Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sannan ta d'auka gyalenta baki kirin tasa, dakuma bak'iin flat shoe." shima Farin yadii ya saka mai aikin bak'ii, sannan da bak'iin links, bak'iin takalmi, da hula bak'a, sunyiii masifar kyau idan kagansu,"
kansu fita sanda *hanna* tamusu selfie, fesa turare yakeyi tamiqa masa hannu alamun yabata, girgiza kai yayi yace wannan turaren yayi k'arfii za'ayita kallonki fa, zaija hankalin mutane, turo baki tayi tace, to ai dakai zanyii tafiyan, idan aka kalleni saika hararesu, k'in bata yayi tayi narai-narai da ido kamar mai shirin yin kuka." miqa mata yayi da saurii, tasake fuska takar6a," murmushi yayi yana kallonta, tana fesawa yak'ura mata ido yace, cutie naga alamun kindawo drama queen, kaman asmy d'in AJ." dariya tayi tace nidai dear, asmy tafini rikicii, fara gaba yayi yace toh najii, mutafii time is going, futowa tayi harsun fara jerawa tayi saurin yin gaba, dan kadasu ummii sugansu haknne yasa tawuce gaba." hakan kuwa bak'aramin kyau yayiba." gabaki d'aya sai suka d'auki hankalin mutannen palour d'in dan bak'aramin kyau sukayiba."
Kuma sundace da juna, sosai da cewar su tafito, sauk'a sukayi har zuwa gabansu, d'an sosa kai yayi sannan yace, uhmmmm bari mud'an fita, murmushi ummii tayi tace saikun dawo, Itama umma murmushin kawai tayi, sai mundawo *hanna* tace sannan tajuya suka nufiii hanya, muryar labba ne tatsayarda ita cawe, plz antys asiyo mana ice cream, toh dear kawai *hanna* tace, harta juya, muryar intisar takatsesu da cewa, kujirani, am bored here, Zaman ya gundu renii, juyawa *hanna* ranta abace lallai yarinyarnan y'ar rainin hankaline," itama ummii har ranta batajii da d'in yanda intisar ta nuna zata bisu ba, dan hakan shiga hakk'ii ne, amma bazatayi maganaba, dan batason rikicii yanzu saita fad'awa kilishii kan anmata wulakancii." 6atarai MG yayi yace, baki kallon y'an uwanki azaune agidane, uhmmmm su daban ai, nidai nagajii, yabud'e baki zaik'arayin magana *hanna* tayi saurin riqo hannunsa, juyawa yayi ya kalleta, girgiza masa kai tayi, sannan tajuya ta kalli intisar tace kizo mutafii, yatsina fuska tayi ta surii gyalenta, juyawa yayi yakalli, hameeda yace ku taso mutafii, wani bak'iin cikine yatokare intisar amma dai dukda hakan aita hanasu jin dad'ii." tashi sukayi suka d'auki mayafinsu, labba ma cike da haushin intisar, kwata-kwata abunda tayi bata kyautaba, tasan kowaye aka masa hakan bawai dad'ii zaijii ba."
marshall ne yafara futa, itakuma *hanna* tatsaya jiransu su fita tare, atsaye taga, marshall abakin wata black car, mai tinted bak'ii wulik." k'arasawa tayi gabansa tace munfitoo, kuzo mutafii, yace, labba ne tayi saurin katse zancen da cewa yaa yareema, dama kasa d'aya daga cikin soldier's dinka yajamuu, sai mubiku abaya."
Murmushin jin dad'in shawararta yayi yace, allrt habibty barina masa magana, harara intisar tawatsawa labba, itakuwa labba ta d'auke kai kamar bataganii ba."
Dawoawa yayi yanuna musu motar yace, kuje cann ga motarnan, hameeda da labba ne suka nufii motar suna tad'insu, itakuwa intisar tsayawa tayi ba abun tace takoma ba." haushi duk yacikata."
Juyawa tayi cikin bak'iin ciki ta nufii d'aya motan."
Wani soldier ne yazo da niyyar kar6an key na motan, marshall ya tsayardashi, yace shi zaiyii driving da kansa, bbu musu yaja baya, shikuma ya bud'ewa *hanna* k'ofa sanda ta shiga tazauna sannan ya zagaya driver seat aka bud'e masa ya shiga yazauna.", d'aukan hanyan sukayi, dukda bashi kad'ai bane da soldier's amma ratansu baiyi kusada kusaba."
Yana driving d'aya hannunsa, Yana cikin na *hanna*." Yana driving ahankali suna shan hiransu abun gwanin ban sha'awa😍."
intisar a motan banda tsaki bbu abunda takeyii, ganin tacikasu suka fara tad'ii. suna shewa."

