Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

kuɗin gado da katifa na yafe miki tunda ke matar gida ce. Kuɗin kwai naira dubu talatin. Cikin kakari Jiddah tace ai ba duka naci ba , damuwarki ne wannan inji Yazeed yaci gaba da cewa + naira dubu biyar ta-ra akan kin tari numfashin miji yana magana kina sako mishi baki..... Duka abinda kuɗinki suka kama dubu ɗari biyu da tis'in da biyar , amma ɗari 3 zaki bayar hada ladar lissafi dubu biyar , ya ƙarasa maganar yana sakin wuyarta ya turata can baya. Riƙe wurin daya shaƙa tayi tana ta tari , ƙuhul² kamar sakin mayu.

Wai wannan wane irin zalinci ne ? A fusace ya nufi wurinta ya ɗaga hannu yace zan....... Da sauri ta duƙe. Wayarta ya ɗauka ya miƙa mata tare da cewa maza inji alart. Jiddah na kuka tayi ma Yazeed transfer. Dariya yayi bayan yaga tabbacin kwanciyarsu a asusun bankinshi ya rumgumeta yana sumbatar ta. Ina sanki haɗaɗiyar matata abun alfahirina bugun zuciyata , gaskiya yafa kamata azo a ƙulla hanyar neman wasu kuɗin kafin asusunki yayi shiru , ya faɗa yana fita daga kicin in sweetheart kisha shagalinki lafiya , lambar lokacin ki shine. 0 3 4 9 am. Wato yana nufin lokacinta da zai bata na katin danbe da ta siya shine 03:49am ya yada mata katin yayi gabanshi....... Kuka Jiddaah tai tayi tana Allah ya isa. Saida tasha kukanta har ta gode Allah ta kira Nabeela ta rattafa mata komai tayi ƙari akan abinda yayi mata ta kulle da cewa kuma yace baya sakinta. Abunka da ɗan uwa Nabeela taita kuka ta kira Rabiya ta faɗa mata. Rabiya ma taita tsinewa Yazeed wai zata faɗawa Dikko wallahi sai an kaso auren nan , yasan ashe Yazeed tsinannen Allah ne yasa aka haɗa auren saboda cuta irin nashi kaza² , taya Yazeed zai kulle yarinya a gida ba abinci yana bata gwale² sai duka ? A yinin ranar haka sukai ta yaɗa magana tsakanin su "yan ɗakinsu.

Daga baya suka bawa Jiddah haƙuri tare da tura mata kuɗi ta siya abinci kafin a samu mafita saifa Yazeed ya sakota ɗan iska mara mutunci anyi masa rana zai yiwa mutane dare. Rabiya da kanta tazo har gida taba Dikko labari , mugu yaji mugunta yasha dariya harta zarce musali. Saida yasha dariyarshi sannan ya turawa Sultana saƙo tazo palonshi , bayan naje yace Rabiya ta maido labari baya. Ran Rabiya kuwa ya hayaƙa taita zagin Dikko , waishi wane irin ɗan iska ne ? Ta faɗa mishi ciwo yana ta wata dariyar iskanci ? Cikin dariya yace bakinki ko nawa ? Fuuu Rabiya tai zuciya ta ɗauki jakarta , Dikko yace Hajjaju tsaya da Allah , naƙi in tsaya tunda kai ɗan iska ne. Allah ya baki haƙuri karki tafi. Tsoki tayi ta tsaya a bakin ƙofa , daga ni harshi duk fita mukayi , jingina yayi da ƙarfen bene ya ɗora hannuwanshi ta baya ya rakuɓe kamar mijin ɗiyar soja da yayi dukawa ita a barek kuma itace da gaskiya , haɗe rai yayi yana kallon Rabiya nima kusa dashi naje na tsaya ina kallonshi. Gyara bakinshi yayi shima ya kalleni. Murmushi nayi shi kuma ya sake gaggaɓewa da dariya.....

Rungumeshi nayi nima ina dariya , safko hannunwan shi yayi ya riƙeni. Wai anci ƙaniyar iskanci mata na buking in mijinta , ita da haƙƙinta a nuna mata fin ƙarfi , kam balasti nan taff ya jinjina kanshi da mamaki cewa "yan iska duniya basa ƙarewa ko kunyar faɗa ma baiji ba tirrr. Dariya itama Rabiya tayi amma badan ranta yaso ba , haka dai da damuwa , ciki muka koma duk a palo muka zauna. Dikko yasa aka sake karanto labarin ni da bana nan naji da kaina.

Shi kam Yazeed ma baida mutunci ko tsoron Allah bayayi ? Taya matarshi zata siyeshi dan yayi kwanciyar aure da ita ? Duk a raina nayi magana , tun daga wannan bansan inda zance su yaci gaba da tafiya ba , hankalina da tunanina kuma ya koma karatun rayuwa ta , ta baya. A gajiye na kwanta jikin Dikko ina ƙara hasko rayuwa da yadda ita kanta rayuwar tayi min hajijiya.

Maganganun Dikko da kuma dalilinshi na sawa a karanto min rayuwar gidan Jiddah. Shima wannan duk hikima ce , yana so inyi gyara ne a inda nake da matsalolin zamantakewar aure. Sai zan tukan Inna , taƙaitacciyar jiyar zuciya na sauke dakel a hankali na furta Allah ya jiƙanku iyayena yasa kun dace da kyakkyawar makoma. Saukeni Dikko yayi daga saman jikinshi zaije ma Rabiya rakiya. Nidai ban bisu ba nace ta gaida gida ina daga kwance..... Duk inda kake ka godewa Allah kuma ka nuna haƙuri da jajircewa. Bazafa a gane matsalar ba sai tafiya tai nisa. Allah ka rufamin asiri ka ƙarawa mijina haƙuri da halina , Allah kasa in daina mishi abinda baya so.

Tun daga wannan rana kamar anmin allurar natsuwa haka na zama wata baiwar Allah , har abun ya dami Dikko danshi a tunaninshi ko banji daɗin maganarshi akan "yan gidanmu shiyasa nake fushi ? Me yake damuna ne ? Ko banda lafiya ? Idan yayi min wani abu banji daɗi ba inyi haƙuri kuma in faɗa masa miye bazai sake ba. Nace masa babu komai amma hankalinshi ya gagara kwanciya.

Ko yau a makaranta burus² nake kamar garin kwaki bai jiƙu ba. Shima daya kawoni makaranta dai ranshi bai mishi daɗi ba , wai shi baya san wannan fushin da nakeyi , dan Allah in saki raina mana , ya zanta haɗe mishi rai shi bayajin daɗin gani na a irin wannan yanayin , ko na gaji da ganinshi yaje hutu idan naso ganinshi saiya dawo ? Nace ba komai , tou kiyi murmushi mana An matana...... Yayi maganar yanayin murmushi mai tafe da yaudararren kallonshi. Kaɗan na yaƙe bakina tare da kwantar da kaina gefe kaɗan nayi mishi ɓarawon kallo kamar liman yaga wawan zama , so kike dai in koma gida da baƙin ciki ko ? A , a , tou wai meke damunki ne ? Ba komai , cike da ƙunar zuciya yace An mata wai yaushe kika zama munafuka ne ? In banda munafurci ni zaki riƙa munafurta ? Me nayi miki ne iye ? A kwana biyun nan kina ta ƙoƙarin riguzamin farin cikina laifin me na aikata ? Gaskiya ce na faɗa bayan nan miye aibu na iye...? Babu , hmmm yayi tare da gyara zamanshi yace jeki....... Fuuuuu na fita ban rufe motar ba. Bin bayanta yayi da kallo. Banyi tafiya mai tazara ba na dawo raina a duƙunƙune nayi ma motar shigar bulet nima. Da sauri yaɗan ja kanshi baya. Kusa dashi na tsallaka na dafa hannuna a jikin gilas in murfin motar da yake zaune ɗayan hannuna kuma a saman kujerar da yake , na sakashi tsakiyata kenan , wasa nayi da girarena sannan na kakkaɓa mishi ido da logo mai ibar yanayi muuuuuu muah nayi masa a bakinshi. Wahalallen murmushi yayi tare da fitar da sautin numfashi a gajiye yana ƙoƙarin riƙoni na sauka a wurin na zauna saman kujerar mai zaman banza sannan na fice daga motar..... Murmushi yayi tare da rufe murfin motar yaja yai tafiyarshi.

Cass² coss..... Gaba ɗaya class in idon kowa ya koma kan Mai gilashi. Tana tafe tana wata irin girza mai tada hankali ta huro kwan cingom ta ciki ta hankaɗe kanta sama ga ƙaton gilashinta ya cinye rabin fuskarta. Duk lokacin data ajiye ƙafarta domin taka tazara wurin tafiya sai kaji kacau , tana ɗagawa zakaji ta sake wani irin kuka cauu coss , buɗe hannayenta tayi kamar zata rumgume wani take cewa. Aini kwarƙwassa ce tashi mai gida da gidanshi. Turnuƙuƙiy faɗan ibilas yaron idan baka sha duka ba kasha ƙura. Zama tayi a saman decks ta fara kirara kanta tana coka ma wani malami zagi. Malamin dake cikin ajinmu yace mata ta fita.....? Sch bag inta ta ɗauka ta fara tako. Wai su sune jihar katsina , kuma taurari a cikin duk wata jaha dake nigeria , tana alfahiri da karuwancinta domin shi ya kaitagacin nasara , tana alfahiri da tarihinta tana bugun ƙirjinta da zuwa nahihohin afirika da tayi ta silar kasuwancinta , duk wanda ya nemi ya ƙalubalantar mata sana'a zata sa a ɓatar dashi a gari. Malamin yace ta fita karta mishi ranshin kunya.....

Saida ta fita gaban aji ta kallo "yan kilas tace. Duk ɗalibi ko ɗalibar dake ajin nan wai tasan asalin kowa da tarinhin rayuwarshi har principal , shima malam dake tsaye tasan ko ƙafa nawa ne da ɗigo nawa na gidanshi {{ ƙarshen sani kenan }}. Kuma duk marecen ranar lahadin ko wane sati yana bi ta wurin gidan "yanci yana wucewa. Malam ci gaba yayi da rubuta babu a saman allo. Tsoki Mai gilashi tayi cewa idan yace ƙarya ne sai in faɗa mishi cikin motar da yake zuwa.... {{ furuci ne na "yan tasha , tana nufin karuwanshi , shi ya gane yaren amma "yan aji basu fahimci yaren ba sai mu damu ka ɗan karanta karatun bariki }} yo ai mu munsan komai wallahi shiru kawai muke muna ƙyalewa , wallahi babu wanda ya isa yasa naci gurasa inta wani wahalar da kaina wurin neman kayan haɗi ni ba mayunwaciya ba , ra'ayi ne abun ba muradi ba , bana ra'ayinta ne kwata² bare inci ta wahala tayi ta gurjemin makoshi , masu ra'ayi sai su siya suci ko ba ƙuli nasu ra'ayin ne ansa a haka tunda duniyar tana da faɗi biyan buƙata ga masu buƙata. Ba dalili na tattauna goro ni banci sigari ba , "yan aji...... ? Iye , shin ana dole ? A , a , gaba ɗaya suka ansa matsuwa da rashin wadatuwar muhalli kesa masu bada gidajen haye faɗa girman gidajensu dan suyi kasuwa. Amma a tunani na ra'ayi ne rayuwa ɗaki ɗaya da wani , babu abinda zaija min haɗiyar kwaɗo ina kallon kifi. Kuma bari mutum ya sake kai ƙarata yaga yadda zansa shi biya karatun bebe dan a tafiyar ai ba dole , kuɗi mutum yake bayarwa a bashi ɗaki a hotel idan har aka samu matsalar ruwan bayi ko rashin wadatuwar hasken wutar lantarki ƙorafi yake a canja mishi wani. Da lafiyata bani rayuwar tsohon gida bare rufin daya sha "yan dabaru ya faɗo ya kasheni. Kallon rainin wayau tayi mishi tare da cewa wutar lantarkinka bata da haske idan an hana kuwwa ai ba'a hana tsalle ba. Ka , taga ni anan nasan inda zan tarfaka.Tana faɗin haka tabar ajin. Shi kuma malam ya fara zage² yana fidda mutane waje.

Nima gaggaɓewa nayi da dariya , na farko dai su matan aure ba'a dukansu kuma ba'a zaginsu , ƙa'idar makarantar ne saida a haɗasu da mazajensu suja musu kunne idan kuma aka wonasu da yawa za'a koresu daga makarantar. Ci gaba nayi da dariya sosai ina kallon Malam domin dai maganganu ne masu zafi ta faɗa mishi a hikimance irin tasu ta "yan tasha. Kenan shi malam yakai tayin kasuwarshi ne wa Mai gilashi taƙi yadda , kamar yadda take nufi bai da gudun tafiyar dokin da take so , shine taƙi ansar tayinshi shi kuma yakaita ƙara yana goga mata laifin ƙarya..... Kallona yayi tare da cewa nima in fita in bar mishi aji. Ta window Mai gilashi ta leƙo tare da cewa fito in baki labarin yadda yake tafiyar da nashi dillanci. Cewa yayi in zauna. Ƙin zama nayi na fice waje nima , ina tahowa yace zan faɗawa mijinki kin fara abokai marasa tarbiya. Daga waje Mai gilashi tace shima Malamin baida ita.....

Har na fita waje ina dariya , dariya Mai gilashi tayi tare da cewa ɗan iska tsoho ɗan nakusa exp kai..... ? Ɗan an rubutamin best before ritayar..... Ta ƙunduma wata irin ashariya ta "yan tasha masu lasi. Leƙowa yayi yace mu tashi daga nan. Kallona yayi yace wallahi saiya faɗawa mijina iskancin da nakeyi. Mai gilashi tace kafi zuciya sauri kuma duk saina tona muku asiri , ni zan turo nawa shugaban har makarantar sai yasa an rufe munafikan banza kuci tuwon gidanku kuci na kasuwa , na makarantar ma dan haɗama duk sai kun cinye ku uwayen zalama. Ƙara kakkaɓewa nayi da dariya , nan ma magana ce mai jimla ta faɗamishi. Baiyi magana ba ya koma ciki ita kuma ta fara magana...

Izzar karuwanci ake gaya miki Sultana. Karuwanci na ni bana matsuwa bane ba. Na ƙara isa ne da neman suna sai inji nakai wata shegiya. Ga ciyamomi , sanatoci ministoci ham shaƙan "yan kasuwa kiga an nuno kamilin mutum a talabijin yana ta wani bubbuɗe ido dana ganshi nasan na shanye rubutun nayi gaba. Nayi mu'amula da mutanen dani bana iya lissafosu adadin yawansu amma ina da jerin sunayen duk namiji daya haɗa ƙirji dani , sassauta murya tayi cewa idan aka fiddo dubun maza a garin nan ai inaji ɗaiɗaiku ne banja zariar wandonsu ba...... Tsoki tayi cikin takaici tace amma har yanzu gwamnatin jaha bata san da zamana ba. Fashewa Mai gilashi tayi da kuka tana cewa Allah yasa kar in mutum ban shiga cikin talabijin ba , a nuno ni a matsayin tantiriyar karuwar data buwayi kowa a gari. Nidai kawai a jinjina min shine burina , idan ba da list ina zan tafi ba saina faɗo sunan kowa ta yadda lungu da saƙo idan na wuce ansan nima nakai jajirtacciyar karuwa.

Kidai ci bugun banza , dan duk wanda kika faɗo sunan Babanshi da sunan kin zare inajin kafin ki fito daga gidan talabijin ɗin katsina gaba ɗayanta ta haɗu. Yadda ake sara na nuna cewa saidai kiji ance attakabir wallahi gunduwa² zasuyi miki gawarki ma kanta baratayi kyan gani ba. Jakarta ta buɗe ta ɗauko leda mai layi² tana cewa sai ince duk subi layi....... Idan zasu sassarekin ? Ke ana maganar arziƙi kina san kawo min mutuwa wallahi , mtsww anshi nan ni kinji.

Ansa nayi na buɗe , wasu irin duwatsu ne masu masifar kyau kalar burgewa. Meye wannan ? Jigida ce banza. Jigida haka kuma ? Ey mana , irin ta saman ƙuguna ce , sirrin jaka sai kin ɗaura a ƙugunki. Ke ina kika samota ne ? Karki ɗaukeni wawiyar layi kinji. Buɗo idanuwa tayi sosai tace wanna jigidar babbar sirri ce , idan na fara lissafo miki "yan wasan data ciyomin zakisha mamaki gwargwadon yadda kikayi ɗimuwa. Ba katako bane banza duwatsu ne na sirrin rayuwa. Kinga wannan jigidar idan basai ta hana mijinki fitar dare ba kice bamai madubi nake ba. Da ɗan yanayin tsoro nace jigidar magani ce ? Kusa dani ta matso sosai tare da cewa magano.... Maganin ƙaniya... ? Ba'a wanka da ita na farko kenan , sannan na biyunsu ba'a kwanciya da namiji da ita. Maɓalli gareta kawai ɓallewa zaki idan zaki shigar jami'ar gadon aure. Amma mu masuyi dan kasuwa muna kwanciya da ita ne dan ƙararta itace ke buga kwalwar maza a taƙaice. Idan dai kin kwanta da ita tou lallai karkiyi wanka da ita domin kina bata ruwan wanka ta tashi aiki.....

Kuma da kikeji tanayin ƙara bawai itace da kanta takeyin motsin ba , kece zaki cire ƙyashi ganda hasda da baƙin cikin rayuwa kiyi tafiya da isarki. Tashi tayi tai tafiya lafiya lau , tace kinji kukan tane ? Nace a , a , tace an kallo ni ne ? A , a , wani yasan na wuce ? A , a , tou tsaya kiji sharrinta. Wata irin girgiza tayi tare da fara bada matakala. Wani irin kuka jigidar ta farayi coss׳. Sake tafiya tayi tace cakas² cas² , ta saman inda muke ta diro ƙasa cosssssssssssssss.. Cissssssss duk malaman dake kusa da inda muke a cikin aji saida suka leƙo. Dariya tayi tare da cewa ai da gayyarmu muke komai idan mutum yayi kuka muna da tsumman goge hawaye..... Aikinta ga maza ne bayan shekaru biyu take tashi daga aiki. Kyauta na baki wannan idan tayi miki kinji kina muradi saiki riƙa bada kuɗinki a siyo miki.

Zata fara bani labarin abinda ya haɗata da malamin dake cikin aji , da Alhajin da suke gidanshi aka aiko ana kiranta. Tashi tayi ta tafi ni kuma nabi jigidar nan da kallo. Tunani na farko daya zomin shine wasiyyar Inna , da tace kar inyi wani abunda mijina banyi shawara dashi ba. Shin da yaddar Dikko zan ɗaura ko kuwa da yaddar zuciyata....?

Har aka tashi makaranta ina tunani. Yau ba Dikko yazo ɗaukata ba Ashiru ne. Kuma dana koma gidan faɗa. Har an faɗa mishi abinda nayi a makaranta. Shi mutuwa zaiyi , ina zai saka kanshi , kinsamin ciwon zuciya sai na tafi na bar miki gidan nan , badai zaki barni in zauna lafiya ba ko ? Idan nayi miki faɗa kiyi zuciya dani kaza². Duk haƙurin dana bashi rufe idonshi yayi bai saurareni ba. Yaci gaba da masifa shi saiya haɗa kayanshi yanzu²n. Bazaki sake gani na ba sai kiyi duk iskancin da kika dama ? Kuma idan ya kama yarinyar nan sai ya kasheta............. Tou shikenan kaje ka kasheta , kuma wallahi sai nayi kuka , wayyo............ Allahna na kurma wani irin ihu na nufi ɗaki da gudu. Jin ya daɗe bai shigo ba nasan yayi zuciya. Fitowa nayi har yanzu yana nan zaune a inda yake. Daga sama ban sauko ba nace ai sai ka tambayeni me nayi kuma shi malamin me yayi min ? Kawai anzo an karanta maka ƙarya da gaskiya ka hau ka zauna. Gani ina da hawan jinin masu juna biyu. A asibiti ance na rage yawan damuwa da ƙuntatuwa. Kullum saika ɓatamin rai ga ciki kuma , shin dakai da cikin duk sai kunsa na mutu. Idan kin mutum ko baccin rana nayi in huta da halinki. Ƙaramin yaro yafiki daɗin zama. Mtsww. Shigowar Abbakar palon yasa nayi shiru. Shima bawan Allah a bindige yake da ganin idonshi yaji bala'en mace. Dikko bai kalleshi ba nima kuma ban koma ba ina daga sama duk ina kallonsu.

Magana yayi ƙasa² , banji abinda yace ba saidai shi Dikkon yayi murmushi mai ciwo. Ƙara kasa kunnuwa nayi amma duk iyakar masifa ta banji abinda suke faɗa ba , saida suka gama ƙus²ɗinsu Abbakar ya fita. Yana fita Dikko ya fara faɗa. Wai ashe Abbakar shima ɗanyen kai ne mahaukacin banza baima san matarshi tafi wannan wayau ba ? Wai me yace ne ? Tsoki yayi sannan yace wai matarshi zai kawo kiyima nasiha. Nace mishi tou wallahi ya rufa ma kanshi asiri karma ya kuskura matarshi tasan hanyar gidan nan idan kuwa ba haka ba tou fa lallai zamanshi da ita ya ƙare. Fashewa nayi da kuka cewa wannan baƙar shedar kayi min kuma.......? Ƙarya nayi ? Yanzu ba tsayawa kikayi daga nan kinamin rashin kunya ba ? Na tambayeshi shin tana baka abinci ? Yace min ey , tana maka sannu da zuwa yace ey , tana wanka tana wanke ido tana gayu ? Ey. Rashin kunya take maka ne ? A , a , nace tou idan dai ba tauye haƙƙinka takeyi ba ka koma kaita haƙuri nima haƙuri nakeyi , nace mishi gaki nan rashin duka yasa kwana biyu kin warware.

Shiru nayi na juya mishi baya ina magana ƙasa². Tsoki ya sakeyi tare da cewa Allah dai yaso ban faɗa mishi haka ba , cewa nayi dai yayi haƙuri bance kema fama nake dake ba. Kawai dai haƙuri na bashi cewa mata ai lallaɓasu akeyi , ni abinda ya ban takaici wai ke kallon mai hankali yake miki , har yana tutiya zai kawo matarshi tayi koyi da halinki , baisan nima ƙurmusa min takaici kike ba , yadai kamata kisan abinda kike gashi nan har za'a fara baki gabata. Kace ya kawota in mata nasihar. Ki fara ma kanki sannan kiyi ma wani , yana faɗin haka ya fice daga palon.......

Mai gilashi daga inda aka kirata tana gama abinda take gidansu Sharifa ta wuce. Anan palon gyatimar Sharifa aka zazzage kolin rashin wayau. Daga uwar har ɗiyar dan ɗimuwar tunani Mai gilashi duk ta maidasu wasu lusarai.... Mama wallahi matarshi ce duk take ta shige da fice. Yadda yake san Sharifa kika ga gaba ɗaya ya ɗauke wuta tabbas wata irin gagarumar jifa ce , sai kunyi da gaske kun ƙara miƙewa dan wannan tarayyar da babu "yan al'adu ai nasan da tafiyar bata yuwu ba. Tayi maganar dan bugun cikinsu. Ai nan uwar Sharifa ta saki baki taita hawa gefen layi , ina shi Malamin naku ne Mama ? Sharifa dake full charge tace yai tahiya tayi maganar cikin muryar mashaya tana layi. Cikin faɗa na duniyanci Mai gilashi tace gaskiya Mama kuma da laifinku. Laifin meye nawa ni a ciki ? Saboda Allah Mama kuɗan ƙiyasta dihun kai da wayayyar rayuwa , maza fa yanzu idonsu kallon rana yakeyi , akwai wanda baya san mace ? Taya Sharifa zata riƙa zuwa zance da hijabi dan Allah ? Su wa'annan "yan duniyar ai bakya nuna musu hijabi ba domin wayayyar rayuwa zaki fahimtar dasu kin iya , cake take dan haka maganarta bata fita.

Mai gilashi tace da Allah rufewa mutane baki muyi magana da magabata. Shiru Sharifa tayi Mai gilashi taci gaba da cewa Mama ni ina da Malami acan Zandar aiki yake kamar yankan wuƙa , saidai shi aikinshi sai an ɗebo fitina zama ɗaya yake buga aiki fitina ta koma tayi bacci. Malamin shine kika ga ya ɗauremin ƙugu nake baza hajar iskancina kasuwa². Kuɗin mota dana aiki duk ni zan bayar idan buƙata ya biya saiki bani abu na. Mamar Sharifa tace wane irin malami ne sai an jawo fitina yake aiki ? Izzar aiki ake gaya miki Mama , su bala'en suke kwantarwa dan dai kawai su nuna muku jajircewar su a wurin iya aiki , kuyi shawara sannan ku taro bala'e ni zan tsotse muku duk dafin masifar bala'en. Miƙewa tayi ta jawo Sharifa suka fito waje. Wuri suka samu dan ɗan keɓancewa gefe tace ke jaka bakuzo kun daki matar Dikko ba , sautin maganar kaɗai ke fita amma bakajin maganarta. Mai gilashi tace idan kunga dama kuzo ku daketan , tana faɗi haka tayi gaba abunta.

Shegu masu wayan tsiya , na gano kuma kuna haɗawa da ɗan tsibbunku , fashewa Mai gilashi tayi da kuka tana tafe a mota tana cewa Allah ya tsinemiki albarka Sharifa. Kin cuci rayuwata ƙarshe na ɓuge ga zaman b q , wai me nayi miki ? Laifin nena aikata haka da ciwo a rayuwarki ? Me na tsare miki a duniya ? Haɗu barimi rabuwa idan kowa ya tuba shine kika bini kika daƙilemin tafiyar sa'ar rayuwata. Na rantse da girman Allah yadda kika hanani kema sai kin jibge a gidan mai gadi ko ɗan share²n filawowi. Shima malamin naku zan ganoshi duk sai watse a sarari kuma idan na tashi uwar watsi zan muku yadda za'ayi rabuwa ko gaisuwa babu tsakaninku dashi. Wayarta ta ɗauka ta kira Sultana. Saida ta gama karatun da zatayi ta kashe wayarta tana cewa ki auri D ' K in zan gani , dani dake dashi da ita matar tashi an watsa kifi abinci a ruwa........

Misalin ƙarfe 10:19 na dare. Kai mai karatu ka tuno wacece ni tun farko dana fara baka labarin rayuwata. Na kira kaina da ma'abociya iya shafa turare tsantsar kyau da cikakken body. Da gudu turaren dake jikina
DOWNLOAD
DOWNLOAD

2 Comments On KWARATA RETURN
avatar
fatima-kasim

4 months ago

Reply

Naji dadi sosai sosai Allah y kara basira

avatar
daiy

4 months ago

Reply

Replying to fatima-kasim

Ameen muma munji dadin kasancewarki anan.

Please Login or Register in order to submit comment