Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

toh tareda kamata sukafita yan'uwanta dalibai sunayi mata SANNU.

dakyar dai *SEERAJ* ya'isa gida yana shiga falo yazube kasa, dai-dai lokacin da, Ammi tafito daga kicin saikawai ganin Mutum tayi kwance kasa, saifaman juyi yake hannu shi "akan kirjinsa idanun sa rufe, sai surutai yake yanafidin "Ina SONKI *JEEDAH,*

wlh kedin *ZUCIYATA CE* bazan jure rashin kiba, Cikin tashin hankali takarasa gurishi tareda dago kanshi tadora akan cinyar ta dai-dai lokacin da yatafi luuuuu yafado daga jikinta Cikin tsoro tace?...

Aha

_*wayyo Soyayya zata kai yan MAZA*_

Muje zuwa

A
๐Ÿ’˜Zuciyata ce๐Ÿ’˜

Tareda Alkalamin

โœ๐Ÿฝ

๐Ÿ’˜Lufhat ce๐Ÿ’˜
[6:07PM, 3/8/2018] โ€ช+234 902 288 0912โ€ฌ: ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜

๐Ÿ’˜ZUCIYATA CE๐Ÿ’˜

_Based on true life Story_
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜

(Labarin Sarkakkiyar Soyayya)

1โƒฃ6โƒฃ

WRITTEN BY

๐Ÿ’˜ยฉAMEENA UMAR FARUQ๐Ÿ’˜
OR
๐Ÿ’˜MEENAT๐Ÿ’˜

________________________

*_ยฎPEN:WRITERS ASSOCIATION_*

*_PEN THE STRONGEST WEAPON_*
________________________

*_only the exquisite and Whizkid writers are opportune to be pen writers_*



โœ๐Ÿฝ


"Innalillahiwa'ina'ilaihirraji'un! mezan gani yau ni Raihana?.. dai-dai lokacin da sake jawoshi kan cinyarta Cikin tashin hankali take girgiza shin tareda kiran young pilot "amma Ina KO dan yatsanshi bai motsaba balle tasan ran numfashin sa zayadawo.

Cikin tsoro tasaki wani matsananci kuka tareda kururuwan "akawo mata "agaji, *ZUBEE* ce tafito da sauri saka makon jin kukan Ammi, ganin *SEERAJ* tayi kwance sharban "akasa kamar matattace,

Cikin tsoro tace wayyo Ammi meyasa meshi?...Cikin kuka Ammi tace' ban saniba, saidai Ina kyautata zaton gamo yayida mutanan boye domin naji yana kiran wani suna wai *JEEDAH*,

Jekira Malam Adamu "aikashi asibiti da sauri tace toh" zata fita kenan saigasu zasu shiga falon sunkai sukusan biyar, daya gacikin su yace' Lafiya munji kamar kukan Hajiya?

Da sauri tace "eh "yah S p ne bashida lafiya sukace subhanallahi meyasa meshi?..,dai- dai lokacin da suka karasa shiga ciki falon da sauri Ammi tace' don ALLAH Ku dauke shi muje asibiti, sukace toh tareda kinkimarsa suka nufi waje yayinda *ZUBEE* taje tadauko hijab din Ammi danata suka bi bayan su.

*SAJEEDAH* kam da taimakon Allah dana yarinyar data rakota suka isa gida da kyar, Saboda wani irin zazzafan zazzabi ne yakamata, Inna tana ganinsu" taji gabanta yafadi da sauri tace' lafiya meya faru?.. Mariya tace" wlh batada Lafiya ne shine "ya Sayyadi yace' narakota gida.

Inna tace assha dai-dai lokacin da take shinfida tabarma Mariya, ta taimaka ma *SAJEEDAH* ta zauna tanayi mata sannu, sai tace sai anjima *SAJEEDAH* Allah yakara sauki Inna tace Ameen mun gode kinji?..

Bayan Mariya ta tafisai Inna ta kalli *SAJEEDAH* daketa rawar sanyi, tace" meke damunki? Cikin rawar murya tareda sakin hawaye tace' Inna kaina ke ciwo,

Inna assha toh"sannu bari Baban Ku yashigo sai kuje kyamis tace toh" sukayi shuru na Dan wani lokaci, caidai sai *SAJEEDAH* takatse shuru Cikin shasshekar kuka tace' Inna kingani ko" fushinki ne yatabani don kiyi hakuri kiyafe mun wlh bazan karaba kinji Inna?.. takarashe da kuka.

Inna ta kalli yartata cike da tausayin tace nayafe maki, saidai kisani karya dabi'ace Mara kyau bansan ki dai taba Saboda haka karkiyi kokarin dauka kidorawa kanki,

Sannan kisani mutunciki shine DARAJARKI, dazaran kinzubar da mutuncinki toh" shikenan bakida sauran wata DARAJA ga idanun kowani namiji Saboda haka saiki kula.

Cikin shshhekar kuka tace toh" Inna, Inna tace
kiyi shuru kidaina kukan haka kar kamu kanaki yakara yin ciwon, tace toh tareda share hawaye.

๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜

Koda suka isa asibiti emergency room aka nufada "shi da, taimakon ALLAH dana likitoci yafarfadon, saidai sunyi masa" alluran bacci don sunga yana bukatar hotu.

Likita ne yakewa Ammi Karin bayani "akan abunda kedamun *"SEERAJ*, tace hmmm Likita nafada maka gamo yayi, murmushi yayi yace nace maki baiyi" gamo ba, kamar yadda nafada maki kawai akwai "abunda yatayar masa da ahankali so, shine yahaifar masada ciwon Kai tareda zazzabi mai zafi kuma harda rashin bacci da,

So kinga KO rashin bacci ma babban matsala ne, amma yanzu insha'Allahu bawata matsala mun bashi taimakon daya kamata, so karkida mu zaya farfado normal, Ammi tace' Likita mun gode sannan tamike tanufi dakin da *SEERAJ* din yake.


Sannu *SAJEEDATU* ga magani tashi kisha tunda kedin basan allura kikeyi ba, "amman kamata yayi "aimaki allura tunda tafi sauri saukar da zazzabi, amma dai yanzu Fara shan wannan magani tukun mugani, inji cewar Baba kenan.

tace toh" tareda tashi ta zauna Sajeed ne yaje da sauri yadebo mata ruwa, yace sannu Aunty *JEEDAH* ga ruwan ta karba dai-dai lokacin da Inna taballo mata maganin, takarba tasha suna tayi mata sannu bayan tasha ne saita sake kwantawa.


"A hankali yabude idanu tareda tashi zaune mamaki ne Yakama shi ganin shi agadon asibiti, ahankali yafara tunani idanu yarinte tareda tura hannu shi saitin kirjinsa, Cikin sanyi murya yace *JEEDAH*.
Inason ki,

dai-dai lokacin da Ammi tadago dakai kasan cewar tana gurin zaune, tace' sannu yaji kin?.. Cikin sanyi murya yace' da sauki my Ammi saidai kaina yana ciwo kuma kirjina yana ZAFI, Cikin tausayin sa tace Sannu ailikita yace zakasamu sauki insha'Allahu ga magungunan "ansawa yace toh".

tace ummh amma wacece *JEEDAH*
Idanu ya tsurama Ammi batareda yace komai ba, tace nace wacece *JEEDAH?..* " idanu yarufe ahankali yace *ZUCIYATA CE,* Cikin tsoro tace subhanallahi nace yaron nan yayi gamo bakace a ah.

Dai-dai lokacin da *ZUBEE* tashi Hannun ta rikeda kayan abinci Cikin Wani Dan kwando, ta'ajiye agaban Ammi tareda cewa ya mejikin?.. tace' dasaukin saidai kam yaron nan yayi gamo, *ZUBEE* tace gamo fa?... tace "eh yanzu yasake fadin wannan sunan daban tabajiba wai *JEEDAH*.

*ZUBEE* tace caf nima haka kilan aljanace' "ahankali yabude idanu tareda watsa ma, *ZUBEE* lafiyayyan hararan tareda Jan tsaki mtsww "aikam da sauri tashiga taitayinta, Ammi tace' kin gani KO"?.. *ZUBEE* dai batace komai ba domin Anyi mata allurar tanutuda idanu.

tace bari Likita yazo ya rubuta mana Sallama muje gida Ai magani aljanu domin dai kam tabbas gamo yayi, "ahankali yace my Ammi nifa banyi gamo Da komai ba,

tace' toh" idan ba gamo kayi ba, wacece *JEEDAH?..* yace *ZUCIYATA CE*
tace oh ni Raihana sannu kaji?.. *ZUBEE* hada masa shayi yasha, Da sauri yace a ah bansha yanzu sai anjima tace toh" kwanta kahuta,
(itakam Ammi taduka da gaske gamoyayi)


๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
"Aha kadai masoyan sukaita jinya har sukaji sauki saida kowane *ZUCIYAR SA* Na nan mane Da *SON* dan'uwansa,

********
Yauwa alhamin yayi dai-dai da sauran kwana biyu *SEERAJ* yakoma gurin aiki wato Jordan, kuma yau kwanan *SEERAJ* biyar rabonda yaga *SAJEEDAH* jiyake kamar ya shekara biyarne baigan taba,

Don haka ne yau yakudurta aranshi zayaje yaganta KO" yasamu sassauci a *ZUCIYAR* shi, gakewar Baba data Sajeed data dame shi don haka ne ya shirya yanufi gidansu".

Baba yace' a ah mlm *SEERAJO* sannu dazuwa yaushe kadawo?.. yace baba "aibanje ko'ina ba saboda banida lafiya, yace assha "ai naga kara toh"yaji kin?. yace da sauki dama nazo nafada maka ne, jibi zan koma gurin ai kin kuma zan kwana biyu ban zoba.

Baba yace Allah sarki toh" Allah ya taimaka yace Ameen, Baba yace yau kam ka shiga kugaisada Inna taku, yace toh" tareda mikewa yanufi Ciki gidan, kuma wannan ne Karina farko dazaya shiga gidan.

Da Sallama yashiga inna tana zaune bakin murhu, *SAJEEDAH* tana wanke-wanke da sauri tadago kai saka makon jin murya Wanda *ZUCIYARTA* take muradin San gani,

karaf suka hada idanun "aikam yasa kar mata lallausan murmushi yayida yaji wani irin sanyi yaziyarci *ZUCIYAR* shi da sauri tadukarda kai, Inna ce ta amsa yayinda Sajeed yajeda gudu ya rungume shi,

tabarma ta shimfida masa tareda yi masa sannu dazuwa, Bayan yazauna sanna suka gaisa yayinda idanun shi suna "akan *SAJEEDAH*, yayinda Sajeed keyi masa firan Aunty *JEEDAH* tayi rashin lafiya, batareda ta kalleshi ba tace' inayin?..dasauri ya'amsa da tafiya lau yajiki?. tace Alhamdullah yace' Allah yakara sauki ameen tace.

Sunyi firakadan Da inna sannan yayi mata Sallama yafita,yafita kenan sai baba yakwalawa *SAJEEDAH* Kira ta amsa tareda saka hijab tanufi waje.

tace Baba gani, yace dama nace kizo Kuraka yayan ku zaya tafi, Cikin sanyi murya tace toh'Sajeed yace baba nima nadauko takalmin narakashi?.yace "eh.

"Ahankali sukafara tafiya kafin Sajeed yaiskosu', yayinda *ZUCIYOYIN SU* keta bugawa, sunshiga lungun kenan, saitaja ta tsaya tareda kallon shi, tabbas tajidadi ganisa har cikin *ZUCIYAR* ta amma Sai kuma tadaure fuska tareda kaudakai gefe sannan tace?...

Aha

Muje zuwa

A

๐Ÿ’˜Zuciyata ce๐Ÿ’˜

Tareda Alkalamin
โœ๐Ÿฝ

๐Ÿ’˜Lufhta ce๐Ÿ’˜
[6:07PM, 3/8/2018] โ€ช+234 902 288 0912โ€ฌ: Y ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜

๐Ÿ’˜ZUCIYATA CE๐Ÿ’˜

_Based on true life Story_
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜

(Labarin Sarkakkiyar Soyayya)

1โƒฃ7โƒฃ

WRITTEN BY

๐Ÿ’˜ยฉAMEENA UMAR FARUQ๐Ÿ’˜
OR
๐Ÿ’˜MEENAT๐Ÿ’˜

________________________

*_ยฎPEN:WRITERS ASSOCIATION_*

*_PEN THE STRONGEST WEAPON_*
________________________

*_only the exquisite and Whizkid writers are opportune to be pen writers_*



โœ๐Ÿฝ


"Bakace' "indai rashin zuwanka gidan mu shine farin Ciki na toh" bazaka zoba,"amma kuma sai gashi kazo, wato hakan yana nufin bakasan farin ciki na kenan ko?..toh" yanzu kuma meya kawoka?..

Cikin sanyi murya yace' tabbas din mesan farin Cikin kine fiyi da tunani ki, saidai kiyi hakuri nakasa cika maki "alkawarin Dana daukar maki, kwana biyar din danayi bangan kiba, jinayi kamar nashe Kara biyar ne bangan kiba, *ZUCIYATA* sam takasa jure rashin ki.

Jikinta yai sanyi dajin abunda yafada ita kanta ba karamin jigata tayi narashin Saba, hartana fadi "aranta nima *ZUCIYATA* takasa juriyar rashin ka, sai koyamata nake tajure tajure amma takasa, yazanyi?..

yah *SEERAJ* yazanyi datarin SONKA "a *ZUCIYATA?..* jitayi wata *ZUCIYAR* tace' hakuri zakiyi, tunda shidin yabullo dawata manufa "acikin lamarin naku, Wanda idan bakiyi hankali ba za'iya kaiki ga'aikata babban kuskue nan gaba.

"Ahankali tadago Kai takalleshi cikin sa'a shima ita yake kallo "aikam suka hada idanu sukai wa juna kuri, suna kallon cikin kwayar idanun juna yayinda kowa yake hango son dan'uwansa "aciki *SAJEEDAH* ce tafara kauda Kai.

Cikin sanyi murya yace' dama kuma nazone nafadawa "Baba zan koma gurin aiki, kuma Zan dan'dade ban dawo ba shine nazo na sallame Ku", jitayi gabanta yafadi saidai bata bari yagane hakan ba.

Cikin sanyi murya yace' don haka *JEEDAH* kiyi hakuri kiyafe mani kinji?...Cikin sanyi murya tace' yah *SEERAJ* aitun ranan tace nayafe maka, wani irin sanyi yaji yaratsa *ZUCIYAR* shi har yasaki lallausan Murmushi.

Yace yauwa my *JEEDAH* nagode sosai toh" Soyayya tafa?.. "aranta tace yana Cikin *ZUCIYATA* "afili kuma sai tace' babu ita, idanu yazo tareda cewa haba my *JEEDAH* karkice" haka don ALLAH, dai-dai lokacin da Sajeed yakaraso gurin su".

Sajeed yace Aunty *JEEDAH* nadauko tace toh" muje "A hankali suke tafiya, batareda kowa yace komai ba saidai sunayi suna San kallon juna, sunyi tafiya sosai sannan ta tsaya Cikin sanyi murya tace Allah yakiyaye hanya Jeed mu koma gida.

Da sauri yace pls *JEEDAH* kiyi hakuri, batace komai ba tajuya ta tafi, yayinda yabi bayanta da kallo *ZUCIYAR* shi cikeda dembin SONTA, Sajeed ne daya tsaya ya kalle shi tareda cewa yah *SEERAJ* my friend kayiwa Aunty *"JEEDAH* laifine?.. Kai yadaga masa alamar "eh.

Fuska Sajeed yadan bata tareda tabe baki yace nima idan nayi mata laifi, wata Rana harsai nayi kuka Sannan takeyin hakuri, amma idan kayita bata hakuri zata hakura shikam *SEERAJ* "aranshi fadi yake aini dama idan nayi mata kukan, zata yarda muci gaba da Soyayyar mu tabbas danayi don batasan yadda nakejin tabane a *ZUCIYATA* shiyasa,

_*Nikam nace kut melesi harda su kuka tab lallai Soyayya me karya lagon yan MAZA lol*_

Nan dai suka rabuda Sajeed yana yimasa Bye-bye shima tanayi masa, hakanan ya isa gida jikiba kwari koda yashiga afalon bakowa don haka "anan ya yada zango, tareda kwanciya akan lallausan kushin din idanu yarufe, yayinda yakejin SON *SAJEEDAH* yana bin jinin jikin shi.

Ammi ce' tafito daga shashinsa tashiga bata Ganshi ba tafito kenan sai taganshi kwance, "ahankali takarasa kusada shin tadan jima tana kallon shi Cikin jimamen halinda yake ciki, Sannan tasa hannu tadan bubbugi kafadar shi.

"Ahankali yabude lallausan idanun Sa masu cikeda shaukin Soyayyar *SAJEEDAH*, tashi yayi tareda cewa Sannun my Ammi, tace' hmmm Kaine da Sannun, ya'akai naga bakasha maganin ka ba kosau daya?...Cikin sanyi murya yace' my Ammi nifa banida wasu aljanu danayi gamo dasu don hakane maban shaba.

tace au kana nufin ita *"JEEDAH* din dakake kira "ashe Mutum ce ba 'aljana ba?... da sauri yace "eh my Ammi Mutum ce ita kamar kowa, tace' toh" meye hadinka da'ita?... "aikam da sauri yafar zuba mata bayani wanda "inagani baimasan yanayiba, domin gabadaya idanun shi sunrufe da *KAUNAR SAJEEDAH*,

fadi yake' budurwa tace "Ina SONTA" da dukka *ZUCIYATA* itama tana SONA Sosai, har munyi "alkawarin aure da'ita mundan samu sabani ne "atsakanin mu, kuma nine naimata laifin shine take fushi dani don my Ammi mujekib...

tsawar Da Ammi tadaka masa ne yasashi yinshuru da sauri yadago kai ya kalleta, kasan cewa magana kawai yakeyi batareda yana kallon taba, "aikam gaban shine yafadi sakamakon ganin wani irin matsananci baci rai "afuskarta,
Wanda tunda yake da'ita bai taba ganin shiba.

jiyayi gaban shi yaci gabada matsananci faduwa wani irin miyau yahadiye jikake Kut, cikin bacin rai tace' nikake fadawa cewa kayiwa wata "alkawarin aure toh" shi kuma Alkhairi da kayi Mani na auren *ZUBEE* Ina yake?..

Da sauri yace' yana nan my Ammi "aidukkan suzan aure su, harara Ammi ta watsa masa tareda cewa kana nufin dukkan su" zaka aure a lokaci guda?..

Da sauri yace "eh my Ammi Zan iya, tace' Hmmm yaro man maza aiba wai nace baza ka'iyaba, tabbas zaka iya Sosai kodan dan yadda "a kace namiji mijin mace hudu ne, toh" saida bada ni za'a wannan shashancin ba taya za'ace kamar kana karamin yaro dakai kace'zaka auri mata biyu alokaci guda?..

toh" Bari nafada maka kada ka kuskuren na sake jin wannan magana tafito daga bakin ka, Sannan kasani baka dawa data mata data wuce *"ZUBEE* domin ita nasani bansan wata *"JEEDAH* ba Saboda haka kar nasake jinka kira wannan sunan,

Idan kuma harka nasan ganin bacin rai na toh" sai ka cigaba da kiran wannan *JEEDAH* KO *JEERA* Oho maka Kai kasani.

Jiyayi wani irin zufa ya karyo masa gawa ni ZAFI dayaji kirjinsa yanayi saka makon gani bacin rai Ammi, shikam *SEERAJ* idan "akwai Abunda yatsana "arayuwar shi toh baiwuce bacin rai Ammi shiba.

Hankali shi ne yai mumunan tashi najin abunda Ammi tace' ga *SAJEEDAN* shi Cikin tsoro yace?...


_*dafatan Anyi jumma'a Lafiya.*_


Muje zuwa


A

๐Ÿ’˜Zuciyata ce๐Ÿ’˜

Tareda Alkalamin

โœ๐Ÿฝ

๐Ÿ’˜Lufhat ce๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜

๐Ÿ’˜ZUCIYATA CE๐Ÿ’˜

_Based on true life Story_
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜

(Labarin Sarkakkiyar Soyayya)

1โƒฃ8โƒฃ

WRITTEN BY

๐Ÿ’˜ยฉAMEENA UMAR FARUQ๐Ÿ’˜
OR
๐Ÿ’˜MEENAT๐Ÿ’˜


_*Slm wannan page din nakuna ZUCIYATA CE friends kuyi yadda kukeso dashi, nasan kunayi dani shiyasa nima Wlh inayin Ku irin Sosai din'na Allah yabar ZUMINCI DA kauna*๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜._

________________________

*_ยฎPEN:WRITERS ASSOCIATION_*

*_PEN THE STRONGEST WEAPON_*
________________________

*_only the exquisite and Whizkid writers are opportune to be pen writers_*



โœ๐Ÿฝ


"My Ammi kikace' Karna sake kiran sunan *"JEEDAH*?.. Cikin bacin rai tace' "eh haka nace' idan kuma kanasan ganin bacin raina toh", saikaci gaba Da kiran wannan sunan.

tashin hankalin shi yakaru don hakan ne yasa zufa natake to masa tako'ina, "ahankali yadago Kai ya kalleta "aikam yaga bacin rai karara afuskarta Wanda yakeda tabbaci shine silar bacin ran'nata, jiyayi kirjinsa yasake bugawa Cikin sanyi murya yace' kiyi hakuri my Ammi,

"Inadai fadin sunan *"JEEDAH* shike saki bacin ranki toh" bazan sake fadin shiba, Cikin bacin rai tace' yauwa ai hakan yafi, Sannan tawuce, bin bayan tayayi da kallo harta shige daki.

"Sannan ya rintse idanu "ahankali yafurta kiyi hakuri my Ammi bakina ne kawai zaya daina fadin *"JEEDAH,* koshi don gudun bacin ranki ne, "amma *ZUCIYATA* kam bazata iya daina fadin taba domin ina SONTA sosai, SON daban taba jin shi gakowace ya'mace ba Wanda inaji dashi aka halicci *ZUCIYATA.*

Jiyayi "anja tsaki mtswwwww! da sauri yabude idanu "atunanin shi Ammi ce tafito, ga mamkin sa saikawai ganin *ZUBEE* yayi tsaye tana kallon shi, "aikam tuni yahada girar sama data kasa yadaure fuska tamau tareda cewa keh! Ubanwa kikeyiwa tsaki?..

batace komai ba saida baki data turo, tsawa yadoka mata tareda mikewa tsaye yace waini tsaranki ne?..."aikam dagudu tashige daki tareda banko kofa,
tsaki yaja mtsww yace wawuyar yarinya kawai,

duk Saboda kene "akesan hanani cikar burina, kuma insha'Allahu sai burin yacika saina mallaki *"JEEDAH* "amatsayin mata ta Sannan yanufi daki ran'nan nashi abace.

Koda *SEERAJ* yashiga daki wayarsa ya iske tana takara, koda yaduba saiyaga daga can Jordan ne "aikam sai yafara macifa yana cewa dallah garara malamai karkudameni kunji KO?..,

"aikinan fa ninasa kaina idan kuma na gadama sainace' bazanyiba, banga kuma Ubanda zaya sani dole ba, nan dai yaita masifa shi kadai batare kuma da yadaga wayar ba saida yagama Sannan yafada toilet.

"Adaki kam *ZUBEE* saida fada marwa ta keyi tareda fadin asha dama yah S.p wannan *JEEDAR* dayake kira budurwar save?... wani irin kishine yaturnu keta' da karfi tace Amma ko wacece" wannan *"JEEDAH* din ranan dana kamata KO?.. Hmmm mtsww tayi tsaki tareda fita dakin.

_*Nikam nace' tofa*_


*SAJEEDAH* kam tana komawa gida buta tadauka tashiga bayi tana shiga sai tafara kuka, "Ahankali takeyi tana fadin yah *"SEERAJ* Ina SONKA da dukkan *ZUCIYATA* amma meyasa kaimani haka?...yanzu shikenan da gaske mun rabu?...

Da sauri tace' "a ah nasan koda gangar jikinmu sunrabu toh" *ZUCIYOYIN MU* bazasu taba rabuwa da SON junaba, hakanan dai taita kukanta tareda surutai data gama tawanke fuska tafito.

Inna ta kalleta tace tace lafiya meyasa mi'idanunki?... jitayi gabanta yafadi "ahankaci tace' Inna wani abune yafada mun "acikin ido shine nawanke, "aranta kuma tace yihakuri Inna SON yah *SEERAJ* ne yake wahalar da *ZUCIYATA*,

Inna tace' assha sannu tace yauwa toh" yanzu abun yafitakosai nahure maki?... da sauri tace yafita, tace" Allah sarki har *SEERAJON* yatafi?... tace "eh yatafi tace' toh Allah yadawo dashi lafiya tace ameen.

**๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜**
Bayan kwana biyu *SEERAJ* tattara yakoma gurin aiki *ZUCIYAR* shi cikeda Soyayyar *SAJEEDAH*, "a Jordan kam.

*SEERAJ* fly yake kamar mahaukaci fasinjan ko'ina dauka yake shida "abokin aikin sa, aikam sukam kamfanin Na Jordan sunjidadi kasan cewar sunasan "aikin shi saboda kwarewa shi don hakane yasa suketa bulbula masa kudi "acikin account dinsa,

Yayinda shikuma "abokin aikisa yafara nuna ga jiya warsa Da wannan Aiki dasu keyi haka bahutawa, sai kace "agogo shikam *SEERAJ* ba'abunda yada meshi,

fly kawai yake, koya samu yarage jin"abinda yakeji gameda *SAJEEDAH,* saidai kam ba'abunda yaragu saima karuwa Da *ZUCIYAR* shi yakeda kaunarta,

"idan kagan shi duk yara me sai hanci gawani kasumba (saje) dayabari "abuga fari sai yakara farin sosai fatarnan shar kamar kataba jiniyafito *SEERAJ* kenan'na *SAJEEDAH* ikon Allah.


"Abangaren *SAJEEDAH* ma haka "abun yake kullum da SON *SEERAJ* "a *ZUCIYARTA* take kwana da shitake tashi itama duK tarame, sai dukiyar Fulani da hips kawai ke takama "ajikinta Wanda Da "alama basusan halinda take Ciki ba, ga kuma karatu datasa "aranta don haka sai "abun yazamar mata goma Da "ashirin,
Haka dai rayuwa tai tafita fita ga masoya yayida *ZUCIYOYIN* suketa "azabtuwa da SON juna.

******๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜****
Ayau watan *SEERAJ* biyu kenan dakoma gurin "aiki, Wanda yayi dai-dai dati uku kenan da kwantawar Baba rashin labiya tun yana iyafita har yazo yanzu baya'iyafita ko'ina saboda ciwon yayi tsanani,.

Kwance yake "atsakar gida kan dan lotsatsen katifa, Inna ce' keyi masa firfita, *SAJEEDAH* nagefe kamar zatayi kuka gani yadda Baba ke shan wahala, hartana tambayar kanta wannan wani irin zazzabi ne haka da baya jin maganin?...

Maganar Inna ce yakatse mata zancen zucin datake, da cewa shin wai Malam ranan Da kaje asibiti me Likita yace yana damuka?.. idanu yarintse "aranshi kuwa tunani yake meza yace mata?...
nafada mata Likita yace ciwon koda keda mushi?...

_*Kai! Nikam tsoro yakamani dataji irin ciwon dayakama baba, KODA?.. tabdi toh Alla yakawo sauki baba*_

"a ah Saratu kiyi hakuri bazan "iyafada makiba domin fadin yananufin tashin hankalinku, nikuma "Abunda banasan gani kenan afuskarku,

"Ahankali yabude idanu cikinjin "azaban ciwo yace' kin manta nace miki yace zazzabi da taifot neke damuna ba?... Cikin sanyi murya tace' "eh hakane toh" Allah yabaka lafiya yace' Ameen Cikin tausayi *SAJEEDAH* tace' sannu Baba,

yace yauwa *SAJEEDATU* Sajeedu yana can gurin teredar KO?..
tace, "eh baba "aikayan tiredar duksun kare saidan kadan yarage, yace bakomai Allah zaya rufa mana asiri.

******
DA misalin karfe shida na yamma
"Ahankali take tafiya yau ita kadai ce' batareda Sajeed ba tana sanye da uniform Na islamiyya, tafe take tana tunani yadda rayuwa tafara canjawa "agaresu'

musamman ciwon baba dayake ta kara tsananta gashi "abicin da *"SEERAJ* yakawo masu duk yakare hakanan kayan tiredan shima duk yakare, kudin kuma sun siyi magani "amma ciwo sai gaba yake,

Saiganin Mutum kawai tayi "a gabanta dasauri tadaga Kai ta kalleshi jitayi gabanta yafadi ganin irin Kallon dayake yimata, fuska "ayamutse yace kinganeni?..

"Ahankali tadaga kai domin kuwa bazata "alamar "eh domin kuwa bazata taba mantawa da shiba, tsaki yaja mtswwwww Sannan yace natsaneki idanu *SAJEEDAH* yazaro Cikin tsoro tace?...

Aha

Muje zuwa

A

๐Ÿ’˜Zuciyata ce๐Ÿ’˜

Tareda Alkalamin

โœ๐Ÿฝ

๐Ÿ’˜Lufhat ce๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜

๐Ÿ’˜ZUCIYATA CE๐Ÿ’˜

_Based on true life Story_
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜

(Labarin Sarkakkiyar Soyayya)

2โƒฃ0โƒฃ

WRITTEN BY

๐Ÿ’˜ยฉAMEENA UMAR FARUQ๐Ÿ’˜
OR
๐Ÿ’˜MEENAT๐Ÿ’˜


_*Page din nakuna ne kuyi da yadda ku keso dashi, Aunty Na Hadiza Bamalli*_
_*MySweetheart*_ _*Sadiya*_
_*yar fillo tawa*_
_*FateenJos*_
_*Ummu Sadiq*_
_*Kaida duk wani masoyinZUCIYATA CE.*_
________________________

*_ยฎPEN:WRITERS ASSOCIATION_*

*_PEN THE STRONGEST WEAPON_*
________________________

*_only the exquisite and Whizkid writers are opportune to be pen writers_*



โœ๐Ÿฝ


"Don ALLAH Alh karufa Mani asiri kamar yadda Allah yarufa maka, wlh Babana bayada Lafiya nadogara da Allah nadogara da kudin nan saboda samu siya masa magani ne, don girman ALLAH karka hana Mani kudin nan takarashi dasaki wani irin kuka maiba tausayi.

taki Mtswwwww Alh yaja tareda cewa "aifa saikiyi nikam nagama magana kuma, ya kalli Anas yace Oya tafi inda zaka yawuce Sannan shima yawuce, jiki Hajiya sanyi dajin abunda Alh yafada domin tasan halin shisarai idan yace' toh" fayace kenan, itakam wani lokaci Mamaki yake bata yadda yake nuna rashin "adalci DA tausayi acikin Lamarin shi.

_*Hmm Allah sarki rayuwa kenan, narasa meyasa wasu mutane sukeda sankansu dayawa, (bi'ma'na son ZUCIYA kenan ) wai saikaga kirikiri yayansu suna "aikata badai-dai ba, me makon su tsawata masu"sununa masu cewa "abun'nanfa dasukeyi ba'abune mai kyauba, amma a ah saisukiyin haka saima kaga suna goyon bayan yayan'nasu wani lokaci ma sainaga "anrufe Wanda akaiwa laifin dafada toh" wannan wani irin rashin Adalci ne haka?*.._

"Ahankali tadaga *SAJEEDAH* dake tafaman kuka tace Don kiyi hakuri ni kudi dake hannun Na duk baifi dubu daya ba, Bari Na daukomaki dai-dai lokacin da Abba yashiga cikin sanyi murya yace' Hajiya Lafiya meya faru naga tana kuka?.. Nan dai tafada masa duk Abunda yafaru,

Kai ya girgiza Cikin takaici halayyar DA dan'uwansa yakeyi marasa kyau, hannun yasa aciki "aljihun wandonsa yaciro walat dinsa tareda zaro kudi yan dubu-dubu guda biyu ya mikawa, *SAJEEDAH* tareda cewa kiyi hakuri nima banida kudi takarba tareda yin godiya, Hajiya mataje tadauko mata dubu daya takawo mata tareda cewa don kiyi hakuri kinji?..

Cikin kuka tace Hajiya nagode Allah yasa kamaku Da Alkhairi hijab dinta dake rataye saman igiya tadauka tasa Sannan tayiwa Hajiya Sallama tafita. tana Cikin tafiya kawai sai gani tayi ansha gabanta, da sauri tadaga Kai gabanta yafadi saka makon ganin Anas.

Cikin rawar murya tace Don Allah kayi hakuri kar kaketa Mani mutuncina, Murmushi mugunta yayi tareda cewa "Ayya yarinya marinafa kikayi, tace toh "aikarama yace ban ramaba yarinya yanzu dai

Please Login or Register in order to submit comment