Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

"Hhmmm Allah ya gafarta mana Rabiu nasan ba halinka bane, babu zargi tsakaninmu."

Yace "Nagode, gashi. A wannan karon hijabinta ta santa ta rufe tafukan hannunta shi Kuma ya saka Mata, suka yi sallama ya tafi cikin damuwa.

Shaidan mugune, la'ananne, masheranci, Allah ka Kara yi Mana katangar karfe da dashi. Adduar da Rahima keyi kenan har ta shiga gida ta iske Umma da 2000 din da ya bata.
Nan take ta fara fada "Anya Rahima ba nace karki sake karban ko sisi daga hannun yaron nan ba, yaro dan makaranta da wane hidimar zaiji taki ko nasa?"
Ta durkusa "Umma naki karba ya tilastani Wai Hajiyarsa ce tace ya kawo min."
Umma ta kyalkyace da dariya "Hjy Kaltume kenan, aikinta yafi da haka, wallahi kasancewar danta ne zaki aura yasa nike farin ciki, domin duk unguwar nan kowa yasan macece mai matukar sanin yakamata, ba a taba jin kanta da surukanta ba balle na tsakaninta da 'ya'yanta. Gashi Allah yasa babban danta ya saya mata wannan babban gidan take zaune da kowa lami lafiya, keni yadda labari yazo min ance ba irin wahalar da bata sha ba da mijinta na fari daga ita har danta, ance yai masa kaskanci kamar bashi ya kawosa duniya ba to ga sakamakon Allah nan tana gani, shi yaron ya zama kwararren likitan kwakwalwa ba unda sunansa bai Kai bba daga Nigeria har kasashen waje, ke naji ance ma har turawa hayarsa suke yaje can yai musu aiki su biyasa.."

Tunda ta fara bayaninta ba tace komi ba Saida ta numfasa tace "Umma kema kina sauraren gulmar matan gidan buki ko?"
Tace "Ba gulma bace, wafannan batutuwa da kika ji ba karya ba za'ida, Ni nasa aka binciko min don dole insan halayyar mutanen sa zan Kai Diyata cikinsu, ko nayi kuskure.

Rahima ta kada Kai "Uhmmm Uhmm Ymma, Ni zani in kwanta.".
Ta kalli kudin tace Dauka ki ajiye a jakarki ba zaki rasa amfani dasu ba bai kamata in kashe kyautar sarakuwarki ba ta karike tana dariya.
Cikin shagwaba tace "Umma abin ya koma zolaya Kuma, Saida safe.
03/09/2020, 22:19 - Anty saliha: ...RAHIMA...doc by jami

8
Suka ci gaba da shirin buki har zuwa ranar daurin auren, Yayan ango ya biya sadakin Rahima lakadan, an daura aure lafiya an tashi lafiya, shagali ya rage na mata inda suma suka ci gaba da saukar qur'ani mai girma aka dora da wa'azi da nasihohi yayin walimar don taya ma'auratan murna da fatar alkhairi.
Iyayen amarya sunyi rawar gani wajen gyarewa diyarsu dakunanta ras, sai wanda ya gani, sun kuma nuna bajinta wajen kawowa ango garan buhunnan abinci da su Mai da sauran tarkace harda kudin cefane a sama, a yayinda dangin angon suja karbi sabuwar 'yaruwar tasu hannu bibbyu.
Sati guda suka dauka sua amarci sannan suka koma school don ci gaba da neman ilmi. Kafin nan Saida Rabiu ya zagaya da amarya gidajen 'yanuwansa kaf da abokan arziki don you musu ban gajiya su Kuma san juna, gidan Ya Haseeb ne farkon ziyarta inda suka yi karo dashi zai fita cikin hanzari domin ana nemansa a asibiti, sama-sama suka gaisa don Rahima ma ba zata tantance kalarsa ba, saurin da yake bai bashi damar tsayawa ba balle suyi masa godiya.

Washegari Ya Hasseb ya Kira kanin nasa bayan ya bashi hakurin rashin tsayawa su gaisa a jiya ya mika masa key din mota "focus" a matsayin gift dinsa na aurensu tareda taya su murna da adduoi. Murna a wajensu bai faduwa, Hjy Kaltume kuwa harda hawayen dadi Saida ta fitar tana ci gaba da sanyawa Haseeb albarka.
Wani weekend Rabi'u da amarya suka shiga kanti suka cikowa yaran Hasseb kayan kwalam suka nufi Galadanci misalin karfe sha daya na safe. Tuni yaran da mahaifiyarsu sun tashi sunata Kara kaina a kicin, Rabi'u ya sallama Rahima na biye dashi a baya dauke da ledan tsaraba. A guje yaran suks rugo suka nufo shi "Uncle oyo-yo. Ya duka ya dauki karamin mai suna Junaid suna kiransa Khalifa sabida sunan mahaifin maigidan kenan, shekarunsa biyu harda rabi, ya rike hannun babban Mai suna Mohammad suna kiransa Abba shima kasancewar sunan shakikin Haseeb ne Wanda ya taimaka masa kwarai a rayuwa kana shine surukinsa mahaifin matarsa Zuwaira, shekarunsa hudu.

Zuwaira ta daina abinda take yi ta juyo garesu cikin murna ta rungume Rahima "Maraba lale da amare da ango, Rabiu ba kace min aure kake so daman tuni, kaga kibar da kayi kuwa, ko zan San sirrin?"

Yayi wani irin juyi a tsakiyar kicin yace "Wasa Ni da kyau Auntyna amma kash sirrin tsakaninmu ne Rahima ko in Fadi?"
Cike da kunya tace "Kyaleshi don Allah Aunty har akwai wani sirrin da ya wuce shagwabamun da kuke kullum."

Zuwaira tayi dariya "Laifin Dakta kenan na fada masa ya rage Kar nan da shekara guda muga Rabiu ya aje tozo."

Kusan awa biyu suka kwashe suna hira saboda ance Yayan nasu bai tashi daga barci ba.
Rahima ta zauna gefe ta zuba tagumi tana kallon yadda Rabi'u ya kwanta su Khalifa nata dumurmusarsa,ya daga wannan ya aje, yaiwa gudan cakulkuli, su fada a jikinsa dukansu suna dariya, gefe guda ga kayan wasansu da suka watsar sunyi kaca-kaca, shaawarsu ya cikata Nan take tayi shaawar samun nasu babyn harta fara imagining yadda babansu zai rinka wasa dashi kamar yanzun, gaskiya Rabi'u mutum ne Mai son Yara..
Bata ankara ba taji yana gaida Ya Hasseb, tayi saurin gyara mayafinta ta zamo daga kujera ta durkusa gwiwa bibbyu ta gaida wan mijin nata cikin ladabi da biyayya.
Ya amsa cikin yanayin da bata iya fassarawa don babu sakin fuska a tareda shi sam.
Bai zauna ba ya koma falonsa Kaninsa ya bishi can ita kuma suja ci gaba da hira da Zuwaira inda ba a dau dogon lokaci ba ta lakanci halin Antyn tasu tas
Zuwaira macece Mai harka,tafi mijinta sakin fuska nesa ba kusa a, tana da son mutane da saurin sabo saidai fa akwaita da surutu don cikin awanni kalilan ta fayyace mata labarinta kaf , na iyayenta da 'yanuwanta da na shi kansa maigidan nata, ta fada mata irin zaman da suke da irin matukar son da take masa.

Wani Abu da ta lakanta Aunty Zuwaira irin matan Nan ne masu son rayuwar jin dadi kota halin kaka, masu son kashe kudi da neman kudin kota wacce irin hanya Kuma..

Da alamun ilmin addini bai gama ratsata ba, abinda tafi sani shine ta daura zani komin tsadarsa, ta saka latest takalmi ta rataya jika cike da dimbin naira ba tareda tunanin komi ba, tana da son cin dadi daoilin hakane yasa ko ta dafa nama a tukunyarta ka'ida ne duk daren duniya a sawo mata gasashshiyar kaza, 'yan shila, tsire ko balango taci ta kwanta.
Babban abinda ya bata mamaki babu wani kusanci Mai karfi tsakaninta da mijin da take ikrari tana masifar son, kowa harkar gabansa yake.....
Saida ta tabu kafadarta ta dawo daga duniyar tunani..
"Duk tunanin angon ya barki ne haka? Tafdijan da kece matar Dakta ya za kiyi?"
Rahima ta share maganar tace "Aunty lokacin dora abincin rana yayi ko?"
Ta zabura "Tabbas Ni bana manta inada baki cikin gidana ba, taso mu shiga kicin yau muci girkin amare."

Suna aikin Zuwaira naci gaba da yi mata bayani nau'in sanaar sa take yi, Dubai take ziwa saro manyan bedsheets harda zinari, a cewarta ba zata iya wahalar karatu ko wani aikin gwamnati ba.
"Me kike karantawa ne a school? Ta tambayi Rahima.
Ta amsa "Special Education ne, tunda shi accountancy yake yi."
Tace "Me ya kaiki karatun wani special education?"
Tayi 'yar dariya "Wallahi Aunty Zuwaira Ina matukar tausayin yara makafi, gura gu da bebaye da kurame, da ma wadanda ake haihuwarsu da karamar kwakwalwa, a ganina hanyar da Zan iya taimaka musu kadai kenan."
"Kice kawai kina son wahalar da kanki da rai da lafiyarki baki koyar a normal school ba sai makarantar kurame, ah ah wahala dai kike shaawa."
Ta girgiza Kai "Banyi tunanin wata wahala ba gaskiya, abinda na sani shine kowanne aiki na zabawa kaina dole in zama Mai dauriya da hakurin jure kowacce irin wahala ke tattare da aikin, na zabi wannan fannin ne don bada tawa gudumuwar."

Zuwaira ta gyasa Kai "Daukarwa rai dai Allah ya taimaka ai kin kusa karewa ko?"
" Da ikon Allah karshen shekara nan zamu gama
Basu tafi ba sai bayan laasar, zuwa lokacin maigidan ya fita tuni kafin ya fita ya ba Zuwaira kudi a baiwa sarakuwarsa. Da kyar ta amsa, a ganinta dawainyyar tayi yawa ta isa yanzun su ya rage su nemi nasu na kansu su ci gaba da kwatanta alkhairin da ake musu don shege kawai ke mance alkhairi Dan halas bai mantawa komin kankantarsa.

Watanni takwas kacak suka rage su kare digirinsu na farko, cikin watannin ne Rahima ta Kara shakuwa da mijinta, kaunarsa ta fara zurfi da tasiri cikin zuciyarta har abin na daure mata Kai. Yanuwa da abikan arzikinsu sai shaawar zaman nasu suke musamman yanayin tafiyar da rayuwar auren nasu
Tunda akayi auren sai Kara ji da juna suke, suna samun natsuwa da kwanciyar hankali irin wadanda ake samu muddin aka yi katari da dacen abokin zama, ba abinda yafi musu dadi illa Kara fahimtar juna da suke ko yaushe.
Rahima bata da damuwar data wuce taga ta kare karatunta lfy, bayan so da kaunar mijinta tayi dace da sarakuwar da take ji tamkar ita ta tsugunna ta haifeta itama, koda wasa Hjy Kaltume Bata son ganin bacin ran Rahima ko na dakika gudane, duk abinda ta samu indai naci ne sai taba Rahima taci kafin takai bakinta, idan kudine ko yaushe tana tattalin ta bata su Wai karta zauna baby na kashewa, dangane da abubuwan hidimomin yau da kullum kuwa kamar su man shafawa sabulu wanka dana wanki duk wata zata kebe kudu a sayo ta kirata ta damkasu a hannunta, kayan lashe-lashe da tande-tande ba a maganarsu, ita dai Kar Rahima ta nemi komi ta rasa.
Ita Kuma bata zubar sa tarbiyyar da akai mata tun a gida ba, daraja na gaba ko a Ina ne musamman tsoho, to ta mutunta wadanda bata San inda suka fito ba a titi ballanta uwar mijinta Mai kaunarta tamkar ta lasheta. Sai ya zama cikin surukanta babu kamar Rahima ba don ta kasance matar Dan autanta ba ah ah kima da girmamatan da take yi tun zuwanta gidan ya haifar da hakan.

Kafin su fara karatu gadan garan ne suka shirya suka nufi Gumel gano kakanta da sauran dangin mahaifiyarta, duk sati zasu ziyarci gidajen 'yanuwa ba inda ta tsani zuwa sai gidan Hayatu sabida rashin zaman lafiyar da matansa keyi, ta tsani tashin hankali.

Ba zata manta ba ranat da suka fara zuwa gidan ta riga Rabi'u shiga ciki tayi sallama aka amsa ta durkusa don gaida matar data gani zaune bakin famfo tana wanke-wanke, ta dago Kai ta Mike tsaye tana fadin "Lalle yau nayi farin gani, amarya Ina angon naki?"
Kafin ta amsa Rabiu ya sallama yace "Aunty amarya gamu mun taho me kuka aje mana?"
Sai nan Rahima ta gane wannan ce amaryar Yaya Hayatu sunanta Haulatu...
Haulatu tayi dariya" Me kuka kawo mana goron amarci dai, ku shiga dafa ciki ka barta a tsakar guda tsaye."
Yai musu jagora zuwa dakin uwargidan suka sallama bata amsa ba sai da ya daga labulen dakin suka ganta zaune abinta, Rabiu ya shiga ciki Rahima ta bishi syka zauna suka gaisheta ta amsa a ciki, suka zauna shiru-shiru na mintoci bata Kara ce musu kanzil ba, ya kada Kai ya umurci matarsa ta tashi su tafi, suka sake mara sallama ta share, suna fitowa suka shiga dakin Haulatu don su sake gaisawa itama su bata hakkinta, ita Kam tayi ta jansu da wasa har ruwa ta kawo musu da lemu tace su tsaya suci abinci kuma..
To ai kuwa zaman nan da suka yi dakin amaryarta ya tunzura Jamila, ta fito tsakar gida ta shiga masifa tana sakin habaici "Ahayye ayyririru, yau Ni za a gwadawa gulma da makirci irinta dangin miji, dadin abin kafin a auro wata Ni aka fara gani da sani dole a zauna dani komin kiyayya, magulmatan banza munafukan wofi."..
Ba Wanda ya futo balle ya tanka mata, ana haka Allah ya dawo da Hayatu gida daga wajen aiki, malamine a makarantar Shekara. Yana shiga gidan nasa yai katarin surutan da Jamila ke Fadi, Rabiu na jin muryarsa danuwansa ya fito Rahima ta biyo shi suja gaishe shi
Yana amsa yace "Lafiya meke faruwa Rabiu?"
Ya shafawa idonsa toka yace bai sani ba ya tambayi matarsa. Jamila tayi farat ta amsa "Dole kace baka sani ba mana algungumi, ka dauko wannan kekasasgahiyar matar taka Kun haddasa fitina, ta juya Kan mijin wallahi kayi mishi kashedi, hawainiyarsa ta kiyayi ramata....
Hayatu yaji zata zake ya buga Mata tsawa "Ke ar wallahi ko ki min shuru ko ranki ya baci sai in tattakaki yanzun nan inga me za ayi mutumiyar banza, ni kenan bani da ikon fita in dawo in tadda gidana lafiya, kaina farau aje mata biyu? To wallahi kinyi kadan, duk iskancin da za kuyi ku tsaya kaina Kar shegiyar data shiga sabgar 'yanuwana, sakararu marasa tunanin abinda zaije ya komo."
Kafin ayi haka Haulatu ta banko labule ta fito a fusace " Ah ah Hayatu wasa yai wasa banda tsikarin uwar miji da tabarya, mene nawa a ciki Ni da na tarbesu nace su jira abinci, tambayesu kaji data fito tana masifarta wa ta bi ta kanta balle ya tanka, gaskiya ni ba shegiya ba ce da ubana kafi kowa shaidawa tinda Saida ka Kai masa sadakina ya baka aurena, shegun sakararru na inda suke."
Tana rufe baki Jamila ta zabura sai tau! saukar mari, Haulatu ta rike kuncinta tace "Kika mare Ni? Wallahi baki isa ba sai na rama, itama ta zaburo tana jiran a dabance, Hayatu yai saurin riketa "Kyaleta Haulatu itace babbar kwabo ta yada girmanta.".
Su ma bakin suka bata hakuri, da kyar aka ciwo kanta ta hakura suka iza keyarta ta shiga daki.
Maimakon jamilan tayi shuru sai cewa tayi "Ai da Kun Kyaleta tazo ta rama din yau in gwada muku yadsa ake kirba mutum in lallasata in mata dukan da uwarta bata taba yi mata tunda ta fito duniya.
Takaici ya kama Hayatu ya harzuka ya dumfareta yace "Bari ni in karairayaki kafin ki lallasata, tana ganin ta dau faskaren icce ya dumfareta ta sheka daki ta danne kofa gudun kar a sabauta ta.

Suka bar su Rahima tsirma-tsirma a tsakar gida, yana basu hakuri, suka dawo gida su basu ci abinci ba su hankali bai kwanta ba..
Tun a lokacin bata sake marmarin zuwa ba, gidan Ya Haseeb Kuma iya yin Aunty Zuwaira ke damunta
04/09/2020, 00:24 - Anty saliha: ...RAHIMA...doc by Jami

9
Sauran watanni uku kacal su zana jarabaea akayi bukin Maryam ta auri Alh Abbas dinta, matarsa guda da yara shidda maza da mata suna zaune a sabon fegi. Da alamun Maryam ma Bata dace da Uwargida ba sai abinda Allah yayi kenan domin ita ma ba baya ba wajen kishi da rashin hakuri sam bata yarda a takata ko a wulakanta ta.
An dai yi buki an kare lfy babu wani gagarumin tashin hankali sai 'yan kunji -kunji ko Kuma don Alhaji Abbas namiji ne daya iya rike gidansa ba kamar Hayatu ba da ya zama shakulatin bangaro, yayi sake iyalinsa suka fi karfinsa.
A kwana a tashi Rabiu da Rahima sun kare jarabawarsu sai adduar Allah yasa ayi nasara.
Bayan sun huta na sati biyu ta rokeshi ya kaita gidan 'yaruwarta, ya amince ya dauketa suka tafi. Sun shade awa uku suna hira amma Rabiu bai sa niyyar tashi ba, Maryam tace "Ni fa ban gane ba shin ba tafiya zaka yi ka bar min ita anjima ka dawo daukarta ba?"
Ya kwashe da dariya "Kina nufin in koma gida Ni kadai? Gaskiya ba zan iya ba, kafarta kafata."

Maryam ta kalli Rahima "Say something kinji Wai ba zai barmu muyi hirar zumunci ba."
Ta danyi dariya "To shin din bare ne?"
Yace "Kyaleta kawai ta nuna min 'yan ubanci alhalin an zama daya Ni da Rahima.
Maryam ta daga Kai "Ai ga alama nan na gani tun zuwanku, Ina ruwan Romeo & Juliet.
Yayi dariya "Kuma ba a hanaku ba."
"Ah ah Wannan irin soyayyar sai ku yara, Ni mijina tsohone bayan haka ina yaga wani lokacin soyayya Yana can yana neman mana na sakawa a bakin salati."

Rahima ta jinjina "Ke din yadda kike?"
"To naji na amince Amma don Allah Rabi'u ka tsahirta mana kona rabin awa ne, magana Nike son yi da ita, zancen na Mata ne Kasan akwai sirri."
Ya kalli matarsa "Kin amince in tai in dawo Nan da awa guda?"
Rahima tayi masa irin kallon soyayyar nan tace "Is okay, nagode."

Ya mike ya sumbaci gefen kumatunta "Sai na dawo kenan.".
Yana fita Maryam ta juyo gareta "You surprised me, I was impressed Kar dai ince kun kamu?"

Ta kishingide ta amsa "Ina zaton hakan Nima, a hankali so da kaunar mijina suka rinka shigata saboda duk da kasancewar sa yaro matashi ya iya tafiyar da al'amarin rayuwar aure yadda yakamata, ko ya fahimci feelings dina ne ya bi duk hanyoyin da suka dace ya mallaki zuciyata, idan kinga irin kishina da yake sai kin rike Baki, ya fara fadin Wai anya zai barni inyi aiki kuwa, ga kulle, idan kuwa ya bari na fita to ki tabbatar da tare zamu fita, ke al'amarin nasa tun Yana ba Hajiya shaawa ta fara nuna damuwa tace tun kafin aje ko Ina zai bullo da sabon al'amari? Ni kuwa maimakon ya dameni ko inji haushi sai dadi nike ji, Ina Kuma ji a zuciyata muddin ya tsaya kan va zanyi aikin ba zan amince don ko kusa ban son abinda zai batawa masoyina rai."

Maryam ta kura Mata idi sosai tace "Tabbas kina kaunarsa amma har yanzun da sauranki baki shiga matakin da Zaki ji amsarki ba, akwai sauran lokaci tukunna."

Rahima tace "Haba dai duk nike ji dinnan da saurana?".
"Kwarai kuwa idan lokaci yayi zaki fada min da kanki, yanzun kashi talatin kike dashi cikin dari kina awo aiki ko rabi baki Kai ba."

Ta nisa "Ashe in Kara zage damtse tun kafin bakon dake tafe ta/ ko ya kutso kai ana hanamu shakatawa."

Maryam ta bude baki cikin mamaki "Lah kema ciki gareki Rahima? Labarin da zan fada miki kenan Nima, shikenan za mu yiwa Umma tagwaye sunan da take kiranmu."
Suka rungume juna suna adduar Allah ta inganta musu ya Kuma saukesu lfy idan lokacin yayi."

Bai Kara ko minti guda ba, awa dayan na cika suka ji horn din motarsa suka kalli juna, Rahima ta mike ta dau Jakarta ta gyara mayafinta tace "Mu zamu tafi sai kinzo kenan?"

Tace Insha Allah, uhhmm did he know about the pregnancy?"
Tace "No but yau zan sanar dashi tunda na tabbatar"

Suna fita Maryam ta riko hannunta ta mika masa tace "Rabiu manya, to ga matarka, ban cinyeta ba balle in gutsuri namanta "

Ya sosa keya "Ba haka bane Aunty...
Ta katsesa "Kwarai na fahimta to Allah ya bamu alkhairi, sai nazo."


A wannan ranar wani sabon nishadi ya rufesu suka jima suna hirar soyayya kasancewar a ranar suka shekara daya cif da aurensu, sunyi nafilfili da adduoin godiya ga Allah SWT kana suka kwanta.
Bata yi hanazarim shaida masa batun cikin ba Saida dare ya tsala ta tashesa daga barci, ya tashi ya kunna fitila ga zatonsa ita a bata da lfy yace "Lafiya?
Ta kura masa idanu tana nazarinsa, duk da cewan barci ya farka yai Mata wani irin kwarjini, fuskarsa sai sheki, ya Kara kiba da haske, tayi ajiyar zuciyar, Rabi'u yarone matshi amma girman jikinsa kansa ayi kuskuren shekarunsa, suna mugun kama da Hayatu sai dai ya darashi tsayi da jiki, Hayatu farine mi yar doguwar fuska,mutum ne Mai fara'a da son mutane ga ban dariya, kusan ko yaushe ka gansa hakoran nan bude suke Yana dariya, da wuya ayi masa Abu ya bata masa rai har yai fushi, wadannan kyawawan halayen nasa yasa yake da jama'a da abokai babu iyaka.
Ya kagu da kallon da take masa ya girgizata "Wai shin lfy.
Tayi "yar dariya "Hakan nan kawai kwana nan sai inji kana matukar burgeni ko kallonka nayi sai inji wani dadi a zuciyata.".

Ya zumburi baki cikin wasa "Kawai kika tasheni barci don ki kalleni kinji sanyi a ranki ne?"
"To me zanyi maka da dare Nan, kishi ko yunwa?"
Ya janye matashin da take rungume dashi a cinyarta ya maida kansa ya kwanta a wurin Yana mai sakin kyakkawar ajiyar zuciya yace "Ni kuwa ni'ima nike ji duk lokacin dana kalleki, shin Rahima kinsan irin mutuwar son da nike miki kuwa?
Ta rufe bakinsa "Rayayyen so dai mijina idan kace mutuwa ai ba zance kenan, na yarda da so da kaunarka, nima hakan yake a zuciyata, domin Ubangiji ya karfafa mana dankon soyayyarmu ne ya bamu wannan." Ta kamo hannunsa ta dafa cikinta.
Da farko bai fahimci inda zancen ya dosa ba, daya dago ya zabura ya cakumota ya riketa gam ya fara tsalle Yana sumbatarta "Da gaske cikine dake Rahima alhamdulillah."
Tace "Da gaske Ina dauje da bebinka Rabiu amma idan baka daina juyi dani haka a tsakar daki ba zamu ita rasawa don likita ya shaida mun saina rinka kukawa in bi a hankali mahaifata Bata da kwari.
Nan da Nan ya ajiyeta a hankali yace "Are you ok?"
Tace "Banda wata matsala sai adduar Allah ya rabamu lfy."
Murna ta rufesa ba sauran barci kenan, ya zauna ya fara plan din tarbon jaririn da sauran kusan watanni bakwai kwarara kafin ya fito duniya.

Alla- alla yake ya kare sallar asuba, ya shuga gaida Hajiya yai Mata albishir, saboda tsabar farin ciki ranar tuni tayi Bata ci komi ba, farin ciki ya kosar da it's, can gidansu Rahimar ma abinda iyayenta suka kashe suka tsare kenan, jiran ranar haihuwar 'ya'yansu biyu, Maryam da Rahima.
04/09/2020, 13:45 - Anty saliha: ...RAHIMA..doc by jami

10

Lokacin tafiya bautar kasarsu yazo, Rabi'u ya shiga ya fita aka barsu a garin Kano, inda shi yake Bank Rahima Kuma ke koyarwa a makarantar kurame.
Watanni bakwai da 'yan kwanaki Rahima ta kamu da zazzabin malaria, Rabi'u ya rikice musamman da yaji likita ya gaya masa ba a son mai ciki ta kamu da zazzabin saboda yana iya haddasa miscarriage ko yaiwa uwar lahani.
Kowa ya dukufa adduar Allah ya bata lafiya ya kareta da abinda ke cikin, kwana biyu kamar taji sauki ana uku zazzabin ya dawo wannan karon hade da ciwon baya da mara. Likitoci sunyi kokarinsu amma kafin awa guda nakuda ta taso haihuwa ce gadan-gadan, da taimakon Allah ta haihu lafiya ta sami danta bakwaini. Iyaye da 'yanuwa da abokan arziki suka cika asibiti sai dai kash da kyar aka barsu suka ga jaririn a hannun nurse aka wuce dashi aka saka shi cikin incubator sabida bai gama yun kwari ba ga rashin lafiyar jundice da akan haifi wasu jariran dashi.

Ba a sallamesu ba sai ana gobe suna tare da gargadin Kar a bari a rinka daukar yaron gudun jagwalgwalo

Hajiya Kaltume ta Kira Rabiu don su shawarata sunan da za a sanyawa jaririn yace "Hajiya na riga nayi masa huduba tun ranar da aka haifesa kinsan addini ya koyar daamu da zaran an haihu mu yiwa yaranmu huduba,bayan munyi musu Kiran sallah da kalimatu-shahada a kunnuwansu ba sai an jira sai wani ranar suna ba. Koyar Manzon Tsira ne."
Tace "Naji ustaz, wane suna ka saka masa Ina fatan ba irin na zamanin nan masu wuyan Fadi ba."
"Ko daya, wannan ko sau nawa zaki iya fadi cikin mintu guda kacal."
"Wai zaka fada min ko
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment