Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

amshi abinmu ne idan zata sake aure to tunda ba alamun hakan gara mu karbeshi kawai."

Ta zaro ido " Zaka tayar mata da hankali, da wanne zata ji, yaron nan shi take gani tana jin sanyi, idan an nuna mata fun karfi a kansa zaku dau hakkin yarinyar Nan."

Ya bata fuska "Ai munyi mata Kara Hajiya, Ni ke, 'yanuwanta ita kanta da sauran jamaa sun san haka sai dai in za aki gaskiya."
Ta daga masa hannu "Naji, naji meye hujjarka na son amsar sa?"

Ya gyara zama "Hujjata ya dawo cikin 'yanuwansa ya zauna gaba days ba a rinka yawo da hankalinsa ba, Kuma ke da kike wannan magana da zaran ita iwar tasa ta sami miji ba dawo mana dashi za a ayi ba?"

Ta dade Bata ce dashi komi ba zuwa can tace "Hakane na amince da batunka amma Ina ganin da abinda za ayi a magance wannan matsalar ta bangarenmu da na uwar yaron saurara:

Ni a hakikanin gaskiya tunda Allah ya amshi ran danuwanka nike tunanin baka shawarar auren Rahima....

Bai bari ta karisa bs ya buga kirji ya zabura kamar zai tashi tsaye ya koma ya tsugunna jikinsa ba inda baya rawa, ya kama kansa da hannu biyu ya rinka jinjina maganar a ransa, nan take idanunsa suka rikide suka canza launi maimakon farare sol, ya bude baki yai magana kalmar ta kasa fitowa ya koma ya zauna yaraf saboda matukar sanyin da jikinsa yayi sai kace Wanda ya kwana ya yini Yana aikin wahala ba ci ba Sha.
Ta dauki tsawon lokaci kafin ta kallesa da kyau tace "Maganar da nai maka na auren ne ya firgita ka har ka fita hayyacinka?"

Yaja dogon numfashi ya saki ajiyar zuciya, sannan ya dago Kai a hankali ya kalli mahaifiyarta yace "Hajiya idan ma auren zan kara in rasa wace zan aura sai matar kanina da ya rasu, ki tuna yadda muke dashi fa, idan anyi hakan ba a kyauta ba."

Ta danyi murmushi saboda tayi niyyar hada auren nan ikon Allah ne kadai zai hana yuwwarsa. Tace "Ni kuwa a nawa tunanin yadda kuke da danuwan naka ne zaisa ka amince a kulla wannan abu don kaji dadin rike amanar da ya damka maka?"
Ya girgiza Kai "Kayya ba sai na kaiga hakan ba duk inda take zanyi kokarin taimaka mata gwargwadon zarafina, yaro kuwa dama namu duk da haka ba Zan tauye mata hakkinta matsayinta na uwa ba dole zamu bata damar kulawa da al'amuran danta a duk lokacin da bukata ta taso."


Hjy tasha mur "To ka ga ni shawarar dana yanke kenan kaje kayi nazari, na baka sati guda kacal bayan haka ka taho ka fada min abinda ka yankewa zuciyarka, yi ko tsallake maganata?"

Da jin zancenta yasan ba zata kara saurarensa ba,bai hana ya durkusa yana rokonta Allah da Annabinsa ta bar wannan batun da baida ko dadin ji.
. Tace " Ka daina yi min magiya, Wai ma tsaya tunda ka girms kasan ciwon kanka na taba tursasaka kayi min abinda nike so ko kuwa na taba baka shawarar da ba kaga amfaninta a rayuwarka ba?
Yace "Ah ah!
Tace "To kaje ka dawo bayan sati guda Ina saurarenka, na riga na gama maganata."

Yayi shiruuu ya rasa me zai sake ce Mata in har zata sauraresa kenan, yafi kowa sanin halin mahaifiyarsa kaifi daya ce ita, idan ta tsaya akan abu babu daga kafar ba ja da baya don haka Kar ma yace zai sake bata baki, ta riga ta kudurtawa ranta sai abinda Allah yayi kenan.
05/09/2020, 12:14 - Anty saliha: ...RAHIMA...doc by jami

14

Hjy Kaltume bata tsaya nan ba, aikawa tayi makarantar da Rahima ke koyarwa tace direba ya daukota yace tana nemanta.
Ba a jima ba ya hangeta ta fito tare da wasu malaman bayan an tashi, ya tareta ya durkusa ya gaisheta ta kallesa cikin mamaki "Bala lafiya?"
Ya amsa "Lafiya kalau Hajiyar ce ke nemanki da gaggawa."

Alamun damuwa ya bayyana a fuskarta, kace kuma lfy? Bata taba min haka ba ka tabbata ba matsala Bala?"
Yace "A sanina ba komi."
To shikenan mu hanzarta Amma sai mun tsaya in shiga gida in Fadi Kar Umma taga ban dawo da wuri ba su damu.".
Yace "Ai tun hanyata ta zuwa na shiga na fadowa Umman uzurun Hajiyar kamar yadda ta umurceni."

Jikinta dai yai sanyi, ta shiga sake-saken zucci har suka isa. Ta shiga cikin gidan da sassarfa, ta isko Hajiyar a tsakar gida tana alwala, ta saki ajiyar zuciya don a zatonta ko rashin lafiya ce, Hajiyar taga alamun a firgice take, ta danyi dariya tace "Maraba lale Rahima, yi hakuri 'yan nan ban so firgita ki ba, zo ga buta kiyi alwala."
Saboda jin nauyinta tace "Na riga nayi, a zahiri kuwa tana period.
Kai tsaye ta shige dakin, Hajiyar ta miko mata kulolun abinci tace "Ci abinci kafin inyi Sallah."

Ta zuba abincin amma ta kasa cin ko loma guda sabida tsananin tunani.

Ta kosa ta kare adduoin da take yi bayan idar da Sallah.
Zuwa wani lokaci ta Kai makura kagara da son jin dalilin nemanta, da kyar ta amsa gaisuwar Mairo data shigo daidai lokacin.
Hjy Kaltume ta aje tasbaha bayan shafa adduarta ta juyo tana fuskantar Rahima tare da kallon plate din abinci ta danyi murmushi " Ba ki ci abincin ba lafiya?"
"Na koshi ne.'
"Ko dai kin razana da sakona ne?"
Ta gyada kai "Gaskiya na dan firgita tunda baki taba min irin wannan Kiran ujula ba."
"Karki damu alkhairin."

Rahima tace " Hajiya meke faruwa?"
Hajiya tace "Kafin kiji komi Ina son sanin shin ya kika daukeni lokacin da kike auren marigayi da yanzun?"
Tayi wani da fuska "Hjy ban fahimce ki ba."
Hajiya tace "Abin nufi wane matsayi kika bani a zuciyarki."
Ta saki fuska tace "Baki da wani matsayi a gareni daya wuce na uwa tun a da da Kuma yanzun saboda kin rike tamkar 'yar da kika haifa a cikinki, baki taba nuna min rashin kauna ko na dakika guda ba, akwai lokutta da dama dana kan tuna korafin marigayi kan cewa kamar kin fi sona dashi, na kance don baki da diya mace ce shiyasa kike kaunata amma a zahiri kishin yadda muka shaku yake."

Hajiya tace "Alhamdulillah naji dadin wadannan kalamai, Ina so ki sani har gobe ina kaunarki Rahima, kauna fisabilillah irin Wanda Allah ke dasawa mutum, halayenki suka karfafa kaunarki a zuciyata. Itace Kuma tasa nayi tunanin sama miki miji Wanda banyi hakan ba Saida nayi nazari sosai na tabbatar idan Allah ya hada zuciyoyinku anyi auren nan zaku dace da juna matuka.

Rahima tayi wani irin gingirin tace " Miji Hajiya? Gaskiya ban shirya sake aure yanzu ba don ban samu Wanda ya kwanta min a rai kamar Rabiu."
Hajiya Kaltume tace "Na fahimci haka, wanda na sama miki zai kwanta miki a rai ne idan kuka shaku da juna, ina tabbatar miki zaku sami ingantacciyar rayuwar auren da zai ba kowa sha'awa. Nasan haka ne kuwa saboda sanin halayyanku kusan daya ne, na lakanci ke yarinyace data san ya kamata, kinsan girman na gaba, kina da hakuri da juriya da dauriyyar kowacce irin matsala ta taso miki, kinada tawali'u , kinsan yadda ya dace ki zauna da wanda ke matsayin mijinki cikin ladabi da biyayya, kin iya mutunta mutum cikin kowanne yanayi, kinada tausayi da jin maganar na gaba dake koda abinda zai gaya miki bai miki dadi ba. Rahima ke yarinyace mai yawan ibada, rayuwar duniya bata shagaltar dake barin bautar Ubangijinki ba, kina daure rashi, kiyi farin cikin samu komin kankantarsa, kinada yasan kyauta ba irinta almubazzaranci ba, da wuya inji kin Fadi karya komi rashin gaskiyarki, a yayinda gaskiyar ta zama Miki abin Fadi duk runtsin da kika shiga, baki da kyashi balle hassada ko munafunci. Kin zauna da mijinki damu tsakani da Allah.. Wadannan halayye naki sunzo daidai da namijin da nike so ki aura Rahima, zan iya cewa ma wasu abubuwan sunfi naki inganta kasancewarsa namiji, Kuma ya dandani wahalhalun rayuwa fiye dake amma duk da haka bai gaza ba."

Rahima tayi kasake, gaskiya tayi mata yawa, ba shakka Hajiya ta santa tamkar tafin hannunta, lalle ta lakanceta tsaf fiye da yadda ta lakanci kanta, idan kuwa haka halin mutumin yake lalle ta samu abokin rayuwar aure irin Wanda take mafarkin samu tun tasowarta zata Kuma iya zama dashi saboda halayyensa ko bata son sa...

Tunanin So da tayi yasa ta juya ta kalli Hajiyar dake kallonta, tayi saurin dukar da Kai kass tace "Hajiya naji bayaninki Kuma nagode sai dai abin tunani, ya ayi kisan shi din Yana son wannan auren hadi yadda kike so?"

Tace "Amincewarki kawai nake jira, Ina son ji daga bakinki kin amimce da shi ko Yaya?"

Ta Kara sunkuyar da Kai tace "Amincewarki dashi shine nawa Hajiya don nayi imani ba zaki sani hanyar da zan wahala ko yin dana sani ba."

Hajiya tace "Alhamdulillah kamar yadda amincewata ya zama naki shima din amincewata shine nasa, Amma kafin a fara wanzar da komi kije kiyi nafila ki karanta istikhara ki roki Allah zabinsa Kan al'amarin kamar na kwanaki bakwai, idan kin gama sai inji daga gareki. Nima zan tayaku, Allah ya taimakemu, ameen."
Rahima tace "Wai a Nan garin yake ko danuwanki ne da ban sani ba?"
Ta boye murmushinta " Me kike ci na baka na zuba, zaki San ko waye, karewa ma muna fatar kuyi zaman aure tare, kije dai bayan sati dayan zamu fahimci komi da yardar Allah."
05/09/2020, 22:21 - Anty saliha: ...RAHIMA..doc by jami

15
Ta koma gida cike da mamakin Hajiyar, ta zayyanewa Umma dukkan yadda suka yi, Habiba tace "To Allah ya yaji shemu alkhairi ai zaman ya isa haka, muma za muyi adduar, Baffanku ma zaiji dadin labarin nan don da yadda zaiyi da tuni ya aurad dake ga duk wanda ya dace...


Kwanaki hudu bayan maganarsu da Hjy Kaltume ta fara sakankancewa sa ikon Allah, Al-Hakeem gwanin hikima da basira. Bayan adduoin data dukufa yi haka kawai take jin wani irin dadi da nishadi a ranta, zuciyarta ta fara kamuwa da kaunar mutumin da labarinsa kawai taji, ko sunansa Bata m sani ba abinda ta manta ta tambayi Hjyr kenan. Shin wanene wannan mutumin da kaunarsa ke neman mamaye mata ilahirin zuciyarta tun kafin suyi ido biyu dashi? Shin wanene mutumin da yake da kwatankwacin halayenta? Wanene wannan mutumin da take rokon Allah dare da Rana cewan ta hadata da irinsa tun tana budurwa? Shun wane irin gwagwarmarya ratuwa ya fuskanta da yasa Hjy ke jinjinawa?

Tun kafin ta gansa tausayunsa ya cikata har taji ta matsu ta kosa ta gansa ko hankalinta ya kwanta."

Umman tasu ta sade tsaye tana magana bata ji ba har Saida ta buga kofar dakin da karfi tayi firgigit ta dago Kai...
"Meke damunki haka na dade tsaye Ina magana baki san Ina yi ba?"..

Ta tashi zaune "Umma tunanine kawai ya isheni....
"Kiyi taka tsan-tsan da tunane-tunane nan Rahima, yaro dai ya riga ya rasu, kafin shi maza nawa suka rasu suka nar matansu, ki sahalwa kanki kici gaba da duain Allah ta tabbatar mana da wannan da Hjy tayi batun,itama fa kenan data haifesa ta dangana har itace ke kawo miki wani mijin, don me ba Zaki hakura ba, ko sai kin jawowa kanki wata cutar?"...
Ta mike tsaf tace "Umma naji na daina, bari in shirya inje gidan Maryam, idan kunji shiru can Zan kwana "..
Umma tace "Shine nazo in tambayeki zaki biya ki dauki Abdul ne ku tafi tare?"
Ta girgiza Kai " A kyalesa can Unma, damunmu za suyi idan suka hadu da Walida..
"Kuma fa gara ya saba da zaman can din ku rinka nesa da juna Kar ayi aurenku ya ishenmu da rigima."
Ta kalleta "Kaji Umma da wani zance, sai kace an sa ranar auren daga magana, bamu ko San juna ba fa, idan muka hadu abin bai yuwwu ba fa?"
Tace "Ai Ni Ina ji a jikina wannan auren an gama daura shi da iznin Ubangiji.".
Haka kawai taji sanyi a ranta ko meyasa oho.. Mhmmm ta suri Jakarta ta saka after dress ta lullubeta kanta suka yi sallama ta nufi gidan 'yaruwa...

Bata sami damar ba 'yaruwar nata labarin labarin dake cinta ba saboda ta taras da gidan nasu a hargitse, itada Uwargidanta basa ko ga maciji, karin abin haushi harda raba Kan 'ya'yansu kowa harkarta take da diyanta. Ran Rahima ya baci,hankalinta yai matukar tashi, bata saurari Maryam don ita ta dorawa lefin abubuwan dake faruwa.
Maryam tace "Banyi tsammanin zaki ki fahimta ta ba Rahima, ki duba irin bautar dana yiwa matar Nan da yayanta tun zuwana gidannan tun kafin in haihu na kula da yaranta, Ina bata girmanta, yanzu kuwa na gaji don shiru ba tsoro bane gudun fitina nike yi, yanzun kuwa ban damu ba aje ayi tayi idan tace kule zance cas! Ba abinda zata nuna min, idan tana takama da miji ne nima dashi nike, idan yarane nima ina dasu to sai me? Haka siddan mace ta isheni ta gallabeni tamkar ita ta aje Ni?
"Hhmmmm inji Rahima "Maryam don Allah numfasa ki saurareni da kyau, ya za ayi ki taho ki taras da mace da mijinta da yara kice zaki nuna mata iko? Mijinta fa kika aure...
"Don na auri mijinta sai me, don ita kadai aka halilto shi ne, mijin mace hudu yake, don me idan ta yayo shararta bata zubewa a kansa sai nawa? To na gaji da rainin wayo, ya isa haka."

Rahima tace "Ban ce bata da irin nata laifin ba don bai yiwwa ace koda yaushe mutum guda ne ke da laifi da duk magana ta tashi, dole ace tanada irin nata problem, kawai so nike ki fahimci bai kamata ki biye mata duk ku haukace koma ince ku kafirce gaba daya ba, haba 'yaruwa a matsayinki na musulma ki tsiri gaba da 'yaruwarki musulma, makwabciyarki Kuma?"

Ta kada Kai "To ya kike son inyi, ita ta fara, sau nawa Ina gaisheta tana shareni tun ina daurewa nace mu zuba mu gani, ko abinci na aika mata bata ci sai ta maido min ta wanke tukunya ta dora wani ta ci, naga bai dau wani mataki ba bayan ya gani da idonsa, nace tunda haka ne bari nima in maida martani tunda ni ba shegiya bace da ubana, ta hana yaranta shigowa dakina balle suyi wasa da yanuwansu, tun Ina damuwa na dake na fara ramuwar gayya Wanda tafi gayyar zafi inji hausawa."

"Kash! Inji Rahima, da baki biye mata ba, me zaisa ki bar shaidan ya samu gurbin gina katangarsa a zuciyarki, don me ba za kiyi aiki da ilmin da Allah ya hore miki ba ki nuna mata abubuwan da take yi tsagwaron jahilici ne?"

Ta tabe baki "Kishi da jahilar mace ko masifa, duk yadda kika so ki fahimtar da ita ba zata taba ganewa ba, kullum inda kika dosa daban inda ta dosa daban, kina gabas tana yamma, to yaushe zan bata lokacina a aikin banza."
Rahima tace "Da kike kiranta jahila ba gara ita dake ba? Laifinta ragagge ne don dama bata da sanin, ke kuwa kin sani kin take sanin laifi biyu kenan, to wai shi maigidan bai san abubuwan dake faruwa cikin gidansa tsakanin iyalinsa ba?"

"Kwarai ya sani Mana, cewa yayi in dominsa muke muje mu kashe kanmu ba ruwansa tunda yai kokarin sulhunta mu Abu ya faskara."

Taja tsaki "You see, ya maisheku mahaukata wadanda basu San ciwon kansu ba, tun anan bai isa ku hankalto ba? Shi da kuke kishin dominsa bai damu ba Wai ma in mutuwa za kuyi ku mutu, eh lalle yace muku haka, in Kun kashe kanku ai bashi kuka yiwa asara ba illa iyaye, 'ya'ya da 'yanuwanku, baida asara Kona miyaun barci iyaka ya auri wasu ya zuba a rufe chapter dinku ku bar 'ya'ya da abun kunya."

Maryam ta juyo "To naji ustaziyar zamani, zanyi nazari in kwatanta in gani, idan da canji in ci gaba, idan babu riba Zan watsar mu ci gaba da zaman doya da manjan don babu macen da zata takani in kyale."

Rahima tace" Allah ya ganar damu baki daya, Kinga da na taho da niyyar kwana amma na fasa don ba zan iya zama gidan da ake gaba ba "

Nan da nan ta marairaice "Don Allah yi hakuri na bari, muyi kwanciyarmu.".
Ta nufi kofa "Ba zan tabbatar da kin bari ba sai munje har dakinta na gaisheta tukunna, mu dawo in baki labarin dalilin zuwana."
Da kyar ta amince suka tafi, suka sallama ta amsa,suka shiga ciki.
Tayi mamakin ganin 'yaruwar kishiyarta da suka shafe sati biyu suna gaba da juna, da ita kanta. Rahima ta gaisheta tamkar bata san me ke faruwa ba ta amsa, suka Dan jima suna kame-kamen magana, zuwa can Nafi'u yaron da Maryam ke goyo ya nufi gaban Tv ta ya dauko wata flower vase na glass, uwar tayi saurin tashi ta amsa ta bubbugeshi.
Hjy Suwaiba ta kalleta "Meye na dukan wannan Dan yaron kinada hankali kuwa?
Ta amsa "Ba kiga barnar da zai yi bane?".
Hjy Suwaiba ta dauki vase din ta sake mikawa yaron "Idan ya fasa naki ne?
Maryam tayi shiru
Rahima tayi murmushi "Nima shi na gani yaro da kayan uwarsa.".
Hjy Suwaiba tace "Kila so take in bar mata danta ko daman Walida ce tawa, ta rike kayan barnarta kin ganshi mummuna."

Maryam ta kalli Rahima "Kinji ta ko? Wallahi tunda aka haifeshi take tsangwamarsa Wai Walida ta fishi kyau ko Ina kyaun da katon hanci oho._
Hajiya Suwaiba tayi dariya " munji ba komu muma da kayan gyara, naki a sa masa 'yankunne da janbaki mu gani."
"Ah ah Hjy gaskiya cun fuskar tayi yawa, ki dai rike taki mu rike namu."
A haka suka ci gaba da wasa da dariya har kusan magriba sannan suka koma dakin Maryam suka yi Sallah. Suna idarwa Hjy Suwaiba ta aiko musu da kulolin abinci wai a kawowa Rahima, da gani abincin yafi karfin ita kadai dole suka ci tare da Maryam din ita ta fasa dora tukunya. Rahima ta kalleta tace " Don Allah da kika shiga dakinta, kikai Mata magana gashi har kinci abincinta me ya rage a jikinki? Inda za a bude Miki file dinki yau kiga dimbin ladan da kika samu da ba zaki yards ki kara yin gaba ba koda wasa."
"Wallahi Kuma Nima sai naji wani irin dadi a Raina, duk kuncin da nike ji a zuciyata ya yaye na yarda sai kaso abu ya dameka yake damunka din."..

Rahima tace abinda har yanzun mu mata bamu gane ba kenan, mu ke creating ma kanmu problems din da zasu dawo su dame mu, namiji ba ruwansa, sai un har kunyi dace da Mai kula ne zai fahimci halinda kuke cikin, wani ko ya gani ba abinda ya damesa tunda yawancinsu sunfi son haka, su tara Mata cikin gida ayita adawa a kansu, ya fito Yana jin dadi da hura hanci ya rinka ikrarin sabida tsananin son da kuke masa kishi ya hanaku zaman lafiya. Wani shaidanin zaman lafiyar ce bai so, yana ganin kun hada kai sai ya kasa sukuni ya shiga zargi da fargaban shifa sai yadda kuka yi dashi kenan domin da wuya daya ta yarda a ci amanar guda shi kuwa bai son hakan, yafi son ya zama bakin ganga, ya buga nan, ya Fadi gaibu can, yai munafunci a nan sai kunada kyakkyawar kula zaku gane in ba haka ba sai kuga kowacce ta fito tana kuri da fankamar ita yafi so.
Idan anyi dace da irin mazan da suka san ciwon kansu sai kiga su zaman lafiyar suke matukar bukata a gidajensu, idan Allah yasa ya dace da matan kwarai sai sai ya kula dasu matuka ya rinka kyautata musu har kiji danginsa na fadin sun mallakeshi sun gama Mana dashi alhalin jin dadin zaman lafiya da kwanciyar hankalin da yake samu dasu ya haifar da hakan. Kin ganni nan Maryam bana shakkar zama da kowacce irin mace Allsh zai hadani da ita matsayin kishiya."

Ta gatsina baki "Karki cika baki Rahima, me kika sani game da zama da kishiya, kowacce mace fa da nata salon munafunci da kisisinar data kware, idan an debe masu shige-shigen gidan bokaye da malamai don wata ba zata zauna dake da bakin hura wuta kadai ayi kishi ba."
Tayi murmushi "Aunty Maryam kenan ai ba wani cika baki, in har hakane Kuma Ina iya ce miki yes na cika baki ne domin nima da nawa baiwar da Allah yai min, ba wani abu bane da ya wuce kakkarfar madogora."


Ta kada Kai "Ko Zan San wane irin madogara ne?"

Ta girgiza Kai "Nima ki bini bashi zuwa nan gaba in har Allah ya kaddareni da auren kiga matsayins zamana a gidan mijin da wajen shi kansa mijin tukunna, yanzun dai muyi sallar isha'i ki bani amsar tambayata ta tuntuni don Ina jin ga wannan karon na fada kogin nan na so da kauna sai dai ko za ku iya tsamo ni?"
05/09/2020, 22:48 - Anty saliha: ..RAHIMA..doc by jami

15
Ta koma gida cike da mamakin Hajiyar, ta zayyanewa Umma dukkan yadda suka yi, Habiba tace "To Allah ya yaji shemu alkhairi ai zaman ya isa haka, muma za muyi adduar, Baffanku ma zaiji dadin labarin nan don da yadda zaiyi da tuni ya aurad dake ga duk wanda ya dace...


Kwanaki hudu bayan maganarsu da Hjy Kaltume ta fara sakankancewa sa ikon Allah, Al-Hakeem gwanin hikima da basira. Bayan adduoin data dukufa yi haka kawai take jin wani irin dadi da nishadi a ranta, zuciyarta ta fara kamuwa da kaunar mutumin da labarinsa kawai taji, ko sunansa Bata m sani ba abinda ta manta ta tambayi Hjyr kenan. Shin wanene wannan mutumin da kaunarsa ke neman mamaye mata ilahirin zuciyarta tun kafin suyi ido biyu dashi? Shin wanene mutumin da yake da kwatankwacin halayenta? Wanene wannan mutumin da take rokon Allah dare da Rana cewan ta hadata da irinsa tun tana budurwa? Shun wane irin gwagwarmarya ratuwa ya fuskanta da yasa Hjy ke jinjinawa?

Tun kafin ta gansa tausayunsa ya cikata har taji ta matsu ta kosa ta gansa ko hankalinta ya kwanta."

Umman tasu ta sade tsaye tana magana bata ji ba har Saida ta buga kofar dakin da karfi tayi firgigit ta dago Kai...
"Meke damunki haka na dade tsaye Ina magana baki san Ina yi ba?"..

Ta tashi zaune "Umma tunanine kawai ya isheni....
"Kiyi taka tsan-tsan da tunane-tunane nan Rahima, yaro dai ya riga ya rasu, kafin shi maza nawa suka rasu suka nar matansu, ki sahalwa kanki kici gaba da duain Allah ta tabbatar mana da wannan da Hjy tayi batun,itama fa kenan data haifesa ta dangana har itace ke kawo miki wani mijin, don me ba Zaki hakura ba, ko sai kin jawowa kanki wata cutar?"...
Ta mike tsaf tace "Umma naji na daina, bari in shirya inje gidan Maryam, idan kunji shiru can Zan kwana "..
Umma tace "Shine nazo in tambayeki zaki biya ki dauki Abdul ne ku tafi tare?"
Ta girgiza Kai " A kyalesa can Unma, damunmu za suyi idan suka hadu da Walida..
"Kuma fa gara ya saba da zaman can din ku rinka nesa da juna Kar ayi aurenku ya ishenmu da rigima."
Ta kalleta "Kaji Umma da wani zance, sai kace an sa ranar auren daga magana, bamu ko San juna ba fa, idan muka hadu abin bai yuwwu ba fa?"
Tace "Ai Ni Ina ji a jikina wannan auren an gama daura shi da iznin Ubangiji.".
Haka kawai taji sanyi a ranta ko meyasa oho.. Mhmmm ta suri Jakarta ta saka after dress ta lullubeta kanta suka yi sallama ta nufi
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment