Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

ya fita daga jikina ya tafi......... Saida ya zagaye kaf ilahirin gidan sannan ya dawo mazauninshi. Ƙarar tafiyar takalmina da ƙaraurawar da jigidar keyi ya haɗu yake fitar da wani irin halakken sauti mai daskarar da zuciyar duk wanda yaji sautin. Na wanku daga jiki har kayan dana saka. Fili na iba na fara bada taku. Pa - Pi dake kwance yana kallona yace unguwa zakije....? Ƙaniyar anguwa. Dariya yayi tare da cewa kuma wayyayi baci cau ba. Kusa dashi na matsa nace niɗin ce banyi kyau ba ? Dariya yayi tare da rufe idanuwanshi yace waca nike wayyayi... Tsoki nayi cikin jin haushi na koma gefen gado na zauna. Buɗe idanuwanshi yayi tare da cewa baci zuwa ? Ka rufe min baki munafiki kuma bazan sake zuwa dakai ko ina zanje ba tunda kace banyi kyau. Ɓata fuska yayi ya fara kuka yace wayyayi waca ne. Cike da masifa nace ka rufemin baki kuma bana sanka. Shiru yayi ya tura ɗan yatsashi cikin hanci yana kallona. Ka daina kallona. Sauka yayi daga saman gado yana kuka , duk kiran da nake mishi tafiyarshi yayi yabar ɗakin.

Yaya wai Momy tace bata sona. Tsoki Dikko yayi yace ka wuce ka bani wuri. Gefen kujera ya raɓe yana kallonshi cikin kuka yace kaima baka can Pa - Pi cikin ɗaga murya yace fita ka bani wuri nace.... Fita yayi da gudu yana kuka kaima wayyayi na fata dakai , Daga ɗakin Dikko wurin Ashiru ya tafi kai ƙara...... Tashi nayi tsaye ina miƙewa naji jigidar nan tayi wata irin tsuwwa , cassssss....... Burgeni abin yayi na ƙara bada tako ina matsawa jikin madubi. Tana cossss casss. Dariya nayi na samu abin wasa kamar yaro sabon tafiya da takalmi mai tsuwwa.

A wannan yanayin Dikko ya sameni , shi kuma ya biyo Pa - Pi ya dakeshi daya ce wai ya ɓata dashi. Kamar wani gele ya kafeni da ido yana muzurai. Murmushi nayi danni ina cikin shauƙi ne , iska yaja ta baki sannan yace ina Pa - Pi....? Kaje can ka nemeshi mana. A fusace ya shigo ciki , gudun da nayi dan hawa saman gado yaba jidar nan damar yin ihu sosai , cacasss.. Cosss cisss² cuuu. Wahalallen dariya Dikko yayi dakel a gajiye yace menene ke ƙara......? Yayi maganar yana ƙoƙarin riƙo ƙafata. Da sauri na fizge nayi baya. Tsaya in gani mana. Yayi maganar yana fizgoni da ƙarfe. Da sauri ya hanakaɗe rigar jikina ya kunce zanin jikina. Na tsani jigida sai kin cireshi......... Wace karuwa ta baki ita.....? Ni zaki maida mahaukaci ki riƙa kaɗamin ƙaraurawa , da kokawa ya kamata yana ƙoƙarin tsinkawa. Karka tsinkamin abu , saina tsinka ni ɗan iska ne da zaki riƙa min alama iye ? Yayi maganar yana gauramin mari in sakar mishi hannunshi dana riƙe , cizon hannun nayi cike da ɓacin rai nace bazan saki ba , kai................ Ni kika cizarma hannu. Saina kashe ki.... , a tsorace nace shikenan tsaya baka so ko ? Ey bana so An mata. Shikenan bara in ciro maka , nayi maganar idona cike da hawaye. A tausaye ya kalleni ni kuma na cire jigidar na miƙa mishi. Taro hannunshi yayi dan ansa yana kallona..............








11/02/2020





*JAMILA MUSA...*
[2/14, 12:12] ~M K: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_



*KWARATA RETURN...*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_


Rubutawa...
*JAMILA MUSA...*



*SAI NA AURI D ' K*



🅿 ------ 11


Hararata yayi yana jinjina kanshi baraki bani ba. A shagwaɓe nace umm² ina maƙale kafaɗa daga kwance. Tou bani ya sake tambaya a karo na biyu da kwantacciyar murya. Kuka na farayi ina cewa nidai ka barmin kayata idan baka barmin ba aradu kashe kaina zanyi..... Hawowa yayi saman gadon a shagaɓe yace baki iyawa. A hankali na juya mishi baya ina shashshekar kukan ƙarya na rufe idanuwana tare da ɗora hannun damana a saman fuskata. Kusa dani ya kwanta ya fara ƙoƙarin cire hannuna daga saman fuskata.

Juyowa nayi da sauri na riƙeshi. Yiyh.... Yaja ajiyar zuciya da yanayin buƙatuwa tare da lumshe idanuwanshi da shauƙi. Wai me yasa ne.... ? Da yanayin matsuwa yace riƙe jigidarki mayi magana daga baya.

A makare na fito daga ɗakina da sauri. Yau na makara ko kalaci bazan tsaya yi ba. Ɗakinshi na wuce yana ta wani tattare²n wasu "yan guntattakin tarkacen dashi buƙatuwar shi ne , a ɗan zumuɗance nace muje na makara fa. Ba tare daya kalleni ba yayi ɗan gajeren tsoki wai ya manta bai faɗamin ba zaiyi tafiya. Cike ɓacin rai na matsa kusa dashi da hannuna na tambayeshi cewa ina kuma zakaje ne ? Nima ban sani ba saina fita , cika idona yayi da hawaye da siririyar murya nace haba Dikko bana baka haƙuri ba ? Shine kuma zaka tafi ka barni ? Riƙe kunnuwa na nayi a dai² lokacin hawayen idona suka samu damar gangarowa a saman kumatuna cewa dan Allah na bari na ƙarasa maganar ina riƙeshi. Tunda na baka haƙuri sai kayi haƙurin kuma ka bari idan na sake sai ka tafi haba Dikko........ Na ƙarasa maganar ina ɗagowa daga jiki nai mishi jigataccen kallo.

Kiyi haƙuri bazan wani daɗe ba. Ya faɗa yana taɓa hancinshi da ɗan yatsa manuni. Nima gaskiya idan ka tafi yau zanji kamar ince ban yafe maka ba , taƙaitaccen murmushi yayi tare da duƙawa yana gyara takalmin ƙafarshi. Ci gaba nayi da cewa tou kafa sani tafiya yau gaskiya shiga haƙƙina ne idan ka tafi ka barni zanji irin yanayin daka faɗamin jiya dan Allah , wallahi idan ka tafi gaskiya zan shiga tashin hankali. Da sauri ya ɗago kanshi ya kalleni da yanayin damuwa yace ke meye haka ? Ai gaskiya na faɗa idan ka tafi fa matsala za'a samu. Riƙeni yayi jikinshi ta baya da kwantacciyar murya yace wace irin matsala ƙaramar yarinya? Faɗamin inji mana yayi maganar yana wasa da gashin gemunshi a jikina. A kasalance nace kawai dai zanyi kewarka , mtsww yaja tsoki dan a yadda na fuskance shi ba haka yaso in faɗa mishi ba.

Rufe idanuwanshi yayi cewa taya ake kewar miji ? Faɗomin da me zaki ibe kewa yayin da kike tunowa idan muka kasance a inuwa ɗaya ? "Yar marainiyar dariya nayi cikin yanayin jin kunya nace Dikkkkoooo. Wata sheɗaniyar dariya yayi mara sauti mai ƙarewa da hmmm An mata kenan , yanzu dai idan na fahimceki kar inyi tafiya ? Ey wallahi kawai muyi zamanmi mu daina faɗa na ƙarasa ina juyowa na rumgumeshi. Me yasa baka san jigidar da aka bani ?

Takawa ya farayi ina kwance a jikinshi har zuwa bakin gado yake cewa. Mace ita gaba ɗayanta ƙyalƙyali ce , da hannunshi ya nuna yana ci gaba da cewa tangaram ne saboda su mata an haifesu ne domin kwalliya shi yasa ana haifarta ake mata huje dan ado. Baki ga komai na mace yasha ban²n dana namiji ba ? Maganarta tafiyarta kallonta sigarta da komai nata ya ban²ta. Tayi ado da kayan ado masu burgewa da ɗaukar hankali kamar zinari saboda yana gyara mata jini. Ko cikin duhu kikaji maganarta basai an faɗa ba kinsan ita mace ce , domin zakiji maganarta da sanyi² cikin natsuwa tako nagarta matsayi da kuma aji. Ha kuma maganar namiji yake. Kalli takalmin ƙafata kinga irin nawa da naki da ban²ci , naku masu ado ne na maza kuma ko oho. Ayi masu wani tsini² a saka musu duwatsu da maɗauri macen kenan shi yasa komai nata yake da burgewa. Ni ina san matana ta kasance mai ado da zobe , "yan hannu , ɗan kunne tsarkar wuya da ƙafa amma tsabar sharri yanzu ba damar mace ta saka tsarƙar ƙafa shike nan an kaita wani wurin daban dan rashin adalci. Hmm itama dai ado da ita wani ɓoyayyan sirri ne. Jigida duk tana cikin kayan ado na mata sirrinta daban ne amma matan bariki su suka sanshi shi yasa sukafi yin amfani da ita....

Mata 10 idan kika tarasu zaiyi wuya a cikinsu kaf ɗin su ki samu mace ɗaya data saka jigida a ƙugunta. Amma idan zaki tara karuwan da suka san kansu suka goge suka kuma daɗe tare da sanin sirrin bariki zaiyi wuya kika haɗa mace 10 ki samu mace biyun da ƙugunta bata ɗaura jigida ba....! Dalilin ɗaurata da sukeyi ni nasani amma bazan faɗa ba. Dalilinsu na sakawa da motsinta ai sunsan abinda take haifar da , kuma nima nasan dalilinsu. Nine dai ke baki isa ki ɗaurata ba tunda bana ra'ayi amma duk abubuwan da kikaji na faɗa a farko idan kika saka wannan ra'ayi na ne har tukuici ma saina bayar. Nidai dan Allah ka barmin abuna in saka , An mata na barki a saka lafiya amma da sharaɗi , tom , karki sakata ki fita , na yadda , duk kuma lokacin da kika buga ƙaraurawar tou fa lallai zanzo kuma kinsan ni bana zuwan banza. Wannan shine idan kin yadda ni da kaina ma zan ɗaura miki ita..... Na yadda , kin yadda ? Ey na yadda , banajin yi haƙuri babu wani wallahi² , jinjina kaina nayi tare da tabbatar mishi da ey na amince. Saukeni yayi daga jikinshi yace ina zuwa , inda ya ajiye jigidar yaje ya ɗauko da kanshi ya zagayamin ita so adadin ruɓin daya ruɓanyata a ƙuguna. Nima na shiga sahun mata masu ɗaura lambar ƙugu.

Yau banje makaranta ba haka kuma Dikko baiyi tafiya ba. Yadai shiga gari. Pa - Pi kuma yana wurin Momy dan tun jiya da yaje yakai ƙara wa Ashiru ? Ashirun cewa yayi suje yakai shi wurin Momy. Shine yakai shi kuma yace a faɗa mana dani da yaya ya fata damu , kuma duk bamuyi cau ba wayyayi. Itama Momyn goyuba bata hatu ba. Shima Yaya baiyi cau ba. Dokin ma shima baiyi cau ba. Itama motarshi bata da cau ta Dady tafi hatuwa. Kuma kada mu sake muma muzo musu gida.

Saida na gama hidimar gida kaf duk abinda zanyi nayi na ƙare sannan na ɗauki wanka na kulle wanka da wani irin kafirarren leshi mai sauƙin nauhi. Nasha ado da duwatsunan wuya kunne hannu da "yan yatsu. { bawai dutse ba no׳ cikin tsarabar da mai gida ne ya kawo na saka wani daga ciki dan burge shi a wannan sansanyar maren sakaliya. } na wani kawo ɗaurina dai² da zamani na kafe wankan dashi. Naɗan yayyafa ruwan turare bawai yadda kamshin zai zama mai cutarwa ba haka kuma bazai tashi zuciyar mai shaƙa ba. Cikin kujera na koma na soke da zama irin na matan masu kuɗi ina ta ƙasaita ni matar Dikko. Wayana dake gefe ta na ɗauka na kira Mai gilashi , cikin sakonnin da bata wuce 30 ba ta shiga , tana shiga ta ɗauka. Bayan gaisuwa nace mata maganar jigida wai meye sirrin ne ? Ke malama wannan jigida da kika ganshi yasha ban² da jigidar da zaki je kasuwa ki bada kuɗi ki siya kinji ? Wannan ɓoyayyar sirri ce kuma bawai na baki dan kije ki saka weldrop kiyi ajiyarta ba , ki ɗaurashi a ƙugunki hajiya kiyi tafiya da isarki.

Halbawarta ɗaya tsallen zuciyar duk namijin daya ji kukanta , adadin buguwar zuciyarshi adadin buƙatuwa , ke wannan jigidar bala'enta yasa sukayi mata suna da huce takaici. Baga namiji ba har kishiya saita shafa miki lafiya , idan uwar naci ce da rashin zuciya taita zama tana haɗiyar baƙin ciki , idan kuma tunburƙuƙu ce wato mai zuciya a maƙoshi filin gidan zata barmiki. {{ miye ribarki idan kin kora wata ? Idan ta tafi ma wata zata zo , itama idan kika sake korata wata rana a kawo wacce kema zatayi out dake.... }} Ma damar dai zaki motsa ? Idan har tayi kuka tou fa lallai ke kasuwa ya buɗe ba gareki ba garemu masuyi domin kasuwanci.

Hmmm amma ni kinaji da farko Dikko cewa yayi baya so fa , dariya tayi tare cewa ɗan duniya wai ko yace miki akan wani dalili ne ? A , a , kawai dai yace bana ɗaurawa danshi wai baya ra'ayin lambar ƙugu. Sake sheƙewa tayi da dariya tace kai kiyi haƙuri amma duniyanci mijinki ya shafe tudun da bakya tunani , yanzu ina jigidar ne ? Ce masa nayi dan Allah ya barmin ina so , shin ya baki ita ne ? Ya bani mana gashi a ƙuguna ɗaure. Taf lallai kam Sultana sannu da ƙoƙari. Yawwa na faɗa ba tare dana sake magana ba ita kuma taci gaba da cewa. Baice miki komai ba bayan haka ? Ni baicemin ba ? Karfa kiyi ƙarya ? Ai kinsan ni ƙarya ba ɗabi'a na ne ba. Ki ranste baice wani abu ba , Mai gilashi kinsan bana san ayi ta tsayuwa a magana ɗaya mu matsa gaba ko macimma matsaya. Gaskiya sirrin irin jigidar nan rufaffen sirri ne , buɗeshi da sanin matsayinshi sai tuɓaɓɓin mata. Mafiya yawan maza dubu a cikin ƙaso miliyan zaiyi wahala ki samu namiji dubu dake ra'ayinta , domin ɗaurata cikar duniyanci ne shi yasa mafi'akasari mu matan bariki ne mukafi amfani da ita. To ke me yasa baraki sakawa naki ba idan dai harshi mai ra'ayi ne domin gyara adonki da burgewa. Sarƙa "yan kunne zobe da ɗan hannu duk domin mata akayi su , shin "yan hannun basa ƙara ne ? Ke kanki da kika saka shin ya kikeji kanki dan Allah idan suka motsa ? Mata masu hikima sune suka san yadda abun yake badawa , amma iya ado dasu sai jajirtaccin mata masu duniya , ƙasaitacci bugun farko a filin sanin sirrin rayuwar zaman takewar aure.

Idan dai har ke mace kinsan damarki da haggu bazakiyi sake ko sakaci da ado ba. Kaso casa'in na mata , auna sauke min gashin kansu kiga yadda suffarsu zata zama ? Amfanin wanka da ma'anar yinshi ya tattara a wurin mu da mukeyin shi. Idan har mace ta sauke gashin kanta domin rashin buƙatuwarshi idan har ta haɗa da girarenta wane suna mu zamu kirata dashi ? Duk da dai cewa gaban rigarta ya turo. Zuwan farko ba'a kallon structure saidai a kalli yawan ado da wanka. Buƙatar duk data barki barin gashin kanki da gyara , gyaran gira a duk ƙarshen mako ko wata dalilin ne ya kamata yasa ki kasance cikin ado da kayan ado masu burgewa. Misali , macen data bar gashin kanta bujur² bata tajewa ba kitsawa da banbanci da wacce ta gyarashi , wacce ta kitsashi kuma fitar ainahin kyawun fuskarta yafi na wacce ta taje ta barshi a kunce , matsayin "yan kunne da rashin su a jikin mace tamkar ƙururrumar buta ce mara murfi. Kallo ɗaya zakiyi mata ta baki kyankyami ko amfani zaki da ida tou zakiyi shine ba cikin natsuwa ba , kema kanki idan kikayi baƙon kunya kinajin kunyar bashi ita yayi amfani , tou haka macen da babu ado matsayinta yake a wurin mijinta. Gugar zana , fushi ga masu ɗabi'ar riba ga masu ɗaukar gyara.

Idan baki manta ba kwanaki na fara baki labari akan naje asibiti ranar da muka zo gidanki dasu Hadiza ko ? Umm , yawwa tou tsaya kiji kaɗan daga ɓarnar jigidar Mai gilashi. Tunda na ɗora idona akan Alhajin da muke zaune a gidanshi raina ya biya dashi , duk wata alama da akeyi nayi mishi ɗan iskannan yaimin taurin kai. Gadai yadda abun yake.....

Banda murƙushe² babu abinda Mai gilashi takeyi. Lokaci bayan lokaci ita Hadiza takan ce mata sannu , haka suka kasance a asibiti har layin ganin likita yazo kan Mai gilashi. Tunda ta miƙe ta fara tafiya hankalin duk wani mace ko namiji dake wurin saida ya kallonta har ta shiga inda zata ga likita , tunda ta maida ƙofa ta rufe bayan ta shiga taci gaba da bada tako jigida taci gaba da kuka , wuri ta samu ta zauna inda marasa lafiya ke zama domin shi likita yayi miki "yan tambayoyi dan gano damuwarki. Tana zama jigidar ta bada wani zutt² domin dai²tuwa kamar yadda mai sarrafata tayi.

Kiran sunanta likita yayi bayan ya kalli fayil inta sannan yayi ɗan rubuce² yake tambayarta abinda yake damunta ? Ciwon sha'awa shine amsar data bashi , ummm ? Ya sake tambayarta a karo na biyu , a ɗan yatsine ta sake cewa ciwon sha'awa nace maka , kallonta yayi tare da cewa ban fahimta ba ? Kauda kanta tayi gefe cewa kai likita ne ko kuwa dai ? Meya sameki ne ? Nadai fahimce ka kanajin daɗin kalmar nan kaji , sake maimatawa tayi , shiru yayi bai sake tambayarta ba , ita kuma ci gaba tayi² da maimaitawa cike da iskanci. Hajiya ai naji , yawwa wai idanma bakaji ba dan dai kasan nidai bana gaji da faɗa ta ƙarasa maganar tana faɗar kalmar sha'awa. Rubutu yayi a fiyel ɗin sannan ya rubuta mata magunguna yace ta ɗauka taje ta siya....!

A malam likita da sauri haka har ka gano ciwona ? Bayan kuma ni banyi maka bayani ba ? Ɗauka ya faɗa a ɗan ɗaure. Taɓa takaddar tayi tare da dafa hannunshi da yake turo mata cewa idan kuma ban ɗauka ba fa ? Sai kici ƙaniyarki , murmushi tayi tattare da salon yaudara tace saidai kai kaci min ita , ta faɗa tana masa kallon saka shi a tarko take ci gaba da cewa ka taɓa ganin inda aka yanka ka kaci kanka kuma bayan ka mutu ? Adireshin gidanta kawai taci gaba da faɗa mishi tare da ɗaukar biron gabanshi ta juya takadar daya rubuta mata maganin ta rubuta lambar wayarta , sakaran likita mai zubar da abinci a tsari. Tana faɗin haka ta miƙe ta fara tafiya , jigida kuma taci gaba da tsuwwa , kamar wani gelele haka ya bita da kallo , saida tazo bakin ƙofa tace ai nasan maganin ciwona ɗan raini , bana muradin shan maganin saidai in shanye mai rubutawa. Harararshi tayi irin ta kwaɗayi sannan ta riƙo saitin jigidarta ta kakkaɓa mishi , wani irin ihu tayi cocas casss chuss , na barka lafiya ta fice daga ofishin.... Dariya yayi bayan Mai gilashi ta fita tare dayin ɗan gajeren tsoki yana jinjina ma lambar iskancinta...... A maimakon abinda ya kawoni saina ɓige da karatun ƙarya domin amfani da wata manufa sai nabar waccan buƙatar nayi amfani da wacce ta samu. Likita ya biyoni kuma na ƙaddamar dashi a jam'iyata.

Alhajin da muke gidanshi kuwa , can wurin gantalina na ganshi ya rumgumo wata tsohuwar mace. Matsalar gidanshi shi matarshi ma'aikaciyar gwamnati ce , bata da lokaci da safe da dare kuma tana bacci. Ba'ayin wata shaƙuwa sai weekend. Idan ɗan abu yasa tayi masa sai tasa a kira mata ni , inzo inyi mata kaza². Ɗan sharomin ɗakin Alaji fita zanyi na makara Office ? Ɗan dafa mishi tea da Allah na dawo a gajiye , idan na dafa zatace ɗan miƙa mishi ya cika tsattsafa. Tsayayyen namiji ne mai ji da kuzari , yana da shekaru kusan hamsin da "yar ɗoriya amma nidai a hakan yayi min wallahi. Ina buƙatarshi , karo na farko nace masa Alhaji zan baka jikina wurin E yane idan dai har zaka iya jurewa har gari ya waye. Ka more ƙuruciyata da tsufanka ni kuma in more da dukiyarka. Yamin wulaƙanci ya korani.

Shine dana ganshi da wata mace a hotel naje wurinshi nace masa Alaji wai miye banyi ba ? Sirrin da akayi da ɗaki ai ya isa ayi da tsakar gida. Bai bani amsa ba ya wuce sha'aninshi. Wata rana ina gyaran ɗakinshi ya shigo dan gaskiya yayi faɗawa matarshi akan ta daina tura mishi ni ɗakinshi taƙiji , ina gyaran gado ya shigo zai wuce toilet , aiko na bishi ina cewa ina ne zakaje haka ? Ka tsaya in raka ka..... Shigewa yayi ya kullo ƙofa. Da gudu na fita na nufi sashinmu.

Jigida ta na ɗauro na dawo , daga nan na fara ɗanashi a tarko shima , dan gaskiya da bana ɗaura jigida a gida sai zan fita saina gane ashe duk inda ka kasa kasuwarka siya akeyi saidai idan baka baza abun siyarwa ba. Ashe da wauta nake ƙoƙarin jibgawa rashin saka hannun jari a gida dan na fahimci rashin ɗaurata a gida yin hakanan babban kuskure ne , tou jigida ce ta ciwon ɗan wasa a gida. Tun yana ɗan satar kallona har ya fara dogon kallo. A falonshi dai in goge tv na sakar mishi zani. Shikenan nan fa muka riƙa ɗauke wuta tare , tana can tana bacci ya kulle mata ƙofar ciki ni kam ya buɗemin ta baya naje mu shige bargo ayi dani ba matar gida ba , maganin macen da bata taya miji bacci kenan.. Tun daga wannan ranar nayi saving nashi a alminjar na jawo banza izuwa cikin duniyar rayuwata. Kashi saba'in na kuɗinshi nice nake cinye kaso arba'in , matar gida taci goma mijina yaci biyar Alhaji da sauran matan waje suyi maleji da sauran. Karatuna motar hawata kuɗin mai da duk sauran buƙatuna shine abu a sauƙi fa dare da yawa na ɓata kafin na taka babban matsayi. Malaman makarantarmu suma dai muna ɗan rage yinin karatu a ofisoshinsu. Na samu kuɗi wannan harkar fiye da yadda bakya tunani Sultana amma dai matsalar har yanzu ko gwamna ban samu gani ba , bayan kuma naji ance manyan karuwai gwamnati tasan da zamansu. Ashe ban sani ba farashin karuwanci yanzu ta faɗi har haka ƙasa wan²r. Tirr da karuwancin zamani marar digi wallahi. Karuwan wancan ƙarnin su sukaji daɗin karuwanci banda karuwan yanzu da gwamnati take ma hassada , a iya a hasko ka a talabijin domin a bawa sauran masu sha'awar shiga karuwanci su shiga da ƙwarin guiwarsu gwamnatin jaha ta daƙile wannan hanya. Jinjina ga gwamna mai kishin jahar sa , mai daƙile gudun tafiyar ɓarna a yankinshi. Allah ya ƙarawa mai girma gwamnan jihar katsina lafiya da nisan kwana...... Irin wannan shuwagabanni muke fatar samu masu daƙilar da ɓarna suyi ƙoƙarin bada ƙwarin guiwa wurin kafuwar ci gaba da ƙoƙarin koyar da ci gaban rayuwar yara masu tasowa , da su gane shi iskanci ba wani riba bane dashi.

Mutanen kirki masu daraja su suka dace da a nuno hotunansu a akwatin talabijin ba mutanen banza ba , na gari sune abun nunawa duniya domin al'umma tayi koyi dasu , tsakanin karuwa da talabijin saidai a nuno hoton shegiya ana zaneta...... Hmmm gaskiya Nana Mai gilashi ina zuwa nayi baƙuwa zan kiraki zuwa anjima idan kuma ban samu kiranki ba sai mun haɗu makaranta.... Ina faɗin haka na ajiye waya inawa baƙuwa barka da zuwa. Bata ansa sannu ba tace ashe yasan baya nan yacemin yana gida ? Mai bin Rabiya ce , kila yana kusa ki kirashi kiji , ina faɗin haka na gaisheta tare da wucewa ciki dan gabatar da sallah magrib.

Dikko shida Pa - Pi ya dawo can ta matsoshi da Momy itama yayo mata yaji , yace itama wayyayi ya fata da ita abincin su ma babu daɗi Momy goyuba ta iya , zagi yayi ta zane mishi baki yace bazai ƙara zuwa ba kuma ko ta ganshi idan tace Pa - Pi zaice ya manta ta. Shi Yaya baya dukanshi. Shine ya
DOWNLOAD
DOWNLOAD

2 Comments On KWARATA RETURN
avatar
fatima-kasim

4 months ago

Reply

Naji dadi sosai sosai Allah y kara basira

avatar
daiy

4 months ago

Reply

Replying to fatima-kasim

Ameen muma munji dadin kasancewarki anan.

Please Login or Register in order to submit comment