Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

da Saurayi DA budurwar suke sha?..

Wani irin shu'umin Murmushi yai "aranshi KO fadi yake aiyau saina tabbatar da abunda "akefadi akanki da gaske ne kalarku daya da kawarki KO" "a ah,

Yace ah irin kiss din'nan mana da romance
kindai gane "ai yakarasa fadi tareda daga mata gira, yanzu kam *SAJEEDAH* jitake kamar kirjinta zayafaso rigarta yafito Saboda tsabar bugawa,

Cikin rawar murya me cike da tsoro tace' wlh niban iyaba bansan ma "anayin irin shiba, yace ah karki damu zan koya maki dai-dai lokacin da yakai hannun shi yakama nata yarike,

jikinta ne yadauki rawa tace "a ah don ALLAH yah *SEERAJ* kabiri banaso, cikin zafin nama irin nazu Na maza yafinciko ta tafado saman kirjinsa, haduwar jikinsu yasa gaba daya jikin su yadauki rawa musamman ma ita, yayinda yake kokarin hada bakin su gurin daya ita Kam KO" Karin kwance kanta take aikam Allah yabata sa'a ta kwance kanta

Yayinda *SEERAJ* yakeji kamar 'ana kara fizgarshi zuwa gareta, "aikam hannun shi yasake kaiwa zuwa gareta daniyar yasake rungumota, saidai cikin rashin sa'a hannun sa yasauka "akan dukiyar Fulanin ta,

Saukar hannun shi saman duniyar fulanin ta yayi dai-dai da taukewar numfashi, *SAJEEDAH* jiyayi kamar wutar lantarki yajashi da sauri yadauke hannun shi tareda zuba mata idanu gani yai idanun ta sun kafe kuma bata numfashi cikin tsoro yace?..

Turkasa

Aha

muje zuwa

A

๐Ÿ’˜Zuciyata ce๐Ÿ’˜

Tareda Alkalamin

โœ๐Ÿฝ

๐Ÿ’˜Lufhat ce๐Ÿ’˜
[6:04PM, 3/8/2018] โ€ช+234 902 288 0912โ€ฌ: ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜

๐Ÿ’˜ZUCIYATA CE๐Ÿ’˜

_Based on true life Story_
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜

(Labarin Sarkakkiyar Soyayya)

1โƒฃ3โƒฃ

WRITTEN BY

๐Ÿ’˜ยฉAMEENA UMAR FARUQ๐Ÿ’˜
OR
๐Ÿ’˜MEENAT๐Ÿ’˜

________________________

*_ยฎPEN:WRITERS ASSOCIATION_*

*_PEN THE STRONGEST WEAPON_*
________________________

*_only the exquisite and Whizkid writers are opportune to be pen writers_*



โœ๐Ÿฝ


*"SAJEEDAH* shuru da sauri yadafa kafadar ta "aikam sai ta tafi luuuuu tafada jikinsa, jiyayi gabansa yafadi harsaida yaji "antar cikin shi yakada,

idanu yarintse tareda furta YA SALAM yayinda yaji wani irin mummunan tashin hankali yaziyar ceshi, wanda tunda yake "arayuwar shi baitaba shiga irin saba sai yau,

Da sauri yabude idanu shi tareda girgiza ta yana kiran sunanan ta da "iyakacin karfin shi, "amma ina tayi nisa domin ko" batajin kiran shi,
duk da sanyi a c motar hakan bai Hana shi jin wani matsananci gumi dake tsatsufo, mashi tunda ga tsakiyar kanshi har zuwa tafin kafar shi ba,

Kiran sunan ta yake yana bubbuga kumatun ta tareda fadin don ALLAH kitashi, ni wasa nakeyi maki pls *JEEDAH* karkiyi Mani haka wlh tsakani da Allah nake SON KI bazan CUCE KIBA, ba'abunda zanyi maki dama fakawai Zan gwada kine, sai faman surutu yake Wanda kanaji kasan baya cikin nutsuwar shi,

Yayinda ita kam bata Masan yanayi ba tunda KO" Dan yatsanta bai motsaba ballan tana numfashi taya dawo, gaba daya hankalin shi yatashi matukar tashi da karfi yafurta Na shiga uku ni *SEERAJ* mena aikata yau?..

Jiyayi wata *"ZUCIYA* tace mashi *KISAN KAI* yayida wata *ZUCIYA"* ta amsa DA bata mutuba' suma tayi da sauri yace' yesss bata mutuba suma tayi, da sauri yamaida ita jikin kujera yajingina ta,

DA sauri yakai hannun shi kujerar baya yana laluben gorar ruwa, aikam ya lalubo gora har uku saidai kam duk wadda yadauko babu ruwa acikin, cikin tashin hankalin yafurta oh my god tareda dafe kai, can kuma sai yadago ya tada motar dakarfi yafizgeta,

gudun yake sosai yanayi yana kallon ta amma har lokacin KO" motsi batayi, saida yayi tafiya menisa sosai Sannan yayi fakin agefen titi Sannan yafito tareda kulle motar, wani shigo siyarda kayan masarufi yanufa yana zuwa yace abashi ruwan gora,

Me shago yace yallabai wani irin za'abaka? da sauri yace' bani kowani irin ne amma dai me sanyi nakeso, yace' toh tareda miko masa gorar faro watar, da sauri yaciro walet a "aljihun wandon shi yazaro dubu daya yamika masa tareda karban goran ruwan, cikin zafin nama yajuya yanufi mota meshago yanafadin yallabai ga chanjinka amma Ina baimasa yanayi ba,

Yana zuwa yashiga motar tareda fizganta dagudu saida yayi Dan tafiya kadan Sannan ya tsaya, da sauri ya bude marfi goran ruwan ya bulbula mata "afuska aikam firgigi tafarka tareda sakin nauyayyan "ajiyar *ZUCIYA*,

Hannun tasa tana share ruwan tareda sakin wani irin kuka mai ban tausayi, kuka take sosai yayinda jikinta ya dauki rawa cikin kuka take fadin don ALLAH, yah *SEERAJ* kayi hakuri wlh ni ba iya irin shiba kumani ba yar'iska bace',

Sai kuma takama kofar motar tana kiciniyar budewa tace kabude Mani "intafi gida bazanje asibiti ba, shi kam kuri yayi mata da idanu yana kallon ta tausayin tane yaka mashi yayinda yaji wani irin Sonta da KAUNAR sun sake ninkuwa "a *ZUCIYAR* shi fiye dawanda yakeji Da,

Yayinda yaji wani irin tsanar kanshi ya darsu *A ZUCIYAR* shi "aranshi kuwa fadi yake meyasa nayi maki haka?.., meyasa *ZUCIYA TA* batagane cewar kedin kamilalla ba ce har saida Na yarda da shawarar S A NASKO?.. meyasa meyasa...

Kukan tane yakatse mashi zancen zucin dayake, ahankali yace' don ALLAH *JEEDAH* kiyi hakuri ba'abunda zanyi maki, tace' toh" kabude Mani intafi gida bazani asibitin banace KO" dole ne?.. jiyayi kirjinsa yabuga, domin dakarfi tayi tayi maganar Wanda tunda yakeda ita baitaba jin tadaga murya haka ba,

Da sauri yace' toh" tareda tada motar tace' mlm bude Mani nace" kayi Zan fita, cikin sanyi murya yace' kiyi hakuri daga nan zuwa gida akwai nisa sosai amma yanzu zamu isa kinji?..

Banza tayida shi tareda komawa tajingina kanta da kofa, tana cigaba da Kukanta mai tsuma *ZUCIYAR* me saurare Kuku take me cikeda DA NASANI biyoshi, "aranta KO" fadi take alhakin "Inna ne ya kamani na karya datayi mata, "agogon motar ta kalla yanuna mata karfe 10:40pm gabanta yasake faduwa,

"aikam takara sakin wani sabon kukan, shikam *SEERAJ* kallo daya zakai mashi kagane baya cikin nutsuwa,
domin kuwa sai zuba Uban gudu yake akan titi ba kaukautawa, yayinda yakeji kukan *SAJEEDAH* har cikin *ZUCIYAR* shi tamkar Ana chin'na masa garwashin wuta, gumi kam hmmm nabar muku sani domin kuwa gaba daya rigarsa tajike sharkaf,

"A haka suka isa yanayin fakin tana kokarin fita saidai taji kofar gam, ahankali ta kallon shi tareda cewa bude mani infita, cikin sanyin murya yace don Allah *SAJEEDAH* kiyi hakuri wlh ban.. katseshi tasakeyi dacewa kabude Mani nace,

Da sauri yace toh" tareda bude kofar yafita Sannan yaza gaya yabude mata kofa, saida tafito Sannan tayi mashi wani irin kallo Wanda narasa gane kowani irine, saidai tuni shikam yagane kallon tsana tayi mashi, Sannan tace ban yafeba tareda wucewa da sauri
tanufi gida,

Bin bayan tayi dakallo har tashiga lungun gidansu,Sannan yaje yashiga motar tareda fizgarta dakarfi a 360 yabar unguwar.

"Ashe duk abunda kefaruwa akan idanu Inna ne tun lokacin dayayi fakin,

_*Nikam nace wayyo SAJEEDAH yau sunan ki Sorry agurin inna*_

"Abunda yafaru kuwa bayan firar *SAJEEDAH* daga gida, shine bayan Inna ta gama yiwa Sajeed tatsuniya saibacci yakwashe shi, tana nan zaune shuru har tsawon wani lokaci bataga *SAJEEDAH* ta dawoba gida ba, hakanan saitaji hankalin ta bai kwanta na don haka saita tada Sajeed takaishi daki bayan tafitoh"saita saka hijab tanufi gidan Alh Siddi,

Shahin Mama yanufa bayan sungaisa sai Mama tace yasu" *SAJEEDAH,* kwana biyu bamu gantaba tunda kawarta batanan, gaban Inna ne yafadi tayi dariyar yake tace" sunan tafiya, sundan taba fira Sannan Inna tace saida safe dama nazo gaidaku ne, Mama tace toh" mun gode saida safe sannan tafita gida.

*ZUCIYAR* ta cikeda tunanin idan *SAJEEDAH* taje tana shiga gida Baba yana shigowa, tace sannu zuwa yace' yauwa harsu" *SAJEEDATU* sunyi bacci ne?..tace' eh Sajeedu ne yai bacci ita tashiga gidansu *SADEEQAH,*

yace' toh" sun taba fira kadan Sannan Baba yaduba tsohon agogon hannun irin me kacadin nan Nada, yaga karfe goma shadaya saura mitin biyu, yace Saratu kije kikira *SAJEEDATU* tazo ta kwanta dareyayi, Inna tace' toh" tareda fita toh"su kuma adai-dai wannan lokacin suka iso,

tana gani *SAJEEDAH* tafito daga mota sai tayi sauri komawa gida batareda tabari *SAJEEDAH* taganta ba, yayinda Inna taji gabanta saifaduwa yake Baba na ganinta yace' Ina *SAJEEDATU?..* tace' gatanan zuwa,

Da sauri tashiga gida Baba yace *SAJEEDATU* "atafi'a kwanta hakan dareyayi, toh"tace tareda shigewa dakinsu suma su lnna suka shiga nasu" dakin,

lnna ce' tafito hannun ta rikeda buta kamar zata ke waya saidai kuma bakewa yawar zatayiba, domin kuwa dakin *SAJEEDAH* tanufa isketa tayi tana kokarin cire abayar, amma jinshigar Inna dakin yasata fasa,

DA sauri takoma gefe ta tsugun'na yayida jikinta sai rawa yake, faduwar gabanta yatsananta gawani irin kunyar Inna dataji yakamata, domin kuwa gani take kamar Inna tasan Abunda yafaru, tsakanin tada yah *SEERAJ*

Inna kam kallon *SAJEEDAH* take kallo me cikeda tuhuma, yayi da take mamaki wai *SAJEEDAH* "asauke wannan bakar mota?..innalillahiwa'ina'ilaihirraji'un, shine "abunda inna tafura, jitayi hankalin ta yatashi tareda jin matsananci bacin ran, yayinda take tambayar kanta shin "ina tarbiyar danaiwa yarinyar nan badai ta watsarba?..
Tabdi,

Da sauri lnna tace' daga ina kike?.. *SAJEEDAH* kam takasa magana Saboda tsabar tsoro, tsawa Inna tadoka mata tareda cewa ba dake nake magana ba?.. yanzu kam me makon tsuguni, zaune take "akasa dirshan cikin matsanancin tsoro *SAJEEDAH* tace?..


Aha

Muje zuwa

A

๐Ÿ’˜Zuciyata ce๐Ÿ’˜

Tareda Alkalamin

โœ๐Ÿฝ

๐Ÿ’˜Lufhat ce๐Ÿ’˜
[6:05PM, 3/8/2018] โ€ช+234 902 288 0912โ€ฌ: ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜

๐Ÿ’˜ZUCIYATA CE๐Ÿ’˜

_Based on true life Story_
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜

(Labarin Sarkakkiyar Soyayya)

1โƒฃ4โƒฃ

WRITTEN BY

๐Ÿ’˜ยฉAMEENA UMAR FARUQ๐Ÿ’˜
OR
๐Ÿ’˜MEENAT๐Ÿ’˜

________________________

*_ยฎPEN:WRITERS ASSOCIATION_*

*_PEN THE STRONGEST WEAPON_*
________________________

*_only the exquisite and Whizkid writers are opportune to be pen writers_*



โœ๐Ÿฝ


'Gidansu" besty naj..takasa karasa wa saka makon dakuwa da lnna tawatsa mata, cikin mamaki tace wata karyar zakiyi sakeyi mani bayan wadda kikayi Mani dazu, toh" waike yaushe nema kika koyi karya ne?...

Da sauri lnna ta Karasa kusada ita kun'nanta takama Da dan karfi, tareda cewa Uban waye" yasaukeki "amota?..yanzu kam *SAJEEDAH* mutuwar zaune tayi yayinda taji kamar zatasaki fitsari saboda tsabar tsoro, tabbas yau tasan kashinta yabushe toh" wazatace,

yah *SEERAJ?..* Ina tasan kotasha giyar wake bazata ce shibane, domin kuwa tasan daga lnna har Baba cikin su" ba wanda zaya yarda dacewa da yah *SEERAJ* ne suka fita 'amota,

Inna ta katse mata zancen zucin datake, dacewa *SAJEEDAH! SAJEEDAH!! SAJEEDAH!!!* saida Inna takirata sau uku, Wanda yasa tashin hankalin ta yakaru domin kuwa tunda tayi wayo bata tabajin Inna takira sunan taba sai yau,

Cikin bacin rai tace sonawa kikaji nakiraki sunan ki?..cikin sheshhekar kuka tace so uku Inna, tace toh" narantse da Allah duk ranan dakika kuskura kika salwantar da mutuncin ki Saboda "abun duniya KO" kuma kikabi rudin da namiji yaje yakaiki yabaro,

toh" daga ranan saidai kinemi wata *UWAR* Amma bani *SARATU* ba kinji nagaya maki, tace kai! waike "aka sauke amota?.. wlh kinban mamaki shashashar yarinya kawai, sannan tasakar mata kunne tareda fita daga dakin ranta abace,

"inda tabar *SAJEEDAH* cikin matsananci tashin hankali, kuka take tana fadin kacuceni yah *"SEERAJ* wannan shine karo nafarko "arayuwa ta da Inna ta tuhumeni kuma shine Karo nafarko danaga mummunan bacin ranta,

meyasa zakayi Mani haka dama ba tsakani da Allah kake sona ba, dama da wata manufa kake SONA?..idan KO" hakane tabbas kazalinci *ZUCIYATA* data Aminta dakai haka dai take tafaman surutai irin Na Wanda baya cikin nutsuwar SA.

*SEERAJ* kam bai tsaya ko'ina ba sai gidansu" *SAGEER* dama motarsa ya ara, cikin tashin hankali yayi fakin yafito yanufi shashin *SAGEER* yana kwala masa kira, yana zaune yana kallo yaji kamar ana kiran shi yamike kenan saiga *SEERAJ* yabanko labule da karfi,

key motar dake hannunshi da'iyakaci karfin shi yajefi *SAGEER* dashi "akirji, da sauri yadafe gurin tareda cewa washhhh! domin yaji zafin jifan, saida kuma baigama fita daga radadin jifarba,

*SEERAJ* yakaraso gurin shi tareda kai masa wani mahaukacin naushin, wanda badan *SAGEER* din yayi saurin karewa da hannun shiba tabbas daya hada masa jini da majina,

Rai abace *SEERAJ* Yace ashe Kai bad friend ne ban saniba? cikin tsoro *SAGEER* menayi maka?..yace kasan abinda shawarar daka bani takusan haifar mani yau?.

Kai ya girgiza "alamar "a ah, yace toh" banzar shawarar daka bani tasa nakusa aikata abunda da har na mutu bazan daina danasani "aikata shiba,
gaba daya *SEERAJ* yabir kice wa *SAGEER*
Cikin bacin ran ya chakumi kwalar rigasa tareda cewa kuma kace abokin barawo barawo neko?.. Kai yadaga masa alamar "eh, sakin shiyayi tareda chusa hannun shi "acikin sumar kanshi yayi tafiya kadan sannan yadawo yasake chakumar kwalar rigan *SAGEER* din yace toh" abokin manemi matafa ina nufin kai namamajo?.. Yanzu kam *SAGEER* yafahimci dashi *SEERAJ* yakeyi, don haka cikin sanyi murya yace' balallai bane yazama manemi mata, da sauri *SEERAJ* yace ton" haka nan shima dan'iska balallai abokin sa yazama dan'iska irin shi ba, saboda haka kasani cewa Hannun nane kawai yasauka akan breast din *SAJEEDAH* ta sume mani, cikin tsoro *SAGEER* yace' me?..

Yace "eh dogon Suma tayimun amota Wanda hankali yai mummunan tashi, don haka idan har *"SADEEQAH* yar'iska ce toh" *"SAJEEDAH TA* ba yar'iska bace itadin kamilace Na tsattsiya,

Saboda haka kar ka sake kiranta yar'iska Sonta kuma wlh yanzu nafara saboda haka karkasake tunanin cewar narabu da'ita, kuma daga yau bazan sake daukar shawarar kaba, yana kai nan yafita ransa bace.

yayinda yabar *SAGEER* cikin tashin hankali domin kuwa lamari yabashi tsoro tareda mamaki haryana firta daga taba breast sai suma?...caf.

Ciki tashin hankali *SEERAJ* ya'isa gida, direct toilet yashiga batareda tsayawa cire kayaba ya sakarwa kanshi ruwa, yakusa Kai minti talatin yana zubawa kamshi ruwa sannan yacire kayan yadauro tawul yafito, saidai har lokacin beji *ZUCIYAR* shi tarage *ZAFI* da abinda ya'aikata wa *SAJEEDAR* shiba,

musamman idan yatunada kukan ta tareda Kalmar Da tafada masa duk sai yaji *ZUCIYAR* tana tafasa, hakanan yasa kayan bacci ya kwanta saidai da'alama idanun shi basuga bacci ba,

domin kuwa juyi kawai yake akan makeken gadonshi har kusan 2:30 bairintsa ba dadai yagaji da juye-juyen sai kawai yatashi yashiga toilet yadauro alwala yazo yafara lafilfili.

"A bangaren *SAJEEDAH* ma hakan ya kasan bayan tagaji da kukan domin har wani jiri-jiri takeji, dakyardai ta tashi taje tadauro alwala tafara gabatar da lafila tanayi tana kuka,

hakanan dai *SAJEEDAH* da *SEERAJ* suka kwana batareda ko dayansu" yarintsaba.

****************
Washegari tunda *SEERAJ* yayi sallar "asuba yafito, "Ahankali yake tafiya kamar wanda kwai yafashi masa aciki, kwata-kwata bayajin dadi jikinsa garahin baccin Da baiyi bajiya, harda shiyasa yake jin wani irin ciwon kai "ahaka har ya'isa gurin Da suke tsayawa da *SAJEEDAH* saboda yasan yau lahadi dole zasuji islamiyya, don haka ne yai sammako don yabata hakuri zama yayi "akan da Kalin da wani lokaci suke zama suyi fira.

๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
Aunty *JEEDAH* injiraki agurin baba?..kai tadaga alamar "eh, dasauri Sajeed yafita yayinda barta tana karasa shiryawa, "ahankali tatsugun'na gaban Inna cikin sanyi murya tace Inna "Ina kwana, banza inna tayida ita ta sake fadin Ina Kwana nan ma shuru,

Saikawai tafashe da kuka tareda fadin don allah inna kiyi hakuri wlh bazan sakeba, fushin ki agareni masifa ne idan kikaci gabada fushidani rayuwa ta bazatayi dadi ba *ZUCIYATA* bazata taba samu sukuni ba har saikin yafemani, kinji inna don ALLAH kiyafe mun nayi miki "Alkawari bazan sake yimani karya ba insha'Allahu.

"Ahankali lnna tada gota kalli yartata tsakanin jiya da yau har tafada tayifayau da'ita kamar tayi zazzabi, tsakanin ya' da uwa sai Allah take taji tausayin ta yakamata,

"Amma duk da haka ta naji "aranta sai ta hukunta ta,saboda gaba kar tasake "aikata laifi makamancin wannan, "ahankali Inna tace ki tashi ku tafi karku makara tace to tareda tashi tana share hawaye,

Tundaga nesa tahangoshi, jitayi gabanta yafadi yana zaune akandali ya rungume hannu wa akirji, yana sanye jallabiyya baka,
tun kafin su karasa gurin shi Sajeed yafara cewa lah Aunty *JEEDAH* ga yah *SEERAJ* my friend can,

Yana ganinsu yatashi dasauri yanufosu Sajeed ne yace' yah *SEERAJ* Ina kwana ya'amsa lafiya lau, Sajeed yace my friend yau idon Aunty *JEEDAH* yana ciwo, jiyayi kirjinsa yana bugawa yayinda idanun shikuma yanakan *SAJEEDAH*,

"Itama kirjinta bugawa yake idanun ta suke kallon Sajeed dayake rikeda hannun *SEERAJ*, cikin sanyi murya tace jeed kafara tafiya nima yanzu zan iskoka kaji? Yace toh tareda tafiya,

"Ahankali ta kalleshi jitayi gabanta yafadi ganin yadda yarame, gawani son shi dataji yakara shigarta tawani gefen kuma tana jin haushin shi har tanaji "aranta dolene tarabu dashi kon gudun fadawa halaka,

Shima *SEERAJ* haka yaji musamman dayaga idanun ta sunyi luhuluhu, alamar tasha kuka tagaji jiyayi son tayana ratsa ilahirin jikinsa, musamman ma *ZUCIYAR* shi dayake tabbacin "anan akahalicci Sonta,

"Ahankali ya dukar dakai kasa domin kuwa wani rin kunyar ta yaji yakama shi, saka makon tunawa da "abunda yai matajiya cikin sanyi murya yace'?..

Aha

_Tofa su *SEERAJ* meza'acewa *SAJEEDAH?..*_

Muje zuwa

A

๐Ÿ’˜Zuciyata ce๐Ÿ’˜

Tareda Alkalamin

โœ๐Ÿฝ

๐Ÿ’˜Lufhat ce๐Ÿ’˜
[6:06PM, 3/8/2018] โ€ช+234 902 288 0912โ€ฌ: ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜

๐Ÿ’˜ZUCIYATA CE๐Ÿ’˜

_Based on true life Story_
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜

(Labarin Sarkakkiyar Soyayya)

1โƒฃ5โƒฃ

WRITTEN BY

๐Ÿ’˜ยฉAMEENA UMAR FARUQ๐Ÿ’˜
OR
๐Ÿ’˜MEENAT๐Ÿ’˜

________________________

*_ยฎPEN:WRITERS ASSOCIATION_*

*_PEN THE STRONGEST WEAPON_*
________________________

*_only the exquisite and Whizkid writers are opportune to be pen writers_*



โœ๐Ÿฝ


*"JEEDAH* don ALLAH kiyi hakuri abunda yafaru jiya wlh sharrin shed... kasa karasa wa yayi saka makon dago kai datayi suka hada idanu, wani rin kwarjini tayi masa itadin ma haka taga yayi mata kwarjini sosai,

"A hankali tadukar dakai kasa cikin sanyi murya tace' "Abunda yafaru jiya yariga yafaru wanda nayi mamakin faruwar haka daga gareka,

Saidai kuma ba'abun mamaki bane idan akayi la'akari da kokai waye, da sauri yace' haba *JEEDAH* don Allah karkiyi mani mummunan fahimta ni wane dazan aikata haka din?...

tace ah Kaine mana *SEERAJ ABBAS SARDAUNA* shahararran matukin, jirgin sama dayayi suna "acikin Nigeria da dawajan ta,
so kaga kanada damar dazaka aikata fine da hakan KO?..

Wani irin matsananci mamaki yakama shi "aran shi kuwa fadi yake ya'akai tasan haka?..katse shitayi dacewa kana mamaki ne KO? yadda "akayi nasan haka?.. toh' karkayi mamaki domin kuwa duk wanda Allah yadaukake shi yariga yadauka keshi, koda bayaso mutane susani, toh" dole sai sun sani domin ita daukakar Ubangiji bata boyuwa.

taci gaba dacewa Tun ranan da kace kana SONA nake mamakin tareda tambayar kaina meyasa kake kesona?..

Mamakina yakaru ne shekaranji jumma'a naje office din malamai, domin nakira malamin dazaya dauke mu darasin ranan sai naga jarida akan teburinsu, hotonka nagani "ajikin jaridar Da farko nayi zaton idanuna ne sukeyi mani gizo saida naduba sainaga cikakken sunanka.

Wani malami na tambaya waye kai?.. saiyayi mani cikakken bayanin KO kaiwaye,

Nafito office din ina tambayar kaina "amatsayin kana kyakkyawa Saurayi, me kudin me'aji tareda matsayi meyasa kake so Na?

toh" nidai nasan ba kyakkyawa bace, balle nace KO" kyauna ne yarudeka saidai nagode wa Allah Da wannan daya bani, domin nasan nafiwata, sannan kuma ni ba me ilimi bace balle nace KO iliminane ya birgeka, shima nagode wa Allah dawanda yabani domin shima nasan nafiwata,"

hakazalika Babana ba me kudi bane balle nace KO saboda kudin shine yasa kake sona, saidai nagode wa Allah DA yabani shi "amatsayin Ubana, duk dayaka sance bai kudi bane Ina "alfahari da kasan cewar shi Uban "agareni domin yawadatani da abunda Allah yahore masa,

tace' sai yanzu ne nafahimci abundaya yasa kace kana sona saboda nidin bakowa bace, hakanne zaya baka damaka yaudareni yadda keso, kaga koda kayi nasarar cutata ba'abunda za'ayi, wannan shine manufarka nakin baiyyana mani KO" Kai wanene,
saidai kuma dakaki baiyyana Mani kanka sai gashi
Allah ya baiyyana ka tareda manufarka akaina,

Da sauri yace pls *JEEDAH* kidaina wannan maganganun walh zasu tarwatsa mani kwakwalwata, idan harzan cigabada sauraren su nasan bankyauta ba, shiyasa nace don kiyi hakuri tunda yariga yafaru kuma nayi maki alkawari hakan bazata sake faruwa ba kinji?.. yakara she magana cikin sanyi murya me cike da nadama.

tace tabbas Abunda yafaru jiya tsakanina dakai yarega yafaru Na kuma nayafe maka, domin Kai din Mutum ne mekima da daraja a *ZUCIYATA* saidai ni bazan iya cigaba da Soyayya dakai ba,

Cikin tashin hankali yace No *JEEDAH* karkiyi Mani haka wlh ke kadai *ZUCIYATA*, ke SON,
"aran ta tace wlh nima Kai kadai *ZUCIYATA* ke SO "amma dole narabuda Kai domin idan har zanci gabada zama dakai toh" KO tabbas watarana SON kazaya iyasani Na "aikai abunda zandawo inada nasani,

"Afili kuma batace komai saida ta kura masa idanu jin SON shi take yana saketrasata, shima din kallon tayake yayinda yakejin ta "aranshi fiyeda yadda takejin shi, cikin sanyi murya yace" kiyi hakuri wlh bada wata manufa nayi maki haka ba, nayine kawai daninyar nagwadaki.

Da sauri tace gwaji gwajifa kace?..yah *SEERAJ* duk tsawon zaman mu baka gane halina ba harsai ka gwadani?.. jitayi wani irin haushin sane yaturniketa gawani SON shidake faman nukurkusan *ZUCIYAR* ta,

Dago Kai tayi tawatsa masa wani irin kallo me cike da SON shi da kuma haushi sa, tace ka cuceni yah *SEERAJ* tunda baka yarda daniba, da sauri yace wlh *JEEDAH* Na yarda dake sharrin shedan nekawai,

Tace baka yarda daniba tunda harsaida ka gwadani ta wannan hanyar, gwajinda yasa Na shiga tashin hankalin daban taba shigarsa "arayuwata ba,Wanda harsaida nasaka mahaifiyata cikin,

bayan karyar da kasani nayi mata Wanda bantaba yiba tadalilin haka naga mummunan bacin ranta tabbas baka kyauta maniba,

Saboda haka bani bakai yah *SEERAJ* dai-dai lokacin da tafara tafiya tanajin *ZUCIYARTA* Na *ZAFI* narabuwa dazatayi dashi, ga wani irin sarawa DA kanta yakeyi saidai ta ganin rabuwa dashi shine abumafi "a ala "agareta,

Cikin tashin hankali yasha gabanta tareda cewa don ALLAH *JEEDAH* karkiyi Mani haka wlh Ina SONKI dawa kuma *ZUCIYATA* bazata juri rashin ki ba,

"Aranta tace nima ina SONKA dayawa *ZUCIYATA* nima bazata jure rashinkaba, saidai kuma dole Zan koyama *ZUCIYATA* juriyar rashinka,

"A hankali tace ka koyamata, da sauri yace bazata iyaba
Domin da SONKI "aka halicci *ZUCIYATA*, batace komai ba saidai tabita gefensa zata wuce Da sauri yace' pls *JEEDAH* tareda rike hijab dinta Wanda baimasan lokacin daya rike din'naba domin gaba daya hankali shi yatashi sosai gani yake idan ta tafi yarasata kenan,

Kallon datayi masa neyasa shi sakin hija din yace don *SAJEEDAH* ki' saurareni, cikin bacin ran tace bazan saurareka dinba
kuma karka sake zuwa gidanmu"

Idanu yazaro Cikin tashin hankali yace' a ah *JEEDAH* hukuncin nan yayi Mani tsauri, bazan iyajure rashin Baba. tace shikenan idan kuma kazo saina fada masa Abunda kayimani, cikin tsoro yace toh" shikenan idan har rashin zuwa shine kwanciyar hankalinki toh" bazan zoba,

"Amma don Allah kiyi hakuri karki kafada masa kinji?. Baba yana ganin mutunci na,
"Aranta tace shiyasa banasan mutunci nakaya zube "a idanu shi, sannan tajuya jiki "asanyaye ta tafi yana tsaye yana kallon ta hartashige lungu.

Ahankali yadaga kafafunsa dayaji sunyi masa nauyi yafara tafiya, Cikin sanyi jiki yayinda yakejin jiri yana kwasanshi gawani sarawa dakanshi yakeyi *ZUCIYAR* kuwa ZAFI takeyi masa aha kadai yanufi gida.

*SAJEEDAH* kam dakyar ta'isa islamiyya karatu "akeyi amma ita sambata fahimtar komai, domin kuwa wani irin rawa jikinta yakeyi kanta kuwa sai famanyi mata ciwo yake, gashi dai lokacin sanyi ne "amma ita sai gume takeyi, domin kuwa har hijab dinta yajike sharkaf dagumi alamar zazzabi yana San kamata,

Ya Sayyadi ne yakula da halin datake ciki yace' *SAJEEDAH* lafiya meke damunki?.. cikin rawar murya tace kaina keyin ciwo yace asshi sannu kitafi gida kawai Allah yakara sauki,

tace Ameen tareda da mikewa saidai kuma da sauri takoma ta zauna, saka makon jidatayi jiri zaya yarda ita kasa da sauri yace Subhanallahi, Mariya kamata kirakata gida tace
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment