Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

bakinsa ya gutsura kana ya mika Mata sauran ta karba cikin mamaki, har zata Kai bakinta ta tuna bata san ko waye ba, ko kafin ta dago Kai ya haye dokin ya fara tafiya, ta daga masa hannu tana kiransa da muryar data shake, waigo wan da yayi yasa taga fuskarsa a zahiri ... Ganin ko waye yasa ta nemi yar da rabin gwaibar da ya bata Amma abin mamaki taki faduwa kamar ansa gam an manne gwaibar a hannunta, cikin hanzari ta sake juyowa ko za tayi katarin sake ganin fuskar.. aka yi dace shima ya sake waigowan yana murmushi a gareta, kamar walkiya dokin da Mai dokin suka bace...

Alhamdulillah Hamdan Kaseeran...
A nan littafin RAHIMA na daya yazo karshe. Za mu ci gaba dana biyun insha Allah.
Ina godiya ga Masoyana a duk inda kuke ina muku adduar fatar alkhairi a gareku.

Nayi kuskure ban bada number waya ba a farkon wannan littafi, to ga masu son saye da nemana ta WhatsApp a neme ni a wannan num 08034243456 WhatsApp kawai plss

Masu son kirana Kuma a nemi a wannan num 07036391747


06/09/2020, 19:50 - Anty saliha: ...RAHIMA..doc by Jami

16
Karfe tara na dare sun nutsa cikin hira, har Hjy Suwaiba ta shigo neman shawara wajen Rahima, sun tattauna kan problem din yaron kanwarta data haifa kurma, tayi musu sallama ta tafi da yake Alh a dakinta yake.
Har zasu rufe kofa, Alh. Abbas ya shigo suka gaisa da Rahima kana ya roketa data fita su gaisa da abokinsa da har lokacin yana magiyar son aurenta.
Ta shiga falon ta sallama fuska a murtuke ta gaisheshi, ya amsa yaci gaba da 'yan dabarunsu na maza don ta saki ranta. Rahima ta zauna kamar wata mutum-mutumi,ta rinka mamakin lokacin da ta rayawa zuciyarta amincewa ta auri Alh. Abbas, Lalle da tayi wauta, yes a da can da bata San muhimmancin soyayya ba zata iya zama dashi but a yanzun Kam sai dai yayi hakuri, soyayyar wani ya riga ya fara shiga zucciyarta. Wani wa? Ta tambayi kanta, hhmmm wannan wauta nata da yawa yake, to Wai why take jin son bawan Allah nan da aka mata maganarsa?

Alh Suraj ya gaji ya gyara zama tumbinsa ya Kara bayyana cikin babbar rigarsa yace "Rahima ko don nace ba Zan amince kici gaba da aiki bane yasa ba Kya ra'ayina? Idan wannan ne na canza shawara wallahi, na amince kici gaba da aikinki, gidanki Kuma daban zan aje ki "

Ta gyada Kai "Ko kusa Kar tunaninka ya Kai can, aure ai nufin Allah ne, idan ya kaddaro ba makawa, mu dai ci gaba da adduar zabinsa."
Yace "Lalle kin cika 'yar boko, Baki ce eh ko ah ah ba duk da na fahimci komi, duk mai hankali zai gane inda kika dosa, sai dai na hakura, ban Kuma ji zafi ba saboda baki nuna kwadayin abin hannuna ba, nagode Zan tayaki addua, Ina rokon idan lokacin auren ta taho a kawo mun kati da goron gayyata, Zan m bada gudumuwata matsayin yayan amarya."..
Tace "Godiya nike sosai Allah saka da khairan."
Yace "Ba komi Rahima."

Goma da mintoci har Maryam ta fara barci Rahima ta tashe ta "Barci tun yanzun?"
"Yes tunda ranar hutun kenan da Alhajin ba nan yake ba."
"Kina nufun idan yana nan ba Kya hutawan?"
Ta amsa "kusan hakan ne kina wasa da Alhajin nan da kike gani, wallahi duk ta sangarce, daidai da spoon bai iya dauka da hannunsa ya Kai baki idan ina kusa."
."Su soyayya masu gari."
Maryam ta gyara kwancita "Karki zargeni, ke din wa yasan abunsa za kiyi nan gaba, ya kuka kare da Alh Suraj?"

Rahima ta sanya rigar barcinta kafin ta amsa "Na fada masa gaskiya yai accepting wai sai Kun Kai masa Iv."
Maryam tace "Ko nifa bana amince dashi bane just tsokanarki nike da naga baki da niyyar fidda kowa, yanzun shi Wanda Hajiyar tayi magana ne a fagen?"

Wani irin murmushi da farin cikine suka bayyana a fuskarta, Maryam ta daki kafadarta da matashi tace "Lalle wannan ya samu karbuwa a zuciyarki, fada mini ya kike ji?"

Saida ta kwanta ta tasa kafadarta da matashi tace "Za kiyi mamaki Yaruwa domin nima cikinsa nike, ashe mutum Kan so Wanda bai taba gani ba, ni fa ko sunansa ban sani ba, labarinsa ma not in details naji amma na kagu na kosa in gansa inji yaya zanji ranar dana fara ganinsa?"

Tayi dariya "To ya zaki kwatanta abubuwan da kike ji yanzun da wanda kika ji game da marigayi."

Ta tashi ta zauna "Ai sun Sha banban 'yaruwa, son Rabiu a hankali ya riga shigata kwatankwacin mutum ta dora ruwan zafi bisa wuta, a hankali ya fara dumi, ya kai ga zafi har ya nuna alamun tafasa sai wutar ta mutu, to yadda ya fara zafi hakan ya rinka hucewa yana sanyi a hankali har ya zamto yanzun na hakura, dana tunasa adduar samun rahama nake ci gaba da yi masa kullum, wannan kuwa gaba daya ruwan ya dau zafi, kafin in ankara har ya tafaso ya fantsama koina, zuciyata na kuna, babban abinda ke firgitani addua nike lamarin na kara tsanani, ko yanzu ji nike kamar in rufe ido in gansa a gabana don inga wane irin mutum ne da yai saurin raunana min zuciya?"

Maryam ta gyara "Tirkashi! Babbar magana, Lalle lokaci yayi da ya dace in baki amsar tambayarki akan menene so?

To a iya fahimtata soyayya itace ni'imar mafi daukaka da Ubangiji yaiwa bayinsa baiwarsa, soyayya itace zuciyoyi dunkule ko a cure waje guda, abin nufi idan mutum yaso wani ko wata son nan kesa ko yaushe a kasance cikin tunanin masoyi, rashin damuwa da kowa sai shi/ita, mutum yakan zama bai jin son ji da ganin kowa sai masoyi kamar yadda kika kasance a halin yanzun.

Ba abinda so bai haifarwa, so na sa mutum yai hauka ya zauce, idan zuciyar bata samu abinda take so ba ta Kan fita hayyacinta, tayi rauni wani har sai an hada da addua kafin a sami komawa normal. So kansa mutum yanke hukuncin da bai Dana sani matukar ya shafi masoyin, a cikin lamarin so na hakika babu shakka, ba munafunci ba yaudara, ba karya balle zargi, so nasa masoyi tsananta addua ga Wanda yake so ko da sani ko basa saninsa ba.
Mutum Kan gane ya kamu da son wani/wata ce ta faduwar gaba a duk lokacinda aka ambaci sunan masoyi, ko gani a zahiri, hoto ko murya. Zaki yawaita son ambatonsa ko son kiji ana labarinsa ko hirarsa, zaki rinka jin son sirrinsa maana halinda yake ciki, jin dadin zancensa, tausayi, fadar gaskiya, nisantar karya in har son na gaskiya ne, haka nan zaki rinka yaba kyautarsa komin kankantarsa da son kema kiyi masa alkhairin komin yawansa, zaki so ki kula da al'amurransu ko yaushe, sannan uwa uba akwai kishi tsakanin masoya na gaskiya but ba irin kishin nan Mai haifar da zargi ba saboda da zaran Kun amince da so da kauna tsakaninku, girmamawa, yarda da aminci ne za suyi tasiri a zukatanku.

Ki kula ba kowanne so ne na hakika ba, majority mu kanyi kuskuren fassara shaawa da kalmar so, irin sa za kiga ko an Kai ga aure lokaci kalilan an fara samun problem musamman idan an riga an gusar da sha'awar, hakuri da juna sai yai karanci saboda ba a gina zaman kan tubalin so da kauna na gaskiya ba. Masoya na hakika Kan jure komi don su zauna da juna.

Maryam ta numfasa ta kalli Rahima kina fahimta kuwa?"
Ta amsa "kwarai kuwa, karance-karancenki ya amfana ta wannan bangaren, kinji bayaninki kamar wata marubuciya?"
Tace "Da kenan dana rinka mafarkin zama daya daga cikinsu..
Rahima tace "Ko yanzun kina iya farawa dauko alkalami da takarda ki gani, gashi kina tsaro min zance kamar kina karantawa ba?"
"Rufan asiri don Allah, ai na kwatanta naga ba ci dole na hakura, nan na Kara yarda da batun wani malaminmu cewa rubutu baiwa ce, duk Wanda Allsh yaiwa baiwar hikima da basira yaita gode masa kullum domin a cewarsa koda mutum ya sauke kundin karatu ba lale ya iya rubutu ba, don sai in Allah ya bashi hikimar ne zai rubuta a karanta a fahimta har a sami darasi ciki a amfana, Kinga shiga hurumin da Allah bai kaddaro maka bama shishshigi ne da karanbani in dai ba so kike in rinka satar basirar wasu ba."
"Ah ah a Kan me, zauna matsayin da Allah ya aje ki,in kinyi hakan ma ai baki kyautawa kanki ba ko?"
Maryam ta kyalkyace da dariya "Ban ma ja da nisa ba kin sani, dana gwada naga bai yuwwa bane na hakura, na dai ci gaba da saye Ina karantawa Ina karuwa....

"Karuwa ta wani fannin ba, wani bangaren kam karatun kawai kike don jin dadin labari amma ba Kya daukar darasin komi. Da kina dauka da baki biyewa Hjy Siwaiba kunyi gaba ba, da baki bi nata Kun raba kan yaranku ba, zumunci fa kenan kuke neman yankewa tsakaninsu alhalin Ubangiji yace Duk Wanda ya yanke zumunci bai tare dashi gobe kiyoma, ban da haka, mijin Nan naku fa na iya mutuwa ya barku kowa ta kama gabanta zaman tsakaninku ya farraka, amma yaranku dole suyi zumunci da juna sabili da jininsu daya, ko Allah ya karbi ran daya daga cikinku takalihun yaran ya koma hannun dayanku dole, ko Kuma ma ya kasheku gaba dayanku, mijin naku ya auro wasu su o suci gajiyar yaran da kuke tinkahon Kun haifa, kinsan dai ba yadda Allah bai iya juya lamarinsa ba don haka ake son mu kasance masu hangen nesa, idan ka ciza ka hura, idan kace zaka biyewa zuciya sai ya kaimu ta baro tunda batavda Kashi, shyasa ake son mu rinka adduar Allah yasa mufi karfinta, Kar shaidan ya rinjayeta, ya karfafa mana imaninmu, Ni da zanga dayan marubutanmu ko dana nunaki cikin days daga cikin makarantarsu amma masu karatu suji dadin labari kawai ba daukar darasi balle ku amfana."

Ta bude baki "Tafdijan Rahima yau kin gama dani tsaf...
"No ba haka bane 'yaruwa, wajibine in taroki idan naga Zaki ksuce hanya in fada miki gaskiya komin dacinta, marubutan fa suna yi don gyaran tarbiyyarmu dana zuriyyarmu don al'ummanmu su samu nagarta mu gyara rayuwar duniya dana lahira."

Maryam tayi kasake tana saurarenta, yes Rahima gaskiya take fada mata ba karya ko kadan, Ina amfanin badi ba rai?

Wajibi ta taho ta gyara halinta dana zamantakewarta da abokiyar zamanta ko tace makwabciyar ta inji Rahima,ko bata kyautata mata don komi ba tayi don samun ladan, shin sai nawa ma wani lalura ke tasowa daya daga cikinsu Wanda suke takamar shi ya ajiyesun bai nan bai kusa balle ya magance musu? Su jawa suka taimaki juna musamman lalurar rashin lafiya maigidan na can bai ma sani ba sai ya dawo yaji labari? Idan har Ubangiji zai jarabci bawansa ba mu san ta hanyar da jarabawar zata zo mana ba kuwa ya dace mu saduda mu zauna lafiya da juna muyi hakuri tunda ba wace ke zaune kan wata, babu mai korar wata sai in kaddara ta gitta Wanda ba a fata, kowacce da halinta take zaune kota bangaren mijin ne, to wahalar da Kai na menene?

Me zai hana suyi hakuri da juna har mai hadawa ya raba, ko tunanin mutuwa ya isa katsewa duk mai imani hanzari, rayuwar guda nawa take mutum ya tsaya Yana batawa kansa lokaci, duniyar guda nawa take, dubi yadda Allah ya dauke Rabiu farad daya aka raba Rahima da mijin da suke zaune lafiya, yaronta ya shiga maraici ko shi bai isa bawa tsoron Allah ba? Wannan duniyar da ba matabbata ba? Hawaye suka rinka gangarowa zuwa kuncinta.
Rahima ta gani ta gigizata cikin damuwa "Lafiya kuwa?"

"Hawayen godiyar Allah ne da ya kubutar dani ya ganar dani ya hana min biyewa sharrin zuciya, wallahi ba domin zuwanki na na kuduri aniyar mugun zama za muci gaba da yi nida Suwaiba don nayi sakacin barin shaidan ya shiga zuciyata ya fara dora min tubalin gina katangar da zai ci gaba da dora bulo Yana zugani Ina hauka, yanzun nasihohinki sunsa duk nayi sanyi na saduda na hakura na barwa Allah dukkan lamurrana, nayi imanin tunda bana nufun kowa da sharri zai kareni idan an nufoni, zai Kuma yi min sakayya muddin aka zalunceni."

Rahima tayi murmushi "Alhamdulillah tsarki ya tabbata ga sarkin sarakuna, munyi salati ga Manzonsa Masoyinsa Muhammad SAW, mun godewa Allah da ya baki ikon ruguje wannan ginin, Ubangiji ya Kara Mana kariya da kayangar karfe da shaidan la'ananne ya karemu daga dukkan sharrin abin ki. Abinda Nike son ki gane dukkanmu Nan masu laifi ne kullum cikin daukar zunubi muke amma Ubangiji ya Kan yafe mana idan mun roki gafararsa, wani zunubin ma ko bamu roka ba sai ya shafe mana kasancewarsa Mai tausayi da jinkan bayinsa, to kai waye da zaka ce ba zaka yi hakuri da wasu al'amurra dake faruwa da Kai ba, balle ka yafe, kana ajizi kaskantacce? Haba don Allah ki zage damtse ki bautawa Ubangijinki, ki kyautatawa mijinki, kiyi tarbiyyar 'ya'yanki, kiyi zumumci domin Allah, ki kyautatawa iyaye da yanuwa kiga irin daukakar da Allah zai miki."

Maryam taja numfashi ta rike hannyn Rahima "Wallahi naji na amince na dauka na Kuma gode da nasihohinki 'yaruwa Allah ya saka miki da khairan. Yanzun kenan mun shafe chapter mutumin naki?".
Ta zabura ta mike "Ina ai hankalin rabuwa yayi, Ina nan, Ina can, yanzun dai kiyi kwanciyarki don sulusin dare yayi, Sallah zanyi da adduoi na musamman in roki ya Azeez ya nuna min shi ko mafarki ne don hankalina ya kwanta."

Maryam ta gyara kwanciya " In Kun hadu Ina Mika gaisuwa da jinjina masa saboda ya sace min zuciyar kanwata ya Kuma tsamota daga duhun jahilcin rashin sanin menene *so*


Ta shifa toilet ta dauro alwala ta shumfiea sallaya ta fuskanci alkibla tare da natsuwa da kaskantar da Kai domin ganawa sa Mai rufan babu dogara, Mai amsa adduar bayinsa babu shamaki ...


Ta dade tana zuba adduointa, ta rufe da salatin Manzon tsira, ata kwanta ba saida sallaci asubah kana tayi matashi da hannunta na dama ta bingire bisa sallayar.



Hanyace data kasu har uku, ta rasa wace zata bi, dama,hagu ko tsakiya? Ta yanke shawarar bin hanyar dake damanta, 'yar siririyar hanyar cike take da itatuwa da ciyayi Korra shataf, bata yi nisa ba sai gata gaban wani tafkeken kogi Mai shakare da wasu garai-garain ruwa masu kalar sararin sama, nan ta gane baby hanyar wucewa kenan.

Ta juyo cikin hanzari da niyyar ta koma baya nan ta rikice dalilin hanyar ta rikide ta hade danyen ciyawa da itatuwa ga ruwa male-male ta ko' Ina, daga saman bishiyoyin wasu irin kyawawan tsuntsaye ke kuka tamkar suna busa sarewa, sanyin tafkin nan ya fara ratsata, sanyi ya kadata ta shiga makyarkyata, hakan yasa ta waige-waigen da tunanin ratsawa ta cikin ruwan ta fita wannan wajen, tsoro ya kamata, nan take ta daga hannayenta sama ta fara rokon Maiduka ya kawo mata dauki..

Cikin ikonsa Allah sarkin sarauta sai taga wani mashahurin haske ta ko'ina, wani doki Mai fuka-fuki da ya ratso ta cikin hasken nan a guje ya sauko daf da ita. Jikin dokin ba irin dawakan data sani bane, wannan ilahirin jikinsa kalar azurfa ne, gashin bayansa gazar-gazar da kwarar idanunsa ne kawai bakin kirin.
Tsananin ganin wannan halitta daya cikata yasa bata lura da mutumin dake Kan dokin ba, bata ankara ba taji an dagta sama an dorata bisa dokin nan ya tashi sama suna tafiya tamkar wasu tsuntsaye, basu dade ba taga sun sauka daf da kofar wani farin gida gewaye da furanni, hancinta ya shaki wani hadadden kamshin data rasa inda yake fitowa, kamar tafiyar slow motion ta tsinci kanta cikin wani lambu cike da kayan marmari, ta mika hannu don ciro nunanniyar goba tsawonta bai Kai ga iccen ba, Mai dokin Nan ne ya matso yasa hannunsa ya ciro goban Nan har zai Mika Mata sai dokin yai haniniya ya kada fukafukinsa sai ya fasa bata Saida ya saka a bakinsa ya gutsura kana ya mika Mata sauran ta karba cikin mamaki, har zata Kai bakinta ta tuna bata san ko waye ba, ko kafin ta dago Kai ya haye dokin ya fara tafiya, ta daga masa hannu tana kiransa da muryar data shake, waigo wan da yayi yasa taga fuskarsa a zahiri ... Ganin ko waye yasa ta nemi yar da rabin gwaibar da ya bata Amma abin mamaki taki faduwa kamar ansa gam an manne gwaibar a hannunta, cikin hanzari ta sake juyowa ko za tayi katarin sake ganin fuskar.. aka yi dace shima ya sake waigowan yana murmushi a gareta, kamar walkiya dokin da Mai dokin suka bace...

Alhamdulillah Hamdan Kaseeran...
A nan littafin RAHIMA na daya yazo karshe. Za mu ci gaba dana biyun insha Allah.
Ina godiya ga Masoyana a duk inda kuke ina muku adduar fatar alkhairi a gareku.

Nayi kuskure ban bada number waya ba a farkon wannan littafi, to ga masu son saye da nemana ta WhatsApp a neme ni a wannan num 08034243456 WhatsApp kawai plss🙏🏿

Masu son kirana Kuma a nemi a wannan num 07036391747

Kasancewar littafin RAHIMA na sayarwa ne masu son saye Acccnt number mu shine 0598537268
GT Bank.


07/09/2020, 21:32 - Anty saliha: ...ˆRAHIMA..doc by Jami

17

Ta farka cike da mamakin murdadden mafarkin da tayi, cikin gigita ta rinka karanto adduar shugaban ayoyin alqur'ani kana ta dora da adduar neman tsari daga mugun mafarki, tsorene ya hanata jin sautin muryar Maryam da take karatun qu'ani can gefe daya, ta kasa yin wani kwakwkwaran motsi, da kyar ta tashi ta nufi toilet ta sake dauro alwala ta gabatar da sallar dhuha sannan itama ta dauko qur'anin ta fara karatu .
Basu tashi Kan sallayarsu ba saida suka dauki dogon lokaci don sun saba tyn suna gida duk bayan sallar asubah sai sunyi karatun sa'annan su dora sa azkhar din safe don kwadayin dacewa da lokacin amsar addua.

Goma daidai sunyi wanka sun kintsa tsaf, Rahima ta kalli Maryam 'Ba zanyi breakfast ba, gida zan koma yanzun nasan Umma na zuba idon ganin na koma da wuri."

Ta kura mata ido "Akwai abinda ke damunki duk kin canza wayewar garin nan, ko baku hadu da surukin nawa a mafarki bane?"

Ta koma ta zauna jiki babu kwari kamar wace aka zare mata lakka tace "Ke dai bari 'yaruwa, nayi adduoi na roki Allah yadda kika sani but Wanda na gani cikin mafarkina... Kai!!! Ta girgiza Kai, na firgita wallahi."

Maryam ta kalleta "Shakka kike?"

Ta kada Kai "No mamaki nike ji da fargaban mafarkin nawa ya zama real."
Maryam ta kalleta cikin damuwa "Kinata kwanare, shin wa kika gani ne?"
Rahima ta jinjina "Hhmmmm bana jin zaki amince da abinda zan fada miki."

"Me zai hanani yarda after all Allah muka roka Ya amsa mana mene na al'ajabi? Ni wallahi ko waye na yarda na amince shi dinne zabin Allah."

Ta kauda Kai tayi shiru na dakika kana tace.. Maryam *Ya Haseeb* fa na gani a mafarkina."

Duk da dakewan da tayi itama taji mugun mamaki ta buga kirji "HASEEB! Ba dai Dr Haseeb wan Rabiu ba?".
Hawaye suka ciko a idanunta yayinda ta amsa " Shi din ne, me hakan ke nufi Maryam?"

Ta taso ta matso kusa da ita ta dafata cikin rarrashi "kwantar da hankalinki za kiyi mu saurari Hajiya muji nata manufar amma a hakikani mafarkinki gaskiya ne,zaiyi wuya aure bai shiga tsakaninku dashi ba Ina ganin tun farko shi Hajiyar ma ke nufi."

Cikin sheshekar kuka ta dago "In hakura dame? Haba Ina! Idan har shi take nufi na fasa amsa batunta, ba Zan iya zama dashi matsayin miji ba."

"Kina son zancen yai tsawo kenan, shikenan mu bari har zuwa sauran kwanaki ukun data diba miki mu gani, mu ci gaba da addua Allah ya tabbatar mana da khairan"

Hankalinta a tashe ta shiga tayi sallama da Hjy Suwaiba ta wuce gida.
Nan da Nan Umman ta gane akwai abinda ke damunta tana cikin matsala saboda tunda ta shigo ba walwala a tareda ita, abin mamaki ko Abdul bata tambaya ba.
Har zuwa karfe biyar na bayan la'asar babu canji a tareda Rahima hakan yasa a matsayinta na uwa Umma ta kira cikin daki ta yambayeta meke damunta.

Nan take ta musa cewa babu komi, Umman ta kalleta cikin damuwa tace "Shikenan tunda ban isa ki fada min matsalarki ba."

Rahima ta saka mata kuka tace "Idan ma akwai matsala nina janyowa kaina Umma imda nayi aurena tuni da ban shiga kangin Nan ba, yanzun ya zanyi da Raina?".

Umma ta Kara rudewa "Ya za ayi in baki amsa tunda ban san damuwar taki ba?"

Da yake sun saba basu boye Mata komi ta zayyane mata labarin mafarkinta da yadda suka yi da Maryam"

Ta dade bata iya magana saboda zancen ya daketa itama amma ta daure ta kalli 'yarta "To in banda shirmenki mene na tada hankali harda koke-koke? Aure ba nufin Allah bane, matar mutum kabarinsa, kin taba ganin mijin da bai auri matar da ba tasa ba? Idan Allah ya kaddaro Haseeb mijinki ne babu Wanda ya isa ya hana, don haka ki natsu ki barwa Allah muga abinda zaiyi tukunna."

Tasa handkerchief ta share hawayen dake fitowa tace "Ba abinda ke damuna irin alkawarin dana daukarwa Hajiya na amince da zabinta ba tare da tunanin wai shi take nufi ba, haba Umma ya za ayi wannan danyen aikin?"

Umma ta kalleta "Ta yaro kyau take bata karko, tashi jeki share hawayenki, Zan nemi Hajiyar mu tattauna mai yuwwa in har hakanne."

Tace "Don Allah Umma idan zaki, ki kwashe kayan Abdul ki Kai musu na hakura dashi, don ina ganin ita kanta Hajiyar sabida shi ta yanke hukuncin Nan, watau Kar in auri wani can daban in tafi dashi."

Ta bude baki tana mamakin kalaman diyarta, lakle sai sunyi da gaske, tace "To Ina Kuma ruwan Abdul da za ayi masa mai gaba daya, ki bari zan maidashi gidansu idan lokaci yayi Kuma don Allah kar in sake jin kin zargi Hajiya kinsan ba zata cuceki ba, ko alama bai dace kiyi furucin da kika yi ba."


Ta kwana ta yini cikin zulumi da fargaba abinda zau faru. Gaba daya komi yai mara dif, brain dinta ya hargitse, zuciyarta ta kasa sarrafa komi sai tunanin yadda akayi ta amince da so da kaunar wanda bata taba gani ba, to ai yanzun ta daina ikrarin haka, shin ba Ya Haseeb ne ta tsunduma cikin kogin soyayyarsa ba?
Satin data dauka tana adduoi suka cika amma ta kekasa kasa taki komawa gidan Hjy Kaltume, bata aika an dauko Abdul din ba ma, ko da tanada tabbacin Umma ta ziyarci Hajiyar amma bata ce mata komi, ita da Baffa sun sa mata ido sai wani lallabata suke, ta share kowa a gidan hatta Maryam data taho ta rasa gane kanta.

Babu Wanda bai san asibitin nan mai suna *HASEEB MEDICAL CENTRE* ba, ba don komi asibitin tayi fice ba sai domin kwarewan babban likitan(CMD). Dr Haseeb Junaid Galadanci dogo ne mai dan jiki, launin fatar jikinsa chocolate ne hakan yasa tsakar mallacin da aka yi masa suka fito sosai a gefen kumatunsa a 'yar doguwar fuskarsa wadanda suka kara fito da kyaunsa na zahiri.

Yana da zafin nama sosai, hanzarin nasa ya dace da irin aikinsa watau kwararren likitan da ya shahara yai suna bangaren daya shafi rashin lafiyar kwakwalwa, kashin baya da halittun da suka danganci wadannan ababe masu matukar muhimmanci a jikin Dan Adam
Dr H.J.G yadda ake kiransa yasan hallitar kwakwalwar bil adama tamkar yadda yasan tafin hannunsa, kazaliza don ya
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment