Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

*KWARATA RETURN...*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_


Rubutawa...
*JAMILA MUSA...*



*SAI NA AURI D ' K*



🅿 ------ 4



Saida Yazeed ya ɓace ɓat Jiddah ta kalli agogo. 10:29pm , tou ? Wannan wane irin farashi ne haka ? Kuma farashin wai mai tsoka....! Haka kidahumar ta gaji da tunani amma tsabar doɗewar basira ta gagara gane irin farashin da Yazeed yake nufi. Haka ta haƙura itama ta koma motar ta taja ta nufi gidansu Dikko da ɓacewar tunani...

Zaune suke a gaban bokan Al ' Ameen. Saida bokan yasha kuka sosai dan rashin Al ' Ameen a cikin wannan duniya. Yana faɗin Allah ne kaɗai yasan tsakaninshi da Al ' Ameen da irin girman amanar dake tsakaninsu , bayan yayi shiru ne ya warware wani bakin ƙyalle yayi tsafe²nshi ya wurgashi sama , cikin ƙanƙanin lokaci ya dawo ƙasa fari fat dashi. Ɗauka yayi ya miƙawa Mardiya yace taje ta cire kayanta ayi mata wankan gawa , idan ta gama ta fito ga mankara can ya nuna mata yana ci gaba da cewa a cikinta zaki shiga a sallaceki bayan an gama za'a kaiki maƙabarta ki kwana. Zaki dawo nan wurina alfijir yana ketowa , idan kika yi wannan idan har Dikko bai aureki ba , ni ba ɗan sunna bane ba....

A gigice Mardiyya ta kalli Aunty Suwaiba cikin kuka tace tsoro nakeji Aunty , Aunty Suwaiba tace duka² miye wani abun tsoro a wurin ? Da Allah malama tashi , Mardiyya tace ita dai tsoro takeji , boka yace ai magana ya ƙare wannan shine abinda rauhanai suka aiko dashi , ko taje gida ta kwanta zata tashi ta ganta a maƙabarta ne. Kuma wallahi iskokai zasu shanye mata jini ta mutu , wankan da sallah shine zaisa basa iya mata komai , shawara ya rage nata. Ihu Mardiyya tai tayi , ta bani ta lalace , amma Aunty Suwaiba ta riƙa ƙarfafa mata guiwarta dan na yau kaɗai ? Tou meye a ciki ? Taje tayi kawai.

Aunty Suwaiba itace ta raka Mardiyya inda boka ya nuna musu wurin wankan gawa , gurguwar banza itace ta zauna kamar gunkin baƙin kafurawa , Mardiyya ta kwanta irin yadda matacci sukeyi akayi mata wanka , bayan an gama aka saka likafani , sallah a makara tafiya zuwa kaita maƙabarta....

Tunda Mai gilashi tabar gidan Sultana bata koma gidanta ba har 11 ta dare tana ta yawo a gari tana neman Sharifa amma bata ganta ba. Ganin bata samu ganinta ba yasa ta tafi anguwarsu , tayi bincikenta kamar haka.... Sharifa tana bin malamai ne ? A , a , amma mahaifiyarta muguwar mai neman asiri ce kamar rainon maguzawa. Ƙarfe nawa take komawa gida ? Aka faɗa mata , Dikko yana zuwa gidansu ? Baya zuwa ! Ya yanayin ibadarta ? Bata damu da sallah ba gaskiya danko azumin ramadan batayi , idan an mata magana sai tace tana ulcer , mutanen da mahaifiyar Sharifa ke mu'amula dasu a cikin anguwa ta nema tayi musu wasu "yan tambayoyi , tana gamawa ta wuce babban gida , a wurin ne takejin wai ta tafi kano wurin taro Dikko.

Idan hankalin Mai gilashi yayi dubu ya tashi ɗaya bayan ɗaya. Kiran wayar Sultana ta farayi amma ba'a ɗauka , ta kira so adadin da ita bata iya ganewa amma sam Sultana bataji ba dan wayar baya tare da ita. Kai tsaye gidan Sultana ta dawo , amma fur aka hanata shiga , number Sultana ta nuna da duk wani abu da zaisa a yadda tasanta , amma aka hanata shiga idan dai Sultana ta ɗauka waya zata sanar dasu ne su kuma sai su yadda taje , tou bata ɗauka ba. Har 11:38am Mai gilashi bata tafi ba , Sultana bata ɗauka waya ba kuma bata kira ba haka basu barta ta shiga ba. 11:40am ta daki get in gidan cikin tsananin ɓacin rai da takaici tabar ƙofar gidan....

Saida tayi tazara mai nisa ta fara kiran wayar Sharifa , ita kuma saida ta mula tasha iska ta ɗauka cikin yauƙi da rainin wayau tana wani cakal² da cingom irin na riƙaƙƙin "yan bariki , hmmm Mai gilashi tayi tare da cewa suna na Sa'adatu Mai gilashi...... Saida Sharifa ta sake cakal׳ tace ai na sani. Kina ina ne haka ? Mai gilashi ta tambayeta. Kin aikeni ne ? Murmushi Mai gilashi tayi tare da cewa , dani dake babu wanda ya aiki kowa ko yasa nake tambaya , inda kike kawai nake so ki faɗamin..... Zaki zo ne ? Dariya mai Mai gilashi tayi cewa ai hannun haggu ba baƙon inda kike amfani dashi bane ba. Yanzu dai ba wannan ba , naji ance zakiyi aure ?

Cike da ƙwarin guiwa tace eh , waye zaki aura ne ? D ' K , ba naki bane ba. Sharifa tace nawa ne , Mai gilashi tace ƙarya kike ba naki bane ba... Sharifa tace wallahi saina auri D ' K , kamar ya kikejin shi ne ? Shine duniyata , zaki iya faɗamin ko adadin mutane nawa suka bar duniya ne duk soyayyar da suke mata ne ? Suna santa kuma sunajin daɗin ta , amma dole sun tafi sun barta suna can ƙasa sun kwanta badan ransu yaso ba dalilin yasa kikaji nace ba naki bane ba yana da dubunki , amma kuma tunda kika kirashi da duniyarki tou ba naki bane ba. Me yasa kika ce haka ne ? Mai gilashi tace yawwa, bara na baki misali. Hafsa Jiddah Mardiyya Yusra ga kuma Sharifa matarshi na gida , ita ta gidan ƙaddara kawai bata a lissafi tunda an aureta. Nawa zai aura a cikinku nawa zai bari bai aura ba ? Su waye su ? Sanin su waye su da matsayinsu a wurinshi ansar tambayarki tana wurin D ' K ki tambayeshi abinda yace miki ki kirani ni zan buɗe miki yadda abun yake , tana faɗin haka ta tsinke wayarta.....

Mai gilashi da damuwa ta koma gida. Addu'arta ɗaya Allah yasa Sultana taje makaranta idan Allah ya kaimu gobe , yanzu dai tasan gidan Dikko bazai zuwu wurinta ba tunda ya dawo , itafa bawai tana gudun kar ayi ma Sultana abiyar zama bane ba , a , a , ita abinda Sharifa tayi mata kawai zata rama , kuma itama yadda ta sata ta kashe kuɗaɗenta wurin bin malamai dan ganin wancan daya fasa aurenta ta sameshi amma Sharifa tayi mata zagon ƙasa tou itama sai tayi gwale² da Sharifa da duk kuɗin data tara a bariki. Dariya tayi cikin farin ciki cewa an kunna. Yarinya da *MAI GILASHI* kike wasan , muje zuwa..........

Saida na farka kamar yadda na saba a ko wane dare. Bayan nayo alwallah na fito na ɗauki wayata , missed calls na gani babu iyaka. Sai text in Dikko daya cemin inzo ɗakinshi yana kirana... Cike da fushi na fita na nufi ɗakinshi , da sallama na shiga ! Palo na sameshi kwance saman kujera yana cht , gitsi² nace gani. Ba tare daya kalleni ba ko ya daina abinda yakeyi a waya yace zo nan , wurinshi naje na tsaya ina fushi. Ɗago idonshi yayi ya kalleni cikin sigar zaman lafiya yace bacci kikeyi ne ? Ey na faɗa ina turo baki a tsiwace , to ? Sai yanzu kika ga text ina ? Ey , yayi kyau kije kawai. Bazar² na juyo , bayanta yabi da kallo saida ta fita ya maida hankalinshi a wayarshi yaci gaba da abinda yakeyi...

Ina dawowa ɗaki na fara kiran wayar Mai gilashi , kuma a lokacin 2 saura. Bata ɗauka ba , saidai ta turomin text cewa tana ɗakin Alhaji waya bazai yiwu ba , amma in sani Dikko yana zuwa katsina , kuma yana tare da Sharifa , abinda take so ta sani shine. Bawai tana zargin shi bane ba , abu ɗaya take so inyi a daren nan in baibaita rayuwa kawai nayi mata ƙoƙari na kyautata a daren nan cht inshi da Sharifa takeso na cire kaf na turo mata dan Allah ! Kar in kirata kuma kar in maido mata reply kar ince a , a , tamin alƙawari zata bani labarin da bata faɗamin ba , idan ban turo ba kuma wallahi bazata faɗa ba. Kiyi ɗamara..... Ki tuɓe , kuma ki kife gidadanci , ai kin gane abinda nake nufi , kiyi tunani , ki tuna. Tuna׳... Ki tashi ƙura kuma kiyi ƙoƙori a yada dogon zango in jini...

Shiru nayi bayan na gama karatanta saƙon Mai gilashi , wato nine zata latsa ? Tou wai meye ma matsalar ta da Sharifa ? Bata zargin Dikko kamar ya kuma ? Shi Alhajin ina iyalin tashi take ne a wannan dogon daren ne ? Ita Sharifar kuma wai me yasa ne kowa yakejin tsoronta ? Nima lallai ina san sanin abinda kowa yake tsoron ma Dikko Sharifa , ina san gani kuma nima ina san sani. Ajiye wayar nayi tare da ɗaukar ɗamara kamar yadda Mai gilashi tace , cire hijabi na nayi na ƙara mammatsa turare naɗan kakkaɓe dai bayan na tabbatar nayi na nufi ɗakin Dikko.....

Da sallama na shiga , yana kwance a inda na barshi , amma yanzu ya juya baya yayi takurarriyar kwanciya mai nuni da gajiya. Itama sallamar a gajiye ya ansa ta. Saman hannun kujera na zauna tare da cewa sannu da zuwa. Ba tare da wani damuwa ko rashin jin daɗin da farko ban masa ba yace yawwa , shiru ya ziyarci palon har na tsawon mintuna 3. Nice na katse shirun da cewa ina Papi da Sharifa ? Shiru yayi baiyi magana ba , dakai nake. Juyo da kwanciyarshi yayi yana kallona amma baiyi magana ba , ɗan kauda kaina nayi gefe haka nan naji gabana yana faɗuwa. Ban sake magana ba na miƙe , riƙoni yayi tare da jawoni a hankali zuwa saman jikinshi yakai hannunshi yana shafo cikina.

Kwantar da kaina nayi haka ta tsaye ba ta gefen fuska ba ina kalloshi cikin damuwa. Murmushi yayi kaɗan ya tsareni da ido , gyara kwanciyar fuskar tawa nayi zuwa gefe fuskata na fara wasa da gemunshi. Zame hannuna yayi daga wurin , sake maidawa nayi ya sake zameshi duk munyi haka yakai sau biyar , zuciya nayi na tashi da niyar fita , karki fita zo kiji , shiru nayi fuuu na wuce , An mata dake nake fa kizo nace , haka nan naji zuciyata tanamin tuƙuiƙi. Da ɓacin rai naje ɗakina , ina zuwa toilet na wuce na wanke hannuna ina cewa kuma bazan sake taɓa gemunka ka ba har abadan duniya , dan kaga ina taɓawa shine zaka ciremin hannu tou bazan sake taɓa maka ba tunda baka so Dikko...

Cike da damuwa yabi bayan Sultana. Ita kuma a dai² lokacin data fito daga toilet. Rufe ɗakin yayi sannan ya matsa jikin bedsite ya ajiye tarkacen wayoyinshi bai mata magana ba ya wuce toilet shima. Gefen gado na zauna naci gaba da haɗe rai kamar an sace uwata , shima ranshi a haɗe ya fito kamar an kaiko mishi saƙon mutuwar uwa uba a lokaci ɗaya....

Bedsite in kusa dani ya zauna tare da bani umarnin ni in matso kusa dashi , ƙin matsawa nayi na ɗauki wayata ina latse². Ki matso nan nace kuma ki ajiye wannan wayar tun kafin raina ya ɓaci , basar dashi nayi naci gaba da latsan waya cikin taurin kai da ƙaddarawa ma bashi a wurin. Miƙewa yayi ya ɗauki wayoyinshi ya tunkari hanyar fita , me yaji me ya gani ? Oho ya dawo , saida ya zauna ya ajiye wayoyinshi ya ɗan riƙoni jikinshi da soyayya , hannuna ɗaya ya riƙe tare da ɗorawa a saman fuskarshi yana shafawa a hankali harya gangaro saman gemunshi yana shafawa kuma ya tsareni da ido da kallonshi mai burgewa yanayin wasa da iskar bakinshi cikin salo mai yanke damuwa.

A ɗan damuwance nace ai tunda baka so ina taɓa maka na daina , ina so yayi maganar yana rage girman idanuwanshi. Ai nayi fushi , na bari , ya faɗa yana min kallon rainin wayau. Ey dama dole zakace ka bari tunda ga Sultanar banza yanzu ne kasan amfani ta rashin kunya kawai. Da yanayin tsinkuwa ya kalleni yace wai me ke damun kanki ne ? Haba An mata ni banajin daɗin abinda kikemin haka ! Ey dama ai dole zakace bakajin daɗi tunda ka ɗaukeni Sultanar bayan fage.

Tou waye ta bayyanannen fage An mata ? Kasan inda ka barta , ya za'ayi in sani tou ? Jakar da ta rakaka tafiya , taje ta rakoka Katsina tunda baka san hanya ba , ni danma ka ɗaukeni bansan abinda nakeyi ba ai baka faɗamin zakayi tafiyar ba saidai na tashi na gani zaka tafi , ko inda zakaje baka faɗamin ba sai wasu "yan iska karuwan banza , kuma bana sanka dama jira nake ka dawo Allah bazan sake zama dakai ba na ƙarasa maganar ina fara kuka , cikin kuka naci gaba da cewa da wata "yar iskar karuwa mai turo maka hoton tsiranci tunda dai yanzu ka daina so na kawai ka sallameni nayi gaba abuna , dan dana fita daga nan wallahi wani babban Alhaji zai kwasheni ya tafi dani can ya gina min sabuwar rayuwa mai inganci. Wacce babu firgici ko tashin hankali a cikinta. Ni ɗawisuwa ce kuma ai kasan babu yadda za'ayi abar ɗawisu sake yana yawo. Martabashi ake , ɗawisu baka rayuwa gidan matsiyata sai gidan kuɗi. Idan ba gidan kuɗi ba sai gidan sarauta , da rubibi za'a kamani kuma duk sai masu kamanin sunsha wahala duk sai sun bugu da wahala sannan mai rabo zai sameni dakel , a dakel inma sai mai tsanantaccen rabo gidan kuɗi nawa ka leƙa amma babu ɗawisu ? Kuma kaji kunya an girma ba'a san an girma ba mai gemun yaudara. Taƙaitaccen murmushi yayi ba tare da yace wani abu ba ya tsare Sultana da ido.

Ci gaba nayi da feƙa rashin mutunci , Dikko ya tsareni da ido cike da mamaki shi al'ajabi ma ya hanashi yayi magana yadai bita da kallo , kuma gidanka banza kaje ka ajiye duk jakar macen da zaka ajiye ni bana zama da kishiya , ai da daka dawo sai kaje can inda kake zama sai 3 na dare ka dawo gidan , a gajiye ya jawoni jikinshi ya rufe idonuwanshi cikin ɓacin rai yace ƙaramar yarinya. Daga haka bai sake magana ba ya fitar dani daga jikinshi yanayin fushi. Nayi kwanciyata naci gaba da bacci....

Bayan Sultana tayi bacci Dikko ya tsareta ido yana sake² a zuciyarshi. A daren yau baiyi bacci ba , kuma ɓacin rai bai barshi yayi cht in dare ba , gyara mata kwanciya yayi tare da jan bargo dan lulluɓeta sai kuma ya tsaya yana kallon cikinta. Na tsawon wasu mintuna sannan ya tafi da bargon a hankali ya lulluɓeta cike da soyayyarta a zuciyarshi. Wayoyinshi ya ɗauka ya fita bayan ya kashe hasken ɗakin.

Ya so a daren nan yaɗan rage nauhi amma An mata ta ɓata mishi , a gaban idonshi take cewa wani babban Alhaji zai kwasheta ! Ashe idan ya mutu An mata mantawa datayi dashi ? Bara tayi mishi addu'a ba ? Papi da wani babyn zata zubar dasu taje tayi sabgar gabanta ? Tunani barkatai a ranshi. Ya saƙa ya warware baisan iyaka ba , ƙaramar yarinya ta zauna tai ta faɗo mishi maganganu na yarinta , mtsww wannan damuwa tasa kafin safiya ta waye Dikko ya kwanta rashin lafiya..... Fatarshi ya wuce kawai kar yaga wannan baƙar ranar wallahi.....

Ni bansan Dikko bashi da lafiya ba , gari yana wayewa na shirya nai tafiyata makaranta banje ta ɗakinshi ba. Papi kuma yana can wurin Momy dan Nabeela ta dawo da suka fara zuwa tacan shine ya liƙe wurinta......

A makaranta. Yau ajin ba daɗi dan Mai gilashi bata zo ba , dana kirata na tambayeta abinda yasa bata zo ba , cemin tayi ina cht in da tace na turo mata ne ? Sai anjima zan turo miki , tou ya akayi kikaje makaranta bayan kuma ance D ' K baida lafiya ? Wata irin mummunar faɗuwar gaba naji , meya samu Dikko na tambayi kaina......? Meke damunshi har abun ya fita waje yabi duniya ni banda labari ? Tsinke kiran Mai gilashi nayi na fara kiran wayar Dikko , bai ɗauka ba , Ashiru na kira shima bai ɗauka ba , Umar na kira , tana shiga yana ɗauka , Umar kana ina ne ? Qerau , wai me yake faruwa a goruba ne ? Ba komai , kowa lafiyanshi qalau ? Lafiyan kowa qalau ya bani amsa... Kashe wayar nayi na sake kiran Mai gilashi. Tana shiga ta ɗauka , Mai gilashi waye yace miki Dikko bashi da lafiya ne...? Sharifa , ki duba a whatsapp na ajiye miki saƙo kiga cht inta da mijinki , gaskiya Sultana baki da wayo , duk kina ina wannan iskancin ke faruwa ne ? Waton shi mai wayau idan yayi magana sai ya goge maganarshi , na turo miki dai ki gani abinda na fahimta ni zanji da sauran aiki , saboda yaƙin yafi ƙarfinki nima nace na Dikko An mata , tana faɗin haka ta tsinke wayarta....

Haka nan naji gabana yana halbawa ɗil׳ sai tashin hankali da nakeji gaba ɗaya wani ruɗu yazo min na kasa zama. Wurin Farisa nabar jakata na nufi gida cikin tashin hankali , a ƙofar shiga palon ƙasa nayi parking kuma gidan yana nan cike da mutane maza da mata kamar yadda yake kasancewa a ko wane rana. Kowa yana hidimar gabanshi da gudu na shiga ciki kai tsaye ɗakin Dikko na wuce ko takalmi na ban cire ba danni bana shiga ɗakinshi da takalmi komai sabuwarsu dana shiga palo zan tuɓesu......

Zaune na sameshi gefen gado ya jingina bayanshi da kan gado ƙafafuwanshi miƙe ɗaya saman ɗaya ya rungume hannayenshi kanshi yana kallon ƙasa. A tsorace na isa wurin ina cewa Dikko me ya sameka ? Bai ɗago ba kuma baimin magana ba , kusa dashi na zauna na ɗago fuskarshi , kallona yayi. Kuka ? Na tambayeshi ? Gyara bakinshi yayi yana ci gaba da kallona , rumgemeshi nayi nima na fashe da kuka , cikin kuka nace me ya sameka kakeyin kuka ? Zuciyata , shine amsar daya bani , amma me yasa baka faɗamin baka da lafiya ? Na ƙarasa tambayar ina riƙe fuskarshi da duka hannayena biyu. Ba kinsan na kwana gidan ba ? Idan har ina da mutunci da daraja zaki tafi makaranta baki zo kika ce wannan banzan ka tashi lafiya ?

Kefa yarinya ce , ni kuma na tsufa inji ki fuskata ta fara squeezing. Kamar ƙaramin yaro yake cemin nima fa ɗan saurayi ne , duka²na a nawa nake hararata yayi cike da soyayya sannan yace , ni a haka nayi miki tsufa dai ko ? Idan dai ni tsoho ne kema tsohuwarce tunda daga ni harke kowa ɗanshi ɗaya da zaki wani kalli tsabar idona kicemin wani Alhaji zai kwasheki. An mata wannan mutunci ne ? Ke da , da ne lokacin ina Dikkona har kin isa ki faɗamin wannan iskanci ban kashe ki ba ? Kika mutu murus , babu wanda yaji ba kuma wanda yasan anyi saidai a nemeki a duniyar nan a rasaki. Ko yanzu ni ba iya dukanki ne banayi ba wallahi tausayinki nakeji saboda kina da ciki. Duk wannan iskarcin da kikeyi ba tsoro yasa na zuba miki ido ba , ko zan mutu idan bana tare dake ni banajin kaina ke nakeji. Duk a wahalce yake magana cikin shashsheka a sanyaye cikin laushin murya maisa natsuwa....

Ki kalleni tsaf daga samata har ƙasa na kinsan ni ba sakaran namiji bane ba , kuma kinma san na tsufar kikace kina so na ? Tou ni ba tsoho bane ba , duka² shekaruna nawa ma ? Tsoki yaja sosai , tare da nunani yana cewa a gabanki ma zan zauna ina kwancewa har nake da lokaci maida miki magana , tsohon ne yayi maganar yana min wasa da harshenshi cikin salo mai ɗaga hankali ya raka wasan da kallonshi maisa mutum yaji cikinshi na halbawa , a kasalace na matsa da fuskata kusa da nashi na ɗora bakina a bakinshi. Maida harshenshi yayi yana murmushin jin daɗi tare da lumshe idanuwanshi a hankali cike da shauƙi , yana nuna yanayin zaƙuwa kuma har yanzu idanuwanshi a rufe , baya nayo da fuskata ina kallon kyakkyawar fuskarshi , bai buɗe idonshi ba yana a rufe kenan yana jiran tsammani , jina shiru yasa ya laliboni tare da riƙo kaina da hannunshi jikinshi yana kyarma ya haɗe cikin soyayya , bayan wani lokaci ya cire "yar guntuwar hijabita ya kwantar dani gefenshi ya kwanto shima har yanzu idonshi a rufe cikin yanayin farin ciki. Battery low......

Mai gilashi kuwa saida ta gama tuɓe kaf sirrin Sharifa sannan take tambayarta shin ko Dikko yana da wani logo ne ? Sharifa tace bashi da. Shi miskili ne kuma yana da wahalar sabo baya maganar data wuce biyu , baya dariya kuma baya murmushi idan kuma surutunki yayi mishi yawa zai tsareki da ido ne. Kinga taya kuwa za'a iya gano logon shi ? Amma da me kike da ibar mishi fili ? { abinda takeyi tana ɗaukar hankalinshi kenan } Sharifa ta faɗa mata , Mai gilashi tace tou ko ya taɓa faɗa miki aibun matarshi ne ? Da dalilin yasa zai aureki ne ? Sharifa tace gaskiya a , a , yadai cemin shi yana san matarshi sosai kuma yana tausayinta bai haɗata da kowa ba kuma yarinya ce ni na girmeta. Duk kuma wanda ya taɓota tou ba itace ba shine aka taɓo. Idan An mata tayi kuka shine idan tayi farin ciki shine. Wanda yaso mata farin ciki shine yaso , kuma duk yadda yake san mutum idan ya aibata ko munana mata tabbas zaija layi tsakanin shi da koma waye , shine kaɗai ya isa ya ɓata mata kuma shine farin cikinta duk duniya bata san kowa ba saishi , haka bata gane kowa saishi. Shi kuma itace rayuwarshi , lumfashi , bugun zuciyarshi , itace komanshi dan haka in kiyaye. Kuma shi abinda yasa zai aureni shi bawai ra'ayin shi bace ni , ba irin tsarinshi bace ba. Umarnin Dad inshi ne , Mai gilashi tace tou me ya kawo akayi maganar ne ? Ko haka kawai ya faɗa ? Sharifa tace nice dai naɗanyi maganarta , duk dalilin maganar nan kuwa matar Babanshi ce tayi wani aiki akan shi bansan ko na miye ba shine tace idan naje wurinshi naɗan aibata ita matar tashi kome yace nazo na faɗa mata ta nan zasu gane idan nasara ta samu karɓuwa...... Bayan ta gama jin duk abinda take so taji. Ta turawa Sultana saƙo duk abinda takeyi ranar yau tayi ƙoƙari tazo gidanta , bayan ta ajiye mata adireshi gidan....

Hafsa da Amisty gurfane a gaban sabon malamin da ta samawa Hafsa kamar yadda ta faɗawa ita Hafsat in. Saida ya zana ƙasa ya goge , ya sake zanawa , ajiyar zuciya ya sauke bayan ya gama zane²n
DOWNLOAD
DOWNLOAD

2 Comments On KWARATA RETURN
avatar
fatima-kasim

4 months ago

Reply

Naji dadi sosai sosai Allah y kara basira

avatar
daiy

4 months ago

Reply

Replying to fatima-kasim

Ameen muma munji dadin kasancewarki anan.

Please Login or Register in order to submit comment