Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

meye haka lapiya?" kallonta kurun hafsat tayi tace "yaa shaam na jiranki a waje" tana kaiwa nan ta juya abinta bata ko kalletaba,da gudu taje tariqe rigar hafsa ta baya tasanya hannu ta dungure mata kai tare da kai mata ranqwashi tace "y'ar gidan uban waye me dazaki wa mutane iskanci haka ake fadar saqo" atake idon hafsat ya cicciko tace " Yar gidan uban yaa shaam ceni kuma nice qanwarsa dayake da ita hafsat,akwai wani magana ne??" da sauri leemah ta seseta kanta tace "Allah sarki hafsat kulele,ya kike wlhy ban ganekiba,nasha fitsararrun yaran unguwane ashe babbar sis ce,umma kinga qanwar shaam" tafada tana kallon umman tare da kashe mata ido daya alamar a saisaita zancen,murmushin yaqe umman ta somayi "Laa wai itace kinsan fani nafi ganewa ace shammaz sam datace shaam ban gane wa take nufi ba,kikace hafsat sunanta sannu kinji 'yata zonan kusa dani,kinga munata surutu wlhy bamuji sallamarkiba" ahaka dai suka rinqa zuba uban surutu wananna yace mata wannan wancan yace wannan,dazasu fita kuwa aka rinqa kwaso mata kyaututtuka,itadai shigowar farko dukda tanada kuruciya gidan be mataba wayannan yan matan masu zubin karuwai.....!!!! Amota kuwa leemah se janta takeyi da hira ita kuwa taqi ta saki jikinta gaba d'aya a tsure take hankalinta baya jikinta tunaninta daya yazatayi kar yaya ya auri wannan itafa lokaci daya taji ta tsaneta da yan gidansu gaba daya,haka sukaje siyan wayar yaa shaam ya siya mata iri daya dana leemah wanda atake ta fahimci cewar bataji dadi ba sabida kallonsa tayi tace "Boo me wannan qaramar yarinyar zaka siyawa danqareriyar waya irin wannan a gaskiya kunaso ku b'atata da yawa" a yanda kuma hafsat ta fahimta shima beji dadin yanda tayi ba domin kuwa be kula da zancenta ba,daganan ya siya musu ice cream da kaza ya mayarda leemah gida....tana shiga kuwa tacire mayafin ta fada tsakiyar parlon da sukecin kasuwa tace "Umma wlhy da matsala wannan shekiyar qanwar tasa itace matsalar tamu,baya shayin mata komai,kinga yawan kaza da ice cream d'aya ya siya mana abin haushin ma wai hatta waya iri d'aya ya siya mana yarinya sekace kishiyata,ina wannan yarinyar ina riqe babbar waya har haka wlhy rashin hankali ne tsantsa,kuma tsaf maganinta zamuyi domin idan ba haka ba ita zata takurawa rayuwarmu ta hanamu cimma burinmu" gyada umman tayi tace "Ai maganin shegiya zamuyi ku barni da ita gashi sam batada kunya ko kadan wlhy amma damu take zancen!!!!

*Washe gari pooja a bisa rashin sani tashiga interview na wayanda ke neman shiga ss3 kuma abun mamaki tazo na daya acikin su kusan 32 koda suka je bincike aka tabbatar musu taci akan ta soma zuwa on monday,monday tana zuwa taga an kaita ss3 mamaki ya kamata tace dasu kuskure ne ita ss1 zataje su kuwa suka kafe akan ko exam datayi na ss3 ne kuma itace overall gaba daya,haka ta zauna ita kadai qaramar yarinya acikin manya kowa se tsokanarta yake dukta takura,tana dawowa gida kai tsaye part din yaa shaam ta nufa harda kukanta ta sanar masa "ke wace iriyar sakarai ce dazaki shige exam daba nakuba?" share kwallanta tayi tace "yaa shaam nifa na gaji dajirane inajin ankira badge 3 seniours sena shiga kawai ashe ss3 ne" shiru yayi yace taje se gobe,juyin duniya yayi dasu akan yarinyace amma sun dage akan bazasu mayarda overall student tasu abaya ba,seda aka qara bata exam din lapiya lau ta lashe komai dole haka ya hakura akan ta zauna din,data dawo gida yayi kiranta akan ya akayi ta iya abubuwan ss3 anan yakeji cewar a library na school dinsu har books na nursery take karantawa dana ss3 kuma abinda bata ganeba taje gun malaminsu ko principal idan besan amsaba ya hada ta da malamin dake subject din" gamsuwa yayi da bayanan yamata fatan alkhairi sannan ta juya ciki......

Mom Nua'iym
[1/10, 9:57 PM] Billy Galadanci:       *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

   Love story 2018

Billy galadanchi

Vote me on wattpadd@68billygaladanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)
 
*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*

                                04
Sam yaa shaam baya saurarawa Elham indai zancen karatune,har me extra lesson yanema bata dawowa gida se 5,kuma anayin isha  malamin islamiyyarsu zezo ita da mero sekuma 9,wannan ne ya sanya sam batada time,a haka har lokacin waec da neco yazo lapiya lau sukayi suka gama a wannan lokacin hafsat takeda shekaru sha biyar a duniya qawayenta dasuke school tare duk sun girmeta babbar qawarta me suna huda shekarunta sha takwas ma,sosai suka shaqu ba kadan ba tana d'aura hafsat akan hanyoyi masu kyau sabida tanada hankali kuma ba laifi tana ragewa dukda yake shagwab'a irinna hafsat bawai tana denawa bane kurun dai ta rage yiwa mutane rashin kunya......wannan kenan

    Yaa shaam shine babban yaron da Alhaj muhammad gaya dakuma haj Nasara suka haifa wanda bayan haihuwarsa sun cire rai gaba daya da cewar zasu qara haihuwa kasancewar kafin samuwarshi ma ansha fama,sosai suke qaunar shammaz ba kad'an ba wanda bayan an haifi hafsat ma soyayyarshi ko kad'an be ragu ba a zukatansu,sedai fa sun d'auki soyayyar duniya sun d'aura akan hafsat basu bama har Abba haris wanda ya kasance qanine a wurin daddy uwa d'aya uba d'aya,a wurin mahaifansu su hudu ne kacal maza biyu mata biyu haj maryam dakuma autarsu haj Harira,Abba haris yanada yara bakwai,Surayya itace babba se yan biyu hassana da husaina,se khairiyya da Auwal sannan Abduljabbar da Abdurqadir...Maryam kuwa yaranta biyu rak Bunyameen da yusuf,harira keda biyar saratu,sa'adatu,shamsiyyah, sha'awanatu se autarta safiyyah.batada namiji ko d'aya gaba dayan wannan babban family din su a qaunar junansu baka tab'ajin wani munafurci ya taso a tsakaninsu ko rashin jituwa koya yana kokarin hakuri da d'an uwansa kazalika kuma dukkaninsu 'yan boko ne masu ji da kud'i muhammad shine  babban cikinsu sannan kuma gaba dayansu yafisu kud'i,mahaifiyarsu wacce sunanta hafsat taci tana nan daram ita da mijinta mlm Abubakar gaya,sune ma sukafi kowa shagwaba hafsat domin kuwa suna matukar kaunar yarinyar.......

     Shaam tun yana secondry school yake soyayya da leemah lokacin yana ss3 ita kuwa tana jss3,sam leemah bawai yarinya ce,sabida yanzu tayi 27 yrs ko shaam shekarunshi 8 baya kasar be dawoba seda yazama cikakken likitan zuciya kuma ma kan yaje yayi kusan 2yrs da gama makaranta bejeba,duk sanda ya dawo hutu suna manne da juna,sam wlhy 'yan gidansu leemah basuda kunya ko kad'an akansu sannan kuma dukkansu basusan girman mahaifinsba yan matane su bakwai rasss se uwarsu mara kunya da hankali sun mayarda mahaifinsu wagili basa ganin girmansa sabida bashida karfi sune da kansu suke karuwanci suna cida kansu da uwarsu,sam ba dan Allah leemah ta nacewa shaam shikadai yake haukansa amma itakam ta da biyu takeyi......

    Hafsat zaune asaman stairs dake sadaka da saman gidan tana latsa wayarta,sam hankalinta baya kan wayar ta rasa dalilin daya sanya zuciyarta take azalzalarta akan yayanta shaam,sam idan bata ganshiba a wuni wani zazzafan zazzabi takeji yana rufeta,ganin har shabiyun rana ya gota be shigoba ya sanya tamiqe ta nufi part d'inshi,knocking tasomayi a hankali shikuwa ya taso ya bud'e,kallon mamaki yamata yace "poojah yadai" d'an murmushi ta msa tace "Dama nayi tunanin baka karyaba bane kuma banga ka shigo cikiba,shine nace barinzo in duba inga ko lapiya" mamaki yarinyar ta bashi sosai sabida shidai wannan yarinyar har yanzu be gama gamsuwa da nutsuwartaba gyaran murya yayi yace "Tunda aka fara zancen aurennan senakeji ko yunwar ma banaji mantawa ma nakeyi da abinci abubuwa sunmin yawa gashi im all alone" murmishin yaqe tayi haka kawai taji gabanta na faduwa jin yayi zancen aurennan,kuma ta rasa dalilin jin hakan dukkuwa dayake sam ita bata damu da wannan shegiyar matar da yayan nata ze aura ba "Aikam yaya daka dena zama da yunwa,baka ganin zaka kasa hidimomin idan ulcer ya damk'eka mezan dafa maka ne??" murmushi yayi yace "ke me kika iya lelen daddy?" shagwab'e fuska tayi tace "yaya bayan tunda ka dawo gaba daya ka sauyamun rayuwa,tare dani fa ake girki a gida,nifa yanzu koma meye zan iya girka maka tumba snacks ba" shi mamakin wani shagwaba da take masa ma yakeyi,san yan kwanakinnan ya kasa gane kan kanwar tasa se kallonta yayi yace "jeki ki kawo mun koma meye da aka gika kuma kizo ki tayani zaben kalan decoration da zamuyi gun dinner" batayi magana ta juya tanajin wani zafi a ranta,abincinma kasa dawowa kawo masa tayi shikuwa dama hankalinshi na online yana neman decor na bugawa a jarida sabida yaci burin wannan auren.....koda taje daki ta kwanta kasa yin komai tayi a haka huda ta kirata
"Huda yadai?"

"lapiya lau lil friend,zanzo gidanku da mijina da zan saura zuwa 4 na yamma seku gaisa,jiya jiyannan ya dawo daga uk ya matsamun yanaso yaga wannan poojah din danafi santa dashi" murmushi kurun tayi tace "toh" har yamma bata fitoba gashi mommy tana abuja, a haka har Huda tazo gidan,kallonta tayi bayan ta shigo bedroom din ta ganta a zaune tace "Poojah lapiyanki kuwa?? Tunda na kiraki naji muryanki wani iri" dan guntun tsaki taja tace "Huda wlhy na tsani inji ana zancen aurennan na yaa shaam gaba daya dena riqa ji jikina yana mutuwa,kuma banajin dadin rayuwata" kallon nutsuwa huda ta mata sannan tace " Hafsat lapiyanki kuwa?? Meye hadinki da auren yayanki keda ya dace ace kina masa murna ma kinmaga yanda kika dawo kuwa,waini yau dinnan ma kinci abinci?" lumshe idonta tayi sannan ta bude su a hankali zuwa yanzu har sun cicciko tace "Huda wlhy banida lapiya wataqila aljanaine suka shafeni,bana iyacin abinci tun bikinnan saura wata d'aya sannan kuma bana iya zama banga yaa shaam daga zaran na wuni ban ganshiba sena ringa jin zazzabi na damuna kuma idan muna tare banaso mu rabu,huda anya kuwa ba aljanai bane suka shafeni??" sosai huda ke nazarin kalaman hafsat,secan ta nisa tace "Poojah da gaske uwarku d'aya kuma ubanku d'aya da yaa shaam?" d'an tab'e fuska tayi sannan tace "wannan wane irin tambaya ne huda,wlhy uwarmu daya ubanmu d'aya dashi wannan bako tantama,bayan haihuwarshi kuwa ancire rai za'a kara samun haihuwa Allah ya kawoni" jinjina kai huda tayi jikinta duk yayi sanyi,tabbas hafsat abin tausayice domin kuwa wannan ba tantama san yayan nata takeyi kuma ta sani sarai koma menene akwai wata a qasa,ubangiji baya taba jarabtar bawansa da abinda baze iya d'aukaba,tayaya ma kanwa zata so yayanta har haka,amma a sarari se wayancewa tayi tace "Hafsat kiyayyar dakikewa matar da yayanki ze aura tayi yawa hadda kasa cin abinci har haka"murmushi kurun tayi domin kuwa ita kanta batasan cewar soyayya bace aranta!!!!!!!!!
[1/10, 9:57 PM] Billy Galadanci: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

   Love story 2018

Billy galadanchi

Vote me on whattpad@chi
*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)
 
*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*

                                05

Da dare bayan isha malaminsu na islamiyyah yazo,sam hankalinta baya jikinta haka tafito tafiya takeyi tamkar wacce k'wai ya fashewa a ciki gaba d'aya hankalinta baya jikinta,motsi d'aya idan tayi da tunanin yayan nata take yinshi, A farfajiyar gidan ta hangoshi yana waya se raha yakeyi kallo d'aya zaka masa ka tabbatar cewar yana cikin farin ciki,haka kawai lokaci d'aya ta tsinci kanta dajin wani haushi mara misaltuwa ta tabbatar da Aunty leemah yake waya,kan tayi aune hawaye ya fara sintiri akan fuskarta,juyawa tayi sam bazata iya zuwa makarantar ba,karo tayi da mero tana kukan,kallon mamaki mero ta mata tace " kulele lapiya dai?? Meyake damunki?" batace komai ba tayi sama abinta rufe kofar tayi tana rusar uban kuka tarasa meke damunta...Allah sarki hafsat ga quruciya yarinya yar shekaru goma sha biyar na neman shiga damuwa akan abinda ta kasa gane meye shi,haka hafsa ta dawo sukuku dukta rame tayi baqi sam bakace ita bace,a haka har lokacin bikin yayan nata yazo.....

A parlo zaune ta tarar da Daddy da momy suna hira,zuwa tayi ta zauna kusa da momy batace komai ba,kallonta baban yayi yace "Hafsatu kulele na meyake damunki ne wai kwana biyu?" murmushi tayi kurin batace komai ba momy tace "Girmane fa yatasowa Hafsat ai Alhj baka ganin wani sabuwar nutsuwa daya tasowa kulelen taka" dariya yayi yace

"yar daddy gashi kinyi qanqanta da zuwa jami'a wane skul zaki je ko computer school zan sakaki?" murmushi takumayi sannan tace "Daddy naci jamb fa,kusan 240 kumama ai yanzu na girma banwa jami'a qanqantaba dan Allah idan na samu admtn ka barni naje"

"ba damuwa yar daddy Allah ya sa ki samu admtn din,wane couse kikeso?"

"Education English nacika dakuma pure Elhglish duk wanda na samu zanyi ne" adua ya mata kanwani yayi magana sega yaa Shaam ya shigo durkusawa yayi ya miqawa daddynshi envelope,wasu invitation cards ne masu kyau aka ciro daga ciki,daddy se washe baki yakeyi yana ya kalli yaronshi yace

"Allah ya sanya Alkhairi my son,ranar da akayi reception ranar zamuyi tarin bude clinic dinka,sabida yafi" haka kawai hafsat ta kasa controling kanta ganin invitation card na d'aurin auren ta saka kuka wiwi,kowa hankalinshi ya dawo kanta se tambayarta suke lapiya? Amma i a da gudunta ta ruga dakinta,ta fad'a kan gado se kuka me karfi ya subuce mata hannu ta saka ta dafe inda takejin wani azababben radad'i a haka Shammaz ya shigo ya sameta hannu yasaka ya d'agota ya d'aurata a jikinshi yana mejin tausayinta a hankali ya furta

"Little sister meya sameki har haka? Waye ya tab'aki kike wannan uban kukan haka?" acikin kuka tace

"nima ban sani ba yaa shaam ko wane lokaci idan akayi zancen aurenka sena riqa ji tamkar zan mutu nabar duniya gaba daya,idan na wuni ban gankaba banajin dadin Rayuwata idan naga kana murna kana farin ciki indai akan zancen aurenkane sena riqajin zuciya na yana tafarfasa yaa shaam wlhy banasan kayi aurennan kaga nan? Ta nuna zuciyar ta da hannunta "zafi yakemun zogi nakeji tamkar zan mutu,tun saura wata daya aurenka na rasa nutsuwata duk sanda na tuna ko abinci bana iya ci bansan meyake damuna ba anya yaa shaam baka ganin aljanaine suka shafeni?? Mesa ada ba ruwana dakai? Mesa ban damu da rashinka ba akusa dani? Mesa ada bana leqen shige da ficenka ta window? Meyasa ko maima yaa shaam,a yanda nakeji gameda zancen aurennan idn akayishi mutuwa zanyi" k'ura mata ido kurin yayi harta kai aya,mamakin kalamanta ne yake shirin birkita masa k'walwa sam yakasa saisaita tunanin shi idan har abinda zuciyar ke sanar masa gaskiya ne lallai kuwa da babbar matsala a gaba,sabida sam shi wannan yarinyar kallon qanwa yake mata uwa daya uba daya,kai koda ba haka ba shisam idan ba leeman shiba se rijiya,gaba daya hankalinshi ya tashi cikeda dabara ya kalleta yace mata

"Lallai kam hafsat se aljanai sabida kin taba ganin inda qanwar mutum uwa daya uba daya tayi kishi kotaji haushi akan zeyi aure,ki sani su e sukeso su shiga a tsakaninmu sam basa san suga muna qaunar junanmu,kuma ta Allah ba tasu ba sabida haka kiyi hakuri ki dinga adua kinji,inshaa Allah zasu rabu dake,kuma karki sake ki fadawa kowa wannan maganar" kai kurun ta gyad'a masa yayi da mero dake jikin k'ofa a lab'e ta dafe qirji tana salallami domin kuwa tun ba yauba ta fahimci sarai hafsat san shaam takeyi,inkuwa hakane iska tana wahalar dame kayan kara domin kodajin wannan zancen dayaa shaam yayi ta kula baya ma buqa tar ta sanarwa wani atilastashi aurenta yafi san son nashi ya kasheta kenan,aranta ta kudirta gayawa momy gaskiya sedai ya kashe ta......

Bayan isha mero taje ta samu momy a d'aki bayan ta gaidata ta zauna ta fuskanceta sannan tace

"Momy wata muhimmiyar magana nakeso muyi dangane da hafsat domin kuwa akwai matsala akasa" kallonta momy tayi batare da bawa maganar muhimmanciba tace "Ina jinki"

"Momy na sani bani kadaiba dukkan nin mutanen gidannan sun kula cewar Kulele bata cikin nutsuwarta da walwala sam,sa'annan ko abinci bataci gashi batama koda kallon data sabayi" gyada kai kurun mony tayi taci gaba "To wannan kukan dakikaga tanayi a d'azu ba komai bane illah kishin zancen auren yaa shaam datakeyi domin kuwa da bakinta naji tana sanar masa,take ta kwashe komai ta sanar mata har sanda taji tana baiwa qawarta labari da abinda qawar tace mata har tambayar data mata akan zancen yayanta ne kuwa uwa daya uba daya?" shiru momy tayi tana nazarin kalaman mero tabbas idan basanshi takeyiba ba abunda ze sanya taji hakan,inko hakane to wlhy da sake domin kuwa so sone amma sankai yafi komai,da wannan tamiqe zuwa b'angaren daddy......ita kuwa Hafsat a daidai wannan lokacin ta shirya zuwa roqar daddy akan ya barta taje gidan abba haris batasan yan biki su cika gidan ana hayaniya,zama momy tayi ta zayyanewa daddy komai shi kuwa cikin fada yace

"Haba Nasara!!! Ina nidake muka zauna muka roqi dangi akan su rufe zancen cewa shaamaz da Hafsat ba uwarsu daya ubansu daya ba har abada,tayaya ma yarinya zata so yayanta inama hafsat ina sanin meye so?? Meta tauna vare ta had'a arayuwa?? " cikin fusata momyn tace

"Haba Alhj mesanya agaban duniya ka nuna kanasan gmhafsat amma a bad'ini ba haka bane,karfa ma manta tsakaninta da shaam waka haifa da cikinka?? Itace 'ya daya tilo da Allah ya baka,tayaya akan abunda bekai ya kawo ba seka dau zafi haka,tunda har tana sanshi mezai hana a hadasu susu biyu a aura masa kowa ya huta" hara daddy ya wurga mata yace

"wlhy kinji na rantse kobada shaam ba bazan wa hafsat aure yanzu ba,tsabar mata bakuda hankali,ke kinga karma ki nuna mata kinsan tana sanshi ki barta tayita haukanta,amma ba zancen auren a tsakaninsu yana da wacce yakeso ita kuwa taji dashi karna kuma jin wannan maganar wlhy" hafsat dake a waje kuma taji komai dafe qirjinta tayi tace "Ba daddynmu daya dakai ba yaa shaam to waye babanka?? Menene ma dangar takarmj dakai?? SO SO kuma tayaya meye mashi? Wannan shine abunda nakejin friend kullum tana mun magana akanshi game da saurayinta da gaske san yaa shaam nakeyi? Anya ban dakkowa kaina wahala ba kuwa? Lallai kuwa da babban aiki jaaa ma agabana.

Mom Nua'iym

            
[1/21, 7:15 AM] Mmn Sadeeq: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

   Love story 2018

Billy galadanchi

Wattpad@galadanchi
*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)
 
*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*

                                  06
Jiki ba k'wari ta juya zuwa d'akinta,sam hankalin hafsat beyi yawan dazatayi zurfin tunaniba ta kasa tariyo komai,wayarta ta ciro daga k'asan filo ta kira huda,d'agawar farko tace

"Huda dan Allah kina ina yanzu??" da mamaki hudan tace "Ina kan hanyar zuwa gun Ashraf tela" to yayi nima ganinan zuwa da maganar danike so muyi" kan huda tayi magana ta katse wayan,da sauri ta zari hijab tayi k'asa a hanya tayi karo da yaa shaam ko kallonshi batayiba sabida hankalinta sam baya jikinta,driver din momy ta gani tayi kiranshi da hannu,ta fada mota sukayi gaba....a shagon janyo hannun huda tayi suka dawo mota ta kalleta bayan tayiwa driver din umarni daya fita waje tace

"Huda wai da gaske sosai ni Hafsat ina san yaa shammaz??" kallon ta huda tayi cikeda nutsuwa tace

"Ban fahimce kiba?" kwashe komai tayi dataji su momy na fada ta gayawa huda ta qara da cewan "ke kadaine zaki iya fadamun gaskia dan Allah waida gaske wannan abun danaketaji gameda yaa shaam shine so? Kuma shi din suwaye iyayenshi??" sosai huda ta gano hafsat kuruciya ya mata yawa, banda haka ina zatasan su waye iyayen shaam,ni sawa tayi tace "poojah ki nutsu mana,zancen gaskiya ko shakka banayi kina san yayanki kuma sosai bawai kadanba,amma abunda nakeso dake shine kibi komai a hankali sabida kinga already an kusa aurenshi kuma tunda su momy basusan kinji maganar suba karki fadawa kowa karkuma ki nuna musu,wannan abun dakikeji idan yana waya da wacce ze aura da kuma idan ana zancen aurenshi shi ake kira kishi,kuma kishin ya miki yawa ina tausaya miki sabida tunkan kisan meye so da kishi kika fara kinsan kuwa illan kishi a tattare dake? Kishi masifane kamar yanda yake halittane na Allah ajikin d'an adam sedai da yake na wani yafi na wani zafin,dan Allah hafsat ki daure ki yakice sanshi a ranki,a yanda na fahimta da kika masa bayanin abinda kikeji game dashi sarai ya gano sanshi kike sabida baya muradin ki yasanya yace karki sanar wa kowa,ki manta dashi kici gaba da kallonshi a matsayin yayanki uwa d'aya uba d'aya" hawayen daketa faman tarewane suka gangaro mata tace

"Huda lallai so masifa ne kuma kishi fitinane,indai haka so yake to a gaskiya da matsala,ni bansan sanda na fara sanshiba tayaya zakice in cire sanshi a raina? Nida bansan yanda ya shiga ba ya zansan yanda zan cire?? Wlhy bazan iyaba" tausayinta huda taji ta janyota ta rungume tana bubbuga bayanta a hankali,a haka suka rabu jiki ba k'wari.....

*Bayan sati biyu*

Sosai aka cashe wurin bikin yaa shaam kuma acikin part d'inshi dake gidan anan aka kawo amarya Haleematu,yau sati daya kenan da tariyarta,kullum hafsat ke zuwa tayata aiki,kasancewar ba abinda takeyi agidan,ta d'auki shawarar qawarta ta dena nuna komai a idon mutane harma momy ta soma qaryata zancen cewar hafsat tana san yayan nata....yauma kamar kullum tana kitchen din Aunty haleema tana tayata aiki,suna d'an tab'a hira yaa shaam ya shigo,ba kunya suka rungume juna har tana manna masa sumba a wuya

" Baby yadai? Bana hanaki yawan aikinnan ba? Kije ki huta mana tunda ga Hafsat ta iya komai" kallon shi tai cikeda kissa tace

"Haba honey yaya daga zuwan yarinya tayani aiki seka wani ce na barta tayi,nooo ni banasan small oga ta tasha wahala" hancinta ya danja ta saka qara yace "Kinga Baby da gaske ki rage yawan aikinnan ita wannan sakaryar yarinyar shagwab'abb'iyan yarinyane yanzu take koyan aiki ki barta ta koya kekuwa semu huta abunmu" wani langwabe kai tayi tace "Haba shaam meye hakannan wai,nika tafi idan muka gama zanzo" hannu biyu ya saka dukda zaman ta katuwa ya dauketa yabar kitchen din da ita,ita kuwa dama gulmane haka takeso ya sanya bata wani musa masa ba, hannu hafsat ta sanya ta share k'wallan daya kwaranyo mata

"Yaa Allah ka yayemun wannan masifar,Allah ka rabani da k'aunar yaa shaam,Allah ka ciremun kishinsa,Allah ka kawomun agaji" wannan itace adu'ar datakeyi a sarari cikin kuka,tafi mintuna biyar a haka,kanta barwa Allah taci gaba da aikinta.....haka rayuwa taci gaba wa hafsat kullum itace da bauta agidan yaa shaam sekace wata yar aiki,shi kuwa kullum kwanan duniya qara tsanarta yakeyi yakuma rasa dalilin tsanar dayake wa kanwar tashi wanda a sanda tana qarama bashida wacce takeso sama da ita,amma yanzu tun sanda yagano sanshi takeyi seya dauki hakan a matsayin raini ya d'auki karan tsana ya d'aura mata kullum acikin bautawa gidanshi take ita kuwa yi hawai takeyi domin ta faranta masa,momy kuwa komai akan idonta take tafiya yanda ake takurawa yarta ba karamun damunta yakeba,duk kuma sanda tayi magana sekaga fuskar daddy ta sauya akan hakan.
Hafsat da huda sun samu admsn a Usman d'an fodiyo university dake sokoto,inda dukkansu suke karantar English,dabadan hafsat tanada kokari ba dabazata gane komai ba a makaranta kasancewar gaba daya hankalinta yana kan yaa shaam kullum kwanann duniya da begensa take kwana kuma take tashi,shekarunta goma sha shida yanzu yakamata ace ta qara girma irinna tashen balagan nan amma sam damuwa ya hana ta,tanaso ta yakice wa kanta soyayyar yaa shaam amma ta kasa,ganin rayuwar gidan yamata k'unci ya sanya tabar sama road gaba daya ta tattare kayanta tace gidan Abba haris zataje gun khairiyyah dayake itace tsarar haihuwarta,momy bata hanataba kasancewar tasani sarai 'yar tata tana cikin damuwa,gwara ma tane candin kota samu sassaucin abinda yayan nata kemata wannan kenan.

Tunda hafsat takoma gidan Abba haris se kewar shaam ya taso mata,shaam seyayi sati biyu bezo wurinsu abba haris ba,dukkuwa dayake sune iyayensa na ainahi,sabida kawaici,lokacin da yayan abban haris yayi aure wato mahaifin hafsat yajima be haihuba kai har haris yayi aure suka haifi shaam,shine fa suka baiwa yayanshi shi na har abada ganin yana matukar san y'ay'a amma Allah be kawo masa ba shiya sanya hafsat datazo sanda ba'a zataba bata gane cewar ba mahaifansu daya

Please Login or Register in order to submit comment