Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

Alh. Mamman kan shiga su fita suyi wakilcin aurarraki da dama har sau sunga an kulla sunnar Manzon Allah SAW suke numfasawa to Ina ga Kuma ana batun auren diyarsu aka zi yi, 'yar lelensa wace yake ji da ita?

'Yanuwan Rabiu da sukayi tattaki zuwa wajen neman auren sunsha mamakin irin karamcin da akayi musu bayan an karbesu hannu bibbiyu. Sun rabu kan cewan an basu yarinya saura batun sa ranar daurin aure sai abinda 'Yanuwa suka tattauna zasu nemi dangin angon.

Mutunta su day aka yi ya karawa Hasseb kwarin gwiwar aiwatar da abubuwan da suka kamata dangane da auren. Kudi ya ware masu yawan gaske ya baiwa matarsa ta hado kayan lefe setin akwatuna uku dankare da tufafi, kayan shafa, jakunna, takalma da sauran tarkacen da ake hadawa budurwar data hadu Kuma ta dace da Mai yin. Shi kansa Rabi'u akwati guda ya cika masa da tsadaddun shaddodi na shigar angonci kana ya samar masa Dan madaidaicin gidan da zasu zauna amma mahaifiyarsu taki amincewa da hakan, tace tafi son ta zauna tare dasu tunda daga amaryar har angon yarane suna bukatar zama kusa da manya domin tsawartawa lokaci-lokaci.

Dalilin haka yasa Haseeb ya gyarawa kanin nasa dakuna biyu dake saman bene, kicin da toilet a gidan Hajiyar tareda Kara yiwa nata bangaren kwaskwarima duk da ko can ko ina a gyaren yake.

Lokacin da Alh Mamman Mai yadi ya tafi gidan aininhin mahaifin Rahima batun auren bayan ya sanar dashi ko su waye maneman, Mal Ali Mai goro ya nuna masa halacci, din kekasa kasa yayi yaki amincewa ayi maganar dashu ya kare da fadin "Wannan yarinya diyarka ce Alh. halak makak, kana da damar aurar da ita ga duk Wanda ka so, mene nawa a cikin wannan zancen? Babu ruwana, Kuma don Allah duk abinda ya taso karka sake tuntubata, kaida uwarta kun isa ku zartas da hukunci."
Tunda Rahima ta dawo hannunsa sanin kansa ne mahaifinta bai taba nuna masa ba shine ubanta ba, yana yi masa kawaici fiye da yadda ake zato, Yana jin dadin haka, sai dai halaccin da ya nuna masa yau ya tabbatar da Alh. Ali ya cika dattijon da yasan yakamata yasan ciwon kansa. Dadi ya rufesa, zuciyarsa ta Kara zurfafa da kaunar diyar tasa bai san lokacin da ya fara zuba godiya ba...

Alh Ali yace "Ni ke da godiya Alhaji, a yau da zamani ya canza harka sami Mai rike maka d'a tsakani da Allah, ba cuta ba cutarwa, ba wata tsangwama balle banbanci ai sai mutum ya godewa Allah, ya rinka wansa yai masa namijin kokarin nan addua, wallahi ni nakan rasa irun godiyar da zanyi maka ma, Allah dai ya saka da khairan yasa diyan suji kanmu."
Alh. Mamman yace "Ameen Nima nagode, zamu je mu Kara tattauna batun sa ranar buki da uwarta tunda naga dangin yaron tuni sun shirya."
Mal Aliyu yace "Ba laifi Allah ya sanya alkhairi yasa za ayi damu, insha Allahu Nima goben ko jibi Zan tafi Gumel in shaidawa tsohonmu halinda ake ciki, kasan tun fil azal shi ta tayar da rikicin Nan."

Alh Mamman yace "To ya za ayi, duk inda tsoho yake sai lallabawa da lallashi har Allah yasa a rabu lafiya, Ni da nawa tsoffin suka dade da rasuwa har shaawar irinku Nike, yawanci wadanda suka manyanta da iyayensu sai kaga suna musu yadda suka ga dama ko su rinka cewa rigimarsu ta ishesu."
Mal Ali ya nisa "Wani abin da muke ganin rigima ce sai kaga sunada dalilin aikatawa, yanzun shi wannan wa yasan dalilin kafewarsa Kan lalle sai a fiddata makaranta ayi Mata aure? Mu dai har kullum albarkarsu muke nema dole mu bi son zuciyarsu don mu gama lafiya."

