Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

Gyara bakina nayi ina kallon ƙasa , bai sake kallona ba yace zo muje. Da sauri na wuceshi na tafi ɗakina , hijabi kaɗai na ɗauka ko wayana ban tafi da , nayi waje. Pa-Pi shima biyoni yayi yana kuka jaije.... Kafe kai yayi shi bazaije da Pa-Pi ba , shi kuma Pa-Pi riƙeni yayi idan ba'a zuwa dashi nima babu inda zanje. Dikko yace ka sakarmin mata kaji ? Yayi maganar yana zaro mishi ido. Da ita zanje kaine bazan tafi dakai ba. Riƙeni yayi Momy karci tafi ci barni. Dikko yace kai so nawa ka tafi ka barta ɗan rainin hankali sakarta nace maka. Kamar an matsi bakinshi yace kaicuwa jakuje....? Ya faɗa da yanayin tsoro ! Yaci gaba da cewa kuma fa'a cuwa da Pa-Pi ya ƙarasa maganar yana ma Dikko wani irin kallo haɗe da murmushi. Kete Momy ce cinyi kuka , jinjina kanshi yayi sannan yace cima Yaya ce yayi kuka ya ƙarasa yana dariya. Nuna kanshi yayi sannan na nunamu yace ni kuma can muku dayiya wayyayi.

Yadda yayi abun ne yaba Dikko dariya , yace ni kuma wallahi in zaneka. Dariya Pa-Pi yayi cewa kowa ce yayi kuka wayyayi. Yana ƙara yawan dariyar wai zaiga Yaya yanayin kuka. Wata irin mummunar faɗuwar gaba naji lokaci guda wata irin zufa ta ketomin , murya a sanyaye nace ma Dikko nidai na fasa zuwa. Dariya Pa-Pi yayi tare da cewa wayyayi Momy taji tsoyo. Dikko yace keda Allah manta dashi taho muje yayi maganar yana jan hannu na , kinga sai kirana takeyi zo muje kinji....? Ƙwacewa nayi nidai kawai kai kaje , cikin rarrashi yace ke An mata haukan Pa-Pi zai tsorataki ? Da Allah zo muje yana ci gaba da jana. Fizgewa nayi nidai na fasa , cikin ɗaga murya yace kada Allah yasa kije kuma tunda har kika ce zaki kika fasa , idan na fita sai 2n dare zan dawo.

Jiki a sanyaye na kalleshi. Ɗagamin gira yayi tare da kwantar da idonshi na haggu , a hankali ya fidda sautin sumba cikin natsuwa da salo mai tada hankali yana ƙara riƙe ganin idanuwanshi , duk iya masifar sa idonka bara ka gane abinda yayi ba , wannan karatun daga ni saishi kaɗai muka fahimci yaren juna. Ajiyar zuciya nayi kaɗan cikin ƙarfin hali , shi kuma ya ɗagamin hannu ya wuce. Tunda na fasa zuwa ya tafi da Ashiru....

Dariya Pa-Pi yaci gaba dayi yana riƙe da hannuna har muka shiga ciki. Saida muka zauna na tambayeshi wai waye yace mishi zamuyi kuka ? Zama yayi kusa dani yace wai a cikin wayar Yaya ya gani , cike da ɓacin rai nace dan ubanka a wayar aka ce zamuyi kuka ? Kallona yayi ya ɗaure fuska shima da yanayin fushi yana hararata wai saiya faɗawa Yaya nayi zagi ya zaneni , shima ai jiya Yaya ya dakeshi da yayi zagi wa kare.... Tsoki nayi sannan nace ya tashi ya bani wuri. Ƙin sauka yayi saidai ya juyamin baya wai yama fata dani. Kaje ka ɓatan. Ba'a ciyyawa dake.... A palo na barshi na koma ciki , kasancewar zufar da naji inayi dole tasa naje nayi wanka. Ina fitowa kuma masassara tace gata nan zuwa , dakel na iya shafa mai kaɗan sannan naɗan kashe masƙin man da fauda , kayana na saka na kwanta.

Dikko jin kiran waya yayi yawa , ya fara faɗa wai ita Rabiya bata da haƙuri gashi yana tafiya zuwa wurinta amma ta dameshi da kira. Wannan ɗan abun harya hasalar dashi danshi baida wahalar fushi amma yana saurin sauka. Cike da ɓacin rai ya ɗauki wayar a inda take ajiye amma sai yaga Inna ce take kiranshi. Ɗauka yayi da sallama ba Inna ce ta ansa sallamar ba mijinta ne ya ansa dakel yace kana ina ne ? Saida Dikko ya kalli hanya sannan ya faɗa masa ta inda yake. Tou wai kazo gidan Kaka dakai da Sultana. Lafiya Dikko ya tambaya ? Umm ai na tura maka saƙo ka duba , a , a , wai meye ne....? Baiyi magana ba ya ajiye waya.

Wai Allahna , Inna ta tafi itama..... Lahaula walaƙuwat illabillah shine abinda ya furta. Dakel ya nunawa Ashiru ya koma gida , taya Ashiru yaci suka dawo gida , dawowarsu ne shi Dikko ya shigo ya samu Sultana tana wanka , ɗakinshi ya koma yana tunanin ta wace hanya shi zai iya furtawa Sultana wannan saƙo....? Ita ya zata kalleshi ? Saƙon mutuwa baƙin saƙo ne , har abadan duniya baraka manta da wanda yazo maka da wannan aike ba. Ya juya ya rasa yadda zaiyi , ko Ashiru bai faɗawa ba. Wane hali An mata zata shiga ? Zatayi kuka kamar zata cinye ranta ya sani , shima kuma za shiga tashin hankali , duk duniya a wannan rayuwa idan akwai abinda ke tada mishi hankali yake firgita mishi tunani yake sashi ɗimuwar rayuwa da manta shi ɗin ko waye wallahi bai wuce tashin hankalin Sultana ba. Shi kaɗai ya isa yayi mata amma idan wani ya taɓota bayan shi ? Tou fa lallai zaici gari da yaƙi.....

Kira ne yake ta shigowa a wayata babu ƙaƙƙautawa. A wahalce na miƙa hannu na dakel dan ɗauko wayar dake saman bedsite. Kafin in ɗaukota a hannuna tuni ta tsinke har wani kiran ya sake shigowa ya fita. Saƙo ne ya shigo dan haka ban fara duba rashin kiran dana samu ba na fara da saƙon.

_Ke Sultana an faɗa miki uwarki ta mutu baki tahowa ? Tou ta mutu can wurin siya ma ɗanki abun wasa , mota tayi ƙoli² ta dakota da ƙasa sannan tabi ta kanta ta wuce. Ba wata tsiya nake kiranki ki bani ba bare kijamin aji ke surukar gwamna..._

Yayar Inna ce surukar Sultan wanda zan aura da farko tasa aka fasa auren ya auri "yar ta. Duk me ya kawo wannan dogon bayani tou ? Salati nayi na sanar da mahalicci na daya isa da rayuwata. Dakel na iya gano number Dikko a wayata na fara kiranshi komai bana iya gani kasancewar inaji na a cikin wata irin baƙuwar rayuwa. Shikenan na zama marainiya gaba da baya , babu uwa ba uba , Allahu Akbar , tabbas ubangiji shine mai iko akan komai da kowa.

_Kema ɗayar mara zuciyar_

Itace kalmar data fara dawomin a cikin kaina , ina hango Inna palonta a daren jiya......

_Me yasa shi ba'asan kawoshi ne wai ? Har sai wannan lokacin ? Kubar shi bana so tunda ba zaizomin yini ba._

Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un , wani irin ihu na kurma , na fara magangu na sakin layi , kai... Wai Allahna , innalillahi wa'inna ilaihir raji'un , nayi kuka sau adadin yadda naji ciwon mutuwar Inna a zuciyata , haba Inna sai kuma kema ki tafi ki barni ? Shikenan ? Tou wai mema yasa kika je siyen wani abun wasa ? Waye ya aikeki ? Haba Innata meya sa²..... ? Kema shine dai kika tafi kika barni ? Gaskiya nadai zauce nayi maganganu marasa daɗin rubutawa. Dikko yayi maganar shi banama jinsa dan gaskiya bana iya gane abinda yake cewa. Kukan da nakeyi ne shine ya tayar mishi da hankali shima yaita kuka kamar ƙaramin yaro wai zai mutu. Shi baya so yaga inayin damuwa , in rufa mishi asiri nasan bashi da lafiya , shima yaji ɓarin maganganu kamar aradu ta faɗo.

Ko a gidan rasuwa haka naita bori ina ihu mai tayar da hankali duk wani imani , babu wanda ya damu dani bare yace ke daƙiƙiya ki gyara kalamanki ko kiyi ma mutane shiru , Kaka ce kaɗai take rarrashi na , sai Pa-Pi daya riƙeni yana ta ihu wai waye ya dakeni. Yayar Inna ni bansan abinda yasa bata ƙaunana ba , bansan me nayi mata ba ta tsaneni da zafi haka. Ko waye ya rasa yayi kuka , nidai a duniyar rayuwata banga abinda yafi rashin iyaye raɗaɗi da ciwo ba. Inajin yadda aketa faɗar yadda mutuwar Inna ta kasance. Wai bayan tayi waya dani a yadda shi mijinta ya basu labari.

Baiwar Allah ashe abinda tayi mana jiya ya dameta. Ta faɗawa mijinta cewa gaskiya Dikko jajirtaccen namiji ne , kaifi ɗaya ne ita a yadda ta fahimta , tsaye yake babu munafurci a lamarinshi. Idan zaiyi kawai zaiyi idan bayayi ko za'a mutu zai tsaya a wurin. Wai tace masa idan yaji fushi ya sakar mata "ya , shine yace bai gaji ba , wai me yake nufi ? Ta ɗauki biro da takadda tayi rubutu akai , bayan ta gama sukazo gidan Kaka dashi da ita. Yace shi baisan abinda ya kawota ba , haka kuma baiji firarsu ba. Yau kuma tace a kawo mata Pa-Pi , wai shine taje ta sissiyo mishi abun wasa wai tasan Dikko zaiyi farin ciki dan ta goge damuwar data saka mishi a daren jiya. To shine fa ta gama sissiye²n tana zuwa wurin motar ta mota yabi ta kanta ya wuce.....

Ni ɗaya a wurin Inna , banda Ya banda ƙani haka nake ni ziƙau ina , ba uwa ba uba ba Yaya ba ƙani. Ga "yan uwan Inna ni basa so na , ahalin Babana kuma gasu dai ga yadda suke , "yan uwan Dikko sune suketa bani haƙuri , bawan Allah shi kuma ya kasa zaune ya kasa tsaye sai turowa Rabiya saƙo yakeyi wai An mata tayi haƙuri ta daina kuka , bayan wani lokaci kuma ya rubuto cewa wai shi yana nan bazai tafi ya barni ba insha Allah , hmmm haka dai yaita rubuce² har akaje aka rufo Inna aka dawo.

Duk ahalin Dikko sun tayani zaman makoki har Momy. Mai gilashi da zugar ƙawayenta "yan tasha amma banda Halima tayomin gayyarsu zuga guda. Akayi ta gulma na wai ni na tara karuwai a wurin rasuwar Mamana , Nabeela ma tazo kuma tayi kuka kamar yadda taga inayi itama , ta tausayamin sosai , tamin sannu da rashi. Sati ɗaya nayi a gidan Kaka nan nake kwana , Dikko kuma idan yazo sai dare sosai yake tafiya dashi da Pa-Pi.

"Yan uwan Inna kuwa bawai ta mutuwarta suke ba , abinda ta bari kawai suke ta lissafi. Babu kunya bare tsoron Allah suke farfaɗo suturunta kowa yana cewa ya kamasu , ita surukar Sultan itace take maganar kayan ɗaki wai dama wallahi ita kafinta yayi mata ha'inci kullum tana fama da "yan ƙwanƙwashe² gado ba kirki , kujerun ma duk sun rubza kaza². Shin aisai ta kwashe ita da zata tsaya tsaron duniya.

Ranar da akayi addu'ar 7 a ranar na bar gidan saboda wulaƙancin da sukemin. Da zan tafi ne Kaka ta bani wata takkada cewa Maryam gashi mahaifiyarki tace a baki. Meye a ciki ? Nima bansan ko ta miye ba , tadai cemin zata turoki ki ansa , amma itama kanta gaskiya batayi tunanin zaki anshi takardar bata a raye ba. Ansa nayi nabar palon. Dikko da kanshi ya ɗaukeni muka koma gida.

Nidai babu wanda a cikinsu yayi min magana game da duk wani abu daya shafi Inna. Basa gabana dan ni basu ne damuwata rashinta shine ƙaton ciwon dake damuna. Suke san abun duniya wanda har ya gusar da imani daga zukatansu , ana kukan mutuwa suna lissafin abinda zasu gada. Tun a mota Dikko kemin nasiha har muka je gida. Da kanshi yayi ma Pa-Pi wanka ya kwantar dashi. Duk inda na juya Pa-Pi sai yayi ta kallona sai kuma ya kalli Dikko.

Har bacci ya fara fizgarshi ya buɗe idonshi yace cinci abinci ? Murmushi nayi kaɗan tare da nuna mishi da kaina alamar eh. Shima murmushi yayi ba tare daya sake magana ba ya rufe idanuwanshi yaci gaba da bacci. Nima saida nayi wanka sannan naɗan taɓa fura. Saman gado na koma na warware takaddar da Inna ta bayar a bani , Dikko kuma yana tacan gefen Pa-Pi yana latse² a wayarshi...... Ga abinda Inna ta rubuta a takadarta.

_Aminci Allah , yaddar Allah wadatar zuci zaman lafiya da kwanciyar hankali su ƙara tabbata a gareki ɗiyata...._

_Sultana ki gafarceni a rayuwa. Nasan bakyajin daɗin abinda nake miki... ? Ni wallahi duk abubuwan da nakeyi ma Dikko dake banyi da nufi ba. Saidai ina hasko miki rayuwar gaba. Ke ɗaya na haifa a duniya baki da Baba haka kuma baki da "yan uwa da kika fita ciki ɗaya dasu. "Yan uwana kuma bakya gabansu , daga ni saike muka rage a duniyarmu , ina neman yafiyarki dan Allah , ki yafemin kuma insha Allah bazan sake ba..._

_Amma ki san wani abu a rayuwa. Nifa ba san Dikko ne banayi ba , a , a ni iskancin shi ne gaskiya bana so. Idonshi ya waye da yawa. Ni gaskiya a tsarin rayuwata bana sha'awa ko muradin namiji mai buɗewar ido da gogewar rayuwar irin na Dikko , amma ya za'ayi tunda haka Allah ya rubuto ? Nidai ina neman yafiyarki karki ɗaukeni a matsayin uwar data fi san kanta akan "yarta. Ban hanaki zaman aure ba haka kuma ban tilasta ki kashe ba. Saboda aure dai sunna ne mai ƙarfi daga cikin sunnonin Manza Allah S. A. W , kamar yadda ayoyi da dama suka nuna mana:•_

_Allah {{ S W T }} yana faɗa a suratul rum cikin alqur'ani mai girma. "Kuma daga ayarSa ne ya halitta daga garemu mataye domin mu samu natsuwa daga garesu. Kuma ya sanya tsakaninmu ƙauna da tausayi , haƙiƙa wannan aya ce ga ma'abota hankali. "Wannan aya ta tattara duk wani ma'ana na aure a cikinta. Saura namu farfasawa mu auna mugani , shin ma'anar aure da abinda yake cikinsa kuwa kamar yadda Allah ya nuna mana hakan mukeyi. Da farko Allah ya ambaci ma'aurata da ababen samun natsuwa duk anan ya kawo jinsin mata ne. To amma ai mun sani idan har macen bata samu natsuwa ba ? Shi kanshi namijin natsuwarshi ragaggiya ne. Tambaya anan ta ina ma'aurata zasu sami kwanciyar hankali.......?_

Hah. Ci.. Nayi tare da yin murmushi mai ciwo na goge hawayen dake bin idona. Ina ci gaba da kuka. Naci gaba da karatun takardar Inna.....

_Na farko:• a samun natsuwar aure shine hadafin yinsa. Bai taɓa yiwuwa aure ya kasance an ginashi kan wani hadafi sannan ya zamo ɗorarre. Wannan shi yasa Annabi {{ S A W }} bayan ya zayyano kaso na matan da ake aure. Ƙarshe yace "na hore ku da ma'abociyar addini. To haƙiƙa abun nufi anan shine ba wni hadafin da zai haifar maka da cikakkiyar kwanciyar hankalin aure sai hadafin tarayya domin Allah..._

_A cikin aure mai kawo natsuwa kenan. Haƙiƙa a yau munyi sake tare da watsi da haƙƙin junanmu ta yanda takei har wasu abubuwan ma an shafesu daga rayuwar auren sai wajen mutane jefi² mun barwa turawa wanda kuma mu addininmu ne ya koyar damu su. Ina horonki da ki zama mai biyayya , ki zama mai kunya da juyawa abin duniya baya. Kiyi kara ki zama mai haƙuri. Rayuwar gaba ɗayanta haƙuri ce , ki guji yaɗa sirrin mijinki wa kowa da koma waye. Kar kiyi abinda bakiyi shawara da mijinki ba , ki kiyaye fushin shi ki guji ɓata masa rai da gudun duk abinda baya so idan har bai tsaɓawa Allah ba. Haƙuri׳ ki zama mai haƙuri da biyayyar aure kinji uwar masu gida. ?_

_Ki kiyaye munanan kalamai. Karki kuskura ki jiyar da kunnuwan mijinki ɓatattar magana daga gareki. Magana mara daɗi ko muni kiyi ƙoƙarin kare kunnuwan mijinki dasu. Kar kiyi masa:• ƙarya. Ki kula dashi , ki zama mai tsafta , kar kici amanar shi , banda zargi ki guji abokai , karki raina masa iyaye. Ki kiyaye kuma kisan yadda zakiyu ma'amula da "yan uwansa._

_Kinga wa'anan abubuwan da zan lissafo su ? To ki kiyayesu domin sune ke taka rawa wurin rusa aure matsawar ba'a kiyayesu ba._

_Rashin ilimin zamantakewar aure , al'adu , rashin binken halin miji , rashin binciken halin mace , matsalar iyayen miji , rashin tsafta , matsalar dangin miji , rashin iya magana , rashin iya ciyarwa , rashin iya kwanciyar aure , rashin adalci , auren kisan wuta , cin amanar aure , ƙawaye , zafin kishi , sata , gulma , wayar miji {{ phone }} , rashin lafiyar miji wajen gamsar da iyali da itama rashin lafiyar macen wajen gamsar miji , sharrin boka. Ke kina tunanin ni bana sanki ? Taya ma zaki yadda ki fara wannan tunanin ? Tunda kike a duniya kin taɓa ganin uwar data haifa "yarta tace bata santa ne....? Ni ina so ne ki goge da rayuwa ke ɗaya , ki kuma iya haɗiyar baƙin ciki da magance damuwa dan ki zamar da kanki garkuwar rayuwarki. Domin idan yau ina nan gobe bana nan , yadda kike ke ɗayan nan babu abokin shawara ko na bar duniya barakiji wahalar rayuwa da kowa ba. Ina so ne kawai in auno iya girman soyayyarki a zuciyar mijinki. Na gani kuma ni nasan yana sanki dan nayi masa wani abu a abuja. Wallahi nayi tunanin yadda ake faɗar rashin mutunci zaizo ne kawai ya sakeki. Sai baiyi ba kuma nima baimin rashin kunya ko kallon banza ba kamar yadda nayi tunani... Wallahi inajin kunyarki ne , abun nan da nayi muku banyi da nufi ba , yayi ta damu nane banji daɗi ba , shi yasa na fara rubutun neman yafiya kafin mu haɗu dan mashala.Tou dake dashi duk ina san ganinku domin na nemi gafararku , sai kuma kema zamuyi zama na musamman...... sai mun haɗu kafin inyi tafiya_

_Fatima Salis Abbakar {{ Inna }}_

Wata irin ƙara nayi tare da cewa da yaushe ne zamu haɗu ? A ina me zaki ce man ne iye ? Cike da tashin hali ya kallo inda nake yace haba An mata wai meye kike haka ne ? Cikin muryar kuka na raunana murya tare da cewa ƙarshena yazo. Wannan kalma dana furta shine yasa Dikko kakkafawa , wani irin birkitaccen ihu na ƙarayi tare da matsawa inda yake , sautin ihun yasashi ɗaukewa gaba ɗayanshi. Da gudu na fita na gayyato Ashiru , cikin tashin hankali muka dawo tare dashi , shi ɗakin Dikko ya wuce sannan yazo ɗakina , haka yaita mishi shaƙe² harya dawo. Ɗan gajeren tsoki yayi tare da cewa insha Allahu saina mutu tunda dai baki bari in zauna lafiya. Fita Ashiru yayi ni kuma na matsa kusa dashi ina kuka , a gajiye ya jawoni jikinshi idonshi cike da hawaye yace wallahi bana san kina ihu , ki ƙyaleni in huta dan Allah. Kwanciya nayi a jikinshi nace na bari. Gefenshi ya nuna min in sauka daga jikinshi in kwanta , sauka nayi na kwanta ina kallonshi dakel ya lumshe idanuwanshi cikin yanayin jigatuwa kiyi bacci , rufe idanuwana nayi hannuna a saman gemunshi.

Bayan wani lokaci mai nisa ya sauke ajiyar zuciya tare da sauke hannun Sultana daga jikinshi. Wayoyinshi ya ɗauka ya fita a ɗakin. A gefen gado ya ajiye wayoyinshi bayan yaje ɗakinshi sannan ya wuce toilet kai tsaye. Wanka yayo ya fito ɗaure da rigar wanka yana tunane² , shi kaɗai yasan yadda yakejin rayuwarshi da kuma yadda yakeyinta a daddafe. Taƙaitaccen tsoki yayi tare da zuwa wurin wayoyinshi dan ganin mai kiranshi , Sharifa ce. Ɗauka yayi ba tare daya bari tayi magana ba yace yana zuwa....

Ajiye wayar yayi ya matsa wurin madubi. Kamar mace yaita ƙwasƙwarima , yana gamawa yabi kayan da zai saka ya bulbulesu da tulare shi zaije zance. Kallon kanshi yayi sosai a madubi shi kanshi yasan haɗaɗɗe ne shi ɗin. Murmushi yayi kaɗan tare da ɗan shafa gemunshi da bayan hannunshi na haggu sannan yayi kallonshi na gefen ido mai tabbatar da shi ɗin cikakken ɗan duniya ne.

Taf yauma Sharifa ɗif take ta ibi wuta sosai. Har bata iya tafiya sai layi takeyi , ga wasu irin kaya data saka kuma ko breziya bata da , kaf halittar surar ƙirjinta babu wanda baka gani kawai kamar buɗe yake. Full light yayi a dai² lokacin da yayi parking. Dogon kallo yayi mata daga cikin mota inda sukayi zasu haɗu dan yau ba g r a aka haɗe ba. Wasa yayi da fitilar mota ta nufoshi tana rangwaɗa , tana isowa ta wani kama murfin mota ta inda yake ta buɗe , rufe ta da faɗa yayi wai ita wata irin jaka ce ? Haka ta ratso duniya ta taho kowa yana kallonta ? Irin barinkinta zata yi mishi wai Dikko zata runguma , ƙara ƙufulewa yayi dan duk duniya ya tsani ana taɓashi , turata yayi baya da ƙafarshi cike da ɓacin rai yace Dikkon zaki kaiwa hannu eye ? Cikin hayaniya yace kai...... Lallai kin isa yayi maganar yana buɗo duk girman idanuwanshi. Ƙara nufoshi tayi da sauri ta ƙara ƙaddabeshi , ta ɗauka shiru zaiyi ya fara aiko numfashi kamar yadda Mai gilashi ta faɗa , sai taji karatu yasha ban². Da tsiya² ya fitar da ita jikinshi dakel. Kafin ya fito mota ta ƙara komawa ta cakumeshi , kai........... Da Allah ki daina riƙemin jiki , riƙo fuskarshi tayi tana matsar da nata kusa da nashi. Tureta ya ƙarayi da ƙarfi tayi baya. Da sauri yasa hannunshi aljihu ya ciro cingom kasancewar warin sigari da sauran wasu kayan mayen da yaji warinsu daga bakinta zuciyarshi ta tashi.

Tsalle tayi ta anshe cingom in tasa a bakinta wai yaci daga bakinta , kakarin amai Dikko ya farayi yana matsawa gefe tare da riƙe bakinshi. Caɓoshi tayi ta baya , aiko kamar jira yakeyi ya kakkaɓota ya fara kwallo da ita , saida ya bata kashin bala'e ya shige motarshi yai tafiyarshi ya barta kwance a hanya tana kuka.

Tsoki yayi tare da ɗaukar wayarshi dake wata ƙara zutt². Yusra ce , reject ya latsa yana gunguni. Cike da ɓacin rai ya koma gida duk saima yaci uwar matan nan dan ubansu , kawai ma dan ana magana dasu zasu ɗaukeshi wani daƙiƙi ? Bari har itama mai turo kanta tsirara zaici uwar ubanta ta sake zuba mishi banzayen hotunanta a waya saiya kasheta..... Ya faɗa yana kaiwa gado harbi da ƙafarshi. Dama su mata ma basu da wayau jira suke ayi musu magana su fara rainawa mutane wayau. Kamar shi ? Sai kace wani sa'ar wasansu ? Shi waccan jakar yarinyar ma zata wani daƙune ? Jinjina kanshi yayi da damuwa yace sai kace wani jaririn da yazo inda aka daɗe ana addu'ar samun shi , kai wallahi ya raina kanshi da har shi wata daƙiƙiya zata runguma. Tuno yadda Sharifa ta kasance a jikinshi da yadda harma ta samu damar tallabar mishi fuska , duk yana ina ? Aikin me yakeyi ina zamarshi ? Aiko wallahi da bai daketa ba har abadan duniya da baida kwanciyar hankali , tsoki yayi tare da cewa duk dai haka ta moremin wallahi...... Balgazar mace. Haka yaita masifa shi ɗaya
DOWNLOAD
DOWNLOAD

2 Comments On KWARATA RETURN
avatar
fatima-kasim

4 months ago

Reply

Naji dadi sosai sosai Allah y kara basira

avatar
daiy

4 months ago

Reply

Replying to fatima-kasim

Ameen muma munji dadin kasancewarki anan.

Please Login or Register in order to submit comment