Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register



Bismillahirahmanirrahim

Writing by
Zaynab Bawa (z33iiyyb3rw3r)

Page 5

*
Baki tasake tana kallonsa jitayi yace
Rufe bakin,
Saurin rufe bakin tayi sannan takauda kai gefe,
Tareda jan dan siririn tsaki ahankali tafara magana damme dakabugeni a school,
Kuma kabini abaya haryanda nazo kuma kasake bibiyata
Tsaki takara ja
Gani tayi yazuba mata idoh kaman wani wanda yakeson gano wani abu atattare da itah, kara tamke rai tayi cikin tsafin murya tace mekuma kake kallo,
Wani abu nakeson ganowa shin wae kece kuwa ta dazun nan kallon gefe da gefenta yayi wadda hakan yasata itama bin yadda ya kalla da kallo

Kai bake bace,
rike havansa yayi cikin zolaya yace oh namanta ashe yanxu kinyi makeup ne wani kololon bakin cikine yatokareta,
Wato nufinsa dazu batayi kyau ba kome,
Gyaran murya yayi tareda cewa idan kagama shirmenka saikaban hanya nawuce,
Sosa kyeyansa yahauyi, yayah bafah shirme nakayi ba koma meye nidai bani hanya *hanna* wanda kunya tabi tacikata jin kiran mijin anty da yaya Wato shine kaninnasa Wato ba ita yabiyo ba oh sh*t tace tareda dan dukan goshinta da tafin hannunta, meyasa na aikata haka wayyo yanxu shikenan zaidauka tunaninsa nakeyi tafada acikin ranta,

Saurin juyawa tayi tashige daki, murmushi yayi sannan yafurta,
She's amazing, ahankali yadda yah mahmood bazaijiyoshiba, abinda bai saniba shine tun tsayuwarsu yake kare musu kallo tass, daya Bayan daya. idankagama saikawuce mushiga cewar yah mahmood, Sosa kansa yayi sannan yashiga da sallama, antyne tafuto cikin fara'a tanamasa barka, yaude naga najeeb, dariya yayi sannan yadan waiga ko zaiga ta inda zata bullo amma shiru, yaya mahmood dake zaune gefensa yagane wanda yake nema dafashi yayi cikin sauri yajuyo daga masa gira yayi, mekake nema, bbu kawae inaduba yanayin gidanne ow kawae ya mahmood yace danyaga rainin hankalin najeeb yawuce yanda yake tsammani,

Waye najeeb??????
NAJEEB
najeeb kanin mijin antyne wanda yakasance shine autansu,
Su bakwae ne awajan mahaifinsu , iyayensu asalin yan bauchi ne wanda yanxu hakama anan suke zama babansu yarike mukamai da yawa a high court,
Sanda yakai matsayin Grand cady sannan yayi ritaya, matarshi tafarko itace hadiza, hadiza irin mutanan ne masu masifa,
Amma kuma tanada kirki sosai dasanin darajar dan adam, yaranta hudu da alhaji masa'ud babbar yarsu itace ikilma wanda yanxu tanada aure da yara shida sai aminu wanda shima yaransa hudu dakuma halima wacce ke aure acikin garin bauchi da yara shida itama, awajan haihuwar salima ne Allah yamata rasuwa, tarasu tabar yarta kyakkyawa maikama da ita, alhaji mas'ud yayi kuka narashin, mata mai nagarta, daga baya yafawwalawa Allah komai, yarungumi yayansa hudu databari hannu bibiyu, yaki jinin kallonsu cikin bacin rai,

Ana haka Allah yakawo wani wani justice, daga maiduguri, asalunsu shuwane dayarnsa mata da maza, lura yayida alhaji mas'ud baitaba Gani yayi maganar matarsa ba, adah yayi tunani koh danbasu saba sosai bane Amma yanxu abin yasha bambam dan wata rana yakirashi akan yazo gida yasameshi dan akwae wasu takardunda yakeso yazo yakarba yaje office yayi aiki akansu, sanda yakara kusan, hour biyu akan yadda ya umurceshi yazo, Bayan ya isoneh yake tambayrsa mayya zaunar dashi nan yake shaida masa cewa yatsaya shirya yaransane tambayarsa yayi ina matarsa nan yake shaida masa Ai Allah yamata rasuwa, hakuri yabashi sannan yace masa zama bbu mata banasa bane, yanemi wata ya aura domin yaransa, shaida masa yayi yanatsoron ya auro wanda zata musgunawa marayun yayansa neh shiyasa don yanxu samin mata tagari yayi karanci.

Shiru justice yayi wani tunani sannan yayi gyaran murya yace, to Ai bakazauna hakaba, gayata nan nabaka dan inada tabbacin baxata musgunawa yarankaba, amma kaje kayi tunani kafin kayanke hukunci, shiru yayi sannan yamasa godiya yatafi,
Bayan kwana biyu ya yanke hukuncin amincewa da auran, amma kuma akwae fargaba aransa don baisan wani irinzama dasuyiba Bayan haka gata dangin shuwa kuma masuji da dukiya da mulki amma kuma bazai iya duban fuskan justice yace bayason auran yarsaba, zuwa yayi yashaida masa ya amince, wanda tuntuni ita ba'asamu matsala tawajan tava danta kasance mai biyayya ga iyayenta, dangin mahaifiyarta ne suka fara magana akan za'adauki karamar yarinya akaita bauta wajan yara, dan wannan auren bautane, toshe kunnuwanta tayi dan ita tansan mijinta kuma tana respecting duk wani wish nasa. cikin kwanciyar hankali yaturo magabatansa akayanke rana wanda suma danginsa bakarin farin ciki sukayiba ganin shidakansa yace sujemasa tambaya, dansunyi akan yayi aure harsun gaji, andaura aure ba'ayi wani shagaliba walima kawae akayi akakai tadakinta, dafarko yayi zaton samun matsala daga wajanta amma hakan bata faruba dan tana kula da yaransa kamar ita ta haifesu, dalilin dayasa yadauko salima daga gun mahaifiyarsa kenan yadamka mata

ba'a dade dayin aurenba ciki ya bullo tahaifi yarta fara sol mekamada mahaifinta amma hasken mamanta, itada kanta tabukaci asawa yarta hadiza bakaramin dadi yajiba, Bayan tayaye halima wacce suke kira da maamaa ta haifi danta mahmood shima kammannin babansa sak sanda tadau shekaru kafinnan ta haifi najeeb wanda shikuma bbu abinda yabaro namahaifiyarsu sai ma ince yaso yafita kyau, ammashi kalan babansa yadauko dan bakine shi daganan bata sake haihuwa ba nan duk gidan suka daukiso suka daurawa najeeb tundaga kan iyayen har yayun bawanda yakeson laipyn autansu,

Najeeb dan kimanin shekaru ashirin da shida kykyawane baki yanada tsayi amma ba sosaiba yayi karatunshi tundaga secoundry har zuwa doctarin deegree dinshi akasar waje wanda yanxu dawowarsa kenan daga can kasar yayi gam da katar da zinariyarshi😍😍

Back to labari tashi anty tayi tanufii dining sannan tamusu Iso karasawa sukayi dukkansu kowa yakama kujera yazauna kwala mata kira anty tayi kan tafuto itada amal suci abinci sannan tadauko wa uncle dinsu yaganshi,

Futowa tayi daukeda bashir akafadanta sannan dayan hannun yana rikeda amal zuba mata idanuwa yayi tundaga nesa yakasa daukewa jiyayi an dafashi........

Ur's
Z33yyb3rw3r

BIBIYATA AKEYI

Bismillahirahmanirrahim

Writing by
Zaynab Bawa (z33iiyyb3rw3r)

Page 6

Sorry for the last Page there are some several mistakes wllhy bansamu nagyaraba.

*
Jiyayi andafashi saurin juyowa yayi, nan take kuma kunya ta lullubeshi, ya mahmood ya kamashi yana tsare masa kanwar mata da idoh,

Karasowa tayi tajama amal kujera tazauna sannan itama tazauna, dama kujeran dining din mai kujeru shidane, anty nazaune kusada yah mahood, najeeb kuma yana dayan gefen ya mahmood itakuma tasa amal atsakiyanta da najeeb,

Anty tatashi tafara saving dinsu tana bude food flask din wani kamshi yadaki hancinsu lumshe ido najeeb yayi sannan yabudesu, saukesu yayi akan *hanna* wadda ita batasanma yanayiba, dan tunda ta iso tadauke idanta daga kansa,
Anty ne data zubawa amal abinci saurin rike hannun anty anty tayi, owh owh nibake dakiyi saving dinaba ni ummah ne data zubamin, ohoh kyaji dashi keda ummankin,

Juyawa tayi wajan najeeb daniyar zuba masa saurin langabar da kansa gefe yayi sannan yace owh owh nibake daki zubamin ba ummane data zubamin yakwaikwayi maganan amal amma kuma harcikin ransa yafiso tazuba masa, wata harara tawatsa masa kamar idanunta dasu fadi kasa, idoh daya ya kanne mata tare dayin murmushin dashikadae yasan ma'anarsa,

Juyawa anty tayi ta kalleta, maza tashi kizuba muku abinci, batareda tayi wani tunani ba dan Azatonta koh yabi maganar amal ne kawae, shikuwa yaya mahmood yagama gane yanda yadosa,
Idan haka tafaru bakaramin farinciki zaiyiba dan yafi kowa yawa kaninsa addu'ar samun mace tagaari, fatanshi kawae Allah yasa bata tsayarda miji ba,

Kunkuni tatashi tanayi ciki ciki tamikawa anty bashir, no kawoshi haka nan muryar najeeb takatseta, yitayi kamar bataji shiba takara mikawa anty yaron wae bakiji mai akafada miki bane, kibashi yaron turo baki tayi, sannan tanufeshi ta dangwara masa yaron, akan cinyarsa, anty baki kawae tasake tana kallon ikon Allah,
Idan kingama shirmenda kikeyi saiki zuba muku abinci, kara turo dan bakinta tayi,
Wani irin kyau yaga tamasa tashi daya tsikar jikinsa tazuba, gashinda ke kwance ahannayensa suka tashi, Jiyayi kaman yaje yayi kissing din bakinta dan yanda take turoshi bakaramin kyau tayiba, saida shi Allah yayishi bameson taba matar daba muharramarsa bace, with time yafada acikin ransa dan duk randa Allah ya mallaka masa ita amatsayin mata wannan dan karamin bakinnata daga ranan bazai kara yin tsauri mawaniva,

Zuba masa abincinda tafarayi ne yadawo dashi daga tunanin daya wulla, zuba masa tagamayi sannan takoma kan amal itama tazuba nata tazauna,

===============

Inah mukabar masu *bibiyan* *hanna* ne tun fitarta daga gida suka fara binta har tashiga lectures tafito, fitarta daga lecture zuwa shop duk lokacin suna bib *bibiyarta* Bayan takarasa shop ne daya daga cikinsu fitsari ya mugun kamashi, dama kunsan ance tsautsayi baya wuce ranarsa domin oppotunity come at onces just like mistake come at onces either dakadauki tsaawon shekaru kana kare abu but na lokaci guda kayi sake da wannan kariyar wannan mistake din da za'asamu ayan secound itx really hard to make it up,

Fitsarine sosai yarikeshi wanda bazai iya jiraba gawajen wajen wucewar jama'a balle yayi awajan, yabukaci dayan dayakai shi yayi aiba wata damuwa tunda akwae mutane ashop tun har dasu dawo kafin asallameta,

Rakashi yayi kafin sudawo abinda suke gudu ya auku wandasu basuda masaniya akan faruwar hakanma domin alokacin najeeb yabige hanna haryaji zuciyarsa takamu da sanda, itama hakanne tafaru awajanta luv at first side,

Dawowarsu yayi daidai da fitowarta daga shop din, nan sukaci gaba da binta, wanda saken dasukayi nayan wannan minute din yana daidai darasa rayuwarsu,

Harzuwa lokacin da tajuya me keke napep zuwa gidan antynta harnan suna biye da ita sanda tazo gidanne ta shiga sukuma sukayi parking car dinsu, sunajiran fitanta,

Koda lokacin da najeeb yashigo tareda yaya mahmood yazo wanda yaje hargida yadaukeshi kuma sunriga da sunsan motar yaya mahmood kuma sunsan matsayinsa a wajanta so basu damu daduba motarshi ba koda wani acikinta dake motan nada bakin tinted,

Haka yayita kallon ta harsuka karasa cin abuncin, anty amma kin iya abinci wallahi nima Allah ya bani wacce ta iya girki yafadi haka tareda satan kallanta ta kasan idoh, to Ai baninayi ba cikin zumudi yace wayayi gata Zaune kusa dakai, hmmm yaja gauron numfashi anty amma mijinta yayi sa'a sainaji dama nine wannan mai sa'ar,

Siririn tsaki taja kaifa kafara wuce gona da iri ha'ah ta murguda masa baki, wow😍 gaskiya fushi yana miki kyau kamar karkiyi dariya,hakan dayafada ne yasata murmusawa wow to Ai kuma dariyan yafi miki kyau kainama kasa tantancewa

Ahaka yayita jan ta da kalamai masu dadin sauraro harta bashi phone number dinta,
Saida tayi la'asar kafin tafara shirin tafiya,
Bayanda bayiba akan yasauketa agidah amma fir taki,
Haka sukayi sallama da anty kafin tafuto da niyyar wucewa gida batayi mamakin ganin motarsu,
Sanda tayi dan tafiya kafin tasamu abin hawa gida tawuce,

DUBAI

Major general MG Abudullahi ne Zaune a office gabaki daya tunda karfe 11:30 tabuga a agogon nigeria wadda yayi daidai da 2:30 a agogon akasar dubai wani irin faduwa gabansa keyi kuma yarasa dalili tunyana daurewa avun har zazzabi yake shirin sa masa ba shiri yabaro office yayi gida amma duk da haka yakasa samun nutsuwa kamar wanda wani mummunan lamari ke shirin faruwa dashi,
Captain ahmad yafada cikin dagun murya cikin tsafin nama wani dan saurayi wanda bazaifi kimanin shekaru 30 ba ya isoh wajen cikin girmamawa yace Gani yallabai yisauri kakiramin Captain bala jiki harayana bari yaciro waya a aljihunsa dan yasan halin ogannasa bayasan wasa barinma daya fahimci ransa yana bace, ringing daya akadauki wZ33iiyyb3rw3rikawa MG wayan yayi ya karba tareda karawa a kunnensa.....

To be continue



Ur's
Z33yyb3rw3r

BIBIYATA AKEYI

Bismillahirahmanirrahim

Writting by
Zaynab Bawa (Z33iiyyb3rw3r)

_This Page is sincrely dedicated to u My dear *Ayeshert* *Aly* *garkuwa* u r such a wonderfull person i want u to know that u r _amazing_ so _much_ _love u_

Page 7

*_

Saurin karban wayan yayi tareda karawa a kunnensa, yafara, magana duk da bawae jin maiyake cewa nayiba amma nafahinci yanayin sa yasauya dan damuwar da take fustarsa ta sassauta, duk da dama bawae yakasance mutum mai fara'a bane amma akan iya gane lokacin dayake cikin bacin rai,

Sauke wayan yayi daga kunnensa tare da sauke wata nauyayyar ajiyan *zuciya*
Bawae dan yagama yadda da abinda Captain bala yace bane, amma hankalinsa yadan kwanta, domin yasamu sassauci daga yanda zuciyar sa ke bugawa,

Mikewa yayi akujerar dayake Zaune, ya lumshe idanuwansa, abubuwa kala kala yake sakawa acikin *zuciyarsa*

================
Bata isah gida ba sai karfe biyar na yamma, tura dan karamin kofar dake jikin gate din gidansu tayi tashiga da sallama duk da tasan bakowane awajan dazai amsaba amma yanada kyau shiga gida da sallama,

Cikin gidan tawuce kaitsaye, tasamu ammah zaune tana yanke, farcen kafanta, sannu da gida ammah tafada koda batasa ran amsawaba, amma dabi'ar tane koh bazata amsaba saita gaishe ta,

Idontane yakai kan kayan dake jikinta, ke zonan tayi saurin kwala mata kira, yitayi kamar batajiba dan idan zaka shekara kana ce mata ke bazata amsaba,

Sanin halinta ne yasa tayi saurin cewa *hanna* badake nakeyiba juyowa tayi au banji lokacin bane, Wani kululun bakin ciki ne yatokareta, aranta tanacewa yarinya batasan komai ba sai rashin kunya, afili kuma tace A'inah kikasamu wannan kayan jikinki ?????

Kallon gefe da gefenta tayi sannan tadago tace wanne???

ungo naki wannan najikinki mana to aini banga wani kaya ajikina ba nawane, oh namanta ashe ance idan mutum yafara tsufa yanada saurin mantuwa,

Tana fadin haka tayi saurin juyawa, dantasan abinda ta aikata don kokadan ammah batasan tsufa, Saurin shigewa sashin mama tayi tabar Ammah nata surfa ashar,

Shigewa tayi tana dariya afalo tatararda mama Zaune tana kollon wisal hausa, kewani irin shashancine haka zaki shigowa mutane daki babu sallama kamar wata tababbiya, turo vakinta tayi mana nayi sallama fa bakiji bane, kyaji dashi dai tafada tareda juyawa taci gaba da kallonta,

Wucewa tajeyi mama tayi saurin tareda keh A'inah kikasamu wannan kayan kuma, mama gidan anty na'ilah fah naje, shine kika samata kaya kaimama me shiga tsakanin yaya da kanwa fa zaiji kunya.

Uhm kawae tace tacigaba da kallanta, Bayan mangaruba kamar yadda suka saba kowa nacikin gida yana Zaune, antadi saikuma yan habaice habaicen daba'a rasasu acikin gidan, itade hankalinta gabaki daya baya wajensu yanakan phone dinta,

Jira takeyi kawae kiran najeeb yashigo, amma shiru saida
Har tayi shirin kwanciya tagama cire rai da kiransa, dan harta kwanta bacci, taji wayanta yafara ringing, koda taga number ne tarigada tasan waye yasa batayi Gigin daukaba sanda ta katse,

Tajira koda'a sake kira amma shiru harataji haushin kanta naja masa aji datatsaya yi gashi yanxu yakikira, Wani irin haushin kanta takeji nakin daukan wayan

Kusan 30 minute yakara kafin yasake kiranta, mai halidai bayafasa halinsa dan sai wayanna dab da tsinkewa kafin tadaga, shiru tayi takiyin magana, sallama yamata daga nasa wajan, amsawa tayi adakile,

Kingane waye A'a tabashi amsa shiru yayi danransa yadan sosu datace masa A'a kuma yasan bawai bata gane waye bane saitsan tsan rainin wayo,

Shitunda yakema bai taba kiran mace taki dauka ba saiyau, najeeb neh, oh yakake, lafiya ya mama da baba, kowa kalau, yayikyau amma meyasa kikace baki ganeba, hmm tace kawai tana masa magana cikeda rashin sabo,

Haka yayita jan ta dahira mai dadi hartadan sake dashi sai wajen 11:00 sukayi sallama dan bacci ne tab a idonta,

Sanda ya tabbatar da, yadasa mata wata irin soyayyarsa a zuciyarta kafin yabarta, bacci ne mai dadi yadauketa, cike da farin ciki da annashuwa,

Zaune take abakin wani ruwa awani hadadden beach gawasu tsuntsaye masu kyan gaske sunata zagaya wajan najeeb ne Zaune agefenta, inibi yadauka dake cikin wani faranti agaban Su cike yakeh kayan marmari,

Kana kallonsu kasan suna cikin wani irin yanayi na nishadi, Da farin ciki domin yadda fuskokinsu ke dauke da murmushi mai tsadan gaske,

Dauko inibin yayi yakaimata bakinta, lumshe idoh tayi hadeda bude bakinta, shirun dataji ne yasata bude idoh,

Sojojine zagaye da wajan da suke Zaune ga najeeb ahannun wani mutum wanda kana kallonsa daka tabbatar da balarabe ne sak

Yasawa najeeb bindiga akansa, magana yajuyo yanayi yana kallanta,
*Hanna* meyasa bayajin magana nahanaki meyasa kikeson sa rayuwar Su cikin halaka,meyasa kikeson saka zuciya na cikin kunci zankasheshi kuma zankashe duk wanda ya kusanceki da sunan so,

Ke tawace nikadai dan nafi kowa sanki, yana gama fadin haka ya sa kan bindigan akahon zuciyar najeeb sannan yadana kunamar bindigan wani irin raza nannan ihu tasake,,,,,,,,,,,,,

To be continue

Ur's
Z33iiyyb3rw3r

BIBIYATA AKEYI

Bismillahirahmanirrahim

Writing by
Zaynab Bawa (z33iiyyb3rw3r)

_This page is dedicated to _you_ *_hajja_* *_ceh_*

Plx kuyi hakuri wannan page din bayawa

Page 8

*
Wani irin raza.. Nannen ihu tasake... Tashi daya kuma tafarka daga wannan bacci mai mummunan mafarki

Ihun datayi ne yasa mama saurin farkawa daga bacci
Saurin riketa tayi ita,,,, kuma sai fisge fisge takeyi tana ihu,,,,,,,, na shiga uku sunkasheshi wayyo Allah na dama nasan baxasu bari in aureshi ba wallahi sun kashe shi,,,,,,,, duk maganan datakeyi cikin kuka take yinsa, Addu'a mama taringa tofa mata duk wanda tazo bakinta,,,,,,,,,
Dan itama gabaki daya tarude,,,,,,,,,,,,.
Sanda tadauki kusan awa biyu awannan yanayin,,,,,,,,, kafin tasamu tadan lafah,,,,,,,,, aranan baccin da batayi ba kenan domin gani take kamar wayannan mutane suna iya dawowa,,

Daga ita har mama babu wanda yarintsa,,,,,,,,,,,,,,,,,
sallah suka kwana sunayi suna rokon Allah,,,,,,,,,, yakaresu daga sharrin makiya,,,,,,,,,, dakuma sharrin mutum da aljan,,,,,,,,,,,,,,,,,

Koda asuba tayi,,,,,,, tada ikama kawae sukayi suka gabatar da sallan asuba,,,,,,,,,,,, bawanda yayi gigin komawa bacci aciknsu,,,,,,,, azkar sukaci gaba dayi har rana tafuto,,,,,,,,,,, sai lokacin hankalinta yakwanta da dad`a tabbatarwa da mafarki ne ba gaskiya ba,,,,,,,,,,,,,,,,

Bayan gari ya waye ne,,,,,, tashiga dakin babansu da gaidashi,,,,,,,, ganin idanuwanta a kumbure ne yasa shi zaida ita,,,,,,,,,,,,,,,, *hanna* yakira sunanta cikin yanayi nason gano wani abu dake tattare da ita,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,, amsawa tayi sannan yace dawo nan kizauna,,,,,,,,,, zama tayi cikin nutsuwa
Meya faru haka naga idanuwanki sun kumbura gabaki daya,,,,,,,
Shiru tayi nayan wasu sakonni,,,,,,, danbata da amsar tambayarsa,,,,,,,,,, shirun datayine yasa shi fara ganewa akwae abinda ke damunta,,,,,,,,,,

*Hanna* badake nake magana ba,,,,,,,,,,, babu komai da baba jiya bansamu bacci bane nayi karatun test, kuma gashi yace yadaga zuwa next week,

Tafadi hakanne domin kare kanta,, daga tambayoyi,,,,,,, kuma tasan tabbas idan yaga batayi shirin tafiya makaranta ba sayya tuhumeta,,,,,,,,,, kuma yau ayanda take batajin zata iya zuwa, makaranta,,,,,,,, toh adai ringa hutawa Dan irin haka karatun sayya ki zama koh ,,,,,,,,,,,,

Toh kawae tace sannan ta tashi tafuta daki tawuce,,,,,,, takwanta,,,,
Tayi tsurfi cikin tunani batasan mama tadade akanta tana kallon taba,,,,,,,,,,,,,,,,,

Taba ta tayi cikin firgici ta tashi tazauna,,,,,,,,,,,, gefe mama tasamu ta zauna itama,,,,,,,,,, *Hanna* inason intambayeki kuma banason kimin karya koki boyemin wani abu daga cikin abinda kika sani,,,,,,,,,,,,,,,,
Dan na gaji da kallon ki kullum cikin damuwa na dade dasanin akwae abinda yake damunki kina boyemin,,,,,,, amma nayi miki Shiru toyau gaskiya nakeson kifada mun,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,

Meyake damunkii????? Wannan dakike mafarki an kasheshi wayeshi????? Kuma waye kike ambada kan dama kinsan bazai barshiba????? Ajere da zuba mata wannan tambayoyin

Shiru tayi na yan wasu dakikae kafin tafara bawa mama labarin tun lokacin da tasamu Ammah da kawarta suna tadi zuwa jiya haduwar su da najeeeb,,,,,,,,,,,,,,,

Abu daya taboye mata shine wayannan mutane dasuke bibiyar ta Dan,,,,,, idan tafadawa mama batasan wani irin hali zata shiga ba,,,,,,,,,,,,,,,,

Yanxu ma kenan kuka takeyi hadda shassheka,,,,,, balle taji labarin wannan mutanen damuwa saita yi mata yawa,,,,,,,,,,,,,,,,,

Kuka takeyi tana meyasa,,,,,,,,, Hanna meyasa baki fadamun tunda wuri ba wannan ba karamar matsala bace,,,,,,,,,,,,, dole mudage da Addu'a kar Allah yabasu galaba akanmu,,,,,,,,,,,,,,,, bansan me muka tare musu ba wallahi ta Allah batasu ba kuma in sha Allahu saikin auri mijinda zai soki ya kaunaceki idanma sunaso babanku yagaji Z33yyb3rw3ri wanda zai wulakantaki ne to ta Allah batasu ba kuma wallahi damu tsuba nidasu,,,,,,,,,,,,, sai na yakesu da kafin Addu'a,,,,,,,,,,,,,

Share hawayenta tayi,,,,,,,,,,,,,, sannan tacewa *Hanna* da Allah share hawayenki wallahi Allah baxan bari suci galababa tana gama fadin haka tatashi tafuce,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,, wani Kuka ne mai karfi ya kara kubuce mata ci gaba tayi da rerashi kaman wanda dama an aikota duniya Dan kukane kawae,,,,,,,,,,,,,,,

Sallamar wanda tajine yasata saurin hadiye kukanta tareda,,,,,,,,,,,,,,

To be continue

Ur's
z33iiyyb3rw3r
BIBIYATA AKEYI

Bismillahirahmanirrahim

Writing by
Zaynab Bawa (z33iiyyb3rw3r)



Page 9

*
Sallamar Wanda tajine yasata saurin hadiye kukanta,,,,,,,, saurin
goge hawayanta tayi,,,,,,,,,,,,,, damin bataso afahimci akwae damuwa atattare da ita,,,,,,

Fita tayi daga dakin aguje taje tayi hugging dinta,,,,,,,,,, duk wani damuwa dake tattare da ita jitayi kaman ba wani damuwa bane,,,,,,,,,,, Don Baza ta iyah misalta irin farincikin da take cikiba,,,,,,,,,,,,,,,, bawae Kuma Dan Bata cikin damuwar ba,,,,,,,,,,,,,,,,, saidan farincikin ya danne damuwar da take ciki,,,,,,,,, ,,

Juyowa tayi itama cikin farin ciki takara hugging dinta,,,,,,,,,,,,,,,,, Koda ba'a fada bah kallo daya zakayi musu ka gwano farin cikin dake tattare dasu,,,,,,,,,,,,,

Gyaran muryan baba ne yadawo dasu cikin hankulansu,,,,,,,,,,,,
To yaran mama sun hadu Sai wani farinciki da annashuwa kukeyi koh daga zuwanki Kinga yar uwarki,,,,,,,, koh azo agaishe da baba gashi Yana shirin Fita office,,,,,, mama ce ta amshe maganan da cewa au danma bakaji meh jiya tacemun ba,,,,,,,,,,,,
Wai meshiga tsakanin Yaya da kanwa zaiji Kunya,,,,,,,,, Dariya duka suka saka daga baban Har anty hajja da zuwanta kenan,,,,,,,,,,,,,,,,, toh nidai nafita sai nadawo tukunna ma gaisa cewar baba sannan yasakai yafice,,,,,,,,,,,,

Daki suka nufa dukansu,,,,,,,,,,,,,, sai farin ciki sukeyi
Sai da suka shiga ne mama tarufe ta da fada,,,,,,,, kancewa menene dalilinta nakin fada musu tana hanya aiko ba komai ma tayaki da addu'a wannan tafiya Bata wasa ba ga Yara aiko abincii matana dar Miki,,,,,,,,,,,,, mama aitoh bebaci bah tunda Ga wannan beb din kawae tashiga kitchen tadafa mana,,,,,,,,,,,,,,,,,

Cikin farin ciki *Hanna* tatashi da niyar zuwa ta daura musu abinci ,,,,,,,,,,,,,, kitchen da nufa tafara girka musu abinci cikin dan kankanin lokaci,,,,,,,,,,,,,, tagama hada musu breakfast,,,,,,,,, domin itama bawae tayi Karin kumallon bane,,,,,,,,,,,

Gama kimtsa komai tayi sannan takai musu falo ta ajiye musu komai,,,,,,,,,,,,,
Sannan tadawo tazauna,,,,,,,,,,, jawo yarinyar anty hajja tayi tazaunar da ita bisa Kan cinyarta,,,,,,,, duk da bawani sabawa sukayi da yaran anty hajja sosai ba sakamokon nisan wurin rayuwa dasukee,,,,,,,,, Amma tasan dasu ebe Mata wata kyawar,,,,,,,,,,,, Dan anty hajja takan Dan dade kafin takoma,,,,,,,,

Zama sukayi sukaci abinci sukayi nakk Kamar babu wata damuwa atattare da dasu,,,,,,,,,,,,,,,
Sai Bayan sungamacin abinci ne anti take tambayan cewa koh suna tattare dawata damuwa née????? Mama ne tafara Bata labarin abinda yake faruwa Dan kokadan bataji zata iya boyewa yarta damuwar taba,,,,,,,,,,,,,,,,

Tashi *hanna* tayi tashige Daki tabar mama tana Bawa Yaya hajja labarin,,,,,,,,,,,,,,

Wajan wayarta tanufa dake Kan bed side drawer,,,,,,,,,,,,,,,
Daukan Wayan tayi missed calls tagani bbu adadi wadda duk yawancinsu na Amira neh sai 3 miss calls na najeeb,,,,,,,

Zama tayi agefen Gadon tana tunani shin Kota kirashi ne kokuma tafasa,,,,,,,, Bata Gama yanke shawara ba,,,,,,,,,,, taji muryan antyy tana kwala Mata Kira,,,,,,,,,,,,

Tashi tayi cikin nutsuwa ta nufi falo,,,,,,,,,, wurin anty tanufa tazauna,,,,,,,,,,, hanunta anty tarike sannan tafara magana cikin murya medauke da tashin hankali acikinta,,,,,,,,,,

*Hanna* meyasa Daki boye mana wannan lamari kinsan wannan ba karamar matsala bane,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,
Shin kina yawan mafarki na tsoro

Please Login or Register in order to submit comment