Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

ƙasarshi sannan ya fara rattafo mata bayani kamar yana karantawa a rubuce. Ya kuma ɗora da cewa ta gode Allah da tazo wurinshi daga yau kuma damuwa ya ƙare. Aurenta da Dikko anyi an gama kuma a ƙarshen watan nan ne , yaci gaba da labarta mata rayuwarta ita kanta , Hafsa tayi na'am da wannan bayani sosai dan haka akayi ciniki bugun farko miliyan biyu ba tayi idan aka taya ko anyi aikin baya ci , za'a siya jajayen raƙuma da jajayen sanaye jajayen tumaki tattabaru jajaye da kaji suma ja kuma duk ko wane za'a siyo mata da mijinta guda biyu² , shanaye maza biyu mata biyu kenan huɗu² mace da namiji a cikin ko wace dabbar daya faɗo....

Zatayi magana Amisty ta rufe mata baki tana cewa malam yi haƙuri zamuyi magana , jibi idan Allah ya kaimu za'a kawo kuɗin , tana faɗin haka taja Hafsa suka tafi. Bayan sunje gida ne Hafsa take cewa ita ina zata wani samo 2million ne ? Tada ma sigari wuta Amisty tayi saida ta ibi hayaƙi tace riba zaki ci ne , duk gidan da kika ga anyi zazafen abinci tou karki bincika ma'ajiyar abinci dalilin haka da sanin gaskiyar sirrin yana wurin mutanen gidan. Ki zuba kuɗi gona yarinya ko kin samu albarkatun gona , wannan malami da kika gani malamin "yan siyasa ne shi yasa kikaji aikin nashi da kuɗi sosai , ga tsada fa amma akwai biyan buƙata , gwamna kanshi wurinshi yake zuwa shine ya ɗaurewa gwamna ƙugu ya koma mulki , ai ya miki sauƙi ma ne saboda ni. Ai da banje ba aikin nan kila sai ya kai miliyan huɗu , ba nace miki shine yayi ma Sultana aiki ba? Kinga tana can ta shige abunta. Hafsa tace miliyan biyu fa Kaka ? Amisty tace miliyan biyun , miliyan har kuɗi ce da zaki tsaya kina wani jinjinata ? Hafsa tace ai inda zan samosu shine damuwata....

Kashe sigari Amisty tayi sannan tace ke kuwa kike da miliyan biyu da wurin samunta. Idan baki dashi ai Babanki yana da. Kije kawai ki tattaro takaddar wani ƙaton gida ki siyar , idan aka ɗaura aure ƙarshen wata D ' K zai biya. Kinga basai mu siya ma Dady sabon gida ba a manyan anguwanni dake cikin garin nan ba ? Murmushi Amisty tayi tare da nuna Hafsa da ɗan yatsa manuni tana cewa anya ma mu D ' K zai barmu muje gidanshi......? Dariya Hafsa tayi cikin jin daɗi cewa sai kunje mana tunda yana aurena ai dole ma ne yaso duk abinda nake so. Amisty tace yawwa "yar gari yarinya ta gano hanya mai takaba ta buƙaci kwarto...

Hafsa kuwa dariya tayi tare da warware hannunta taci gaba da cokalar ciwon tsakiyar hannunta , ihu take dan azaba amma cikin yanayin kafurci take ƙara faɗaɗa wurin dan bata so ya warke tunda malaminta yace idan hannun ya warke bata babu auren Dikko har abadan duniya , shi yasa ta hanama hannun nan zaman lafiya kullum sai ta kwareshi , sai rami hannun yake yana tafi , wani irin wari yake mara daɗi har ya kusa ɓulewa ta baya , dan dai karya warke ta rasa Muhammadu Dikko. Ba magani kuma ba'a buɗeshi yana shan iska kullum sai caɓewa yakeyi abunda zot takaici......

Mardiya tsakiyar dare ta firgice. Bayan an kaita maƙabarta a daren , ganin gari yana tafiya , shiru yana ƙara dosowa. Maƙabarta tana daɗa ɗinkewa duhu yana ƙara bayyana ta gigice , hmmm hausawa dai sunce komin hasken farin wata dare abun tsoro ne , ga dare ga matacci kwance a cikin ƙasa , wadda su duniyar da komai sun tattara sun ajiye badan sunso ba suka tafi suka kwanta. Duk kashedin da Aunty Suwaiba tayi mata bataji ba , saida dare ya kusa rabawa biyu taji sukuwa saman bedinan dake zagaye da inda aka ajiye ta a cikin mankara kukan tsuntsaye da duk wasu ƙwarina dake cikin maƙabarta ya ƙara yawa kasancewar duniyar tayi shiru. Dan haka ta yada likafanin da aka lulloɓota dashi ta tsallake katanga ta ibi hanya tsirara , hauka sabon kamu......

Boka da Aunty Suwaiba basu san ba Mardiyya ba. Saida alfijir ya fito , bayan anyi da Mardiyya zata dawo alfijir yana ketowa , har 6 saura ba Mardiyya ba labarinta dan haka suka tunkari maƙabartar ba labarinta sadai mankarar da likafinin data yada ina ta tafi............???

Kwance take cikin kujera , ba kwanciya irinta ta yadda ake kwanciya ba , zaune take tayi irin kwanciyar nan ta "yan gayu kujerar ta riƙeta dai² burgewa , wani fitsararren ɗinki ne jikinta , halittar jikinta tayo waje ta kashe ɗauri dai² da zamani , hoto tayi tare da turawa daga ƙasa ta ajiye mishi barka da dare... Tun kafin daren yayi har anyi an ajiye. Yusra... Bayan ta gama hotonta kuma ta fara tallar surar jikinta tana video , duk saida ta safke kayan jikinta tayi ma Dikko video ta nuna mishi muhimman wurare a jikinta tare da faɗa masa ta sadaukar mishi. Tana video tana faɗa mishi nashi ne fa duka ya gani ya daina kawaici , kuma me yasa baka kallona idan nazo wurinka ? Baka cewa nayi kyau ? Videon ma har yanzu baka cewa ka gode ? Ƙafarta ta ɗaga ta ɗora saman madubi tana ci gaba da ɗauka tanayi tana dai maganganu irin nasu na gogaggin karuwan da suka san hannunsu , saida ta gama tasharta da iskanci iri² ta yadda duk musulincin namiji da tsoron Allahn shi idan ya gani saiya ƙara kallo sannan ya fara istigifira ya goge , idan kuma sheɗan yayi galaba ya tafi ruwa , maida kayanta tayi sannan aka yi ma Dikko vye² aka wani ajiye mishi a whatsapp.....

Murmushi yayi a wahalce. Cikin jan hali da jarumta bawai dan yanajin daɗin yinshi ba , shi kaɗai yasan bala'en dake zungurar mishi zuciya , danben ma dakel ya maida naushi saboda baiyi shi cikin natsuwa ba , wallahi baida lafiya zuciyarshi tun jiya take zugewa. Dakel ya kalli Sultana dake kwance gefenshi tayi ruf da ciki tana kuka , a wahalce yace An mata ki rufamin asiri ki dawo nan ya nuna bayanshi yana cewa kuma ki gyara kwanciyarki. Bazan koma ba , da damuwa yace to² ba komai haka ma yayi , daga haka bai sake magana ba ya dafe ƙirjinshi yana yin bayyanan nen numfashi , jin bai sake magana ba kuma na gaji yasa na tashi na koma inda yace in koma in kwanta tun farko ina mita cewa kuma a saman cikin zan kwanta , shiru yayi yaƙi magana yana kallo bango da yanayin tunani. Jin zan mutu yasa na ɗauki wayata na nufi ɗakina...

Saida nayi wanka na gyara jikina sannan na ɗauki wayata na buɗe data nake duba saƙon da Mai gilashi tace ta ajiyemin , ganin cht in da yawa yasa na kasa binshi na tattara na ajiye , amma na duba saƙonta da tace ni duk yadda za'ayi inzo gidanta , kuma zanje , saida nayi azahar na shirya dan zuwa gidan Mai gilashi , komawa da nayi ɗakinshi ɗaukar makullin mota yasa yasan fita zanyi , duk da baida lafiya ya balbaleni da masifa waini wace irin mahaukaciya ce ? Baya faɗamin baida lafiya ba shine zan fita ? Tou inje in fitar idan na dawo zan samu ya mutu sai in zuba ruwa ƙasa insha. Wuri na samu na zauna ina kallon ƙasa , yaci gaba da cewa zaki ga kamar ina takura miki ne duk girman duniyar nan wanda kike ganin yafi ni ko yafini sanki yaudararki yakeyi , niɗin dai da kika raina nine zan faɗa miki ko zai miki zafi , ai baka san abinda zanyo ba. Koma me zakiyo bazaki fita ba , kuma na rantse da girman Allah idan dai kika fita yau wallahi idan kika dawo saina zaneki ki fitar wawiya dake. Ƙasa² nace dole kacemin wawiya tunda ka samu abinda kake so har ka samu bakin magana , tsaf ya jini yace kije duk inda kike so , in Allah ya yadda zan zuba miki ido kuma saina ƙara aure ke kije kiyi yawo tunda shi kike so , yadda kika san katsina ko ni kaina bansan garin nan ba , lungu da saƙo sai ance Dikko naga matarka kullum kina bisa titi ke da kikafi ƙarfin mijinki. Idan na ƙara auren ta zauna ta kula dani , ta dafamin abinci ta bani inci da soyayya bata bari yunwa ta kamata , abinci akan lokaci kalami masu daɗin sauraro bata barin kunne na yaji magana mara daɗi saboda soyayya bare taimin gori na kwanta da ita , kullum ma nema na zatayi ko bana so sai ta bani tana ƙaramin cikin san kasancewa da tsari. Taimin wanka ko ɗakina an gyaramin , idan banda lafiya ta riƙa bani magani insha tanamin sannu. Ta faɗa da launin so. Kije can kita haukarki ta kwaceni miki ni sai gani na yayi miki wahala. Ina can inda ake riritani kamar yaron goyo , da nace uhum za'ace ina ne ....? Ya faɗa a shagawaɓe yana wasa da idanuwanshi. Kallonshi nayi ina kuka , yace ey aure ba fashi tunda ke kinajin yarinya ce kije kita rashin wayonki , duk kyan ɗawisu idan baida ado ai komai kuɗi yai maka banza bara ka siya ba , magana ce ya faɗa mata a kaikaice ta zancen da tayi mishi a daren jiya...

A tsiwace nace zan gyara maka ɗakin , bana so zan gyara abuna. Yi haƙuri , ki naɗa gammo ki ɗauka keda za'ayi ma abiyar zama , ƙara kallonshi nayi yace daina kallona kar in cake miki ido ya ƙarasa maganar yana fiddo duk girman idanuwanshi , ƙara fashewa nayi kuka na tashi na fara gyara ɗakin ina kuka. Murmushi Dikko yayi tare da bin Sultana da kallo cike da tsantsar so , yanzu ya gano ciwonta , a ranshi yace kaji yarinya da baƙin ciki zata hanani zaman lafiya ta firgice ta tafi Mama tace ta gama aurena , da gaskiyarta fa , wallahi An mata babbar ƙaddara ce sai mai rabo zai sameta , tabbas idan ta tafin a tsautsayi labari zaisha ban² , ki rufemin baki bana san kuka kin sani ko ? Bazanyi shirun ba , tou kiyi zanzo in kamaki. Amma ai kasan mai ciki batayin aikin wahala kace inyi , ni nace kiyi aiki ne ? Amarya nace ko kece amarya ? Allah yana kallon ka na faɗa a dai² lokacin dana zo ina goge gado kuma har yanzu banyi shiru ba...

Da amaryar da zan auro ce idan tazo kusa dani sai ta sumbaceni a nan ya nuna yana min kallon ƙasan ido , cikin fushi na sumbaci inda ya nunamin , riƙeni yayi yana wannan kukan yaudarar nashi da bana so , a gajiye na kwanta saman jikinshi. Murmushi yayi sannan yayi magana da yaudararriyyar muryarshi ya faɗa a wahalce An mata daina kuka yayi maganar yana hawo dani saman gadon , kalli , kallonshi nayi ina fushi , kwantar da idonshi yayi yanamin kallon rainin wayau , yi haƙuri ya bada haƙurin yana rufeni a bargo....

Kwaɗo...
A gajiye ya shigo gidanshi ya ɗibo gajiyar makaranta , yunwace yake dan ya fita baiyi kalaci ba haka ko wanka baiyi ba , saboda da ya dawo masallaci tuni Hadiza tazo gidan har ta shiga toilet in tanayin wanka , haka nan ya fita waje ya ɗan wanke jikinshi ya goge bakinshi da omon wanke baki ya fice daga gidan. Yanzu ya dawo palon kuma cike yake da mutane , hada Mai gilashi data gangaro kwaɗo itama dan rage rana take zaman jiran kiran Sultana amma shiru kakeji , ita kuma tana tsoro ta kirata ace Dikko yana nan... Mijin Halima yana shigowa Mai gilashi ta gaishe ta fice da damuwar rashin kiran wayar Sultana....

Gaishe shi kowa yayi tare da mishi sannu , ansawa yayi da yanayin anshi karka rasa ya wuce ciki. Shiru² Halimatu ta shigo amma taƙi ta shigo , ga yunwa yanaji kuma a matse yake yana san ya fita yaje toilet amma yana jin nauhin ratsasu suna zaune a palo ya shiga ya kuma ratsotso ya fito yanajin kunya gaskiya...

Matarshi ya fara kira a waya , amma sai bata ɗauka ba daga palon tace ya akayi ne kake kirana ? Bayan kasan ina gidan , baiyi magana ba ya tura mata text tazo yana kiranta , duk saida ta nunawa ƙawayenta wai kiranta yakeyi , shewa akayi gaba ɗaya aka dunƙule kawuna wuri ɗaya ana zance maganin data sha shine haɗarin , ashe ba dare kaɗai yake aiki ba harda rana , saida ta ballabaɗashi tayi bedroom..

Halimatu dan Allah kuɗan koma daga tsakar gida zan shiga toilet , cike da rashin kunya tace mu koma waje duk iska da ƙura ta barbaɗemu muyi datti ? Da yanayin san zaman lafiya yace duka mintuna nawa zanyi in fito in bar muku gidan , gaskiya bazamu fita kaje kayi abinda zakayi ai su basa kallonka , haba Halimatu sai in ratsa matan aure da gajeren wando in tafi toilet tsabar ɗan iska ne ni ? Tou meya damesu da kai ? Kaje kayi huɗɗoɗin ka , Halimatu wai me yasa haka ne ? Tou taramin mutane kai mai gida , dama tun jiya naga kakejin masifa , kace buhun shinkafa bai kai maka yadda kake so , maganar jiya ya wuce kiyi haƙuri.....






*Jinin Katsinawa ce....* 👇🏻




*JAMILA MUSA....*
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_



*KWARATA RETURN...*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_


Rubutawa...
*JAMILA MUSA...*



*SAI NA AURI D ' K*



🅿 ------ 5



Ai ba maganar inyi haƙuri bane ba. Idan dai na fahimce ka kawai dai kana mana kora da hali ne. Ah² yi haƙuri ba haka nake nufi ba , yayi maganar yana nunawa da hannunshi da yanayin ladabi. Inda ya ajiye rigarshi daya cire ya matsa ya ɗauka yana cewa ai duk abun bai kai haka ba , nayi wankan ma da daddare idan sun tafi , da ka rufawa kanka asiri. Ɗan shafa gefen fuskarta yayi yana murmushi tare da cewa idan akwai sauran abincin ki bani sai in tafi can shagon Salihu inci....

A tsiwace tace na ajiye maka sai naga bai ishemu ba. Kawai dai mun cinye nasan ka siya can waje idan ka fita. Da kinɗan silalamin ko taliya tunda akwai miya wallahi yunwa nakeji sosai , abincin sayen nan ina ci zuciyata tanamin ba daɗi , tsoki tayi ta fice tana gunguni har palo ba tare data bashi amsa ba. Tana isa wurinsu Hadiza taci gaba da cewa wallahi babu wanda zaisani tsira wata girki yanzu danni ba jakace ba , gidajen abinci nawa a garin nan ? Dan dai kawai kar ya fita ya isa. A shi a dole sai yazo gida yaci shi mai mata....!

Hadiza tace ya akayi ne ? Shi mana , shi waye ? Abdul mana , meya faru ? A dai² lokacin daya fito dan fita ita kuma tana cewa wai in dafa mishi abinci. Ko tausayi na ba'ayi a gidan nan , tun safe nake hidima da mutane a ya kamata na riƙa hutawa. Cike da ladabin ɗan ƙunama Hadiza tace haba dan ɗan wannan ? Ai komu kika ce a cikin mu wani yayi zamuyi , ba komai ki huta bara a dafa maka tayi maganar tana miƙewa , Halimatu tace ai da kin barshi tunda fita zaiyi ai yace zai siya a waje. Hadiza tace ah yi haƙuri Oga a girka babu jimawa , tayi maganar tana shiga kicin... Salam² ya koma bedroom.

Ita kuma Halimatu ta zauna a palo cikin ƙawayenta akaci gaba da maida yadda akai ana shewa.... {{ Kina aikin me "yar uwata...? Ƙawar banza ƙawar wofi...? Wace ce ita ? Me kike nema a wurinta da har zaki fi²ta ta akan miji ? Wacce yau tana iya canja ki , shifa miji ? Ko kun rabu idan da zuri'a an zama "yan uwa. Hmmm ki kiyayi kanki da duniya kinji ko....??? Murmushi , kuma bawai nace kici ƙaniyar ƙawarki ba , a , a adai riƙa abun da lissafi... Karki canja ma ƙawarki fuska tace ƙawata lafiya ? Kice Jamila Musa tace a sakeku a riƙe miji , ba haka nake nufi ba , kudai fahimci inda na dosa. }} cikin ƙan²nin lokaci ta gama dafo abincin ta kawo mata , da farko tace Hadizar ta miƙa mishi , Zainab tace a , a ki kai mishi mana... Wai ita a dole nan tayi fushi wai wallahi bara takai mishi ba tunda jiya yace ana cinye abinci da wuri , {{ ba dole yayi miki faɗa ba ? Kin san wahalar daya sha ya samo ? Wace ce ke da baraya yi miki magana ba ? Ke kaɗai ya ɗauki alƙawari zai ciyar , yasharwa , tufatarwa , ilimantar magani idan baki lafiya wurin zama da kuma kyautatawa a gaban magabatanki haka ya ɗauko alƙawari , baice dake da ƙawayenki ba , ke kaɗai ya biya sadaki aka bashi kuma yayi alƙawari ya ɗauko ki. Duk abinda yayi ko ya bari kikayi da dukiyarshi ko abincinshi da komai nashi tou wannan shine kyautatarwa. Idan kuma bai fita haƙƙin naki ba zai haɗu da sakayya. Akan me zaisa ya samo abunshi ki wulaƙanta mishi ne ? Ko kece kike nemo mishi kuɗin ? Ba kuma nace ki riƙa yiwa mutane rowa ba , idan kinji maƙota ki noƙe risho. Ba rowa zakiyi ba , abinda ka bada shine naka. Kar kuma kina cin abinci idan wasu suna zuwa ki ɓoye kiƙi basu. Ko ki daina fita haƙƙin masu haƙƙin ku basu ba , kar abun duniya ya rufe miki ido. Ki bada , wanda kika bashi zaiji daɗi. Kuma zaiyi godiya da addu'a wa mijinki Allah ya ƙara buɗi da rufin asiri. Bana nufin kiyi rowa wa mutane a , a , ba haka ba , ina nufi dai abun komai kiyi shi dakai... Bawai duka "yan anguwar ku zaki ciyar ba , sai ki duba dai² ƙarfin mijin naki , wani yana da ikon ciyar da jaha ɗaya ma , amma mugun marowaci ne , tou karki almubazzarar masa amma a hankali ki riƙa nuna masa matsayin kyauta da kuma kyautata ma wanda baya da ƙarfi sai kiga a hankali yau da gobe ya rage , wani kuma yana san ya ciyar amma baida ƙarfi , kawai dai duk abinda za'ayi a riƙa sa nazari tunani da kuma lissafi... }} shine take fushi dan yace abinci yana saurin ƙarewa. Shin tasan dalilinshi nayi magana ne ? Ga nauhi yayi mishi yawa , gidansu shine yake riƙe dashi , ga Allah suka dogara shine sukayi ma zuru , itama gidansu Halimar ana aika musu da kasafi duk watan duniya , tou ke zaki nuna masa yadda zai kyautata a rayuwa ? Wace ce ke ? Daga "yar karo baki kau ba fa..... Sai wani kumburin banza take tana cika fuska tunda taga gareta ya miƙa wuyanshi. Mai abun hana miji idan ya buƙata , waye yace miki hana miji haƙƙi shine zai siya miki mutunci ? Tou idan dai wannan shine mafita a gareki zero.......

Dakel Zainab tasa Halimatu takai ma mijinta abinci , tana zuwa ta dungura mishi tayo waje. Shi kuma yaso taɗan zauna yana ci ana ɗan tattaunawa irin nasu na ma'aurata , amma ita ba ruwanta tunda dai ta samu ya ɗaure mata ƙugu zataci tasha tayi gulma tou an biyata , sai idan an kawo kayan mata ta loda ta riƙa mishi ƙarya yana bata kuɗi , ita kuma taita loda ma cikinta kamar akuyar mahaukaciya.....

Yau babu abinda na girka dan tunda na kwanta bacci sai bayan la'asar na farka , bai kuma wani tasheni ba saida na gaji na tashi dan kaina. Babu inda ya fita yaje saboda bayajin daɗi kuma ma ai dama shi ba ma'abocin fitar rana ba ne. Ganin na kasa tashi ne yasa aka kawo mishi abinci daga gidansu , na nashin dandai ina da cikin amman da ko ba abinda zanyi mishi saiya tasheni dan dai ya ɓatamin rai. Ba abinda naci tun kalacin safe sai bayan sallah isha'e na jiƙa garin rogo { garin kwaki } kuma Dikkon nasa da kanshi a siyomin , dan bana ra'ayin abincin da aka kawo. Shine yasa aka kawo buhu ɗaya. Bayan yayi faɗa wai salan inje inba babynshi wahala zanci wani gari bana daijin magana , nace baby ne zaici garin ai bani ba , wai babu wani ya faɗa yana hararata nace da gaske shine yasa aka kawo.

Bedroom na sameshi zaune saman gado da irin zaman ɗazu yana kallon ƙwallo. Kusa dashi na zauna , ina zama ya gyara min zamana tare da matsowa ya kwanta ya ɗora kanshi a jikina ya riƙe ƙuguna da duka hannayenshi yana kallona , nima kallonshi nayi tare da cewa tashi muci , ɗauke idonshi yayi daga kallona yana kallon tv yace me ye ? Gari , murmushi yayi me sauti yana cewa Allah ya sawaƙe , garin ne Allah ya sawaƙe ? Ah ni bana iya cin garin gaskiya sai kace inyamuri....? Aini inyamurar ce shi yasa zanci , shiru yayi bai sake magana ba , ya ɗauki wayarshi yana duba dokuna.... Shikenan tunda bara kaci ba bari in tafi nayi maganar ina ƙoƙarin tashi , riƙeni yayi sosai yaci gaba da abinda yakeyi a waya....

Ni tafiya zanyi , ba tare daya kalleni ba yace kinyi fushi ? Ey , tou ina ci kawo min cokali , ai bada cokali akeci ba , da me akeci ne ? Da hannu , tou bani ya ƙarasa maganar yana buɗe bakinshi ba tare daya kalleni ba... Ai haka kayimin haggunce , ya zanyi ? Ka tashi.... Tashi yayi zaune amma har yanzu hankalinshi yana kan wayarshi saidai bakinshi a buɗe yake , bashi nayi , riƙeshi yayi a bakinshi tare da ɓata fuska ya taɓe baki yana juyashi , ƙara ibowa nayi. Da garin a bakinshi yayi magana cewa dan Allah An mata ki kyaleni kinga banda lafiya..... Dan Allah kaci , kallona yayi a sakace yace baya tafiya , jeka dashi kawai ka kora da ruwa..... Idan banci ba zakiyi kuka ? Dariya nayi dan yadda yayi maganar kamar ƙaramin yaro wallahi. Shagwaɓa tana mishi bala'en kyau kuma yana burgewa idan yayi , hada hawaye. Na faɗa ina kallonshi da irin kallon da yakemin. Ɗan kauda kanshi yayi gefe tare da shafa kanshi yaci dakel , yace ngode. Hahahaha bawan Allah , yau da Jiddah tana nan da nace mata Dikkon ma da kowa da kowa yake taƙa dashi ni nasa ma yaci garin kwaki dan ubanta....

Aimu dama mun saba , kuma ni ban manta ba har yanzu nasan martabar gari , duk irin matsayin da nake a yanzu baisa na manta da rayuwar baya ba. Ai gari yayi mana kuma mu bama wulaƙanta shi duk matsayin da mukaje muna tare da gari gaskiya , kuma ina ƙara godiya da Allah yasa nake a wannan matsayin , haka nan naji ina sha'awar garin. Na ɗan
DOWNLOAD
DOWNLOAD

2 Comments On KWARATA RETURN
avatar
fatima-kasim

4 months ago

Reply

Naji dadi sosai sosai Allah y kara basira

avatar
daiy

4 months ago

Reply

Replying to fatima-kasim

Ameen muma munji dadin kasancewarki anan.

Please Login or Register in order to submit comment