Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

sai ka gama ja min rai Rabi'u?"
Yayi dariya "Sunan Ya Haseeb yaci, Abdul Haseeb karami ne Hajiya."

Ta gintse dariyarta tasha mur "Maimakon ka sa sunan mahaifinku da Allah yaiwa rasuwa, mene naka na saka sunan wanda yake raye?"

Rabi'u yace "Ina Sunusin Ya Hayatu sunan baban yaci Hajiya, tunda yasa ba lale nima sai na saka ba, bukata a samu magaji an samu ai, ba Kuma sai mutum ta mutu ake saka sunansa ba, Hjy Ya Haseeb ya cancanci wannan adalcin daga garemu din da taimakonsa Allah ya hadamu aure, don haka kiyi fatar alkhairi kawai.".

Daman ba Wai bata ji dadi bane, ah ah ta yaba da kaifin hankali da tunaninsa kwarai, ta gyara zama tace "To Rabiu Allah ya raya mana shi yasa dadin musulmi ne yasa ya gaji mai sunan."
"Yauwa yanzun ki Kai magana, Ameen Hajiyata."
Anyi suna an ci an sude, Hasseb babba yana can wani aiki a babbar asibitin dake kasar Morocco, sai labarin haihuwar yaji da labarin anyi masa takwara. Da zai dawo sayayyan musamman ya yiwa uwa da namesake dinsa din nuna jin dadin karamcin da aka yi masa, yazo har gida yaga jaririn da ake fadin yafi kama dashi a bisa mahaifinsa.

Cikin watanni biyu Abdul Haseeb ya murje yayi 'yar kiba har ya fara wayon gane iyayensa da kakarsa da yake yini can wajenta.
Suna gab da kare bautar kasa wata rana, Rahima ta gama shiryawa maigidan abincin rana ta girka masa tuwon shinkafa miyar alayyaho abincin da yafi so kenan, sai gashi ya dawo ya hayo sama dauke da Abdul a kafadarsa yana rike da jakar aikinsa a hannu daya. Ta tarbesu ta amshi jikar tana masa sannu, ya amsa Yana ci gaba da yiwa dansa wasa, ta tsaya ta zuba tagumi tana kallonsu tace "Kana bani mamaki, yanzun daga shigowarka kaje ka dauko yaron nan ko kunyar Hajiya baka ji, haba ana son kawaici don Allah."

Ya kyalkyace sa dariya "Ita Hjyr bata damu ba, ki tuna tun safe yake wajenta sun yini tare, Ni kuwa sai yanzun na Sami damar wasa dashi."
Ta kalli Abdul "Hhmmm ko baka koya masa kimi ya koyi kyuya, duba yadda ya kura maka ido Yana kallonka."

Rabiyu ya zaunar da Abdul bisa cinyarsa yace "Da Kuma fa gaskiyarsa gashi ba nine babansa ba."
Ta bude baki cikin mamaki "Ba kaine ba to waye ubansa?"
Ya amsa "Maida wukar, nina haifi abina mana Amma Ya Haseeb ne babansa."
Ta hararesa cikin wasa "Tunda aka haifi yaron nan kake wannan furucin, kowa yasan a mtsayinsa na yayanka dole a kirasa baban Abdul ka taba ganin an raba anta da jini?"

Yace "Inda Mai iyawa ai sai a basa ya gwada mu gani."
Ta gyara zama "Hhhh Ni dai kawo sa kaci abinci."

Ta karbesa ta goya, ta jera masa abincin ta zuba masa suna hira, yana cin abincin yana dan tsayawa , can ya ture plate gefe yace "Na koshi."
Ta kallesa cikin damuwa" Abinda na lura kwanannan baka son cin abinci ka koshi har ka fara rama, wani Abu na damunka ne?"

Ya girgiza Kai "Ba wani abu bane, just cikina ne ya cushe ko naso cin abincin sai inji na koshi dole nakan hakura."

Tace "To muje asibiti mana, mutym ya zauna sa cuta a gida?"
Ya taso ya dafa kafadarta "Karki damu kanki da yawa, dazun da ya taso min a office Nan da Nan na ziyarci clinic dinmu suka ban magani nasha naji dadi wallahi sai anjima karfe tara na dare zan Kara sha."
Fuskarta ta canza "Rabi'u baka da lafiya ka boye min?"
Ya rungumota "Afwaan Rahima ba wani sabon Abu bane da baki sani ba, kinsan na kanyi ciwon ciki muna school amma after 3-4 days nakan sami sauki inci gaba da harkokina, a gaskiya na dade ma banji ya tashi ba that's nima ban koma asibiti ba amma insha Allah gobe sai mu tafi."

Tace "A takaice ma baka San kowacce irin cuta ke damunka ba."
Yace "Sun Fadi Amma ban wani rike ba na manta."
Ta sassauto "Hhmmm to Allah ya saukaka ya baka lfy, Amma don Allah ka kula da kanka, we do need you."
Yayi murmushi "I need you too my love."

Gari ya waye, bayan sun kammala ibadarsu da yin kalacin safe suka fara Shirin fita wajen aikinsu, Rahima na duke tana shirya Abdul taji wata irin kara mai firgitarwa, ta saki Dan ta nufo Rabi'u dake kwance dafe da cikinsa tabbacin karar daga makoshinsa ta fito, a rude tazo ta dafa shi tayi kokarin dagasa ta kasa, ta kira sunansa ya amsa da kyar yana numfarfashi yace "Cikina Rahima....
"Sannu, bari in Kai Abdul wajen Hjy mu tafi asibiti...
Ta sungumi Dan ta sauka kasa a guje ta isko Hjyr na azkar ko gaisheta bata tsaya yi ba ta mika Mata Abdul tana fadin "Hajiya babansa babu lafiya asibiti zamu tafi."

Ganin yadda take a rude itama ta goya Abdul ta bi bayanta suka hau saman tare a ranar bata ji wuyar data kance yana mata ba .
Taga halinda yake ciki, har kamaninsa sun canza, ta sake fitowa tayi waje neman makwabta suzo a taimaka musu a fito dashi. Kafin kiftarwa ido maza sun taru an daukoshi an saka a mota suka nufi asibiti, Rahima da aka hana binsu kuwa gidansu ta nufa tana kuka, suna jin abinda ke Nan, Alh Mamman da kansa ya daukota da Ummansu suka nufo gidan Hajiyar inda suka taras ta kira Yayyinsa tana fada musu su wuce asibiti suma gasu nan tafe.

Asibitin Murtala aka kaisa inda da shigarsu ba bata lokaci manyan likitoci su kayi caa a kansa, nan da nan babban likita yace aje ayi hoton cikin don sanin matakin dauka da gaggawa.
Dr Haseeb da Hayatu suka isa hankali a tashe, suna ganin halinda yake ciki suka dimauta.
Anje anyi hoton, likita ya duba ya fara rubuce-rubucen magungunan da za a fara bashi kafin su gama bincike Rabiu ya bude ido da kyar ya hango dushi-dushin Haseeb, ya dago hannu a galabaice ya miko masa, Haseeb ya fahimci magana yake sonyi don haka ya duka daf da bakinsa...
Cikin rada maganar ta fito "Ga amanar Rahima da Abdul....
Yace "Na karba Rabiu Allah zai baka lafiya...
Haseeb bai gama rufe bakinsa ba Rabiu yai kalimatu-shahada ya cika.. Nan aka yita .
Dagowan da bai ita yi da kansa ba kenan Saida aka kamashi yana salati .Innalillahi wa Inna ilahirrajiun.

Mutuwa kenan, daci Mai kore Zaki, Mai raba da da mahaifi, Mai raba Mata da miji, Mai raba danuwa da danuwa, Mai raba masoyi da masoyi, Allah yasa mu cika da imani.
Duk da cewa Ubangiji yace bai halicci wani don wani ba, a ko yaushe muka yi rashin daya daga cikinmu al'amarin Kan zama sabo, bamu iya dauriya dole muyi juyayin rashi da tausayin kanmu tare da fargaba da tunanin cewan muma fa komin dadewa wata rana sai mun tafi lahira. Allah yasa mu cika da imani
Maganar halinda yanuwa da abokan arzikin marigayi Rabi'u suka kasance bata ko taso ba balle matarsa Rahima, Hajiyarsu kawai Allah ya saukarwa dauriyya ta dake ita ke baiwa jamaa hakuri

Bayan kwana bakwai kowa ya watse sai wasu daga cikin dangin uban Rabiu da kanun Hjy Kaltume Mata biyu don suci gaba da debe musu kewa. Hayatu ma Kan kawo matansa su yini. Wani ikon Allah rasuwar Rabiu ne ko shiriyar Ubangiji ne yasa yasa su natsuwa da kama kansu har jamaa na mamakinsu oho. Shima Haseeb matarsa na zuwa ta koma da laasar, Maryam ma na tafe duk bayan kwana biyu, jamaa kowa nata kokarin ganin an debe mata kewa.

Ita kuwa sai kallonsu take, hawaye sunki kafewa a idanunta musamman idan ta dauki Abdul tana bashi nono. To tun hawayen na zuba har sun kafe ta fara kukan zucci. Idan ta tuno rayuwar da suka yi, watau haka Allah ya kaddari rabon Abdul ne yasa akayi aurensu a gaggauce, rabuwar ma Allah ya kawo kwatankwacin hakan. Oh Allah ka jikan Rabiu ka sanyaya masa, hakika sunyi rayuwar auren daya dace, rayuwa mai cike da nishadi da farin ciki abin shaawa fa kowa, da karshen tazo Allah yasa shakuwa tsakaninsu bayan so da kaunarsa da suka fara tasiri a zuciyarta, Ashe Wai ba za akai ko Ina ba, Ashe rayuwar tazo karshe.... Hawaye masu zafin gaske suka gangaro zuwa kumatunta suka diga kirjin Abdul, ya saka kuka, ta lallasheshi, ita tama manta Yana bisa cinyarta, da Hjy Kaltume ta lura ta shiga yi Mata fada, ta dawo tayi nasiha taci gaba da lallashi, maimakon tayi shuru hawaye sai Kara fitowa suke Saida ita kanta Hajiyar da sauran mutane suka koka.
04/09/2020, 17:24 - Anty saliha: ...RAHIMA..doc by jami
11
Kafin ta gama takaba 'yanuwa, iyayenta da dangin mijinta kaf sun nuna mata gata Kuma ita wata ce a gare su don Haseeb ma ba a batun dawainiyar da yake musu ita da danta Abdul karami, tun bai saba da wan uban nasa ba har yai sabo dashi kwarai saboda yawan dauka da fita dashi yawo da yake in baida aiki sosai a asibiti...
Kwanci tashi ba wuya Rahima ta gama takaba, ta Kara sati guda da kyar kana ta tattara kayanta tace gidansu zata koma. Wani sabon tashin hankalin, ranar Abu ya koma sabo to amman barin gida ya zama dole don ci gaba da harkokin rayuwa.

