Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

a tsakiyar falon.
Yasha lemu kawai yace ya koshi, Alh ya jima yana kallon yaron da ya shiga zuciyarsa farad daya ki domin baida da namijine ohom.

Yaso yaji dukkan labarinsa but Abdul Haseeb ba haka yake ba, bayan miskillanci yanada rike sirrinsa domin ba ayi ciki don tuwo kadai ba, to ma haka kawai ne daga haduwa da mutum bai San kowanne irine bane zai zayyane masa sirrinsa, no bai san abinda zaije ya komo ba, bai san me mutumin ke nufi dashi ba.

Alh Muhd ya tabbatar da ba zai Kara jin komi daga bakin bakonsa ba ya hakura ba don ya gamsu ba sabida har zuwa lokacin Yana mamakin uban da zai samu hazikin yaro kamilalle irin Haseeb yai biris da al'amarin neman ilminsa, da daure kai sosai amma tunda yaron ya dage kan cewan Yana kwadagon don ya taimaki kansa ne ya kyalesa a haka yai masa taimakon da zai iya yi masa.
09/09/2020, 23:56 - Anty saliha: ..ˆRAHIMA ...doc by jami

22

A ranar yaiwa Haseeb albishir din cewan saboda ya yaba dashi matuka gaya zai taimaka masa Kan harkar neman ilminsa tun daga kasarmu zuwa kasashen ketare har ya cimma burinsa. Yace Yana son ya dau masa alkawarin zai amince ya zama dansa saboda shi bai taba haihuwar da namiji ba, 'ya'yansa takwas duk matane. Bai yi saurin amincewan ba ya nemi ya bashi kwanaki uku yaje yai shawara tukunna, Alh.Muhd ya amince ya kawo kudi ya bashi yace yai kudin mota.
Ya amsa yai godiya ya tafi. A ranar ya sallama gidan mijin mahaifiyarsa Yana kiransa Baffa, ya shaida musu duk abinda ya faru, Kaltume ta tsaya shiru ta rasa ta cewa, maigidanta yace mishi "Kaje ka amshi taimakon nan da hannu biyu ka rikesa da zuciya guda bisa amana tareda adduar Allah ya taimakeka bukatarka ta biya."
Kaltume ta nisa "Anya? Ina jinjina batun mutumin nan Malam, kana ganin za'a kwashe lafiya, ka fa san halin mutanen zamanin nan na mu."

Mal. Sunusi yace "Insha Allah na komi, Ubangiji fa ba yadda bai iya tsara al'amarinsa ba, idan cikin hikima da basirarsa ya kaddaro Alh. Muhammadu ya taimaki yaron nan ba makawa, ai shine kaddarar, zaki ga wani mutumin ba ko a mafarki tunani bai taba kaika cewan zaku hadu ba sai kwatsam Allah ya hadaku a shiga cin gajiyar juna. Kai dai har kullum gargadina gareku shine Wanda duk Allah ya hadaku dasu ku zauna dasu tsakani da Allah da zuciya daya, banda hassada ko kyashi, Banda biyewa zuciya ko mutanen duniya 'yan Kai kawo su shiga tsakaninku, banda daukar jita-jita.
Ka sani daukaka Allah ke yiwa mutum ba kowa ba, idan ya so ka daukaka iya hassadar makiya basu isa su hana ba, kazalika in baiyi nufu ba ba Wanda ya isa ya kaika inda Allah bai Kai ka ba.
Banda wulakanta mutum da kowacce irin halitta, banda kwadayi don yana janyowa mutum wulakanci da kaskanci, kayi imanin komi ya same ka cikin rayuwarka rubutacce ne daga Allah, wani ko wata, mutum da aljan basu isa suyi maka abinda ba Allah ya rubuto zai faru dakai cikin *Lauhul Mahfuz* ba.
Ka riki gaskiya duk inda ka tsinci kanka cikin kowanne yanayi, Ina gargadinka daka rike addininka hannu biyu, ko da Allah zai daukaka nan gaba ta azurtaka karka butulce masa son duniya ya shagaltar dakai bauta masa gwargwadon iyawarka...
Ka rike mutumin daya taimakeka da hannu biyu, ko da ace baiyi maka komi ba kaunar daya nuna maka ta isa domin duk Wanda ya kaunaceka irin haka, ba don wani Abu naka ba sai domin Allah ya gama maka komi, karka sake samun duniya ma'ana dukiya ta hadaka dashi, Kar ka zame masa mutum mugun icce.

Da wadannan nasihohi masu mugun shiga jiki Abdul-Haseeb da mahaifiyarsa suka yi na'am da Alh. Muhd.
Shi kuma can ya kosa yaron ya dawo yaji ta bakinsa domin har ya nemi alfarmar gwamna cewan yana da d'a idan mai girma gwamna zai tura hazikan dalibai karatu kasashen waje a saka sunansa.

Gwamna ya amsa da alkawarin idan lokaci yayi nan da watanni uku zai sanar dashi.

Lokacin da Abdul Haseeb ya koma gidan Alh Haseeb kansa ya daure, an nuna masa ya riga ya zama dan gida, kowa sai ji dashi yake kamar daman a gidan yake tafiya yayi ya dawo, hidimomi salamu Alaikum.
Kaltume da maigidanta musamman Abdul Haseeb ya kaisu yi masa godiya shi da iyalinsa.

Kafin watanni ukun Alh Muhd yaja Haseeb a jikinsa sosai ya Kuma bashi labarinsa tas, shima yace ya taso cikin wahala sakamakon iyayensa sun rasu tun Yana karami amma daga dangin uwa har na uba aka rasa Mai daukar nauyin karatunsa, nan ya shiga neman abinda zai hucewa kansa takaici, ya fara da yiwa wani attajiri kiwon doki, ya kanje ya yanko ciyawa ya share turkensa ya kula da dawakin ana biyansa, daga nan ya koma sayar da sigari, da goro, minti ashana da sauran tarkacce a tire a tashar mota, daga nan Allsh ta tarfawa garinsa nono,ya kafa dan tebur daga nan sai shagon kayan masarufi, daga nan Allah ya daga shi sannu-sannu ya fara kwangila tareda taimakon Allah, Ubangiji ya daga har ya Kai matsayin da yake ciki yanzun.
Ya auri mata uku bai Sami haihuwa da wuri ba, da ya samun sai Allah ya azurta shi da diya Mata.
Alkawarin da yayi suna gama sakandire zai aurad dasu, Amma duk ranar da Allah ya bashi d'a namiji sai inda karfinsa ya kare.. Zuwaira ce diyarsa ta biyu, Mai bala'in kama dashi saboda hakane yake sonta kwarai da gaske, irin son da ya janyo mata sangarcewar.
A lokacin da ya hadu da Haseeb duk suna makaranta, Zuwaira na aji uku kacal.

Duk wani takalihunsa ya koma hannun Alh Muhd, duk da haka bai saki jiki ya daina buga-bugan sa ba. A hankali ya fara koyon hanyoyin kasuwanci ya rinka aiwatar da abinda ya saukaka a garesa.
Yayin da gwamnatin jihar Kanota dauki nauyin fitarsu zuwa kasar *Neatherlands* domin zama kwararren likita.
Abdul Haseeb ya zama *Neurologist* ya zamewa uwa da uba dashi kansa Alh Muhd din d'a daya tamkar goma, ya cika dan halas domin matukar girmamawar da yake masa yasa koda yai masa tayin auren diyarsa Zuwaira bai musa ba duk da Yana ji da ganin irin gurbatacciyar tarbiyyarta.

Wajen hidimar auren Alhajin yaso daukar nauyin hidimar komi, Abdul Haseeb yaki yarda yace hakkinsa ne ya dau nauyin iyalinsa.

Tunda Allah ya azurta shi yake dawainiyya da iyaye, 'yanuwa dana matarsa. Da Allah ya tashi ikonsa ya aikowa Mal Junaid hadarin motar da yai sanadin dakushewan kwakwalwa, bai iya tuna kowa da komi, hatta mata da 'ya'yan cikinsa.
Asibitin Murtala aka kwantar dashi lokacin bai bude nasa ba.

Duk da haka shi ya dau nauyin hidimar komi Wanda yasa matar uban kuka da hawayenta sharaf -sharaf tana roko gafarar Kaltume da danta, Wai Ashe tun kafin ta auri Mal Junaid tayi asirin farraqa shi da mahaifin gudun Wai kar tazo ta haihu ya nunawa Haseeb fifiko (Kunji wani rashin tunanin) to ta cimma burinta amma ta dawo tana dana sani wace a baya takan tsaya inji hausawa.
Shin mu mata bama tunanin cewan duk yaron da aka tsana cikin gidansu Allah na iya daukaka shi ba? Shin bamu tunanin tunda bamu muka halicci mutum ba bama iya tsarawa wance ko wane abinda zasu zama a rayuwa? Allah ya kiyashemu aikata aikin dana sani, domin da mutane sun san hassada takin arziki ga Wanda ake yiwa da ba ka yi ba.
Ta roki Kaltume da danta gafara sun yafe mata to shu mijinta data ha'inta yake kwance bai san inda yake ba fa, wanda ya rasu kwanaki uku da yin hatsarin, wata shari'ar sai gobe kiyama.

Bayan rasuwar mahaifinsa ya dauki nauyin kulawa da dukkan hidimomin kanninsa da uwarsu. Bayan an raba musu gado ya budewa kowannansu shago a kasuwa saboda sun nuna sunfi son kasuwanci ba karatu ba balle aikin gwamnati, ko da aurensu yazo ma shi ke kan gaba wajen basu gudumuwarsa, uwarsu sai godiya take tunda ta dawo hanya ta tuba Allah ya sahale mata bakin cikinta kullum cikin istigfari, tsakaninta da Haseeb sai san barka.

Mahaifinsu ya rasu da shekara guda tal Allsh yaiwa mijin mahaifiyarsa rasuwa, Haseeb yayi babban rashi yai kukan rashinsa, a dalili da duk fadin duniya su hudu kawai ke zaunar dashi su fada masa gaskiya, daga mahaifiyarsa sai shi sai Alh. Muhd sai kuwa abokin mahaifinsa daya saba dashi tun Yana zuwa daukar karatun allo, to ko da ya girma bai yada malaminsa ba
Bayan ta gama takaba ne ya saya mata gida a Yakasai da yake daman gidan Mal. Sunusi na tarayya ne, shekara na zagayowa ya kaita ta sauke faralli, ta dawo ta bata jali tunda ta nace sai tayi sana'a.

Dr Haseeb Junaid ya saki wata doguwar ajiyar zuciya, ko me yasa brain dinsa tariyo masa abinda ya wuce oho don wasu tuni ya fara mantawa sai fa yau. Tunaninsa ya koma Kan yadda ya rike kaninsa da suke ciki daya, ko girmamawar da suke masa ya isa yai hidimta musu cikin kowanne hali in ya ture batun shakuwar da yayi dasu kenan, su Hayatu na kaunarsa fiye da zatonsa musamman marigayi Rabi'u, ya tuna yanayin aurensa da ya taso a gurguje haka ma haihuwar ashe ba dadewa zaiyi a duniya ba
A kullum ya tuna wasiyyarsa garesa inda ya bashi amanar Rahima da Abdul ransa kan dugunzuma ya bacu ya rasa me ke masa dadi a sararin duniya, to sai gashi wai shine da Shirin auren matarsa, babu irin tunanin da bai yi ba kan issue din but tabbas akwai Shirin da Allah cikin al'amarin, yes da akwau hukuncin Malikal Mulk don haka gara ya cire komi a zuciyarsa ya rungumi kaddara.

Shigowarsa biyu kenan yana ganinsa cikin zurfin tunani don bai ko san ya shigon ba sai a na uku ya sallama ya fada falon, ya amsa yaga kamar Daktan na share hawaye tunda ya cire glass dinsa, yai kamar bai gani ba ya mika masa hannu suka gaisa."Ka dade kana jira ko afwaan." Cewar surukinsa.

Ya manna dark glasses din a fuskarsa tukunna kafin yayi dan murmushi "Ai ban wani dade ba Alhaji". Ya mayar masa.

Sanin miskilancinsa da rashin son yawan magana yasa Alhajin baiyi masa shishshigi bai tambayarsa sai abinda yaso fada masa da bakinsa, ganin halinda yake ciki na damuwa ma baisa ya nemi jin ko menene ba har suka yu 'yar hirarsu, zuwa can Alhajin yace "Wai Ina Zuwaira ne tazo ta zubar da yara daga zanje un dawo yau kwana biyu kenan bata ba labarinta?"

Ya amsa "Tana can suna hidimar bukin wata kawarta ce, nasan ko zata waiwayesu sai an kare komi."

Uban yaja tsaki "Watau ita dai ba zata daina halinta ba ko? Amma ban zargin kowa sai kaina Dana shagwabata, na manta cewan diya mace ce komin dadewa aure zata yi, nasan da wani take aure da tuni ta sako min it's, an taba mace na sanin ya kamata ba kamun Kai?"

Haseeb yace "Allah ya kyauta a ci gaba da yi Mata adduar shiriya don tayi nisa Alhaji."
Ya nisa "Wallahi tuni na fahimta wace bata damu da yayan cikinta ba ma? Wallahi ko jiya Saida muka yi maganar nan da uwarta, duk dai kuskuren ne, gata ko cuta? Shawarar dana yanke idan ka gaji da halinta ka sakota ko Allah zaisa tayi hankali karta gurbata maka tarbiyyar yaranka."

Haseeb ya sunkuyar da Kai "Allah ya tsare, tsakanina da ita babu saki unless haka Allah ya rubuto Mana Ina Nan Ina Mata addua."

Alhaji ya girgiza Kai "Duba Nan Dakta wallahi kasan rantsuwar musulmi kenan ko? Idan kaga ba zaka iya zama sa ita ba ka sauwake mata ka huta, nuna haifeta nasan halinta sarai don haka na baka izni, kar kaji nauyin komi Kar Kuma kayi tunanin yadda muke da Kai, tsakaninmu da ban hulda da matarka daban, ni ba zanso ace ka zauna da ita tana cutar ka kana hakuri sabida ni ba, nima na fara gajiya da halinta, uwarta ma tayi fushi da ita muddin Kuma ba zata zauna gidan aurenta tabi dokokin Ubangiji ba bani bata."

Ya fara rarrashun tsohon yace "Allah ya huci zuciyarta insha Allah muna fatar ta natsu, may be idan taji zanyi aure."

Alhajin yace "Alhamdulillah kamar ka shiga zuciyata, shawarar da nayi niyyar baka kenan ince ka Kara aure ka huta da wahala wannan yar banzan."

"Don Allah Alhaji ka daina zaginta kayi hakuri, daman abinda na zo shaida maka kenan batun auren amma har ga Allah bani na nema ba, iyayene suka ga ya dace in auri matar marigayi Rabiu, gaskiya da ban amince ba amma daga baya sai Ina ganin watakila auren ya zama sanadiyyar shiriyyar Zuwaira domin yarinyar tasan addinita na yaba da hankalinta kwarai."

"To Masha Allahu haka ake so, Allah yasa ayi damu, yaushe ne daurin auren?"

Ya gyara zama "To ai kune masu neman auren Alhaji shine nazo sanar maka gobe idan Allah ya nuna mana sai ku tafi, nan dai Yakasai inda aka daura auren marigayin, daga nan zan nufi wajen Malam Nuhu ne in sanar dashi shima."

Alhaji yace "Karka damu amma Ina fatar ba za a dau dogon lokaci ba."
Haseeb yace "Nima hakan nike so."

Daga nan ya nufi Sharifai gidan Malamin nasa ya shaida masa halinda ake ciki. Malam yai murna ya shiga yi masa nasihohi musamman kan kwatanta adalci tsakanin matan daman tsoronsa kenan tunda yaga yadda mahaifinsa yaiwa Mahaifiyarsa.
Malam ya Kara masa da shawarwari da adduoin fatar alkhairi da neman jagorancin Ubangiji.

Yana Kan hanyarsa ta komawa gida yana mamakin irin na'am da farin cikin da kowa keyi Kan wannan auren, zuciyarsa ta Kara karfi, nan bisa hanya ta fara tsara yadda yake son a tafiyar da sha'anin amma har sai ya isa gida yaji ta bakin Zuwaira da ita kanta yarinyar da akeyi dominta.
10/09/2020, 06:02 - Anty saliha: ...RAHIMA..doc by Jami

23

Karfe goma sha daya na dare ya isa gida amma har zuwa lokacin Zuwaira bata koma ba, ya tube ya shiga wanka ya fito ya hada ruwan shayi tukunna kafin ya zauna kallon tv
Sai sha biyu saura na dare yaji maigadi na bude mata gate din gida ta shigo da motarta.
Ko da ta shigo falon bata lura yana kwance bisa settee ba, tana tafe tana 'yan wake-wakenta, sai wani irin kamshin turare Mai shegen haea Kai take, har zata wuce bedroom ta gansa taja ta tsaya masa kerere bisa Kai "Oh ashe ka dawo ban lura da motarka ba."

Ance tankawa yabawa biyan bashin matsiyaci, bai ce Mata uffan ba, ta fasa shiga ciki ta dawi ta zauna kusa dashi ta fara kame-kame, kusan minti biyar tana ta surutu ba tareda ya tanka ba ta gaji tayi shuru.
Ya kalli matar da suka shafe shekaru fiye da takwas da aure Amma m har zuwa lokacin Nan bai San dadin auren ba, bai San me zai karas ba, ya kanji dai abokansa na hirar hidimar da matayensu keyi musu.

Ya sake kallonta ya rasa me zaice Mata, to bata jin wa'azi, in anyi mata fada ta tashi tana masifa tace an tsaneta, idan aka rarrasheta ta zake har tafi da don haka ya zabi yin biris da ita kawai yafi masa alkhairi ya ci gaba da yi mata addua

Da taga yaki ce mata komi ta mike zata shige ciki harda sakin dogon tsaki...
Takaici ya kamashi kawai ya sakin mata bom "Zuwaira Ina sanar dake Zan Kara aure."


Tayi wani irin juyi gaba daya, hankalinta ya dawo garesa sosai taga Yana kwance lakadan kamar bashi ya furta Mata wadannan kalaman masu dacin gaske ba, ta buga kirji "Aure! Aure fa kace??
Ya amsa "Kwarai ba kince gara inyi ba zai fi Miki nono fari?"

Ta sake buga kirji "Ni din wace sakaryar macece zata ce da mijinta ya kawo Mata kishiya?".
" Sai ke Kuma shawarar taki na dauka."

Amsarsa ya sake tunzurata "Oh ashe zargina ya Zan gaskiya da wace ka aje a waje that's why kake wulakanta ni kana nuna min halin ko in kula."

Yace "Ni ban wulakanta ki ba, ban Kuma ajiye kowacce mace a waje ba don Ni ba fasiki bane."
Tayi tafi " Abokiyar yin naka dai zaka auro a tahi a cakuda min 'ya'ya da shegu."

Ya tashi daga kwance da yaji zata wuce gona da iri yace "Kinga karki batawa yarinyar mutane suna, ba wata daban da baki sani ba Zan aura, ai kinsan Rahima maman Abdul ko,Allah yai nufin ita Zan aura "


Taji dum amma hakan bai hanata yin shewa ba "Ahayye girma ya Fadi, su Yaya babba anji kunya, to daman kace ka gani ka kyasa tuni ba damar yi masa snatching ne da ransa, yo Ashe duk shan mur da kau da Kai na munafunci ne ana so ana kaiwa kasuwa, to me yasa tun farko bka aureta ka barshi ta aureta. Gaske naga danta ya zama dan lelenka sabida son uwa ke sa na d"a. Amma wallahi ka ban mamaki ka bani kunya, ka rasa matar da zaka aura sai matar kaninka Haseeb, wannan abun kunya dame ye kama?"

Maimakon yaji haushin magsnganunta dariya suka bashi yace "Zuwaira wane irin kunya Kan abinda addininmu ya halasta bayan kinsan ance babu kunya a addini? Abinda ya halasta ne mu mutane muke haramtawa kanmu sabida jahilci, to in ba tsintsar jahilci ba Ubangiji ya halasta abu Kai bawa ka kawo al'ada da wasu shirme ka gindaya? So ki fahimci akwai aure tsakanin wa da matar kaninsa idan ya rasu za Kuma ayi shine na sanar dake don shi Alhajinku ma rokona yayi ayi da wuri Kar a dauki lokaci, to na bi shawararsa sai kije kiyi tunanin me kike bukata inyi miki ma fadar kishiya?

Ta tabe baki "Idan duk jikina kunnuwane ba Zan taba yarda cewan Alhajinmu da kanshi zai goyi bayan ka yiwa diyarsa kishiya ba.
"Me zai hana tunda diyar bata neman albarka bata faranta ran iyayenta?"
Ta balla masa harara "Don zaka auro wannan yarinyar ce kake fada min magana?"
Yace "Ke Kika ja yai nisa, and ki bar tunani cewan yarinya karama zan auro shekaru nawa kika bata?"

Ta gatsina hanci "Yo Ashe ma tsohuwa ce kake wannan rawar jikin da dimirgishi Wai dafa kauri ba da."

"Nima ai tsohon ne tinda na na Kai 41 yes Kinga za mu yiwa juna daidai kenan."
Ta kallesa ta watsar "Kaji dashi Wai ciwon ajali a Dan yatsa."

Ya dagi ya kalleta "Please shiga ciki ki kwanta kin dameni da surutu sai da safe."

Tayi kwata "Surutu yanzun na bude chapter sai dai Kuma idan dinke bakina za kayi tunda baka da tausayi a zucci ka yanka ka dinke, Kuma gobe gidanmu za ni."

Ya amsa "Allah ya Kai mana rai suma nemanki suke kije kije ki kwaso yaran da kika zube a can tamkar basu da gata."

Yana fadin haka ya gyara kwanciyar sa nan alamun ba zai ma shiga bedroom din ba balle taci gaba da bala'in.

Ta gaji da zama taja jiki ta nufi ciki tana Kun kunai kamar wata yarinya karama.
10/09/2020, 12:29 - Anty saliha: ...RAHIMA..doc by jami

24
Gari na wayewa ko wanka bata yi ba tana idar da sallah ta nufi gidansu, Kai tsaye ta wuce dakin mahaifiyarta, Hajiyar na zaune tana lazumi don al'adarta kenan.

Ta dago taga Zuwaira ce taci gaba da karatunta ba tare da sake kallon inda take ba, ita kuwa ta haye bisa gadon uwar ta kwanta.

Ba a jima ba taji muryar mahaifinta ya shigo yadda yake yi duk safe ya zagaya dakin kowacce mata yaga yadda ta kwana tareda iyalinta yaji ko tana da wata matsala su tattauna hanyar da zasu bullowa al'amarin.
Ya zauna falon uwargidansa Hjy Lami yana jiran ta kare adduointa, Zuwaira taji muryarsa ta taso ta fito ta durkusa ta gaishe shi. Ya kalleta cike da mamaki "Ba dau Zuwaira nike gani yanzun ba, tun yaushe kika shigo gidan Nan?"

Ta sunkuyar da kai tace "Ban dade da shigiwa ba, ina kwana?"

Ya kalli agogon hannunsa yaga ko karfe takwas bata cika ba cikin tsawa yace "Wace irin sakayyar yarinya ce, ki baro gidan mijinki tun sassafe ki zo me zaki dauka?"
Ta marairaice "Karansa na kawo Baba, wallahi duk ya canza, yanzun ma wai aure zai yi, da karya ma har yana cewa ka bashi goyon baya?"

Uwar ta shafa adduarta ta fito ta durkusa gaban mijinta ta gaisheshi ya amsa kana cikin bacin rai yace "Ya akayi kika Kyaleta a zauna har tana kwanciya miki a dak?"

Hjy Lami ta kada Kai "Yadda ka ganta hakan na ganta ko gaisawa ba muyi ba."

Yace "Mutumiyar banza kina nufin kin kwaso kafafunki ne kinzo muyi miki mene, mu hana sa aure? Wallahi Mamana (haka yake kiranta saboda sunan mahaifiyarsa yasa mata) kin ban kunya, ban taba tunanin ba zaki zauna gidan aureki cikin mutunci ba,yarinya kin zama sai kace goyon arna?"

Hjy Lami tace "Ya za ayi mijinki ya kalleki da mutunci bayan kin zama tamkar maras mafadi?"

Ta saka kuka "Wallahi Mama Haseeb kazafi yake mini."

Alh Muhd ya sake daka mata tsawa "Rufa min baki ko in tashi in tattakaki, wallahi muddin baki canza dabi''unki ba daga yau mun sa kafar wando daya ni dake, bar ganin na sake miki ina ksunarki, zata koma kiyayya tsakaninmu Kuma kin sanni sarai kamar yunwar cikinki, wallahi ko ke kadai na haifa ina iya yafeki har abada don banga amfaninki ba."

Hjy Lami ta kalleta cikin bacin rai tace "Dubeki yarinyarki dake kin bata rayuwarki da kanki ga kinan duk kin jeme kin lalace, Kuma da kike cewa kazafi likitan ke miki su mutanen duniya da kike mu'amala da kawayen banzan da kike hulda dasu duk kazafin ne? Duk inda kika shiga ana ga 'yar wance da wane."


Alh Muhd yace "Dalili kenan da muka bashi goyon bayan ya auro mai mutunci tunda ke kin zubar da naki, idan kinga ba Zaki iya zama dashi ba ga hanya nan bude to banga amfanin zama da igigiyar aurensa a kanki ba, sai kije kiji da zunubi daya."

Uwar ta fashe sa kuka "Alhaji kalli yarinyar nan ka gani ba abinda ta sawa gaba sai burin duniya da kyale-kyale, dan rayuwar da take takaitatta. Wai don Allah wane irin gata ne ba a nuna miki ba? Me kika nema kika rasa a gidanku ko na mijinki? Allah ya hore dukiyar da ake taimakawa wasu ma, to me kike nema ne?"


Maimakon ta nuna alamun nadama sai ta dauko wani zancen da bai danganci fadar da ake Mata "Mama ni gaskiya ba Zan zauna da kishiya ba, kishiyar ma yarinyar data san sirrina, bayan duk wata takama da Haseeb ke yi da wani ji da kai, mahaifina ne silar duk abinda ya samu, duk abinda yake takama dashi Kai dinnan Baba kaine sanadin, ko yana nufin anci moriyar ganga ne za a yarda kaurenta, to gaskiya Baba da sake...

Bata ga mikewarsa ba, ji tayi kawai an dauketa da tafi ta kifa kasa, ya bita ya taka yana zagi, uwar ma ta rufeta da duka, Nan ta fara kwarma ihu sauran matan gidan suka taru don cetonta..
Da kyar da rarrashi aka kwaceta, ko kafin ayi haka fuska ta kumbura jiki ya murzu da duka.


Alh Muhd ya fara haki, jiri ya kwashe shi, matan suka tareshi, akayi hanzarin dauko masa maganin hawan jininsa aka bashi yasha kana suka kamashi ya koma daki ya kwanta.

Hjy Lami ta dawo dakinta ta cimma 'yar nata kuka tace "Ya jikin Baban?"
Ta kalleta ta watsar "Tashi ki bace min da gani, ina ruwanki da jikinsa? Ai kinsan yanada hawan jinin don kece sanadi, to ki dage ki zama kece ajalinsa."
Ta Kara fashewa da kuka "Don Allah Mama ku yafe min, Allah zan daina komi, bacin raine yasa
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment