Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

idan na farfado yana a rufe baze taba budewa ba ya sanya naji gaba daya na samu mafita,karka sanar da kowa se bayan aure na dakai" murmushi yayi yace a sarari

"Alhamdulillah,amma hafsat kya baiwa kanki wahala duk akaina? ,
Zama a matsayin makauniya anya ba wahalar da kanki bane" murmushi ta masa

"Uncle sayyeed banida burin daya wuce na ganni a tare dakai,babu abu mafi soyuwa agarareni daya wuce na zamto mata agareka,babu abu mafi bani kwanciyar hankali illah in ganni kusa dakai kusanci mafi dad'i acikin kusance kusance,dan Allah ka tayani cimma wannan burin nawa" murmushi ya sakar mata yace

"Babu damuwa Babyn ubcle say,Allah ya baki lapiya amma kin kware a pretending" dariya tayi sannan tace

"Kaina yana masifar yimun ciwo,da kuma hannun nan,ni samosa zanci" dariya ya kwashe dashi jin excuse nata nasan cin samosa yace

"Madam ina zan samo miki samosa yanzu?" turo bakin tayi

"Ni koma a inane" To naji barinje season seven su dama 24hrs service sukeyi" bata ce dashi komai ba ya miqe yayi waje.....

Shammaz kuwa ya kasa bacci,ga haleema zaune a kusa dashi amma sam yama manta danita,ita kuwa se hotuna take faman dauka tana sakawa a snap gashi batada maraba da tsirarara,kallonshi ta d'anyi a kaikaice tace dashi

"Shaam lapiya nka kuwa ?" dan waigowa yayi ta gefenta ya marairaice

"Hafsat ne tayi accident shekarnjiya fa,kuma idonta ya kuma rufewa gashi babu chance yanzu sabida shine na biyu,ya kamata kije ki duba ta" tsaki taja

"Yo sabida nakasasshiya ta qara naqashewa shine kwana biyu duk ka canja,Allah ma yasanya ta zama gurguwa a had'a mata double" kallon mamaki ya mata sannan kamar ya maketa yace

"Tsabar ba Allah a ranki zakiwa yar uwata kuma jinina mugun fata har haka?"

"mtsww aikin banza,ai inada labarin accident din biris dai na maka wai kare ya taka sisi,in banda rainin wayau akan kanaso ka auri wannan karuwar zataje ta kara mota ya kadeta,kaji na rantse ba inda zani,kuma ka sani wlhu idan kace zakamun kishiya sena yanka tsuliyar uban kowa ma ya huta" tana kaiwa nan tayi waje,dama ya zama mujin hajiya se shiru yayi,shi yanzu damuwarsa lapiyar hafsat......

Muhammad Jalalludden Auwal,shine mutumin daya kade hafsat shekarnjiya,yaune kuma yake shirin zuwa lapiyarta domin tunda ya baro asibiti be koma ba sabida ayyuka sun sha kanshi,sanye yake da babbar rigar farar shadda dinkin sufani yasha kyau,gabaki dayanshi komai na jikinsa fari ne kaikace shirin zuwa qabari yakeyi, hatta hanky daya tiqe fari ne,agogon hannunsa ma haka haka ya taka yace asibiti,hadaddiyar mercedese benz dinsa ya parka a harabar asibitin ya fito yana tafiya irin ta manyan mutane dududu shekarunsa bazasu wuce 37 ba aduniya amma gabaki daya manyance ya masa yawa,ga uban kwarjini daya keda koda ya fito acikin motar kowa qura masa ido yayi,a yangace ya isa kofar dakin dayake tabbacin nanne,a hankali ya tura kofar ya shiga da sallamar sa,momy ce zaune kusa da ita tana ganinsa ta miqe suka gaisa sedai bata shaidasa ba,sabidanita basu hadu ba ranar,murmushi yayi yace

"Mama nine wanda na kade hafsa,nazone in duba lapiyarta sabida gobe zan bar qasar,kuyi hakuri banzoba kwana biyu ayyukane suka sha kaina" kallonsa hafsat tayi da qasan idonta ta dauke kanta lokaci daya,gaisawa sukayi da mama sannan ta masa godiya sosai

"Mama yanzu menene matsalar hafsat?" sadda kanta tayi tashiga rero masa tundaga matsalar farko data samu har zuwa wannan akan rashin ido,taqarashe sanar dashi cikin kuka sosai, girgiza kanshi yayi cikeda damuwa yace bayan ya zare madubin dake fuskarsa ya shafi idonsa

"Bazan yadda cewar idon baze bude ba sedai idan basu san kan aikinsu ba,akwai likitana dake a china,a can zamu da ita,idan mahaifanta zasu yarda zan dauki nauyin komai na aikin da tafiyar" shiru momy tayi hafsa ce tace

"Niba inda zani,ku barni anan kawai Allah ze bani lapiya" kallonta yayi yace cikin fada

"Hafsat idan kika kuma saka bakinki amaganar manya sena sassa b'a miki wlhy" tsoronsa ne ya darsu aranta lokaci daya,tanajin tsoron ayi tafiyar aje garin gyara ayi barna,tunda lapiya ta qalau,amma dai bata kuma cewa komai ba" sallama ya musu akan zece wurin su daddy da kanshi,yana fito wa ya hadu da shammaz,kallon kallo suka tsaya yiwa juna sannan ba tare da sunwa juna magana ba suka raba kowa ya wuce


Hmmmmm toophaa ga oga muhammad ya iso

Mom Nu'aiym
[2/8, 8:47 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)

Wattpadd@ 68billygaladanchi

*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*

22

Tunda hafsat taji zancen zuwa china se tafara tsoron tafiyar,lallai idan har ta kuskura akayi tafiyar nan tofa se an ce za'a yi mata aikin,kuma lallai garin neman gira rashin idone ze biyo baya,tana kwance tayi shiru uncle say ya turo kofar dakin ya shigo da sallamar sa,yunkurawa tayi ta tashi zaune sabida yanayin hannunta da har yanzu da sauransa ta tashi zaune,kura mata ido yayi yana murmushi sun dad'e sosai suna hirar su ta masoya kan ya mata sallama harya kai kofa ya juyo ya kalleta,murmushi ta sakar masa tace

"Uncle say yau nakula ka nacewa kallona lafiya dai?" girgiza mata kanshi yayi "Ai dama can kinsan ni sam bana gajiyawa da kallon kyakyawar fuskar nan taki" lumshe idanta tayi cikin sanyin murya tace "Nima haka baby say" batare dayayi magana ba ya juya sanye da murmushi a fuskarsa, gabaki d'aya wani tsoro ne yakeji da yawaitar fad'uwar gaba yarasa dalili seyakeji gabaki daya duniyar tana juya masa....


Shaam zaune yana dannan wayanshi a farfajiyar shan iska dake cikin gidansa haleemah tazo ta sameshi,cikeda rashin mutunci tace dashi

"Wai kaikam me kake nufi dani tunda qanwar ka ta qara zama naqashashiya kake wani shamun mur sekace nice nan na nakasata?" dagowa yayi ya kalleta yace

"Me kuma ya kawo maganar hafsat anan?kuma ban sanar miki cewar kidena ce mata naqasashiya ba?" tsaki taja

"Meye laifina danna kirata da sunan dayafi dacewa da ita? Wlhy akan hafsat zan baka mamaki"

"Kya daiji dashi,amma ki sani wlhy sena aureta a nakashen,ni tazo ma ta haifamun yara tunda kin zama juya,narasa me kika dauki duniya dabazaki haihu ba hakanan,shasha kawai me bakin hali" a fusace ta furta

"Kafi kowa sanin cewar niba juya bace tunda na haifa maka ya qanwarka ta kashe,kuma ka sani wlhy koba hafsa ba indai banice zan haifa maka yara ba kaida haihuwa har gaban abada kuwa" tsaki yaja ya miqe yabarta gun a tsaye......

Tunda haleema taji zancen auren hafsat da say zeyi seta tashi hankalinta ta sani sarai boka ya sanar mata ba ita ba haihuwa har abada sannan kuma gashi yanzu sam asiri ya dena tasiri akan sa,bokansu ya sanar musu sun sanar mata cewar lallai ya riqe addininsa yafi karfinsu ko kusantar sa ma gaba daya bazasu iyaba, wurin ummansu taje ta zayyane mata komai atake kuwa aka shirya cewan ayi airin akan hafsat gaba daya tunda itace banza.....hmmmmm

Say yana zaune tare da hafsat suna hira muhammad ya shigo cikeda taqama yaud'inma acikin shigarsa ta shadda fara amma ba babbar riga bace, yau dinkine dai na zamani me kyau komai nasa fari,hannu ya miqa masa suka gaisa sannan ya mayarda dubansa akan hafsat da alokaci daya qirjinta ya soma dokawa

"Hafsat ya jikin ki?" kallon sa tayi tace

"Naji sauqi Alhamdulillah" shiru sukayi dukansu su uku can muhammad yace "Ke baki iya gaisuwa bane,ko bakisan girman manya bane?" idon tane ya ciciko sannan tace

"Kayi hakuri yaa muhammad" dan guntun tsaki yaja sannan yace

"Mesa zakiyi karyan bakya gani kuma bayan sarai idanki lapiyanshi qalau,bayan yanzu gashinan kina kallo na kuma kallo daya na miki na tabbatar kina gani kema kuma kina kallo na ido cikin ido duk sanda nayi magana" shiru tayi yayinda say ya miqe tsaye yace

"Amma yallabai anya bakayi shishigi da yawa ba kuwa,baka ganin cewar mu doctors mune mukeda haqqin komai nata bawai kaiba,kuma mun tabbatar cewar idan nata bashida lapiya kai miye naka aciki? Kuma idan taimakonta zakayi mu bawai mun kasa bane ka barshi kawai mune family nata zamu mata komai ma har fita wajen" shiru ne ya ratsa wurin dukkansu sun bata dakiku suna kallon juna kafin muhammad yace

"mesa arayuwa zaka kalli girma na kace zaka kirb'a mun k'arya,zanyi magana a d'aga licence dinka na zama likita idan dai har tsabar hauka wannan idan ne zaka ce baya gani" jin ankira hauka ya sanya say ya dago da fuskarsa gaba daya cikeda fusata

"Kai waye? Mekake taqama dashi? Me kuma kakejin ka isa kayi da zaka kalli tsabar idona kace dani mahaukaci,dakake iqirarin cewar zaka sanya akarbe license dina mesa kai bazaka qwace ba idan ka isa,tunda nake ganin mahaukata bantaba ganin mara hankali irin kaba,tayaya zaka kalli idan mutum kace masa mahaukaci beside waye ma ya baka damar yi mana iko anan?" wani murmushin qasaita yayi sannan ya shafi gemunsa yace

"Ba license d'inka ba har abu mafi muhimmanci arayuwarka zan iya kwace wa shine rayuwarka,kuma wlhy kaf fadin Nigeria ba wanda ya isa yamun komai,kuma zaka gani wlhy,ke kuma karna dawo asibitin baki gayawa doctors masu hankali kina gani dakyau ba" yana gama fad'ar hakan ya juya ya fita hafsat ta kasa koda motsi dakyar ta hadiye wasu yawu sannan ta furta

"kayi hakuri uncle say ka rabu dashi,wannan mutumin na tsaneshi wlhy" matsowa yayi kusa da ita yace "Mesa nakejin matukar tsoro da yawaitar fad'uwar gaba hafsat? Gabaki daya banjin dadin tawa rayuwar sekace nine nake ciwo,wlhy hafsat hankalina baya kwance,bawai wannan muhammad dinba da kalamansa aa, komai ma senake ga kamar mutuwa zanyi ayanda nakejin duniyar tanamun qunci" zare idanta tayi waje

"Haba Uncle sayyeed? Ya kake magana haka? Inshaa Allah atare zamu rayu babu abunda ze sameka,kuma inshaa Allah atare zamu mutu" murmushi ya sakar mata yace

"Zanje gida na dawo nanba jimawa inshaa Allah" batayi magana ba haka yaja kofar ya fita, ita dinma dai haka kawai takejin tsananin faduwar gaba me tsanani,hankalinta sam baya jikinta,koda momy tazo bayan isha abinci kurin tabata sukayi sallah seta kwanta,say yazo sun dan taba hira,wuraren karfe tara yamata sallama akan seda safe ze dawo,har kuma ze fita ya dawo ya kalketa yace

"Hafsat idan har Allah yasanya wani abun yafaru dani kimin adu'a ita kadaice nake buqata agareki" kura masa ido tayi dukta rude murya na rawa ta furta

" mesa kake irin wannan tunanin wai? Sabida kawai wannan muhammad din yayi wannan furucin seka damu,inshaa Allah ba abunda ze iya yi maka" murmushi ya sakar mata

"Hafsa nafasan waye muhammad,sam yayi furucin dayayi ne sabida kawai ransa ya b'aci amma mutum ne me nagarta sosai,matsalar sa d'aya kafirar zuciya da rashin human relation amma hes a nice person" shiru ta masa kawai amma bawai danta yarda ba,tanaso ta tsani muhammad dinnan amma zuciyarta taqi aminta da tsanar tasan......

Wuraren sha dayan dare unle say ya dawo wurin hafsat,zama yayi kusa da ita yamata a dua lokacin tamayi bacci sannan ya kashe fitilar dakin ya fito ganin ko momy bacci ya kwashe ta batare data kashe fitilar ba,yana barin dakin ya kula da mutumin daya wuce part din fuskarsa a rufe da mask se suaune kansa yakeyi,harya wuce kuma seyakasa nutsuwa ya dawo baya gaba daya,binsa yayi yaga lallai dakin ya dosa,ya murda sad'af sad'af ya shige aikam say da sauri ya biyo bayansa shima yafada dakin,ganin yayi mutumin ya dauki filo ya danne fuskar hafsa se shura kafa takeyi acikin duhun dakin,kuka kura yayi yayi kanshi aikam fada ya kaure har suka tashi momy,da sauri ta haska torch light dinta tana ganin haka ta kunna fitilar dakin kokawa suke sosai da sauri ta kwallah kara,amma kan wani ya farga kasancewar darene har mutuminnan ya daga wuqa ya cakawa uncle say a qahon zuci har wurare biyu......ko kafin mutane su zo wancan mutumin ya gudu,hafsat ma ta farka tuni sakkowa tayi tama manta zancen karaya,sayyeed kuwa tuni rayuwa tayi halinta,se kuka takeyi tamkar ranta ze fita a haka doctors dake nan sukaxo,kowa se hawaye yakeyi ana fadar mutuwarsa ....

Mom nuaiym
[2/9, 8:55 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)

Wattpadd@ 68billygaladanchi

*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*


23

Ba shakka hafsat ta gama haukacewa da mutuwar uncle say,tsakani da Allah tanki tana gani aka fita da gawarsa wanda ko ba'a gaya mata ba ta tabbatar wlhy ya mutu,ko dan ganin jinin daya zuba ajikinsa, kasa zama tayi asibiti dole aka wuce da ita gidansu.......tunda hafsa taje gida take kuka ba qaqqautawa shi kanshi shaam din ya girgiza da mutuwar sayyeed,musamman da yake ko a dakin da hafsat take aka kashe shi,kuma ita bata gane wanda ya danne mata fuska ba da filo,kasancewar acikin dubu ne farkawar momy ne ta ga sayyeed.....

Da yamma yan sanda sukazo gunsu da tambayoyi kallon ta sukayi bayan ta momy ta gama fadar iya abunda ta sani suka ce da hafsat

"Hafsat dukda yake munsha mamakin ance kinada matsalar ido,amma se gashi faruwar abinnan idon naki ya bude,muna san sanin shin sanda abun ya faru kina ganine? Ko kuma aa bayan faruwar abun kika soma gani" kallon dan sandan tayi gaba daya gani tayi ya gama raina mata idan dai har karatun datayi na lauya harta zama qwararriya ba shirme bane a yanda ta fahimci kalamansa zarkin nasa akanta ya fara shi

"Tun ranar danayi a hatsari na farfado komai ina ganinsa lapiya lau" gyaran zamansa yayi ya kalleta sannan yace

"To meyasanya likitoci sukace bakya gani,kema kuma kike ta faman pretending?" kallonshi tayi shima sanda ya razana da kallon sannan tace.."Banasan auren yaa shaam,shikuwa so yake na aureshi sabida wata manufa tashi da ban santa ba,nakuma san ba dan Allah bane da wannan yaje ya sanya kakanmu tace dole sena aureshi,ranar dana samu accident ranar naji doctor yana wa su daddy bayanin cewar idan har na farfado idona ya sake tabuwa baze gyaruba,kasancewar shine na biyu,daganan dabara tazomun ta nunawa duniya cewar bana gani sabida nasan yaa shammaz baze aureniba ina naqasashiya,uncle say da abokinsa Dr.shuraim sunsan ina gani tangaram dama shirine se bayan na auri zabina sannan kowa yasan ina gani clear" nisawa kowa dake wurin yayi ganin tana fad'ar gaskiar ta kai tsaye,police din ya sake cewa

"Menene zaki iya tuna ya faru a daren jiya?" hawayen daya gangaro mata ta saka hannunta ta share sannan tace

" Kawai dai nasan munyi sallama da uncle say tun karfe tara na dare akan se washe gari,daganan yana fita na kwanta nayi bacci,acikin baccin ne naji an sakamun pillow a danne mun fuska sosai bana iya numfashi,can kuma sena ji an sakeni na sanya hannuna da ke lapiya na janye pillow din amma sabida yanayin dakin ba wadatar haske banga komai ba seda momy ta farka ta haska torchlight jin hayaniya,ananne naga uncle say da wannan mutumin me mask a fuska suna kokawa,harya caka masa wukar,kuma kan momy tayi wani yunkuri mutumin ya fita da gudu,amma fa ni naga face d'insa asanda uncle yaji azabar ya caka masa wuqa ya da damko face mask din wacce ina saran tana hannunku" nisawa police din yayi yace

"mungode da amsoshinki kai tsaye,dakuma hadin kai,muna fatar idan muka dawo zamu samu hadin kanki idan buqatar hakan ya taso" a fusace ta miqe tace

"Sabida yana da kudi? Ko sabida yana taqama da isa dacewar shidin wanine ze kashe mun muji ya zauna lapiya,ku sani akwai sadakin sayyees akaina wanda yake nuni ya kuma isa hujjar kasancewata matarsa sabida haka wlhy sena ga karshen shari'ar nan,matsayi na na cikakkiyar lauya nice zanyi bincike me ma'ana idan har ku bazakuyi ba" cikeda rashin fahimta suka kalli juna sannan dayan yace

"Ban gmfahim ceki ba?" atake ta zayyane musu abubuwan dasuka faru tsakanin muhammad da sayyeed da kuma furucin muhammad ta qara da cewar "A shari'ance muhammad ya aikata babban kuskura furta wannan kalamin kawai balanta na yakai ga aikatawa,nice zan sameshi da nawa tuhumar nice zan bincikeshi dan kaina ina ikon tsayawa kaina nima din cikakkiyar lauya ce meji da kanta" kallonta mutumin yakumayi yacewa

"haj amma ina ganin kamar Barrister muhammad kike magana ko?,a iya sanina dai shine mutumin da akace ya kade ki,kuma babban lauya ne da ake fafatawa dashi a fadin kasar nan gaba daya" tsaki taja ta sanya hannunta me lapiya ta bubbuga kirjinta

"Sabida yana taqamar shi babban lauyane seya kashe mutum? To nima babbat lauyace ta kaina,kuma wlhy senabi jinin mijina" shiru sukayi ganin yarinyar nacikin zafin mutuwar....

*Bayan kwana uku*

Shirin ta tayi tsaf kasancewar mahaifinta yamata komai na lauya me zaman kanta bata gwamnati ba,domin kare haqqin sayyeed daya mutu akanta,kai tsaye gidan Barrister muhammad jalalludeen Auwal yana zaune a harabar gidansa yana kurbar lemo a hankali cikeda yanga,dama kuma yasan da zuwanta kuma police ma sunzo sunyi nasu har sun wuce,har a news paper an sanya tuhimarsa da yake wanda wannan ko kadan be daga masa hankali ba sam sabida yasan meya taka hmmmm.....A yangace ta fito daga cikin motar zuwa inda yake zaune shi kuwa tun daga nesa yake kallonta yana wani murmushin kin rainawa kanki hankali,Tana zuwa ya miqe tsaye sinfi mintuna biyu suna kallon juna,hannu ya miqa mata,sanda tabi hannun nashi da kallo sannan a wulaknace ta miqa masa nata yace cikin muryarsa me tarwatsa littafinta

"Bar.muhammad j Auwal AkA j.A" murmushi tasaki me ban haushi ta furta a yangace

"Bar. Hafsat muhammad gaya AKA Miss poojah" murmushi ya sake meban dariya

"Nice meeting u young barrister"

"Nice meeting u too the oldest one" murmushin ya sakeyi tace "ina fatan kasamu labarin suing naka damuka yi a court,ina kuma fatan ka nemi qwararren lauya macecinka" juice ya dauko ya kurba sannan ya zauna ya kalleta ya nuna mata da hannu kujera

"Have a sit miss poojah" zama tayi ta dauki cup na juice da hannunta me lapiya ta kurba sannan ta kai dubanta zuwa gareshi tace

"Bakace komai ba" sanda yaja numfashi sannan yace

"Hafsat lallai kin dakkowa kanki abunda bazaki iya karasawa ina so ki sani bakin rijiya fa ba wurin wasan makaho bane,ni dinnan nafi karfin tunanin ki wlhy"Murmushi tayi har haqwaranta suka bayyana sannan tace

"Tabbas zancenka dutse ne Br. J.A,Amma ina san ka sani wlhy bazan saurara maka ba harse naga bayanka" cup dinshi ya dire akan table yace cikin nutsuwa batare daya kalli inda take ba

"Miss poojah courage dinki yana burgeni sosai,abinda nakeso dake shine wannan fafatwar tamu ta zama deal" kallonshi tayi ta kauda kanta gefe batayi magana ba yace

"Idan har kikayi wining case dinnan zan karbi hukuncin kisa kuma zan mallakamiki daukacin dukiyar dana mallaka fiye da rabinta zan baki,dukkanin abubuwan dana gada awurin mahaifina kuwa kashi uku zan masa in baki kashi biyu in yarona daya tilo dayan kashin,idan kuwa har nine nayi wining wannan case to kuwa ko kina so ko bakyaso sekin aureni" da sauri ta dago ta kalleshi taga shidin ba ita yake kallo ba,sai saita kanta tayi ganin deal din ba wani babba bane kasancewar tanada yaqinin shi yayi kisan kuma zata diddigo abun,tace

"Na amince da wannan kuma zanyi" ta miqe kallonta yayi yace
"Bakida wayo,shiyasanya nace dake bakin rijiya ba wurin wasan makaho bane ai,an tab'a deal ba'a rubuceba idan na cuceki fa? Zama zakiyi mu rubuta muyi sighning inada photocophy machine se nabaki copy daya nima na ajiye dayan kuma ke zan baiwa orijinal ma" yafada yana murmushi kauda kanta gefe tayi sannan ta zauna amma sam bata karayaba,sanda suka gama komai sannan ya miqa mata hannu yace

"Deal?" murmushin yaqe ta masa tace

"Deal" daganan ta karba ta juya yace

"Semun hadu a court poor poojah" juyowa tayi ta washe masa baki sannan tayi gaba abunta ta shige mota sukayi gaba,ya koma ya zauna yace "Smart poojah".

Toophaaa jama'a wasa farin girki yanzu ake book kam,yanzu race ya fara.

Idan kaji dadin wannan page dan Allah comment and vote.....
[2/10, 10:05 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

   Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)
 
Wattpadd@ 68billygaladanchi

*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*

                                      24
Tunda hafsat ta koma gida take nazarin abubuwan da suka shiga tsakaninta da J.A sam bata ankare da wautar data aikata ba se yanzu,idan ya kasance shi yayi wining na case din fa? Ko kuma ya kasance ba shi bane yayi kisan fa?" wani tsoro ne ya shigeta lokaci d'aya qirjinta ya soma wani irin dokawa,dafe kanta tayi ta shiga rero adu'o i kala kala na tsari.....

   Brr. J.A kuwa  bayan fitar hafsat a fusace shima ya fita,be tsaya ko ina ba se asibitin uduth kai tsaye wurin masu bada katin shiga wurin ya nufa bayan sun gaisa ya nuna musu ID card d'insa sannan yace

"Nazo bincike ne akan wani case na murder da aka samu anan asibitin kwanakin baya,ina matukar buqatar had'in kanku domin tallafawa family d'in wannan babban rashin ba bisa haqqi ba,nima kuma da ake zargi ku taimakamun matsayin na na baban lauya me matsayi ace ana zargina da kisan kai" sosai suka fahimce shi dama mutane da dama sun dad'e da qaryata zancen zargin da ake masa kasancewar mutane da dama sunsan halinsa na nagarta, babban cikinsu yace "Wane taimakao kakeso mu maka yallab'ai?" gyaran zaman madubinsa yayi sannan yace

"Record nakeso na dukkanin motocin dasuka shigo asibitin nan aranar 11/11/2016 tunda shabiyun daren shigar ranar har zuwa shabiyun daren wucewar ranar,na kuma san kunada cctv camera anan so idan ba damuwa ina buqatar video d'in" gyaran zama ogan nasu yayi sannan yace dashi

"Dama plate number ne muke d'auka mubaka card na shiga,se kuma sunan motar da color dinta da model number na motar,cctv kuwa yana daukar shiga da fice na kowa a asibitin nan,sabida haka yallab'ai komai daya dace zamu baka inshaa Allah" godiya ya masa sannan yashiga tattare muhimman informations da aka lokaci daya ya harbo bakin zaren.........

Shammaz kuwa tunda abun yafaru yakejin wani tausayin hafsat,a qasan zuciyarsa kuwa yanajin wani iri tamkar laifin sane komai,zuwa yayi ya samu haj Innah ya sanar mata yafasa auren hafsat baya santa kuma ta janye qudirinta,dama ita tunda taji cewar sabida auren sa da aka ambata hafsat ta gigice harta samu hatsari ta kudurta aranta bazata qara wannan furucinba kuma idan ma hafsat taji sauqi zatace abata zab'inta,shi kenan kuwa ta amince wa shaam akan ya gayawa iyayensu......

*Court*

        Hafsat ce a zaune tare da lauyan me kare J.A se wasu lauyoyin guda biyu,acikin babban court dake jihar sokoto,Justice d'inne ya rero bayanin zargin da akewa Brr. J.A tare da baiwa masu qara damar bayyana hujjojinsu daya sanya suke zarkin sa da kashe likitan,batare da bata lokaci ba hafsat ta zayyane komai daya faru agabanta ta qara da cewar

"Furucin sa kad'ai ya isa ya nuna mana cewar shine yayi kisannan" dayan lauya din me kare wanda ake qara ne ya miqe yace

"Objection my load" kallon sa justice din yayi shikuwa yaci gaba

"my load be kamata lauyan wanda suke qara ya riqa alaqanta laifin kisan kai kacokam ga wanda ake zargi ba,tunda ai zargin sa ake bawai an tabbatar ba" justice ya kalli hafsat yace "A kiyaye" ya sake kallon Brr. Khaleed yace

" yallab'ai zamu so akara mana lokaci kadan domin gabatar da shedunmu kuma zasu so a gayyato mana babban Abokin marigayin anan wato Dr. Shuraim" dama aka basu daganan aka d'age zaman sena da sati d'aya.

*Bayan sati d'aya*

     Lauyan wanda ake qara ne yace fara magana kamar haka

"My load wannan gabaki d'aya record ne na motocin dasuka shiga asibitin ranar da abun ya faru,acikin mun samu mota iri daya kirar honda civic kalar ja wacce aranar tashiga asibitin kusan 7 times a wannan ranar cctv camera ta main gate data ward din da akayi kisan duk sun tabbatar mana da shigar mamalakin motar so bakwai a wunin ranar, kuma duk shigar sa kai tsaye ward d'in yake nufa wato inda sin din ya faru kuma mayannin dayayi duka ba face mask a fuskarsa se ziyartarsa ta karshe inda har yayi nasarar hallakar da sayyeed,sannan kuma a binciken da muka gabatar,makashin

Please Login or Register in order to submit comment