Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kayi Mani toh" nayafe maka. Yace yo tonidama laifin mezanyi maka don haka Allah yayafe mana bakidaya, baba Yace toh Ameen nagode.

Sannan kuma amatsayin ka namakocina Inason kazama shaida ni Abubakar nabawa *SEERAJO* gashi nan auren *SAJEEDATU* Kobay...Cikin masifa Alh Siddi yace toh" same don zaka bada auren yarka saina sani Ko-ko salon kace nai mata kaya dakiko?.. toh" karkaji dawai bazanyi ba kaji KO?..yarka kuma duk Wanda zakaba kaba ba'abunda yadameni ehe fuuu yasa Kai zaifita Da sauri baba yace toh" Alh Siddi nagode datasowa "asauka Lafiya Mtswwwww! yayi tareda banko kofa gafffff.

Shikam *SEERAJ* baki yasaki yana kallon baba aranshi kuwa fadi yake shin baba wani irin mutun ne haka,?.. wata iriyar *ZUCIYACE* Allah yai masa?.. itakam *SAJEEDAH* hawaye neke tamalala afuskarta, na bakin cikin "abunda Alh Siddi yakeyiwa BABASU kuma ba wannan bane nafarko dama yasaba,

akwai wani lokaci daya tabayi masa irin wannan cin mutunci zatayi magana, baban yace kul karta kuskura tasa baki idan manya suna magana aiba'irin tarbiyar dayayi mata kenan ba, shiyasa tundaga wannan lokacin KO "Alh Siddi yana fadawa baba maganganun nacin mutunci bata cewa komai saidai tayi kukata tashare hawaye.

Zumbur *SEERAJ* yamiki yazabi Alh Siddi Baba yarike hannun shi, da sauri juyowa yayi yakalli Baba yayinda baba yake girgiza mashi kai alamar a ah, domin yafahimci abunda yakeshiri zuwaya aikata, yace baba kabar ni naje Na fadawa mutumin nan koda kalma dayace, konaji sanyi a *ZUCIYATA kaji?..*

Baba yace "a ah *SEERAJO* idankayi haka "aibaka kyauta ba domin shindi babban ne agareka, Saboda haka kayi hakuri ka kyale "shi kasan mutane kowada irin halin shi, komawa yayi ya zauna tareda rintse idanun shi, wani irn bacin rai yakeji tareda jin tsanar Alh Siddi a *ZUCAYAR SHI.*

"Ahankali *SAJEEDAH* tamike tafita daga dakin tana share hawaye da hijab dinta, da Inna da Baba sukabi bayan tada kallon, "ahankali yabude idanu tareda zubasu inda *SAJEEDAH* take zaune saidai be gantaba, da sauri yace baba Ina *JEEDAH* yace tafita waje, zumbur yamike yabita. bin bayanshi baba yayi da kallon Murmushi yayi tareda rufe idanu yanaji ajikinsa KO" yanzu yabar duniya *SEERAJO* zaya kula mashi da *SAJEEDATU.*

Inna ce tace toh"shin BABAN Sajeedu kafasan cewa ciwo bamu tuwa bane KO?..Murmushi yayi yace nasani mana Saratu, tace toh" nifa bangane wannan maganganun daka keyi ba?.. gashi sai sawa kake ana kiran mutane harda, wannan mutumin da be dauki Dan Adam da DARAJA ba,
Don Allah nidai kabari tafadi ranta "abace Murmushi yayi tareda cewa toh" Saratu nabari.

tsaye yaganta bakin kofa idonta rufe cikin bacin rai yace shiyasa natsani wancan banzan mut.. dasauri tabude idanu tareda cewa "a ah *yah SEERAJ* karka zageshi Cikin mamaki yace saboda me?..tace Saboda shidin baban Besty nane, tsaki yayi mtswwwww! yace kar azageshi amma bakiga cin mutunci dayayiwa baba bane?..

tace "a ah ba baba yayiwaba kanshi yayiwa, Yace "eh haka ne toh" karbi hankacif share hawaye ki ni banasan gani kukan ki jinakeyi *ZUCIYATA* tana *ZAFI,* da sauri takarba tana cewa nabari *yah SEERAJ* yace yauwa *my JEEDAH* toh" muje can gurin mu zauna tace toh,akan wani dutse suka zauna, dai-dai lokacin dasuka hango Inna Da Sajeed sufito sun nufi can gurin fishiyar dasuke zama sun zauna, "ahankali ya kejan tada fira saidai kuma yafahimci kamar wani abu nadamunta.
"Ahankali Yace *my JEEDAH* meke damunki? ciki sanyi murya tace bakomai saidai idan natuna maganganun da baba yakeyi saina jin gabana yana faduwa kamar wani abu za'yafaru.