Wani k'aton mall suka nufa, bayan sun isa, yad'auki wayansa yakira soldier d'in da kejan motan su yace masa yashigarda su, duk abunda sukeso su saya." Yana ajiye wayar yajuya ya kalli *hanna* wanda itama shi d'in take kallo yace, cutiee piee, yes honeyy boo," jibi zamu koma gida, jijjaga kai tayi sannan tace inadai baka manta alqawarinda kamun ba?, ban mantaba, dear amma ai maman ma zatazo, dan za'ayi walima najii mai martaba Yana fad'ii." komadai menene idan tazo zanbita naje muyii satii, zaro ido yayi yace satii dai cutiee? eh satii, gaskiya bazan iya barinkii kiyii satii ba, hmmm kawai tace, bata k'ara cewa komaiba, aranta tana cewa idan na tafii basaiga ganni ba." kinsan me ya tambayeta, a'a ta bashi amsa, bilal fa yafad'amun yatura iyayensa sun tambaya masa, 6ta dinki hafsat kuma anbashi, yanzu haka dai saura biki," dariya tayi tace ai nidai naga alamu tun bikinmu amma tace ba haka ba, shima dariyan yayi yace yanzu ai batada bakin musu."
Shiru sukayi na y'an seconds, kwantarda kanta kafad'unsa tayi tace, kasan mene?" a'a dear saikin fad'a, inason hameeda ta aurii captain Ahmad, lumhse idanuwa yayi yace, in sha Allah, zancika miki burinkii." Shiru tasakeyi tace dear, yafii 2minute kafin yace, uhumm, yanzu idan babuni zaka manta dani sannan ka sake aureko? D'agowa yayi yadubeta yace, wani irin zance kikeyi haka? Kawai jinakeyi kamar wata rana zamu zama seprated, kwananna wasu irin mafarkai nakeyi, ganii nakeyi kamar zanmutu inbarka, ganii nakeyi kamar rayuwata ta gaba da zanyii dakai batada nis,,, daka mata wata rikicecciyar tsawa yayi wanda har jikinta sanda yafara rawa yace shutupp, shutupp, baki da hankaline, kinfara ta6uwa ne zakina mun irin wannan zancen." harwani hucii yakeyi, hannu takai zata ta6ashi yayi saurin bige hannunta, yabud'e yafice, idanuwantane yaciko da hawaye, ita kanta batasn maiyake damunta ba." goge hawayen tayi itama tafuce, cann nesa ta hangoshi, da gudu taje tayi hugging back d'insa." dasaurii yajuyo shima yayi hugging d'inta tight, yafara magana cikin tashin hankali yace, plz kada kisake mun irin wannan maganar Yana d'agamun hankali, gabaki d'aya yasa jikina yayi sanyii." kada ki kara, kwantarda kanta tayi aqirjinsa dai-dai saitin zuciyarsa, tanajii yanda zuciyarsa ke bugawa da k'arfii ga saurii." D'agowa tayi tace nabarii kayafenii, dan Allah zuciyarka tadaina bugawa da k'arfii haka." kidena tsoratata idan bakiso ta bugada k'arfii, nadaina wallhy nadaina."
Zama yayi awajen itama tabishi tazauna ta kwantarda kanta akafad'ansa," iskane mai dad'ii take kad'awa awajen, lumhse idanuwanta tayi, shikuma ya nata tunani, har yanzu zuciyarsa tasaka cire zullumin abunda *hanna* ta fad'a masa." lumhse idanuwa yayi yace cutie, uhum ta amsa alamun bacci yanason kamata." baza kisha ice cream d'in bane?" zansha mana, to ai naga bacci kikejii." kacewa hameeda tasiya mun idan muka koma saina k'ar6a." wayanta yak'ar6a yakira hameeda yace ta siya mata ice cream." Ganin bacci yacii k'arfinta yasa yad'auketa cakk yayi mota da ita."
Suna zuwa dai-dai mota saigasu sunfito, kallon takaicii intisar tamusu ta ebesu tawatsar." aranta ta kudurta, sai ta rabasu dan bazata jurii Ganin abun takaicii ba."
Sakata aback seat na motan yayi sannan ya miqawa, wani soldier car key, yashiga yakwantarda kanta acinyansa."
Har suka k'arasa gidan Suna haka lokacin baccinta yayi nauyii, d'aukanta yak'arayi yafito da ita, yadubii hameeda yace ki sakamata afrigde, yana fad'in haka yawuce, sama yahau da ita, kwantarda ita yayi sannan shima ya kwanta dan dare yayi."
Washe gari da sassafe suka shirya suka nufii get together da soldier's suka had'a, basu suka dawo ba sai dabb magrib, sallah sukayi sannan, suka cii abincii, sai alokacin *hanna* tasamu suka zauna itada yaya jalal, tad'ii sukayii sosai yana bata labarin amira tanashan dariya." sai dare sosai tukunna *hanna* tatashi tayiwa yaya jalal sallama, har ta juyawa, tajuyo takalli yaya jalal, tace yaya jalal ni bakaga wani canjii daga garenii ba?." dariya yayi yace kinyi kyau mana kanwata, girgiza kai tayi tace yaya bahaka nake nufii ba, ba ka kallon yanayina ya canja, kallonta yayi yasake yace nikam banga komai ba, meya fari?" yaya haka kawai nakejina kaman baniba, wani lokacin sai injii kamar inzauna inyitayin kuka, kokuma inshiga duniya." subhanalhi me kike fad'ii haka *hanna* wallhy nima yaya bansaniba kwata-kwata bansan abunda yake damuna ba." kinfad'awa umma ko masa?" A'a banfad'a ba yaya dan Allah kaima karka gayamusu banso hankalin su ya tashi, bazan fad'a ba amma kirink'a yin addu'a to yaya ta fad'a sannan tajuya."
Marshall dake saukowa jin irin maganrda *hanna* tajeyi yasashi tsayawa, ga baki d'aya jikinsa yayi sunyiii, baisan maiyake damun *hanna* ba?" juyawa shima yayi yafasa abunda zaiyii ya juyawa yakoma, kwanciya yayi yabawa k'ofa baya, itama shigowa tayi ta kwanta gefensa, kiran sunansa tayi jin bai amsa ba yasa ta d'auka yana baccine, kashe bedshide lamp tayi tamatso kusadashi tayi hugging back d'insa, runtse idanuwa yayi yanajin, sonta cikin ransa, ahaka bacci yayi gaba da ita, shikuma duk satan barcii haka yaganshi yabarshi."

Washe garii da sassafe flight d'insa yatashi, zuwa NIGERIA."

_Safe flight marshall and *hanna*_

To be continued

Ur's
Z33iiyyb3rw3r


. *BIBIYATA AKEYI*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

Writing by
*©zaynab bawa*
*(Z33iiyyb3rw3r)*

_Like my page on Facebook=zaynab BAWA novels_

_Join my group on Facebook= ZAYNAB BAWA NOVEL'S_

.
```Manzon Allah SAW Yana cewa," Wanda ya yi alwala, bayan ya kare alwala sai ya ce Ash-hadu alla ilAha illallAh wahadahu lasharika lahu wa anna muhammadan Abduhu wara suluhu. Allahumma Ja'alni minattauwabina waja'alni minal mutadhahhirina.
Duk wanda ya fadi wannan bayan gama Alwalar sa to za'a bude masa kofofin Aljanna guda takwas ya zabi wadda ya ke son shiga.```


```Manzon Allah SAW Yana cewa," Wanda ya yi alwala bayan ya kammala alwalar sa kaf, sai ya ce Subhanakallahumma Wabihamdika ash -hadu allah Ilaha illallah anta astagfiruka wa'atubu ilaika.
Zaa rubuta wannan acikin wata takarda baza'a bude ta ba sai ranar lahira ya ga alkhairin da ke cikin ta.```

================

*wayyo Allah cikina😂😂😂😂 u guys are funny, BIBIYATA AKEYI FANS, WALLHY kunyi arayuwa, ranar nacii dariya Allah, Ina la6e Ina kallaonku, masu kuka yanzu kuka fara fa tamm🤷‍♀ Danni Dai bbu ruwana."😬😛 saidai kada acikamin group da hawaye."😭 Hawwer😘 darling wato hadda ke ay'an kuka nidai bzan hanaku ba🤷‍♀ bbu ruwana." _~ILYSM~_* ```INASONKU HAR CIKIN RAINA```😍❤

================

page 82

*
Cikin jirgii *hanna* nazaune kusada Marshall, ta kwantarda kanta akafad'ansa, tayi shiru alamun wani abun take tunanii."
Shikuma marshall yak'ura mata idanuwa kawai ganin yanda tayi nisa Cikin tunani."
Wata doguwar ajiyar zuciya tasauk'e, sannan ta lumhse idanuwanta, kallonta yakeyi ko kiftawa bbu, itakuma bata dad'e da rufe idanuwa ba bacci yad'auketa."
Shima runtse idanuwansa yayi Cikin zuciyarsa yana addu'a ya Allah kada ka jarabceni da abunda bazan iyaba, ya Allah kada ka nunamin ranarda zan rasa *hanna* arayuwata, bansan wani halii zai shiga ba." Ahaka har jirginsu yayi landing *hanna* tana bacci, baisan katseta daga baccinta data lula kuma alamun baccin yana mata dad'ii, hakanne yasa ya cewa su ummii su fara gaba, shi zai k'araso daga baya, akawai abunda zaiyine, su ummiii way'anda sukazo taryansu daga fadah sukabii," shikuma yazauna jiran *hanna*, ga mutane dayawa dasuka zo taryansa, kama daga shugaban k'asa governor's, ambasador's ministers, Senate, dasauran su."
Tafii 30 minute tana bacci, wata ajiyar zuciya tasaki, sannan tayi miqa ta had'a da addu'an farkawa daga bacci, ware idanuwanta tafarayi, akansa ta ware idanuwannata tass, murmushi yasakar mata, itama murmushin tamayar masa," juyawa tayi da niyyar ganin su umma amma taga wayam dasauri tamiqe tazauna, zaro ido tayi tace ina ummii suke?"
Suntafii gida." zaro ido tayi tace toh mu me muka tsaya yi?." kajimun yarinya, me kike tunanin natsaya yii, kozan tasheki a bacci ne?" ehem, common tashi mutafii." marairaice fuska tayi tace yi hak'uri dear, aida ka tasheni." intasheki kuma?." A'a kam gaskiya bazan iyaba." yanzu kawai tashi muje, nasan ana jirana." miqewa tayi tada'uko gyalenta ta yafa." ya riqo hannunta suka futa." ana bud'e door na flight d'in, flashes ne suka fara kashe musu ido, sa hannu *hanna* tayi ta k'are fuskanta, saida tad'an dad'e kafin tabud'e fuskan." sojojine atsaye bakin jet d'in, alamu ya nuna sundad'e a tsaye awajen," suna sauk'owa mutanen da sukazo taryansu, suma suka k'arasaso, hannu suka fara bashi kowannen su wasu na haugging d'in sa." amma dukda haka hannunsa yana cikin na *hanna* gam yariqeta, dan yasan *hanna* yanzu saita rikice batason hayaniya sosai, barin yanda yalurada ita kwana kinnan."
Ahaka har suka rakashi zuwa ga mota, duk yanda y'an jarida sukaso zantawa dashi bai tsayaaba, damuwarsa yakai *hanna* gida ta huta, dakansa ya bud'e wa *hanna* Mota tashiga yayinda mutanen wajan tsan-tsan mamaki ya tsaresu, lallai sun tabbatr duk Mulkin mutum sayya sauk'arda Kai a wajan mace, bud'e masa motan akayi sai shima ya shiga, haka suka tafii gayya guda zuwa fadah."
Bayan sun isa ne aka bud'e k'ofan *hanna* tayi saurin fita tanufii shashin ummii." su kuma dasauran jama'a aka wuce cikin fadah."
A palour tasamu su ummii nan ta shiga tayi sallololinta tafito, tasamu abinciii tacii sannan tazauna A palour tarashe."
Data gajii da zaman ne tashige d'akin labba takwanta dan batajin dad'in jikinta." bacci tayi sosai sai Bayan sallan magrib tatashi." tayi sallan ta sannan tak'ara dawowa palourn tasamii ummii, su afeeya sun tafii."
Har kusan k'arfe 9 tana wajan ummii, sai lokacin marshall yazo suka wuce shashin su, komai agyare suka sameshi." saboda gajiya wanka kawai sukayi sannan suka kwanta."
Washe gari kuwa agida suka yini bawanda yafita, dan sun dad'e basu samii hutu irin hakaba."
Suna zaune afalo hanna tad'aura k'afofinta kan cinyan marshall tana danne danne awayanta," kallonta marshall yayi ya maido duk hamkalinsa gareta, yace, cutie, uhmm ta amsa, yakamata kije kingaida umma (kilishi) yau," kinsan gobe bbu lokacii kina wajan zancen walimah, bata d'ago ta kalleshi ba tace, zuwa jimawa zanje." tom kawai yace yacigaba da kallonsa dayakeyi."

K'arfe takwas dai-dai *hanna* ta zumbula hijabinta tanufii shashin kilishii koda taje a palour tasameta, da fara'a, kilishii ta k'ar6eta sai riritata takeyii, itakuwa *hanna* taji dad'in hakan, kilishii ne tayi wata y'ar dariyar da kana kallonta kasan ta munafurcii ne tace, y'ata nashiga tashin hankali sosai, lokacin tafiyarsu yareema, gashi kuma kema kika shiga wani hali, ga baki d'aya hankalin mu atashe yake, mungaza sukunii, sunkuyarda kanta *hanna* tayi tace, ai gashi mundawo umma yanzu hankalin ku zai kwanta, wata dariyar kilishii tak'arayi tace ai kuwa y'arnan, yanzu munjii sanyii sosai." aff kinga na sha'afah tun d'azu nahad'a miki zobo akan zan aika miki tunda kinzo aisai ki tafii dashi tafad'a tana miqewa, wani irin kwad'ayine yazowa *hanna* gabaki d'aya yawunta ya tsinke, Allah Allah takeyi akawo zo6on tasamu tasha, Har wani had'iye miyau takeyii."
Da k'aton jug kilishii tadawo riqe ahannunta, ajiyewa tayi agaban *hanna*, cikin kunya *hanna* tace umma a'iina zan samu cup, inaso nasha ne," dasaurii kilishii takwala wa wata kuyanga kira, umarnii tamata data d'auko cup, bata dad'e ba kuwa tadawo hannunta riqeda cup, ajiyewa tayi agaban *hanna* sannan tanemi izini ta zuba mata, k'ar6a *hanna* tayi takafa bakin ta tahausha zuciyarta d'aya, sanda tashanye sannan tatshi zata fita, umarnii kilishii tayi da a d'auki jug d'in abita dashi, godiya tayi sosai sannan tafice."
Wata dariyar rainin hankali kilishii tayi tacce lallai wannan yarinya, shsshasha ce, kokad'an batasan mai sonta ba, inbanda abinki niceh zan miki zo6on? toko shi mijinnaki baikai wannan matsayinba, taja tsaki."
Itakuwa *hanna* tana komawa sashenta, da kad'an kad'an taringa shan zo6on harta shanye tass, dan wani irin kwadayin zo6onne yakamata."
Sanda tashanye kafin ta tuno bata ragewa Marshall ba, d'aga kafad'unta tayi🤷‍♀, sannan tace ohow, idan yazo zangaya masa." dan tunda yafita d'azu haryanzu bataga idanuwansa ba, shirye shirye bikkunan da za'ayi yasa Marshall baidawo gidaba Sai kusan 10:15pm." *hanna* na jiransa afalo dan yakanyii wuya ta iya bacci idan baikusada ita shiyasa take jiransa Yadawo." da sallama yashigo ta amsa masa tana murmushi, yana zuwa ya zauna kusada ita."
Sannu da dawowa yauwa cutie ya gidan?" Lafiya klau, ya ayyukan? klau cutie na, gaskiya yakamata abarmunkai ka huta haka, uhmm ainakusa fara hutuna, sai nayi months banfita ko nan da door ba, dariya *hanna* tayi sannan tace," kahuta Sai kayi wanka naga Kamar agajiye kake, kaman kinsani nagaji dayawa." yafii 30minute akwance a cinyanta, idanuwansa alumshe, amma Kuma ba bacci yakeyii ba." *hanna* na wasa da gashin giransa dake had'e waje d'aya, bud'e idanuwansa yayi yace dear nagama hutun zanyi wanka." ok tom tashi muje."
Bayan yafito awankane Har yayi shirin kwanciya, *hanna* ta dubeshi, afff namanta honey, naje nagaida umma, harta bani zo6o." gaban Marshall ne yayi mugun fad'uwa Jin ta ambacii zo6o, shikqnsa baisan dalilin fad'uwar gabanba." shiru yayi baice komaiba, Sai Bayan *hanna* takwanta Har bacci nashirin ebanta, cutie yakira sunanata, uhmm ta amsa alamun bacci yafara kamata." kinsha zo6onne?"
Uhmm nasha kayi hak'urii ban bar makaba amma gobe zanyi mana wani." I LOVE YOU, yafad'a tana k'ara gyara kwanciyarta, uhmm kawaii yace baik'arayin maganaba."
Kusan 3 nadare hanna ke kwance tana baccinta,
Shikuma Marshall Yana sallah, dan tunda *hanna* tafara way'annan irin abubuwan, bai iya bacci."
Bayan ya idarda sallan yazauna Yana addu'oii wani irin ihuu *hanna* takwala, tatashi tana ihuu tana riqe kanta, tana cewa honey zasu kashenii, gasuncan, wayyo Allah tak'ara sake wani ihunn, tana shirin sauk'a daga gadon, da gudu Marshall yayi kanta."

To be continued

Ur's

z33iiyybawa

*BIBIYATA AKEYI*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

Writing by
*©zaynab bawa*
*(Z33iiyyb3rw3r)*

_Like my page on Facebook=zaynab BAWA novels_

_Join my group on Facebook= ZAYNAB BAWA NOVEL'S_

```Wani sahabi yace, rana mun kasance muna Sallah a bayan Manzon Allah (S.A.W) da Annabi ya dakko daga ruku'u sai ya ce Sami'Allahu Liman Hamidahu sai wani mutum daga cikin sahabbai yace Rabbana Walakal Hamdu, Handan Kasiran Dayyiban Mubarakan Fihi da aka gama sai Manzon Allah ya waiwayo sai ya ce Wanene ya fadi wannan sai mutumin yace Ni ne ya Manzon Allah sai Manzon Allah ya ce Naga Malaika talatin da "yan kai suna rigagato wazai rubuta wannan aiki yaje ya gayawa Allah.```

.
================

Page 83
*

Riqeta yayi, tayin saurin shigewa jikinsa tana kuka tanacewa Wallhy zasu kamanii."
Shhhhh yasa hannu abakinta dear bbu wanda xai kamaki." kiyi shiru."
Shirun tayi tana ajiyar zuciya addu'oii yaringa tofamata Amma duk da haka tak'i sakeshi, Kuma tak'yin bacci."
Kiran sallah ne yasashi yatashi yanufii band'aki kank'ameshi tayi tace Ina zakaje?" toilet zanyii alwala ankira sallah." girgiza Kai tayi Kamar mai shirin yin kuka tace dan Allah kayi sallah anan kada kafita, murnusawa yayi sannan yace tom dear taso muje muyi alwala, tare kuwa sukayi dan ko nan dacan bataso yamatsa, bayan sun idarda sallan ne yace cutie jeki kwanta nizan futa."
Girgiza masa Kai tayi hawaye na shirin zuba, matsowa kuasada ita yayi yace ya rabb, bazan fitaba maza wipe ur tear's, bbu musu ta goge hawayan," Jan hannunta yayi yakwantarda ita Shima yakwanta kuasada ita." addu'a yayi ta mata Har tayi bacci." Sanda yaga baccin nata yayi nisa ne, yazare jikinsa yafice, dan biki za'ayii a government house, na murnar cigabanda k'asar tasamu na marshall." 7:00.am dai-dai, *hanna* taji Ana tashinta, cutie, cutie, uhummm ta amsa cikin muryar Mai bacci, tashi maza, bak'i zasu fara zuwa baki shiryaba." toh tace tana k'okarin miqewa, tashi tayi tazauna tana murmurza idanuwanta." cikin shagwa6a tace wallhy ni hone,,,,,,,, saurin yin shiru tayi ganin yadda ta bud'e idanuwa bataga komaiba." wani tsorone ya ziyarcii zuciyarta." tashi tayi jikinta Yana 6ari tayi bandaki, Kai tsaye bud'ewa tayi kozataganshi, nanma Wayan Kuma batajii bud'e k'ofa ba." suran wayanta tayi tafuta, abakin k'ofa tatsaya tatambayi wani soldier nan yashaida mata ai tun asuba yafita, bata iya komawa cikin gidanba, Kiran labba tayi tace, habibty dan Allah kizo yanzu kitayani zama, toh labba tace sannan takashe Wayan."
Kiran hameeda tayi nan ma tace da'allah tazo." jiran labba tayi Sanda tak'araso sannan suga shiga tare."
Tad'ii suka zauna yii, ba'adade ba kuwa saiga hameeda nan tashigo itada hafsat, dagudu ta rungume hafsat tana murnar ganinta."
Sunfii 15 minute suna hira kafin *hanna* taji muryar ammah, aikuwa da gudu tatashi tayi Kan Amma, itama Amma murnar ganinta takeyii." sauk'a sosai *hanna* tamata Har tarasa mame zata kawo mata." Ammah batafii 20 minute ba tatashi tace Jalal na jiranta amota." kuka *hanna* tasaka tana cewa haba Ammah na, wata na nawa bangan Kiba? Da kina zuwa zakice Zaki tafii."
Jawota Ammah tayi tana fad'in haba d'iyata, kibar kuka, zuwa jimawa zandawo dakyar ta lallasheta tayi shiru."
K'arfe 4 dai-dai akafara walima, zuwa 6 aka gama, mama batazoba, saboda su karima."
*Hanna* sashinta tawuce, bayan angama, tayi sallah ne tashiga kitchen, tafara had'a masa abincii, bata d'auki lokacii ba tagama dan dama bawani Mai nauyii bane."
D'aki tashiga tayi sallan isha, tafito tashiga kitchen dan dawoda abincin dining." da k'arfii ta ji muryar Marshall Yana cewa cutieee, itama da k'arfin ta amsa, yess honey, am home, ok boo am coming tafad'a tana wanke hannuwanta tafito."
Wayam tagani babu kowa afalon da k'arfiii tace honey where are you?" Jin shiru yasata shiga d'ayan falon nanma shiru babu kowa, Kuma da'alamu ba'a bud'e k'ofaba."
Komawa tayi nan danan jikinta yad'auki rawa, kudin dinewa tayi Akan Kujera, sai Kusan 11:30 taji k'arar bud'e k'ofa lokacin tayi kuka harta gaji, abubuwan dataji a wannan lokacii naban tsoro baya fad'uwa." Jin bud'e k'ofa tayi saurin juyawa." ganin Marshall dasaurii tak'arasa da gudu ta rungumoshi, tana cewa honey kafita dani daga gidannan, wallhy akwai aljanu aciki nibazan iya zamaba." kuka takeyii Kamar ranta zai futa."
Rungume ta yayi sosai Yana rattshinta, Amma *hanna* ta birkice masa, bayanda baiyiba daga baya Kuma tafara ihuu Kamar wata mai aljanu."
Da k'arfinsa yariqota ya rungume tsam ajikinsa." bayadda batayi ta kwace kanta ba, Amma takasa, dan ko jijjiga bayayi." Sanda yaga tadaina muzul muzul yad'agota, idanuwansa sunyii jawur, yarasa maiyake damun *hanna*, yarasa tayadda zai shawo Kan matsalarta."
Ido ya k'ura mata ganin yanda take sauk'e ajiyar zuciya."
K'ara maida ita jikinsa yayi, ganin bacci yad'auketa yasashi tashi da ita yanufii Sama, kwantarda ita yayi sannan Shima yawanta agefenta, Sanda yakai 2hours kafin yatashi yad'auro alwala, yafara nafila."
Bashi yatashi daga sallaya ba, saida yauma Kamar jiya, da ihun *hanna*, yaukam Har Gari yawaye bbu wanda ya k'ara rintsawa acikinsu."
Gari na wayewa Kuma wani irin bacci yad'auketa,"
Sai 12 tafarka,"
Marshall yab'oye damuwarsa kwataa kwataa yakii gayawa ummii maiyake faruwa, dan gani yakeyi Kamar zaishawo Kan matsalar."
Ahaka ya wunii bbu yanda yajeshi Yana tareda *hanna* itama bataso yafitan dan haka yazauna."
Saida 9 nadare yayi suna zaune akujera, sallamar intisar ce ta ziyarcii kunnuwansu."
Amsawa sukayi ta shigo tazauna, gaisheda Marshall tayi tazauna, sannan ayatsine tadubii *hanna* tace sannuu, *hanna* Kuma ko kallonta batayiba. Balle tasan tanayii."
Miqewa Marshall yayi yace yawwa tunda ga intisarnan barina shiga wajan ummii na nemo Miki kindirmon kijiranii yanzu zandawo." to kawaii tace yamata peck a forehead ya fice." haryad'an fara tafiya yatuno bai tambayeta da yamrii takeso kokuma furaba, juyawa yayi yakoma palour d'in." muryar intisar ce takatseshi daga magarnarda yake shirin yii, tana cewa aike banza ce tunda nafad'a miki Saina rabaki dashi Kuma baki hannani kusantar yanda yakeba." idon Marshall harwani k'ankancewa sukeyi tsabar 6acin rai, idanda kalmar daya tsana arayuwarsa bai wuce a ambacii rabuwa tsakaninsa da *hanna* ba." cii gaba tayi dacewa, Kuma nayi rantsuwa bazanyi kaffara ba, sai kin d'andani rashinsa akusadake." *hanna* wacce kwataa kwataa batason hayaniya ta lumshe idanuwanta ko tanka mata batayiba."
Wata tsawa Marshall yadaka mata wacce ba ita d'aya ba Har *hanna* Sanda tarazana, Yana k'arasowa wajan yad'auketa da marii, bata ankara ba yak'ara mata wani."
Saida tafad'ii Kan kujera yanunata da yatsa yace fucemin, fucemin nace tun kafin na tattaka ki." da gudu tafice tana kallon tara-tara wani ikon Allah ne kawaii yakawota sashin kilishi, Jin kukanta kilishi tafito da gudu, ganin fuskar intisar akumbure, Maiya sameki? tafara tambaya, cikin kuka intisar tafad'a mata abunda yafaru." Wata ashar kilishi ta lailayo tasake, dan kaza kazansa Akan wannan matar tasa zaimiki haka to wallhy

Please Login or Register in order to submit comment