Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da kanki shan kwayoyi kinsan dalilin ciwon kanki ba ruwana da akai min kazafi."
Alh Abbas yace "In don ciwon kaine meye na raki kinada likita a hannu, hala bai San amaryar bata jin dadi bane?"
Da taga sharrin nasu zaiyi yawa ta juya fuu tace "Mu kwana lafiya, sarakan sharri."
Yaja motar Yana dariya.


A dakinsu sun dade itada Umma suna hira, tun tana kaucewa har ta gaji ta kalli Rahimar maganar na cin ranta tace "Ashe yau likita ya zo."
. Ta amsa a ciki "Eh ya taho Umma ko da yace dolene a garesa, wallahi Raina ya baci kwarai da furucinsa tunda nima ba son nike yi ba, Zan fi farin ciki idan Allah zai hadani da wani daidai Ni." Ta share hawaye
Umma ta matsa kusa da ita ta kama hannayenta ta rike "Haba Rahima bai dace kin rika gaba kina dawowa baya ba, mun riga mun gama magana kince min kin amince yanzun ya kike son sakawa zuciyarki damuwa da bacin rai a banza? Ko wane hali ya nuna ai ya zan shiririta tunda gashi ya biyoki har gida ya baki mutuncinki na diya mace Kuma ki tuna ba fa mu iyayenki muka nema masa ke ba, daga can wajensu batun ya taso don haka bai isa ya wulakanta mana ke ba, kina da damar bugun gaba diyar Umma don haka share hawayenki kinji, muna nan muna adduar idan babu alkhairi a cikin al'amarin nan Ubangiji ya musanya miki da mafiyinsa."
A nan ta danji dadi tace "Allahumma Amin Ummana, nagode."
08/09/2020, 23:11 - Anty saliha.....ˆRAHIMA...doc by jami

20
Dr Haseeb ya dade tsaye cikin office dinsa yana jangen motocin dake kara kaina ta windon amma kallon kawai yake tunanisa ya kasu. Na farko yana tunanin rabonsa da gidansu Rahima kwanaki uku kenan kacal amma zuciyarsa na kwadaita masa sake komawa ya ganta don wanke laifin kalaman da ya fada mata wadanda basu dace ba.
A hakikanin gaskiya ya yaba da hankalinta, amma addinin data rike hannu biyu ya fara burgesa. Tunaninsa na biyu ya danganci matarsa Zuwaira, wajibi ya bata hakkinta ya fada mata halinda ake ciki na Shirin auren matar kaninsa, kana ya zama dole yaje ya nemi shawarwarin da suka dace wajen abokin mahaifinsa shahararren malami don Kara tabbatar da alkhairin auren, sai ziyartar surukinsa mahaifin Zuwaira saboda kar yaji daga sama ya dauka zaiyi auren ne don yaci amanar diyarsa."

Bai san abinda yasa duk cikin wadannan tunanin zuciyarsa tafi karkata da son zuwa gidansu Rahimar gashi bai San dalilin da yasa da duk ya tuna yai mata alkhairi ya kanji wani irin farin ciki ya lullubesa ba.

Itama Hajiyarsu taji dadi, tunda hakane kenan kafin ya sake komawa shiga boutique ya gansa....
Ya nutsa har baiji bude kofa da shigowar abokin aikinsa Dr Kabir office dinsa ba saida ya iso daf da teburinsa waya Kuma tayi ringing, kana ya dawo hayyacinsa yasa hannu ya daga wayar dake bisa tebur ya fara magana da harshen turanci kafin ya juya harshe zuwa larabci, sin dau lokaci suna magana da Wanda ke wancan bangaren kafin suyi sallama
Ransa a bace ya kalli Dr Kabir yace "Dr Taariq ne daga Riyadh Wai suna neman taimakonmu by nextwk sabida suna da patient da patient da yake cikin *coma* suna tunanin zai sami amnesia idan ya farfado .
Dr Kabir ya dan sosa keys "To ai wannan aikin kane Dakta."

Dr Haseeb ya zauna ya jawo wani file yayi rubutu ya mayar ya rufe ya ajiye gefe sannan yace "Gaskiya I have commitments next week, so I think they've to do without me this time.".
Dr Kabir ya zauna shima yace " Kana ganin in an kyalesu an kyauta kenan? They relied on your services ka sani.".
Ya dago Kai ya kalli Dr Kabir yace "Nasan haka Dakta amma inada wani uzurine next week din, Ina sa ran a daura min aure by then kaga kuwa da wuya in sami yin abinda suke so."

Dr Kabir ya bude baki cike da mamakin da al'ajibi don ko kusa bai taba tunanin Daraktan nasu zai Kara auren ba...

Yayi murmushi ya daga masa hannu "Don't be surprise, kasan shi aure nufin Allah ne, sai kaga Wanda ya shafa ma bai taba mafarkin faruwansa but idan Allah ya rubuto mutum baida wani dabara "

Ya gyada Kai "Kwarai da gaske, may I then offer my congrts Sir?" Cewan Dr Kabir.

Ya sake daga masa hannu "Thanks a lot, by the way mahaifiyar yaron nan Abdul da ka sani amaryar."

Yaga ya fadada murmushinsa sabanin yadda ya zata, ya Kuma Kara da fadin "Wallahi kayi abinda ya kamata, Allah ya sanya alkhairi "

Dr Haseeb yai ajiyar zuciya "Nagode sosai Dakta, I really appreciate your support and prayers."

Yace "Haba ba komi, Ni zan shiga office, batun tafiyar a bari a ga abinda haki zai yi ko?"

Ya amsa "Gaskiya sai yadda na gani still a shigar da tafiyar cikin schedule dinmu mu gani.".

Yace "Ba damuwa Dakta."
Ya fita ya bishi da kallo, yasan yanzun batun auren nasa zai karade cikin asibitin.


Yau kwanakinta takwas kenan da dawowarta Umrah amma basu yi zaman ko rabin awa ba tareda mijinta, ita wannan hali na Dakta na daure mata kai kuma ta fara gajiya don haka ta kashe ta tsare dole yau ta saurateta su tattauna problems dinsu, idan Kuma yaga bai auren ya gaji ne y sauwake mata taje ta nemi wansa zai san darajarta ya rinka kulata, amma Ina amfanin zaman aure irin nasu? Duk da tasan yawanci laifinta ne, zuciyarta taki amincewa, to yaushe zata yarda ta dorawa kanta laifi haka siddan.

Ko da ya dawo gidansa bai taba tunanin zai sameta a gida ba tunda Allah yayi ta mai yawon tsiyace.
Doguwar riga ce a jikinta Wanda duk da ta rufe tun daga hannayenta zuwa kafafu shara-sharar yadi ne marar kauri dake nuna duk ilahirin surar jikinta, kallo daya yai Mata ya kauda Kai, ta amshi briefcase dake hannunsa tare da rungumarsa "Sannu, ka dawo da wuri lafiya?"

"Lafiya." Ya amsa mata yana tafiya zuwa bedroom dinsu domin yai wanka."

Zuwaira ta hada kayan abinsa a bisa carpet saboda bai cin abinci bisa dining table, ya fito sanye da kananan kaya a jikinsa Yana zuba kamshi, ya zauna kafin ya fara cin abinci ya tambayeta "Ina su Khalifa?"

Ta amsa "Suna can gida."

Ba Kara ce komi ba, ya karbi plate din data shakare da shinkafa da miyar data dafa, yayi bismillah ya saka cokali daya a baki ya tauna ya hadiye da kyar, yaja tsaki ya aje plate din yace "Sabida Allah Zuwaira a matsayinki ta mace baki iya sarrafa wani nau'in abinci bane sai shinkafa da miya kullum, ta yau ma bata nuna ba, miya ga tsami sai kace ba mace ba?"
Ta harzuka nan take "Yauwa daman maradinka bai kunya ai, kai kenan babu ranar da zan dafa abinci kaci lakadan ba tareda complain irin na sauran maza ba, ni kenan komi ban iya ba a idanunka."

"Ni bance ba ki iya komi ba, ina fada miki ki rinka kwantar da hankalinki kina abinda ya kamata cikin gidanki, ai ga abincin nan dauki kici kiji Mana idan zuwa anjima indigestion bai kamaki da heart burn basu dameki ba...
Tayi shewa "To idan kwarnafin ya taso ba sai ka bani magani ba? Kaga idan ba zaka ci ba kace da inda kake zuwa kana ci ka koshi, to da hakan kuwa gara ka aurota zaifi min nono fari."
Ya shareta bai ce komi ba, ya dau remote ta canza channel zuwa CNN yaci gaba da sauraren news.
Ta mike ta kwashe tarkaccenta ta mayar kicin ta dawi ta zauna, zuwa can tace "Ina son magana da Kai."

Yace "Hhmmm Ina saurarenki bismillah.".
Ta kura masa ifo na wasu dakikoki tukunna, ta gyara zama tace "Tambayarka zanyi, saboda Allah irin zaman da muke yi ya dace da tsarin rayuwarmu, kana ganin shine daidai?".
Bai dagi ba ya kalleta ba ya amsa "Wane irin zama kike nufi?"
Taji haushin amsar da ya bata tace "Ai baka ma sani ba ko? To in fada maka, Zama ne muke yi tamkar ba ma'aurata ba, kowannanmu na harkarsa, ba shakuwa, baka San halinda nike ciki ba, nima ban san halinda kake ciki ba, in har ya zama dole muyi magana bata kaiwa ko Ina m gayyar take watsewa, ko yaranmu baka ja su a jiki ba, Ina iya cewa ma yadda ka shaku da wannan yaron Abdul baka shaku da 'ya'yan cikinka ba, basu Sami wannan gatan ba."

Yaji tayi shiru, ya aje remote ya fusknceta " kin gama?"
"Eh ta amsa.
Yace "Tunda Allah yasa yau da kanki kie son ayi batun sai ince alhamdulillah do n many times nayi yunkurin mu zauna mu tattauna issues dunmu kika ki yarda kika nuna abinda ke faruwa duk laifinane, Amma tunda kin yarda akwai problems a zamantakewar mu sai ki fadi muji a Ina na kuskureki?

Zuwaira tace "Baka ji abubuwan dana lissafo bane?"
Yace "Oh sune kike ganin problems dinmu kadai? To bari ni in bayyana miki ko ince in baki amsa ki hujjojina na sanya miki ido da nayi.
Na farko duk matar arziki tana nunawa matukar kulawa da harkokin maigidanta na yau da kullum, har idan akwai shawarwarin da zasu amfaneshi ta bashi , idan gari ya waye ta kula da dawainiyar breakfast dinsa Dana yaranta in akwaisu, idan zai fita aiki tayi masa adduar fatar alkhairi, su rabu cikin farin ciki su yini begen juna, idan ya dawo ya sameta cikin suturar mutunci, ta tarbesa da da abinci masu gamsarwa, idan lokacin barcinsu yayi suyi hirarsu Mai sanyayar da zukatansu har in suna cikin mood su kusanci juna ta hanyar da Allah yai mana umurni Kuma Manzon Allah yai mana koyi a addinance sabida hakan zai haifar musu da nishadi da Kara musu shakuwa ba a kwana ana jin haushin juna ba.
To ke kuwa duk safiya na Kan tashi ne in barki kina barci baki sa niyyar tashi ba ma saboda kinada rauni a addinin naki, batun hidimata dana Yara kuwa kin halastawa mai aikinki tayi Mana, lokacin da na dawo gida ba lale in sameki ba, kin dau mota kina garari a gari, ba Kya gidan wannan buki ba Kya gidan wancan abokiyar kasuwanci.

Idan anci saa kin zauna a gidan, Zan shigo in taras dake da kawayenki ne yan duniya, wadanda suka fi karfin mazajensu iskar duniya na dibansu.

Abincin da kikan girls so da yawa nakan gwammace zuwa ci a hotel da inci naki sabida baki zauna kin kula yadda mutum zaici hankali kwance ba, ke kanki ba Kya cin abinda kika dafa a tukunyarki kin gwammace kullum ki aika a sayo miki nama ki ci.

Batun rashin kusantar yara da kike kin basu damar zama cikin gidansu ne? Ko kuwa kin kaisu wajen mahaifiyata tace na zata iya ba? Nasan gidanku kike kaisu but mun san zama gidan ubansu yafu musu fa'ida.

A nan ta hayyayako "Ai da tuntuni ka nuna rashin amincewarka dana rinka barin maka yaranka muga tsiyar da zaka basu a gidan..
Yayi wanumi dan murmushi "Duk takamarki kudi ko? Gidanku ba matalauta bane, to Ni dinma ba matsiyaci bane.
Yanayin aikina yasa na amince miki Kan ki rinka kaisu gidanku din sabida da kina zama a gida da yaran basu rinka watangaririya ba.
09/09/2020, 14:13 - Anty saliha: ...RAHIMA...doc by jami
21

Dr Haseeb yaci gaba da fadin "Shin kin taba tunanin kai yaran nan wajen Mahaifiyata su rinka debe mata kewa? Ah ah ke sam babu ruwanki da harkar dangina sai wadanda suka zama miki dole, yau satinki nasa rabonki da gidan Hajiyar? 'yanuwana sunyi korafin kin kama 'ya'ya kin rike basu san kowa ba sai danginku, sun gaji da complain sun hakura.

Kina korafin bamu shaku da juna ba ko? Ta yaya hakan zai kasance bayan kin nunawa duniya mutanen da kike hulda dasu a waje sun fini mutunci da matsayi a zuciyarki, ya za kiyi tsammanin ni Haseeb in zama second best a rayuwarki?
To bari ayita ta kare yau Zuwaira, shin kinsan nasan fa duk shigi da ficin da irin mu'amalar da kuke yi da wasu mazan da sunan kasuwanci in and outside Nigeria? That's why naja baya dake, na sakawa sarautar Allah ido, duk ranar da Allah ya kawo karshen aurenmu shikenan don na gaji da zama da wace zuciyata ke mata zargin fasikanci."

Tana jin yai shiru ta tuma gefe ya dafe kirji tareda zaro idanu "Kazafi Kuma za kayi min Haseeb?"

Ya girgiza Kai "Kinji Kuma daya daga cikin halayenki dana tsana *karya* duk maganar da zaki Fadi aka yi nazari aka tace sai an gano karyarki tafi gaskiyarki yawa a cikinta, kinga bani ba har Allah daya haliccemu ya la'anci mai yinta, yai hani da yinta, kince Kuma kazafi wane irin kazafi ga dahir nan kowa na gani?
Ba ma sai an kaita da nisa ba, fara tuhumar kanki tun daga Kan irin shigar da kike yi, yadda kike gudanar da tsarin rayuwarki, na mijinki da zuriyyarmu, yaya tarbiyyarki ke tafiya, shin kina kokarin tsare abubuwan da Allah ya umurceki kiyi, kina gujewa abubuwan da suke munkar a gareki?
Look at you now, just look at irin shigar da kika yi a matsayinki ta musulma, fara da gashin kanki, gaki nan roba ce ko yizgar doki ko wace tsiya ce kika Kara a kanki oho wai ke gayu, gayu ko yin biris da hanin addininki, ke kin isa kiba kanki abinda mahaliccinki bai azurtaki dashi ba?
Dubi tun daga yatsun kafarki zuwa hannu, yanke kumba bai cikin tsarinki abinda Manzon tsira yai mana koyi da yanketa duk ranar jumma'a don inganta tsabtar jikinmu da samun lada saboda ita din najasa ce, wani lokaci har fenti kike musu wai duk cikin gayu tunda ibadar bata tsaya miki bane, bki ma san hukuncin barin lam'a wajen al''wala ba, kalli suturar dake jikinki, gata nan har Kara amma bata kare a hango yanayin surar jikinki ba....

"Karfa kaga laifina a nan, wallahi kai nikewa kwalliya saboda idan banyi ba ka isheni da korafi.'

Ya kalleta wani iri "In don nine kike sabon Allah irin haka na yafe. Duk matar data san mutuncin kanta ba zata rinka irin shigar da kike yi ba, idan Kuma domina kike, ai ko Ina kasar ko ba nan hakan kike shigarki, haka kike fita duk inda kuka ga dama keda kawayen naki, mutuncinki a zube, na iyayenki a watse, Ni Kuma duk irin matsayina a garin nan wasu na min kallon namijin hotiho wace matarsa tafu karfinsa, to ba fun karfina kika yi ba, Allah ne shaidata tunda naga kin fara canza salon rayuwarki na fara yi miki nasiha, baki ddauka ba, na gaji na hadaki da iyayenki duk a wofi,maimakon ki canza sai kika Kara fekewa, Kika ce wai Ina neman hadaki dasu ne, to sai na gaji na sanya miki ido kije duniya taci gaba da rudinki, shaidan yaita busa miki sarewa kina taka rawa, abinda na sani gida biyune, da inda zamu tafi komin dadewarmu a duniyar, yau Ina Rabiu, kina ganin lokaci kalilan Allah ya rabamu farad daya, kafin shi mutane miliyan nawa suka rigamu gidan gaskiya, mu din ma ba zama za muyi ba, tun muna jin na wasu wata rana za aji namu, ke don Allah ko tunanin mutuwa ba kya yi?
A kance wanda duk yai nisa bai jin Kira, Zuwaira ta fara nisa, tafiyar ta tafi sai nema mata shiriyar Ubangiji saboda rabi -da rabi take saurarensa, hankalinta ya dauku da tunanin irin cakewar da zata yi wajen bukin wata kawarsu da za ayi a Hotoro, Kuma a kullum ta kanso tayi shiga ta burgewa da tsadaddun kaya don ta nunawa duniya ita 'yar business ne, matar shahararren likitan da ake damawa dashi a kasarmu Dr Haseeb Junaid.

Ya lura hankalinta bai tare dashi, ya kakkabe rigarsa ya tashi ya dauko key din motarsa yai bar mata gidan

Bai zame ko'ina ba sai gidansu Zuwaira ya wuce Kai tsaye cikin gidan y gaida matan gidan su uku, sarakuwarsa ce Uwargida sai masu bi Mata. Dr Haseeb ya koma falon surikin nasa ya zauna Yana jiran fitowarsa, nan ya tsudumma tunani, kwakwalwar sa ta tariyo masa tarihin rayuwarsa tun yana karami da dalilin haduwarsu da Alh. Muhammad..

Shi dai an haifesa a unguwar Galadanci, mahaifinsa Mal Junaid rikakken dan boko ne daya kware a fannin kimiyya, malamine a jami'ar Bayero. Ya mallaki mata daya Kaltume da albarka da guda daya tilo, sun day dogon lokaci basu Kara samun haihuwa ba a dalilin haka Mal ya nemi auren wata bazawara Kuma daliibansa ya aure. Tun tarewan amaryar ta nuna ita babu ruwanta da Uwargidanta balle wani danta daya tsone Mata ido. Yaron ya zama wajen uwarsa kadai yake samun sararawa wace ganin halin ko in kula da uban ke nunawa danta bayan ya Kara auren yasa ta ajiye kunya ta rungumi abinta.

Yana kara shekaru yana fahimtar yadda mahaifinsa ke yin nesa dashi Wanda da ya dauka kunya ce irin wanda iyaye kanji na dan fari but daga baya ya gane wata irin kiyayyace da bai San mafarinsa ba

Abinda ban mamaki ace farad daya uban daya haifeka ya dawo bai kaunarka, duk da haka daga Kaltume har Dan basu danganta hakan da komi ba.

Amaryar malam ta fara haihuwar diya mace ta rasu, tun daga lokacin Abdul Haseeb ya fara karaya da lamarin mahaifinsa domin rashin jaririyar nan da akayi tamkar zautu yayi, bayan nan Allah ya bata haihuwar diya biyar, mata biyu, maza uku, Allah ya sake amsar matan ya bar Mata mazan.

Duk da ya kasance shine babba, a kullum mafarkin mahaifinsu ya ta'allaka Kan kanninsa ne kawai na su din su gajeshi fannin karatu. Ba zai taba mantawa wata rana suna zaune gewaye da uban suna hira,kowa na fadin abinda yake son ya zama idan ya girma, Abdul Haseeb yace shi likita yake shaawar zama maimakon uban yaji dadi ta bashi kwarin gwiwa sai ya hantare sa ya daka masa tsawa yace "tafi can da wace dakusassar kwakwalwar? An fada make batcu ake a tashi a zama likita? Ko da wannan tsamin bakin da in inar taka ce zaka zama likita?
A lokaci bai wuce shekaru goma sha biyu amma yaji zafin gorin da mahaifinsa yai masa, kalamansa sun sa hawaye masu zafi gangaro masa wadanda uban ya lura yace ya tashi ya bashi waje ..
Kaltume ta gansa yana kuka ta tambayi dalili yaki fada Mata don ta fara wayon gudun bacin ranta, sai dai tun daga ranar ta Kara zage damtse ya daukarwa kansa alkawarin zama wani abu a rayuwarsa duk wuya iya wahala, ij karatu nasa mutum yai suna to sai yayi suna gabas da yamma kudu da arewa sai an San da zamansa.
Ya dage da karatu ita Kuma uwa ta dage da neman maganin gyaran tsamin baki da in Ina da ya tashi dasu, duk inda taji magani zata nema ko Saida wani Abu nata ne ta amso ta bashi bayan adduoi da yake karya kummalo dasu,idan zai kwanta barci su din zasu masa bargo. Kullum cikin sanya masa albarka da Kara masa kwarin gwiwar cin ma nasarar abinda yasa a gaba take.
Tsakaninsu da mahaifinsa ba wani canji haka yasa yaja baya dashi da 'yanuwansa da tun farko ba a nuna musu muhimmancin zumunci da junansu ba balle su kusance sa."

Yayi kokarin gano dalilin rashin samun kyakkyawar kulawa daga mahaifinsu abu yaci tura a yayinda uwar ke kokarin hanashi kullatar mahaifinsa da komi cikin zuciyarsa tunda itama ta kasa gano komi zaman hakuri take duk da tana zaune dashi fisabilillah

Kwatsam aka wayi gari malam ya saki Kaltume har saki uku, wannan Abu ya tsayawa Haseeb a rai, a nasa wautar yaso uwar ta zauna gidansu komi wahala amma zama ya kare.

Tana gama idda ta sake aure inda Allah ya azurta ta da Yara biyu maza, Hayatu da Rabiu.

Ba a taba tabbatar da hazakarsa ba saida ya shiga jami'a ya samu gurbin karatu kan koyon aikin likitanci.
A nan Abdul Haseeb ke matukar neman taimako da dukkan kwarin gwiwar da ya dace iyaye da duk masu kaunarsa su bashi sai dai ina kana uban yayi alfahari da godewa Allah da ya bashi hazikin yaro amma Ina ! Bai samu ba, gashi uwa duk ta gama sayar da dan abinda ta mallaka a Kan neman ilmin da kwara daya tilo, hatta da yar gonar da tacu gado ta sayar anyi amfani da kudin basu isa ba.
Shi Kuma bai son matsa mata saboda bai da kwanon abinci gidan ubansa, duk wata lalurar ci da sha da sauran abubuwan bukatunsa sun ta'allaqa ne kadai Kan mahaifiyarsa, tausayinta yake har dai da yaga mahainsa ya dara mahaifin su Hayatu karfi sosai, Kuma mahaifinsa na daukar nauyin hidimar sauran 'yanuuwansa shi kadai yake yiwa wannan yankan kaunar.

Wata rana kudun sayen handout yai masa teahe ya rasa yadda zaiyi dole ya nufi wajen uban neman taimako amma me zai faru, fada ya rufeshi dashi yana fadin "Wa yace kaje ka zabi course Mai sa kashe kudin tsiya kassn ba Kai kadai na haifa ba don haka ba zan talike a kanka ba, ya wurgeshi da rabin kudin yace karya sake zuwa ya dameshi don da yai nasa karatun babu Wanda ya taimaka masa kwadago yayi shima yaje yayi ya nemi nasa.

Ance gayawa Mai zuciya buki ba Mai dukiya ba, wadannan kalamai sun Kara zaburar dashi sunsa masa rai kwarai sun Kuma tunzura shi, ya zuciya, irin zuciyar da ake son yaro yayi ya ajiye girman Kai da tunanin shi wani ne ya tashi ya nemi na kansa. Ya fara yawon neman abinyi idan ya gama lectures ya shiga gari neman aikin, duk inda yaga ana gini ko aikin bulo ya nema ya tube yayi a biyashi, bashi wajen kafintoci bashi tashar mota wajen yun dako. Idan ya samu kudin aikin yinin ranar ya Kan raba uku, Kashi daya ya mikawa uwa, Kashi na bukatun yau da kullum Kashi gudan a jefa a asusu na hidimar karatunsa ne.

Wata rana inda yake aikin bulo suka samu kwangilar ginawa wani dan kwangila sabin gida, a cikin maaikatar da aka dauka har dashi ga jarabawarsu ta matso ga bukatar kudin a tare dashi don haka ya kwashi takardunsa ya rinka tafiya dasu site din inda da ya samu lokacin tsaya sai ya duba tukunna kana yaci gaba da aikinsa.
Lokaci lokaci Alh Muhammad Kan ziyarci site din don ganewa idanunsa yanayin aikin da ake masa, a nan ya hango wannan saurayi inda ta dade yana nazarinsa Yana karatu a natse, sau uku kenan yana ganinsa, haka kawai yaji yana son jin labarin yaron. Yasa aka Kira masa shi, ya kwaso littafansa ya zuba a jaka ya iso inda ake nemansa. Yana zuwa ya durkusa gaida Alhajin amma ya mika masa hannu su gaisa, ya dan tsaya saboda jin nauyi, Alh. Muhammad ya riko hannunsa Yana dariya, ya tambayi sunansa ya fada masa, ya sake tambayar dalilinsa na yawo da littafai Yana aiki ya bashi amsa da "Ina neman na kaina ne."
Ya sake tambayarsa wanene mahaifinsa ya fada, nan da Nan ya gane don shi din sanannan mutum ne, Alh Muhd yai mamakin jin sunan mahaifinsa da yadda ya bar dansa na kwadigo bayan Allah yai masa rufun asirin da zai taimaki wani ma ba dansa kadai ba.

Yana son jun ainihin tarihin yaron nan don haka ya mika masa katinsa yace ta samesa a gidansa a ranar, ya karba yana mamakinsa dalilin da yasa yake son ganinsa tareda alkawarin zuwa da dare.
Karfe takwas na dareya isa gidan Alh Muhammad, da alamun an bada labarin zuwansa domin yadda maigadi ya tarbesa yai masa jagora har falon maigidan.

Alh. Ya mike ya sake Mika masa hannu suka gaisa kana ya bashi umurnin ya zauna ya zabi abinda zai ci cikin nau'ikan abincin da aka baza

Please Login or Register in order to submit comment