Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ana Haka Har Allah yasa *Wata* *rana* yadawo lokacin dawowarsa baiyiba, yadawo Dan yayi mantuwa ne, daga bakin kofa yahadu da Ahmad da kayan abinci niki niki, yana futa dasu,
Ga mai abin hawa yana jiransa Ana loda masa kaya, zai dashi yayi ya tambayeshi Ina zaikai kayan??? Cewa yayi zai Kai gidansu goggo ne (gidansu kakaninsa), baba yayi matukar mamaki cikin hikima ya tambayeshi ko yaune farko, aikuwa kunsan yaro" kuma bawai yasan meyake faruwa bane. Atake ya shaida masa ai yadade yana kaiwa.
Betsare yaron ba, Amma cikin zafin zuciya ya nufi dakin Ammah, abinda yaji ne ya matukar birkita zuciyarsa. Wato Ammah yaji suna tadi tadi da kawarta irin makircin da suke shukawa, Anan yaji shirin satar da take shirin yi masa na makudan kudi, kuma su daurawa mama Alokacin tace ta tabbata dole Sai ya saketa.

Wani irin tausayin mama ne yakamshi, da tuno irin abubuwan da yayi ta Mata, Har zai juya yaga Idan be tabbatar wa da Ammah yajita ba" toh wannan sace sacen da takeyi bazata daina ba, bude dakin yayi ya shiga da Sallama, amsawa sukayi, cikin kid'ima Dan basuyi tsammanin ganinsa yanzu ba.
Neman waje yayi ya zauna, tareda fuskantar su.
Kiji tsoron Allah halima duk wannan abunda kikeyi dan kikori Aisha Wanda ita ta daukeki amtsayin yar uwa.
Wannan abinda kikeyi bashi zaisani rabuwa da "itaba" mai yasa bazaki riki kaddara ki dauketa amtsayin yar uwarki ba' shiru tayi yayi ta mata magana mai sanyaya jiki hadeda wa'azi.
Alokacin jikin Ammah yayi sanyi, amma cikin zuciyarata, haryanzu son ta kori mama yana nan.

Sai bayan yafita kawarta ta kara zugata, Kan yacimata mutumci akan kishiya, Ana tadaura Mata aniyar zuwa gun boka, dan takori mama.

Mama taga sauyi sosai awajan baba, Dan wancen lokacin ma tabari akan sauyin yanayi, yasashi canja Mata.

Sosai baba yake nuna Mata kulawa, dan mama cikin ta bai hana Mata kula dashi ba yanda mama takasan ce, mace mai tsafta.

Wannan kulawa ba karamin cin ran Ammah yakeyi ba, ko lokacin suna su kadai bata samu wannan kulawa bah.

Bayan Wata biyu, ta haifi yarta mace, akasa Mata sunan umma, wato khadija Ana kiranta da (hajja), sosai baba ke nuna Mata soyayya, ma yarinyar dayake duk yaran Ammah maza neh, guda uku.

Haka rayuwa taci gaba da tafiya, lokacin inda yaran Ammah shida" uku maza uku Mata, yaya Ahmad shine babba yana aiki a lagos yanzu da matansa biyu da yara hudu. Sai yaya jabir da yaya unais da anty Maryam duk rana daya akayi auransu, Sai rabi ' ah da hafsat.

Yaran mama uku tanada cikin na hudu, Anty hajja itace babba tanada yara uku, Muhammad shine babba Sai Aisha (mamii) karamin shine aslam, Sai maman amal itama yaranta biyu, Anty hundatu ne Wanda bata dade dayin aure ba, ta auri babban dan umma.

Alokacin da aka haifi *hanna* ne kuma Ammah tadauki tsana ta daura Mata.
Alokacin ne tamata asiri, aka tura Mata aljanu Wanda bbu tabbacin akwai su ajikinta.
Sai saleem da abba.
Nisa wa yayi sannan yace kutashi kuje ku kwanta, dare yayi, tashi sukayi duk jikinsu yayi sanyi, danjin hali irinna Ammah.

Dakin mama suka nufa, da Sallama suka shiga ganin momy sukayi zaune akan kujera, harara ta watsa musu daga Ina kuke??? Mama daga dakin yaya jalal muke, sauke ajiyan zuciya tasauke, shine zaku Kai dare Haka??? , kallon agogo sukayi, shadaya nadare 11:00, mama wallahy bamusan dare yayi Haka ba, kuwuce ku kwanta,

Bamusu sum-sum suka wuce daki.

Bayan sun shiga ne" *hanna* tadauki wayarta ganin misscalls din najeeb tayi kusan 10, ganin dare yayi ne kawai yahana ta kiransa dan rabonta da muryarsa tun safe,
Kwanciya tayi cikeda kewarsa aranta.

Jarabawa suka fara sosai, kanta yayi zafi, kokadan bata da lokaci duk tarame.

Gashi ansa ranar auran Anty samha yarinyar umma.

A ranar yaune MG yake shirin dirowa kasar sa ta haihuwa.
Jirgi guda kasar Dubai ta bashi Dan tafiya da duk sojojinsa. Sai dai sukansu sunsan dasuyi rashin masu tsaro sosai, tareda Ummii da intisar da affan.

================

*Masarautar* *kano*

Shirye Shirye akeyi sosai na tarban *yareema* abdallah, kota Ina gyara masarautar akeyi, hatta garin kano sanda tasan da sunada bako inda, Har shugaban kasane yazo" dan taryansa,

Karfe uku 30:00 dai-dai jirginsu ya dira a Nigeria, garin kano.

Dumbin taron jama'a ne suka zo taryansa, inda daga masarautarsu ma gayya gudane. Sannan ga governor da sauran Manya, hadda shugaban sojoji wato chief wanda afuska Sai farin ciki yakeyi sosai, azuciyar sa kuma da dadama daya kasheshi a wajan.

Gabaki daya suka dugun zuma sukayi, masarauta.

To be continued

_Ur's_
_z33yyb3rw3r_

*BIBIYATA AKEYI*
_
_Bismillahirahmanirrahim_

_
Writting by
© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )

Page 23

*
Masarauta duka suka nufa" nan da nan kowani sako da lungu, na cikin masarautar ya dauka " *yareemah* ya isoh, dan ko ba'a fada ba yanda masarautar tadauki kidan algaitu da ko ina hakan ya'isa yasanar da isowar *Yareeema*".

Cikin fada suka nufa kai tsaye" inda mai martaba da mukarrabansa suke jiran isowarsu".

Sanda suka gama kwaasan gaisuwa, sannan suka nufi dakin da mai martaba da iyalansa suke cin abinci ".

Aranan idan kaga fuskan MG koda bai kasance mai fara'a ba" amma fuskansa ya nuna yana cikin farinciki".

Sosai aka tanadar musu kalolin abinci", duk daman sababban abu ne agidan sarauta, amma nayau daban yake".

Duk iyalan mai martaba suna tare awajan".

Abinci sukeci cikin kwanciyar hankali da farinciki, irin wanda suka dade basuji ba.

Dan sundau tsawon lokaci basu hadu haka ba.

Bayan angama cin Abinci ne " duk suka tare a falon mai martaba, tadi sukeyi Sosai irin na yan uwan da suka dade basu zanta ba".

Kana kallon wannan zuri'a sai sun burgeka" sun baka sha'awa irin yadda suke tadi kai ahade, dan awajan baza ka taba banbance cewa wannan dan wannan bane.

Affan ne ya kalli MG yace" ya yareemah wai Yaushe wannan antynmu mai sa'ar tadazo ne???? Kallon sa MG yayi" cikin tsolaya ya kashe masa idoh daya, eh ai ya kamata musanta yanzu gaskiya, nan da nan kamar wanda suke jira ayi magana suka hau kansa kowa so yake koda hotonta a nuna masa, dan sun tabbata tacika mai sa'a, samun miji irin yareemah yana wuya"

Gaban intisar sai faduwa yakeyi, Cikin zuciyarta tana addu'a Allah yasa itace wannan mai sa'ar",

Wacce naji sun kirata da anty surayya ne da karbi zancen, itace first born a yaran mai martaba.

Yareemah yakamata ka duba wannan zancen, tajuya ta kalli duk mutanen falon, sannan tace " ka kalli irin farincikin da muke ciki yanzu, kuma inada tabbaci da'akwai matarka a ciki, farincikin mu saiya fi haka, bakunan mu sayya fi haka budewa.

Duk danginna bamuda burin da yawuce" muga iyalinka kai kanka kasani duk zuri'ar mu babu mutumin da ya kaika soyuwa cikin rayukanmu.

Kokasan iyayaenmu basuda burin daya wuce ace" yau sunga 'ya' yanka, kokasan shiru kawai suka maka dan basasan abinda zai takura ka, amma bawai dan sun hakura da zancen auranka ba" shekarunka fa talatin da biyar 35 'yan mata sun kusa su fara cewa kamusu tsufa, sai irinsu affan, tafada cikin sigar tsolaya.

Ganin kansa akasa yasa suka fidda ran samun amsa".

Mai martaba dama yasan basuda amsar wannan tambayar, yasa bai samusu baki ba, dan sau dayawa yakan zaunar dashi yana masa wannan maganar" amma amsar sa daya na wannan yarinyar, sujira da sauran lokaci, amma da mamakinsa gani yayi ya dago kansa da murmushi.

Wanda duka falon Sanda abun yabasu mamaki, dan irin wannan murmushin yin su awajan sa nada wahala",

Cikin zumudi wanda kwata kwata basusan shi da hakan ba yafara magana cikin muryarsa mai dadin sauraro baga mata ba har maza" wanda jinta yakanyi tsada", kodan yasan hakanne yasa yake rowar jinta" ohow"🤷‍♀ idan wannan ne karkudamu matsalarku tazo karshe, nan da 1 to 2 month mai martaba zasuje nemamin aure" gaban kilishi ne ya fadi cikin razana da dubur bur cewa tace " a'iinah???

" Bauchi" yafada batareda kawo komai aransa ba".

Wuta ne ta daukewa intisar da kilishi"

Inda duk dakin sai farinciki ya lullubesu gabaki daya sun rasa yadda zasusa kansu don murna.

Affan harda taka rawa, inda mai martaba da ummii kuwa yanda kasan anmusu albishir da gidan al'jannah, Sosai baku nansu yaki rufuwa.

Inda duk Abinci akeyi kilishi da intisar basa fahimtar komai.

Halima ce ta zakud'o cikin zumudi sanda tazo gabasa taruko hannuwansa, *ya* *yareemah* itace wannan wanda kake dakon santa kusan shekara goma,??? d'aga mata kai yayi " yaya kaima Allah yasa tasoka kamar yadda kake sonta.

Affan ne yayi saurin karbe zancen da'allah malama rufa mana baki, wacece zata kalli yaya tace bataso" ke kanki kinsan duk zur'ar mu bbu mai kyau da kwarjininsa, kallon ummii yayi cikin tsolaya yace" aiko ummii wanda take cikakkiyar balarabiya bbu abinda zata nuna masa, duka ummii takai masa tana girgiza kai irinna shirmen affan.

Kayyyah" affan barta tamun addu'a dan banida wannan tabbbacin akan zata soni, akwai mutanen da kyau da kudi da dukiya bai damesu ba, batasan koni waye ba balle tasoni.

Amma inada tabbbacin arananda nayi asarar ta aranan rayuwata amfaninta kalilan ne, kuma har inde narsata toh bazan iyayin aure ba, yakarasa maganar cikin sigar da duk wanda yake zaune awajan sanda matsanancin tausayinsa yqamasu,

Ummii har idanuwanta ya cicciko dan ita take zaune dashi ita kadai tasan irin son da yake yima wannan yarinya".

Mai martaba ne cikin sigar kwantar da hankali yace " *Yareeema* na karfa kamanta kai soja ne, mai juriya da kuma gwarzon taka, eyyah abba ata wannan fannin gaskiya ni rago ne.

Yana fadin yatashi da niyyar futa, wanda bayar iyayensa da yan uwansa da dumbin tausayinsa, affan ne yayi karfin halin cewa yaya baka fada mana sunanta ba".

================

Nayi tafiya ya plz fans kuyi hakuri dan banida tabbacin kullum zakurunga ganin post dina harsai danawo zai dawo normal bye love uuuuu olll

To be contunieud

_Ur's_
_Z33yyb3rw3r_

*BIBIYATA AKEYI*
_
_Bismillahirahmanirrahim_

_
Writting by
© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )

Page 24

*

Juyowa yayi ya kalleshi sannan" da murmushin dake boye da damuwa acikinsa".

Girgiza kai yayi yajuya daniyar futa" mai martaba ne yatsareshi" yareemah " fadamun sunan surikata kaji".

*"Hanna"* wow"😍 halima tace" hadeda hada yatsunta biyu waje daya sannan taware guda ukun amma sunan yayi ".

Murumushi yayi kawai sanna yajuya ya fuce.

Sojojinsa ne" suka rufa masa wasu na gaba" wasu na baya" suka sashi atsakiya, harzuwa wani tangamemen sashi wanda idan kagani, za'a iyacewa na mata hudu ne", amma gefen MG ne wanda yake rayuwa shi kadai".

Gefe daya gida ne mai hawa biyu" sainabiyun wanda suke jere amma shi plat ne mai matukar kyau duk yanda zan kwatanta muku kyawun wannan gida bamai yiyuwa bane, iya karshen kyau" gidan yayi kyau " plat din ya nufa" wanda kofarsa duk ta glass ne' irin glass din da ko bullet baya 6ulashi".

Wasu lambobi aka danna ajikin kofar, da'alamu kofar mai sucurity ce ", kofar ne tabude inda wasu daga cikin sojojin suka fara shiga, sannan shima yashiga", wani falo ne dan madaidaici mai kyawun gaske" komai na falon farine sol har daukan ido yakeyi",

Daga dukkan alamu dai yafisan kalan farii".

Har mamaki irin kyawun falon yakeban, amma nace bafa abin mamaki bane dan idanna yi la'akari da falon MG ne, kuma sanin kankune kunsan waye MG".

Daki kai tsaye yawuce dan yin wanka ".

Can cikin falon mai martaba kuwa, farin ciki ne da kuma tausayin *yareemah* da yabarasu dashi, sa6anin kilishi da intisar Wanda bakin cikine fall a zuciyarsu, intisar jitakeyi kamar zuciyarta zai futa dan bakin ciki ga wata irin kishi daya lullubeta, har cikin ranta ba karamin so takeyiwa *Yareema* ba" ita kuwa kilishi zafin dukiya da mulki yakusan kubucewa ahannun su " amma duk yanda za'ayi bazata bari ya auri wannan yarinyar ba" duk rintsi sai ta rabashi da itahh".

================

*Hanna* sun gama exam lafiya", inda se shirye shiryen zuwa kano, inda zuwansu yahadu da bikin anty samha da za'ayi sati biyu masu zuwa, inda soyayyarta da najeeb sai karuwa yakeyi kullum idan basa maqale a waya toh suna gidan anty suna zuba soyayya, abu daya dayake damunta shine yanda najeeb yayi shiru da zancen turowa gidansu kokadan yadaina mata maganan,

Yau sauran kwana biyu sutafi kano, yaya jalal ne zaizo yadaukesu, sai shirye shiryen tafiya sukeyi.

*Hanna* ce" tafito cikin sauri " daga alamu wani waje takeson zuwa, ammah ce azaune acikin gida, lokacin hanna tafuto wayan tane tafara ringing, hankalinta baikai kan Ammah dake zaune acikin gidan ba, daukan wayan tayi tana cewa, myn gani fa ahanya inazuwa, gaban Ammah ne yafadi dan dagajin wayan da wani take" kuma da alamu saurayinta neh, me hakan yake nufii kenan???? Ta tambayi kanta".

Fucewa tayi cikin sauri dan zuwa gidan anty dasu hadu da najeeb, yaso ace shizai kaisu Ammah yasan hakan ba mai yiwuwa bane, bbu yanda za'ayi iyaye subar yayansu yakaisu" yana matsayin saurayi ba muharramunsu ba".

Bayan isarta gidan anty, tasamu najeeb ya dade dazuwa, sun dade suna hira, sweety" dagowa tayi ta kalleshi" kinji haryanzu bance komai gameda maganar turo manya ba ko???"

Sunkuyar da kanta kasa tayi"

Yaci gaba da cewa"!!!!!

Narasa mai yasa duk lokacin da zansamu abba da wannan maganar, sai wani abu yatsareni" kuma nakan dade bankara tunowa ba kuma akowani lokaci nayi tunanin zuwa hakanne take faruwa " muringa yin addu'a dan jinakeyi kamar akwai wanda keson rabamu, narai narai yayi da ido" idan narasaki zan shiga wani hali, irin son da nake miki ni kaina bazan iya fadin sa ba", wani irin tausayin kansu ne yakamata'.

Murmushi tayi, addu'a ne yakamta muyi dan babu abinda yafi karfin addu'a".

Shima murmushin yayi zanyi kewarki" amma zanbiyoki kano, kinji sweety, umm lokaci yana tafiya, hameeda tana jirana zamu shiga kasuwa," ok bari inkaiku" no kabari" kollon tuhuma yamata" wai meyasa haka" hah" nafarko idan na baki abu bakya karba" idannace ko makarantarku zanzo saikikii" dan bakyaso kishiga motata?? Eyehh??

Langa6ar da kanta tayi" hava myn tayaya zan karbi abu ahannunka" ace a'iinah nasamo?? Kaikanka kasani dole sai an tuhumeni".

Sannan zancen zuwa makaranta kuma" kaikanka kasan zancen duniya baya buya idan akaje akasamu, babanmu akafada masa fah," mai zai dauka yaturani karatu natafi soyayya??"

jikinsa ne yayi sanyi" yasan duk laipinsa ne, in sha Allah yakusan zuwa karshe kinji sweety,"

Murmushi kawai tayi amma aranta itama tana fatan faruwar hakan".

Kallon agogon hannunsa yayi, yatashi yana fadin zantafi, abba zai aikeni" zanyi missing wannan kyakkyawar fuskar" rufe fuskanta tayi daa tafukan hannayentaa," dariya yayi ya nufi kofar fita" bazakayiwa anty sallam ba??" eh kice mata na tafi" fita tayi da niyyar rakashi har bakin motarsa tarakashi" sannan yatafi".

Dawowa tayi tayiwa anty sallama, sannan tafito da niyyar wucewa gida,

Turus tayi na ganin wayannan mutanen masu *bibiyarta* sunyi parking motarsu," wata zuciya ce da tunkarota" yau ko kasheta za'suyi saita tunkaresu".

Cikin karfin zuciya ta tunkaresu" gabanta sai faduwa yakeyi".

Cikin wani irin mamaki mutanen suke kallonta ganin su take tunkarowa."

To be continued

_Ur's_
_Z33yyb3rw3r_

. *BIBIYATA AKEYI*
_
_Bismillahirahmanirrahim_

_
Writting by
© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )

_
*_Ina mika sakon ta'aziyata ga feedoh yar ficika marubuciyar (matata gimbyata)narashin mahaifiya Allah yajikanta"._*
*yakuma sa aljanna ce makomarta, idan namu yazo Allah yasa mucika da imanii" ameen*

*

Page 25

*
Cikin mamaki suka tsaya kallonta," na ganin su take nufowa ".

Har takai tsakiyan titin wani mummunan tsoro ya dira a zuciyarta".

Juyawa tayi da sauri, da niyyar komawa".

Tsayuwa sukayi suna kallonta," su kansu sunsan tayi kokari," shekara da shekaru, suna *bibiyarta* kuma sun dade da gane cewa ta fahimci ana binta amma ko sau daya bata ta6a tunkararsu ba,"

Sun sani tabbas yau sotakeyi tasan kosu suwaye??"

Wata zuciyar ce takara tunzurota" shinke haka zaki zauna ana *bibiyarki* bakisan kosu suwaye ba?? "

Ko dalilin *bibiyarki* dasukeyi yakamata ki sani wata zuciyar ta kara tunzura ta."

Kara juyawa tayi ta nufesu, alokacin zuciyarata sai dar-dar takeyi."

Ganin yanda suma suka zuba mata idanuwa ne" yasata tsayawa cak,"

Alokacin wani mai mashin ya karyo kwata."

Kasancewar anguwar bamai jama'a bane yasa abun hawa basu cika wucewa ta layin ba,"


Irin 'yan isakan yara masuji da tashen girma ne, wanda suna kallon kowa suka kade bbu mai Iya daukan mataki, dan suna kallon iyayensu sunada kudi. "

Ganinta atsaye a tsakiyar titin dake GRA kano road, yasa ya Kara karfin gudun _power bike_ din dan aganinsa rainin hankali ne ta tsaya atsakiyar titin,"

Kanta ya nufa gadan-gadan da wani mugun gudu kamar me shirin tashi sama, "

Hankalinta kwata kwata baya jikinta, wanda Ita batamasan da zuwansa ba,"

Gani kawai tayi daya daga Cikin, wayannan mutanen yabude motar ya nufeta gadan-gadan Cikin sauri, "

Wani Irin razana tayi," ganinsa ya nufota gashi takasa motsawa konan da can, "

Gani tayi yana matsowa kusa da Ita, ya daga kafanshi kaman mai shirin yin naushi," sa hannu wanta biyu tayi ta kare kanta tana jiran saukan naushi kawai."

Rufe idonta tayi Ruf!! Jin shiru yasa tabude idanuwanta, budesu yayi dai-dai da lokacin da yasa kafa ya naushi mai mashin din dayazo dapp da Ita da niyyar kadeta,

"iyah! Kacin razana ta razana, ganin mai mashin din da yake shirin kadeta, yayi gefe mashin din yayi gefe,"

Wani Irin buguwa yayi, ganin hakan yayi" sanadiyar da yasa ta kwala Wani raza nenen ihuu!!

Sosai tarazana ganin mutumin ko motsi bayayi alamun ya bugu, dayawa, "


Juyawa tayi afusace wajan wannan mutumi,"

Cikin tsiwa tafara magana."

Aibashi yakamata kakasahe ba " nizaka kashe, dan bashi ne wanda kukayi tsawon shekaru kuna neman hallakawa ba"

Cikin kuka tace menayi muku ne kam da baza kubarni nayi rayuwata ba??"

Wai kusuwaye mah??"

Ganin yayi shiru yana kallon ta ne yasa tace"

Au nagane dan ku bakowa bane face azzalumai masu maida rayuwar mutum kamar ta dabba,

Meye ka tsaya kana kallo na , ka kasheni mana, tafada Cikin karaji,"

Cikin nuna girmamawa ga wanda akeyiwa magana da ladabi, kamar wanda yake wajan wanda yagirmeshi, yafara magana."

Kiyi hakuri "mam" hakkinmu ne kare lafiyarki, iya tsawon lokutan da akadauka mana. "

Duk Wani amsosin tambayoyin ki" k'ijiyesu kina gab da samun amsoshinsu, dan lokaci kalilan ne yarage" tabbas nasan kinada tarin tambayoyi amma ki ajiyesu saura kiris" mutumin dazai amsa miki yana tafe."

Ina so kisa aganinsa muka masu cutar dake bane."

Yana fadin haka yajuya" zuwaga dayan, har lokacin ta na tsaye ko motsawa batayi ba" sai magan ganunsa ne suke mata yawo a kwakwalwanta,"

Magana sukeyi amma batasan mai sukace ba taga ya tsaida adai-daita, ya nufota,

Alama yamata da ta shiga bbu musu tashiga.

Tana kallo yayi wajan wannan na kwancen itakuma mai adai-daita yaja suka tafi dayan ya biyo bayanta."

Suna isa tacire five hundret, kojiran change batayi ba tashige gida da sauri-sauri gudu - gudu, ko sallama batayi ba ta bude kofan dake jikin gate din tawuce ciki."

Direct d'akin

Please Login or Register in order to submit comment