani baban shege , Sharifa kuwa ai suna tare amma ba'a ɗaki ɗaya ba. Yau ko namiji ɗaya baiyi magana dashi a waya ba saidai a cht , tunda ya buɗa wani saƙo ya haɗe leɓunanshi tare da riƙe na ƙasan ta ciki da haƙori ya kura ma hoton wata kyakkyawar yarinya ido , ɗayar wayarshi ya ɗauka ya kawo hoton Sultana a bayyane yace akwai tazara har yanzu..... Ajiye waccan wayar yayi yaci gaba da kallon hotunan Sultana yana murmushi wani kuma yayi dariya yace An mata rigima Allah ya saukeki lafiya jarumata.......

A dajin data gama tsibbunta a wurin ta kira Dikko tayi magana dashi kamar yadda mushiriki ya faɗa cewa idan ta gama ta kirashi kuma zai ɗauka idan harya ɗauka a lokacin ruwa da iska baya hana Dikko ya aureta sai sunyi aure ,

Ɗan madaidaicin gidane a nan cikin anguwar kwaɗo duk yara²n mata ne suka taru suna ta gulmar mazajensu.......... Har 12:39am gidan cike yake wai ana fira , wasu mazajen su matafiya ne basa nan , wasu kuma suna da abokan zama mazansu suna gidan abokiyar zamansu , ita kuma mamallakiyar gidan mijinta yana can majalisa.

Jakar mace da ita , duk sauran mata sun gyaro gidansu sun gogo ɗakunansu sun saka turaren wuta sunsha wankansu sun taho gidan ballagazar mace fira , ita kuma daƙiƙiyar ta kora mijinta waje ƙawaye sunfi miji dai. Bursunai² da ita sai wari takeyi ba wanka bare wanke ido , wacce batayi haka ba wace fikra gareta na sanin rayuwar duniya....? Tou hausawa dai sunce wanda maciji ya sara idan yaga igiya guduwa yakeyi , masu iya magana kuwa cewa sukayi wanda aka mara yayi hankali yafi wanda aka haifa dashi. Ɗaki daya ne tsal a gidan , nan kicin yake bedroom da toilet , palon nan da kujerunta sunyi daƙa² kalar tashin zuciya , kwanukan da sukaci abinci da wanda aka zuzzubar duk ba'a ɗauke ba , tunda sun ɓata palon kuma wai sai suka koma ƙuryar ɗaki ana fira ,

1 saura mijinta ya shigo gida , a palo ya ajiye ledar biredi daya shigo da ita da ɗan naman daya riƙo musu ya fara tattara kwanukan dake palon , jin buruntu a palo yasa ita mai gidan tace Hadiza leƙa kiga waye , ita Hadiza data tashi fita sai ta cire hijabi ta gyara ɗaurin kallabi tayi palo.....

A palo , da sauri ta isa wurin mijin Halimatu tana riƙe tsintsiyar dake hannunshi cike da makirci irin namu na mata tace haba "yar laɓai ai wannan aikin ba naka bane ba , a gafarcemu tayi maganar tana murmushi mai tattare da ɗaukar hankali , shima riƙe tsintsinyar yayi yana cewa ta bari kawai zai share ya faɗa yana murmushi , suma na bedroom sunaji amma Halima bata fito ba sai kuma Zainab ta fito aka baro Fadila da Halimatu matar gidan kenan a bedroom. Ita kuma Hadiza tana riƙe da tsintsiyar suna jayayya da mijin Halimatu akan bazai saki ba zai share...

Itama Zainab tana isowa ta riƙe tsintsiya haba ranka ya daɗe ina za'ayi wannan abun kunya ka rufa mana asiri mu share , daga cikin bedroom kuma Halimatu tayi dariya tana cema Fadila ai dake bashi da matsala shine zai share bazai basu ba , a palo kuma Hadiza sai cewa takeyi ya bada tsintsiya , ganin dai sun dameshi yasa ya haƙura ya bata tsintsiyar kuma idan sun gama shine ai rakasu gida ,.......

Idan namiji bashi da matsala kece kike koya mishi ya zama mai matsala , idan namiji bai iya yawon majalisa ba kece kike koya mishi , Halimatu da mijinta auren soyayya sukayi , mijinta bashi da kuɗi amma yana da rufin asiri kasancewarshi ƙaramin ma'aikacin gwamnati , sauran matan nan dana lissafo su 3 , ɗayan su huɗu ne a wurin mijinta , bata yini gidanta kuma batacin abincin gidanta kuɗin cefanenta da komai nata take aikashi wa iyayenta tunda ta samu na mijin ballagar mace iyayenta suna buƙata tunda ta wadata saita wadatasu da kasonta na gidan miji. Kullum da ita ake majalisa amma idan mijinta yazo gidanta zata zauna ta kula dashi ta bashi duk irin kulawar da yake buƙata asha soyayya sai ya tafi taci gaba da zuwa kuma shi baisan tana wannan iskancin rashin zama gida ba.

Ita kuma ɗaya mijinta driver ne , idan ya tafi sai yayi wata biyu bashi nan , itama a gidan jakar mace take ci tana sha tayi wanka da wanki itama kuɗin da mijinta yake bata idan zai tafi sai ta shiga adashe tunda an samu na mijin daƙiƙiyar mace , ɗayar kuma mijinta gadi yakeyi a asibiti shi dama baya bayar da wani kuɗi saida idan an samu albashi ya ɗan sissiyo abinda ya sawwaƙa daga ita har mijinta a gidan mijin wawiyar mace suke ci suke sha , itace Hadiza , Halimatu kuwa matar gida ba , mijinta yana aiki a C B N ubangidanshi ya cusashi da satifiket ƙaramin ma'aikaci ne amma dogon buri yasashi yakeyin digiri karatun asabar da lahadi , { part - time } ya kusa gamawa ubangidan nashi yake san ganin ya tashi daga ƙaramin ma'aikaci ya zama babba.

Sai 4 saura na sauka a abin sallah , kuma sai a lokacin naje inda wayata take , bayan na ɗauketa ne naga miss calls inshi 7 , data na buɗe nasan yana online , baya online ya daɗe ma da sauka amma ya turo min hotonshi shida Papi suna kwance a saman gado , wai suna gaisheni kuma in sa Allah a raina in daina fushi. Su basuda zuciya kamar yadda nake mishi gori suna gaisheni. Murmushi nayi tare dabin hoton da kallon , ko ina zaije da Papi ? Oho......! Bakuyi kyau ba shine abinda na tura mishi nima na sauka.

Yau na samu damar zuwa makaranta , kuma Mai gilashi ta bani labarin Sharifa ta tsoratani sosai akanta ta firgitani , na gigice na tsorata , ta ƙara da cewa idan ina maido hankalina jikina tou in tashi daga wannan asararren baccin da nakeyi , ta nunamin hotunan Sharifa ita da Dikko wanda koni da nake aurenshi ban taɓayin irinsu ba , bawai riƙeta yakeyi ba ko taɓata ba dan shi baya da ɗabi'ar taɓe²n mata kawai dai anyi hotunan cikin takon so. Hotunanshi shida Yusra , abindai yamin babu daɗi , raina ya ɓaci matuƙa , amma dake ina da ɗanyen kai kamar yadda Dikko yace sai nayi ma abun bahaguwar fahimta akan yadda ita Sa'adatu ta fahimtar dani , maimakon nabi abun a sannu naji yadda sirrin abun yake saina fara kiran wayar Dikko , wayar a kashe take ma wacce baya rufemana ita kwata² duk lokacin da mune muka kirashi zamuji shi.... Haka na haukace cikin aji naci gaba da turawa Dikko saƙon zagi na kirashi da mayaudari munafuki ɗan iska , Farisa taci gaba da zugani ina ta ɓarke²n zagi kamar mahaukaciya tana cewa ai wannan ma nuna miki yakeyi tsaron gida ya barki , ya barki gadi matar tana waje ya tafi da ita ke kuma an barki tsaron gida , haka taita tunomin lokacin da yayi mata liƙi na ida ƙwacewa gaba ɗaya na warware kamar falfela , duk yadda Sa'adatu taso ta fahimtar dani naƙi saurarenta saida na gaji dan kaina na tsaya , bayan wani lokaci kuma na tura masa cewa tunda dai kai ka lalace ka zama karuwa saina fitar da cikin nan. Duk haka bai isa ba na farakiran wayar Ashiru , shima nashi a kashe yake , shima na tura mishi saƙo cewa Allah ya isa tsakanina dakai har kaga ana cin amana bazaka faɗamin ba , munafukai "yan partyn amarya.....

Umar na kira shima na zage tatas kuma nace masa munafuki da kilbibin faɗi ba'a tambayeka bane ka iya faɗa , dake shi Dikkon tsoronshi kakeji shine baka faɗamin ba yana tare da "yan mata , shima dai na tata mishi ɗan ƙaramin haukata na kashe waya. Wannan duk ya zama zargi da wani tunani daban irin namu na mata , duk lokacin da akace miki mijinki yana can yana kaza ko yayi kaza ko kaza yake aikatawa karki kuskura ki yanke hukunci akan abinda baki da tabbaci akanshi , zargi baida kyau haka kuma yanke hukunci cikin fushi yake haifar da ɗa mara ido , domin ita zuciya kamar iska haka take halbawa hawa take da sauka , ƙoƙari ake ana danneta ba'a biye mata haka kuma ba'a bata abinda take so domin za'ayi nadama da dana sani idan ta kwanta.....

Har aka tashi makaranta ban sake magana ba , haka na koma gida jikina suku² duk abin duniya ya dameni na rasa ina zansa raina , sai yanzu na fara tunanin hukuncin da zai biyo , dariyar shi na tuno da yake cemin ki daina ganin kwana biyu na zuba miki ido ina nan yadda kika sanni ban canja ba halina yana nan yadda kika sanshi. Me zai faru idan Dikko yaga texses in nan ? Me zaice ? Ya zaiyi ? Ni kuma ya zaimin ? Me zai faru.............??? Zuciyata tace duk abinda ya faru sai me ?

Jikin madubi na matsa na kalli kyakkyar fuskata da idanuwa na masu burgewa zararan giraren idona da suka ƙara fitomin da kyan idanuwa na , girata yadda tayi wata kyakkyawar ziririyar saƙa su biyun suka haɗe suka ɗanyo ƙasa , dogon hancina na kalla da kyakkyawan bakina , murmushi nayi tare da maida idona saman goshina. Lallausan gashi ya kwanta luf abun gwanin burgewa , ida cire kallabin kaina nayi nabi gashin kaina mai cikar kyau da ɗaukar ido irin na cikakkin fulanin asali da kallo , dirina na kalla ga haskakakkar fatata komai yaji ga hutu ya tabbata a gareni , zuciya tace kallarki Sultana ɗanyar yarinya dake kin cika ta ko ina komai ya zauna kalar burgewa , shekarunki ma yanzu suke tafiya dan zuwa 20 , me zakiyi da Dikko wanda yaƙi yadda ma ya faɗa miki shekarunshi saboda yawansu , gashi nan ma harya fara squeezing , Allah ma yasa yayi fushin kiga yadda zakici wuta a garin nan , ga kuɗinki a account ga mota ga tsadaddun suruta masu yawan gaske. Sarka "yan kunne zobe ɗan hannu duk na zinari kala² , idan kika fita zaki ci gaba An mata da hannuna na nuna da bakina yadda jirgi ke tashi sama , dariya nayi tare dayin rawa a jikin madubi dan mafitar dana samu , kai zanci uwar² uwayen masu wuta , ashe ma hauka yasa nayi aure a Katsina ? Ai ban taɓa lura da haka naɗu ba sai yau , ana ta faɗamin ban ɗauki abin serious sai yanzu na ƙarasa ina wasa da kyawawan idanuwana.........

Rawa naci gaba dayi ashe dai na haɗu da yawa shi yasa shima kanshi Dikkon yake cemin An mata , gani da tsawo dai² kuma ni ba ƙatuwa ba. Kai gaskiya inada siga da kuma launin burgewa gani kuma yarinya , Sultana yanzu lokacinki ya fara........







*JAMILA MUSA...*
[2/14, 12:12] ~M K: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_



*KWARATA RETURN...*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_


Rubutawa...
*JAMILA MUSA...*



*SAI NA AURI D ' K*


Naki ne "yar uwata 👇🏻
*ASMA'U ZAYYANA*
{{ Asmeenat Xeyyan }} alfaharina bugun zuciyar *JAMILA MUSA...*



🅿 ------ 3



Bani kaɗai ba , mafiya yawan mata haka muke. Duk lokacin da muka shiga cikin wata ni'ima ta daban sai kanmu ya fara rawa mu riƙa yin wani hange na daban , wasu matan basa fara gilu² da kansu sai sun ƙoshi nan zasu ɓalle ƙofar iskanci da rashin kunya. Kamar dai ni yadda na kasance. Gani na tsaya a jikin madubi ina ta kallon kaina yayin da wani sashe na zuciyata ke nunamin in kalli kyauna ! Ashe haka na haɗu ? Haka nake kyakkyawa ? Aiko yadda nake mai kyan nan baima kamata ace ni ina aure a katsina ba , kamata yayi ace ina irin su Abujar nan idan ba Abuja ba ina can wasu ƙasashen duniya mijina ya ɗaukeni yabar nigeria dani , abun ba haka yake ba kuma ba'a kyau take ba. Jin daɗi da arziƙi duk kyanki da iya haɗuwarki sai Allah yaso zakiji. Ba'a kyau , asali ko nagarta yake ba. Arziƙi da hutuwa baiwa ce daga Allah idan yaso sai ya baka ya kuma sa kaji , ni'imar aure daban ce. Allah ya darata ta haka kuma ya martaba ma'aurata. Idan kina ƙarƙashin inuwar aure kinfi ƙima daraja da kuma martaba duk kuwa irin talaucin da mijinki yake fama dashi , kiyi haƙuri kiyi zamanki a gidan aurenki arziƙi na Allahna , kuma wannan ɗin dai shine hatimin tsirarki. Yayin da kika kalli kanki a madubi kika ga ke kin kai ƙarshe wurin haɗuwa ko kyau tou albarkacin martabar aure kika ci , daga zaran inda kikayi yarinta irin tawa kika zuge auren nan kin tashi aiki.

Saboda kiyi duba da wani abu. Gidanku da gidan miji akwai ƙaton banbance² , karki kalli gidanku ana kashe kaji goma duk rana , ana yanka rago duk sati , kina da ɗakin sama ƙaton gado da a c ba'a ɗauke wuta ga wata ɓarkekiyar talabijin ta cinye rabin bango. Kuna cin shagali shayi da biredi duk safiya a haɗa da wani lafiyayen kayan cikin rago , dankali doya kwai da rana a samu wani lafiyayen abinci aci ku kulle na dare da wasu kayan marmari , idan zaki fita a baki driver ko ke ki tuƙa kanki , idan buƙatar shiga bayan gida yazo zaki sauko ne kawai daga saman gado ki shiga toilet hmmmm. Gidan miji kuma koko , tou wallahi wannan kokon ya fiye miki mutunci da kuma kwanciyar hankali , idan kuma kina ganin kin haɗu bara ki kashe auren kiyi gaba , tou budurwar bana tafi ta bara , duk haɗuwarki duk nasabarki duk mutunci duk yadda kike jin kina da nagarta siga ko kyau duk haɗuwarki duk kuɗin gidanku duk iyakar gogewarki da haɗuwarki idan wasu matan na wure tou wallahi ke mayino ce , da kika kalli madubi kika ganki ke kyakkyawa ce ko kin haɗu tou darajar aure ne yasa kika zama haɗaɗɗar idan har tsautsayi ya kaiki kika cire auren nan kina tunanin zaki auri sarki tou fa lallai ko dogari ba naki bane ba danma karki ji ƙamshin masarauta. Ku kiyayi rashin kunya wa mazajenku , kar kuyi irin nawa kuga zagin miji ko rashin kunya ƙauracewa shinfiɗarshi ko rashin mishi sannu da zuwa hanashi abinci da rashin yi mishi magana shine mafita , a , a , wannan babban zunibi ne ga kuma ke mai aikatawa kina kashe kanki ne , kuma kina rage ma kanki mutunci , duk duniya babu abinda yafi mutunci haƙuri da kuma biyayya , zaman lafiya yafi komai karki kuskura ki zama mai tashin fitina a gidan aurenki , ki zaɓi zaman lafiya yafi komai ki kuma kiyayi kanki da haƙƙi....... Karki ce irin halina ya burgeki uhum a , a kar kiyi....

Har dare haka na samu aiki jikin madubi. Saidai inyi sallah in dawo inci gaba da kallon kaina , saida aka kira isha'e nabar jikin madubi naje nayi wanka tare da ɗauro alwallah dan gabatar da sallah , ina gama sallah na fito dancin abinci. Zama na kenan ban fara cin abincin ba akace min wai Umar yana jirana a palon ƙasa ,

Cewa nayi aje ace masa banda lokacinshi , tunda dai na gano makircinshi nasan yadda zan zauna dashi. Ai ni lokacin nida Dikko zai aureni shine yaje ya faɗawa Jiddah , amma ni za'amin bazai faɗa ba , shima Dikkon zai dawo ya sameni sai ya sakeni tunda ba tare aka haifeni dashi ba....

Momy kuwa idan hankalinta yayi dubu ya tashi ɗaya bayan ɗaya , Aunty Bilki baƙar muguwar munafuka ne ta bugawa a jikin mujalla , Umar yazo ya faɗawa Momy Mai gida fa yayi tafiya da Sharifa , wai duk girman Dikko ita Momy bata daina fargaba akanshi ba , ga kuma Papi data matsa mishi tace dole sai yaje dashi tunda hada su Ashiru zai tafi. Saida aka kai ruwa rana ya yadda yayi tafiya da Papi.

Dikko kuma koda yaga saƙonni Sultana baima da lokacinta bare kuma yasa ran zaiyi tunanin bata amsa , mafiya yawan mata suna da cusashshiyar ƙwalwa , ƙalilin ɗinsu ne zasuji zancen ƙarin aure suyi abu na hankali da tunani , ita An mata bai ɗauketa mai hankali ba. Amma insha Allah idan yaga wanda zai auri mai ƙaramar shekaru irin An mata saiya bashi shawara kar ya aura yaje ya auri macen da tasan abinda takeyi , shidai yau gashi har An mata tace mishi karuwa wai shi.... Shine karuwa kamar An mata ta zauna ta rubuto mishi zagi na rashin mutunci , haka Jiddah itama tayi lokacin da zai auri An mata tayita hauka tana zaginshi. Jinjina kanshi yayi cikin ɓacin rai yace aure ba fashi sai nayi idan kin gune ki gyara hali. Kallon Papi yayi dake kwance jikinshi yana bacci duk ya rirriƙeshi saboda gajiya , a bayyane yace idan An mata batayi hankali yanzu ba yaushe zatayi hankali ? Shi kuma yana ganinshi babba duk ya wuce irin wa'anan shirmen , da kuma anyi rashin sa'a suna wuri ɗaya tayi wannan maganganun zai ɗauki zafi shima ya yaɓa mata magana mai zafi ita kuma ta kasa riƙewa ta tattaro nata ɓacin ran da yarinta ta kwaɓa mishi rashin wayau.

Daga nan sai duka , ita kuma a kunne take sai fuuu ta tafi gida tayi yaji. Yadda Mamarta bata sanshi bata ko ƙaunar ganinshi itama sai ta tafasashe ta fara turo doguwar wasiƙa a saki "yarta , ƙalilin matsala ta fito amma ƙaliliyar magana bata iya kashe wutar dake ƙoƙarin ruruwa. Yana ta ƙoƙari wurin ganin ya farka da ita daga baccin rashin wayan data tafi amma baida lokaci kuma shi a ganinshi abinda yasa An mata ta rainashi girmanshi tun farko daya buɗe a gabanta. Yana gani shekarunshi yakai na ita ta girmamashi tasan matsayinshi da ƙimarshi ta kuma riƙa kiyaye wasu kalaman akanshi bata
DOWNLOAD
DOWNLOAD

2 Comments On KWARATA RETURN
avatar
fatima-kasim

4 months ago

Reply

Naji dadi sosai sosai Allah y kara basira

avatar
daiy

4 months ago

Reply

Replying to fatima-kasim

Ameen muma munji dadin kasancewarki anan.

Please Login or Register in order to submit comment