Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zanrama.

"Ina kudin da su brother "Abba suka baki cikin tsoro tace' gasu tareda mika masa, hannun shi yamika zaikarba saiyana kokarin hadawa da hannun ta, "aida sauri tasaki kudin kasa tareda Da budawa a 360, tsaki yaja mtsww tareda cewa kin kuru yarinya da yau kinga ne bakida wayo kudin yadauka tareda juyawa yatafi.

Saida tayi nisa Sosai Sannan ta tsaya tana maida numfashi, tareda cewa Allah ya'isa mugu Azzalumi macuci kawai kuma sai Allah yabi mani hakkina, sai kuma tafashe dakuka mai ban tausayi tunani take yanzu shikenan duk lokacin da tabata tanayi masu "aiki tayi " don tasamu kudin dazasu siyawa baba magani yanzu yatashi abanza kenan?.., Allah ya'isa tasake furtawa hakan taita tafiya tana kuka har ta'isa gida.

Da Sallama tashiga gida direct gurin Baba tanufa tsugun'nawa tayi tareda cewa sannu Baba ya jiki?, yace' yau kindawo? tace "eh har ta tashi tamike, yace zonan *SAJEEDATU* tace toh" tareda tsugun'nawa "ahankali yace matso sosai,

"Ahankali takara gushi kusada shi Sosai idanu yakurawa fuskarta tareda Kai hannun shi saman kumatunta, inda shatin hannun Ana's yafito rudurudu Cikin sanyi murya yace' *SAJEEDATU* wanene yai wannan Aiki haka baisan cewa fuska gurine mai "DARAJA" ba?. amma shine ya mareki harsai da shatin hannun shi yafito "afuskarki.

Kuka tafashe dashi "aranta kuwa tanaji dole tafada masa gaskiya domin boyewar batada "amfani, wama yasani ko rashin fada masane alhakin shi yakamasu , a hankali yasake cewa *SAJEEDATU* wane yamarar Mani ke?.. Cikin kuka take fada masa duk "abunda yafaru.

Shuru yayi can kuma sai shima yafashe da kuka Wanda yasa hankali *SAJEEDAH* yatashi tareda Na Inna dake zaune kusa dasu, Cikin kuka yace oh Allah inada rayuwata wani yafaracin zarafin zuri'ata akan takare mutuncin ta, Oh ni Abubakar toh" inaga banida rayuwa?...

"Oh Allah kasani cewa nimarayane banida Uwa banida Uban yan'uwana sunkini, batareda nayi musu komai ba Ya UBANGIJI hakan yana nufin banida kowa bani komai sai KAI RABBIL'IZZATI, sai ko" zuri'ar daka bani,

Ya UBANGIJI kazamo gatana kakareni kakaremani zuri'ata KO" bayan baraina kajibanci lamuransu, Allah karkawa mutum ko Aljan damar cutamasu haka Baba yaita Addu'a mai ratsa *ZUCIYA*, yanayi yana hawaye suma *SAJEEDAH* da Inna sunayi suna fadin Ameen haka Sajeed yazo ya'iskesu shima yabi kayi, hakanan sukai tayin kuka babu mai lallashinsu saida sukayi mai isarsu' Sannan sukai shuru.

"Ahankali Baba yakalli Inna tareda cewa Saratu meyasa zakiyi Mani haka?.. Cikin kuka tace toh" Baban Sajeedu sokake mubarka Cikin wannan halin kullum ciwo sai Kara gaba yakeyi, yace toh idan ba ku barniba ya zakuyi dani kune zaku yaye Mani "Abunda Allah yadora mani?...

tace "a ah yace toh tunda baza ku'iyaba kubari ALLAH da yadora mani yayaye mani, ninasan wannan ciwon jarabawace "ina kuma rokon Allah yabani ikon cinyewa sukace' Ameen.

_*Ikon ALLAH wai duk wannan halin dasu SAJEEDAH suke Ciki Alh Siddi dashi DA iyalinsa, suci me kyau susha me kyau sukuma kwana a me kyau, Anya Alh Siddi makocin kwarai ne kuwa?..wai "ace kanada makoci ka kwana daya biyu sati daya sati biyu Kai har watan'ni baka ganshi ba, "amma kodai kace Bari dai nagani wannan mutumin ko Lafiya kwana biyu ban ganshi ba "amma bakayi haka ba toh" dama haka makotata yake? Kai Allah kaimana tsari DA makoci irin Alh Siddi Ameen*.._


****๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜***
*JORDAN*
Firgigi yafarka daga firgitaccen mafarkin dayakeyi kwana biyu nan salati yakeyi, ga sanyi a c amma kuma saifam share gumi yake "ahankali yafurta meyasa nake ganiki kina kuka kullum saina ganki cikin barcina kina kuka, saidai kukan ki nayau yafi Na kullum Why! Why!! Why!!! *MY JEEEDAH* meyasa kike kuka?.. hakan yana nufin wani "Abu mara dadi yana damunki KO?..

Dasauri yatashi tareda cewa No my *My "JEEDAH* *ZUCIYATA* baza tajuri jin Kukan ki "afiliba balle "amafarki, saboda haka yau gida zani Inason ganin ki *My "JEEDAH* kayan shi yaketa hadawa "a trolley bag dinsa, saidaya gama hadawa Sannan yafada toilet donyin wanka Bayan yafito Ya shirya Cikin wani bakin suit sunyi masa kyau sosai Sannan yaja trolley bai tsaya ko'inaba sai gurin aikinsu.

Direct office din Ogansu yanufa yaimasai bayani zayatafi gida da Ogan zaya hanashi toh" amma *SEERAJ* din yataka masa burki don haka yanaji yana gani yawuce.
badan yasoba, saboda basuda kamar *SEERAJ* "agurin Aiki su.

_nikam nace hmmm *SEERAJ* kenan *SAJEEDAH* ikon hadari sagabanka inda kake so toh" aima yayi kokari kusan wata hudu. bega *ZUCIYAR* shiba lol._

Shikam *SEERAJ* yanafita yanufi inda girgin Nigeria yake yashiga sai gida girginsu, ya'isa gida Nigeria lafiya Abuja suka sauka kasan cewar girginsu bai saukada wuriba, shiyasa yasai Cikin dare suka iso Minna direba yakira yazo ya dauke shi wanka yayi yai sallah Sannan Ya kwanta domin yagaji saida *ZUCIYAR* shi cike dasonganin *SAJEEDAH.*

Washegari DA misalin karfe 6:00Am nasafe
*SAJEEDAH* da Inna ne "akan Baba saikuka sukeyi kasan cewar kwana yayi yana suma, dasauri naga tafita gidan Alh Siddi naga tanufa buga kafar gidan take da'ita kaci kar fita, megadine yabude batareda tace masa komai ba tanufi Cikin gida.

Sha-shin Momi tanufa nanma kofar take tabugawa kasan cewar basu ta shiba, Momi ce tabude kofar tana ya tsina fuska tareda cewa lafiya kike bugani kofa haka tunda sa sassafe?..kasa *SAJEEDAH* yazube cikin kuka tace don Allah Momi ketaimaka mana da direba, yakai baba "asobiti wlh kwana mukayi yana suma kinji?..

Tsawa Momi tadakama *SAJEEDAH* tareda cewa dalla gafara malam zo ki fita daga gida nan, wane za yadauki wannan matsiyacin UBAN naki amotar sa?.. dasauri tamike tareda cewa dakata Momi duk abunda zakifada toh" kifada "akaina kada kikuskura ki aiban ta mahaifina, kuma da tsiyarsa dakomai betaba nema sisi agurikuba Mom itace eye ni zakiyi wa rashin kunya?..

batareda tace' mata komai ba tajuya tana kuka tafita daga gidan, ba gida *SAJEEDAH* tanufaba Bayan gidan Alh Siddi taje tazauna saman wani sokawe, kuka takeyi Sosai tareda tunani ina zataje tasamo abun hawan da zasukai Baba asibiti?..can dasauri naji tace?....


Aha

muje zuwa

A

๐Ÿ’˜ZUCIYATA CE๐Ÿ’˜

Tareda Alkalamin

โœ๐Ÿฝ

๐Ÿ’˜Lufhat ce๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜

๐Ÿ’˜ZUCIYATA CE๐Ÿ’˜

_Based on true life Story_
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜

(Labarin Sarkakkiyar Soyayya)

2โƒฃ1โƒฃ

WRITTEN BY

๐Ÿ’˜ยฉAMEENA UMAR FARUQ๐Ÿ’˜
OR
๐Ÿ’˜MEENAT๐Ÿ’˜

________________________

*_ยฎPEN:WRITERS ASSOCIATION_*

*_PEN THE STRONGEST WEAPON_*
________________________

*_only the exquisite and Whizkid writers are opportune to be pen writers_*



โœ๐Ÿฝ


"Yah *SEERAJ* dasauri tamike tafara tafiya tafiya take tamkar tababbiya bako hijab kasan cewar tana sanyeda wata doguwar rigar atamfa data kode sosai dayake dankwali yanada Dan girma saita yatashi saidai kam kallon guda zakai mata kafa himsi bata Cikin nutsuwar ta
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜

๐Ÿ’˜ZUCIYATA CE๐Ÿ’˜

_Based on true life Story_
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜

(Labarin Sarkakkiyar Soyayya)

2โƒฃ2โƒฃ

WRITTEN BY

๐Ÿ’˜ยฉAMEENA UMAR FARUQ๐Ÿ’˜
OR
๐Ÿ’˜MEENAT๐Ÿ’˜

________________________

*_ยฎPEN:WRITERS ASSOCIATION_*

*_PEN THE STRONGEST WEAPON_*
________________________

*_only the exquisite and Whizkid writers are opportune to be pen writers_*



โœ๐Ÿฝ


*"JEEDAH* meyasa kika jawo kafar?. "ai idantarufe bata buduwa sai "ansa key, kuma key din yanata can waje.

Cikin sheshshekar kuka tace "a ah yah *SEERAJ* bafani narufe ba, cikin tsoro yace wane yarufe toh?.. wadda ta nuna manu inda kake bayan nashigo saitaja kofar tarufe.

Cikin matsananci tashin hankali yace yakamanin tayake?.. tace farace gaje tas... cikin bacin rai yakatse ta dacewa naganeta, *JEEDAH* naganeta *"ZUBEE* ce bansan meye nufinta nakulle Mani dakiba alhalin kuma tasan ina ciki, yana maganan ne yana Neman lambar *ZUBEE* "awayar shi.

Cikin sa'a yasa meta sai Kara take wayar Amma bata dagaba harta tsinke, cikin bacin rai yasake kiranta ga mamakin shi sai yaji wayar "akashe, "aikam sai kiranta yake Amma amsar daya ce' "wato switch off.

Cikin matsananci takaici yadaina kiran lambar *ZUBEE,* ta yakoma kiran lambar Ammi ita kuma sai faman Kara take amman bata dagaba, yakira Ammi yafi'akirga Amma haryanzu bata daga ba. idan ran *SEERAJ* yakai miliyan toh" yabaci.

Da sauri yafara kiran daya layin na "Ammi saidai kuma kash.. wai akashe take, yanata Kira "akashe jiyayi kamar yasa hannun "akai yayita kurma ihu, saboda tsananin takaici Kuma duk "abun nan dayake hannun shi yana "akan kofar, yana murdawa tareda jan kofar Wanda Kuma yanada tabbaci cewa kofar bazata taba buduwa ba har saida key.

domin haka kofar take bawani key dazaya budeta idan banataba, kuma yasan da haka saidai yanayin hakane ko"a hankalin *SAJEEDAH* yakwanta, saboda jin dayayi tana tafaman kuka "ahankali, Wanda hankalin ta yafara tashi nagani kofar batada ninyar budewa ballesu fita har sukai Baba asibiti.

Ga sanyin a c Wanda har yafara sa *SAJEEDAH* rawar sanyi narashin sabo, saidai shikam *SEERAJ* wani irin matsananci gume yakeyi Wanda kanagani shikasan natashin
Hankalin ne.

"Aikam idan ran *SEERAJ* yakai miliyon toh" yatashi ciki bacin rai yabugi kofar DA hannun shi tareda kaiwa kofar shuri da iyakacin karfin shi yace Why! Why!! Why!!! *ZUBEE* kikai Mani haka?????????....

Daidai lokacin *SAJEEDAH* tasaki wani matsananci kuka dama gansanyin a c don haka tuni jikinta yadauki rawa, mehade da tausayi halinda tabar "Baba "aciki, cikin tashin hankali ya karasa gurinta yace pls *JEEDAH* my kiyi hakuri kibar kukan "ai kofar zata bude zamuje mukai Baba "asibitin kinji KO?.. my *JEEDAH.*

Duk maganar nan Da yakeyi gabada "abirkice yake domin idan akwai, "abunda yatsana "arayuwar shi bai muce jin kukan *SAJEEDAH*, Kai tadaga "alamar "toh. da sauri yakoma bakin kofar yacigaba da bugawa kofar wadda take dankam KO" motsi batayi balle yasan ran zatabude.

Rayuwar shi "abace Wanda tunda yake baitaba jin bacin rai irin nayauba, yayinda "acikin ranshi yake tunani irin hukuncin Da zayayi wa *ZUBEE*, cikin takaici yafinciki marfin kofar saidai kash...

Cikin tsautsayi wani glass dayake hadeda marfin ya yankeshi sosai, saidai kuma tsabar zafinda *ZUCIYAR* shi takeyi besa yaji zafin yankarba, sai *SAJEEDAH* ce' ta hango jini yana sauka akan kafet din.

Jitayi gabanta yafadi Cikin tashin hankali ta isa gabanshi tareda Kama hannun shi, Wanda batamasan lokacin da tayi hakan ba, tace yah *SEERAJ* you hand is bleeding, tana fadin hakane tareda hura masa hannun domin jitake yankar kamar tamayar jikinta.

domin tasan yanajin ZAFI don haka itama takejin zafin har Cikin *ZUCIYAR* yayinda hawaye kezuba tamkar "anbude fanfo tace Sorry yah *SEERAJ* idanu yatsura mata jiyayi SON tayana Kara shigarsa gawani matsananci tausayin tadaya kebin jikinsa,

Dazafi Ko" yah *SEERAJ?..* "ahankali yagirgiza matakai alamar "a ah, Da saurin taciro dankwalin ta tayaga kasan cewar yafara taushi, Dan haka beyimata wahalar yagawa biyu ba takama hannun dajiniketa bulbulowa sai kace "anyanka kaza Cikin sauri tafara nannade mashi.

Kamshin man shampo datayi "amfanidash gurin wanke kai, Wanda Hajiya Asma'u tabata shine yabugi hancin *SEERAJ* "ahankali ya lumshe idanu domin yaji dadin kam shin har cikin *RANSHI,* Wanda yaji wani irin sanyi ya ratsa *ZUCIYAR* shi.

" Ahankali yabude lumsassun idanun shi tareda zuba su "akan lallausan bakin suman kanta, Wanda yake cike taka mashi da ribbon tadaure ya kurama ladanin sallanta, idanu wanda yai baki sosai kamar ta Shafa masa wani bakin abu agurin gawasu kanana-kananan suma dasuka kwanta luf-luf agefe-gefen fuskarta, girarta data kusan hadewa ga dimple dinta guda Wanda ko motsi tayida bakin ta saiya lotse, *SAJEEDAH* tanada kananan kyau Amma sauka kura mata idanu zaka gane hakan.

"Ahankali *SEERAJ* yakare mata kallo wanda baitabayin hakaba sai yau, wani irin sanyayyan "ajiyar *ZUCIYAR* yasaki shidai kam komai na *JEEDAH* yanason shi musamman natsuwarta, wani irin numfashi yafurzar Kasan cewar sundanyi kusa Da juna sosai don haka sai, tanaji saukar numfashi sa "akanta yayi dashi kuma yakeji saukara numfashi ta,'atafin hannun shi datake kokarin daurewa idanu shine ya sauka "akan kirjinta wanda sukayi kamar zasu fasa rigarta.

dasauri ya dauke kanshi "aransa yake fadin yanzu tundaga unguwar su *JEEDAH* ta taho haka babu hijab balle mayafi, wato kowama yagama gani ta kenan haka ko?..wani irin "abu yaji yadarsu a *ZUCIYAR* shi mezafi(damafa *SEERAJ* gurin *KISHI* badama).

"Aikam baisai lokacin da yasaki wani irin tsaki ba mtswwwww!, Wanda yasatayi saurin dagokai ta kalleshi, shidin ma itayake kallo sundan dauki lokaci suna kallon juna Sannan tasukuyar da kanta kasa dai-dai lokacin takarasa daure masa hannun.

Cikin danjin haushi yace tundaga Layin ku kika taho hakaba hijab ba mayafi meyasa haka?.. *JEEDAH*, tace daman daga gidansu besty na taho nan dasauri yace me kikajeyi gidan?..nan tafada mashi baice komai ba,Amma aranshi yace dama wayan nan mugayen mutanan yaushe zasu taimaka maku.

"Ahankali yace mata ina zuwa yanufi cikin daki,can saigashi yafito hannun shi dauke da hijab Cikin leda irin yadin'nan ne Dan' abba, ash Colon ne yamika mata tareda cewa kisa takarba tareda cewa toh" sannan taciro cikin leda tasa yayi mata kyau.

Bakin kofar yakoma yazauna tareda rufe idanu cikin matsanancin bacin rai toh" waiyaza yayine?..can yasaki ajiyar *ZUCIYA* tareda daukar wayar shida tuni yayi wuni dai kasa atunani shi batada wani sauran "amfani

Number *SAGEER* yakira tayi Kara daya biyu sai "ana uku yadaga,dagajin muryar shiyasan yanacan yana "aikata tsiyarda yasaba, "aikam daga bangaran *"SAGEER* yana cantare dawata yarinya da'alama ma tare suka kwana,

*_Wa'iyazubillah hattaradai Samari dayan'mata kuguji "aikata ZINA kusani duk_abunda mutun yayi_ za'ayimasa* *_Allah ka shirya mu shirin addinin musulumci UBANGIJI kasamufi karfin ZUCIYOYIN MU Ameen._*

Saida *SAGEER* yadai daita numfa shin sa sannan yace LARABAWAN Jordan saukar yaushe?.. Cikin takaici yace bansani S.A Nasko nace bansani bakajiko?.. waika wani irin mutun ne da bazakayi hakuri da yadda Allah yayika ba, saunawa zafada maka Karinga yin "azumi amma bakajiko?..

Daga can yace ka yimani Addu'a inaji "ajikina nakusa dainawa wani Uban tsaki yaja, mtswwwww tareda cewa dan'iska kada Allah yasaka daina kagani yadda karshen irinku yake komawa, yace "ainasan bazaka so nayi mugun karshen bako "abokina?..

*SEERAJ* yace dallah gafara mlm nikyaleni kajiko?..inakey part dina dana taba barinshi "agurinka?.. shuru *SAGEER* yayi nadan wani lokaci, Sannan yace gaskiya yanzu bansan "inda yake ba fa, dasauri yace don katashi kaduba Mani. yace "Ok *SAGEER* yadauki lokaci yana dubawa Sannan yaga key din, yace nagani toh" me za'ayidashi?...

Dasauri *SEERAJ* yace yauwa nagode pls kazo yanzu kabudeni,Amma kar ka biyo ta babban falo,ka biyo ta kofar baya pls kayi sauri kaji?.. *SAGEER* yace "Ok gani nan zuwa,Cikin abunda baifi minti talatin ba ya'iso ya kuma yi kamar yadda *SEERAJ* din yace.

Koda yashiga sai bai ganshiba don haka sai yanufi falo, wani irin matsanancin tsoro da Mamaki ne yakama *SAGEER* saka makon gani *SAJEEDAH* da sauri yace?...


Muje zuwa

A

๐Ÿ’˜Zuciyata ce๐Ÿ’˜

Tareda Alkalamin

๐Ÿ’˜Lufhat ce๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜

๐Ÿ’˜ZUCIYATA CE๐Ÿ’˜

_Based on true life Story_
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ›ซ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜

(Labarin Sarkakkiyar Soyayya)

2โƒฃ4โƒฃ

WRITTEN BY

๐Ÿ’˜ยฉAMEENA UMAR FARUQ๐Ÿ’˜
OR
๐Ÿ’˜MEENAT๐Ÿ’˜

________________________

*_ยฎPEN:WRITERS ASSOCIATION_*

*_PEN THE STRONGEST WEAPON_*
________________________

*_only the exquisite and Whizkid writers are opportune to be pen writers_*



โœ๐Ÿฝ


"Kul! kasake marinta lafiya me tayi maka haka?.. Cikin takaici hanashi sake marin ta da Ammi tayi yasauke hannun shi, Sannan ya watsamata harara tareda mika mata hannu yace bani key dakina.

Dagudu tanufi gurin Ammi tana kuka yayinda ta rungume tana cewa, yi shuru muje naji dalilin dayasa ya mareki" suka nufo gurinshi, shikam *SEERAJ* tuni yabaje "akan kushin yajingina bayan shi tareda daukan hannu wanshi duk biyu, yamayar baya ma'ana yayi filodasu idanun shi rufe yadauki kafa daya yadora akan dayaz yayinda yake kada fafafun "ahankali babu abunda yada meshi tamkar bashi yayi Marin ba.

Zama Ammi tayi kusada shi tareda zaunar da *ZUBEE* kusada ita, kallo daya Ammi tayi masa tafahimci RANSHI "abace yake, domin tunbai Kai haka ba take gane idan RANSHI yabaci,

Sai yarufe idanu yayi shuru duk lokacin data ganshi haka takanji badadi don haka, KO" yanzuma data ganshi haka sai taji ba dadi .

"Ahankali tace Ina daga kichin naji saukar Mari har biyu yanzu Kuma nafito, zaka Kara mata wani marin me tayi maka haka?...Cikin bacin rai yabude idanu tareda cewa my Ammi nafasa "auran *ZUBEE*.

Ba Ammi ba hatta da *ZUBEE* saida gabanta yafadi yayinda taji tsoro ya kamata, har batasan lokacin datadago Kai ta kalleshi ba yayinda shikuma ya watsa mata harara, Da saurin Ammi tace Kai! kasan "abunda kafada kuwa?... batare da ya kalleta ba yace "eh my Ammi nafasa aurenta domin itadin batada ce da rayuwata ba.

Cikin bacin rai tace "eh haka ne toh" saidai kuma idan kamanta da abunda kafada "anan gurin toh" niban manta ba domin kuwa cewa kayi tsakanin mu babu "alfarma saidai umarni KO?...batajira yabata "amsaba tacigaba dacewa, sai nikuma nabaka Umarni yayinda Kai Kuma ka tabbatar manida cewa zaka cikamani shi ko?..

Cikin sanyi murya yace "eh domin yaga "alamar ranta yafara baci, tace toh" yanzu Kuma sai "akaga bankai matsayin daza'acika Mani Umarnin bako?.. da sauri yace my Ammi nifa ba nufina kenan bada?.. tace toh" meye nufin ka nacewa kafasa auren *ZUBEE?..*

yace shin "amatsayin ta Na wacece zata zama mata agareni shin ba itace mace ta farko dazata fara kare Mani mutunci naba?...Ammi tace tabbas itace, yace toh" yaza'ayi Kuma "ace itace mace ta farkoda zata fara zubar manida mutunci a idon mutane saboda me toh?..Ammi tace kamar yayafa?

Cikin bacin rai yace my Ammi "Wata yarinya ce tazo gurina nataimaka naje nakai babanta "asibiti bayada lafiya, to" wai Kuma bayan ta nuna mata inda nake kawai saita rufemu 'adaki don iskanci Kuma shine tawuce da key din
toh" akan wani dalili zatayi Mani haka, mene ne nufinta Na rufemu "adaki "eh? jifa yadda tasa naji ciwo gurin bude kofar yanuna mata hannushi rai bace.

Da sauri Ammi takama hannushi tareda cewa subhanallahi "aini ba kulaba, ah lallai *ZUBEE* baki kyauta ba Sam wannan aiba dabi'ar kwarai bace, gashikinsa dan'uwanki yaji ciwo sannan kuma baki gudun mutumin yasamu matsala saboda rashin kai shi asibiti dawuri?..tace Ammi toh" ai yar...harara *SEERAJ* ya watsa mata me kunshe DA gargadin cewa muddun kika kuskura kikace' *JEEDAH ce* saina karyaki harda yimata misalin da hannu.

"Aikam dasauri tayi shuru yayinda Ammi tacigaba dacewa karki sake irin haka kinji ko?.. kai tadaga alamar toh" tace toh" bashi hakuri tace Sorry yah S P batareda ya "amsa ba yace dallah bani key na nidai, Ammi tace Ina key din?.. tace yana daki toh jeki dauko masa abun shi tace toh tareda mikewa tanufi daki.

tace sannu yace yauwa my Ammi sannan tace kai kuma Baban Jordan "aiba haka "akeyi ba, idan tayi maka laifi fada mun zakayi saina yimata fada bawai kace kafasa aurenta ba shin bakasa auren ku yanada yadaga cikin barina ba ummh?..aranshi yace my Ammi Zan cika maki burinki ba dan *ZUCIYATA* nasabo saidon farin cikin ki'.

"Afili kuma sai yayi murmushi yace ki kwantar da hankalin ki my Ammi burin ki zaya cika insha'Allahu, dama dai raina ne yabaci Da abunda tayi mani shiyasa nafadi haka. karki damu my Ammi badai aurena da *ZUBEE* shine farin cikin ki Da cikar burinkiba?..tace "eh Babana yace toh" ki kwantar Da hankalin ki za'ayishi Da izinin Allah.

tace Allah yasa Babana yace ameen tace toh" ya Baban yarinyar ka kaishi asibitin?.. yace "eh nakai shi harma anyi duk abunda yakamata sun ma bashi gado, tace Allah sarki toh" Allah yabashi lafiya yace Ameen. Sannan tace Don Allah kuma "a cigaba da taimakon mabukata yace insha'Allahu my Ammi,

"Anacikin haka saiga Abba yafito(kasan cewar yana gari) dasauri *SEERAJ* yasauka kasa tareda gaida Abba ya'amsa, dai-dai lokacin da yazauna kusada Ammi, murmushi tayi tareda cewa kafito?..yace hayaniyar kuce tafito dani meke faru wane?.. nan Ammi tafada masa "abunda yafaru, Abba yace "ah *ZUBEE* bata kyata ba.

saigata tadawo hannun ta dauke da key, gaida Abba tayi sannan tamika mashi key yakarba tareda hararar ta, Murmushi Abba yayi tareda yiwa *ZUBEE* fada, yamike yana cewa Abba my Ammi zanje nayi wanka, sukace toh" sai kafito yanufi sha shinsa, yayida ita kuma tamike tace Alh barina duba masu shirya breakfast yace toh" miko mani jarida can tabashi, sannan suka nufi kichin tana sakeyiwa *ZUBEE* fada kam abunda tayi baidace ba karta sake yin haka.

_*Yan'uwana biyayya ga iyaye abune mai mahimmanci "arayuwar mu, muyi musu biyayya koda ZUCIYAR MU bataso hakan zaya sa ZUCIYAR SU tayi FARI,har suji DADI susa mana ALBARKA wanda ALBARKAR takine shi "arayuwarmu ALLAH kabamu ikonyiwa iyayanmu biyayya Ameen.*_

Bayan yafito wanka saita shirya cikin wani yadi sky blue me Kyan gaske, wanda kallo daya zakai mashi kagane tsadadde ne yafesa turaruka masu sanyin kamshi Sannan yadauki key mota tareda wayoyinsa sannan yafito.

Direct kinchi yanufa gurin Ammi tana ganin shi tace' har kafito?... yace "eh my Ammi Zan fita, tace "ah bazaka tsana kayi breakfast ba?...gashi "an kusa gamawa yauma dai su kulu sun makara guri shirya breakfast din, yace "aiba dadewa zanyi ba zandawo tace toh" sai kadawo yace toh"tareda fita.

๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
Da Sallama yashiga gidan *SAJEEDAH* ta amsa tareda mikewa daga zaunen datake kasan cewar tashin shi takeji ta, sanyetakedadayadagacikin abayar dayasaimata tun wancan lokacin, saidai wannan jace sabani waccan baka dama mayafin babban don haka shiga yafa, kallon tayake fuskarta fayau ba kwalliya Amma dai saiyaga tayi mashi kyau.

Murmushi tayi tareda dukar dakai kasa wani irin kunya taji yakamata saka makon kallon dayake yimata, Cikin sanyi murya tace sannu da dawowa *yah SEERAJ* yace yauwa *my JEEDAH* kinyi kyau sosai barina yi maki hoto, dasauri tarufe fuska tana dariya tace kai *yah SEERAJ* ahaka?..

yace yesss let me snaps u my dear pls remove u hands, dariya tayi har beauty point dinta yalotsa "ahankali tacire hannun saidai baduka ba hakan sai yabada style, dasauri ya dauketa tareda cewa *my JEEDAH* "aikam tayi kyau sosai nan da nanya'ajiye hoton "agaban wayar, sannan yace kin shirya kenan mutafi?.. tace "eh OK muje tace toh"
tareda dukawa zata dauki buhun baggo datasa kayan da zasu bukata, sai yayi saurin dauka dasauri tace Lah *yah SEERAJ* kaida hannun ka yake ciwo kawo na dauka, yace lah *my JEEDAH* barina dauka dawannan hannun yafadi yana kwaikwayon maganar ta me sanyi.

Dariya tayi tareda rufe fuska tace kai *yah SEERAJ* shima dariyar yayi tareda fara tafiya yac' Oya muje tace toh" tareda bin bayan shi, yace *my JEEDAH* naga book da school uniform dasu Zaki asibiti?.. tace "eh gobe zamu fara exam, shine zanyi karatu kuma ni gaskiya tsoro nakeji bazan iyakwana gida nikadai ba dariya yi dai-dai lokacin da yabude mata mota. "ahankali yake yin tuki da hannu daya kasan cewar daya hannun daya yanke yanayi masa ciwo sosai KO" kwana zayayi saiyayi dabara.

Shuru tsakanin su bawanda yacekomai can sai yace' *my JEEDAH* wai tun yaushe ne baba bayada lafiya?.. tace hmm yanzu fa yakai wata uku, yace Kai! *my JEEDAH* har _three month_ baba bayada lafiya amma ban saniba, gaskiya nidai baki kyauta mani ba. Cikin sanyi murya tace kayi hakuri *yah SEERAJ* kasan duk abunda Allah ya shirya zaya faru toh" faba babu maka wa sai yafaru.

Yace hakane toh"Allah yabawa baba lafiya tace ameen dai-dai lokacin dayake shiga ciki asibitin,yauwa *yah SEERAJ* me "doctor yace yanada mun "baba? yana kokarin yi parking yace mata befadaba tukun saisunyi test din jininsa da fitsari, Ahankali tace toh' ni "abun tsoro yake bani,

yace tsoro kuma? ke daza kiringa yin Addu'a toh" amma meyasa kike jin tsoro?... tace saboda gani nakeyi kamar ciwon koda kedamun shi Kuma kaga shi idan tayi tsananisa kaji "ance sai anyima Mutum dashen, shiyasa nakejintsoro shikam *SEERAJ* gaban shine yafadi yayinda yasaki baki yanakallon *SAJEEDAH* Cikin mamaki.

Dasauri yace ke waya fada maki?..tace a school "a fada mana alamonin masu ciwon koda Kuma kaga duk alamomin ciwon Baba, irin na masu ciwon koda ne kaga yawan fitsari Kuma Da jini sannan yawan barci, sunada yawafa alamomin Kuma duk

Please Login or Register in order to submit comment