Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yaje kashe hafsat ne ita kadai bawai da sayyeed,sabida sayyeed ba asibiti bane gidansa,kuma idan ma kasheshi zeyi sedai yaje gidansa ya kashesa acan,abinda muka sani shine sayyeed taimako yaje a yanda muka gani a camera shine harya fito ya ganshi ya shiga seya bisa a baya,abinda camera ta kasa nuna mana shine menene ya soma faruwa acikin dakin kasancewar babu wadatuwar haske ya sanya se bayan yayi kisan ya juya ze fita haske ya wadata kuma har fuskarsa mun gani,abunda masu qara sukace wanda yaje kisan hafsat itace wacce yafara dosawa pillow a fuska kafin sayyeed ya cece ta,idan ko har hakane furucin da muhammad yayi sam bashida alaqa da wannan kisan na sayyeed" shiru yayi hafsat gaba daya kanta ya daure sabida batayi wannan tunanin ba shi kuwa yaci gaba

"Munyi nasarar cafke wanda yayi kisan,kuma munaso yazo nan da bakin sa yayi bayanin wanda ya sakashi kisan idan har kotu ta bamu damar yin hakan" izini. Aka basu akan su gabatar da mutumin......koda alqali ya tambayi mutumin seya fara bayani kamar haka

"Da farko dai sunana kamilu,kuma ni dan area boy ne ina zamane a unguwar iraqi dake cikin garin sokoto,ina zama wani likita me suna shuraim yazo ya sameni akan yanaso in masa aiki akan wata mara lapiya me suna hafsat,ni kuwa dama ba ruwana aiki ko wane irine indai na kudine to kuwa zan yishi yabani details na komai da komai na dakin datake da time da babu yawaitar mutane awurin yakuma ce na danneta da pillow sabida gudun zargi ganin zan samu kudi ya sanya na amsa tayinsa naje nagama monitoring na wurin da komai,nashirya rana daya naje,shine qaddara ya fadowa wanda yazo tare fadan na kasheshi da wuqa ta,shine wayannan suka bi ta hanyar kotar danake hawa suka kamoni" jinjina kai kowa keyi yayinda hafsat ta rikice tabbas wannan shine mutumin data gani kuwa,dama sun buqaci ganin shuraim shi kuwa be karaji daga wurin wannan mutuminba so bezata hakan zata faru ba,koda aka buqaci yazo beyi gaddama yazo a rude ,tambayar sa akayi dalilin san kashe hafsat baiwar Allah yafara magana kamar haka

"Na kasance ina matukar san yarinyar tun tana secondry schoool amma ta wulakantani,har kuka nake mata amma bata damu dani ba,ganin nayi nayi taqi kulani yasanya nashiga malamai na sanya duk wani namiji idan ya kalleta zeji yana matukar tsanarta idan kuwa me riqon addinine yafara santa semu saka masa mafarkai na tsoro akan zamu kashe duka su biyun harse yagaji ya kyaleta,kwatsam mukazo asirinmu damuke mata ya dena tasiri bincike ya nuna mata an mata magani kuma turarukan datake using ba wani aljanin daze iya rab'ar inda take ma, da wannan naji zuciyata tanamun zafi a yanda nakesan hafsat lallai na qudurta araina idan har ban sameta ba to kuwa bazan taba bari ta mori wata rayuwa da wani namiji ba,a wannan karon kuwa naga bazan iya kashe abokina ba kuma asirin yaqi cinsu shine nayi amfani da damar kwanciyar ta asibiti na aikata hakan,amma wlhy nayi nadama musamman rashi aminina na sosai sosai" shiru aka danyi kan mutane su fara mamakin dan wannan guntun laifin ze saka tsabar rashin imani ka kashe mace har lahira,hukuncin daya dace dashi aka yanka mai aka tarwatse karar aka kuma gargadi muhammad akan furucinsa daya janyo masa cin zarafi.......



*Washe gari*

Tsaf J.A ya shirya yaje gidan su hafsat a parlor akai masa masauki,sannan akaje kiran hafsat,jiki a mace ta sakko yana ganin ta ya miqe tsaye yazo suna fuskantar juna yace

"Bakin rijiya poor barrister,the youngest one,nazone in sanar miki ki gayawa iyayen ki one week kawai na saka d'aurin auren mu,lokaci yakusa zuwa dazaki san waye muhammad,menene kuma matsayin wanda ya tozartar dashi yakuma bata masa suna a idan duniya" wasu miyau ta hadiya masu dacin gaske ta runtse idonta sosai ta bude su a hankali sannan tace

"Kayi hakuri muhammad" bece komai ba ya miko mata waya kirar iphone 6 yace zan miki waya,idan buqatar hakan ya taso,yana gama fadar hakan ya juya a nan ta durqushe ta saka kuka me tsuma zuciya.....

Mom nuaiym
    
[2/11, 8:52 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)

Wattpadd@ 68billygaladanchi

*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*



25

Da k'yar ta iya lallasr kanta tayi ciki,tarasa wazata tunkara da wannan maganar a duniya,ganin shirun baze amfaneta da komai ba ya sanya for the first time tun bayan rabuwarta da yaa shaam ta d'aga waya ta kirasa,mamakin ganin sunan ta yayi amma seya dauka da sauri ya kara a kunne tare da cewa

"Hafst ya jikinki" amaimakon ta ansa shi se kawai ta saka masa kuka,mamakin jin kukan tane ya kamashi yace cikin rud'u

"Subhanallah hafsat meya faru? Bakida lapiyane ko kuma shari'an ne be miki ba mu d'aukaka qara?" cikin sheshekar kuka tace

"Dan Allah idan baka komai mu hadu a season 7 park,inaso muyi wata magana dakai ne" batare da bata lokaci ba yace "Babu damuwa in the nxt 25 mnts zan isa wurin"

"To yaa shaam nima a haka" da kanta tayi tuqi tana isa wurin ta tarar ya rigata aranta ta ayyana wata qila yana kusa da gun dama,motarshi ta nufa kai tsaye ta bud'e gidan gaba ta zauna,gaidashi tayi sannan ta miqa masa takarda,cikeda mamakin takardar meye ya karb'a ya bud'e zare ido yayi bayan kammala karatun takardar sannan yace yana kallonta

"Hafsat se yaushe zakiyi hankali ne wai e? Mesa komai naki bakya san ki saka tunanin mezeje ya dawo aranki? Yanzu gashi kin janyowa kanki sabida babu wani wanda ya isa ya watse wannan maganar yanzu,kuma sanin kanki ne j.A babban lauya ne wanda ya shahara a fannin iya shari'a,ni bawai auren sa bane banso kiyi sabi kowa ya masa shaidar halayya ta kwarai kuma sosai reputation dinsa ya girgiza da faruwar wannan abun waya sani koda wata manufar ze aureki ta cutar wa? Babban burina shine ki samu nutsuwa a gidan mijinki wannan shine dalilin daya sanya sam kikaga na janye zancen aurenki da zanyi sabida na tabbatar wa kaina bazaki tab'a samun nutsuwa dani ba musamman akan halima,yanzu sanar dani yaya kikeso muyi kuma yazo miki da wata maganar ne?" Kallonshi tayi tama kasa kukan yanzu kam tace

"Yazo da yamman nan,yake cewa dani wai nagaya wa su daddy aure nan da sati daya yakeso kuma zan fahimci ba'a cin zarafinsa a zauna lapiya,har ya bani wannan wayar akan zemun waya idan buqatar hakan ya taso" nisawa yayi yace

"Hafsat gaskia kinyi kuskure da kika aikata wannan shirmen,babu abinda zakiyi illah kije ki gayawansu daddy ayi masa yanda yakeso kije kiyita hakuri,danni nan matsalolin dakike fuskanta suna daukarmun hankali bamu sani ba ko wannan auren dazakuyi dashi ya zamo sanadiyar jin dadin na har abada ta yiyu ma adu'ar iyayen mu ne Allah ya karba zakiji dadi" kallonshi tayi qirjinta na dokawa tace

"Baka tunanin cewar wani zargi ze iya shiga tsakani na da mutane? Baka ganin wasu ma zasu iya cewa hadin bakine kisan da aka yiwa sayyeed nida muhammad? Baka ganin kuma idan sun fada haka basuyi karya ba,muhammad so yake ya batan suna nima so yakeyi gaba daya nima duniya ta zageni,idan har na yadda da zancen aurennan tofa wlhy kowa zega tamkar ban damu da mutuwar sayyeed bane musamman lokacin nan daya diba kadan,dama ace nanda watanni hudu yace ko biyar"

"Hafsat kije ki lallab'asa da dabarunku na mata cikeda hikima sabida ya yarda abar auren har nan da koda watanni uku ne,kuma kije gidansu sayyeed na nan garin ki nunawa mahaifinsa wannan takardar ta yar jejeniya ,shima mahaifin na say kizo masa da hikima ta hanyar rokarsa akan ya nema miki alfarmar muhammad ya janye wannan agrement din ya hakura da auren ki,ta wannan hanyar kadai zaki tsira da mutuncin ki a wurin iyayen sayyeed koda kuwa an daura auren nanda sati daya" jinjina kanta tayi cikeda gamsuwa da bayaninsa

"Yaa shaam dan Allah mana muje gida na ajiye motana muyi sallan magrib in yaso ka rakani gun baban sayyeed ni tsoron wannan muhammad din nakeyi wataqil idan ya aureni ma mutuwa kawai zanyi" murmushi yayi yace "Kece mutuwan ai,sekace wani dodo".......

Bayan ta gama yiwa mahaifin sayyeed bayani yakuma ga takardar murmushi ya sake yace

"'yata wannan muhammad din yana sani ya miki haka,sabida yasan bashi bane yayi kisan so kekuma bakida wani hujjan dazaki iya cewa aa bayan an gama shari'ar,shawarata anan shine kije ki lallab'ashi" kallon dattijon tayi tace

"Daddy dan Allah ka bashi hakuri akan ya janye wannan zancen nidai bana sansa,kuma idan su daddy sukaji nayi wannan shirmen bazanji da dad'i ba" kallon ta yayi shima yace "To hafat kije gobe zan sameshi da kaina,suna kokarin barin wurin kanwar sayyeed datazo hutu daga india ta shigo,se kallon shammaz takeyi,suna fita ta biyo bayansu da suruun ganin hafsat,a can tace da hafsat

"T loojah waye wannan?" hafsa tayi sannan tace "Bros shaam my big bros kenan"murmushi tayi
"hes handsome ina sansa kuwa?" zare ido hafsat tayi

"Da gaske Baby?"

"Ea mana da gaske wlhy" murmushi tamata tace "Idan zaki auresa shikenan sena gaya masa" dariya tayi tace "Zan aure sa mana ai yafiki kyau" haka dai suka rabu baby se matsawa take da zancen shaam,koda sukaje mota hafsat ta gaya masa dariya yayi yace

"Ina ni ina ba indiya rufamun asiri" cike da zolaya tace

"Kai yaa shaam banda boye boye fa,Allah ina ganinka se wani kallonta kake kana murmushi" dariya yayi yace "Ina wasa dake zan mareki wlhy" seda sukaje gidan sannan ya karbi numer din baby haka kawai yakejin yarinyar ta masa wannan zankadediyar yarinyar lolxx.

Qememe muhammad ya kafe akan lallai baze janye qudirin saba kuma nanda sati daya zeyi auren danita,su daddy hankinsu ya tashi kowa gani yakeyi auren manufa ne na rama sunansa da aka nemi batawa zeyi.

Waya kawai ya kira hafsat bayan magaribar ranar yace da ita ta sameshi a mota,tana zuwa ta shiga gefen me zaman banza ta gaidashi,fitilar motar ya kunna fiskarsa ba yabo ba fallasa yakai hannunshi ya daga hannunta dake ciwo,dan kara ta saki ya juyo ya kalleta itama d'in shi take kallo harta soma kwallah,dauke kanshi yayi sannan yace da ita

"Har yanzu hannun nan be gama dawowa daidai bako?" batace dashi komai ba se hawaye,tausayin kanta takeji sabida sosai take tsoron muhammad,hannu ya saka ya share mata hawayen daya gangaro mata yace bayan ya dauke kanshi

"Mesa kike kuka hafsa? Banasan ganin saukar tsadadden hawayenki yana zuba a banza kinji" sauke kwayar idonta tayi kasa batayi magana ba,ya sake cewa

"Yanzu sanar dani me dame kike buqata,bazakiyi shagalin biki ba,ni zanyi dinner da reception sabida yanzu ne zanyi auren soyayya na kuma zab'ina" kallon shi tayi tana kuka tace

"yaa muhammad dan Allah kayi hakuri" dagowa yayi a karo na farko "Hakurin me kike bani" kukan ta ne ya tsananta ta dukar da kanta taci gaba da yi,tafi minti talatin tana kuka amma bece da ita komai ba seda dan kanta tayi shiru,kanta ne ya soma sara mata ta bud'e mitar da nufin wucewa cikin gida yace cikin izzah

"Nine nace dake na gaji dajin wannan zazzaqar waqar da kika sakani agaba kina reramun? Maza dawo kici gaba dayi harse ya isheni" kallonshi tayi cikeda mamaki idanta ya kad'a yayi jajir,yakuma cewa

"Dawo mana nace ki rufe murfin" a hankali ta sako kafafunta ciki batare da tayi magana ba

"Kalli idanki hafsat,duk yayi ja sabida bakyajin magana,nace dake kukan na menene amma kinki ji,kin zauna kina kuka sekace wacce ke rero waqa,idan ba so kike na sassab'a miki ba karna kuma ganin hawayenki wlhy,sanar dani yanzu tsakanin ki da Allah menene kikewa kukan?" sadda kanta tayi kasa tace "Auren ne bana so" kallonta yayi ya sakar mata murmushi

"Banida maganin wannan gaskia,so kiyita kukan,shika d'aine damuwar kodai da wata bayan wannan?" sadda kanta tai a qasa tace

"So nakeyi ka tausayawa rayuwa ta ka agazamun ka bar aurennan har nan da wata biyu na roqe ka yaa muhammad dan Allah" kura mata ido yayi na yan dakiku kan yace

"sekin mun alqawari guda biyu,tsakaninki da Allah" kallonshi tayi amma batace dashi komai ba yace

"Na farko sekinmun alqawarin bazaki taba kawo matsala me kamada kin fasa auren ba idan na qara miki lokaci,na biyu kuma sekin mun alqawarin bazaki sakeyin kukannan agaba naba sabida gaskia banaso yana batan rai" yawu ta had'iya tace

"Abba haris ya sanar dani muhimmancin Alqwari sabida haka bazan taba fasa auren kaba,sedai idan kaine kace ka fasa,kukan ma zan kwatanta" gyada kanshi yayi yace

"Nima ai alqawarin auren ki nayi,idan ko bazaki karya ba ni mezesa na karya, nasan muhimmancin alqawari ai,kije na yadda nanda watanni uku idan munada rayuwa se ayi auren" godiya ta masa ya tsare ta akan setayi dariya seda tayi dariyar kuwa sannan suka rabu,se dadi takeji......

Shaam ba kad'an ba yake jin yana san baby,sedai be sanar da kowa zancen ba se daddy kasance war shi abba haris har wannan lokacin fushi yake dashi,sedama hafsa ta saka baki yake dan sake masa kadan,cikin sirri kuwa aka shirya auren sa da baby tare da nasu hafsa,sam haleemah batasan wainar da ake toyawa ba,tunda taji hafsa zata auri wani shikenan hankalinta ya kwanta......

Hafsa gabaki daya ta rame tayi baqi,sam wani jarababben tsoron muhammad takeyi gashi abu mafi ban mamaki shine tunda ya tafi akan ya dage zancen aurensu be qara zuwa wurin taba kuma gabki daya ya dena kiranta,ita kuma duk sanda tayi yunqurin kiransa se gabanta ya fad'i, huda ce ta fad'o mata arai ta d'auki wayar ta kirata,komai da ake ciki ta sanar mata,hudan kuwa ta bata shawaran akan lallai ta kirasa,kuma ta basa kulawa as if tana matukar sanshi,wasan da yake so su buga idan ba ta wannan hanyarr ta biyo masa ba lallai akwai matsala,sabida ya shirya daukar fan sane,sosai tayi wa huda godiya koda sun dade basu hadu ba amma sosai suke hurda,huda yanzu tana germany itada mijinta.

Cikin sanyin jiki kuwa tayi kiransa a waya,kamar baze daga bama,se can taji muryarsa me saukar mata da fad'uwar gaba yace

"Hello" sanda ta d'anyi jimm sannan tace "Yaa muhammad Barka da yamma" gyaran murya yayi yace

"Barka dai" a ta k'aice,jikinta ne ya qarayin sanyi tace "Dafatar kana lafiya"

"Ina lafiya" itace amsar daya bata,runtse idonta tayi sannan ta kara budewa tace

"Yaa muhammad ka gane me magana kuwa" kamar baze amsata ba yace

"Na gane mana ba hafsa bace?"

"Ea nice ya kwana biyu?" tafad'a cikeda jin zafin wulakancin data janyowa kanta

"Lafiya lau,ya akayi ne?" dafe kanta tayi dayake barazanar rabe wa gida biyu tace

"Dama naga kusan watanni biyu ban jika ba,shine nace Allah ya sanya lafiya"

"Lafiya lau mana,me zan miki to? Ina auren Agreement ne zamuyi,sekace wata soyayya ke tsakaninmu dazanta damunki,kokuma daze kasance komai nawa sekin sani?" kasa hakuri tayi tace

"Koda na kirak bakaji na ambaci soyayya ba ai,danni a wannan zamanin banajin ma akwai soyayya,kurin dai kamata ya sanya nayi kiranka sabida ni nasanta" sarai ya sani magana ta gaya masa,amma seya dake yace

"Ni ai tun farko na sanar dake yanzu ne zanyi auren soyayah, kuma zab'ina bakijiba ne,kece bakya sona so meye zesanya na nanuqe miki?" jan dogon numfashi tayi sannan ta furzar da wani iska me zafi tace cikin wata rikitacciyar murya

"Yaa muhammad" shiru ya mata tace "Why?" cikin dakakkiyar murya yace

"Hafsatu manga yar sarki wacce maza ke rarrashi,koba haka taken yake ba?" ganin ze raina mata hankali ya sanya tankashe wayar ta ajiye,be kuma kiraba se qarar shigowar message taji a wayarta kamar haka

"This should the very first and last time dazaki ajiye mun waya,koda mun gama magana kuwa lallai nine zan zama na farko da zan ajiye" jikintane ya qara macewa jin kalamansa ta daga waya takuma kiransa yana d'agaba tace dashi

"Yaa muhammad kayi hakuri" cikin sanyin murya yace "wuyarta ka bani hakuri kai tsaye za'a wuce wurin,dama gobe zanzo zancen kayan lefenki ki shirya zuwa dubai"

"To Allah ya kara girma na gode sosai"

"Se anjima" shine abunda ya fada a zatonta ya ajiye wayar ashe be kashe ba,ajiye tata wayar tayi ta sanya hannunta a kirjinta ta shiga rero kuka tana sambatu ta shiga uku,ita dai batayi sa'an zuwanta duniya yazatyi da masifan yaa muhammad,tunda tasan hankalinta take kwasar bakin cikin d'a miji,da karfi ta furta

"Allah na tuba ka yafeni,Allah idan na aikata wani laifin ake jarabtana da wannan masifun Allah na tuba ka yafeni,kuma ka bani ikon cinye jarawar nan daka dauramun" kuka take sosai,muhammad dake saurarenta ma dafe kanshi yayi,ba abunda ke hanashi zuwa gun hafsa illah wannan kukan nata,ya tsani kukan ta masifaffen tausayinta yakeji,shidai bazece yana santa ba kuma bawai wata manufa ta cutar da ita yake da itaba kurun dai tausayinta yakeji yana gani kamar lallai idan ta auri wani zatasha wuya ne,tunda kuwa ya binciki tarihin rayuwar ta kaf,ya sani sarai dabe biyo mata ta wannan hanyar ba,shaam zata komawa kuma matar sa ma masiface a wurinta,kwanciya yayi ya runtse idansa yana mejin zafin zubar hawayenta.....

Menen ra'ayoyinku game da auren hafsat da muhammad? Ina tsumayin jin comments naku.

Vote plss

Mom Nu'aiym ca
[2/12, 8:21 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)

Wattpadd@ 68billygaladanchi

*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*


26
Washe gari da yamma hafsat tana kwance mero ta shigo tace da ita

"Kulele kije guest parlor muhammad yana jiranki yace wai baya samun wayanki" k'irjinta ne ya dan doka ta dago ta kalli meron

"Ke kika ganshi da kanki?" kallon ta mero tayi,batun yauba ta fahimci ko zancen muhammad akayi hafsat tsorata takeyi tausayin tane ya kamata tace tana dafa kafad'arta

"Inshaa Allah babu abinda ze sameki,kuma inaji ajikina tarayyarki da wannan muhammad d'in alkhairi ne mutum ne me nagarta sosai na kula da hakan tun a yanayin gaisawar da yakeyi da mutane,dan Allah ki saisaita nutsuwarki gu d'aya" batace komai ba ta sanya hijab dinta ta sauka zuwa qasan......Da sallama ta shiga parlor d'in kanta a kasa,ansawa yayi batare daya kalli inda take ba,karasowa tayi ta zauna kusa a kujerar dake fuskantar tasa tace

"Ina wuni yaa muhammad?" Amaimakon ya amsa ta seya wurgo mata tambaya

"Mesa kika kashe wayanki,bayan na sanr dake tun jiya yau zanzo?" kanta a kasa yayinda qirjinta keci gaba da uban dokawa tace

"Banida caji ne"
"Bakuda wutane?" ya wurgo mata wannan tambayar cikin tane ya juya ta dago da sauri suka had'a ido saurin janye nata idan tayi sannan tace

"Da Akwai wuta caja nane ya lala ce" D'an kishin gida yayi sannan yace

"Mesa baki saka layinki a wayan dana baki ba,kumama mesa bakya amfani da ita tunda na kawo miki ita da layine a ciki"

"Kayi hakuri" shine abunda ta furta,ya tsani wannan ban haqurin na hafsat wlhy ita komai se ban hakuri qara tubire fuskar sa yayi yace

"Zancen zuwa dubai ne had'o kayan lefe,idan ina irqawa daidai yau saura 27 day's daurin aure,so inasan sanin keda wa kuke da intl pasport wacce ayau zaku iya tashi zuwa dubai ko gobe a misali?" kanta a qasa tace

"Nida khairiyya ne,amma inaga anan ma za'a iya siya ai base anje dubai ba" kallonta yayi na yan daqiqu sannan yace

"Ba zuwa nayi ki bani shawara ba umarnin tafiyar nake baki hafsat,abu d'ayane zaki riqe mu zauna lafiya shine rashin yimun gaddama,nine da kaina zan sanarwa da Abba haris zancen tafiyar nanda kwana biyu zakuyi tafiyar,yanzu zamuje gidan Abba haris mu karbi pasport din nata,kema ki bani naki daga can zan masa bayanin tafiyar,akwai kayan dana saka aka kawo daga saudi wasu daga dubai,suma zamuje ki duba ,kayan gidane abinda be miki ba ki fada a sauya wani" kallonshi tayi taso tace dashi ai su daddy zasu siya mata kayan daki,amma tunawa da tayi yace bayasan gaddama ya sanya taja bakinta ta guntse....

Abba haris bayan ya gama jin bayanin muhammad tare dajin cewar wannan tsarin sane kana yanaso ma aqara sati biyu akan ranar daurin auren kasancewar bayaso a samo matsala tunda tafiya na Allah ne,be masa gaddama ba sedai yace sedai suyi tafiyar tare da babbar Aunty d'insu Aunty surayya,sabida zamanto warsu mata qananun yara,zuwan na surayya kuwa shine ze dauki nauyin sa,idan har mijinta ya Aminta,kara kallon abban yayi yace

"Abba zancen kaya gida kuma,dan Allah karkuga kamar na raina iyawar ku kawai dai tsarinane nine nake siyan kayan gidana da komai,matana ta farko ma nina mata, sabida haka hafsat ma na riga na siya komai,kayan kitchen ne kawai bana siya,amma komai nine nakeyi" nisawa Abba yayi

"Bazamu hanaka yiwa matarka alkhairi ba,sedai muma haqqin mune muyiwa hafsat, gyaran daki sabida haka zamu bata kud'inta tsaba,shawarar yanda zatayi dasu kuwa ze shiga tsakanin kai da ita ne,sabida kaine mijinta" Godiya yayi sosai sannan yamasa sallama,waya yawa hafsat tafito suka kama hanyar zuwa ganin kaya,kallonta yayi sosai ya furta

"Hafsat karki qara yimun karya daga yau,a ina kika samu cajin yanzu? Kuma naga wayar kusan full ma? Bakida labarin karya ba kyau,kuma batada kad'an?" sosai taji kunya wannan ya sanya ta sauke kanta qasa tace "Insha Allah bazan kara ba kayi hakuri" murmushi yayi

"Mesa kika kashe wayar ki?" murya a kasa tace

"Nima dai yau sena tashi banso a kirani,shiyasa kawai amma ba komai" be kara cewa komai ba ita mad'in shiru tayi sanda suka isa wani qayataccen gida me kyawun gaske,tun a gaban gidan zakaga had'uwarsa da qayatuwarsa ba karya...Gate din automatic ne wannan ya sanya ya bud'e kanshi yana ganin dosowar motar, a wani farfajiyar ajiye motoci ya ajiye motarsa wanda had'uwars ba'a ma maganarta, kallon ta yayi yace "Bismillah muje ciki" Batayi musu ba kawai ta bishi suka wuce,ta bayanshi take se kallon cikar halittarsa takeyi yanayin halinsa yanayin maganarsa da uban ikon sa,wata kofa taga ya sakawa wani card lokaci d'aya ta wangale,kai tsaye ciki suka shiga tun a parlor ta raina dukiyar datake taqamar wai suna da ita,gabaki dayan parlor din komai na ciki gold ne se daukar ido yakeyi,dakuna guda biyar ne acikin gidan kuma flate ne me masifar kyau se paluka guda uku da fankacecen ktchn wanda ya gama hadewa da tsadaddiyar carbinet,gas cooker ne kawai aciki se freezer ta kwance da double door,a bed rooms din kuwa duka english bed's ne aciki,dayan dakin red and white,dayan blue wanda shi kuma akwai parlor aciki da lubby me kyau ga coffee chairs a walk way na zuwa barin,kuma komai light blue ne da white,dayan dakin purple dayan kuma pink $ white se thee green wanda aciki duk shine yafi burgeta,ko wane daki da toilet nashi,wanda a iya Bathrooms din idan aka barka zaka kwana kana kallon abubuwan ban mamaki,gidan ya hadu over bayan sun dawo parlor ne ya kalleta yace

"Hafsatu manga,sanar dani tsakani da Allah ina kike buqatar a sauya miki?inda bakyso,ma'ana abun be miki ba?" kallon shi ta d'anyi sannan tace

"Ni ko ina ma yamun ko ince yamun yawa ma,wancen corridor dinne kawai za'a saka mun console,se dining shelf dababu awurin dining,shima kuma zanwa daddy magana,nagode sosai Allah ya qara girma yakuma kara budi,Allah jikan iyaye kuma ya biya bukatocinka na alkhairi" har cikin ranshi yaji dad'in adu'arta tunawa yayi da Zainab wacce sam bata taba cewa dashi ci kanka ba duk girman alkhairin daze mata kuwa,murmushi ya sakar mata yace

"Kinsan ni kwangila na bayar bansan wai ya kamata su zauna awurin ba,yanzu kawai muje shops asiya choice naki,ba wani su daddy" kallonshi tayi
"To ai yaa muham......shhhhhh yafada hade da daura hannunsa asaman lips nashi,tunawa tayi da gargad'insa na rashin son gaddama ya sanya tayi gum da bakin nata,koda suka fito kasa hakura tayi dama hafsa akwai surutu tace dashi

"Yaa muhammad gidannan yayi kyau sosai wlhy" Bece da ita komai ba kurun murmushi ya mata......

*Bayan kwana uku*

Hakan kuwa Akayi,da hafsat da khairii da Aunty surayya suka dauki hanyar dubai a ranar wata wednesday,har suka isa suka kwana suna mamakin hali irin na muhammad,be basu ko sisin siyayyar lefenba,illah kawai tunkan su isa ya sanar dasu akwai driver daze kaisu masauki daga airport,kuma suna cin abincin wurin wanda menu kawai ake kawo wa su selecting,haushi duk ya gama

Please Login or Register in order to submit comment