Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Shahid tace na fahimcii kinason Yara Allah ybaki masu albarka, akunyace ta amsa ta amin. "
Tamakar kanwarsu suka d'auketa suka runga bata shawarwarii,"
Fita rakasu sukayi saida jirginsu yatshi sannan, suka d'auko hanyar dawowa,"
Ganin *hanna* tayi shiru yasa yacewa driver yasanar da sauran idan sun samii wajan da ake siyarda chocolate su tsaya, "
*Hanna* tajishi Amma taba kulaba, Hakan dazaiyi bashi zaisa ta manta alkawarin da jiya yamata na kaitq taga umma ba."
Sanda akazo daidai wajen suka tsaya,"
Bud'ewa tayi zata Fita, yace Ina zakije?"
Ai basusan irin chocolate d'in da nakesoba, "
Sai aka fad'a miki make zansayawa?"
Idan ba niba waye?" tafad'a had'eda Bud'ewa tafice,"
Shiga tayi ta za6o chocolate kala-kala wani soja yabiya kud'in suka nufo hanyar Fita, jitayi tabigi mutun gamm,"
Ledan hanjuntane tafad'ii, cewa yarinyar tayi Wanda zata d'an girmii *hanna* kamarda shekara biyu tace kiyi hakiri dan Allah dake *hanna* ne da laipy, "
Kasa amsawa tayi tatsaya tana kallon *hanna* dan tabatrwa, tana tunano sunanda mahaifinta yagaya mata, *hanna* Kuma ta tsuguna dan d'aukan ledanta, Sanda tajira tad'ago tace mata,"
Dan Allah sunanki *hanna*? eh *hanna* ta amsa da rashin yarda afuskarta,"
Sannan tace wacece ke? "
Zancenda akeyi a TV dake manne awajanne yasawa karima fashewa da matsanancin kuka,"
Alokacin *hanna* takai idonta wajan subhanallhi ta furta lokacin aka nuno gawar ministers of health, alullu6e data matarsa, "
Gidansa yayi gobara, sannan Ana sanarda cikiyar iyalansa ba'asamu gawarsu ba, Kuma ba'agansu ba."
Juyawa *hanna* tayi idanuwanta taff da Kwalla da niyyar ficewa, karimane ta cafko hannunta Wanda Hakan yasa d'aya daga cikin sojojin da sukazo da *hanna* ya nufota da niyyar dukanta, "
Hanashi *hanna* tayi tace baiwar Allah sake mun hannu zantafii, muryarta Har na shid'ewa tace, kiyiwa girman Allah kitafii damu, inahh?"😳
*Hanna* tazaro ido," gidanki dan Allah, dai-dai ta nutsuwarta *hanna* tayi tace intafii daku ku suwa? "
Nuna mata TV karima tayi tace,"
Mune iyalansa da ake nema, wallahy ba gobara bane kashesu akayi, idan kika barii suka tafii damu muma zasu kashemu, jikin *hanna* ne yad'auki b'ari dasauri taja hannunta ta nufii Mota da ita, jaa tayi ta turje tace akwai kannena a can na b'oyesu, shiga *hanna* tace tayi itakuma ta tura wani soldier yaje ya ebosu,"
Suka shige motocin, duk abunda akeyi MG baya ganii hankalinsa nakan wayarda akamasa ake sanar dashi mutuwar minister,"
Yana ajiye wayar *hanna* ta bud'e tashiga, shigewa jikinsa tayi ta k'ankameshi tsamm,"
Jin yanda zuciyarta ke bugawa dasauri yanuna masa alamun ta tsorata. "
Abinda yakawo ransa kawai shine taga gawarsu minister ne a TV,"
Lallashinta yakeyi yana buga bayanta ahaka suka d'auki hanyar komawa gida. "

To be continued

Ur's
*Z33iiyyb3rw3r*

*BIBIYATA AKEYI*

_Bismillahirrahmanirrahim_

Writing by
© _Zaynab Bawa_
( _z33iiyyb3rw3r_ )

*Allah subhanahu wata Ala yace," duk mutumin dakafii k'auna dashi za'a tasheka ranar tashin k'iyama, * Ya rabb ka k'ara mana k'aunar manzonka acikin zuqatan mu, Ameen."*

*Ka/ki kasance mai yawan tuna mutuwa, domin hakan zaisa ka/ki kasance cikin tsoron Allah."*

*Kada ki/ka kasance mai k'askantarda mutane," domin bakisan wataran waye mai taimakon kaba."*


*Nasiha ce*

================

_Wannan shafii sadaukarwane ga duk wani masoyin *BIBIYATA AKEYI* inasonku ina alfaharii daku, dabazarku nake taka rawa_💃

Page 64

*
Najeeb ne zaune gaban mahaifinsa, jinayi mahaifinsa yana cewa Wai najeebu mai kakeson fad'amunne eyeh? "
Mai kakeson nafad'awa mahaifin yarinyar?"
Sunkuyarda kansa yayi yace Abba wallhy bana sonta, kabani time in Sha Allah zanfito da mata. "
Nisawa mahaifiyar sa dake kusa dasu tayi, tace tunda ya amince Kan cewa zai fito da wata, ni aganina abarshi, yanzu ai godiya zamu yiwa Allah daya amince zaiyi auren,"
Macene za'a iya aura mata Wanda bataso tazauna Amma namiji abin zaiyi wahalan gaske."
Maida gilashin idonsa yayi sannan yace to Allah yaza6arda mafii alkhairii,"
Bari nasamu mahaifinta namasa bayanii, zai fahimta, mutum ne mai sauk'in kai, godiya najeeb yayi sannan yatashi yafice,"
Tunanin yakeyi aranshi yanzu idan yasamu Wanda tamasa zai sanarda mahaifinsa, dan yanzu yagama cire *hanna* ababin rayuwarsa, duk da cewa tana cikin zuciyarsa."

Fadah suka shiga, sannan yace ma *hanna* *sweety * kishiga nizantabii, akwai aikinda zanyi."
Kallonsa tayi tace akwai abu mai mahimmanci danakeso muyi Magana akai."
Kallonta yayi yace kibari saina dawo, ankirani gidan minister of health yayi k'one, girgiza kai tayi tace ba k'onewa yayiba k'onawa akayi, "
Zaro ido yayi yace,"
Kinsan me kike fad'a kuwa? "
D'aga kai tayi tace, eh nasani, yanzu hakama iyalansa sunanan na taho dasu, Kuma itace ta sanar danii haka,"
Suna inahh? "
Yatambaya nuna masa motar bayansu tayi tace suna cikin can,"
Fito dasu ku shiga gida inazuwa, ina zakaje? ta tambaya,"
Babu zan biyoku Abaya,"
Zan yiwa soldier's magana ne,"
Bud'e motar tayi tafita, sannnan ta Isa zuwaga motarsu, kar6an kabir tayi dake hannun sa'ad tafara tafiya suka biyota,"
Side d'insu ta shiga suka biyota Abaya,"
Kafin su zaauna har MG ya iso dan dama ahankali suke tafiya,"
Zama sukayi, yayinda k'anannin yaran sun kasa zama zubewa sukayi ak'asa,"
*Hanna* ce tace inkaiku kushiga kuyi wanka? "
Abida cikin muryar kuka tace wallhy bazan iyaba, yunwa nakejii,"
Idon *hanna* har yakawo ruwa na tausayinsu, shikuwa MG binsu kawai yakeyi da kallo na tausayinsu. "
Sa'ad ne yak'ar6e yace yau kwananmu uku bamucii komaiba."
Alokacin Idon *hanna* hawaye yak'i tsayuwa, " Shikuwa MG sa tafin hannuwansa yayi kawai yarufe fuskarsa tausayi da takaicii, bazai barii yace komai ba. "
Jansu d'ayan falon *hanna* tayi tad'auko wermer's d'in da sukacii abincii, zuba musu tayi kowa da nasa sannnan ta ebo ruwa da roba tabasu suka wanke hannu,"
Faracin abincin sukayi kamar wasu mawuyacin zakii, ko k'akkautawa bbu. "
Hassana har tana kwaruwa, kuka ne ya cufcewa *hanna* tayi saurin barin falon,"
D'akinta tashiga ta ringa kukan tausayin bayin Allah nan, "
MG ne yashigo yaja jikinsa yana rarrashi,"
Ce mata yayi yanzu anemo likita ya duba su, nizan tafii wajen, wani likita kake ganii za'a nemo? "
Wa kake ganii zai riqe Amana, dan ita babbarsu ta tabbatarmun, nemansu sukeyi zasu kashesu, wani likita kake ganii zai iya yin shiru da bakinsa?."
Niasawa yayi dan MG shi kwata-kwata ma yaman ta cewa akwai doctor acikin sojojinsa."
Shiru *hanna* tayi nad'an wani lokaci sannan tace,"
Barina kira Yaya Jalal yazoshi,"
Shid'in doctor ne? "
MG Yatambaya, eh kawai tace,"
D'aukan wayrta tayi takira Yaya Jalal, ringing uku yad'auka,"
Gaisheshi tayi Jin muryar ta kaman tayi kuka, yace, *hanna* lafiya? "
Lafiya klau Yaya Jalal, dan Allah kazo gidana, and Yaya idan zakazo kazo da first aid box d'inka,"
Rikicewa yayi yana cewa *hanna* kifad'amun abunda yasameki? "
Bbu da Yaya kawai saikazo dan Allah kayi saurii tana fad'in haka ta katse Wayan,"
Tass Sanda suka tashi da abincinan,"
Alokacin tafita tasamu wani soldier, ta aikeshi yasiyowa su sa'ad, kabir Hassana da usaina Kaya, amma su Abida da karima nata zai masu."
D'ayan flate d'in da MG yazauna kafin auransu ta nufa dasu, dan ahad'e yake da nasu saidai wata y'ar k'ofa da corridor dake tsakanii."
Bud'ewa sa'ad d'aki d'aya tayi, sannan ta bud'e d'aki d'aya masu karima,"
Haka kawai ta tsincii kanta da kishin d'akin da MG yazauna tak'ii Bud'ewa,"
Sa'ad Bayan yayi wanka yayi wa kabir, alokacin ankawo kayansu basu tayi sukasa, sannan Alokacin Yaya Jalal ya'iso, treatment d'in ciwowin dake jikinsu yayi sannnan, suka shiga danyin bacci su huta, "
Fitowa sukayi shikuwa Yaya jalal yafi to,"
Kallan *hanna* yayi yace, wallhy nad'auka wani abune yafaru danaji muryarki bbu alamun walwala aciki, " yaya ainace Maka bbu komai, Kuma kqima ksan bazan Maka k'aryaba,"
Sallama sukayi harya juya zantafii *hanna* tace yaya, juyowa yayi, tace kada kadamu kanka da tambayan su waye idan lokacii yayi zan sanar dakai, murmushi yayi yace, nasan baki abuu sai mai amfanii dan haka bazan damu kainaba, "
Sallama sukayi ya wuce, sai Alokacin *hanna* tasamu tayi sallar adhahar, dan lokacin biyu tayi," k'ara Zuwa tayi ta dubasu, har lokacin bacci sukeyi dan yaya Jalal harda maganin bacci yabasu. " sai 3 MG yadawo Alokacin *hanna* nakwance akujera ankawo abincii Amma takasa ta6awa, wata irin kewar MG dake damunta,"
Samunta yayi ahaka yak'arasa gabanta, tana kallonsa tamiqe, sannan ta tura baki tace, takafii kawani dad'e, kinyi missing d'inane ya tambaya, girgiza kai tayi tace niii? Aknme? "
A'a, kokad'qn baijii dad'in amsartaba, canja akalar zancen yayi Zuwa, kincii abincii?"
Girgiza kai tayi tace ina jiranka ne, d'an karamin tsuka yaja afili, azuciya Kuma yace kajii mun yarinya da kini bibi, natambayta tayi messing d'ina Kuma tace A'a, "
Tashi muje kicii abincin, A'a muje kafara wanka tafad'a atakaice,"
Zakimun wankan ne? " yqtambaya, niii A'a *hanna* tafad'a had'eda Zaro ido."
Gyara zamansa yayi yace Kinga ni kuwa idan bazakimun ba, is better na hak'ura."
Shareshi tayi kamar bata jisu ba,"
Ganin tana 6ata masa lokacin yasa yahaura yayi wankansa, "
Kamshin turarensa ne doki hancinta, D'aga idanuwa tayi tana kallon sa yanda yake saukowa,"
Fara polo ce kall ajikinsa, sai bak'in wandon Jean's, sai bak'in takalmi, yatsun kafarsa sai suka haska sosai, kamar kita6a jini yafi to, gashin sai sheki farcunansa sukeyi, "
D'auke kanta tayi kada ya kamata tana kallonsa, kawarda idanunta tayi dan karya kamata tana kallonsa, abunda batasaniba yad'ade da Ganin tana kallonshi,"
Kallonta yayi yanda kayan yanzu sukafii k'arbanta fiyeda na d'atsu, "
Akowani shiga tayi k'ara kyau takemasa,"
Bayan yak'arsso sukacii abincii sannan ta d'auki basu takai musu,"
Bayan sungama cii ne, *hanna* ta kira MG, shigowa yayi da sallama suka amsa dukansu, "
Kallonsa dukanta suka tsayayi, dan tabbas idan Ana nufiin had'uwa MG karshe ne."
Ran *hanna* Sanda yad'an sosu ganin irin kallon dasuke masa, "
Kusada ita yazauna, yariqo hannunta, duka suka zauna, karimane tace sa'ad tashiga da hassana da hussaina da kabir d'aki yadawo,"
Bayan yadawo karima tafara basu labarin da mahaifinta yabasu bata rage ba Har izuwa biyosu da'akayi dakuma, ganin *hanna* datayi, tak'ara da cewa, mahaifina yanada y'an uwa dayawa, yanada dangii bila adad'in haka Kuma mahaifiyarmu ma, Amma mahaifina kune yatsaba, way'anda zasu taimaka mana, pic d'inki yabamu yace mu naimeki, dan naiman mijinki zaimana wahala,"
Sannan tafashe da kuka, itama *hanna* kuka sukeyi,"
Balle su abida da sa'ad da sukajii cewa mahaifinsu ya rasu, "
Nisawa MG yayi yace, yanzu haka zannema muku wajanda zaku zauna,"
Dan jibi sassafe zamuyi tafiya ina dawowa Akan, case d'innan zan sauka, Allah yajikansu yabaku hakurin rashinsu, dak'yar karima ta iya amsawa da amin."
Mamaki ne yacika *hanna* ita batasan da wannan tafiya ba, Kuma tajii suu ya ambata. "
Fita yayi *hanna* Kuma tatsaya rarrashinsu."


Tsawa najii andaka masa awqya, sannan akace duk yanda kasan zaka shiga kanemo su kashiga."
Ramka ya dad'e duk wani lungu da sako munbii basanan,"
Sannan wannan gidan, kuwa munduba bbu komai sannan akwai kayayakinsu da wayoyinsu. "
Kuma mun dasu iya dawowa gidan, shiyasa mukasa tsaro ko dasu dawo."

To be continued

Ur's

*Z33iiyyb3rw3r*

*BIBIYATA AKEYI*

_Bismillahirrahmanirrahim_

Writing by
© _Zaynab Bawa_
( _z33iiyyb3rw3r_ )

_Like my page on Facebook :::Zaynab BAWA novels_

Followed me on instagram ::::mhiz_z33iiyyb3rw3r

*Ka/ki zama mai biyayya Wa iyayenki/ka, domin samun rahamar ubangiji."*

*Ka/ki zama mai tuna alkhairii duk k'an k'ancinsa."*

*^Kada ki/ka zama mai son kanka/ki akowani lokacii," Domin manzon Allah yace imanin d'ayanku bazai cika ba harsayya sowa d'an uwansa abunda yake sowa kansa."^*

================

_Yabon gwani yazamq dole, gakiya *SAFIYYA ABUDULLAHI HUGUMA* kinyi matuk'ar k'ok'qri, wajen fad'akarwa, awannan litttafinki na *ABADAN*,_ _Allah yasa ka miki da alkhairansa ta hanyoyi daban daban, Allah yakawo haske cikin_ _rayuwarki, kamar yanda kikasa haske muma acikinnamu_ _rayuwar,"_ _Allah ya albarkacii rayuwarki,_ _yabaki zuri'a tqgqrii,"_
_Ameen ya Allah,"_
_Ya Allah ina tawassali da sunayenka kayiwa wannan baiwa taka albarka, kamar yanda ta tunasar damu da hadisai masu ingancii da asalii."_

================

Page 65

*
Saida taga hankalinsu ya d'an kwanta sannan ta nufii nata shashin, sai 5 hameeda tazota sunyi hira sosai, hameeda sai tsokanar *hanna* takeyi, ganin *hanna* tak'i kulata yasata tunanin MG ya kashe bakinne, Itakuwa *hanna* tausayin ay'annan bayin Allah ne yacika ta,"
Dariya hameeda ta kyalkyale tace Wai, su *hanna* anjii maza baki yayi shiru, aini band'auka akwai abunda zai kashe bakinnan ba,"
Tsaki *hanna* taja tace da'allah malama ni kindameni, idan bazakiyi shiruba Allah saina bar miki falon," Dariya hameeda ta gimtse tace," yi hakurii bani nakar Zoman ba rataya akabanii."
Tsaki *hanna* tak'araja sannan ta juya mata baya. "
Duk wata zolayqrta da hameeda takeyi bata kulata ba, dan tasan ba Hakan bane."
Kiran sqllar magrib ne yasa hameeda tashi da niyyar tafiya, ruk'ota *hanna* tayi tace hava Sis, gaskiya bazakitafii yanzuba, kibari yadawo sai mutafii tare,"
Bud'e baki hameeda tayi tace, kina amaryar zaki fitafita?."
Murgud'a baki *hanna* tayi tace to sai me? "
D'azuma munfita, Allah yashiryeki hameeda tace sannan tace nifa tafiya zanyii,"
Sama *hanna* tahaura t ebo mata turaruka kayan kwalliya, da abubuwa kala-kala."
Har bakin k'ofa tarakota, tana shirin fita hameeda tace kinga ki koma baki tambayi mijinki ba."
Hararanta *hanna* tayi kawai, tad'an rakata tace beb samun abun hawafa zaimiki wuya a, Allah kinga dare yayi."
Suna tsaye saiga captain Ahmad yazo dasauri zaije masallaci,"
Ganin *hanna* atsaye yasashi nufan wajan, tmbyanta yayi mai sukeyi, nan tashaida masa cewa hameeda ce zata tafii, "
Kollon hameeda yayi yad'an basar, yana gyara hannun rigarsa yace," tajira nayi sallah nakaita. "
Yana fad'in haka ya juya yqtafii." . Gidan suka koma Ana idarda sallah, yazo yayiwa *hanna* Magana tarakatq Har gaban mootar, sannan suka tafii tanajin kewar y'ar uwartata,"
Bata dad'e da tafiya ba labba tashigo,, da harara *hanna* tabita tace, " wato akawoni gidanku a ajiyenii, Amma ko leqe, dama bukatarku tabiya nashigo ko?"
Kama kinnuwanta tayi tace afuwan, wallhy tun 12 nakeso nashigo ummii tahanani Wai ba'a Zuwa gidan amare,"
Wallhy bbu yanda banyiba tahanani yanzu ma sulalewa nayi bata sanii ba."
Dariya *hanna* tayi tace dan Allah kaji ummii menene agidanmun da ba za'a zoba? "
Uhmmm kawai labba tace dan batasaon taja maganar."
Hira sukayi sosai *hanna* tajii dad'iin zuwanta sosai, "
MG nafita daga masallaci shashin ummii yawuce, zaunawa yayi akusa da ita bayan ya gaisheta ta amsa."
Cikin sakin fuska tana tambayarsa ya *hanna* sosa kayi yayi sannan yace ummii tun kafin la'asar nafita sai yanzu zan koma, fad'a ummii tabishi dashi sosai tana cewa yad'auko yar mutane zai tafii yabarta ita kad'ai,"
Hak'uri yabata sannan yasanar da ita rasuwar minister dakuma tafiyar data taso jibi,"
Addu'a tamasa Amma Har cikin ranta bataso tafiyar ba."
Amma dai zaka tafii da ita ko?"
D'ago kansa yayi dakekan cinyarta, yace ummii zantafii da ita bansan lokacin da tafiyar zata d'auka ba."
Addu'a ummii tamusu sannan tarinqa masa nasiha akan yarigeta da amana. "
D'aurawa tayi da cewa nasan kana sonta so mai tsanani Amma hakan bashi zaisa nadaina maka nasihar riqeta da amana ba."
Nasan cewa zuciya batada k'ashi, Kuma dole wataran duk dad'ii akan samuu sa6ani, k'arqmar yarinya ce, dole saikayi hakurii harda irin furucinta, sannan abuu na biyu, kaji tsoron Allah kasan yana ganinka, kada ka zalumcii yarinyar mutane."
Nasiha sosai ummii tamasa mai ratsa jiki, " Sannan tace yatashi yatafii yabarta ita kadai."
Tashi yayi yafita,"
Baiwuce gidaba sannin cewa tana tare dasu karima, yasa yawuce shaidawa mai martaba."
Tashi labba tayi tace kada ummii tanemeta tamata sallama tafita,"
Tashi tayi ta nufii shashin su karima, sanda ta tabbatar ta basu komai dazasu buk'ata sannan tajuya zata tafii, muryar karima ne takatseta, mungode Allah yasaka muku da mafificin alkhairinsa, murmushi kawai hanna tayi afili acikin ranta Kuma tace ameen, Juyawa tayi ta futa."
Nasu shahsin tashiga, kawai ganin mutum tayi harta tsorata, sai zuciyarta ta hasko mata taga fuskan awajen diner d'insu, da fara'a tqk'arasa tana mata sannu da zuwa, daqyar ta amsa, gaisheta *hanna* tayi nan ma intisar kamar mai ciwon baki tace lpy."
Ganin haka dake *hanna* ita kanta miskilar kantane, yasa ta ebeta ta watsar."
Sunfii 10 minute bbu Wanda yacewa wani k'ala *hanna* na danne-danne awayrta, Itakuwa tad'aura d'aya kan d'aya taunar chwengum kawai takeyi."
K'as K'as ne ya ishi *hanna* yasa tad'anja tsaki, d'agowa intisar tayi tace, owh srry baki sanni bako, ni cousine d'in sace, owh namanta Kuma budurwarsa, gaban *hanna* ne yayi masifar fad'uwa, lokacii d' aya qirjinta yafara bugun taratara, har wani dushi-dushi take kallo,"
Srry baikamata kisani yanzu ba, Amma gani nayi bbu yanda na iya yakamta ace kinsan wata na shigowa kada ki bararraje,"
Kinsan fa duk nisan jifa k'asa zai dawo,"
Sannan kada kiyi tunani ko wasa nake miki, ki rubuta ki ajiye Har indai inadarai, ya yareema kamar na aureshi angama."
Ta bud'e baki zata k'arayin magana, sqiga sallamar MG, kawarda kai *hanna* tayi azuciyar tana cewa munafuki azzalumii kawai, saurin tuba tayi tana agtasfirulla tunowa da tayi cewa, ma mijinta take fad'awa way'annan kalamai koda azuciyarsane."
Kallon *hanna* yayi yaga yanda ta kawarda kai kamar batajii shigowarsa b, Kuma yanada tabbacin tasan shigowarsa, aransane yace kowa yata6omin yar fitinar tawa, ko rshin dawowata da wurii ne yasa,"
Zuwa dabb da ita yayi sannan yace, sweety wayo ta6ominke?"
Yitayi kamar batajishi ba danko Juyawa batayiba." Muryar intisar ce takatseshi, na cewa sannu da Zuwa ya yareema,
Juyawa yayi ya kalleta, wata irin kunyace takamashi matarsa takasa yi masa sannu Amma wata tamasa, murmushi yayi yace yawwa habeebty yaushe kika shigo?"
Gaban *hanna* ne yayi masifar fad'uwa jinda sunan daya karata wato ya tabbata cewa, ita budurwarshi ce."
Wani irin zafii zuciyarta tafarayi mata,"
Kwallah yacika idanuwanta taff,"
Wannan wani irin ciin fuska ne agabanta yana kiran wata habeebty, lallai dama abunda take gudu kenan tasan cewa MG ba tsaran ta bane, dole zai nemi kyakkyawa da ajee kamarsa, "
Shikuwa MG anasa wajen habeebty daya ambata al'adansu ne tun suna yara aka taso dasu da fad'in wannan kalmar ma y'an uwansu,"
Dan kowa yatashi dason kowa acikin zuciyarsa."
Kok'ad'an dayasan wannan kalma zata k'ona rana *hanna* dabai fad'a ba."
Cikin kissaa da kisisina intisar tace habeeby dear inkawo maka ruwane? "
Kallon *hanna* yayi Wanda kanta ke gefe ganin ba tasan da halittarsa awajan ba sai jikinsa yayi sanyii sosai."
K'ara cewa tayi nagaa amaryar tamu najiin kunya ne."
Shiru yayi sannan yace ok tom, Danshi MG arayiwarsa bai iya baonsa mutumba, "
Tashi tayi tafii hanyar falon data hango frigde aciki tanayi tana karairaya."
Shikuwa Wanda takeyi dominsa baima saniva dan hankalinsa nakan sweetynsa, tashi yayi yazo wajanta, yana tambayarta maiyafaru Amma firr tak'ii magana, bayanda beyiba hankalinsa ne yatashi, baisandai menene ba Amma ya lura kamar Zaman intisar ne ya6ata mata rai, idankuwa hakanne mai take nufii kenan?" batason yan uwansa kome? "
Dawowa tayi da robar fayrouz ahannun ta dakuma na swan, tana Zuwa ta ajiye."
Kallonsu ahaka ya sosa mata rai amma tadake tace ya habeeby dear gashi nakawo maka, tashi yayi da toh, ya isa wajan, intisar hadda kissaa ma Amma asali tafii ki ransa da yaa yareema,ganin yanzu tanayi baya gwaleta ne yasata zak'ewa."
Fayrouz ta Zuba masa acup yak'arba yana Sha, nanne Kuma hakurin *hanna* yak'are ganin cewa dazasucii abinciin rana tad'auko masa fayrouz yace ta canja Amma yanzu ya k'arba, lallai yanzu tayarda namiji dakalin majina ne ka haushi ka sule,"
Shikuwa MG ganin ita matarshine yanadakyau tasan abunda yakeso da Wanda bayaso yasa yace ta canja Itakuwa intisar da saninta da rashin sa bbu amfanii."
Tashii tayi da gudu tayi sama tana Zuwa ta kwanta akan gado tacii gaba da kuka."
Shikuwa MG yayi niyyar binta amma intisar ta tsareshi da sururtu ba ita tasakeshiba sai 10, a lokacin *hanna* tayi kuka Har k'arfinta yak'are tayi samada 2hour's tana kuka."
Banda nishi da ajiyar zuciya bbu abunda take iyawa."
Bayan ya kulle k'ofa d'akinta yfara nufa, ayanayin daya ganta yai, bala'in birkitashi."
Dasauri yak'arsa yad'agota yasata ajikinsa hannu biyu tasa tana dukansa tana tureshi, "
Amma bai kyaleta ba, sanda ya manna ta dajikinsa yacii gaba da lallashi."
Sai kusan 10 tukun tabar dukansa tafara ajiyan zuciya, ganin yak'ii saketa yasata dallara masa cizo ak'irjii, runtse ido yayi yajii zafiin Amma zafin kukanda takeyi yafii k'onashi. "
Ahaka Har bacci yqd'uketa, Jin saukar numfashinta ya tabatrs masa sannu hakan."
Tunanii kala-kala yarunga yi arnsa, sannan shima ahaka bacci yad'aukeshi. "

To be continued

Ur's
*Z33iiyyb3rw3r*

*BIBIYATA AKEYI*

_Bismillahirrahmanirrahim_

Writing by
© _Zaynab Bawa_
( _z33iiyyb3rw3r_ )

_Like my page on Facebook :::Zaynab BAWA novels_

Followed me on instagram ::::mhiz_z33iiyyb3rw3r

Ka/ki zamo mai yawan karanta, ```Allahumma ajirni fi musibati, wa'aklifli khairan minha``` aduk lokacin ka/ki ke cikin wata musiba."

Ka/ki kasance mai karanta ```Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahla, wa'anta taji'alul amra iza shi'itah sahla``` aduk lokacinda wani abuu yashige maki/ka duhu, kukoma kanajin wuyar aikata abun."

*Ka/ki kasance mai karanta,* *```Allahumma antassalamuwaminkal salam tabarak ta ya zul jalalu wal'ikram``` *aduk sallah bayan ka/kin idar."*

*Shawara ce*

================

Page 66
*
Ahaka har kiran sallan farko."
Bud'e idanuwanta tayi ahqnkali da suka mata nauyi, har sund'an kumbura."
Jinta ajikin mutum yasata d'agowa tana dubansa, bacci yakeyi azaune, ita kumbura tana jikinsa gabaki d'aya, tausayinsa ne yakamata tatsaya tana kallon sa yana sauke numfashi ahankalii."
Bud'e hannunshi tayi tasauk'a da niyyar zuwa toilet tad'auro alwala dinyin sallar raka'atanil fijr."
Har tafara tafiya ya ruqota, gabantane yahau fad'uwa dan batayi tunanin ya farkaba, abunda tamasa jiyane yadawo mata, harda cizon data masa, wata irin kunyar sace ta lullu6eta." tashi yayi yazo dabb da ita, itakuna ta sunkuyarda kai k'asa yace ina zakije." alwala zanyi tabashi amsa, sanyi yajii aransa, jinyadda ta amsa masa that means tadaina fushin kenan, murmushi yayi sannan yace, kiyi hak'uri kinjii, kiyi hakuri if i hurt u knwnly or u knwnly, wallhy bansan ganin hawayenki, zafii nakeji acikin raina,"
Hawaye ya sulalo afuskarta dasaurii ta sa hannu da niyyar gogewa, yayisaurin riqe hannun yace,"
Sweety akawai abunda namiki plz kisanar dani."
Shiru tayi yajawota jikinsa, lafewa tayi ak'rjinsa, amma tayi shiru, jijjiaga yayi yace plz say ur mind dear, cikin son yin kuka tace bakai bane kace mata habeebty, gabansane yayi mugun fad'uwa, yaja hannunta suka zauna akan gado yace, Sweety duk family d'inmu haka muke kiran juna, ko bakiji haka nake kiran labba bane, turo baki *hanna* tayi tace, shine itama hadda wani cemaka habeeby dear, ita kuma labba aibabu aure atsakaninku, tafad'a hawaye na gangarowa fuskarta, babban yatsansa yasa ya goge mata hawayen, yace,"
Kiyi hakuri daga yau nabarii."
Gyada kai tayi tace shine ka kar6i fayrouz ahannunta kasha nikuma kace nacanja maka."
Dear ainii banga amfanin cewa ta canjaminba."
Kinga ke matatace dole kisan abunda nakeso da wanda banso, itakuwa banga amfanin saninta ba."
Murmushi tayi tace najii amma Allah kadena kallonta, nadena sarkin kishii, sanda yafad'ii kalmar kishii saikuma kunya takamata."
Gyaran murya yayi sannan yace, haryanzu fa tunanin yanda za'akaisu nakeyi, suwa?" *hanna* tatambaya saikuma tace owh srry natuna way'annan yaran, sake baki MG yayi yace babbar cikinsufa tabaki samada shekara biyu amma kike kiransu yara."
Aidai ita yarinyace tunda nayi aure itakuma batayiba."
Bud'e baki

Please Login or Register in order to submit comment