Bisa yarjejeniyar ba zasu amshi Abdul ba sai ta sami wani mijin ta goya danta suka koma inda tafi wayo, gidan Alh. Mamman.
Makarantar da take koyarwa basu saketa ba ko bayan gama bautar kasarta nan suka dauketa aiki taci gaba da koyarwanta.
Gama takabarta keda wuya masoya suka ce sallamu alaikum, harda wani abokin Rabiu da suka kare school tare, wani ikon Allah saurayine shi ko auren fari bai yi ba, ya kasa dumfararta da kansa sai letter ya tura mata Wai Yana jin nauyi, yadda bata saurare shi ba haka taki sauraren kowa cikin zawarawan dake mata Kara kaina tun daga wajen aiki har gida, da ma wani abokin Alh Abbas mijin Maryam Wanda uwargidansa ce ta rasu ta bar diya biyu, Yana son suyi aure ya rike Mata da ta rike masa nashi, shima bata cewa Abbas din tana yi ko ah ah ba, kusan duk Wanda ya nemi kusanci sai tace a bata lokaci tayi shawara, a zahiri kuwa ra'ayin sake auren ne bashi a zuciyarta, a nata tunanin ma da za a barta haka zata yi zamanta din tasan zata iya tsare mutuncin kanta dana iyayenta tunda Allah bai halicceta kharija ba, wai don a matsa mata da batun auren ne taki yaye Abdul da ya Kai kusan shekaru biyu. Umman tayi-tayi ta gaji tasa mata ido, gara bata son bacin ran Rahima daidai da kwayar zarra, suka ci gaba da lelen Dan da yake gudu koina, wani burgewa ma sai ya gama yawonsa ya dawo ya zauna yace 'Mami zan Sha mama'
Irin sangarcewar da yayi Maryam ta taho ta gani ta fara masifa, Umma ta fara kakkare Rahima, ita din ma tace Umma karki kula surkulenta, shin don ta yaye Walida sai tace sai na yaye Abdul?"

Umma tace "itama ba yayen Allah tayi ba ciki ya sa akayi saurin hanata nonon.".
Rahima tayi dariya "Ah to gane min hanya Umma na makaho da yaso tsegumi. Kin ganni ni ba miji ba, Ni ba wani kwakwkwaran bazawari ba mene nawa na hanzarin cire yaro a bakin nono, Maryam ko tausayin Abdul ma ba kya ji."

Taja tsaki "Ke da Umma ke ban tausayi sabida ga gaskiya kiri-kiru Kun take, shun Umma kin kalli diyar taki da kyau Kinga yadda ta kode tana kanjamewa?"

Cikin damuwa tace "Na lura sosai, nima ramar nata har tsoro take bani, yarinya taki sakin ranta ta hakura, wallahi kullum fadar da nike mata safe da yamma kan ta fauwalawa Allah rashin da muka yi shi Kuma Allah yasa yana cikin rahamar Ubangiji.'

Maryam ta gyara zama daman gangara take nema tace "Umma ban tari numfashinki ba, ya za ayi ta samu natsuwar hankali tana zaune muku haka kawai. Ni a ganina duk halinda data shiga laifinku ne, baku matsa mata ta samu miji tayi aure? Kawai Kun Kyaleta sai biye mata kuke, har kin yayen nan don kar a sami kafar mata batun aurene."

Rahima ta harari Maryam "Umma ki daina saurarenta kinsan halinta da zuga."
Umma ta nisa "Wannan karon Kam gaskiya take Fadi na Kuma gano kamshinta bari Baffanku ya dawo."

Ta sunkuyar da Kai ta dafa Umma "Don Allah karki hadani da Baffa Umma nayi alkawarin yayesa cikin satin nan.".
Maryam tayi Mata gwalo tukunna kafin taci gaba "Ai ba yayen ba ta fitar da miji shine batu, tayi alkawarin zata amince ba zata kara kin sauraren wani abu har Allah ya zaba mata mijin."

Rahima ta rike haba. "Oh ni na shiga uku, Maryam hala kudin kanfen Alh Surajo ya Baki?"..
Umma ta kallesu "Wani ne Kuma haka?"

Maryam ta gyada Kai "Kyaleta Umma da 'yar halas take magana, amma ba za aji mutuwar uwar sarki a bakina ba, ta fada miki ko waye shi."

Baki dai shi kan yanka wuya, dole ta yaye Abdul din ranar jumma'a bayan an aikawa kakarsa. .
Kaji, zabbi,madara dasu bornvita da sauran tarkace banda sabbin tufafi aka tarkato, banda buhun shinkafa da jarkar Mai, matan Hayatu suke takewa Hjy Kaltume baya wajen zuwa diba Dan yaye, shima wan baban nasa kudi ya bashi matansa kuma crates din kwai.
Rahima na gida bata futa aiki ba saboda zazzabin da ciwon nono ya sa Mata, ganin bakin yasa ta tashi ta zauna.

Bayan an gaisa Abdul ya dare bisa cinyar kakarsa yana baje sabbin kayansa.
Umma nata zubawa su Hjy Kaltume godiya.
Hajiya tace "Duk aikin iyayensa tawa tukunyar farfesun na gida sai ya taho zai ci.
Umma ta kalli su Hayatu "Madallah Allah ya baku ladan zumunci."
Yace "Ba komi Umma Abdul danmu ne koda Rabi'u na nan balle yanzun da kasa ta rufe idanunsa."
Tun dai Rahima na dauriyyar Kar suga kwallan da take kokarin maidawa har ta bara sai nishin kukanta suka, hankalin kowa ya tashi din sun san ba shakka uban Dan ta tuna.

Ana haka Baffa ya shigo cikin sauri ya tsugunna suka gaisa da bakin kana ya fara rarrashun diyarsa cikin kalamai masu taushi har hankalinta ya koma jikinta ya kara yin godiya ya fita..
04/09/2020, 21:15 - Anty saliha: ...ˆRAHIMA...doc by jami

12

Sun dade suna taba hira tun Rahima bata saki jiki ba ta warware a nan ne Jamila ke ce Mata "Kiri-kiri kin guji gidanmu Rahima."
Haulatu ta kalli uwargidanta tace "Ke dai bari Yaya nima abinda ke zuciyata kenan."
Rahima tayi murmushi tace "Aikine yai min yawa a school amma kuyi hakuri Ina nan zuwa."

Hayatu ya kalli matansa cike da jin dadin ganin yadda suke tafiyar da al'amurransu yanzun sabanin da, yayi murmushi yace "Idan baki taho don komi ba Kya zo mana murnan tafiya sauke farali ko don Allah yayi bana za muyi arfa Ni da Jamila."

Tace "Iye! Shine baku Fadi ba tun zuwanku, laifinki nan wannan Aunty amarya."

Haulatu tace "Yi hakuri wallahi labarin dana kunso in fada miki suna da yawa ganinki haka yasa nayi sanyi, da gaske Ya Haseeb ya biyawa Maigidan da Uwargida kujerar hajj bana."

Jamila ta amshe "Itama amaryar anyi mata alkawarin badi da ita insha Allahu."

Umma ta kalli Hjy Kaltume tace "Masha Allah Kai Allah yai wa wannan yaro albarka, shi dai dukiyarsa ta dawainiya da jama'a ce, kunga hidimar da yake yiwa su Abdul kuwa?"
Hjy Kaltume tace "Don Allah ki bar wannan maganar Habiba, kula dasu ya zama dole."
Rahima ta kalli su Hayatu tace "Naji dadin jin labarin nan, Allah ya nuna mana anje an dawi lafiya, shi Kuma Allah yai masa sakayya yasa muji na Aunty amarya haka badi idan muna raye."

Daga nan sukayi sallamar tafiya, Rahima ta rakosu kofar gida tayi musu alkawarin ziyartarsu wani satin.

Bata tafin ba sai wajen sati na uku bayan tayi sarai ta koma tamkar bata taba wani shayarwa ba. Tana isa gidansu Hayatu ta kara tabbatar da ba abinda yafi zama lfy da kwanciyar hankali, yanayin gidan ya canza, maigidan ya Kara gyara ko'ina tsaf, mata da yara sunyi shar, shima yayi fes har kiba yayi ya fara teba. Ta kasa boye sha' awarsu cikin hira tace musu "Nifa kun burgeni, Ina mamakin canzawarku, wani shahararren malami yai muku waazi ya shige ko Yaya?
Suka kalli juna suna murmushin fahimta kafin Jamila ta fara magana "Alamarun Allah ne, kinsan idan yaso mutum da shiriya, ba abinda myuke yanzun sai godiyar Allah da ya ganar damu."
Haulatu ta karba "Wallahi mun fahimci ba abinda ke jawo tsiya irin tashin hankali da masifa."
Hayatu yace "Nima kullum cikin godiyar Allah nike, da har fargabar shigowa gidana nike, dana doso kofar gidan sai gabana ya Fadi don ban San bala'in da zan shigo in taras ba, Ina kuwa shigowa abinda nike gudun zan taras, kiji harshensu na tashi kamar zasu dafa naman junansu, inyi -inyi su bari ko kallo ban ishesu ba sabida sun riga sun hau dokin shaidan Yana sukuwa dasu.
"To kuma meye na tashin tashina, kuskure ne munyumi, mun gane mun tuba mun dawi hanya. Jamila ta koro jawabin...
Haulatu tace "Rabu dashi dai Hajiya to waye bai kuskure?.
Rahima tayi dariya "Kwarai dukkan Dan Adam ajizi ne dole a samemu da aikata kura-kurai yau da kullum shiyasa ake son mutum ya rinka rokon Allah ya shiryar damu hanya madaidaiciya ya Kuma ganar damu ya bamu ikon bin tafarkin gaskiya, kana ya yafe Mana zunubanmu na biye da sarari, wadanda muka sani da wadanda bamu sani ba.Amma Ina ganin fa tun farko laifinka ne Ya Hayatu."..
Ya kalleta cikin mamaki "Kamar yaya? Alhalin kullum Ina kokarin yin adalci tsakaninsu, fitina ce kawai amma da suka ga ba riba sun sauke.".
"Au Kuma haka zaka ce?" Suka tara Fadi
Rahima tace "Ni dai na fahimci bala'in son Yaya kuke shi ya jawo muku bakin kishin Nan."

Ya sosa keys "Haka ake so? Ina ce in har son ne competition din kyautata min ya dace suyi ba rigima da juna dani kullum kaina dana aje su ba, tsaya kiji wani sirrin kanwata wallahi da sunci gaba da shirmensu ko da yanzun na Kara aure din har na kusa gama shirya komi, Kuma banyi niyyar hadasu gida guda ba, in. Koma can in tare hankalina kwance su kuwa suci tsiyarsu nan inga karyar kishi."

"Allah ya tona maka asiri, ashe amanar mu kaso ci muna zaune tun baka da komi daka samu shine zaka dauko wata taci arzikin? Da wallahi kun gane kurenku data gwammace bata aureka ba."
Rahima ta dafe kai tana dariya tace "Wai ni kaina Ya Hayatu ka yarda da batuna, Kuma na baka goyon baya muddin suka ci gaba da halinsu ka aikata abinda kace daga nan a ga wacce tafi sonka.".

Suka taso kamar zasu cinyeta danya dyk da sun san wasa take, Saida ta basu hakuri tace ai ba sauran batun wata amarya tunda kun hada Kai Kunji ance zama lafiya yafi zama dan sarki, muddin za ayi hakurin zama da juna sai kuga Allah na taimakanku, wadata ya sameku, maigida yaji dadin kyautata muku, yaranku su tashi cikin ingantacciyar tarbiyya da kyakkyawar hadin Kai da zumunci da son junansu ga kwanciyar hankali da samun natsuwa."..
Suka ce wallahi mun gane kanwarmu Allah ya ganar da sauran mata Ina alfanun mugun zama, mun gode da shawarwarinki, Allah ya kawo mana suruki nagari."

Nan da nan ta bata fuska "Anya zaku same shi da wuri?"
Hayatu yace "To aure dai sunnar manzo ne nasan kinsan hakan, mu ba zamu so ki zauna ba aure bayan rasuwar Rabiu ba sai a rinka zargin wani abu."

Ta nisa "Ai ba cewa nayi ba zanyi ba, Kai kasan zaman da mukayi da kaninka, Ina zan samu Mai kwatankwacin halayensa?"

Jamila tace "Su din dangin gujiya ce, sai an fasa ake sanin na kwarai, ki fasa ki gani Mana."

"Na tabbata zata sami Mai gari kuwa, mu dai mun kosa mu sha buki."

Tace "Tsokanata ma kuke, bari in shige gidanmu.
Ta koma gida tana tunanin hirarsu dasu Hayatu. Aure? Ita har tsoro kalmar ke bata ba don komi ba sai domin rashin cikakken kwanciyar hankalin zabin wanda zai zama abokin rayuwarta da tunanin yadda zata Kara sake koyo kaunar wani da namiji tunda har lokacin bata sami Wanda ma ya kwanta mata a rai ba ko jininsu ya hadu balle a kai ga batun aure..

Maganar abokin marigayin ma bata taso ba don a ganinta da zata aureshin ma taci amanar marigayin kenan duk da ba addini ne ya hana ba, a daya bangaren surutun jama'a fa kasancewarsa saurayi Wanda bai taba aure ba, ita kuwa harta haihu, shin zata iya daure gutsuri tsoman daka iya yiwa auren dabaibayi? Ina batun danginsa, shin zasu karbeta ba tareda wata tsangwama ba,? Ajiye batunsa a gefe shine alkhairi,to Alh. Suraj fa dake da magoya baya irinsu Maryam harda Umma da ta fara shiga ciki, idan bata yi taka tsantsan ba sarkin yawa yafi sarkin karfi lalle suna iya taruwa sufi karfinta, ta tsaya tayi nazarin Alh Surajo lalle yes mutum kamili sai dai ba nan gizo ke sakar ba ta kwatanta kaunarsa a zuciyarta abu ya faskara in ba hakuri zata yi ta auresa hakan Nan ba ta koyi so da kaunarsa yadda tayi na Rabiu amma idan tayi hakan shikenan bata da ranar jin dandanon zakin zumar soyayyar da Maryam ta kwadaita mata kenan? Oh oh Allah gani gareka, kayi min zabin abinda yafi zama alkhairi a rayuwata.

Wasa-wasa watanni sun Mika sunyi nisa har ana neman hada shekara da rasuwar mijinta, amma ba amo ba labari ba alamar zata fidda miji cikin masoyanta da suka kasa rabuwa da ita suyi fushi.
. Abdul karami har ya shiga nursery, mamansa kuwa ta Kara sadaukar da kanta ne a aikinta, lokacinta na yaran da take koyarwa ne Wanda Allah ya dorawa lalurori iri daban-daban, kullum tausayinsu karuwa yake, kusancinta dasu ya fiye mata komi don haka ta manta shaf da wani batun aure, tunanin zama da wani ya shafe ya goge a ranta.
04/09/2020, 23:29 - Anty saliha: ...RAHIMA..doc by Jami

13

Akai-akai take zuwa gaida tsohuwar sarakuwarta, duk sati ta Kai Abdul yai mata hutun karshen mako, su da kansu dangin uban suka raba yadda yaron zai rinka ziyaryar ko'ina don ya saba da sauran 'yanuwansa.
Ko yaushe Rahima ta ziyarci Hajiya saita yi mata fadan kin yin aure, a gida ma tun iyayen nayi sun gaji sun saka mata ido, yaruwarta Maryam ma na irin nata kokarin don ta ciwo kanta su zama matan abokai duk tayi kunnin uwar shegu.

Wannan satin Abdul gidan takwaransa yai weekend, ya daukosa ya maido gidan Hjy don mamansa nan zata taho daukarsa kasancewar Zuwaira bata gari. Tunda suka shiga gidan Abdul ke manne da Haseeb yaki yarda ya sauka daga cinyarsa balle yaje wajen kakar Saida tayi masa dabara aka samu da kyar mairo mai aikinta ta goyasa suka nufi wake sannan ya gaisa da mahaifiyarta..
Hajiya tace "Yaron Nan ya shaku da Kai Kwarai da gaske."..
Ya amsa "Haka kowa ke Fadi, gashi yana jin maganata ko rigimar banzan sa ya fara yaki sauraren kowa Ina masa magana zai daina."

Tayi shuru cikin tunani kafin ta furta "Daman Rabi'u yace danka ne dole yaji maganarka."

Yace "Dalili kenan da in har ya gama nursery mamansa bata yi aure ba zan karbi dans kawai tunda daman an bar mata shi bisa yarjejeniyar zamu
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment