Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gidan 'yaruwa...

Bata sami damar ba 'yaruwar nata labarin labarin dake cinta ba saboda ta taras da gidan nasu a hargitse, itada Uwargidanta basa ko ga maciji, karin abin haushi harda raba Kan 'ya'yansu kowa harkarta take da diyanta. Ran Rahima ya baci,hankalinta yai matukar tashi, bata saurari Maryam don ita ta dorawa lefin abubuwan dake faruwa.
Maryam tace "Banyi tsammanin zaki ki fahimta ta ba Rahima, ki duba irin bautar dana yiwa matar Nan da yayanta tun zuwana gidannan tun kafin in haihu na kula da yaranta, Ina bata girmanta, yanzu kuwa na gaji don shiru ba tsoro bane gudun fitina nike yi, yanzun kuwa ban damu ba aje ayi tayi idan tace kule zance cas! Ba abinda zata nuna min, idan tana takama da miji ne nima dashi nike, idan yarane nima ina dasu to sai me? Haka siddan mace ta isheni ta gallabeni tamkar ita ta aje Ni?
"Hhmmmm inji Rahima "Maryam don Allah numfasa ki saurareni da kyau, ya za ayi ki taho ki taras da mace da mijinta da yara kice zaki nuna mata iko? Mijinta fa kika aure...
"Don na auri mijinta sai me, don ita kadai aka halilto shi ne, mijin mace hudu yake, don me idan ta yayo shararta bata zubewa a kansa sai nawa? To na gaji da rainin wayo, ya isa haka."

Rahima tace "Ban ce bata da irin nata laifin ba don bai yiwwa ace koda yaushe mutum guda ne ke da laifi da duk magana ta tashi, dole ace tanada irin nata problem, kawai so nike ki fahimci bai kamata ki biye mata duk ku haukace koma ince ku kafirce gaba daya ba, haba 'yaruwa a matsayinki na musulma ki tsiri gaba da 'yaruwarki musulma, makwabciyarki Kuma?"

Ta kada Kai "To ya kike son inyi, ita ta fara, sau nawa Ina gaisheta tana shareni tun ina daurewa nace mu zuba mu gani, ko abinci na aika mata bata ci sai ta maido min ta wanke tukunya ta dora wani ta ci, naga bai dau wani mataki ba bayan ya gani da idonsa, nace tunda haka ne bari nima in maida martani tunda ni ba shegiya bace da ubana, ta hana yaranta shigowa dakina balle suyi wasa da yanuwansu, tun Ina damuwa na dake na fara ramuwar gayya Wanda tafi gayyar zafi inji hausawa."

"Kash! Inji Rahima, da baki biye mata ba, me zaisa ki bar shaidan ya samu gurbin gina katangarsa a zuciyarki, don me ba za kiyi aiki da ilmin da Allah ya hore miki ba ki nuna mata abubuwan da take yi tsagwaron jahilici ne?"

Ta tabe baki "Kishi da jahilar mace ko masifa, duk yadda kika so ki fahimtar da ita ba zata taba ganewa ba, kullum inda kika dosa daban inda ta dosa daban, kina gabas tana yamma, to yaushe zan bata lokacina a aikin banza."
Rahima tace "Da kike kiranta jahila ba gara ita dake ba? Laifinta ragagge ne don dama bata da sanin, ke kuwa kin sani kin take sanin laifi biyu kenan, to wai shi maigidan bai san abubuwan dake faruwa cikin gidansa tsakanin iyalinsa ba?"

"Kwarai ya sani Mana, cewa yayi in dominsa muke muje mu kashe kanmu ba ruwansa tunda yai kokarin sulhunta mu Abu ya faskara."

Taja tsaki "You see, ya maisheku mahaukata wadanda basu San ciwon kansu ba, tun anan bai isa ku hankalto ba? Shi da kuke kishin dominsa bai damu ba Wai ma in mutuwa za kuyi ku mutu, eh lalle yace muku haka, in Kun kashe kanku ai bashi kuka yiwa asara ba illa iyaye, 'ya'ya da 'yanuwanku, baida asara Kona miyaun barci iyaka ya auri wasu ya zuba a rufe chapter dinku ku bar 'ya'ya da abun kunya."

Maryam ta juyo "To naji ustaziyar zamani, zanyi nazari in kwatanta in gani, idan da canji in ci gaba, idan babu riba Zan watsar mu ci gaba da zaman doya da manjan don babu macen da zata takani in kyale."

Rahima tace" Allah ya ganar damu baki daya, Kinga da na taho da niyyar kwana amma na fasa don ba zan iya zama gidan da ake gaba ba "

Nan da nan ta marairaice "Don Allah yi hakuri na bari, muyi kwanciyarmu.".
Ta nufi kofa "Ba zan tabbatar da kin bari ba sai munje har dakinta na gaisheta tukunna, mu dawo in baki labarin dalilin zuwana."
Da kyar ta amince suka tafi, suka sallama ta amsa,suka shiga ciki.
Tayi mamakin ganin 'yaruwar kishiyarta da suka shafe sati biyu suna gaba da juna, da ita kanta. Rahima ta gaisheta tamkar bata san me ke faruwa ba ta amsa, suka Dan jima suna kame-kamen magana, zuwa can Nafi'u yaron da Maryam ke goyo ya nufi gaban Tv ta ya dauko wata flower vase na glass, uwar tayi saurin tashi ta amsa ta bubbugeshi.
Hjy Suwaiba ta kalleta "Meye na dukan wannan Dan yaron kinada hankali kuwa?
Ta amsa "Ba kiga barnar da zai yi bane?".
Hjy Suwaiba ta dauki vase din ta sake mikawa yaron "Idan ya fasa naki ne?
Maryam tayi shiru
Rahima tayi murmushi "Nima shi na gani yaro da kayan uwarsa.".
Hjy Suwaiba tace "Kila so take in bar mata danta ko daman Walida ce tawa, ta rike kayan barnarta kin ganshi mummuna."

Maryam ta kalli Rahima "Kinji ta ko? Wallahi tunda aka haifeshi take tsangwamarsa Wai Walida ta fishi kyau ko Ina kyaun da katon hanci oho._
Hajiya Suwaiba tayi dariya " munji ba komu muma da kayan gyara, naki a sa masa 'yankunne da janbaki mu gani."
"Ah ah Hjy gaskiya cun fuskar tayi yawa, ki dai rike taki mu rike namu."
A haka suka ci gaba da wasa da dariya har kusan magriba sannan suka koma dakin Maryam suka yi Sallah. Suna idarwa Hjy Suwaiba ta aiko musu da kulolin abinci wai a kawowa Rahima, da gani abincin yafi karfin ita kadai dole suka ci tare da Maryam din ita ta fasa dora tukunya. Rahima ta kalleta tace " Don Allah da kika shiga dakinta, kikai Mata magana gashi har kinci abincinta me ya rage a jikinki? Inda za a bude Miki file dinki yau kiga dimbin ladan da kika samu da ba zaki yards ki kara yin gaba ba koda wasa."
"Wallahi Kuma Nima sai naji wani irin dadi a Raina, duk kuncin da nike ji a zuciyata ya yaye na yarda sai kaso abu ya dameka yake damunka din."..

Rahima tace abinda har yanzun mu mata bamu gane ba kenan, mu ke creating ma kanmu problems din da zasu dawo su dame mu, namiji ba ruwansa, sai un har kunyi dace da Mai kula ne zai fahimci halinda kuke cikin, wani ko ya gani ba abinda ya damesa tunda yawancinsu sunfi son haka, su tara Mata cikin gida ayita adawa a kansu, ya fito Yana jin dadi da hura hanci ya rinka ikrarin sabida tsananin son da kuke masa kishi ya hanaku zaman lafiya. Wani shaidanin zaman lafiyar ce bai so, yana ganin kun hada kai sai ya kasa sukuni ya shiga zargi da fargaban shifa sai yadda kuka yi dashi kenan domin da wuya daya ta yarda a ci amanar guda shi kuwa bai son hakan, yafi son ya zama bakin ganga, ya buga nan, ya Fadi gaibu can, yai munafunci a nan sai kunada kyakkyawar kula zaku gane in ba haka ba sai kuga kowacce ta fito tana kuri da fankamar ita yafi so.
Idan anyi dace da irin mazan da suka san ciwon kansu sai kiga su zaman lafiyar suke matukar bukata a gidajensu, idan Allah yasa ya dace da matan kwarai sai sai ya kula dasu matuka ya rinka kyautata musu har kiji danginsa na fadin sun mallakeshi sun gama Mana dashi alhalin jin dadin zaman lafiya da kwanciyar hankalin da yake samu dasu ya haifar da hakan. Kin ganni nan Maryam bana shakkar zama da kowacce irin mace Allsh zai hadani da ita matsayin kishiya."

Ta gatsina baki "Karki cika baki Rahima, me kika sani game da zama da kishiya, kowacce mace fa da nata salon munafunci da kisisinar data kware, idan an debe masu shige-shigen gidan bokaye da malamai don wata ba zata zauna dake da bakin hura wuta kadai ayi kishi ba."
Tayi murmushi "Aunty Maryam kenan ai ba wani cika baki, in har hakane Kuma Ina iya ce miki yes na cika baki ne domin nima da nawa baiwar da Allah yai min, ba wani abu bane da ya wuce kakkarfar madogora."

Ta kada Kai "Ko Zan San wane irin madogara ne?"

Ta girgiza Kai "Nima ki bini bashi zuwa nan gaba in har Allah ya kaddareni da auren kiga matsayins zamana a gidan mijin da wajen shi kansa mijin tukunna, yanzun dai muyi sallar isha'i ki bani amsar tambayata ta tuntuni don Ina jin ga wannan karon na fada kogin nan na so da kauna sai dai ko za ku iya tsamo ni?"
06/09/2020, 19:35 - Anty saliha: ...RAHIMA...doc by jami

16
Karfe tara na dare sun nutsa cikin hira, har Hjy Suwaiba ta shigo neman shawara wajen Rahima, sun tattauna kan problem din yaron kanwarta data haifa kurma, tayi musu sallama ta tafi da yake Alh a dakinta yake.
Har zasu rufe kofa, Alh. Abbas ya shigo suka gaisa da Rahima kana ya roketa data fita su gaisa da abokinsa da har lokacin yana magiyar son aurenta.
Ta shiga falon ta sallama fuska a murtuke ta gaisheshi, ya amsa yaci gaba da 'yan dabarunsu na maza don ta saki ranta. Rahima ta zauna kamar wata mutum-mutumi,ta rinka mamakin lokacin da ta rayawa zuciyarta amincewa ta auri Alh. Abbas, Lalle da tayi wauta, yes a da can da bata San muhimmancin soyayya ba zata iya zama dashi but a yanzun Kam sai dai yayi hakuri, soyayyar wani ya riga ya fara shiga zucciyarta. Wani wa? Ta tambayi kanta, hhmmm wannan wauta nata da yawa yake, to Wai why take jin son bawan Allah nan da aka mata maganarsa?

Alh Suraj ya gaji ya gyara zama tumbinsa ya Kara bayyana cikin babbar rigarsa yace "Rahima ko don nace ba Zan amince kici gaba da aiki bane yasa ba Kya ra'ayina? Idan wannan ne na canza shawara wallahi, na amince kici gaba da aikinki, gidanki Kuma daban zan aje ki "

Ta gyada Kai "Ko kusa Kar tunaninka ya Kai can, aure ai nufin Allah ne, idan ya kaddaro ba makawa, mu dai ci gaba da adduar zabinsa."
Yace "Lalle kin cika 'yar boko, Baki ce eh ko ah ah ba duk da na fahimci komi, duk mai hankali zai gane inda kika dosa, sai dai na hakura, ban Kuma ji zafi ba saboda baki nuna kwadayin abin hannuna ba, nagode Zan tayaki addua, Ina rokon idan lokacin auren ta taho a kawo mun kati da goron gayyata, Zan m bada gudumuwata matsayin yayan amarya."..
Tace "Godiya nike sosai Allah saka da khairan."
Yace "Ba komi Rahima."

Goma da mintoci har Maryam ta fara barci Rahima ta tashe ta "Barci tun yanzun?"
"Yes tunda ranar hutun kenan da Alhajin ba nan yake ba."
"Kina nufun idan yana nan ba Kya hutawan?"
Ta amsa "kusan hakan ne kina wasa da Alhajin nan da kike gani, wallahi duk ta sangarce, daidai da spoon bai iya dauka da hannunsa ya Kai baki idan ina kusa."
."Su soyayya masu gari."
Maryam ta gyara kwancita "Karki zargeni, ke din wa yasan abunsa za kiyi nan gaba, ya kuka kare da Alh Suraj?"

Rahima ta sanya rigar barcinta kafin ta amsa "Na fada masa gaskiya yai accepting wai sai Kun Kai masa Iv."
Maryam tace "Ko nifa bana amince dashi bane just tsokanarki nike da naga baki da niyyar fidda kowa, yanzun shi Wanda Hajiyar tayi magana ne a fagen?"

Wani irin murmushi da farin cikine suka bayyana a fuskarta, Maryam ta daki kafadarta da matashi tace "Lalle wannan ya samu karbuwa a zuciyarki, fada mini ya kike ji?"

Saida ta kwanta ta tasa kafadarta da matashi tace "Za kiyi mamaki Yaruwa domin nima cikinsa nike, ashe mutum Kan so Wanda bai taba gani ba, ni fa ko sunansa ban sani ba, labarinsa ma not in details naji amma na kagu na kosa in gansa inji yaya zanji ranar dana fara ganinsa?"

Tayi dariya "To ya zaki kwatanta abubuwan da kike ji yanzun da wanda kika ji game da marigayi."

Ta tashi ta zauna "Ai sun Sha banban 'yaruwa, son Rabiu a hankali ya riga shigata kwatankwacin mutum ta dora ruwan zafi bisa wuta, a hankali ya fara dumi, ya kai ga zafi har ya nuna alamun tafasa sai wutar ta mutu, to yadda ya fara zafi hakan ya rinka hucewa yana sanyi a hankali har ya zamto yanzun na hakura, dana tunasa adduar samun rahama nake ci gaba da yi masa kullum, wannan kuwa gaba daya ruwan ya dau zafi, kafin in ankara har ya tafaso ya fantsama koina, zuciyata na kuna, babban abinda ke firgitani addua nike lamarin na kara tsanani, ko yanzu ji nike kamar in rufe ido in gansa a gabana don inga wane irin mutum ne da yai saurin raunana min zuciya?"

Maryam ta gyara "Tirkashi! Babbar magana, Lalle lokaci yayi da ya dace in baki amsar tambayarki akan menene so?

To a iya fahimtata soyayya itace ni'imar mafi daukaka da Ubangiji yaiwa bayinsa baiwarsa, soyayya itace zuciyoyi dunkule ko a cure waje guda, abin nufi idan mutum yaso wani ko wata son nan kesa ko yaushe a kasance cikin tunanin masoyi, rashin damuwa da kowa sai shi/ita, mutum yakan zama bai jin son ji da ganin kowa sai masoyi kamar yadda kika kasance a halin yanzun.

Ba abinda so bai haifarwa, so na sa mutum yai hauka ya zauce, idan zuciyar bata samu abinda take so ba ta Kan fita hayyacinta, tayi rauni wani har sai an hada da addua kafin a sami komawa normal. So kansa mutum yanke hukuncin da bai Dana sani matukar ya shafi masoyin, a cikin lamarin so na hakika babu shakka, ba munafunci ba yaudara, ba karya balle zargi, so nasa masoyi tsananta addua ga Wanda yake so ko da sani ko basa saninsa ba.
Mutum Kan gane ya kamu da son wani/wata ce ta faduwar gaba a duk lokacinda aka ambaci sunan masoyi, ko gani a zahiri, hoto ko murya. Zaki yawaita son ambatonsa ko son kiji ana labarinsa ko hirarsa, zaki rinka jin son sirrinsa maana halinda yake ciki, jin dadin zancensa, tausayi, fadar gaskiya, nisantar karya in har son na gaskiya ne, haka nan zaki rinka yaba kyautarsa komin kankantarsa da son kema kiyi masa alkhairin komin yawansa, zaki so ki kula da al'amurransu ko yaushe, sannan uwa uba akwai kishi tsakanin masoya na gaskiya but ba irin kishin nan Mai haifar da zargi ba saboda da zaran Kun amince da so da kauna tsakaninku, girmamawa, yarda da aminci ne za suyi tasiri a zukatanku.

Ki kula ba kowanne so ne na hakika ba, majority mu kanyi kuskuren fassara shaawa da kalmar so, irin sa za kiga ko an Kai ga aure lokaci kalilan an fara samun problem musamman idan an riga an gusar da sha'awar, hakuri da juna sai yai karanci saboda ba a gina zaman kan tubalin so da kauna na gaskiya ba. Masoya na hakika Kan jure komi don su zauna da juna.

Maryam ta numfasa ta kalli Rahima kina fahimta kuwa?"
Ta amsa "kwarai kuwa, karance-karancenki ya amfana ta wannan bangaren, kinji bayaninki kamar wata marubuciya?"
Tace "Da kenan dana rinka mafarkin zama daya daga cikinsu..
Rahima tace "Ko yanzun kina iya farawa dauko alkalami da takarda ki gani, gashi kina tsaro min zance kamar kina karantawa ba?"
"Rufan asiri don Allah, ai na kwatanta naga ba ci dole na hakura, nan na Kara yarda da batun wani malaminmu cewa rubutu baiwa ce, duk Wanda Allsh yaiwa baiwar hikima da basira yaita gode masa kullum domin a cewarsa koda mutum ya sauke kundin karatu ba lale ya iya rubutu ba, don sai in Allah ya bashi hikimar ne zai rubuta a karanta a fahimta har a sami darasi ciki a amfana, Kinga shiga hurumin da Allah bai kaddaro maka bama shishshigi ne da karanbani in dai ba so kike in rinka satar basirar wasu ba."
"Ah ah a Kan me, zauna matsayin da Allah ya aje ki,in kinyi hakan ma ai baki kyautawa kanki ba ko?"
Maryam ta kyalkyace da dariya "Ban ma ja da nisa ba kin sani, dana gwada naga bai yuwwa bane na hakura, na dai ci gaba da saye Ina karantawa Ina karuwa....

"Karuwa ta wani fannin ba, wani bangaren kam karatun kawai kike don jin dadin labari amma ba Kya daukar darasin komi. Da kina dauka da baki biyewa Hjy Siwaiba kunyi gaba ba, da baki bi nata Kun raba kan yaranku ba, zumunci fa kenan kuke neman yankewa tsakaninsu alhalin Ubangiji yace Duk Wanda ya yanke zumunci bai tare dashi gobe kiyoma, ban da haka, mijin Nan naku fa na iya mutuwa ya barku kowa ta kama gabanta zaman tsakaninku ya farraka, amma yaranku dole suyi zumunci da juna sabili da jininsu daya, ko Allah ya karbi ran daya daga cikinku takalihun yaran ya koma hannun dayanku dole, ko Kuma ma ya kasheku gaba dayanku, mijin naku ya auro wasu su o suci gajiyar yaran da kuke tinkahon Kun haifa, kinsan dai ba yadda Allah bai iya juya lamarinsa ba don haka ake son mu kasance masu hangen nesa, idan ka ciza ka hura, idan kace zaka biyewa zuciya sai ya kaimu ta baro tunda batavda Kashi, shyasa ake son mu rinka adduar Allah yasa mufi karfinta, Kar shaidan ya rinjayeta, ya karfafa mana imaninmu, Ni da zanga dayan marubutanmu ko dana nunaki cikin days daga cikin makarantarsu amma masu karatu suji dadin labari kawai ba daukar darasi balle ku amfana."

Ta bude baki "Tafdijan Rahima yau kin gama dani tsaf...
"No ba haka bane 'yaruwa, wajibine in taroki idan naga Zaki ksuce hanya in fada miki gaskiya komin dacinta, marubutan fa suna yi don gyaran tarbiyyarmu dana zuriyyarmu don al'ummanmu su samu nagarta mu gyara rayuwar duniya dana lahira."

Maryam tayi kasake tana saurarenta, yes Rahima gaskiya take fada mata ba karya ko kadan, Ina amfanin badi ba rai?

Wajibi ta taho ta gyara halinta dana zamantakewarta da abokiyar zamanta ko tace makwabciyar ta inji Rahima,ko bata kyautata mata don komi ba tayi don samun ladan, shin sai nawa ma wani lalura ke tasowa daya daga cikinsu Wanda suke takamar shi ya ajiyesun bai nan bai kusa balle ya magance musu? Su jawa suka taimaki juna musamman lalurar rashin lafiya maigidan na can bai ma sani ba sai ya dawo yaji labari? Idan har Ubangiji zai jarabci bawansa ba mu san ta hanyar da jarabawar zata zo mana ba kuwa ya dace mu saduda mu zauna lafiya da juna muyi hakuri tunda ba wace ke zaune kan wata, babu mai korar wata sai in kaddara ta gitta Wanda ba a fata, kowacce da halinta take zaune kota bangaren mijin ne, to wahalar da Kai na menene?

Me zai hana suyi hakuri da juna har mai hadawa ya raba, ko tunanin mutuwa ya isa katsewa duk mai imani hanzari, rayuwar guda nawa take mutum ya tsaya Yana batawa kansa lokaci, duniyar guda nawa take, dubi yadda Allah ya dauke Rabiu farad daya aka raba Rahima da mijin da suke zaune lafiya, yaronta ya shiga maraici ko shi bai isa bawa tsoron Allah ba? Wannan duniyar da ba matabbata ba? Hawaye suka rinka gangarowa zuwa kuncinta.
Rahima ta gani ta gigizata cikin damuwa "Lafiya kuwa?"

"Hawayen godiyar Allah ne da ya kubutar dani ya ganar dani ya hana min biyewa sharrin zuciya, wallahi ba domin zuwanki na na kuduri aniyar mugun zama za muci gaba da yi nida Suwaiba don nayi sakacin barin shaidan ya shiga zuciyata ya fara dora min tubalin gina katangar da zai ci gaba da dora bulo Yana zugani Ina hauka, yanzun nasihohinki sunsa duk nayi sanyi na saduda na hakura na barwa Allah dukkan lamurrana, nayi imanin tunda bana nufun kowa da sharri zai kareni idan an nufoni, zai Kuma yi min sakayya muddin aka zalunceni."

Rahima tayi murmushi "Alhamdulillah tsarki ya tabbata ga sarkin sarakuna, munyi salati ga Manzonsa Masoyinsa Muhammad SAW, mun godewa Allah da ya baki ikon ruguje wannan ginin, Ubangiji ya Kara Mana kariya da kayangar karfe da shaidan la'ananne ya karemu daga dukkan sharrin abin ki. Abinda Nike son ki gane dukkanmu Nan masu laifi ne kullum cikin daukar zunubi muke amma Ubangiji ya Kan yafe mana idan mun roki gafararsa, wani zunubin ma ko bamu roka ba sai ya shafe mana kasancewarsa Mai tausayi da jinkan bayinsa, to kai waye da zaka ce ba zaka yi hakuri da wasu al'amurra dake faruwa da Kai ba, balle ka yafe, kana ajizi kaskantacce? Haba don Allah ki zage damtse ki bautawa Ubangijinki, ki kyautatawa mijinki, kiyi tarbiyyar 'ya'yanki, kiyi zumumci domin Allah, ki kyautatawa iyaye da yanuwa kiga irin daukakar da Allah zai miki."

Maryam taja numfashi ta rike hannyn Rahima "Wallahi naji na amince na dauka na Kuma gode da nasihohinki 'yaruwa Allah ya saka miki da khairan. Yanzun kenan mun shafe chapter mutumin naki?".
Ta zabura ta mike "Ina ai hankalin rabuwa yayi, Ina nan, Ina can, yanzun dai kiyi kwanciyarki don sulusin dare yayi, Sallah zanyi da adduoi na musamman in roki ya Azeez ya nuna min shi ko mafarki ne don hankalina ya kwanta."

Maryam ta gyara kwanciya " In Kun hadu Ina Mika gaisuwa da jinjina masa saboda ya sace min zuciyar kanwata ya Kuma tsamota daga duhun jahilcin rashin sanin menene *so*


Ta shifa toilet ta dauro alwala ta shumfiea sallaya ta fuskanci alkibla tare da natsuwa da kaskantar da Kai domin ganawa sa Mai rufan babu dogara, Mai amsa adduar bayinsa babu shamaki ...


Ta dade tana zuba adduointa, ta rufe da salatin Manzon tsira, ata kwanta ba saida sallaci asubah kana tayi matashi da hannunta na dama ta bingire bisa sallayar.



Hanyace data kasu har uku, ta rasa wace zata bi, dama,hagu ko tsakiya? Ta yanke shawarar bin hanyar dake damanta, 'yar siririyar hanyar cike take da itatuwa da ciyayi Korra shataf, bata yi nisa ba sai gata gaban wani tafkeken kogi Mai shakare da wasu garai-garain ruwa masu kalar sararin sama, nan ta gane baby hanyar wucewa kenan.

Ta juyo cikin hanzari da niyyar ta koma baya nan ta rikice dalilin hanyar ta rikide ta hade danyen ciyawa da itatuwa ga ruwa male-male ta ko' Ina, daga saman bishiyoyin wasu irin kyawawan tsuntsaye ke kuka tamkar suna busa sarewa, sanyin tafkin nan ya fara ratsata, sanyi ya kadata ta shiga makyarkyata, hakan yasa ta waige-waigen da tunanin ratsawa ta cikin ruwan ta fita wannan wajen, tsoro ya kamata, nan take ta daga hannayenta sama ta fara rokon Maiduka ya kawo mata dauki..

Cikin ikonsa Allah sarkin sarauta sai taga wani mashahurin haske ta ko'ina, wani doki Mai fuka-fuki da ya ratso ta cikin hasken nan a guje ya sauko daf da ita. Jikin dokin ba irin dawakan data sani bane, wannan ilahirin jikinsa kalar azurfa ne, gashin bayansa gazar-gazar da kwarar idanunsa ne kawai bakin kirin.
Tsananin ganin wannan halitta daya cikata yasa bata lura da mutumin dake Kan dokin ba, bata ankara ba taji an dagta sama an dorata bisa dokin nan ya tashi sama suna tafiya tamkar wasu tsuntsaye, basu dade ba taga sun sauka daf da kofar wani farin gida gewaye da furanni, hancinta ya shaki wani hadadden kamshin data rasa inda yake fitowa, kamar tafiyar slow motion ta tsinci kanta cikin wani lambu cike da kayan marmari, ta mika hannu don ciro nunanniyar goba tsawonta bai Kai ga iccen ba, Mai dokin Nan ne ya matso yasa hannunsa ya ciro goban Nan har zai Mika Mata sai dokin yai haniniya ya kada fukafukinsa sai ya fasa bata Saida ya saka a

Please Login or Register in order to submit comment