Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kama hafsat kusamman ya da Aunty surayyah ke faman masifa akan ya rainawa mutane hankali,ko cewa akayi dashi basuda aikin yi,Wayan hafsa ne tayi qara tana dubawa taga number dinshi,a dake ta daga wayar sabida ba shakka ta shaqa yau kam,yace da ita

"Hafsat ki fito idan kina masauki ina reception na hotel din" da mamaki ta kalli Aunty surayya dake gefenta tana uban mita,sannan tace dashi "A dubai din?" tsaki yaja yace

"Noo a india,danla malama kizo ina reception ma wurin nace dake ko mun fara wasan banza ne haka?" cikin jin zafin gwasaletan da yayi tace "Kayi hakuri ganinan zuwa" kallonta surayya ta

"Keda waye kuma Ina zakije?"

"Muhammad ne wai yana wajen reception ashe yazo,kuma shi da number shi yake amfani niban sani ba" kallon ta tayi "Au dama shima zezo kika barni ina surfa mar ashar?"

"wlhy Aunty bansan zezo ba,ni kawai zancen dan rakiya yamun" jinjina kai Aunty tayi

"Wannan shegen muhammad din anyi miskilin masifa,ko wa yakewa iya shegen oho,jeki kiji" batace komai ba ta zari dan mitsitin mayafi tafito ga rigar irin straight gown din nan ne na roba ya kameta over, tun daga nesa tana ganin fuskarsa tasan akwai magana a d'an tsorace ta karaso wurin da yake,zama tayi kusa dashi a kujerar da yake tace

"Sannu da zuwa yaa muhammad ya hanya?" kallonta yayi fuskarnan a daure yace "Banasan ya hanyar ki sabida jirgi daya muka zo daku ai,sannan wlhy mintuna goma na baki ki sako sutura dan wannan bakida banbanci tsirara,idan kuma na kuma ganinki da makaman ciyar wannan shigan wlhy sena sassab'a miki,sekace ba 'yar musulmi ba" kallonshi tayi se a lokacin ta tuna yanayinta,waifa ita tayi shigar ne a zuwan tazo garin farar fata kartayi qauyanci, jiki a mace ta miqe,zuwa tayi ta cire kayan ta sako abaya baqa har qasa tayi talha ta fito,surayya na ganin yanayinta tasan shigarta yayiwa masifa amma dai vata dameta da tambaya ba,koda tazo baya nan,wayarta ta daga takirashi amma be dauka ba,anan ta zauna tafi 30 mnt be dawo ba ta qara wayar tashi gaba daya ma tajita a kashe,gwiwa a sace ta koma dakin tace da Aunty surayya wai yace gobe zasuyi magana,kallo daya surayya ta mata kuwa ta fahimci da babbar matsala.......

Washe gari tun asuba ta koma parlor tayi kiransa a waya,yana kallonta harta tsinke be daga ba, kusan 3 msd col,kawai seta fara hawaye tama rasa dalilin daya sanya take damuwa dashi zuciyarta sam batayi adalciba,data saka masa wannan tsoron na muhammad,tana cikin wannan tunanin taji qarar shigowar message

"Room no 10,2nd floor" shine abinda ya aiko mata sarai tabgane nufinsa ta sameshi acan,miqewa tayi ta saka hijab dinta tayi hanyar daze sadata da wurin....knockin tayi yazo ya bude fuskarsa a hade,gaidashi tayi sannan ya janye mata ta shige a daya daga cikin kujerun parlor din ta zauna,ta qura masa ido,shima din ita yake kallo,yaukam seda tagaji da kallon nashi ido cikin ido sannan tace "Kayi hakuri bazan qaraba inshaa Allah" amaimakon ya baiwa maganarta muhimmanci se cewa yayi da ita "Meya faru kike kirana daga yin sallan asuba?" tama rasa mezata ce masa,se kawai ta miqe "zan koma bacci zanyi" tazaci ze dakatar da ita amma bece mata komai ba harta fice,a ranta kuwa taji zafin sa sosai....

*Nigeria*

Sun dawo lapiya dauke da lefe da ban mamaki, har masifa su daddy sukayi,amma surayya tace dasu tamasa magana yace hafsa matar sace,babu kuwa wanda ze qayyade masa yawan suturun dayake buqatar wadata su da ita,kuma ya jibgo dogwayen riguna da qananun kaya over.......Aikam rana daya akayi daurin auren muhammad da hafsat,se kuma Shammaz da maryam,kuma aranar aka kai amaren biyu,wanda sam koda ma akayi auren hajia halima batada labari tana wurin gantalen ta dubai,acewarta taje saro kaya shikuwa da gayya ya ganta,yan uwanta kuwa dasuka ga pictures na ebar hankali da ba indiya se hankalinsu ya mugun tashi,amma sam basu sanar mata wai shaam yayi sabuwar amarya ba.......

Hafsat kuwa tunda yan kai Amarya suka watse wuraren karfe goma na dare seta soma jin tsoron zaman gidan ita kadai, shi kuwa be leqo bama se sha daya da rabi, Abinci ya kawo mata sannan ya sanya hannu ya yane mayafin dake jikinta ya ajiye gefe ya kalleta, "Kina bazawara wani kunya zakiji,zaki wani lullub'e fuska" sosai maganar sa ya doki qirjinta amma bata nuna masa komai ba kurun dai murmushi tayi masa,ganin haka ya sanya yace "Kici abinci kazane da drinks ga youghurt da ice cream idan zaki sha" kallon su tayi tace "Gaskia Alhamdulillah na koshi,sedai zuwa safiya" miqewa yayi be wani damuba,kizo ki kulle kofofin gidan ni zan tafi seda safe" ko motsawa batayi ba daga inda take sabida mamakin daya bata,to gidan uban wa ze kwana?" ta tambayi kanta,ganin fa tsorone ze hallakata ya sanya harya kai parlor ta rugo ta riqe masa hannu,da mamaki ya kalleta tace dashi

"Yaa muhammad zan bika dan Allah" juyowa yayi yabfuskance ta gaba daya "Ina zaki bini hafsat?"

"Inda zakaje mana"

"Ba inda zani fa, gidan zainab zanje na kwana,kishiyarki" tafi minti uku tana kallanshi, juyawa yayi ze fita ta riqe masa hannu again "Bazan iya kwana anan ni kadai ba,tsoro nakeji" murmushi yayi

"Ni ban aureki danna tayaki kwana ba hajiya,ko mun rubuta haka acikin agreement namu?" gaba ki daya tsoro ne ya taso mata ta kalleshi sosai tace cikin dakiya idanta yayi ja sosai amma batasan tayi kuka "Na tuna kuwa babu wannan acikin rubutaccen auren mu,na manta bayan signing takardar yarjejeniya da mukayi ta aure,wurin daurin auren ma mun rubuta cewar kalar auren namu na dabanne ba wanda musulunci ya tsara ba,Kaje amma karka qara kawomun komai daya shafi rayuwar aure,idan bazamu kwana a tare ba babu wani abu dazakamun na aure,na yarda haka tsarin namu auren yake,kaje plss" tafad'a tana me d'addage hannayenta duka biyu alamar naci ka fam, matsowa yayi daf da ita ya sanya hannunsa asaman waist nata yamatse ta sosai da jikinsa yace "Ni kike gayawa magana hafsa? Sabida kin samu sake ko? Yanzu ma idanta ta dago sukayi kaura dana juna tace cikin jin haushin sa

"So nake muyi sighning wani yarjejeniya kanka tafi" sakinta yayi yace yana murmushi muje gayamun wane iri ne?" zama sukayi a kujerun parlor tace

"Sona ke mu kwana a roof daya,muci abinci atare,mu sake wa juna soyayya,mu aminta mudin masoya ne,idan har akayi watanni shida kaci cewar baka buqatar tarawa dani,kuma bakaji sona ko daya a ranka ba,to ka rabu dani,kuma tsakani da Allah zamuyi" kallonta yayi ya kwashe da dariya ya sani yanajin tausayinta amma sam baya santa wlhy, yakuma san baze taba san taba,da wannan ya aminta suka rubuta suka ajiye.....

Hafsat ta kuma yin wauta a karo na biyu,yaya kuke zanin wannan zaman? Ze dore kuwa?" anya hafsat bata kirawa kanta zawarci na biyu ba bayan shaam ya aure fara me gashi abinshi? Muje zuwa dai.....

Votes pls
[2/13, 9:28 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)

Wattpadd@ 68billygaladanchi

*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*


27

Muhammad a d'akinsa ya kwana yayinda hafsa ta kwana a nata d'akin,wata hatsabibiyar rigar bacci ta saka iya cinya,da saninta ta cire bra,pant kawai ne ajikinta se wannan rigar,sumar kanta datasha gyara ta gama barbajewa har saman goshinta daga bed room nata tafito zuwa kitchen,a parlor ta hangoshi zaune duk da zuciyarta takad'a qirjinta se dokawa yakeyi amma haka ta daure,tasani idan bata koyawa kanta rashin tsoron shiba akwai matsala,kallon ta yayi sosai ya raya aranshi so take taja ra'ayinshi wanda baze tab'a faruwa ba har gaban abada, bata ko kalli inda yake ba tayi gaba abinta zuwa kitchen,d'an guntun tsaki yaja ya mayarda dubanshi zuwaga film dayake kalla, Ha d'adden break fast tabshirya musu,finger sandwichs da chocolate sandwich,se kuma coffee amor da vegetable potatoe, tun yana daure wa har qamshin yasoma jan hankalinsa,ogar bata baro ktchn ba sanda ta hada samosa, jere komai tayi a fankacecen dining table,ta bude dining shelf ta baje komai da komai da ake buqata,bata wani kalleshiba sabida sam ma yi tayi tamkar bata kula dashi ba,dakinta ta wuce tasha wanka da wata doguwar rigar dress maroon color ta tufke gashin kanta da farin ribon,se flat shoe data saka shima fari qal, har tsakiyar falon ta sameshi kusa dashi sosai ta zauna ta kalleshi dauke da fara'a sosai a fuskarta,tana bude bakinta qamshi alawar datakesha ya daki hancin sa dauke kanshi yayi gefe d'aya

"Barka da safiya yaa muhammad da fatar ka tashi lapiya?" dan juyar da kanshi yayi gefe daya sannan yace

"Barka dai,kin tashi lapiya" Murmushi tayi

"Breakfast kai kadai yake jira oga muhammad kose kayi wanka ne?" dagowa yayi dukda beso ba kasancewar tunda yayi aure da zainab,be taba tashi tabgayar dashi ba kuma yauce rana ta farko da mace ta gabatar masa da abinci,sedai kuku ne yake dafa masa,miqewa yayi yace muje dining d'in" kai tsaye tayi kokarin shiga gabanshi dauke da tafiya me daukar hankali gabaki daya gogan seya shagala da kallon mazaunan ta,susucewa yayi ya wani zama tamkar wani soko,sanda tace dashi "ka zauna plss" zama yayi yaga irin abubuwan data girka acikin lokaci qanqanin,yakuma san be rigada ya kawo cook a gidan ba dama niyyanshi yau da rana ze gabatar mata dashi "Mezan saka maka?" ta katse masa tunani da wannan tambayar

"finger sandwich and veg potatoe zansha wancan abun kuma" batayi musu ba ta zuba masa komai da yace ta matso kusa dashi sosai wai bashi zatayi,kallon ta yayi ya d'an had'e fuska "Meye hakan hafsat?" kafe shi tayi da idanta "Yaa muhammad da kaina zan baka mana" a yanayin yanda tayi magana seya ganta kamar wata yar sha biyu kasa cewa komai yayi se bude bakin dayayi ta aika masa sanwch din ya gutsura,sosai yaji dadin abuncin yama manta inda yake har samosa seda yaci yasha coffee Amor dinshi sosai sannan ya daga mata hannu a lamar ya qoshi,kallon shagwab'a ta masa

"Saura ni ka bani" dan mur ya qara sha "Na baki kuma me kenan?" Take ta hado shagwababbiyar fuska "Abuncin mana" tsaki yaja ya miqe kawai tashi tayi ta bi ta gabanshi tana doddoka kafa wanda ilahirin jikinta motsi yake tana kuma qunquni akan bazata maci abuncin ba yau gaba daya...bin bayanta yayi da kallo harta wuce ned room nata,girgiza kanshi yayi ya dawo parlor ya zauna ganin tafi 1 hour bata fito ba ya sanya ya bita ciki da kanshi, a kwance ya taddata rubda ciki takalmin kafarta kurin ta cire da zata kwanta amma komai najikinta nanan,mazaunan ta sun qara bajewa a yananyin kwanciyar datayi ji yayi tamkar ya sanya hannun sa ya taba wata zuciyar ta haneshi gyaran murya yayi yace

"Hafsa mesa bazakiyi breakfast ba?" tana daga kwancen bata juyo ba tace "Bakai bane kace wai baraka feeding na da kanka ba,ni Allah bazan ciba idan baraka bani ba" shiru ya danyi kanyace

"Naji muje zan baki" mirginowa tayi ta kiqa masa hannun ta waiya dagata,badan yaso ba ya miqa nasa hannun ya dagota,laushin hannunta kawai ya sanyashi runtse idansa cikeda kasala,a parlor kuwa seda ta koshi sannan tace dashi wai ita atabau seya dagata zuwa cikin parlor cikinta ya mata nauyi bazata iya tafiya ba, kallonta yayi yanaso yace kin cika rigima amma ya kasa,dagatan yayi ta wani lafe jikinsa har sukaje parlo ya direta ya zauna saman 3 siter zuwa tayi ta kwanta ta daura kanta saman cinyar sa tace dashi "Ka sosamun kaina zanyi bacci" bece da ita komai ba,aka soma knockin na gidan,dagata yayi yaje ya bude,kukun da yake jirane,koda aka nuna wa hafsat shi masifa ta saka akan itace da kanta zatana girka abunci,dole kuwa ya kyaleta ya sallami kukun, kallon ta yayi bayan fitar kukin yace da ita

"Hafsat mesa kin cika rigima ne? Idan ma bakya buqatar sa mesa zakimun haka a gabansa? Seki bari idan ya tafi ko? Karki qara mun haka nan kina jina ko?" dan kallonshi tayi sekuma ta dake "Idan kayi hakuri kome zanyi ai na 6 month ne ka jira idan matar daba ta yarjejeniya ba tazo ka murza mata iko" sororo yayi yana kallonta ita harta wuce part dinsa, gyara masa dakin tayi ta kwashe kayansa ta wurga a loundry basket sannan ta yaye boxers nashi da singlet data ga ya cire ta wanke su ta shanya a toilet nasa, towel dinsa ta daura tayi wanka,tana fito wa ta ganshi asaman gadon dauke kanta tayi daga dubansa,tazo tana rawar sanyi, kusa dashi ta zauna ta rungumoshi gaba d'aya ta gabanshi "Yaa muhammad ka rufeni da jikinka akwai sanyi wlhy" gabaki daya ta gama da matsalar malam muhammadu,kasa ko motsin kirki yayi sanda taji daidai sannan ta miqe bayanta ya qurawa ido,taje mirror ta dakko wani mai tazo ta zauna,shidai yau ta gama rufe masa baki,shafa manta ta zauna tayi kamar kuma wacce aka tsikara ta laquto man ta janyo hannunshi ta saka aciki,juyawa tayi ta rage towel nata zuwa tsarar ta tace "Hannuna baze kaiba nika shafamun" shiru yayi dole ya murza man ya shiga shafe bayanta dashi,se wani lumshe ido yakeyi soft skin nata na daukar masa hankali sosai.....

Da yamma yace da ita tazo su shiga bangaren zainab,ba musu ta caba ado suka wuce part din na zainab, suna zuwa parlor ya kalli wata yarinyar yace "Ki mata iso wurin zeezee" ya juya abinshi wani bangaren.....A zaune suka taddata ana mata gyaran kai,da alama wasune daga salon sukazo mata aiki a gida,har kafafuwanta ake wanke mata,kallo daya hafsat ta mta taji ta tsaneta,matar ma kallon sheqeqe tawa hafsat

"Sannu" shine abunda tace dasu babu wanda ya koda kalleta acikinsu har masu aikin, duban su tayi tace Aunty zainab sannu" dagowa matar tayi cikeda isa tace

"Kan mijin naki yakawoki gaidani be sanar dake ba'a gaidani a tsaye ba? Kuma ba'a saka ido acikin nawa sannan kuma ba'a kiran sunana hajiya zakice" kallonta hafsa tayi ta baki,ta juya abinta kawai aranta tace "qanin uwarki zanci ni kam wlhy,kajimun masifafgiyar mata,kinjawa kanki dani kuwa rashin mutun cine,gidan kika tarar...

Kumun uzuri kaina ke ciwo
[2/14, 9:00 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)

Wattpadd@ 68billygaladanchi

*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*



28

A babban parlor na gidan hafsat ta had'u da muh'd kallanta yayi sosai ganin ranta duk a b'ace

"Kaddai harkun gama gaisawar?" kallansa itama tayi "Ta dai gama wulakanta ni,Allah bazan qara zuwa wannan part d'in ba" tana gama fadar haka ta banki kofar tayi gaba abunta,binta yayi da kallo da kallo harta kurewa ganinsa,a ranshi yace lallai wannan yarinyar dama wai haka takeda fitina?....zuwa yayi kai tsaye d'akin da zainab take,Kallo daya yayiwa ma aikatan suka saketa suka watse,mutuqe fuskarnan yayi

"Me kikawa hafsat ne?" kallon raini ta masa

"Wacece hafsat kuma?" batare daya ce kala ba ya juya da nufin fita,ya gano raini zata kawo masa "Idan wannan shegiyar fitsararriyar yarinyar kakemun wannan kallon gwara ma ka dena,sanin kanka ne nan d'in gidanane kuma kowa dole ya girmama ni sabida nice babba" cak ya tsaya jin kalamanta sannan a hankali ya juyo ya kalleta

"Gidan tane itama,ai auren mu aka daura bawai yar aiki na kawo miki ba,bakuma wai zama dadiro mukeyi da itaba,sannan da kike zancen girma aini ne me gidan idan baki girmama niba babu wanda ze girma maki wlhy,zaman lafiya nakeso kuyi da juna bawai shirmen kishi ba" miqewa tayi tazo har inda yake

"J.A ni kake kallo kace dani wai kishi? Akanwa zanyi kishin kai? Danake sanka kokuma da aka gaya maka zaman jin dadi nake a gidan naka? Kaga wlhy idan ma mafarki kake ka farka,bazan tab'a kishin kaba sabida kasani sarai ba so araina" murmushi yayi dukda yaji zafin kalamanta sannan yace
"Kamar yanda kikasan ni d'inma hakan take a wurina,nakuma auro matar so idan kin isa kem ki auro mujin so" Kallon mamaki ta masa sabida be taba cewa da ita baya santa ba se yau,qirjin tane ya doka lokaci d'aya taji ranta ya b'aci,kan tasamu bakin magana kuwa yayi gaba abinshi.... Koda ya dawo b'angaren hafsa kuwa a walk way ya sameta tanasham coffee,kallon shi tayi sosai

"Mezaka ci dinner inaso zanyi girki?" kallonta yayi sosai

"Bana cin abinda keda nauyi,so u think of something light"

"Same here" tafad'a had'e da miqewa,sanda zuka parlor ya kalleta "Zan fita akwai wani abu?" matsowa tayi sosai kusa dashi ta hada jikinta da nasa,a kumatu tayi tsalle kadan ta manna masa kiss tace tana murmurshi cikeda rashin damuwa da abinda tayi

"Ina maka fatan alkhairi,Allah ya sanya aje lafiya kuma a dawo lafiya" tana kaiwa nan ta juya abunta zuwa kitchn, yafi 3 mnts tsaye yana tunanin hafsat,tunda yake zeezee bata tab'a gwada yi masa adu'a ba akan wai ze fita ko wani abu daya shafi nasarar sa,wani sanyi yaji yana ratsa shi tamkar ruwan sanyi ayayin daka kwaso rana kake tsananin jin qishirwa, juyawa yayi ya fita amma sam bayan ya fitan seya kasa zama waje,duk motsin dazeyi kuwa zuciyar sa azalzalar sa takeyi akan ya dawo gida haka nan.....

Shaam kuwa da maryam tun daren jiya suka angwance,ya samu nutsuwa me tsananin yawa a tattare da aurenta,yarinya ga tsananin riqon addini,domin kuwa ganin lokacin sallan asuba yayi shaam na bacci koda ta tasheshi sanda tayita mai wa'azi akan hakan,haleema kuwa batada labarin miyan da ake sha a niger da mujinta lolx.....

Waffles sandwich ta musu da pizza ,se creamy la bees,sosai gidan ke tashin kanshi,wanka ta tsala tayi sallan ta na isha,daci ado cikin wasu riga da wando qanana pink and white masu matukar kyau,zokaga yanda heeps nata suka kwanta sosai gwanin sha'awa,kunce gashinta tayi ta taje shi zuwa baya yasha gyara se sheqi yakeyi haka ta zuboshi tamkar wata india,light makeup tayi tana fitowa sukaci karo a parlor,sanda ya lumshe ido ganinta kawai yaja numfashi, kamshin dayaji gidan nayi kawai ya wadatar balantana qamshin dayaji na ratsashi sanda ta fito, da sauri taje ta rungumeshi sosai ta kwantar da kanta a saman faffad'an qirjinsa ta furta a hankali

"Sannu da zuwa yaa muhammad,ina fatan ka dawo lafiya" qamshin sumar kanta ne ya ebe shi besan sanda ya daura hannunsa yashafi gashin kan nata ba,yama kasa magana dama gashi ba ma'aboci son magana ba se kace ba lauya ba,dagowa da kanta tayi jin tayi lamo itama tanaso ta manta da muhammad ne fa,a shagwab'e tace

"Yaa muhammad sekuma ka barni ni kadai,tun yamma fa ka fita" murmushi ya sakar mata me sanyi yama rasa me zece seya tsinci kansa da furta mata "Kiyi hakuri hafsat,wani abune ya tsaidani nima banso hakan ba,amma na kawo miki chocolate" wara ido tayi "Allah yaa muhammad? Thank you so much" ta qara rungumeshi sannan ta sakeshi ta juya,kallon duwawunta yake harta shige da jakar hannunsa da leda data karba,shi yaushe ma yataba samun arziqin a wani riqe masa jaka? Hmm lallai wannan auren yana ganin shine ake kira auren gaske kuwa.....A bed room nashi ma koda yashiga kamshin turaren wutan da aka saka dana freshner gaba daya ya banbanta,be taba kamshin daya kwanta masa araiba irin wannan,kallonshi tayi sosai,zuciyarta na dokawa sabida abinda huda tace tayi ya mata nauyi,haka ta daure sabida yanzu kam ta shirya yin wining wannan,taje kusa dashi botiran shirt nashi ta soma b'alle masa sororo yayi kuwa ita kam se murmushi take "Wanka ne ya dace dakai,a baho na had'a maka ruwan wanka da turaren wanka me tsananin kamshi,bayan kayi wanka se dinner kuma ko?" kallonshi tayi dasanjin amsar tambayarsa "murmushi ya sakar mata ya gyad'a kai alamar e,haka ta cire masa har wandon cikeda dauriya,ya dawo iya boxers de singlet ne a jikinshi, towel ta miqa masa tace "To zan jira kafito semu tafi tare" harta juya ya riqo hannunta yace "Sauran kayan fa hafsat? Su bazaki tayani ragewa ba?" murmushi tayi tace bayan ta kawar da kanta gefe d'aya "Yaa muhammad wannan ma aiya isa,dan Allah ka barni haka?" juyawa yayi zuwa toilet ba tare dayayi magana sarai ya gano nauyin sa takeji,wannan auren yana ganin shine mutu ka raba,shibesan ana wa maza gata ba har haka ai,a gurguje yayi wankan yana mamakin wannan kamshin da ruwan wankan keyi,haka yafito dagashi se towel halittarsa ta faffadan kirji ta kala,gaba daya jikinta ya mace sanda ta lumshe ido tana mafarkin ganin kanta a cikin wannan kirjin nasa,haka ya janyo man shafawa ze shafa,ita ta karb'i karamun towel ta goge masa jikinshi sannan ta shafa masa mai d'in,kayan baccin data ciro masa ta bashi ya karba yana murmushin da sam,yakasa daukewa a fuskarsa,da sauri ta bashi wuri tayi waje,a parlor ya taddata koda yaga pizza kallonta yayi

"Daga ina kikayi ordering pizza,na season 7n kawai nakeci" kallonshi tayi ordering kuma sekace banida kayan had'in pizza d'in? Ni na hadashi ba dadewa fa" kallon mamaki ya mata "A ina kika koyi girki?" ya wurgo mata tambayar "A wurin mama na,kuma a india naje ctring classes yafi a irga,wasu zubin idan muna hutu ban dawo ba senayi joining,i so much like cooking ai" jinjina kanshi yayi yana me jin dadin yanda yake cin girkin matar daya ajiye a matsayin tashi,tunda yake so daya tak zainab ta dafa masa spag ita dinma san beci ba sabida ba taste kowa abincin cook yake ci,a parlor suka zauna kallo bayan sin ida,matashin kai tayi da cinyarsa anan bacci ya dauketa, se wuraren 11 ya dagata cak zuwa bed room nashi, sosai ya rungumeta ya kwanta shima.......

Haleemah kuwa kwana bakwai da auren shaam ta dira niger,kuma a gidansu tafara sauka anan takejin mugin labari,aikam qungiya guda sukayi zuwa gidan amarya domin ciwo kan ubanta danye lolxxxz.

Yau satin hafsa daya kenan a gidan muhammad sukan ci atare susha atare kuma a haka zasu kwana wuri daya,amma fa sam ba wani mu'amalar aure dake shiga tsakaninsu,sedai kullim kwanan duniya tana qara samun wani babban matsayi a zuciyar muhammad har yakeji baya iya daukar a wanni biyar batre daya ganta ba,yauta shirya zataje gidan shaam da gidan Abba haris,izini yamata akan ta karbo key na motarsa Avensus wurin zeezee sabida duka keys suna bangarenta taje da kanta tunda tace tare dasu momy zasuje gidan shaam din harsu khairii ma,koda ta aika wai bazata badaba,kai tsaye taje da kanta ,a zaune ta tadda ana matsa mata kafafu ta kalle ta sama da kasa tace
."Zainab key na Avensus fara zaki bani zanje unguwa"

"shi me gidan naki be sanar miki cewar ni ce nakeda ikon komai da kowa ba agidannan,kice hajiya kuma ki durqusa ki rokeni key sannan zan baki" wata dariya hafsat tayi ta juya abinta zuwa waje,kallon driver na gidan tayi tace dashi

"A waccen benz da key ke hannunka akwai mai ne?" kallonta yayi ya gyada kai,miqa masa hannu tayi kawai ta karba tayi gaba,tana tashin motar ta saisaita kanta sega zee tafito tana masifa ko kallonta batayi ba,tazo tasha gabanta aikam hafsa tayi cikin ta seda ta fadi sannan ta kauce tayi gaba abunta.......

Topha koya zata kaya,su haleema sunyi qungiyar zuwa gidan shaam gakuma su hafsat zasuje koya zata kaya ohoo

Vote and comment
[2/16, 9:28 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

   Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)
 
Wattpadd@ 68billygaladanchi

*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*

             29
Bayan ta d'auki su momy kai tsaye gidan shaam suka wuce,mota biyu sukayi kuwa,mamakin ganin motar gidansu haleema sukayi,kallo d'aya momy ta musu ta tabbatarwa kanta cewar ba lafiya,umartar kowa tayi dasu fito da sauri aikam a take suka fad'a gidan, mamakin ganin da sukayi su haleema sun saka maryam a gaba ta zuqa zuqan durina da kuma sanduna wannan ya mareta tanan wannan kuma ya mareta tacan,ita kuwa bakinta be mutu ba,se tambaya take su waye,da sauri momy tashige tsakiyar parlor d'in ta d'agata,mahaifiyar haleema ce ta wanke momy da mari kai tsaye,cikin fusata ta furta

"Tsohuwar banza la'ananniya banda iskanci tayaya danki ze qara aure matarsa ta farko bata sani ba sannan ku baku nuna masa kuskuren saba? Aikam hafsa kukan kurciya tayi ta yanke uwar haleema da mari,daganan kuwa dambe ya kaure mahaifiyar shaam ta asali

Please Login or Register in order to submit comment