Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

bude kan mutum ko baya ya mayar ya dinke ba wani abu ne mai wuya a wajensa ba, da taimakon Allah duk wata matsala da aka kawo masa akayi sa'a ya duba yai aiki ko bada magani a kanyi nasara.


Dalili kenan da sunansa ya bunkasa tun daga gida Nigeria har kasashen waje, manyan asibitocin ketare ma dashi suke takama don ba inda kafafunsa basu taka ba. Sabida yawace-yawacen da yake yi ne yasa shi jin harsuna daban-daban, yana jin harshen larabci, faransanci, jamusanci, dangane da yaren harsunan kasarmu kuwa tun Yana jami'a ya iya yaren yarbanci, fulatanci dana igbo, abin ban sha'awa duk yaren daya juya harshe Yana yi sai mutum ta rantse daman shine mother tongue dinsa.

Ganin yadda ayyuka suka yi masa yawa, zirga-zirga na neman tauyesa wajen sauke hakkin iyalinsa dana iyaye yasa ya yanke shawarar gina makekiyar asibiti Wanda ya nemi wasu kwararuj likitocin suka hadu suna gudanar da harkar asibitin gadan-gadan.

Babban abin shaawa da yawanci maganar da mutane suke fadi shine ma'aikatan asibitin nada karamci tun daga leburori zuwa nurses da doctor's dinsu balle shi kanshi uban tafiyar, ta ta shahara wajen tsabta sosai, babu wulakanci tsakaninsu da patients, sun dauki Mai kudi da talaka gudane, patient sunansa patient Kuma Abu guda suka zo nema (lafiya) don haka babu banbanci.
Ba nan ya tsaya ba da kyautatawa patients dinsa ba, da duk ya lakanci basu da halin biyansa hakkinsa ya kan taimaka yayi aikin kyauta tareda kulawa ta musamman.

Daga bayan nan yawanci manyan asibitocin gwamnati ke turo masa da patients yai musu abinda ya dace gwamnatin ta biyasa hakkinsa.
Can kasashen waje ko yaushe irin aikinsa ya taso sukan bugo masa waya ya tafi don ceton rayuwar Al'umma, a dalilin hazakarsa ne suka yiwa sunansa laqani da Mr Brain.
Ga Wanda bai taba ganinsa ba kuna yin ido biyu fuskarsa zata nuna maka alamar mutum ne mai ji da kansa domin miskili ne na karshe. Wani irin mutum ne da samun irin halayensa sai an tona, fuskarsa a daure take ko yaushe, baya dariya gaban kowa amma kuma mutum ne mai saukin kai idan aka fahimci halinsa.
Dr Haseeb mutum ne da bai dauki abin duniya da ita kanta duniyar wata tsiya ba face wajen gwaji da neman tsiran gobe kiyama har ya kance mutane na shirme wajen maida duniyar wajen zama tamkar ba za a mutu a barta ba, mutum ne shi mai sadaukar da kai da maida dukkan al'amurranss ga Allah. Bai da saurin karaya don haka ya fita zakka cikin abokai da sa'oinsa musamman ma da wuya suke gane inda yasa gaba.
Mutum ne Mai son rayuwa don ance ka nemi duniyar tamkar ba zaka mutu ba, ya rike addininsa matukar gaske saboda ance ka gyara lahirarka tamkar yanzun zaka tafi. Ya kanyi wuya a tabashi ya hakura in dai har ya tabbatar da gaskiyarsa, mutum ne Wanda baya karya yakan Kuma kure duk Wanda ya nemi yai masa hassada har sai yaga abinda ya turewa buzu nadi.
Bai da fargaba, bai da tsoro, bai da hayaniya, mutum ne natsatstse kamilalle, bai son raini don bai rana na gaba dashi ba, yana son ayi masa biyayya, bai daukar jita-jita, baya son girman Kai ko nuna Kai wani ne, bai taba daukan kansa wani abu ba, Yana son hira da Wanda ya amincewa, idan har an zauna dashi mutum ne da ake karuwa dashi ta hanyoyi da dama, Allah yai masa laqanin iya zama da mutane.

Haka nan yakan kaunaci duk Wanda ya nuna masa kauna ya Kan guji makiyinsa cikin kowanne hali.

Dr Haseeb mutum ne Mai tsananin kusantar Ubangijinsa, wajen ibada da adduoi neman taimakon Mahaliccinsa a dukkan al'amurran da suka jibanci rayuwarsa, bai Kuma taba tunanin Ubangiji bai amsa bam

Ranar da Mahaifiyarsa tayi masa batun auren matar kaninsa Rabiu ya razana sosai, batun ya dameshi ya tsaya masa a rai matuka, amma damuwar data fi masa ciwo itace yi mata musu sabida in har yana kaunar mutuwarsa to zai so abinda zai bata mata rai, baya kaunar abinda zai sosa Mata rai ko kadan.
A kullum yana danganta samun nasarar da yake a rayuwa da dimbin adduointa ne garesa bayan albarkar da take sa masa kullum.

To yanzun data gangamo aure, auren ma na wace ko a mafarki bai taba tunanin faruwarsa ba ya zaiyi da bukatar ta? Ba wani abinyi illa amincewa da bin umurninta da fatar Allah yasa ya zame musu alkhairi duka.

Amma ya yankewa kansa the most difficult decision in his life duk da bai yanke shawarar ba sai da yayi adduoi kamar yadda ya saba ya roki Ubangiji fa'ida kan al'amarin, da alamu akwai haske sai kara neman taimakon Allah.
Tunaninsa ya koma Kan yarinyar ko yace matar da ake son ya auran, zuciyarsa ta amince Rahima yarinya ce mai natsuwa da hankali, tanada biyayya tunda bai taba jin ance wani sabani ta shiga tsakaninta da marigayi ba, yasha jin irin yabawar da Hajiya ke Mata, yasan yadda ita din take girmama Mahaifiyarsu wanda mutuntata da take yi me ya Kara haddasa son hada wannan auren. Idan ya tuna yaronsu Kuma, Abdul ya shaku dashi, shima jaksn fiye da 'ya'yan cikinsa ma wanda bai rasa nasaba da matsalar uwar yaran da tafi son 'ya'yanta su yini su kwana a can gidansu fiye data kawosu wajen Hajiyarsu. Da ya nuna rashin amincewarsa ta kawo masa uzurin sunfi sakeea a can saboda akwai yara sa'oinsu Kuma tunda shi ba mazauni bane meye na complain.

Yan kwanakin nan da Hajiyar ta diba masa ayyuka sunyi masa sauki don hakane ya Sami daman yin nazari da adduoinsa a natse, ysi reaching decision don haka bai bata lokaci wajen dumfararta da shawarar da ya yanke ba.
07/09/2020, 23:52 - Anty saliha: ...ˆRAHIMA...doc by Jami

18

Ganinsa tunda sassafe a Rana ta takwas da yin maganarsu baisa ta saki fuska, ya durkusa ya gaisheta ta amsa a dakale. Daga can cikin uwar daki Abdul yaji muryar babansa ya tashi daga barci ya fito yana mutsuke idanu, Haseeb ya riko sa ya zaunar dashi cinyarsa ya rungume ya kalli Hajiya yace "Ashe har yanzun bai koma ba?"
Tace "Mamansa bata zo ba Ni kuma ban aika ba."..
Ya kalli yaron da kullum idan ya hansa sai ya Tina da danuwansa, ya kada Kai tare da kara rungumarsa, nan da nan ya koma barci, Hjy Kaltume tace "Wannan shakuwa taku tayi yawa, muryarka fa yaji yasa ya taso barcin bai ishe shi ba."
Ya kada Kai hakane, ba a kaishi makaranta ne naga har kusan tara yana barci?"

Ta amsa "Yana zuwa mana ka sani, bai jin dadi ne tun jiya da dare ya kwana zazzabi har yana firgita yana Kiran uwarsa Yana kuka."

Ya dafa kansa "Ashsha subhanallah, ya taba jikinsa, gaskiya har yanzun da alamun zazzabin ko asibiti za a kaishi?"
Tace "Nima tunanina kenan."

Ya Kara duba shi Kuma yace "Ba sai yaga likita ba idan yasha magani ma zazzabin zai sauka bari inyi masa addua yanzun."

Dr Haseeb ya dafa jikinsa ya karanto *BISMILLAHI A'UZU BILLAHIL AZEEM MIN SHARRI KULLI URQIN NAARIN WA MIN SHARRI HARRIN NAAR...
Ya kara dora hannunsa na dama saman goshinsa ya karanto *AS'ALUL LAHAL AZEEM RABEEL ARSHIL AZEEM AN YASHFEEYAKA... Bayan ya gama yace insha Allah zai samu waraka." Ya mike ya maida shi cikin dakin ya kwantar dashi kana ta dawo ya zauna..
Ta daina abinda yake yi ta fusksnce shi sosai tace "Tun shigowarka nike alla-allah inji ta bakinka ka barni inata ci da kuda, wace shawara ka yanke?"
Ya sunkuyar da Kai tare da yin kakkarfar ajiyar zuciya, to in ba domin uwa, uwa ce ba wa ya isa ya tursasa masa yin abinda baiyi niyya ba? Ya dago Kai a hankali yace "Tunda kin ganin auren alkhairi Kuma kin amince shikenan."
Ta saki murmushin jin dadi tukunna kafin tace "Fito fili kayi min bayani, shikenan kamar yaya?"

Ya sake jan dogon numfashi "Ina nufin na yarda Zan aureta, sai dai kin tuna ina tsoron ajiye mata biyu domin shakkar rashin yin adalici tsakaninsu bayan haka kina ganin zamu zauna cikin kwanciyar hankali bayan Ni da ita ba son juna muke ba?"

Dariya ce ta kubuce mata tace "Itama Zuwairar da bata zake a kanka ba da tasha wuya, miskillancinka ba boyw yake ba, wannan Kuma batun soyayya bata ko taso ba ya ma rage naku, ko kuso juna ko ki da zaran Allah ya hadaku addua kawai za muci gaba da yi muku.'
Hhmmmm ya Fadi a zucci Hajiya mahaifiyarsa ce yana alfahari da hakan, har bugun gaba yake yana ganin yafi kowa sanin jakinta but akwai so many times da ya kanyi doubting hakan musamman idan ta murde ta rikice ya kan rasa inda zai bullo mata kamar yanzun. To in ma banda abinta ya za ayi mace da namiji suyi zaman aure da ya dace bayan babu so da kauna tsakaninsu? Har gara ace mutum guda na so, in tafiya tayi nisa sai dayan yaja ra'ayin gudan amma wannan halin kaka Ni kayi dane yai kama?, Da shi da ita duk basa so, sai yaya kenan?..

Tayi kamar baya dakin ta jawo tarkaccenta zata fara kulle-kullen ta, yasan hali muddin bai sake magana ba ta kare nata zancen kenan don haka yai saurin tambayarta"Yanzun me zanyi abin nufi wane mataki za a dauka nan gaba?".
Taci gaba da hidimarta
"To ni Kuma zaka tambaya kana namiji kace baka san yadda ake neman aure ba, Kai don Allah baka ji kunya ba, lokacin da kaje samartakat auren farin nina koya maka yadda zaka yi?"

Ya dafe Kai!Oh oh ya shiga uku, ya lura so take ta tursasa shi, ya daure yace "Hajiya wancan da wannan ba daya bane, kin manta inada matsayi a gidansu Zuwaira tun fil azal bayan kaunar dake tsakaninmu?"

To nan dinma sai ka gwada gidansu Rahimar ka gani su ma wanne matsayin zasu baka idan itama kana neman samun gurbi a zuciyarta kasan hanyoyin da suka dace ka bi, Allah yass a dace.'

Yadda ta hakikice tana maida mishi martani yasa shi dariya da sha'awa yace ",Idan naje anjima da laasar na ganta banyi laifi ba ko?"

"Wane Kuma irin laifi ai sai fatan Allah ya kulla alkhairi, kaje ka gabatar da kanka matsayin mijin dana ce nayi Mata Kuma tayi alkawarin ta amince, idan zaka tafi ka biyo ka tafi da takwaranka yaga uwarsa don da biyu taki zuwa gidannan, Nima naki aikawa dashine saboda jiran wannan ranar, sai kaje Ina saurarenki, Ina gaishets da kyau."..
Ya fita Yana murmushi itama haka.


Ranar a gida Maryam ta yini, Rahima na dawowa makaranta kenan direba na ajiyesu, Walida tasa kuka bata ga Abdul abokin kirinyyarta ba, Saida aka tula mata kayan wasansa tayi shiru.
Su kuma iyayen nata hidimar dora sanwar abincin rana saboda Umman tasu ta tafi Gumel dubo mahaifinsu da bai ji dadi ba, amma tana gab da dawowa, hatta yaran gidan kanninsu basa gida.

Bayan sunci sun koshi sunyi sallar laasar Rahima ta shiga wanka ta fito ta sake dauro wata alwalar kana ta shigo daki ta shirya tsaf Kai kace shirin zuwa buki take.
Maryam ta kalleta "Sarkun kwalliya kina burgeni wallahi karki so kiji yadda Nike sha'awar kirar jikinki 'yar caraf dake, wa zai ce wannan dafaffen cikin ya dauki da kin haihu.""

Rahima ta kanne mata ido guda "Aunty Maryam sarkin mita, ke din ai kike jawowa kanki katon ciki, inda halitta da rashin kulawa, irin naman da kike dankara lafiya ne, ki ci kowanne irin nama, kisha kayan Zaki, kefa duk inda kayan dake Kara kitse suke kina Nan ya ba zaki ajiye teba ba, gaki Nan haihuwa daya kin zama wata guzuma, idan kin Kara sai Alh Abbas ya auro daidai misali don har Hjy Suwaiba barakallsh Masha Allah."

Ta wurgeta da maficin dake hannunta "Shima din ba kiga yadda ya koma ba har tozon wuya ya fara fa."
Rahima tace "Hhmmmm da Rabiu na nan da ya kusan kibar Alhajinku, dubi yadda ya koma kafin rasuwarsa."
Maryam ta shareta, ta sake maimaitawa, a nan ta kalleta tace "Saboda Allah Rahima ba zaki bar wannan bawan Allah ya kwanta makwancinsa lafiya ba, ke kenan da duk aka tada magana sai kin sako zancensa, Ina amfanin haka, adduarmu kadai yake bukata."..
Ta nisa tareda dafe kanta "Nima bana sanin time din da nike ambatonsa Maryam, Ina kokarin dainawa."
. "Ah to gara ki yiwa tufka hanci don ba namijin da zai dauki Yana aurenki kina zancen wani wanda ya rigamu gidan gaskiya."


"Nace miki zan bari, da kike fadin hakan ai mijin fari wuyan mantuwa gareshi, balle ma kowa na aura dole yai hakuri dani."

Ta kalleta a shagube "Sai dai kuwa idan bai sonku, muddin Yana kaunarki zaku rinka Kai ruwa rana ne, Wai ma ba haka ba ya batun Dakta?"

Rahima ta canza nan take "Ki bar batun nan don Allah, ai don in nunawa Hajiyar ba Mai yuwwa bane in har hakan take nufi naki komawa gidanta, har Abdul na bar musu in dominsa suke son aikata abin kunya, ko hausawa sunce ana barin halas....

Maryam ta harareta " Jiya dominki nayi tambaya a islamiyya kan shirmen da kike yi Kuma in fada miki don kin auri Dakta ba abinda ya kaucewa shariar musulumci bane, Malam yace addininmu nai hana wa ya auri matan kani na idan Allah yai masa rasuwa hakan shuma kani na iya auren matsn Wan sa in haka ta kasance.. Har da misalin cewan ko suna da rai ce dayansu ya kamu da rashun lafiyar da ya hana yin sunna da matarsa an nemi magani an rasa na tsawon shekarun da aka gindaya masa zai sahale mata gashi ya yaba hankalinta bai son tabar gidan don kyakkyawar dabi',unta Yana iya yiwa danuwansa maganar cewan iin ya saki shu ya aureta idan sun daidaita tsakaninsu, Kuma auren ya halasta, ke dinma banga abun tada jijiyoyin wuya bayan da bakinki kika fada min kina son Daktan .

Ta kauda Kai "Na dai so mutumin da aka bani labarinsa, da lamarin ya juye Kuma na sanu canjun ra'ayi.

Ta wani kalleta 'Karki kawi mun burgar banza, karyarki wallahi, was yace Miki ana yiwa soyayya yankan kauna, yadda mashin son wancan ya soki kirjinki haka na Daktan zai huda zuciyark tunda batun mutum guda ake in dai dama ba karya kike ba Wanda a sanina ba a karyar so da kauna."

Da taji alamun ta kamo hanya zata kureta saita canza hirar cikin dabara....

Suna cikin hirar suka ji yar karamar muryar Abdul ya shigo a guje Yana fadin 'Mami Kinga jirgina baba ya saya min."
Murnan ganinsa ya rufeta, ta daukeshi tana sumbatarsa "Oyo-oyo Abdul Ina Hajiya?.
Hankalin yaron ma wajen Walida, ganin hakan ta sauke shi, Walidan ta fara kukan sai ya bata jirginsa. Rahima tace Baba ya hada rigima kenan dole gobe inje in sayo miki naki jirgin".

Wani yaro Dan makwabtansu ne ya shigo Yana sallama suka amsa "Wai ance ana Kiran maman Abdul a waje."...
Rahima ta kakki Maryam kinji Kuma Bala da gulma shi daya saba shigowa har cikin gida a gaisa ".
Maryam tace "May be sauri yake, fita kiji in zai koma da Abdul dinne tunda ban gansa da kayansa ba."

Maimakon ta tsaya saka hijab, katon gyalen Maryam ta dauka ta yafa ta fita cikin sauri.
08/09/2020, 13:42 - Anty saliha: ...RAHIMA...doc by jami

19
Tun daga kan soron farko kamshin turaren 'fame' ya fara dukan hancinta, zuciyarta ta fara bugawa cikin sauri, ba dai zarginta zai zan gaskiya ba?
Ta karisa cikin tsakiyar soron gidansu inda tayi arba da *HASEEB* in person, rawar da jikinta ya fara, bai hanata saurin durkusawa cikin ladabi tace "Barka da yini, ya su Aunty Zuwaira?"
Ko kallon arziki bata samu daga gareshi ba
Ya amsa a takaice "Lafiya." Ya shiru
Ta dan jima tsugunne tana jiran taji da wacce ya taho tunda bai taba zuwa gidansu ba.
Da ya tuna bai da wata mafita dole ya fadi dalilin zuwansa kamar yadda yaiwa Mahaifiyarsa alkawari,ya cije, cikin isa da miskillancisa ya tambayeta "Magana ta kawo ni ko zan sami damar Fadi?"

Kamar ta amsa cewan bata da lokacin saurarensa, saita tuna kaninsa,da irin girmansa da yake gani kamar uba ba wa ba, ta tuna dawainiyar da yake dasu, hakan yasa ta hadiye zuciyarta tace "Ba damuwa Ina saurarenka."

Ya gyara tsayiwarsa sosai ya jingine da bango tareda goya hannayensa a kirji yace "Hajiya tace tayi miki bayanin komi don haka ba zan tsaya wani dogon bayani ba tunda kin amince da shirinta nima hakan akan dole yanzun ya rage naki kiyi shawarar yaushe kike ganin ya dace a daura auren?"

Gabanta ya buga rugugu, aure? Haka ake zancen auren cikin isa da kasaitar mulki, aiki jawur, tun kafin tafiya tai nisa bata iya cewa ta fasa, daman ta amsa ne saboda bata san shine ba, wata zuciyar kuma tace zaki zan mai karya alkawari kenan wanda a addinance hakan ya zama munafuci, can ta nisa, tace "Bani da yancin kaina koda nike bazawara, iyayena keda hakkin wannan sai abinda kika ce."

Shi kansa yasan nai kyauta, bai dace ya furta mata wadannan kalaman ba, ba ita ta Kar zomon ba, yaja numfashi yace "Okay zan jira su zartas da shawarwarinsu, nawa iyayen zasu taho in Sha Allah."

Da yaji ba zata kara cewa komi ba,sai ya Kara gyara murya yace "Abdul kuwa bai ji dadi ba amma naga ya warware, dazun jikin yafi masa zafi."

Tana dai tsugunne kanta sunkuye har zuwa lokacin, maganar da yake yi bai sa ta dago ba balle tayi responding.

Ya kada Kai "Ni zan koma, na wani problem ko?'

Ta girgiza Kai.
"Ina Abdul, in koma dashi ko a bar shi?"
sai a nan ta amsa "A tafi dashi, sai an jima a gaida Hajiya Aunty da Zuwaira."

Tana gama magana ta yunkura ta mike ta shige cikin gida ta barshi nan a tsaye.
Tana shiga ta cewa Maryam "Don Allah dauki Abdul ki mika sa waje zasu koma gidane."
Ta kalleta taga fuskar nan tata a daure bata tsaya tambaya ba ta rike hannun yaron suka nufi kofar gidan. Ko da wasa ba tayi zaton shi zata gani ba amma ta danne mamakinta ta gaisheshi, Abdul ya ruga wajensa ya kama hannunsa suka shiga mota suka wuce.

Har tana tuntube wajen saurin komawa cikin gida inda ta isko Rahima ta cika tayi dam, ta kalleta ta tuntsure da dariya tace "Yau Allah ya hadani da famous Dr Abdul-Haseeb Junaid din da ake magana, he's very handsome, ashe ganinsa a zahiri yafi ganinsa a tv."
Rahima ta cafe "May be ganun baiwar kyaun da Allah yai masa da kirar jiki msi kyau ne yasa yake wani ji da kansa."
Maryam tace "Ke fa na lura ba zaki kwantar da hankali ki fahimcesa ba, to komin ji da kansa dai gashi ya taho har gida, ya kuka yi?"

Ta tabe baki "Maganar ma da kyar yake har Yana m fada min shi dole ne ya amince da batun auren Wai Kuma yaushe nike son a daura? Ke kinji wani galari, wallahi ba domin ina ganin mutuncinsu ba da yaji magana daga bakina, darajar Rabiu kawai yaci, ko an fada masa nima da son raina za ayi oho."
Maryam ta tausayawa 'yaruwarta tace 'Gaskiya al'amarin da rikitarwa Rahima amma kiyi hakuri ki rungumi kaddara,Allah da ya shirya faruwan haka daku yasan dalilinsa, mu 'yan tayaku addua ne, ki daure karki dorawa Dakta laifi, shima na tabbatar abin na damunsa dole yaji a jikinsa."
Ta share hawayen da suka gangaro tace "Ya zanyi hakuri ya zama dole but babban bakin cikina reaction din daya nuna min, koni na nemi auren nan iyakar cin fuskar da zai min kenan."

Maryam tace "Ni kuwa ban dauka wulakanci bane, kisa kanki a position dinsa ki kwatanta ya za kiji...

"Maganar ta wuce Maryam, I've already made up my mind and there is no going back, so zsn daure ko me zasu taso, hhmmm Allah dai yaji Kan Rabiu."

Maryam ta mike tsaye "Zaki fara ba, to ba dani ba, naga alamun su Umma sai dare zasu iso ko in dan saurara zuwa karfe tara ma tafi gida?"

"Yes idsn ba wani damuwa nasan suna gab da shigiwa insha Allah kinsan Baffa bai son tafiyar dare."

Takwas saura kwata na dare suka dawo, Baffa yace su tsahirta yayi sallah sannan su gaisa, Umma Kuma ta zauna suna hirar 'yanuwa da abokan arziki na garin Gumel.

Alh. Mamman ya shigo bayan ta fito daga masallaci ya fadawa Rahima tanada bako a waje, taso taki fita Umma ta fara fada.
Direban Daktan ne jingine da mota yana jiran fitowarta, tana isa ya durkusa ya gaisheta kana ya bude motar ya fiddo wasu manyan ledoji guda biyu ya mika Mata Wai sakon ubangidansa..
Ta karba a sanyaye tace ya jirata kadan, ta koma ciki ta dauko masa tukwici ta kawo masa ya karba da kyar yana godiya.
Ta sake komawa tana shifa dakin ta kwashi ledojin ta diresu gaban Umma "Gashi wai inji baban Abdul "
Kafin Umma tace komi Maryam ta zaburo "Masha Allah, iye 'yar gidan Daktan ba, bari mu gani Musa albarka."

Umma ta harareta "Wannan zarbabin na menene?"

Ta kalli Rahima "Kinji Umma tafi son ki bude kyautar da hannunki ko kin ban izni in bude?"

Rahima ta amsa "Idan kin ganin ki wuce dasu na baki banso."

Tayi wani shewa ta shiga zazzage kayan, ledan farko tarkacen cosmetics ne, na biyun atamfar super ce biyu, Holland biyu hade da lallausar hadaddiyar shadda.
Ta kyalkyace da dariya "Ashe ni ras, bari inga wace zan fara dinkawa, ta bude turmi guda wani envelop ya fado mai dauke da rafar kudi Wanda aka rubuta kudin dinki a bayan envelop din..
Sakonsa ya daure mata Kai, shi da ya taho Yana shan kamshi yana fadin an tursasa masa ne meye na wahalar da Kai, ko kayan ma matsa masan aka yi ya aiko?

Baffa ya shigo dakin a lokacin suka gaidashi da tambayar mutanen Gumel, yace kowa lafiya duk zasu taho daurin auren Rahima da bukin tarewa."
Ta zumburo baki ta kalli uwar "Yanzun Umma har Kun karas da abinda babu tabbas?"
"Kunji munafuka inji Maryam, mu kam mun tabbatar tunda dazun nan Dakta Haseeb ya taho wajenta Baffa sannan ya aiko da sakon nan ace babu tabbas?"
Umma ta harareta "Wane irin zuga kike mata ne, kina son Baffan yai fada ne ko yaya?".
Rahima ta saki ajiyar zuciya "Ni nama kosa ta tafi gida hakan nan tunda tazo ta isheni da surutu har ciwon kai ya kamani."
Iyayen suka kalleta cikin tausayi suka ce "Rabu da wannan babbar gwazar kinji sannu, nemi magani kisha ki kwanta ki huta."

Maryam tace "Hhmmm bari dai in zo in gudu tunda sauran girmana tunda taron dangine abin."

Rahima tayi murmushin cin nasara watau ta danawa Maryam bom.
Cikin wasa da dariya suka ci gaba da hira har Alh Abbas yazo dauka matarsa, ya shigo ya gaida surukansa kana ya dauki Walida da tayi barci ya sallamesu ya fita. Rahima ta zubawa 'yaruwarta kayan shafan hade da turmin super ta mika mata, Umma ta diba Mata tsarabar Gumel sannan suka fita Rahimar na rike da kayan har wajen motarsu ta bude ta aje mata su a baya.
Alh Abbas ya leko da kansa ya fara tsokanarta "Ni fa naji kamshin amarci.".
Tace "Amarya za kayi ba labari?".
Yace "Amaryar dai tadan kanta."
Maryam tace "Rabu da ita Alhaji Wai Kai zata yiwa siyasa, bari mu isa gida kaga kayan da angon ya fara kawo toshi ka gani."
Yace "Ki bari don Allah?".
Ta amsa "Zancen kake so kenan." Ta juya wajen Rahima 'yaruwa kije ki kwanta karki wani wahalar
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment