Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ni fadin wannan maganar."
"Da gangar kika yi tunda an Sha gargadinki kan furucin da kike yi, yau kika yiwa mijinki gorin? Maras tunani, da kike fadin ubanki ne silar arzikinsa yanzun hidimar da yake mana ya zama ke Kika sa shi? Yarone dan halas da yasan darajar iyayensa da naki."

Ta daga kai "To Ni Mama so kuke in zura masa ido Kan batun aurensa?"

"Ah ah kike kiyi abinda zaki iya kinji zabin da muka baki ai. Ni tashi ki fita min a daki, ki Kuma dauki yaranki ki maida gidan ubansu tunda baki San ciwon kanki ba, albasa bata yi halin ruwa ba."
10/09/2020, 18:03 - Anty saliha: ....RAHIMA...doc by jami

25
Zuwaira ta tabbatar wa kanta ba zata sami yadda take so wajen iyayenta ba, saita canza shawara ta tuntubi Husaina daya daga cikin kawayenta a tunaninta ita din ce kadai zata iya taimaka mata warware matsalarta.
Tafiya mikakkiya ta isa gidan Husaina dake gadon albasa, Sha daya saura na safe ta matsa kararrawa, saurayin dake mata wanki da guga ne ya bude mata kofar ta shiga yana gaisheta ta tambayesa "Ina Hajiyar?'

"Tana ciki." Ya amsa.
Kai tsaye ta wuce bedroom din Husaina ta taras da ita a kwance "Lalle kina jin dadinki, ni ina ga time din barcin safe?"

Tayi Mika tace "Zuwaira Wai Ina kika shigane tun safe nike neman wayarki?"
Zuwaira ta zauna bakin gado "Kinga ni yunwa nike ji bari in ci abinci tukunna kisha newa."

Husaina ta dago ta kalli yanayin fuskarta ta saka salati ,"Ke ya aka yi haka?"

Tace "Labarine mai tsawo bari in koshi jikina har rawa yake, rabona da abinci tun jiya wajen bukin nan."

Cikin hanzari ta kira yaron gidanta ta umurcesa yaje ya hado musu breakfast, ya fita da sauri."

Zuwaira ta kalleta sama da kasa "Haba Husaina dubi shigarki fa sannan kika yaron gidanki har cikin bedroom dinki?"
"Look Zuwaira nu dake duk kanwar ja ce fa, jirgi daya ya kwaso mu, ya saba shigowa sai me?"
Ta gyada Kai "No duk rashin da'ata ba zan bar wani kato ya shigo min cikin dakin barcinmu ba don na dauke shi matsayin *sacred secret place*

"Hhhmmm ba dai kin koshi ba? Mu bar zancen mu koma na dalilin nemanki, shin ina Alhajin da yaso like miki wajen bukin nan, ya dameni in bashi lambar wayarki, ya isheni da naci that's why na kiraki tunda safe, me ye ra'ayinki?"

Tayi saurin girgiza Kai "Raba da wuya kinji, in don kayan da muka ce muna so ne zamu sara ya taimaka mana ya bar abinsa, irinsu sun cika mita kawai ya hana min sikit.. Ni dai yanzun Kinga fuskata ko? Wallahi aikin Baba da Mama ne suka taru sukai min sukuwar Sallah don nace ban amince Haseeb yai aure ba."

Ta furzar da ruwan da sanyin data kurba ta bugi kirji cikin tsoro "Dr Haseeb zai yi aure? Wonderful...
"Kin ganni nan fa cikin tashi hankali nike, that's na garzayo bidan shawarki don iyayena sun bashi go ahead."

"Yo inya sakeki ba kin huta ba, ga masu sonki ido rufe?"

Tace "Sakin bai dameni ba, hakan nike so Amma wallahi ba zan bar gidansa kafin aurensa ba wannan yarinyar ta dauka ta isa ta koreni, sai tazo ta zauna na nuna mata ruwa ba sa'an kwando bane, wutsiyar rakumi tayi nisa da kasa."

Husaina tace "A ina ya samu matar ne?"

Ta amsa "Matar kaninsa daya rasu dinnan nan, shine iyayenta suka cusa mata ita don sun ga da maiko."

"Tashin hankali inji Husaina ta Fadi cikin karaji "Yarinyar dake teaching makarantar kurame?"

"Yes ita, wani abu ne?"

Ta kada Kai "Yadda nike ji yarinyar nada kamun Kai da rike addininta, Kinga ko nan an samu difference.


"Wannan lalurar tace Husaina ta Fadi tana daga kafada irin bai dameta ba dinnan, fada min meye shawara yanzun?


Tayi shiru tukunna kafin tace " yanzun Kam kwantar bauna za muyi mu jira ta tare sai ki bullo da kissa da munafunci hade da karfar baka Wanda yafi asiri aiki mu gama da ita. Da dai baki da niyyar barin gidan ne da mun hadata da malam Mai gobe da nisa."

Zuwaira tayi hamma tace "Shikenan sai mun sake haduwa, bari in koma gida don yau harda su Khalifa su Mama sunce in kwashesu, na baro an kaisu makaranta ne."

Tayi tagumi "Oh in banda abin Dakta meye na hadaki da iyaye Kuma, ya barki kiji da jinyar kololon bakin cikin daya mulmula ya saka miki a kahon zucci don kishi cuta ce."

Ta mike tsaye" Ki barsa kawai zan bashi mamaki, ni kam na tafi."

"Zan iskoki har gida ba sai kinyi wahalar dawowa ba, yi jinyar tsamin jikinki."


Yau kwana biyu kenan da taji labarin Hjy Kaltume na fama da zazzabi,tayi niyyar ta share ko ta aika kawai a dubota, Umma da Maryam sunce bai dace ba, ciwo ya kore komi Kuma tafi gaban sharewa a wajenta, ita tasan hakan illa dalilan da suka taso suka haddasa nisantar junansu.

Ba domin batun aurensu da ya taso ba ai Hjy Kaltume uwarta ce mai bata nono tasha ta koshi.Tuni ta daina jin haushinta sai kunya data karu fiye da dauri, ta bi maganar iyaye ta shirya zuwa dubo Hajiyar


Karfe takwas daidai ta fito daga gidansu sanye da wata doguwar riga ta yadin Kampala shadda maroon colour, wace ta dora Mata after dress a samanta cream colour.

Tafiyar cikin rashin karsashi a natse take yi alamar dole ne yasa ta fito.

Iskar dake bugawa a hankali ta rinka kada abayar da lullubinta, tafe take tana jan adduoin neman kariyar Ubangiji daga sharrin mazan dake ta son yi mata magana
Yau saita ga gidan Hajiyar yai mata nisa, iya kauda kanta Saida wani Mai motar ya kyala ido ya ganta, ya Kuma bi bayanta har zuwa daidai lungun da zata shiga kwanar gidan Hajiyar, yai parking ya fito ya tsaya jiran fitowarta....

Ta shiga tareda sallama, Mairo ta amsa cikin murna "Marhabin maman Abdul sai yau, idonki kenan?"
Tayi dan dariya "Kinada bakin magana ke sau nawa kika taho wajena?".
"Ai kuwa sai dai ki zargeni na kanje in duba Umma mana" Mairo ta kare kanta...

"To ai shikenan ya jikin Hajiya?"
"Da sauki kin San halinta ai bata son a ga gazawarta."
Rahima tace "In shiga in ganta, Allah ya sauwake.

Hjy Kaltume na kwance bisa katuwar katifar da aka fito mata da ita falo, ta dago kai, tunda taga bakuwarta ta tashi ta zauna "Ni fa naji kamar muryarki sai naki amince ke dince tunda kin gujeni Rahima, Ina dan gidan Baba?"

Rahima ta zauna kusa da ita daf da katifar ta gaisheta tukunna kana ta ajiye ledar data riko mata lemu da ayaba tace "Allah ban gujeki ba Hajiya hidimomin ne sukayi yawa, Abdul na baro sa gida naga darene yasa bance ya rakoni ba, Su Baffa da Umma na gaidaki da jikin."

Tace "Nagode Allah yai albarka Ina amsawa, ita Umma takan lekoni, nima nakan aiki Mairo ta dubota.".

Rahima tayi shiru, zuwa can ta tambayeta "Hajiya ko irin rashin lafiyar nan ce da kika taba yi bayan an kawoni ba dadewa?"

Ta amsa "Ina tsammanin shine, domin yanayin jikin nawa kasala ce ke rufeni inji ko hannuna ban iya dagawa balle inyi motsi mai karfi, ga rashin samun isashshen barci, dare ya tsala kiga kowa na barci Ni kuwa lokacin nawa idanun zasu bushe in kasa barcin in rasa kuzarin tashi in gabatar da kiyamul lail yadda na saba, shi yafi damuna."

"To kin sanar da Yaya kuwa?"
Ta kada Kai "Hhmmm wannan Yayan naku hidimomi sunyi masa yawa, baida kwanciyar hankali wallahi har tausayinsa nike ji shiyasa nayi biris da tawa lalurar."

"Hajiya ba'a yiwa ciwo haka fa, idan ya fahimci halinda kike ciki ba zaiji dadi ba, to Yaya Hayatu fa?"


"Shima bai sanin ba Yana can yana zirga-zirgan Shirin tafiyarsu Hajj."
Rahima tayi dan murmushi "Ai kuwa da sauran lokaci ko azumi ba muyi ba."
"To Rahima Mai kwarmin ido ba da wuri yake fara kuka ba? Duk da ba karamin kuzuri aka biya musu gara dai su nema su Kara saboda mutum bai San yanayin da zai kasance a kasar da ba tasa ba."
"Hakane gaskiya, zuwa Hajj Kam a wannan lokacin said mutum ya shirya, Allah yasa a dace.".

Hajiya tace "To ameen, tabarbarewan al'amurran kasarmu sai addua."

Rahima ta tuna dare ne ba rana ba, ta yunkura ta mike tace "Hajiya dare nayi bari in isa gida Zan dawo in an kwana biyu.'

Ta bita da kallo kawai na ciki na ciki, tana son yi mata maganar Daktan ta kasa, Rahima na jin nauyinta kar ta matsa Mata, taja baki ta tsuke... Kafin suyi sallama amon muryar da kesa gabanta faduwa ce ta tsinkayo yana magana da Mairo... Nan take kirjinta yai mata nauyi sanadiyyar bugawar da zuciyar keyi ba control, tun kafin ya iso kamshin turarensa ya Kara tabbatar mata da shigowarsa.

Ta mutu a tsaye, gaga tsara gaga, wannan shine gaba damisa baya siyaki, Ina zata shiga, uwardakin Hajiya ko saurin ficewa?
Ta juya kwakwalwarta tayi dim ta tsaya cak! taki aiki balle taba sauran sassan jikinta umurnin next step da zata dauka.

Ya kunno kai cikin dakin bayan Hajiya ta amsa sallamarsa, Yana shiga ya doshi gefen katifar uwar ya zauna, ya dago ya kalli Rahima dake tsaye a sandare yace "Ba dai har zaki tafi ba, daga can gida nike Umma tace kina nan."


Da za abata zabi da basu ko gaisa ba ta sulale ta gudu that's in tafiyar zata yuwwu mata kenan da gwiwoyin da suka yi sanyi har kafafunta na rawa, nan ta durkushe ta gaisheshi.

Amsar da ya bata cikin sakin fuska ya bata mamaki, eh to a gaban Hajiya ai ba zai rinka wannan cin maganin ba a nata tunanin.
Cike da farin ciki da jin dadi ta kallesu "Ko zaka rage mata hanya ne tunda tayi shirin tafiya?".

Rahima ta girgiza Kai "Hajiya tafiyar guda nawa ce, ba komi nagode yanzun zan Kai gida, mu kwana lafiya, Allah ya Kara sauki."

Dr Haseeb yayi dan murmushinsa ba tare da yace komi ba.
Hajiya tace "To shikenan Allah ya bamu alkhairi, nagode Allah sa albarka."


Da hanzarinta ta fito waje ta saki wata ajiyar zuciya amma me zata gani? Mutumin dake jiranta ya fito daga mota ya karaso wajenta "Salamu Alaikum don Allah Hajiya ina son magana dake."

Ta kalleshi a tsorace ta amsa "Nima don Allah kayi hakuri bani da lokacin magana da Kai."

Babban mutum ne da ganinsa bata son cin mutuncinsa amma bai fahimci hakan ba ya sake matsawa kusa "Yi hakuri ki bani minti biyar kacal, sunanki da uguwarku nike son sani tunda kina sauri yanzun ki bani time in taho gida ga compliment card dina."


"Hajiyar ta gode rike card dinka don bata bukatar sanin sunanka an riga anyi mata miji.". Bata yi aune taji muryar Haseeb na maida jawabi.

Mutumin ya kalli Rahima yaji bata musa ba, ya kalli Haseeb duk da yana sanye da bakin glass dinsa fuskar nan ba alamun rahama nan da Nan yace "Don Allah kuyi hakuri sai anjima. Suna kallonsa ya shiga mota ya tafi.

Sun dade ba tareda cewa juna kanzil ba, ta tuna gida zata tafi, ta juya tace 'Nagode, ta fara tafiya...
Ya bita da kallo "Na yiwa Hajiya alkawarin kai ki so ki shiga mota mu tafi or are you ready for that kind of attention irin Wanda ya faru yanzun?"

Cikin siriryar murya tace "Ni bani na kirashi ba..

"Ba zarginki nayi ba, mu tafi ko?"

Tare suka shiga motar yaja suka isa cikin minti goma kacal. Motar na tsayawa ta bude kofar ta fito tace "Nagode a gaida su Aunty"

Ya waigo "Magana nike dauke da ita ko kina jin barci gobe na dawo?"

Ta girgiza Kai "Ba damuwa, mu shiga daga soro ko?"

Ya fito ta rufe motar yana biye da ita, suna shiga tace "Zan amso key din dakin baki.

Ta wuce cikin gida ta shaidawa Umman tana tareda bakone, Umman cikin farin ciki take wanda bai misaltuwa don ta gane waye ta Rahima ta kira bako. Har zata fita tace "Haka ake tarbon bakon ko ruwa ba zaki Kai masa ba balle lemu? Ban sanki da rowa ba Rahima."
Ba tareda da tanka ba ta bude fridge ta dauko gorar ruwa da lemo da cup ta dora bisa faranti ta koma soron, Yana ganinta ya mika hannu ya amshi kayan ta bude kofar tace "Bismillah."

Bayan sun shiga ciki ya ajiye farantin ya zauna kan kujera, Saida ta durkusa ta zuba lemun a cup ta ajiye sannan ta zauna gefen tabarma.
Ya dan kurbi lemun kadan ya mayar ya ajiye yana kallonta ta cikin dark glasses dinsa yace "Ina Abdul dina ne ko har yayi barci?".
Ta daga Kai "Ya riga yayi barci."

Yace "Yaron dana san yana kai wajen sha daya bai kwanta ba sai anyi ta fama dashi?"

Tace "Ban da yanzun kuwa ko don bai jin dadi ne oho."
Ya bude baki cikin mamaki "Ya akayi ban sani ba, baki aiko min ba ko Hajiya?"
Can kasa tace "Don naga ba it's not that serious."..
"Ya akayi kika San hakan?" Yai tambayar a fusace.

Ta sunkuyar da Kai "An kai shi asibiti sunce malaria ne sun bada treatment shi yasa naga ba sai na aiko ba."
Ya gyara zama "Daga yau karki sake min haka, duk abinda ya shafesa wajibi a sanar dani komin kankantarsa do you get me?"
Ta daga kai alamar amsa.
Ya kalleta sai Kuma ta bashi tausayi, ya sassauta murya yace "Look why not a daura auren nan this week mu ragewa kanmu jidali tunda Allah ya kaddaro mana haka, daman shawarar dana zo mu hadu mu yanke kenan. Mu ba yara bane, mun San ciwon kanmu naga zaifi dacewa ayi abinda iyaye keso zai fi mana sauki...

Rahima tayi shiru yaci gaba "Ko Hajiya abinda ke damunta kenan saboda ta sanya abin a ranta."

Ta dai kyalesa ya shirya mai yuwwa tana saurarensa yayi ya gama, ya mike zai tafi ya mika mata rafar kudi tareda tsadaddar handset.

Cikin kwanaki uku kacal aka gama tsarawa da shirya komi. Daktan ya aika kayan aurensa akwatuna biyar, ya shaida mata ba zai ajiyesu gida daya da Zuwaira ba ya nemi amincewar yazo su tafi taga gidan da ya saya inda zai ajiyeta a dorayi, tace ba sai taje ba.

Bata da niyyar yin kowanne irin shiri kan auren, Maryam tayi surutunta ta gaji ta kyale, ba tareda saninta ba sun shirya abinda ya dace game da gyaran gidan amarya sun Kuma nemi angon yasa an kaisu suka tsara shi yadda ya kamata amaryar data hadu a ga gidanta.

Ranar da za'a daura aurensu tunda asubah aka nemi Daktan ya taimaka ya nufi Riyadh dubo maras lafiyan Nan, wannan karon ba gardama, aikinsa ceto rayuwar dake neman agajinsa da taimakon Allah in yai nufin patient din ya tashi, in Kuma lokacinsa yayi ba makawa.
Yana gab da tashi ya kira Rahima ya bata hakurin rashin samun daman halatar daurin aurensu, tace ba komi Allah ya kai shi lafiya ya dawo dashi cikin amincinsa, tayi masa adduar Ubangiji ya bashi sa'a yayi nasaran shawo Kan ciwon da yai tafiyar dominsa.
Karfe bakwai daidai na agogon Nigeria jirginsu ya daga suka nufi kasar Saudiyya kan hanyarsu ta isa babban birnin kasar Saudiyya, Riyadh.
10/09/2020, 22:44 - Anty saliha: ...RAHIMA..doc by jami

26

Abin sha'awa iyaye, 'yanuwa, da abokan arziki ne suka tsaya aka daura auren Abdul-Haseeb da Rahima.

Kafin ayi haka labari ya baza gari, jama'a suka shiga fadin albarkaci bakinsu wasu suka ce yaci amanar Rabiu, wasu suce daman can da kulalliya tsakaninsu, surutai dai gasu nan barkatai masu matukar daga hankali musamman ga wadanda abin ta shafa, da yake shi angon yai nisar kiwo sai damuwar ta tattara kan amaryar kadai daman cu
cikinta take. Ta yini babu karsashi ba walwala ba wani kwalliya, bata gayyaci kowa ba hatta collegues dinta basu sani ba, to abu ya taras da miskillancin tsiya, ita Sam bata damu tayi kawa ba a tunaninta Maryam ce kawarta, aminiyarta Kuma 'yaruwa rabin jikinta.

Umman da Maryam sunce ba za suyi taron buki tamkar ana zaman makoki ba don haka suka gayyaci dimbin jamaa bayan 'yanuwa wajen yinin bukin da suka shirya.
Taro yayi kyau, an ci an sha an koshi, bayan azahar masu wa'azi suka dasa tasu nasihohin suka rinka fassara ayar Allah suna fassarawa. Suka fara da fadakarwa kan masu ganin auren wa ta auri matan kani jahilci ne suka yi kaca-kaca da masu kafa tsirku kan fadin Allah, suka dawo suka yiwa amarya nasiha kan hakkokin mijinta da suka rataya a kanta, suka hangaro na tarbiyyar diyanmu kana daga karshe suka rufe da matsalar data fi addaban Mata yanzun 'kishi'

Wa'azine masu ratsa zuciya da shiga jiki ga wadanda keda sauran imani sun kudurta gyaran kurakurensu, ga wadanda suka yi nisa Kuma sai ido .

Karfe biyar na la'asra Jamila da Haulatu suka jagoranci tawagar sauran matan kannin Daktan suka taho, a nan drama ta tashi Rahima na kiransu Aunty a matsayinki na matan wan mijinta, yau kuwa reshe ya juye da mujiya, ita ta koma Auntyn tasu a sabon matsayin da Allah ya bata matar babban Yaya.
A can ainihin gidan Daktan uwargidan amarya ta gayyato kawayenta marasu mutunci sun cika gida makil, hatta 'yanuwanta komawa gefe suka yi suna kallonsu ..
Kawayen sun gama zugata da bata shawarwarin da ba zasu amfaneta ba, harda shirya mata abinda zata yiwa amaryar don tasan ba wurin zamanta bane.
Shashashar ma ashe bata san ma cewan ba gida daya zasu zauna ba, Saida ta aika gidan Hajiya a dubo ko tana can ne aka fada mata dorayi aka kaita.
Ta dakawa Dan sakon tsawa "Dorayi wane gida? Jeka dubo min ka dawo yanzun."
Suna ta yi mata famfo tana hauka cewan ai kamarta raunin hankaline ma ace mijinta yai mata kishiya ko wane dabiun kwarai take dasu da zai hana ayi mata oho.
12/09/2020, 13:05 - Anty saliha: 🦈🦈RAHIMA🦈🦈
28
Ta sauki mintoci heart beat bai koma normal ba, watau a takaice so da kaunar Ya Haseeb na neman mamaye mata ruhinta, ta girgiza Kai wannan ma ai shine abin kunyar, hhmmm da zai fahimci haka ya zai dauketa, maras tunani ko maras matunci? In kuwa hakane gara ta yiwa kanta rigafi ta danne zuciyarta zai fi mata alkhairi.

Ba sauran barci a idanunta don haka ta fito daga dakinta ta nufi kicin inda ta taras da Uwale harta kama aikin hada breakfast, tana ganin Rahima ta durkusa ta gaisheta "Hajiya barka da fitowa."

Ta amsa "Ina kwana Uwale ashe kin tashi tun dazun."
Tayi dariya "Ai mun saba, a can kauye ina muka ga lokacin barcin safe, muna alla-allah bayan munyi sallah mun karya kummalo da dumammen turo mu zuba hatsi a turmi mu shiga neman na abincin rana mu da yara..

Rahima tace "Gaskiya kuna kokari,kuna wahala, shiyasa akace mutum ta rinka kallon na kasa da Kai, nan zaka gane ni'imar da Allah yai masa sai Kuma ka gode masa don wasu sun fi kane Kai Kuma kafi wasu, amma gaskiya idan kika duba rayuwar matan karkara sunada matukar tausayi, sai muce mu aljanna muke."

Uwale ta nisa "Ina ma ki kasan haka Hajiya, sai Kinga macen kauye a ce miki sa'arki ce ki yita rantsuwar ba haka bane don ta kusa haihuwarki a fuska, ta tsofe ta komade saboda wahala, hakora sun zube, ba isashshen ingantaccen abinci, ba hutu, na kyakkyawar muhali balle wani sutura mai kyau ga rashin samun kulawa daga mazajenmu, yawanci mazanmu fa basu San darajar mace, iyakar ki dashi ki dafa abinci, wata har noman abincin ma da ita za ayi, kiyi surfe da daka, idan ya bukaceki ya sarrafaki kamar yadda yakewa jakarsa da yake kiwo,idan kin dauki ciki ki babu wani kulawa, wajen haihuwar ma wani a rabu kacar sabida yaushe ya barki Kika je wani asibiti don inganta lafiyarki balle na dan cikin ko jariririn da aka haifa, wasu kuwa don su doki mace ba wani aibu bane a garesu, to mazan nawa ne suka san hakkokin matan da ya rataya a kansu?" Dalili kenan koda mijina ya mutu zawarawa suka yo min caa!! Nace bada Uwale ba, anyi daya ba za a kara na biyu ba, da in zauna cikin jahilci da rashin sanin me auren ya kunsa da rashin sanin hakkokin juna gara in taho birni in nemi sana'a."

Rahima ta nemi kujera ta zauna tace "Bari in tayaki aikin mu ci gaba da hirar sai mu karu da juna..

Uwale tace "Ai ke Hajiya Allah ta tarfawa garinki nono, da mata na dacen irin mijinki da ba za suyi kukan komi ba, ko su Mairo da suke 'yan aiki sun shaida balle ku, kin kuwa ji ance kyakkyawar safiya tun daga maraice ake fara ganewa, jumma'ar da zata yi kyau tun laraba ake ganeta, wallahi haka nake son namiji yasan mutuncin 'ya mace.

Rahima tayi dariya "Ai ko mazan namu ana samun wadanda basu San darajar macen ba, da na dauka jahilci ne yasa wasu mazan ke maida matansu tamkar jakuna ashe ba hakan bane, ko a birnin haka wasu mazan suke, kiga namiji bai san mutunci da darajar matansa ba, mace bata isa yai shawara da ita ba, don a ganinsa shirme ne, ke wani fa ya dau mace tamkar Mai karamar kwanya ce don haka baki Kai matsayin da zai fada miki wasu sirrinsa ba, sai kiji wani na kiran matarsa Wai dabba ko jaka don rashin sanin kimarta da rainin hankali, amma bai hana ya nemi
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any

Please Login or Register in order to submit comment