Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

a ɗaki dama tusa hali bare anci wake. Fushin mutum ɗaya ke sa idan yana fushi yake haɗawa kowa da kowa , wanda yasan anayi da wanda baiji bai gani ba , ai kuma kunsan laifin wani yake hucewa akan kowa. Yau duk wata macen dake cikin wayarshi Sharifa taja musu anyi blocking insu , anyi adding nasu zuwa blacklist. Wato shi harkarshi ba baƙin ciki bajin haushi sabgar Katsinawa.

Dikko shine ya shiga yai ruwa yai tsaki aka ɗaura auren Jiddah da Yazeed. Rabiya ta labarta mishi komai tsakaninta da Yazeed iyakar abinda ta gani , hankalin Dikko kuwa ya ɗagu domin shi yasan waye Yazeed. Sadaki da lefe har kayan ɗaki shine yayi dan Yazeed yace bashi da kuɗi , Jiddah ta faɗawa Dikko ita ta bada kuɗin aure. Shine Yazeed yace ɓarayi suka sace kuɗin. Andai ɗaura aure amarya ta tare a gidan angonta...... Ita kuma tana lissafin kwanakin fitowarta da ko nawa ga wata zata koma gidan Dikko.

Hafsa. Duk maganin da akayi ma Hafsa a asibiti hannu yaƙi ɗauka bare asa ran samun sauƙi har zuwa matakin warkewa. Bayan dogon bincike likita ya tabbatar Hafsa tana da ciwon shiga. Cire hannun shine maslaha inji malamin asibiti dan idan ba'a cire shi ba matsalar zatafi haka injisu. An cire mata hannu dai² gaɓa.

Amisty kuwa kafin ta gama warwarewa Momyn Hafsa tasa aka cafketa. Bayan tasha shegen duka aka tambayeta kuɗi tace babu , a yadda su "yan sanda suka fahimta Amisty tana da damuwa a ƙwaƙwalwarta. Haka suka gogawa Momy bayani dole tasa suka saketa dan Amisty ta samu ɗimuwar tunani. Amma duk wannan bai ishi Momy ishara ba saida ta siyar da gidan iyayenta da gidan Amisty na Qerau. Amisty dai ga hauka ga kuma yawon haya.... Bariki kuma ta kama gabanta , sheɗan ya fita a kanta ya sake sheƙa. Duniyar yanzu ba Amisty take buƙata ba zamanin wasu ne. Haka takeyin juyin ɗan mangwaro ita duniya dawowa take daga rakiyarka da zaran ta raka ka sai ta dawo ta sake raka wani halakakken wanda sheɗan yayi ma tusa a zuciya.

Halima dai ba kowa bace wannan amarya sai ƙanwar Hadiza. Wata garɗamemiyar budurwa ce takai shekaru 27. An tura anyi ciniki amma bata samu shigewa ba , anyi addu'a an bada sadakar ƙuli da alawa amma abu ya gagara dan haka ta shiga ta fita har gidan uwayen mijin Halima ta basu labari irin uƙubar da take ba ɗansu. Nan fa dangin miji suka fara cacai² , akai ta faɗo baƙin halinta , raina dangin miji uwar miji raina miji da baƙar rowarta. Itama dai Hadiza ta kawo nata sharrin ta raɓa da "yar ta² barikin dai ta samu aka siyi kanwarta. Shima Abdul haka aka ɗaurashi kunsan maza basa wuce tayin mace kamar almajiri ne da sauran abinci... Cikin ikon Allah yaga yarinya kuma tayi mishi. Gata "yar kyakkyawa kamar Rabi'atu Aminu Maman Dee. Mai kunya da laushin magana kamar Asmeenat Zeeyan. Mai kyawun kallo da iya murmushi kamar Aunty Musa Qerau. Ga iya wanka mai ɗaukar hankali kamar Hauwa Musa Qerau. Ta iya adon lalle mai burge kamar Zainab Abbakar Matawalle haka ta iya gyaran kai kamar Fati M Ga magana da salon ɗaukar hankali bakinta kamar Ruƙayya Sharif Maulaya hassan. Kai tafa haɗu haɗuwar haɗewa , idan zatayi kallo tanayinshi ne da salon bugun zuciya kamar Rabi Musa Qerau. Bari dai in daina zugata haka nan karta kamo Halimatu Musa {{ Uwa }} haɗuwa.

Abdul da yaga yarinya tayi mishi sosai dan haka suka antaya a duniyar munafukar soyayya. Ita kuma Hadiza kullum tana liƙe da gidan Halima tana ƙara kakkaɓowa "yar uwarta sirrin gida. Har daren ɗaurin aure duk suna tare da Halima sunajin hukuncin da zatayi wa amarya. Da taji saita dokawa "yar uwarta waya suyi shawara su san hanyar da zasu hudowa lamarin. Ina wanda ya raba faɗa bai kallo ba , sun haɗu sun haɗa ƙarfi da hikima duka ɗaya zasuyi su zare Halima a gidan miji idan tayi wasa saboda sunyi mata ƙofar raggo , ita bata sansu ba , su kuma suna tare da ita suna shirya mata gadar zare.

A kusa da gidan Halima Abdul ya kama haya ya ajiye amaryarshi Amina. Tunda bai shirya aure ba hawoshi yayi kai tsaye. Anan fa akayi uwar watsi , Halima ta fara bori da wallahi² data tabbatar amarya ƙanwar aminyartar ce. Nanfa fitina ya ɓalle suka kashe santa aikata ruwan bala'e babu ƙaƙƙautawa , Hadiza ta biya kuɗi ta ibo hayar "yan daba tace duk matar data sake cewa tuf ko ta leƙo daga gidanta idan dai ba Allah sa alkairi ta fito ba aradu su yagewa koma waye baki. Dan su sunaso suyi hidimar biki cikin natsuwa , a gefe kuma ga masu DJ sunata wulakanci da waƙoƙi na habaici umarni daga Hadiza , c b n gidan kuɗi. Can naga sabbin kuɗi suna wali bisa iska. Shagali wanda ko a bikin Halima basuyi irinshi ba. Hadiza kuwa a yanzu zasuci na ƙurya da bakin gado. Ballagazar mace ga ƙarsheki.

Tunda Mardiyya ta haura katangar maƙabarta ta ibi santa. Mota tahau ? Da ƙafa taje ? Oho , candai Yola ta yadda zango , hauka tuburan marar gane matsayin ido da ciki. A gidan mahaukata aka ajeta shine suka shiga neman "yan uwanta , bayan an samosu aka danƙata wa iyayenta , sai suyi ta magani har a dace , wa gari ya waya ? Ruwa ya ƙarewa ɗan kada bai gama wanka ba.

Amarya Jiddah kuwa an wani saki baki aci kazar amarci. Ai a ranar ango bai kwana gida ba. Tou dama me zai tsaya yi ne ? Abinda za'a tsaya danshi ayi murna da ɗoki ai ansanshi tun a gida. Saboda shi dama za'aci kazar tou yabi ya wuce , anyi karatu an tusa feji , allonta kawai take wankewa gwargwadon yadda ta biya karatun. Sati ɗaya da "yan kwanaki ta fara zance tafiya , Yazeedu yace ina ? Ai yadda baya tare da D ' K a yanzu gara ma yayi ƙoƙarin riƙe auren "yar uwarshi yasan ya mishi sauƙin gani. Haya² ta taso da rashin kunya ya nannagawa banza duka na fitar misali. Wannan shine horonta duk idan ta sake zance saki....

Duk wannan sa'a da Sharifa ta gwada na shawarar da mai gilashi ta bada taga ta faɗi ? Bata daddara ba. Dan haka ta faɗawa Mai gilashi Dikko ya rufeta a waya. Mai gilashi tace mafita na ƙarshe kizo makarantarmu ajinmu ɗaya da matarshi kashin bala'e zaki bata , daga nan idan kika daki matar zai nemeki danjin dalili , sai ki faɗamin ni kuma zan baki shawara na ƙarshe. Idan kika daketa zataje ta faɗawa mijinta , tana faɗa mishi shi kuma zai nemeki danjin ba'asi. Yana kiranki ke kuma ba ɗauka zakiyi ba sai ki kira ita Aunty Bilki ki farfaɗa mata maganar da zan faɗa miki idan kinyi dukan. Daga nan zatace kizo gidan gwamnati. Idan kikaje government house sai ki kira Dikko ki faɗa masa cewa kinga kiranshi bakya kusa ne sai yanzu. Zai ce me matata tayi miki kika daketa ne ? Sai kice ai ina nan gidanku ma. Fuuuu zai tako mota yazo , ai kinsan dai dama bawai wani can² yake santa ba suma nashi familyn basa santa. Ai nanfa za'a haɗu a bata rashin gaskiya duk idan kinyi dukan zan faɗa miki abinda zaki ce ya haɗaki da ita Sultanar.

Sharifa tace amma kina ganin wannan ba matsala ? Mai gilashi tace haba Sharifa idan da matsala harna faɗa miki kiyi ? Matsalata ai taki ce. Dole mu haɗu muyi maganin matsala kodan ci gabanmu. Sharifa tace idan aka faɗi fa ? Mai gilashi tace shikenan sai ki sake ƙawar shawara. Sharifa tace tou shikenan. Batayi tunanin matsalar da hakan zai haifar ba......

Hmmm su kuma zugar gidanmu duk abun nan wai sai yau suka zomin gaisuwa. Ƙwansu da ƙwarƙwata babba da yaro babu wanda aka rago har iyaye , jimillarsu dai su sattin da wani abu. Kacaniya kenan , gaskiya nayi farin cikin ganinsu sosai har farin ciki na yaƙi ɓoyuwa. Haka suka shigo wurjanjan kamar an ɓalle garken shanu. Kowa da irin siffarshi. Kai gaskiya Baba ɗan bala'e ne , wannan kwanyaman "ya "ya inama amfaninsu ba ɗaya na zaɓe. Haka suka shigo palo sukaita hayaniya , har bakajin maganar wani. Abinci nasa aka kawo musu. Ɗiff kowa ya ɗauke wuta suka fara caccaka. Gayam². Gurum² taunar nama. Abinci kuma nakai karo suka ci gaba da surutu......

Da hada "yan gidan Baba ƙarami zamu zo sukace basu zuwa. Cacai² gardama ta buɗe , bafa haka sukace ba ku faɗi gaskiya ni nafi san abinda mutum ya faɗa ana faɗinshi. Daga maida magana sai faɗa , har ana neman bugawa. Haƙuri na basu dakel dai suka haƙura , duk lemunan da aka kawo musu kowa cikin jakarta tasa abunta wacce bata da jaka ta matse abunta a hannu. Tashi sukayi wai zasuje su zagaya gida dan kar suje wata rana anayin labari su kasa ƙarda komai. Kamar wata geliya haka nabisu babu inda basu shiga ba a gidan sai ɗakin mai gidan ne kaɗai basu shiga ba. A store kuwa buhun garin kwakin nan suka jawo , kalluba suka cire ba tare da izinina ba suka hau rabo , wai wannan ai kiran tsiya ne wai meya kawo fir'auna aljanna ga gidan wuta. Haka dai sukai ta zambaɗa iskanci suna maganganun irin nasu na "yan cikin lungu. Duk abinda suka gani yayi musu a store sukayi gaba dashi. A ɗakina kuwa cewa sukayi in basu zazzagar kayan sawa. Fa'iza kuwa cewa tayi saidai wasu a basu kaya wasu takalmi wasu jikkuna , kuma wai waye ma nake bawa kwance gasu ? Duk zasu sakamin numbobinsu idan zamu koma sabon gida a basu kayan tsohon gida , weldrop na buɗe na fiddo musu kaya sukai ta zaɓe. Ciki kuwa hada rigunan da Dikko ya kawomin tsaraba suka ɗauka. Nan dai suka yini sai dare suka tafi nayi musu hasafin kuɗi masu nauhi suka kama gabansu....

Kwanan "yan gidan biyu da zuwa Dikko yana kallon hutana na a waya ya karkatomin waya wai insa mishi wannan rigar yau. So ɗaya na kalleta nace na bada ta. Sake zuƙo hoton yayi yace wannan kalli. Ba tare dana kalleshi ba nace wannan ɗin. Haba yarinya wasa kikeyi , wallahi da gaske na bayar da ita , cike da ɓacin rai yace waye yace kika bayarmin kayata...........?

Kar kuji Dikko yana da kuɗi kuce ya tsaya akan wani banzar riga yana surutunshi. Duk iya kuɗin namiji ke mace yafa kamata da Allah ki riƙa abu da lissafi. Tunatarwa ne. Duk irin kuɗin mijinki baifa kamata haka ba gaskiya , ta yuwu kila a jikin wata ya gani tayi mishi kyau ya siyo shima kiyi mishi gayu. Bawai nace ba'ayin kyauta ko karki bayar a , a abunda dai ina nufi a ɗan riƙayinshi haka dai da lissafi.

Domin shidai Dikko a saudiya yaga riga jikin wata "yar budurwar balarabiya. Shine ya hasko idan tashi matar ta shiga a irin rigar itama zata bada irin abinda waccan ta bayar , ina fatan dai kun ɗan fahimceni. Shine ya shiga shima ya samota kalarta da komai da komai dan ayi mishi ado a gidanshi shima. A ita ga matar mai kuɗin banza idan na bayar gobe ya siyo wani. Ita ya siyo domin ke..., bashi da tabbas idan ya koma siye ya samo irinta , ta yuwu a canja kala ko kuma a samu banbancin company. Shin ba'a shiga haƙƙi ba....? Saboda haka idan dai namiji ya siyo abu ya kawo miki lallai yana da dalilinshi......

Ai na baka ya rabaka da abunka. Ni kike faɗama wannan maganar dan kin ɗaukeni abokin wasar ki ? Yayi maganar cikin fushi yana tashi zaune. Ni zan siyo miki abu ki bayar dashi ? Nayi miki magana zaki faɗamin na baki ya rabani da abuna....? Yayi maganar yana saukowa daga saman gado , miƙewa nayi da sauri. Cikin firgitacciyar murya yace idan kika fita sai nai miki shigar bulet.........

















08/02/2020









*JAMILA MUSA...*
[2/14, 12:12] ~M K: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_



*KWARATA RETURN...*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_


Rubutawa...
*JAMILA MUSA...*



*SAI NA AURI D ' K*



🅿 ------ 10


Shafin nan daga farkon shi har can² karshenshi. Sadaukarwa ne gareku "ya "ya masu albarka.
*ABDULRAHMAN B ' K LAWAL*
&
*JA'AFAR B ' K LAWAL*

Ina roƙar Allah subahanahu wata'ala da ya albarkaci rayuwarku. Ya jiɓanci lamurranku ya jiƙanku ya ɗaukaku darajarku yasa ku gama da duniya lafiya. Ina roƙon ubangiji da yasa kuyi kyakkyawan ƙarshe. Allah ya dafa muku ya kareku da kariyarSa , ya tsareku da tsaronSa a duk inda kuka shiga yasa albarka a rayuwarku ya ƙulle idanuwa da zuciyoyin duk wani gurɓatacce daga gareku. Allah yasa ku dace a gidan duniya da ƙiyama. Allah yai muku albarka don darajar fiyayyen halitta Sallallahu Alaihi Wa'alihi Wasallam. Ameen ya Allah. Duk mai san manzan Allah S. A. W yace amin..... Duk wanda yace amin , ya Allah kasa ya gama da iyayenshi lafiya. Idan kuma sun rigamu gidan gaskiya Allah ka jiƙansu ka sadasu da rahmar ka , kasa can ya fiye musu nan har Babana.... Allah kasa sun huta. Mu kuma ka kyautata namu ƙarshen idan ajalinmu yazo Amin.



Idanuwa na cike da hawaye nace ai dama ba fita zanyi ba haƙuri zan baka. Na ƙarasa maganar ina ƙoƙarin durƙusawa ƙasa. Tausasa murya nayi cike da ladabi na furta kayi haƙuri insha Allah bazan sake ba. Komawa yayi ya zauna danshi yana da karyayyar zuciya , ko yana furta sai na kasheki.......... Saina kashe² idan dai zanyi kuka ko yaga na ɓata rai zaice An mata bakijin magana kaza². Da lallausar murya ya furta gaskiya banji daɗi ba. Kuma karki sakemin irin haka daga yau...? Nace tom. Duk abinda ni nawa ne ? Idan dai har nine na siyoshi da hannuna koma miye ko mene ne ko wane iri ne karki kurkusa ki yanke hukunci ba izinina na faɗa miki. Na sake cewa tom. Ni kwanaki da zan aske ya nuna gemunshi ba kuka kikayi ba ? Shiru nayi ina kallon ƙasa kamar mijin da matanshi suka ritsa a ɗakin "yar aiki.

Ke me yasa kikayi kuka ? Cewa kikayi in rufa miki asiri ko ni ina so idan kika ga masu gemu kiyi ta kallonsu ne ? Cikin ɗaga murya yace tou da irin wannan dalilin da zaisa ki kalli wani mai gemun a waje , tou nima irin wannan dalilin ne yasa na siyo rigar nan. Ko an faɗa miki niba mutum bane ba ? Ance miki ni nawa idon bai iya kallon mata ba ? Ko an faɗa miki ni banajin irin yadda kike ji ? Ko an faɗa miki niɗin dutse ne ni da banajin yanayi a jikina iye ? Ya faɗa yana nuna kanshi da ɗan yatsa. Tou irin abinda kikeji idan kika kalleni da yanayin da kikaji idan kika shafa fuskata ko kika zo kika rumgumeni , duk irin yanayin da kikeji idan kina shashshafa ko ina a jikina ni nafiki na wuce na zarce ki jin irin wannan yanayin. Ko sai ke kaɗai kike so a burge ki ? Wannan ai rashin adalci ne, zalinci ne. Ji nakeyi kamar ince miki ban yafe ba. Fashewa nayi da kuka nace Allah ya isa zakayi min ne ? Cikin ɗaga murya yace dan in nuna miki girma da ciwon da naji wallahi akan bayar da rigar nan da kikayi ? Yau da kin sameni akan tsini duk wanda ya tsaya miki da sai nasa kin anso rigunan nan.... Cikin shashshekar kuka nace dan ci baya ? Kece kika ci baya mai shiga haƙƙi miji. Har wasu banzaye sunfi mijinki mutunci , "yan gidan namu ne banzaye ? Suɗin , duk wacce kika gani a cikinsu idan ta dafe kan mijinta shiru zakiji. Irinki ne masu duhun tunani mutane ke rabawa da miji. Kila ma kin basu labarin ni na siyo sai su ɗauka , ke baki iya sakawa su bara su riƙa sakowa suna burgeshi , kina can kwance kina yarinta za'a buga wasan a barki da hauka. Idan ma kika ɓatamin rai na hasala da yawa duk shegiyar dana sake gani a gidan nan saina bata kashin bala'e. Me yasa nake baki kuɗi ? Dan kiyi rayuwarki karki shigamin rayuwa kije kiyi huɗɗarki da mutanenki ko na hanaki ? Ko nace karkiyi ? Ban takura miki ba ban shiga rayuwarki ba An mata , na barki kiyi sabgar gabanki dan kema ki zama mai "yan ci kamar yadda ko wane ɗa yake da "yanci , amma kin ɗaukeni kamar wani lusari ko an faɗa miki tsoro yasa na barki kike abunda kika ga dama ne ? Bana san na matsa miki ne ke kanki idan na takura miki rayuwar gidan nan bata miki daɗi. Nawa ne ba naki ba.

Ko kayanki ne ba nawa ba iye ? Ke kika siyo su ne ? Nine na gani ya burge na siyo domin ki , ki saka nima inji shauƙi inje irin yanayin da kike shiga idan kika kwanta jikina , ke wai bakya gane komai ? Komai sai an fito ɓaro² an fallasa miki saboda kina da jakin kwalwa. Da kinga na fara sauke²n kaya baki da zama lafiya. Kar in bada miki wannan , kina so kiga na saka wannan , ke wannan yana miki kyau. Ko nace bana sanshi sakani gaba kike kitaimin kuka ke mai idon fitar da hawaye. Shin yanzu ke ba da kanki kike fidda kayan dake baki ra'ayinsu nawa ki bada su ? Duk yadda nake san abu idan kika ce baki sanshi dole haƙuri nakeyi dashi. Duk yadda bana san abu idan kika cemin kina so haƙuri nakeyi. Sanyaya murya yayi yace duk dai dan in burgeki. Amma da yake baki da adalci babu abinda ya dameki inyi farin ciki ko kishirya haka. Ki burgeni ko karki burge kedai kanki kika sani burinki in miki kiji daɗi. Wannan shine rayuwar farin ciki.....? Ya ƙarasa faɗa yana kaiwa katifa duka , baki da adalci sam² kullum baki da burin burgeni saidai neman hanyar musgunamin. Tou daga yau tunda iskanci ne abun naki na rantse da girman Allah kika sake ɓatamin rai saina lalata miki fata.... Tom. Zazzaro ido yayi yace karki cemin tom akan komai kice bazaki ƙara ba.......... Ya faɗa yana rufe idanuwanshi. Da sauri nace bazan ƙara ba insha Allah. Hanya ya nunamin in fitar mishi daga ɗaki. Da sauri na fice na barshi yana ta mita.....

Tsaye take a kitchen tasha ado kamar zataje gasar wanka sai fitar da wani irin sirrintaccen ƙamshi takeyi. A gabanta kuwa kiret in kwai ne take ta dandaƙa ba sassauci. A gefenta kuma "yar matsadiyar wayarta iphone ce keta rero waƙoƙin turanci ita kuma tana rakiyarsu da bakinta. Wata irin zundumemiyar ashariya Yazeed ya ciko bakinshi da ita ya zundumawa Jiddah dake ta farfasa kwayaye....... Wandon jikinshi kuwa sai riƙonshi yake a hannu yana ƙoƙarin ɗaure belt dan wandon ya tsaya. Kuturmar dumadu.....? Kwan zaki cinye dan uwarki...... ? Waye yace miki anacin ganyen filawar da aka jera dan ƙawata ƙawar gida ? Cike da masifa Jiddah tace kai kaima dan uwarka ! Ko an faɗa maka shiru² tsoro ne wai iye ? Idan baka so inci kwai kawai ka bani sakina inyi gaba ai muma a gidan namu anacin kwan. Cike da ɓacin rai Yazeed yace kin taɓa ganin majiyyaci a maƙabarta ? Ai asibiti shine majiyyaci yake zuwa dan ganin likita , shine zai dubashi ya gano ciwonshi ya bashi magani sai ya samu waraka da izinin Allah. Maƙabarta kuwa gidane na matacci , wannan gida da kika ganshi nahir jinyace daga gareni idan kuwa har kika fita a gidan nan gawarki ce aka fidda. Ni bana aure dan saki saidai inci uwar fatar mace tai iskanci. Aurena yana nan ram² baya girgiza no saki an no barkono yaja yaji da bakinshi. Ni nan da kika ganni matakin iskanci na taka bansan iyakar nahiyoyin rashin kunyar dana ƙyetara ba. Ɗan iska ne ni na nunawa a satilayit banda mutunci ga muni banda kyau ko nai wanka..... Da ke a tunaninki na aureki domin kisan wuta ? Nine ma zaki kashe wuta dani ? Tou yanzu na kunnu nayi ta ci gaba da ci daga nan har a tsaida ƙiyama. Bana sanyi bana siƙewa bare kuma kiyi tunanin zan mutu.

Ai wannan auren ko auren da aka daura a coci bai kaishi ƙarko da aminci ba. Yaci uwar auren coci ya zarta na kotu kuma. Yadda bakya tunani auren ya wuce inda kwalwarki bata iya hasasowa saboda ya linka auren zobe dan auren Yazeedu auren kabari ne. Kuma haka gidana yake idan an shigo ba'a tafiya saidai idan za'a tafi kabari , nunawa yayi da hannunsa yana ci gaba da cewa wannan nasan zahiri ne tafiya ɗaya ba dawowa. A bakin tarihin rayuwarki waye kikaji ya shiga cikin ramin kabari ya fito ? Tou ba'a fita sai ranar da ƙiyama ta tsaya , wato ranar yauma tubalasra'il. Ranar girbe abinda ka shuka , ranar da uwa bata gane ɗanta miji idan yaga matarshi zaisha kwana. Tou gidan nan maƙabartarki ne a nan kabarinki yake idan kinga kin fita a gidan nan mutuwa kikayi dan ƙaniyar iskanci. Ya ƙarasa maganar yana shaƙe wuyan Jiddah tare da cewa biyamin kwai na....

Yana shaƙe da ita yaci gaba da cewa shin bana faɗa miki abincin gidana adon idon duniya ne ba ? Dakel tace e , Yazeed yace amma kika ce kinji kin yadda ko ba haka nayi dake ba ? Cikin jin zafi shaƙa tace haka ne. Riƙe wuyanta yayi da hannu ɗaya yace duk kwai ɗaya dubu ɗaya na siyo abuna. Kuɗin mota da kuɗin kunna gas a gidana ba ranar sanwa ba. Bakina dana ɓata wurin ciniki , kin yanka albasa ba'a kan ƙa'idar ma'ikata ba. Zagin miji wanda babu shi a kundun tarihin musulci zunubi ne mai girma , domin wanke kai daga wutar Allah neman gafara da biyan kuɗin diyya dubu ɗari. Cin zarafin miji kin daƙile min guyuwa akan ƙalubantar ciyarwa kince gidanku akwai abinci. Domin samun sassauci kwanciyar kabari cikin salama zaki biya dubu hamsin domin wanke kai daga bugun mala'eku. Naira budu tamanin na neman yafiya ne domin kiyi kwanciyar kabari cikin salama. Da hannun da bai riƙe wuyanta ba ya fara lissafun kuɗin a wayarshi.

Yana lissafa kuɗin yake cewa yau kuma anyi buking ina a wasan danbe ki biya kuɗinki da wuri ki yanki tikiti tun kafin ƙarfina ya ƙare. Ki bada budu goma tunda ke ta gida ce , zan siyar miki dashi ne akan farashi mai sauƙi amma ba haka ake siyarwa ba dan kada jibi ince miki dubu talatin ki fara wallahi² , cikin wahalalliyar murya tace bana so. Basai kinyi muradi ba
DOWNLOAD
DOWNLOAD

2 Comments On KWARATA RETURN
avatar
fatima-kasim

4 months ago

Reply

Naji dadi sosai sosai Allah y kara basira

avatar
daiy

4 months ago

Reply

Replying to fatima-kasim

Ameen muma munji dadin kasancewarki anan.

Please Login or Register in order to submit comment