Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shigo, amsa musu akayi, suka tsaya, curko-curko, "
Can d'aya wanda da'alamu itace shugansu, tace munzo shirya gimbiya ne tafad'a tana rusuna Kai,"
Wata k'awar *hanna* ne tatashi ta musu iso har d'akin da *hanna* take, "
Su amira ne azaune sai rud'awa *hanna* ciki sukeyi duk tawani susuce."
Frnd d'insuce tayi sallama tashigo, labba ne tace shikenan anzo, zaro ido *hanna* tayi tace anzo meh?"
Gyaraki mana yau yau d'innan za'a mikaki d'akin mijinkii, dama ahannu kuke,"
D'azu daga cewa zai gayamiki magana sai d aka shafe 1hour bbu ke bbu labarinku. "
Kama baki amira tayi, tace dama wato d'azu dana nemeta narasa wajansa ttafi." Tabb lallai gwara Tun wurii azo ad'auketa, akqita dan zuwa jimawa zata Iya Kai kanta,"
Takaicii ne yacika *hanna* takasa cewa komai, dan tasan kota fad'a wani kayan takaiciin zasu k'ara mata."
Haka sukayita zolayan ta, suka gajii dan kansu suka barta. "
Nan suka tashi suka fice, sukuma kuyangii da jakadai suka shiga,"
Ruwan wanka aka had'a mata, mai had'eda sindaren turaruka kala-kala, masu kamshin gaske, "
Shiga wankan tayi, *hanna* uwar son kamshii, aikuwa ta bingire aband'aki, sanda takai 30 minute kafin tafito,"
Nan suka hau yimata turaruka irinna al'adan gidan sarauta, "
Kaya tasaka, atampha, dinkin riga da sket, sunkamata dakyar taakeshan lumfashi." Sannan aka rufa mata lifaya,"
Mai kyau farii kall gezan ya sauko yarufe fuskarta."
Bayan sungama shiryata suka nufii kofa suka fice. "
Nan k'awayenta da sauran y'an uwanta suka shigo,"
Fitoda ita sukeyi labba ta bud'e k'ofar, da zata sadasu da shashin, dan wajen ahad'e yake, saidai ginin d'aya benii ne, d'aya kuma plate ne."
Ginin saman suka nufa da ita nan suka shiga, kowa sai bud'e baki kawai yakeyi dan kyau da tsarii irinna shashin,"
Kala biyu aka had'a agidan da kalan da yafiso farii call, da kuma kalan pink, wanda *hanna* ke mutuwar so. "
Falo biyu ne asama da d'akuna biyu, falon farko ne zaka fara shiga," set d'in white funitures ne, hatta paint na falon white ne."
Sai d'aki a left side na falon, shima d'akin komai white ne,"
Falo na biyu kuma right side na falon zakabi,".
Saika sauka mata Kala uku Sannan yasadaka da falon."
Falon ne ke had'e da dining, da kitchen, sai kuma wani room da extra bed room a falon, "
Shikuma wancan saba'anin wancan ne komai pink ne, har paint na Falo d'aki kitchen da dining area duk komai pink ne." Sai sama kuma shima design na falon kusan d'aya ne sandai shi d'akuna biyun marabarsu bbu nisa, "
An then Shikuma bbu kitchen, amma akwai dining coloured na d'akinsa blue da farii ne,"
Har falonma haka, "
Itakuma ashh da farii."
Basu tsaya zagaya gidanba suka suka kaita d'akinta suka ajiye akan gado, Can tsakiyar gadon ta k'ule, "
Sukuna sauran suka fita zagaya gidan,"
Kowa sai sam barka yakeyiwa wannan gida na *hanna*
Hankalin *hanna* bai k'ara tashi ba, saida taga suna mata sallama suna wucewa, "
Y'ar karamar hauka tasoyii amma bbu wanda yasaurare ta, haka suka fice,"
Fitar hafsat amira da hameeda ne yad'aga mata hankali,"
Sosai Hankalin ta yatashi ta ringa kuka ta kankame amira, wanda amira ita kanta dauriya takeyi,"
Hafsat ne tana ahare hawaye zata fuce, *hanna* ta cakumo ta, tana kuka tana hava y'ar uwata kada kitafi Ki barnii dan Allah,"
Amira kasa daurewa tayi kukan dake nukurkusanta ya kwace, "
Aikuwa yahau rerashi,"
Hameeda da labba ne kawai basayin kuka, dan sunsan cewa Su ba nisa zata musu ba. "
Amma duk da haka hameeda na goge hawaye, dole takanjii zafin rabuwarsu cikin zuciyarta."
Amira ne tasamu tafice da gudu, tana rairaa kuka. "
Sai hafsat tabii bayanta, Ahaka suka fice sukabar *hanna* da labba kad'ai, labba nata aikin lallashi."
Amma *hanna* Kamar zugata akeyii. "
Sai kusan 9:30.pm MG suka shigo shida abokanan sa daga Falo suka tsaya, tad'ii sukayi har 10:00.pm tacika," Dan shi aganinsa badacewa bane ace abokanai sun shiga d'akin auranka ba, iyakacinsu Su tsaya afalo. "
Shahid ne yakalli hamood yace,"
Kagaya masa cewa gobe zamu wuce fa,"
Hamood yace, "
Flight na 12:00.am zamu bii."
Idan kasamu fitowa tom, Idan kuma amarya bata barka kafuto ba shikenan."
MG baice komai ba, Ahaka suka gama zolayarsa suka tashi, "
Abubakar ne yace, Kai kasanfa cewa k'aramar yarinya, ka aura, sai Kayi ahankali, tunda kazauna kasha tuzurancii,"
Banda harara bbu abinda MG yabishi dashi. "
Har bakin k'ofa yarakasu yajuyo zuwa ciki, d'akin *hanna* yanufa direct, tun daga corridor yfara jiyo sheshahkar kukanta,"
Da sassarfa yak'arasa, "
Yana bud'ewa yaga *labba* nazaune tana faman lallashi,"
Labba na ganinsa tamike tace alhamdulillahi, "
Sai kazo ka lallasheta ko Kai tajii naka dan nikam nagajii,"
Tana fad'in haka taratsa ta gefensa ta wuce."
Tsayawa yayi Yana kallon *hanna* yace, baice komaiba yajuya ya sauka yarufe k'ofa Sannan yahauro yadawo, "
Ayanda yabarta Ahaka yasameta,"
Kamshiin turarensa ne ya tavvatar mata daya dawo,"
Gabanta ne yahau fad'uwa, tattaki yayi har zuwa gaban gadon da take, "
Jin kashin yak'aru kusada ita yasa tasan ya matso kusa,"
Dan ta cusa kanta cikin cinyoyinta, "
Zama abakin gadon yayi, yajawota jikinsa Yana bubbuga bayanta, yace baby maiyasa kike kuka hakane?"
Tun jiya kike abuu d'aya bkya gajiya? "
Yanzu irin kukan da kikayi sai kace wanda aka aura miki dodo?"
Murgud'a baki tayi aranta tace aikai kafii dodonma,"
Zame jikinta tayi ta turo baki, "
Tace basu amira bane suka tafii ba."
Murmushi yayi ya lakacii hancinta yace To ba gobe zasu dawo ba. "
Sauka daga gadon yayi yakamo hannunta yasauk'qr da ita daga kan gadon,"
Alkyabbar jikinta yasa hannu yacire, "
Tsayawa yayi Yana kallon yanda kayan suka mata kyau."
Har k'ofar band'aki yarakata yace shiga muyi alwala muyi sallah."
Turo baki tayi tace ni bana sallah."
Sake baki yayi Yana kallonta yace, "honey boo bansan k'aryafa yanzu ak'arshen wata muke ba'a tsakiya ba."
Mamaki ne fall aran *hanna* wanda hakan yagaza b'oyuwa afuskarta sanda ta nuna tayaya akayi yasan date na mensturation nata. "
D'aga kafad'a yayi yace kina mamakine?"
Har doctor da kike ganii, saboda mensturation pain nasani, so Ki shiga kiyi alwala bansan musu."
Tana tura baki yashiga yayi alwala, tafito shima yashiga, "
Sallah yajasu raka'a biyu yana zubawa Allah godiya da kirari Sannan yayita musu Addu'r zaman lpy da zuri'a d'ayyiba." Sanda suka idar yatashi yafita, "
Da bags yadawo Sannan yak'ara fita yad'auko fresh milk a fridge, yaciro plates yazuba musu abincii hanna yitayi Kamar bata ganshi ba, takoma ta kwanta."
Taso kici abincii yace atakiace nakoshi tace, "
Idan kika taso gobe zan kaiki gida kiga umma,"
Mikewa zaune tayi tace promise, "
Yes promise ya fad'a,"
Tasowa tayi tazauna, fresh milk yafara bata ta karba tasha kusan half Sannan ta ajiye, "
Abaki yafara bata naman kaza ta k'arba tacii ko musu bbu,"
Sanda ta daiddaiici ta koshi ta garya masa cizo riqe hannun yayi Yana yarfewa, "
Itakuma tahad'e rai Kamar ba ita tayi cizon ba,"
Squra ni ya fad'a mata, "
Nok'e kafad'a tayi tace owh owh kalan karama,"
Nop bazan rama ba kawai dai inason cin abincii da hannun mata tane,"
Sharewa tayi yace, kinmanata u promise to take good care of me, jama'a dayawa sunyi witnessing, turo baki tayi ta fara bashi abincii, "
Sanda yaciika timbinsa tamm,"
Kafin yaruqe hannunta ya sud'e ya tashi yatttara komai dasukayi mafani dashi yayi waje Sanda yazo daff k'ofa yace Ki shiga kiyi wanka ina dawowa, "
Bai jira amsar taba yafuce Sanda yasauka k'asa yakai cikin Sannan yadawo yashige d'akinsa."
Tashi tayi taje dai-dai kofa tace ainii ba kwaduya bace dazakace na k'arayin wanka,
Tana fad'in haka ta datsa Ki ak'ofarta ta koma ciki ta kuskure baki ta wanke hannu, tafito ta kwanta, ko kayan jikinta bata cureba."

To be continued

Ur's
*Z33yyb3rw3r*

*BIBIYATA AKEYI*
_
_Bismillahirahmanirrahim_

_
Writting by


© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )

*Ka/ki zama mai yafiya, " ga duk wanda ya zalumceka*

*Ka/ki, zamo mai yarda da kaddara hakan zaisa ki rayu cikin farin cikin,*


*Ka/ki zama mai yawaita fad'in kalmar Alhmdllhy domin nuna gidiyarki wajan ubangiji.*

*Ka/ki zama mai yawaita fad'in astagfirullah domin samun yafiyaar ubangiji.*

*Nasiha ce*
================
Congratulation *my hajja* for d succesifull complation of ur buk *sab'anin so* hak'ik'a u tried hard,"
D buk is insparing,"
Allah yaimaka *my hajja* u'r such an amazing person, u'r an angel. "
More grease to ur shining elbow."

Page 62

*
MG yana shiga d'aki wanka yafarayi sannnan ya fito, sleeping wear's d'insa yasa, ya kwanta akan gado dan tun lokacin da *hanna* ta murd'a key ak'ofarta yaji, " yakusan 30 minute da kwanciya amma yakasa yin bacci,"
Itakuwa *hanna* baccin ta takeyi, hankali kwance, dan ta tabbata batada fargabar komai ta kulle k'ofar ta."
Tashi yayi yanufi toilet, alwala yad'auro yazo yafara nafil fili yatashi daga sallaya ba saida 12:30 tayi kwanciya yayi baijima ba bacci yad'aukeshi,"
Kusan k'arfe uku ihun *hanna* ya farkar dashi, da gudu yayi d'akinta gabaki d'aya ya tsorata, "
Buga k'ofar yakeyi yana ce mata ta bud'e amma *hanna* kuka kawai takeyi."
Juyaww yayi d'akinsa bedside drawer ya bud'e, spare key's yad'auko, ya nufii d'akinta dashi, "
Dama MG yanada key na d'akinta,"
Yabar tane kawai bawai dan dabarata ko wayonta ba. "
Yana bud'ewa ya hangota acan k'arshen gado ta duk'unkune sai faman kuka takeyi."
Hqwa yayi dasauri yasa hannu yariqota, tana bud'e ido ta kalleshi dasauri tashige jikinsa, "
Hannuwansa biyu yasa yatallafeta ta baya."
Yana d'an bubbuga bayanta ahankali."
Lafewa tayi ajikinsa sai ajiyar zuciya take sauk'ewa,"
D'agota yayi yana wiping d'in tear's d'in dake fuskanta, sanda yagama yafara tambayanta, maiyafqru? "
Girgiza kai tayi tace" wasu yarqne sunata kuka suna kiran suna na, "
Kuma daga kallonsu suna cikin wani hali." sannnan wasu mutane biyu suna cewa sunvar amanar y'ay'ansu ahannuna dakai,"
Jijjiga bayanta yayi yace " to meye nakukan?"
Turo baki tayi tace toba yaran bane sunata matsowa jikina ba, "
Sukuma iyayen har jini ne ajikinsu fa."
Ajiyar zuciya yasauke yace sharrin mafarkine kawai,"
Sannnan Kuma kin kwanta ba kiyi addu'a ba."
K'ara turo bakinta tayi tace nifa nayi addu'a, "
Ok tohm yanzu ki k'arayi ki kwanta,"
A''iina d'in?" ta tambaya tana zaro idoh 😳, anan yafad'q yana k'ok'arin mikewa,"
Riqe hannunsa tayi gam tace tabb ni gaskiya bazan iya kwana ni d'aya ba."
Da waya saki ki kulle k'ofar ki? "
Ya tambaya," turo baki tayi btace komai ba d'aga kafad'a yayi, sannnan yayi hanyar fita, da gudu tazo ta wuceshi, tashige d'akinsa wuff, "
Tsayawa yayi kawai yana kallonta yayi murmushi had'eda Girgiza kai."
Bin bayanta yayi yasa mu hartayi masauki akan gado,"
Zuwa yayi bakin gadon ya tsaya,"
4 pillow's da Kuma mini pillow su sukafii yawa akan gadon,"
Jera pillow's tayi atsakani sannnan ta bubbuga gadon tace kwanta anan, " Zama yayi ad'ayan gefen gadon ya ciccire pillow's d'in yace nida gadona sai anyimiun doka?"
Ki koma d'akinki idan bazaki iya kwana ahaka ba yana fad'in haka ya kwanta."
Ihun kuka tasa tanayi tana shisshure k'afanta duk yanda yasoda tayi shiru amma tak'i, sanda ya mayar da pillow's d'in sannnan tayi shiru. " kwanciyarta tayi batafi 10 minute ba takoma bacci,"
Shi kuma kallonta yatsayayi, she look's innocent, "
When she's sleeping,"
D'an jan hancinta yayi wanda sanda tayi motsi yace but stubborn When she's awake,"
Ahaka har kusan ten minute baccinta yafara yin nauyii. "
Ahankali take mirginawa cikin bacci batason ma tanayi ba, kawai sai jinta yayi ajikinsa,"
Tad'aura kanta a chest d' insa taci gaba da baccinta, "
Abun dariya yabashi yace y'ar fitina yanzu ina pillow's d'in duk kinbii kin haura kansu,"
Ahaka shima bacci yad'aukeshi. "

================

Karimace zaune k'annenta sun sata agaba, akan yunwa sukeji tun jiya bbu Abun da sukacii."
Kabir kuma yadamesu momynsa, "
Sauk'inta d'aya ma data kira wayan abbansu tajii yad'auka." suka gaisa nan hankalinta yad'an kwanta, su dukansu sun rame,"
Abida ne tana kuka tace, gaskiya anty k nikam nagajii, ke baki fad'a mana dalilin kawomu nan ba. "
Sannnan kin azabtar damu da yunwa ki duba yanda, su hassna ke kuka,"
Sa'ad kam da baida dariya, yanzu yana kwance cikinsa yana ciwo, "
Kuka karima tasa tace Abida rashin gayamiki danayi shine, yafii miki saukii kici gaba da addu'a in sha Allahu gobe zanfita ba nemo mana abincii."
Ahaka tayita lallashin su. "
Agogon bango ya buga 4:00am na asuba, minister da hajiya suwaiba sunakan sallaya,"
Basujii shigowa gidanba k'arar murd'a kofa kawai sukajii, "
Wasu k'artaine suka shigo d'akin,"
Salati su minister sukasa sosai jikin hajiya suwaiba yafara 6ari, "
Basu tsaya wata wata ba suka miqa masa waya,"
K'ar6a yayi yana jin muryqr senator yayi yana cewa, "
Shin har yanzu kanakan bakarka?"
Gurgiza kai minister yayi yace nikam nagane gaskiya yanzu saidai namaka addu'ar shiriya, "
Dariya senator yayi yace banso kashekaba taurin kanka yaja,"
Kwace wayar wannan k'aton yayi, senator ne yace Ka kasheshi Ka kashe duk iyalansa sannnan ku k'ona gidan, "
Ahaka sukayiwa minister da hajiya sabuwa yankar rago subhanallhi 😭 sannnan suka bi duk gidan iya bincikensu basu gano kowa ba." kona gidan sukayiwa gabaki d'aya, "
Dan dama kafin su shigo sanda suka kashe sauran sojojin, way'anda kuma suka ga kud'ii suka bada k'ofa sunanan."
Suna gama aikin yak'ira senator awaya yashaida masa bayan shida matarsa basuga kowa ba. "
Rud'ewa senator yayi Dan yasan minister akwai d'an banzan wayo,"
Yab'oye sune. "
Wata dabarace ta fad'o masa, yace kajirani yanzu zan turo naka phn numb d'in d'iyarsa kayi tracing,"
Banso garii yawaye baka gamamun da ahlinsa ba, "
Bazai ta6a barinsu sutafii batareda Wata shaida ba."

MG ya farka tun kusan kiran assalatu ba farko yanaso ya shirya yatafii masallaci, amma baison yatshi *hanna* dake baccinta hankali kwance. " Irin gajiyar da tayi yasata, bacci sosai har batajii kiran sallah ba. "
Ahaka yana gani har akayi sallah aka idar,"
Sai kusan 6 kafin ta bud'e idanuwanta,"
Mayarwa tayi ta kulle, "
Jinta ajikin mutum yasata tashi zaune."
Har zata fara masifa ganinta a jikinsa, "
Juyawar da zatayi ne taga filin data barii acan baya har pillow's d'in data jera ta tsalake," kunyace takamata, sunna kanta k'asa tayi tace, kayi hqkurii bai kulataba, "
Cewa yayi kawai kitashi muyi sallah tym ya wuce, tashi tayi taje tad'auro alwala shima haka, nan yajasu sallah,"

Karima na idarda sallah tatashi tafita bataso garii yayi haske gyara tanema musu abincii, "
Fitanta ta hango wasu mutane na yiwo gidan kuma tabbas bata yarda dasuba, gidan takoma cikin sassarfa da tada kannaneta duka suka yi bayan gidan, da jakkunan takarku dana kud'ii kawai ta iya d'auka su tafa jefawa tabaya sannnan tasamu abunda zasu taka duk ta ingiza kannenta, itama ta samu tahau. "
Jini duk ya6ata jikinsu Dan sucurity wire's sun yayyaankesu."

D'akinta ta koma ta k'ara kwanciya sai 7:30 tafarka wanka tayi ta ta yi kwalliya sosai kana ganinta kaga amrya,, gyara d'akinta tayi sannnan tafito da niyyar gyara nasa d'akin, "
Wata kuyanga tagani tana shirin shiga d'akin, wani irin zafin kishi ne yabai bayeta,"
Batasan lokacin data daka mata tsawa ba ke ina zakije ta fad'a? "
Jikinta na rawa tajuyo na gaisheta, Allah hucii zuciyarki d'aki zan gyara nasa,"
Ajiyar zuciya tasauke tace kije zan gyara,"
Ba musu ta juya tasauka, ita kuma *hanna* tak'arasa d'akin ta gyara shi tsabb, ta cika ko ina da turare, tagyara bai d'aki sannnan tafito k'asa tasauka bata ganshi ad'ayan falonva, tawuce d' ayan anan taganshi zaune akujera, "
Yasa light blue shadda jamfa hannun Yasa links ma light blue,"
Da sallama tashiga yajuyo yana kallonta yakasa d'auke ido."
Sanda ta matsa daff dashi sannnan tad'an rusuna tagaidashi amsawa yayi had'eda miqa mata hannu, "
Bbu musu tariqe hannun yazagayo da ita yazaunar da ita kan kujerar."

To be continued

Ur's
*z33yyb3rw3r*

*BIBIYATA AKEYI*

_Bismillahirrahmanirrahim_

Writing by
© _Zaynab Bawa_
( _z33iiyyb3rw3r_ )

_Like my page on Facebook :Zaynab BAWA novels_

Followed me on instagram: mhiz_z3iiyyb3rw3r



*Ka/ki girmama mahaifanki, domin mahaifa sune abuu Mai girma kicin rayuwar ki/ka*

*_Ki/ka kasance mai yawan yiwa Manzon Allah SAW salati, domin kaima Allah ya yawaita yimaka salati,_*

*_Ka/ki kasance mai yafiya alokacin da aka zalunceki/ka, koda kuwa kinada halin ramawa,"_*


*Nasiha ce*

================

_This page is sincerely dedicated to u my darling, "_
*Aysha hanwa*
_Not 6ter by blood but u'r my 6ter by heart,"_
*ILYSM❤*
_always heart ❤ u dear._

Page 63

*
Zagayo da ita yayi zuwa gabansa, sannan yazaunar da ita akan kujerar da yake zaune,"
Lallen hannunta yafara bii yana shafawa, bak'aramin kyau Lallen yamasa be. "
Hannunta ya had'a duka biyun waje d'aya ya sumbata."
Lumshe idanuwanta tayi ta bud'esu akan sa, "
K'ura masa ido tayi dan wani irin kyau na musamman taga yamata," kansa bbu hula gashinsa yasha gyara sosai. " bak'ikirin Har sheki yakeyi,"
Batasan ta tsareshi da ido ba, kawai jitayi ya hure mata idanuwanta, " kamshin vanilla flavour ne ke fita daga bakinsa,
Sunkuyarda kanta tayi tana murmushi," gyara zamansa yayi zuwa kwanciya, d'aura kansa yayi, acinyanta ya Lumshe idanu Kamar maijin bacci."
Ahankali yafara magana, sweety kitashi ga abincii adining, " dannasan yanzu haka kinajin yunwa amma kike zaune."
Kallon ikon Allah take masa Kamar bashine ya danneta yakuma hanata tashi ba, Kuma yake zancen abincii adining."
Sweety ba magana nake miki bane? " cikin tsiwa da rashin kunya tace, tsuntsu zanyi nqtashi idan baka d'agani ba?"
Tashi yayi kawai yatsaya yana kallonta,"
Ni kikeyiwa rashin kunya? " ya tambaya, kawarda kanta gefe tayi, ciki- ciki yadda bazai jiba tace eh kaid'in,"
Ai kuwa karaf a kunnenta, "
Fisgota yayi ta fad'o jikinsa,"
Bata ankaraba saiji tayi yafara kissing d'inta, da zafi-zafi Wanda kana kallo zakasan tsantsar mugunta yake Mata,"
Iya k'ok'arii tayi ta kwace amma takasa, "
Kwalla ne tafara zuba afuskarta, dan ita kad'ai tasan tsanatsan azabar da takeji."
Sanda yagaji dan kansa yasaketa, yakoma ya lafe akujera yana maida numfashi. "
Itakuwa Kwalla ne kawai yake, kwarara, dan wani irin zogii da rad'ad'ii lips d'inta ke Mata,".
Sanda yadawo normal yajuya ya kalleta yace tashi muje kici abinci,"
Babu musu tamiqe dan batasan mai zai sake aikatawaba, idan tasake masa musu."
Zuwa tayi ta bud'e wermer's d'in tafara saving d'inshi," yana kallo yanda tacika plate da abincii kallonta kawai yakeyi baice mata komai ba, "
Tea tahad'a masa sannan ta juya da niyyar zuba nata," Kamo hannunta gamm yayi yace, "
Wa kike tunanin zaicii wannan abincin?"
Kai tafad'a a dan tsorace, kallonta yakeyi Kamar mai nazarin wani Abu."
Zaunarda ita yayi agefensa yace, zauna kici abincii danke aka kawo, "
Kin ga ni ban iya cii ba."
Kallon mamaki tamasa Wai bai iyacin abincii ba, "
Dariya ne ta kufce mata aikuwa tashiga yinta bbu kakkautawa,"
Shikuma yatsaya kallonta, she's unique yafad'a afili, "
Murmushi yayi yace nabaki mamaki koh." tace eh, "
Amma bani kigani ko zancii,"
Ebowa tayi a spoon takai bakinsa, kawarda Kai yafayi Kamar Angela ta koshi da abincii, "
Daidaitar bakinsa tayi ta tura masa."
Sanda sukayi haka sau uku sannan ya cigaba da karban abincinsa yanacii, Sanda yajishi full, ya lakato kumatunta yace, lallai bakida wayo yanzu da ace nace kibani ne bazaki bani ta dad'in rai ba,"
Turo baki tayi tace wally nima tunda hakane saika ramamin, saika bani,"
Aikuwa yazauna yabata Sanda tak'oshi sosai tukunna, "
Tashi duka sukayi da plate d'aya da cup d'aya da Kuma spoon d'aya ahannunta ta nufii kitchen,"
Binta da kallo yayi yanajin Sonta naratsa duk wani gabbai na jikin sa."
Tana shiga tatsaya Kallon kitchen d'in, gabaki d'aya yatafii da ita, "
Ganin ta dad'e ne yasa yabi bayanta,"
Ganinta yayi Sai bud'e ko''inq takeyi,"
Dariya qbun yqbashi yace Kamar ba itane ta cikaawa mutane kunne da kuka ba, amma yanzu tazaqe tana Kallon kayan."
Batace komai ba, yak'ara cewa duk kinsa ancika mana gida da pink colour's, Kamar yanda kasa aka cika mana da white ba, tabashi amsa,"
Fita yayi tabi bayansa, tana cewa Fita zakayi, eh yace atakaice, "
Marairaice murya tayi tace dan Allah inbiyoka muje mu gaida su ummii,"
Wani irin dad'ii ne yaratsashi Ganin yanda tanuna muhimmancin iyayensa, "
D'auko mayafii yace kawai,"
Up stairs tayi da gudu, ta bud'e wadrope ta D'auko katon hijab da tayi sallah dashi, "
Har k'asa hijabin, tun tana saukowa yak'ura mata ido bak'amin kyau hijab d'in yamata ba," gashi light blue kalan kayansa, "
Sanda tazo kusa dashi kawai tadubi hijab d'inta tadubi kayansa, riqe baki tayi," Dariya yayi ya girgiza Kai, "
Juyawa tayi tace barina canja hijab,"
Riqota yayi yace muje, haka dole yajata, "
Shashin mai martaba suka fara Zuwa, dan Zuwa 9:00.am zai Fita fadaa."
Baijira iso ba taga Kai tsaya ya shige, dan dama shi ba'amasa iso baiso,"
Da sallama suka shiga mai martaba na zaune akujera, yaji dad'in ganinsu sosai addu'a yaringa musu da nasiha."
Sai suka shiga Shashin kilishi daganan suka shiga na ummii, "
Ummii Sai murnar ganinsu takeyi labba kuwa tana baccin gajiya."
Tashi yayi zai Fita ummii tace a'a jira matarka, "
Sosa Kai yayi yace ummii su Shahid ne zasu wuce inaso na rakasu."
Murmushi ummii tayi tace ai itama yakamata taje rakasu, dan ta dalilinta sukazo,"
Kuma nasan yanzu haka basu gana da iyalansu ba, Kuma yakamata ta gansu,"
Ta6ata ummii tayi tace tashi kuje Allah yamuku albarka, da amin ta amsa sannan tafice, "
Ganin yanda take tafiya yasashi rage saurii, ahankali yanda sojojin dake bayansu da Wanda ke gabansu bazasu jiba tace waikai ko acikin gidanma da sojoji kake yawo?"
Shima tambayanta yayi Wai bakisan Sunana bane?"
Daureta yayi bata k'ara cewa komai ba, "
Wani dan k'aramin flate suka Isa,"
Da sallma yashiga yasamu sun Gama Shiri suna jiransa ne,"
Gaidasu *hanna* tayi suka amsa duka suna tsokanarta, wajen matan ta nufa taje suka gaisa, "
Matan duk da yaransu kabilarsu da Kuma k'asarsu baizo d'qya ba Amma ta fahimcii sunada Sabo, dan d'an zamnsu Har suna ta hira sosai."
Kar6ar yarinyar matar Shahid tayi, batafii 7month ba wasa takeyiwa yarinyar, matar

Please Login or Register in order to submit comment