Jiyayi shima gaban shi yafadi amma saiya basar yace ba'abunda zaya faru kiyi Addu'a kinji?.. tace toh" can sai yakalli agogon hannun shi yaga 3:00PM yace *my JEEDAH* bari najena sallamo baba zanigida amma "anjima zandawo tace toh" sai kadawo.

yace ummh toh" mezan taho maki dashi?..Murmushi tayi tareda cewa bakomai yace' ah haba dai harda mutumin naki,?.." (yananufin fruits) dasauri tace lah *yah SEERAJ* kataho mun dashi tafadi tanarufe fuska tana dariya, shima dariyar yayi yana cewa "Oho da'ita wanna zata haba ko?..tacewa?.. yace *KUNYA* mana kuma nace duk abun daki keso ki tambaye ni kibar jin kunyata, saidai nasan bazaki barina tunda abun acikin *JININKI* yake KO?..Murmushi tayi shimayayi yayinda suka mike tare yanufi dakin da baba yake, itakuma tanufi gurinsu inna.

Dasauri naga *SEERAJ* yafito daga dakin dababa yake yanufi office din Dr Kamal,yana zaune yana rubu ce rubu ce sai jiyayi an banko kofa da karfi, *SEERAJ* yace pls Dr zoka duba mani baba nashiga inayimasa magana ga idanunshi bude "amma kuma be amsa maniba,

Dasauri Dr yabi shi suka je babana nan yadda *SEERAJ* yabar shi, dasauri yace kagani ko Dr pls duba shi, "Ok shine abunda Dr Yace tareda fara aikin shi, Ya taba hannun shi yai shuru can kuma saiyasa karfen nan akunnan shi tareda kaishi saitin da *ZUCIYAR* baban take bugawa yaya shuru can sai yadago yakalli *SEERAJ* cikin tashin hankali yace?.


? Kai๐Ÿ˜ณ _me Dr zayace_


Muje zuwa


A

๐Ÿ’˜Zuciyata ce๐Ÿ’˜


Tareda Alkalamin


โœ๐Ÿฝ


๐Ÿ’˜Lufhat ce๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜

๐Ÿ’˜ZUCIYATA CE๐Ÿ’˜

_Based on true life Story_
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜

(Labarin Sarkakkiyar Soyayya)

2โƒฃ9โƒฃ

WRITTEN BY

๐Ÿ’˜ยฉAMEENA UMAR FARUQ๐Ÿ’˜
OR
๐Ÿ’˜MEENAT๐Ÿ’˜


_*WANNAN page NAKUNE MASOYA ZUCIYATA CE INA SONKU INAYIDAKU FIYEDA YADDA KUKEYI DANI, INAJIN DADI YADDA KUKE NUNA KAUNARKU AKAN LITTAFIN NAN, ALLAH YABAR KAUNA, INAKIKE QUEEN ๐Ÿ‘ธ๐ŸปHAFSAT KAWALLIN SURBAJO INAYINKI ALLAH YABADA SA'AN KAMMALA LAIFIN ABBA NA NE AMEEN*._



________________________

*_ยฎPEN:WRITERS ASSOCIATION_*

*_PEN THE STRONGEST WEAPON_*
________________________

*_only the exquisite and Whizkid writers are opportune to be pen writers_*



โœ๐Ÿฝ



"Sai kuma yayi shuru tareda dukar da kai kasa da alama yana tunani girman abunda zaya fadama shine, da sauri *SEERAJ* yadan bugi kafadar shi tareda cewa what?.. Cikin sanyi murya yace am Sorry to say baba ya cika, Cikin matsananci tashin hankali *SEERAJ* yasa hannu shi duk biyu yachakumi kwala rigar Dr, yace me?..

No Dr baka duba shida kyau bane kallifa idanun shi bude kuma Murmushi mayakeyi, ganin tsantasar tashin hankali afuskar *SEERAJ* yasa Dr yace toh" bari nasake duba shi, yasake shi dasauri yace toh" duba shi, Dr kam yaduba baba ya kuma tabbatar yarasu "ahankali yadago yakalli *SEERAJ.*

Wanda shidinma kallon shi yake, saidai kallone me cike da tashin hankali da kuma tsoro, Cikin sanyi murya Dr yace' kayi hakuri Oga *SEERAJ* baba yarasu fa.

da sauri yace Dr wai meyasa kake tafadin baba yarasu?.. baba fa yanzun nan muka gama fira dashi Kai ma aikagani KO?.. yace "eh toh" yazakace yarasu?.. dasauri *SEERAJ* yace baba tareda rike hannun shi saikuma yaga hannun yatafi luuuuu yafadi,
jiyayi gabanshi yacigaba matsananci bugawa.

hannun shi yakai saitin hancin baba sai yaji baya numfashi, da sauri yakai kunnanshi dai-dai saitin da *ZUCIYAR* BABAN take bugawa saidai kuma beji komai ba don haka sai yadago da saurin ciki matsananci tashin hankali yatsurawa baba idanu yace Dr da gaske baba baya numfashi.

Kai yadaga masa alamar "eh sannan yace tabbas baba baya numfashi domin kuwa ya amsa kiran UBANGIJIMU, Ciki tashin hankalin *SEERAJ* yace ya SALAM! tareda rintse idanu wani irin ZAFI yaji acikin *ZUCIYAR* shi, irin ZAFIN nan da'akewa mutuwa tanadashi tabbas yau *SEERAJ* yaji wannan ZAFIN Wanda tunda yake bai tabajin shiba sai yau,

"Ahankali yabude idanu yayinda wasu hawaye masu ZAFI suka sauko akan kyakkyawar fuskarshi, data rikeda takoma jajir Saboda tsabar tashin hankali, hannu yasa yasafe fuskarta ba tareda cewa Dr Inason baba da dukkan *ZUCIYATA* amma meyasa yarasu,?..

yace saboda kwanan shi yakare sannan kuma Ubangijunmu yafika SONSHI, sabada hakane mayadauke kayansa, yanzu soyayyar data rage tsakanin ka dashi Addu'a.

kai *SEERAJ* yagirgiza tareda cewa haka ALLAH yajikan kababa, dai-dai lokacin dasukaji wani irin Kara ta bakin kofar dakin dasauri suka nufi waje,dai-dai lokacin da *SAJEEDAH* tazube kasa Sumammiya.

(ashe tun lokacin da *SEERAJ* yakira Dr suka biyosu yayinda *SAJEEDAH* ta tsaya bakin kofa, itakuma inna ta tsaya tagurin wundo, so duk "abunda yafaru akan kunnan su.)

Dasauri *SEERAJ* yakasar gurinta Cikin matsananci tashin hankali yadago ta tareda fadi "a ah *my JEEDAH* karkiyi Mani haka, girgiza tayake ya nakiran sunanta da'iya kaci karfinsa pls *my JEEDAH* wake up saidai KO" motsi batayi, hankalin shi yayi matukar tashi dai-dai lokacin da Inna ta'isa gurinsu tana sharan hawaye.

ganin *SAJEEDAH* kwance magashiya yasa tace shikenan itama ta mutu ko *SEERAJO?* dasauri yace "a ah inn bata mutu ba, yace Dr do something mana cikin tashin hankali Dr yace "OK daukota cak *SEERAJ* ya dauke ta tareda bin bayan Dr wani daki suka shiga akan gado ya kwantar da'ita yayida Dr yadukufa gani cewar numfashi ta yadawo saidai abun yaci tura, wani irin zufa Dr yashare natashin hankali yace "Oh go help me Cikin tsoro
*SEERAJ* yace Dr me?..yace nayi iya bakin kokari na amma abun yafikarfin tunanina.

Dasauri yace No Dr don Allah kayi wani abu itadin *ZUCIYATA CE* rasata yana nufin rasa rayuwata, dasauri Dr yafara danna kirjinta Wanda hakan yasa *SEERAJ* kaudakai gefe saboda wani abuda yadarsu *ZUCIYAR* shi,

tsawon lokaci Dr yanafama amma bata farfado ba, saidai kuma juyowan gada *SEERAJ* zayayi sai kawai yaga Dr yana kokarin hada bakin shi dana *SAJEEDAH*

wani mahaukaci tsawa *SEERAJ* yada kamashi wanda yasa shidago dakai dasauri ya kalle shi, yayinda shikuma ya watsa masa wani fitinan nan harara Cikin matsananci bacin rai yace?...



_*Nasan wannan din yayi kadan friend amma'aida babu garaba dadi, ko?.. inji malam ba haushe*._

~to'ammadai~

Muje zuwa

A

๐Ÿ’˜Zuciyata ce๐Ÿ’˜


Tareda Alkalamin

โœ๐Ÿฝ

๐Ÿ’˜Lufhat ce๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜

๐Ÿ’˜ZUCIYATA CE๐Ÿ’˜

_Based on true life Story_
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜

(Labarin Sarkakkiyar Soyayya)

3โƒฃ0โƒฃ

WRITTEN BY

๐Ÿ’˜ยฉAMEENA UMAR FARUQ๐Ÿ’˜
OR
๐Ÿ’˜MEENAT๐Ÿ’˜

________________________

*_ยฎPEN:WRITERS ASSOCIATION_*

*_PEN THE STRONGEST WEAPON_*
________________________

*_only the exquisite and Whizkid writers are opportune to be pen writers_*



โœ๐Ÿฝ


"Meye haka kake kokarin aikata wa?. Murmushi Dr yayi saka makon gani wani masifaffen kishi, akwayar idanun *SEERAJ.* yace Sorry Oga *SEERAJ* dama akwai wani taimakon dazan batane shiyasa,
Cikin matsananci mamaki yace taimako for how?.. Dr yace anakama hancin Mutum atoshe yanda iska bazaya shiga ba sai kuma aringa huramasa iskata bakinshi toh" in Allah yasa akadace sai yafarfado,
Cikin bacin rai yace toh" shine zaka hada bakin ka Dana matar dazan aura?..

_*A ah kai su Captain SEERAJ kishi yamotsa*_

Dr yace toh" kayi hakuri yisauri kayi mata da kanka Idan Allah yasa akai sa'a zata farfado yanzu, da sauri *SEERAJ* yaduka yayi kamar yadda Dr yace Cikin sa'a saigashi tafara tari, saida tadan tayi sosai sannan tabude idanu ahankali tafara tunani abunda kunnanta suka yajiyo mata, ciki matsananci firgici tareda bugawar *ZUCIYA* tamike zaune yayinda take baza idanu wanda kallo daya zakai mata kafahimci bata Cikin nutsuwar ta.

sai kuma tayi zumbur tamike tsaye saidai kuma wani irin jiri ne ya kwasheta ta tafi luuuuuu zata fadi, Cikin zafin nama *SEERAJ* yariketa tareda cewa pls *My JEEDAH* ki zauna kinji?..dasauri ta damke hannun shi wanda da'alama batasan tayi hakan ba, cikin matsananci tashin hankali tace *yah SEERAJ* da gaske ne abunda kunne na yaji?...

Kai yake girgiza mata Wanda ban gane nufin shiba "eh KO a ah, tace yauwa nasan ba gaskiya bane baba baza yatafi ya barmu ba KO?..wani irin Zafi yakeji acikin *ZUCIYAR* shi domin kwata kwata bayasan ganin bacin ranta, Cikin karfin hali yace Uhmm! kinga kizauna tukun na kinji?..tace a ah gurin baba zayi, yace "aiyanzu baba yana barci, tace toh" zanjirashi yatashi, dasauri tafara tafiya yayinda suka bibayanta shida Dr tana tafiya tana hada hanya domin jirin be sake taba.

Inna da Sajeed suna tsaye suna kuka basu kulada itaba itadin ma bata kulada suba,
Dakin da baba yake kawai tanufa koda tashiga har anrufeshi da sauri takarasa gurin shi, tana cewa Babana waya rufeka?.. barina bude ka kana barci neko?.. toh" Bari najiraka katashi zama tayi akujera tsura masa idanu. dai-dai lokacin su *SEERAJ* suka shiga shida Dr jiki bakwari, da sauri tace *yah SEERAJ* zomu zauna mujira baba yatashi kaji?..

Daga jin yadda take magana Kai kasan bata ciki hayyacin ta, "Ahankali yakarasa gurinta yatsuramata idanu wani irin SONTA keratsa *ZUCIYAR* shi tareda matsananci tausayin ta, tabbas sunyi rashari rashi me girma rashin da bazasu taba maida kamarshi ba, Cikin sanyi murya yace *my JEEDAH* baba bayanzu zaya tashi ba, dasauri tace *yah SEERAJ* toh" yaushe?.. cemata yayi kawai sai "anjima, tareda mikewa zaifita dasauri tace *yah SEERAJ* katafine bazakajira baba yatashiba?...yace ai zanjira shi inazuwa. yayi waje domin wani irin kuka ne yazo masa.

Dr ne yakarasa gurinta cikin sanyin murya yace' kiyi hakuri kisa cewa wannan barci da baba yakeyi bazaya taba tashiga sai DARUSSALAM, zumbur tamike tanayiwa Dr wani irin kallo dai-dai lokacin da su Inna suka shiga itada *SEERAJ,* dasauri takarasa gurin inna cikin matsananci tashin hankali tace,

Inna kinji Dr wai baba bazaya tashiba sai darussalam?.. cikin karfin hali Inna tace haka ne idanun ta zaro Cikin tsoro tace Inna MUTUWA kenan fa?... tace "eh *SAJEEDAH* babanku Allah yaimasa cikawa tafadi tana mesakin kuka, da sauri takarasa gurinshi tace wayyo baba meyasa zaka tafi kabarmu bakasan bamu da kowa ba, sai Allah saikai bakasan cewa Kaine bango majinginar mu ba?..

Sai girgirashi take tana fadin "a ah babana katashi don Allah kaji Babana?.. Saidai Ina baba kam yatafi wani irin kuka tasa ki mai ban tausayi, dasauri inna tazo tadaga ta, "aikam dasauri ta rungume Inna tana kuka yayinda jikinta sairawa yake, itama Inna kuka take haka shima Sajeed yazo ya rungume su hakan suka hadu saikuka sukeyi babu me bawani hakuri, yayinda Inna take fadin tabbas munyi rashi me girma bani da Uwa bani da Uba mijidana dogara dashi yaushima yatafi yabarni, ALLAH kazama gatana kadumeni nida marayun nan haka nantake tafaman fadi "abundai gwanin ban tausayi.

*SEERAJ* shima yana can gefe yana nashi kukan mecikeda tausayinsu dakuma tausayin kanshin, jiyake kamar yaje ya rungumesu ya lallashesu toh" saidai yasan bazaya iyayin hakan ba domin shima yana bukatar alallashe sa.

Dr ne yaketa lallai shin su" har sukayi shuru, saidai *SAJEEDAH* kam hawaye yaki tsayawa afuskarta, Cikin lokaci kankani suka dauki gawar Baba suka tafi gida don a shirya shi zuwa gidan sana gaskiya.

Duk wani masoyin baba saida mutuwar shita taba mashi *ZUCIYA* musamman mlm barau kuka yake wiwi domin yayi rashin makoci na kwarai, su shikam dai Alh Siddi bamusan inda yadosaba yaji mutuwar makocin nasa ko?.. beji ba "Oho saidai wani daga kai yakeyi,

_*Nikam nace "a aha Alh Siddi indai mutu wace tasan dakinkowa*._

duk abunda "akeyiwa mamaci anyi wa baba shiryashi tsaf cikin likafani yayinda *SAJEEDAH* da *SEERAJ* suketayi masa karatun Qur'an maigirma, sunayi suna kuka saida akai sallar la'asar sanna akakai baba gidan sa na gaskiya.

_*Allah sarki baba mutumin kirki Allah yajikanka da Rahama halin kana Alkhairi yabi ka ameen*_

Hakanan dai akakai Baba gidan sa nagaskiya akadawo aka cigaba da karban gaisuwa,sai bayan sallah isha'i sannan yai shirin tafiya gida Cikin gida yashiga don ya sallamo Inna,
yana tsugunne gaban inna yana sallamar ta amma kuma idanunshi yana kan *SAJEEDAH* datake kwance kan kafar inna hannun ta rikeda chasbi ta naja, saidai kuma tanayin kuka kadan kadan domin haryanzu hawaye yaki tsayawa,

Inna tace toh" *SEERAJO* saida safe mungode kwarai da dawainiya ALLAH yayi maka Albarka, yasaka maka da Alkhairi ka gaida mutanan gida yace toh" ahankali ta tashi daga kwancen datake cikin sheshshekar kuka tace *yah SEERAJ* saida safe yamike tareda cewa zomana *JEEDAH* tace tace toh" saidai kuma bata tashi ba, Inna tace bayace kije ba?.. kai tadaga alamar "eh tace toh tashi kije mana,tace toh"tareda tashi tabin bayan shi, tsaye ta iskeshi jikin motar shi yajingina cikin muryar kuka tace *yah SEERAJ* gani.

idanu ya tsuramata wani irin matsanancin SONTA yakeji acikin *ZUCIYAR* shi ga tausayinta dayake ratsa ilahirin jikinsa jiyake kamar ya rungume ta "akirjinshi ya lallasheta, Cikin sanyi murya yace' *my JEEDAH* kiyi shuru kibar kukan hakanan kinji kinga "ance babu kyau anayi mamaci kuka haka neko?.. tace "eh yace toh" ki daina muyi tayiwa baba Addu'a Allah yakai rahama agareshi kinji?.. tace toh" yace toh"kishiga gida ki kwanta saida safe kinji? tace toh" tareda wucewa yana tsaye yana kallonta har tashige gida sannan yaja jiki yatafi.

"Aban garen Ammi kuwa hankalin ta yatashi tunda 12 :00pm da *SEERAJ* yafita bai dawoba, kasan cewar baitabayin hakaba gashi takira wayar bai dauka ba daga baya ma data kira sai akace akashe take,shiyasa hankali ta yatashi musamman data tuna cewar *SAGEER* yazo nema shi sannan yace shima yakirashi awaya besa meshiba.

Sai faman safa damarwa takeyi a tsakiyar falo, Cikin sanyin jiki yashiga falon bakinsa dauke da Sallama,dasauri tajuyo takalleshi gabanta ne yafadi saka makon ganinshi datayi wujigawujiga, gashi duk yafada idanun shi duk sunzurma fuskarshi tayi fayau sai dogo hanci kawai kake gani, cikin tashin hankali takarasa gurin tareda rikeshi cikin matsananci tsoro tace?...

Muje zuwa

A

๐Ÿ’˜Zuciyata ce๐Ÿ’˜

Tareda Alkalamin

โœ๐Ÿฝ

๐Ÿ’˜Lufhat ce๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜

๐Ÿ’˜ZUCIYATA CE๐Ÿ’˜

_Based on true life Story_
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜

(Labarin Sarkakkiyar Soyayya)

3โƒฃ1โƒฃ

WRITTEN BY

๐Ÿ’˜ยฉAMEENA UMAR FARUQ๐Ÿ’˜
OR
๐Ÿ’˜MEENAT๐Ÿ’˜


_*WANNAN page NAKUNE MASOYA ZUCIYATA CE NA (BAYAN WUYA FANS) INA SONKU INAYIDAKU FIYEDA YADDA KUKEYI DANI, INAJIN DADI YADDA KUKE NUNA KAUNARKU AKAN LITTAFIN NAN, ALLAH YABAR KAUNA AMEEN NAGODE SOSAI,*._



________________________

*_ยฎPEN:WRITERS ASSOCIATION_*

*_PEN THE STRONGEST WEAPON_*
________________________

*_only the exquisite and Whizkid writers are opportune to be pen writers_*



โœ๐Ÿฝ



"Subhanallahi lafiya meyasa meka daga ina kake haka?.. sai tambayar shi take tareda tattaba jikinshi,ahankali yadago kai yazuba mata lumsassun idanun shi ba tareda yace komai ba,
cikin tashin hankali tace nace meyasa meka daga inaka ke kayi shuru?..

A *ZUCIYAR* shi yace my Ammi daga gidan su *my JEEDAH* nake Babanta yarasu Baba mutumin Kirki inason mutumin nan bantaba ganin me halin kwarai irin shiba, saidai bansan taya zanfada miki cewa daga gidan su *my JEEDAH* nafito ba tunda kince KO" sunanta kar nasake kira, my Ammi Ina SON *JEEDAH* ke kuma kince kar nasake kiran sunan ta shin my Ammi yazanyida zallar *KAUNARTA A ZUCIYATA* yazanyi! yazanyi!! yazanyi my Amm?..

wani irin tausayin kanshi ne yarufe shi kawai sai yafashe dakuka tareda fadawa jikinta,dasauri ta rungume shi tareda cewa subhanallahi wai yau meya faru dakaine haka? dakyar ta iya kamashi suka zauna sai kuka yakeyi, mekunshe da Abu biyu nafarko dai kukan rashin baba Na biyu kuma besan yazaiyi Ammi ta amince da maganar *JEEDAH* ba, sai lallashin shi takeyi tareda yafamasa Kai saida yayi kuka sosai sannan yayi shuru.

tace ya'isa haka fada mani meyasa meka sannan inakaje tunda dazu kasan yadda hankalina yatashi narashin sanin halin daka keciki kuwa?..tunda nakira wayarka baka daukaba, daga bayama danakira sai ace akashe har zamkira *SAGEER* tambaye shi don ina tunani kotare kuke da saigashi yazo nemanka, tsoro yakamani sosai da yace yakiraka liyinka besameka ba kuma yace shi besan inda kajeba, shin daga Ina kake haka gashi saifaman kuka kakeyi duk kadaga mani hankali gashi duk kayi wani zuru-zuru gajikinka ma dazafi "alamar zazzabi yana damunka KO?..

Cikin sayin murya yace' daga gidansu abokina nake (yadai fadi haka ne kawai) BABASU yarasu kuma mutumin yanada kirki,bakiga yadda suke kuka ba duk saisuka bani tausayi har Ina tunani idan narasaku keda abba yazanyi?.. pls my Ammi kar kutafi kumarni yakara shi fadi kamar za yasaki wani kukan.

Jitayi jikinta yayi sanyi har taji hankalin ta yatashi saidai kuma tadanne "abunda taji gudun karta sake tayar masa da hankali, Murmushi tayi tace baban Jordan kenan dadina dakai wani lokacin wauta kamar first born sheshi tafadi tana dan' dungure masa kai cikin wasa,

"Ai hanyar kenan guda Wanda dukkan mairai sai yadandani DACINTA kuma dazaran kwanan mutun yakare tofa sai yatafi, wanda ba'abunda yake bukata ga abunda yabari tareda al'ummar annabi bayaga Addu'a,

Don haka koyanzu kaga mun mutu kwanan mune yakare kuma babu wani abunda zakayi bayan HAKURI, saikuma kabimu da Addu'a domin kuwa itakadai ce Soyayyar dazaka nuna mana, Saboda haka yanzu abunda zakaringa yiwa baban abokinka kenan Addu'a domin naga mutuwarshi yatabaka sosai, sannan shima abokin naka kafada masa yarigayi baban sa Addu'a sosai kajiko?..cikin sanyi murya yace' toh" my Ammi, tace yauwa toh" yanzu kaci abinci?..

Tab aran shi harya manta abunda ake kira abinci, yace a ah banci ba tace tace toh" kajiko kanata faman zama dayinwa ga zazzabi yanzu katashi kaje kai wanka, barinaje nahado maka Coffee kasha sannan kaci abinci kasha magani kajiki?..yace toh"tareda tashi yanufi part dinshi ita kuma tanufi kicin tana kiran kulu, me aiki kasan cewar *ZUBEE* batanan tajegidansu can zatayi week shi kuma Abba yayi tafiya don haka gidan daga ita saimasu aiki.

Bayan yayi wanka saiyasha coffee tareda Dan tsakuran abinci kadan Saboda bayajin dadi bakinshi, zaya sha magani kema saiyaji wayar sata nakara koda yaduba saiyaga S A Nasko, haka nan yaji yanasan daga wayar don rabonda su hadu atun rananda 'aka kwantar dababa asibiti, daga can *SAGEER* yace kana Ina?.. Cikin sanyi murya *SEERAJ* yace' Ina gida yace OK gani nan zuwa yace ok sai kazoya kashe wayar tareda watsa magani abaki yakora da ruwa sannan yakoma yazauna jiran *SAGEER.*

Kafayi wuyar gani abokina toh" Ya'akai ne?.. inji cewar *SAGEER,* yayinda *SEERAJ* yace dan dai-dai yace meya faru?..cikin tausayi yace BABAN *JEEDAH* ne yarasu, yace ayya Allah yaji kanshi amma mutuwar nashi neyasa duk kafada haka?..yace hmm bakasan kowaye baba bashiyasa, baki ya tabe tareda cewa toh" kowaye aibaikai Abba ba dazaka wani tada hankalinka abanza,

cikin bacin rai yature' shi da hannun kasan cewa yana kusada shi zaune yace BABAN ne banza?.. "eh lallai balaifin kabane laufinane dana kiraka, So tashi katafi nagode atunanina zaka tayani bakinci abunda yasameni ashe bansaniba wani bakin cikin zakake kunsamani, tashi katafi yafadi da karfi! yace au korata kakeyi?.. yace nakoreka domin baba wani bangare ne narayuwata wandanayi rashinsa barina fadamaka,

baba mutun neda abun duniya beda meshiba mutun ne da idanka batamasa shi kokarin yake yafaranta maka, baba yasani hanyata kwarai zamana dashi nakaruda abubuwa masuyawa kuma masu amfani arayuwa, shine har kake tunani bazan iyashiga wannan haliba harsai idan Abbana ne yarasu?.. sai yafashe dakuka Wanda yasa jikin *SAGEER* yai sanyi.

Yace toh kayi hakuri ba kuka zakayi masaba Addu'a zakayi masa nandai ya lallasheshi, San yake dan jan shida fira wanda rabi firar *SAGEER* yakeyinta,daga ba yadai yaimasa sallama yatafi.

๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
Yau Addu'ar bakwai kuma saiyaune iyalan gidan Alh Siddi suka shiga gidansu *SAJEEDAH* dinsu yi masu gaisuwa, koshi masaida Haj Mama tamasa sannan yabar su suka shiga dukkan suharda yaransu, *SAJEEDAH* ce tace Sadiya su "besty na basuyi Hutu bane?..bakita tabe(kasan cewar itadin ba baya bace gurin rashin kunya) tace anyimusu ammata tafibididi,idanu *SAJEEDAH* tazaro tareda cewa bididi kuma Sadiya?..tace "eh tana can tabi wata "kawarta bauchi wai a can zatayi Hutu, Murmushi tayi tace ayya dayake hutunma bayawa sati uku ne kawai, kwanan nan zakiga ankoma school din tace "Oho itadai ta sani da shegen yawo, Murmushi kawai *SAJEEDAH* daganan sukai musu sallama.

๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜***๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
Akwana atashi bawuya agurin Allah yaugashi satin baba uku darasuwa, wanda yayi dai-daida kwanan *SEERAJ* talatin da uku da dawowa Wanda kuma haryanzu besa ranan komawa Jordan ba, duk da kiran shida sukeyi awaya. a wannan lokacin kuma babu abunda be wa data su *SAJEEDAH* dashiba,

daga fannin abinci harfannin sutura basuda matsalar komai saita rashin baba kuma kullun *SEERAJ,* agidan yake wuyi yana debemusu kewar rashin baba, saidai kuma rashin zamansa agida yafara damun Ammi kasan cewar yanzuko abincin gidan ba yaci sosai.

"A tunanin ta gidansu abokin mashi yake zuwa sai daga baya tafahimci

Please Login or Register in order to submit comment