Alh. Mamman tace "Hakkun, maganarka dutse, Nima Zan shirya in bika mu tafi in Kai masa goro da hannuna in shaida masa diyata ta samu miji yaro danye sharaf ba irinsa ba."
'Yan dattijan suka bushe da dariya kana suka yi sallama cike da murna.
03/09/2020, 10:52 - Anty saliha: *Afwaan jama'a ga number da zaku turo shaidar payment ayi adding dinku.*

*080 34243456*


....ˆRAHIMA...doc by Jami

5
Habiba ta shiga goda tana rafka sallama tun daga sori amma babu wadda taji har saida ta iso daf da kofar daki. Dukkansu 'yanmatan biyu suka amsa salkamar tare da fadin "Lah Umma yaushe kika shigo?"
Rahima tayi saurin amsar jakar dake hannunta tace "Duk laifin Maryam ce, ta kuntuke da surutu ba wakafi ba aya, balle alamun motsin rai."

Maryam ta zaburo "Amma da alamar motsin tambayar da baki bani amsa ba ko?"
Habiba ta cire hijab tana fadin "Anyi babbar kwabo, ke kenan ki tasa kanwarki gaba kiyi ta tsatstsagarta?"
Cikin shagwaba Rahima tace "Tunda kika fita gidan ta bude faifaina dana Rabiu har kaina na ciwo."
Habiba ta jayo kujera ta zauna kafin tace "Bata ko jin kunya, wannan yaushe zaice dake wata Yaya?"
Rahima tayi mata gwalo ba tareda uwar ta gani ba tace "Nima haka Nike fada mata tuni."
Maryam ta Kai Mata bugu cikin wasa "Ni na rasa irin girman da ake son dora min ba gaira ba dalili alhalin watanni uku kacal fa na bata."

Habiba tace "Sai girman jikin ba, kowa ya hanku zaiyi zaton shekaru uku kika bata ko Ina Zaki Kai wannan jikin oho."

Rahima ta sake fakar idon Ummar tasu tayi mata gwalo kana tace "Aure Umma za ayi mata, yanzun nan take fada min wai Abbas ya matsa mata da zancen aure."
Maryam ta kara zaburowa "Allah Rahima ki kiyayeni, Umma karya take min."

Habiba tasha mur ta kallesu "Eh ba shakka, tabbas Kun cika yan zamani, kiri-kiri Kun zauna batun aurenku kuke ba kunya ba wani shakka, Allah ya shirya Mana,wannan zamanin sai shiru. To ni ince ko Kun dora min sanwa ko kuna can kuna hirar samari?"
"Tun dazun muka Dora Umma." Suka bata amsa tare sannan suka nufi kicin din domin duba girkin, ta bisu da kallo, cikin zuciyarta ta ce inda da gaske shi Abbas din ya shirya ai da an hada bukin ayi rana daya mu huta.

Maigidan ya dawo ya shigo dauke da ledojin kayan lashe-lashe da yakan sayowa yara, su Rahima suka fito da hanzari suka durkusa "Sannu da dawowa Baffa."
Ya amsa Yana Mai farin cikin ganinsu yace "Ina kannin naku ne banji motsin kowa ba."
Maryam ta amsa "Wallahi Baffa suna can sama suna kallo ba suji muryarka bane da tuni sun sauko."
"Bari na kirasu." Cewar Rahima. Ta hau a guje ta shiga ta kashe Tv din tace Sarakunan kallo to Bafda ya dawo yana nemanku idan kunga damar sauka.".

Har da zasu tsaya korafin an hanasu kallo sai suka jiyo muryarsa, sanin lalle da abin lasawan da yake tahowa gida dasu yasa suka rugo kasa suba fadin "Baffa oyo yyo me ka sayo Mana "

Maryam ce ta bude ledan ta shuga rarraba musu youghurt da biscuits, Rahima Kuma ta bude ledan nama ra busde ta rabawa kowa nasa, kafin ta mikawa Maryam tasa hannu cikin na Samunu ta diba yanka biyu ta saka a Baki, yaro ya saka kuka, Rahima ta kalleta "Kash Maryam meye haka?"
Umma ta harareta "Zalunci mana, ba Kya tsaya a baki naki ba gandoki?"
Ta saki dariya "Wallahi miyauna ne ya tsunke Umma.".
Rahima ta ce "Ai nasan maganinta, ta kasa rabin Maryam din biyu ta mikawa kaninsu, Maryam ta taso tace ba zata sabu ba bindiga a ruwa ta juyo zata amshe na Rahimar, ta gudu daki, ta bita Yana dariya.
Iyayen suka bisu da kallo cike da sha'awa da tausayin su.
Alh Mamman yai ajiyar zuciya ya numfasa bayan yasha ruwan da Umma ta kawo masa tare da abinci, Ya kalleta cike da kauna yace "Kinsan abinda ke damuna?"
Ta kada Kai "Sai ka Fadi Alhaji."
Ya gyara murya "Ina jimamin yadda yaran nan zasu rabu da juna ne, sauran kwanaki tara kacal fa bukin Rahima, ya 'yaruwata zata ji?"
Tace "Hhmmm kace ya za ayi da kewar juna dai, Ni kuwa nafi tausayin Rahima na rasa dalili."
Yace "Ai kinsan maraya da shiga zucci dole ki rinka tuno 'yaruwarki yanzun musamman da auren nan ya kawo jiki saukinmu idan Allah ya turowa Maryak nata mijin tayi auren sai hankalunmu yafi kwanciya.

Habiba tace " Da fa masoyinta Alhaji ita taki bashi damar ya fito dama ya riga mijin Rahima magana."
"Ahaf ai ban sani ba da an tuntubesa aji in ya shirya a hada auren 'yan tagwayen naki mu huta.".

"Ka shirya auren 'yan mata biyu lokaci daya a wannan zamanin namu?"
Ya amsa "Yo me zai gagara? Nufa duk shigi da ficin kasuwancin da nike yi dominku ne, rufin asiri alhamdulillah don Allah ke yiwa bawansa, idan har batun auren Maryam ya tabbata naji nata masoyin ya shirya to ba shakka tare za a hadasu ayi sha'anin insha Allahu, a shirye nike, Allah zai rufa mana asiri."
"Kamar inyi guda Alhaji saboda jin dadin maganarka, Allah ya Kara budi ya karemu daga sharrin makiya.".
Ya amsa "Ameen bari in dan kwanta in huta kafin a Kira sallah."
03/09/2020, 10:52 - Anty saliha: *A turo shaidar biyan bank ta wannan Number 08034243456, Nagode*

....RAHIMA..doc by jami

6

A dakin 'yan matan Rahima ce kwance bisa doguwar kujera ita Kuma Maryam na kishingide gefen katifarsu rike da wani littafi mai suna *Tun Ran gini ran zane* Rahimar nata magana Maryam bata kulata har ta gaji ta fisge littafin tace "Wane irin wulakanci ina magana kamar ba dake nike ba?"
Ta juyo "Sai hakuri 'Yaruwa na tsunduma, kinsan yadda karatun littafan nan suke, idan kina yi sai mutum ya rinka ganin abin a zahiri, Kinga Sa'adatun nan ji nike inda nice ita ba zan wulakanta Sagir ba tunda Ina sonsa."
"Maryam sarakunan soyayya inji Rahima, kinsan nayi kokarin kwatanta irin soyayyan abu yaci tura, wallahi ban san yadda ake yinta ba."

Maryam ta tashi zaune tace "Rahima batun naki nayi ne, soyayyar dake tsakaninku da Rabiun fa?"
Ta saki 'yar ajiyar zuciya "In gaskiyar kike so, ban taba jin faduwar gaba don na gansa ba balle ma ace na kidime na rasa sukuni sabida rashin ganinsa, that's why nike ganin kamar hauka kawai kuke keda Abbas, infact zakewarku tayi yawa."
Maryam ta gyara zama "Babu zakewa a sha'anin soyayyarmu, bari inyi Miki misali donki fahimce Ni, kin karanta littafan Aunty Saliha ai, tun daga kan *Wani jinkiri, Zumuncin Zamani da Son Zuciya da wannan din nan, ko yaushe ina kwatanta soyayyarmu tamkar nasu Faruk da Surayya ne har nike ganin haka rayuwar aurenmu zata kasance domin ni din nan na karantu na dau darussa da dama cikin littafan, yadda nike ji daahi hakan yake ji dani, meye aibun mu?"
Rahima tace "Ban ce akwai aibu ba fa ina Miki bayanin duk shakuwar da mukayi da Rabi'u ban taba jin kwatankwacin abubuwan da taurarin littafan Aunty Salihar ke ji ba dangne da mazajen da Allah ya hadasu ba, shine nike tuhumar anya na san so dinma kuwa ko kuwa in tambayeki shin menene so dinnan ne?"

Ta tafa hannu "Allah ya kawo mu, Rahima baki san so ba, duk zancen Rabiun da kike kururuwar iblis ne?"

Ta bude ido ta lumshe tace "Ba shakka da na dauka kyakkyawar hulda da shakuwa irinta abota da mukayi da Rabi'u shine shine son da ake fadi, Saida na yawaita karantun littafan nan naga yadda kuke tafiyar da al'amarin naku soyayyar dole na fara doubting, anya are we right for each other?"

Maryam ta kyalkyace da dariya "Is too late to be having second thought."
Ta buga kirji "Ina! Ba abinda zuciyata ke nufi ba kenan ba, na riga na amince da Rabiu dari bisa dari zan Kuma aureshi insha Allah, duk da cewan bashi cikin tsarin mazajen dana yiwa kaina sha'awar aure amma ya na iya da ikon Allah."
Taja tsuki "Tun farko na rasa dalilin amince masa."
"To da in auri wanda ban sani ba gara wanda muka saba, muka san juna, and with time zan kaunace sa "

Maryam tayi shiru kafin tace "Nasan halinki Rahima kusan ince fiye da zatonki, tun tasowarmu Ina lura dake da dabioinki, ke mace ce miskila, hakan ya haifar miki da rashin son kula kowa sai lokacin da kika bushi iska da kanki, sau nawa samaru ke approaching dinki su kyale ki dole saboda rashin samun fuska daga gareki, da yawansu sunyi min complain, suna sonki amma kinki kulasu har muka kare secondary baki da saurayi, da muka shiga B.U.K ma batun gudane baki canza ba. Na dade ina mamakin yadda kuka lakewa juna keda Rabiun naki, don naga ko wanne namiji bai isheki kallo ba. Shin kinsan Umma ta taba tsareni kan batunki har cewa tayi tana tsoron ko kina tareda wani bakin aljani ne mai saki gudun maza? Don in kwantar mata da hankali ba shiri na bata labarin Rabiu duk da nasan babu alakar soyayya cikin zuciyarki game dashi, mind you ban san abinda ke nasa zuciyar ba."
Cikin tausayin Ummar tasu Rahima tace "Allah satki Ummana, ni kaina wallahi na fara jin tsoron kaina tun bai dameni ba na fara damuwar tunda mace nike Maryam Kuma inada masoyan nan amma ko kusa har zuwa yau dinnan banji Ina son wani ba, infact sai ji nike na tsani duk namijin da zai bude baki yace yana sona."

Maryam ta bude baki "Naso in fahimci hakan amma banyi tsammanin yai nisa haka ba to ko dai gaskiyar Umma ne a fada mata ta tashi tsaye?"
Tayi saurin fadin "Ko kusa ba zan tayar mata da hankali ba ai ina addua gashi Kuma Allah ya amsa tunda ya hadani da Rabi'u kuma har cikin zuciyata na amince dashi matsayin mijina, zanci gaba kuma da adduoin, na sani ko nan gaba soyayyar da za muyi a rayuwarmu ta zarce nasu Surayyar, Kausar, Laila da Saadatun da kike magana?"

Tayi shewa "Abin nayi ne, Allah ya rayamu inga wannan ranar, ni kuwa dana aikawa Aunty Saliha suga yadda mai gudun maza ta shiga cikin kogin soyayya mai wuyar fitar."
Rahima tace "Ni har kin tuna min tambayata baki ban amsa ba, shin meye so?"

Ta daga mata hannu "Ina! You're an amateur in love ba zaki fahimci komi ba saboda baki dandani Zaki, daci da sauran abubuwan data kunsa ba, amma nayi miki alkawarin duk ranar da Allah ya dasa miki wannan baiwa a zuciyarki, kika tsunduma ciki sosai, zan baki amsar, ke dai roki Allah idan zai zo ya taho da sauki don irinku ne masu zakewa kuga tamkar kowa bai iya ba sai ku."

Rahima ta daga hannayenta sama "Ya Allah ka dasa min so cikin zuciyata."
Maryam tace "Ubangiji ya amsa don alkawari yayi babu bawansa da zai daga hannu sama ya rokesa face ya biya masa bukatarsa, sai mu jira lokaci da saukar ijabarsa, kin gani zan shiga wanka, Abbas zai taho anjima."
03/09/2020, 13:41 - Anty saliha: ...ˆRAHIMA..doc by Jami

7
Rabi'u Yakasai ya gama shirinsa tsaf, yau shigar doguwar riga yayi dinkin tazarce ta yadin shadda mai ruwan kasa-kasa, taji guga sai sheki take yi, ya kwafa hula kube kalar kayan, ya feshe jikinsa da sauran turaren da Ya Haseeb ya kawo masa tsaraba wata tafiya da yayi, kamshi ya bude cikin dakinsa dake soron gidansu, ya saka takalmansa cover wadanda tun la'asar ya baiwa shoe shiner kwangilar gugarsu, ya fito ya maida kofarsa ya rufe ya shiga cikin gida wajen Hajiyarsu.
Tana ganinsa ta washe baki tace "Dan auta kenan wannan irin shiga hala wajen diyata zaka?"

Cikin kunya ya durkusa ya gaisheta da yini kana ya amsa "Eh wajen Rahima zani mu karike shirye-shirye, Ya Haseeb yace in kai masa kiyasin abubuwan da suka rage ya bani yasan ya gama da hidimar."

Hajiya tace "Gaskiyane, an gode masa Allah ya Kara budi, kaima ince ko kana yi masa adduar?"
Yace "Duk rana ta Lillahi Hjy, tsakaninmu dashi adduar ce kadai abinyu don ko godiya nayi masa sai yaita fada."
Tace karka fasa don nasan yana jin dadi, tashi ka tafi Kar dare yayi kace Ina gaisheta."

Har ya mike ta tsayar dashi ta bude wata Jakarta ta fiddo sabbin kudi ta mika masa bandur na dubu biyu 'yan naira ishirin tace "Amshi ka Kai mata."

Yasa hannu ya karba Yana tambayar "Ina kika sami sabbin kudi haka?".
"Sai kaji inda suka fito? To kyautar Yayanku ne ya bani Ni Kuma na ajiye maka."
Rabi'u yai tsaye shiru.." Kinga Hajiya ko kusa bai dace ba, ya zai miki alkhairi don ki amfana sai ki bani, gaskiya ba zaiji dadi ba."
Ta hararesa "Kai zaka tafi ka fada masa ko wane, to idan ma baka karba ba Hayatu ya taho ya amsa tunda shi kullum cikin neman karin na cefane yake."

Ya maidasu a aljihu yace "Ah ah Ina so Hajiya, Allah ya saka miki da aljanna madawamiyya."
Ta amsa "Ameen Auta, hanzarta ka gani, sai ka dawo."

Ya fito har zai hau babur dinsa sai shaawar takawa a kasa yazo masa, ya fasa ya bi titi yana takawa daidai, irin tafiyar yaro matashi Mai jini a jika.

A cikin gidansu Rahima tuni ta dade da kimtsawa tana jiran Rabiun, a yau shigar wando da riga suka yi ita da Maryam 'yan Pakistan tsarabar Umrah ne da Baffansu ya kawo musu, duk kalarsu guda watau ruwan hoda da zanen kalar gwaiduwar kwai a jikinsa, banbancinsu kawai na Maryam yafi nata girma tunda ta fita girman jiki. Ita Rahima yarinyace gajera, baka mai dan jiki, ba kyakkyawa ba ce ba Kuma za a kirata mummuna ba, Maryam ta fita kyaun fuska nesa ba kusa ba, ita kuwa halittar jiki Ubangiji ya kyautatata mata. Tana da kyaun siga kwarai da gaske, kirar jikin matan Nan da ake Kira masu kirat kwalbar coca-cola. Duk da ita ba Mai kiba bace Allah yai mata halittar wasu guraye murde a wuyanta, layi-layi uku. So da dama akan kirata mai karuwar jiki kasancewar kowanne irin sutura ta saka su kanyi mata kyau suyi ras a jikinta tamkar dominta aka yi. Bayan wannan ba kowa ke yarda idan an fada masa shekarunta sun kai ashirin ba saboda jikin da fuskar basu nunawa.

Sanin yadda sutura ke amsar jikinta suna fito Mata da shape yasa babu yadda za ayi mutum ya ganta ba tare da after dress ba, ga addini ya ratsata sosai domin Alh. Mamman ba daga baya ba wajen kyautata tarbiyyatr yayansa. Alhamdulillah su Rahima sun gogu da addini sun san hanyayoyin tafiyar da harkokinsu ta yau da kullum musamman tsarin addinin islama, tsakar gidansu kadai mutum zai shiga yaga kalar tufafin da ta saka saboda tsananin bin dokar Ubangiji.

Cikin wannan shiga ta kamala ta fito ciiin natsuwa da kamun Kai ta tarbi maigida to be da harkarta yadda suka saba yiwa juna, suka gaisa a mutunce.

Rabi'u ya isar Mata da sakon Hjajiya. Rahima ta amsa da "Kasan kuwa da kace Hajiya na gaisheni wani irin dadi kan rufe ni, ni shar kenan don wannan alama ce ta dace da sarakuwar kwarai."

Ya gyara hularsa cikon jin dadi "In don Hajiya Kar kiji komi, ta yaba dake fiye da zatona, ke ko matan Ya Hayatu da suke kullum cikin bala'i bata kyamace su ba, ba abinda ke tsakaninsu sai kyautatawa."

Rahima tace "Ta hutawa zuciyarta da masifa, daman har addua nike Kar Allah ya hadani da muguwar sarakuwa mai sa ido da kasa kunni a harkar matan danta don in kaji labarin masifar wata tsohuwar sai auren ya fita ran mutum gaba daya."

Yayi dariya "Banyi tsammanin Hajiya zata kula matar Ya Hasseb ba balle na Ya Hayatu koda ace gida daya suke zaunre balle Allah ya raba zaman, Ya Hasseb na Galadanci, Ya Hayatu na Gwammaja ita tana Yakasai, bata zuwa gidan kowannansu balle ta gano abinda zai tayar Mata da hankali, sune dai duk sati suke Kai matansu su gaisheta, mu kuwa saboda kaunar da take miki ne yasa tace da ita zamu zauna."

Tace "Lalle Dan lelen Hajiya, wai Rabiu daman kana da sauran turaren nan ka daina fesawa na daina jin kamshinsa."

Ya kyalkyace da daruys "Kinsan na gaya miki nima fa Ya Haseeb ya bani, da naga ya kusa karewa ne na boye, ban san kina son shi ba dana kawo miki tuni amma zan adana miki sauran in kinzo in baki."

Tace iye dan gatan Ya... Haka kawai ta tsinci kanta da jin nauyin Yayan Rabiun ta kasa fadin sunansa duk da bata taba ganinsa ba.
. Ya girgiza Kai "Ba zaki ma tabbatar da hakan ba Saida batun aurenmu ya taso, gaskiya Ya Haseeb ya cika danuwa kaunar zumunci da taimakon zumunta kamar yadda Allah yai mana horo muyi. Gaskiya kullum Ina jinjina masa, yana kaunata, yana ji dani matuka, nima bani da kamarsa Rahima."

Ta nisa tace "To Allah ya barku tare Rabiu, Allah ya kaika matsayin da zaka kyautata masa kaima.'
Ya amsa "Ameen, insha Allahu zanyi struggling, bari harkar bukin nan ya kare mu gama karatunmu ki gani da taimakon Allah zamu ba marada kunya."

Tace "Ko shakka babu sai mun ba mutane mamaki.".
"Kar ma dai ace 'Yan B.U.K da suke yada surutan banza, kinji maganganun da suke yi dana Kai musu IV, wasu har karyatawa suka yi."
Taja tsaki "Kai kake kulasu, ai ni banda lokacinsu balle in saurari surutunsu.".

Suna nan tsaye Umma da Maryam suka dawo unguwa, ya durkusa ya gaisheta ta wuce cikin gida, Maryam tana tsokanarsa "Ango kasha Mai, har an fara Shirin angoncine?"
Yai dariya "Ban sanki da haka ba Aunty Maryam, Ina kuka fito da dare Nan?"

Ta amsa "Gandun albasa, kasan can za a Kai amaryar taka rufi wajen Inna kanwar su Umma, Kuma don Allah ka daina kirana wata Aunty sai kaina ya rinka girma."

Rahima tace "Girma ai ya hau kanki Auntyn Rabiu."
Ta harareta "Kina korata ne kawai Kar in bata muku hira, Rabi'u Saida safe, ke Kuma zaki shigo ki sameni."
Suka yi dariya suna kallon shigewarta gida.

Rabi'u ya kurawa Tahima ido tun tana kaucewa har ta gaji tace "Wai lafiya?"
Ya jingine da bango ya amsa "Kallon kyakkyawar fuskar amaryar Rabiu nike, wallahi Rahima tunda aka sa ranar aurenmu so da kaunarki dada tofo suke cikin zuciyata, so da yawa ina share awowi ina tunanin zamanmu a school, yanayin shakuwarmu da irin ji da juna da muke ashe soyayya ce ke shigarmu bamu fahimta ba. A kullum godewa Allah nike days kaddaro kasancewar hakan tsakaninmu, da Allah bai rubuto ke mata ta bace Rahima ya zanyi da Raina, Ina zan Kai wannan kololon son da ya cika min Zuciya har ya zamanto babu sauran ko masaka tsinke na kaunar wata, Rahima you're my life, don Allah ki so ni yadda nike sonki.".
Ta saki ajiyar zuciya kafin tace "Ina sonka Rabiu, kaunar da nike maka ne ta haifar da na amince ka zama abokin rayuwata.".
"Na amince sosai Rahima nagode, bari in koma gida, ba sauran abinda kike bukata?"?. Ta kada Kai "Tsakaninmu ba wannan, lalurarka tawa ce kamar yadda tawa take taka, kasan nima 'gata ce su Umma sunyi min komi, kasan sun so a hada bukin nan dana su Maryam amma Allah bai kaddara ba Abbas ya roki arzikin a bari sai ya dawo daga Dubai, sha'anin Dan kasuwa.".
"Lalle naji, Allah yasa shine alkhairi mu dai Allah yasa ba za a daga namu ba."

Tayi murmushi kawai ba tareda bashi amsa ba.

Ya fiddo kudin da Hjy ta bashi ya mika mata taki karba saida yace sakon Hjy ce ta tara jannu biyu domin karba, maimakon ya saka mata kawai sai taji caraf ya kama hannayen nata ya rike yana kallonta...
Tayi saurin kwacewa tana fadin "A'uzu bilahi minal shaidanin rajim, wa iyazu billah."
Shima yai saurin juya baya Yana tasa adduar korar shaidan din, kana ya juyo a hankali yace "Rahima ki gafarceni, banyi da niyya ba wallahi."


DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment