Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zab'i bak'in cikina akan farin cikina,meya sanya zuciyata keson wanda bashida buri illah yaga qarshenta,lallai ina cikin tashin hankali ba adadi,lallai yaa shaam da inada ikon raba wannan wahalalliyar zuciyar tawa da k'aunarka wlhy da nayi a yanzu,inama ace inada ikon raba raba rayuwata da ruhina ko zan huta da wannan baqar soyayyar da batada ci gaba ko kad'an seci baya,ina ma ace zan iya sanya hannu in lalubo inda rad'ad'in sanka yake inyi wurgi dashi,kaico na dana zab'i abu mafi muni arayuwata,kaicona dana zab'i mummunan k'haddara da hannuna khaicona dana siyo makancewar idona da hannuna kaicona ni hafsatu,kaicona ni lelen daddy da Abba" wani razanannen kuka ta saka me tsuma zuciya wanda baya misaltuwa duk kuwa cikin d'akin aka rasa me rrrashinta.......Dr.sayyeed ya tabbatar musu da cewar matsalar bame yawa bace idonta ze iya bud'ewa yanzu,ko gobe ko anjima ko wata ran ko wata shekara kokuma har abada,Allah shine yabarwa kansa sani,haka hafsat tayi wata daya a asibiti gashi sam ya kasa yiwa halima komai sabida san dayake mata kurin dai ya qaurace mata kuma sannan be nuna mata komai ba,har aka sallami hafsat ta koma gidan Abba haris.

A gida Abba haris yayi kiran shammaz agabdan daddy da momy ya kalleshi cikeda nutsuwa yace

"shammaz abinda yasanya nayi kiranka ba komai bane illah zancen komawan hafsat d'akinka wato gidan auren ta" Da sauri ya d'ago ya kalli abba yace dashi "Abba nifa na rigada na saki hafsat kuma bance zan maida ita ba wane komawa kuma zatayi,kurin dai Allah ya bata wani mijin ta aura" cikeda mamaki kowa ya kalleshi wannan karon har daddy abba yayi karfin halin cewa

" Ai wlhy tunda ka nakasa ta seka zauna da ita,so kakeyi ka gama lahanta mata rayuwa" cikin bacin rai yace

" Haba abba nifa ba qaramun yaro bane,sa annan kuma zakuce zakumun dole,yarinyar ban sota tanada lafiyaba se yanzu,dan Allah na rokeku karkuce zakumun dole kalar na farko kundai ga ba aci nasara ba,ba alkhairi a tare da wannan auren,inshaa Allah zataji sauqi ku aura mata wani,kuma ni ba qinta nakeyiba kurun dai ina gudun gurbacewar zumuncine sabida kunga bawai san aure nake mata ba,kuma ma koba itaba banasan auren zumunci" Sosai da sosai maganganun shi suka girgiza rayukan ilahirin mutanen wurin,lallai shaam baze rasa yin shaye shaye ba,Abba haris miqewa yayi yace

" Bazan maka baki ba Shammaz amma kaje duniyace,inshaa Allah kana darai hafsat zataci gaba kaikuwa kana bayan yan baya" yana kaiwa nan yayi waje,daddy ma waje yayi batare da yayi magana ranshi a b'ace momy ce tace

"kaima danane shaam amma dan Allah inaso ka dubi girman zumunci ka taimaki qanwarka,waye ze aureta tana makauniya yarinya ga qarancin shekaru ko haihuwa batayiba" budar nakinshi se cewa yayi

"momy dan Allah kiyi hakuri wlhy bazan iyaba" aikam momy kuka ta saka cikeda takaici shikuwa ko a jikinshi yayi waje abunshi....

Mom Nu'aiym
[1/22, 7:56 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

   Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)
 
Wattpadd@ 68billygaladanchi

*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*

                                     13
Yaukam rayuwar daddy tayi matuqar b'aci da wulakncin shaam akan hafsat,lallai wannan yaron yazo da salo na raini iri iri,banda haka tayaya ma agaban su kaikoma ba agabansuba zece wai baze auri hafsat ba haryana iqirarin be sota tana da lapiyaba se yanzu data zama nakashashiya,ba abunda zece dashi koya nuna masa zega iya gudun ruwanshi tare da jiran matakin da Haris ze dauka.......

   Hafsat zaune tanaso taci abuncin dake gabanta amma bata saka cokalin wurin daya kamata,har ranta takejin wani tuquqi,wannan ya sanya ta ajiye cokalin ta laluba ta gincira,duk wannan abun datakeyi khairri na kallonta tana hawayen tsananin tausayinta,zuwa tayi ta zauna kusa da ita ta kamo hannunta tace "Sister ya bakici abuncin da yawa ba kaddai harkin koshi?" Murmushin yake tayi tace " Na qoshi ne wlhy"

"Nasani baki koshiba hafsat,kawai sabida bakya saka spoon din inda ya dace ne,kiyi hakuri na baki kanki saba kuma inshaa Allah zaki warke ai haka doctor yace zakiji sauqi kinji" hawayen da dukkaninsu ke qoqarin tarewa ya silalo musu hafsat tace "Khairiyya haryaufa yaa shaam bezo ya duba niba,da gaske manufarshi kenan ya rabu dani har abada?" kukane ya kwace mata ta toshe bakinta,khairiyya tama rasa me zatace mata "kiyi hakuri hafsat,amma barin kira miki shi awaya" batace komai ba wannan ya sanya khairiyya taje waje tayi kiran shammaz akan dan Allah yazo hafsat ta damu da rashin zuwansa,beyi musu ba yace yana nan zuwa da dare.....

    A parlor zaune hafsat take a kujera me mazaunin mutum biyu,se shaam dake zaune a me mazaunin mutum d'aya,dak'yar ya iya bud'e bakinshi yace

"Hafsat ya jikinki"

"Naji sauqi Alhamdulillah"

"Akace kina nemana?" sadda kanta tayi qasa "Yaya dama zancen komawa nane gidanka,dan Allah kayi hakuri abubuwan dasuka faru wlhy ko mutuwan khaleefa ba laifina bane lokacin sa ne yayi" murmushi yayi yace

"Haba hafsat,kewai bakya fahimtar abubuwane? Ban soki nakuma zauna dakeba sanda kike mutum me lapiya,se yanzu dakika zama nakashashiya,na dade da fad'a miki sam bakin rijiya ba wurin wasan makaho bane saura miki yaushe ki gama iddah,idan ma banyi kuskure ba aiba idda a kanki,saboda haka kiyi hakuri ki kalli dahir ni bazan taba dawo dake gidana ba,ina miki ao irinna yan uwantaka matsayinki na kanwata amma bawai zancen aure ba" dukda bata gani amma hakan be hanata duban inda take jiyo sautin muryanshiba tace tana kuka

"Yanzu yaa shaam idan kai dakake dan uwana ka gujeni akan inada matsala waye aduniya ze aureni? Kaine sanadin lalacewar rayuwata,ka b'atamun duk wani abu danake taqama dashi,bani ga karatuna babu labarin future na,banida d'a ko d'aya a duniya da wanne kakeso inji?" murmushi ya kuma yi

"Hafsat wlhy kinji na rantse bazan tab'a iya zaman aure dakeba,ke ni idan ma kinamun wannan maganar haushi kike bani wlhy,kimun magana kanki tsaye indai zaki bani matsayin yayanki to zakiga gata na haduwa,amma zancen aurennan yarabu kenan har abada,idn bakida wani abun fada zan wuce"......sanda ta d'anyi shiru sannan tace

" Nayi dana sanin saninka arayuwa,nayi danasanin kasancewarka d'an uwa na jini agareni,nayi danasanin aurenka,nakuma yi danasanin aurenka,nayi danasanin kasantuwar zuciyata tawa ina ma ace canje aka mun bisa kuskure dana roqa a sauyamun da tawan sabida na kaucewa wannan wahalalliyar soyayyar,daga rana me kama da yau inaso ka nemo biro da takarda kakuma rubuta ka ajiye cewar ni hafsat nakashashiya nafita arayuwarka na har abada,na yanke duk wata alaqa dake tsakanina dakai, harta zamanka d'an uwana,ko a hanya ka ganni karka nuna sanayya tsakanina dake,bana buqatarka arayuwata ka sani ayau d'innan wlhy na tsaneka tsana mafi munin tunani,bazan hana zuciyana haukanta na sanka ba amma zan iya haramtawa rayuwata koda gaisawa dakai koda hakan yana nufin zan rasa ilahirin rayuwata kuwa tunda ai ka gama nak'asani meya ragemun,nice nan yaa shaam zan tabbatar maka da cewar bakin rijiya sam ba wurin wasan makaho bane" Yad'anyi mintuna biyu bece komai ba secan ya nisa yace "Hafsat me kuma ya kawo maganar tsana anan nifa d'an uwankine" miqewa tayi ta soma doddogara sandarta tana neman hanyar waje,kasancrwar tasan tsarin gida. Yasanya tayi amfani da basirar ta ta nufi cikin gidan zuwa dakinsu.....duk wannan zantutuukan nasu akan kunnen abba haris tausayinta me tsananin gaske ya rufe shi,daganan ya qudiri niyyar nemawa hafsat lapiya kota halin qaqa koda kuwa dukkanin abinda ya mallaka ze qare.....

    Hafsat tama kasa kuka,gaba d'aya wani mummunan yanayi takeji a zuciyarta game da shaam,tabbas yau tafara jin yana fice mata arai cikin qanqanin lokaci,wayantane ya soma ringing tashiga lalubarta tana kamowa dama wurin sazata amsa kira baze mata wuyaba ya sanya ta d'aga ta kara a kunne

"Assalamu Alaikum" shine tajiyo am fad'a a d'ayan b'angaren tun kafin tayi magana,cikin sanyin murya tace

"Amun wa Alaikassalam,barka da wuni"

"Hafsat ya gida ya kuma jikinki?" "Da sauqi Alhamdulillah" ta bashi amsa "Sunana Dr.sayyeed Hameed Ali uncle d'inki" Murmushitayi tamkar yana gabanta sannan tace "Ayya Uncle say ya aiki yakuma kwana biyu?"

"Alhamdulillah hafsat,dama Number din abban ki damuke da afile nayi tankira baya zuwa gashi kuma emagency case ne ya taso,shiya sanya nace barin nemeki ko zaki had'ani dashi"

"Babu damuwa uncle say barin je ingaya mishi seya duba last call nawa ya kiraka,amma sekayi hakuri ni kadaice adakin khairii batanan,idan tashigo seta rakani gun abban" sosai ta bashi tausayi yace "Babu damuwa hafsat,nagode sosai"
"nima nagode sosau uncle say Allah ya saka ma da alkhairi" har ranshi yaji dadin adu'arta lokaci d'aya ya tuna da matarsa margayiya data tafi ta barshi da tsananin kewa,itace take yawan masa adu'a irin wannan tun bayan mutuwar mahaifiyarsa......
  
   Office Abba yaje ya sameshi,bayan sunyi magana awaya,da suka gaisa Dr.sayyeed ya tattara nutsuwarsa gun Abba sannan ya gyara zaman gilashin idonsa yace da Abba

"yallab'ai Allah shine ya dasamun tsananin tausayin hafsat wanda tunda nake ban taba jin tausayin patient kwatankwacin yanda naji akan hafsat ba,musamman yanda na kula da karacin shekarunta, da farko dai ni haifaffen qasar India ne amma kuma d'an asalin Nigeria,mahaifina likitane kwararre wanda gaba d'aya acn yake aiki acanne ya had'u da mahaifiyata datake Ba'indiya kasancewarta musulma gaba da baya ya sanya basusha wahala iyayensu suka aminta dasuyi aurensu, acan aka haifeni kuma acan nayi karatu na gaba daya,bayan mahaifiyata ta rasune mahaifina ya dawo ainahin qasarsa wato nan Nigeria a kuma birnin sokoto,inada qanne na mata guda biyu suna gidansu mahaifiyata dake Babban birnin indiya wato Goa acan suke karatunsu,ni kadaine nabiyo mahaifina nayi aurena anan har Allah ya karb'i ran matata a wurin haihuwa......Dalilin daya sanya na baka tarihin rayuwata shine sabida inaso kaje kayi bincike kaji koda zaka da abinda zan fad'a maka yanzu,dukda yake dakai nakesan muyi tafiyar idan ma hakan ta kama" Dukda yake Dr.say yayi magana me harshe damo amma abba be katse shiba yace "Ina jinka sayyeed"

"Mahaifina ya mallaki qatotuwar asibiti tashi ta kanshi a k'asar india inda kusan garuruwa hudu a fadin qasar zaka tarar akwai branches nata,zan baka komai sekayi browsing ka gani,akwai wani qwararren likita dake aiki a asibitin na mahaifina wanda shararre ne a b'angaren k'walwa shine nayi waya dashi sabida al'amarin hafsat yana damuna a bakin shi naji cewa inshaa Allah indai tanada rabon gani a duniya Allah ze bashi ikon mata aiki kuma fitowar farko ta warke sabida badashi aka haifeta ba, dama nikuma zanje india gun yan uwana dakuma kula da asibitin ta mahaifina shine nake sha'awar zuwa tare dakai da hafsat idan bakuda damuwa,nidai ayanda nake tausayin hafsat bana san ko sisin ku har jirgi ma nine nan zan dauki nauyi amincewarku kawai nake buqata dakuma uwa uba adu'arku" sosai Abba haris yaji dad'in wannan zancen yace "wannan ai babban ci gaba ne sayyeed,kuma zancen yadda tun yaushe aina yarda zancen kuma wai kyauta duk bata taso ba nine nan zan biya komai har zancen tafiyar ma,kuma wlhy na gode nagode maka sayyeed Allah ubangiji ya albarkaci rayuwarka ya sanya haske acikinta yakuma d'aukaka,Allah ya jib'anci lamuranka ya baka wata matar ta gari ya ilmantar da bayanka yakuma tallafi bayanka sayyewd" godiya sayyeed din tun kafin abba yabar asibitin yafara processing visa batare da sanin kowaba.......

     Ranar wata juma'a hafsat na kwance ta rufe idonta acewarta ba amfanin bud'asu wayanta ya soma ringing janyowa tayi ta kara a kunenta bayan ta d'aga,jin muryanshi kad'ai ya sanar mata waye me kiran cikin shagwaban dabata masan tana dashiba tace "Uncle say se yanzu,ni baran ma kula kaba Allah kuwan" murmushi yayi tamkar tana gabanshi

" Beauty kefa rigimanki baya qarewa,wlhy Aikine yasha kaina matuqa kiyi hak'uri yanzu ya jikinki ina fatar kinji sauqi?" turo baki tayi "Ni bazan kulakaba" dariya sosai tabashi amma sabida bayasan ya b'ata ranta yace "Kiyi hakuri mana Beauty,aina sanar miki uzurina kuma fa yau zan siya miki pop corn da ice cream plus frozen coffee amor" murmushi tayi

"Ni bazaka siye ni da wannan ba bazan ma shaba,nidai kawai ka kawomun qawata dan Allah itane take d'ebemunnkewa"

"Naji zan kawo tan indai suhaila ce amma dai gaskiya se gobe,yau ina riqe sosai" murmushi tayi tace "Babu damuwa uncle say Allah ya kaimu goben" sallama sukayi sannan suka ajiye wayoyin su, hafsat se murmushi takeyi tun zuwan suhaila arayuwarta take jin sanyi abubuwa da dama suna canja mata ko yanzu tanata faman tunanin yanda zatayi idan tabar qasar,shiya sanya taso ayi auren uncle say da suhaila kafin tafiyarsu india dase su tafi tare da qawar tata me yawan d'ebe mata kewa......

Yauce ranar tafiyar su hafsat india,kowa se adu'a fatar samun nasara suke musu, tafiyar har da umma aciki, da abba......nima ina musu fatan alkhairi..

Don't forget to vote and comments......
[1/23, 9:57 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)

Wattpadd@ 68billygaladanchi

*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*




13
*FLASH BACK*

A ranar da yaa shaam yaji komai a ranar Haleemah taje wurin bokanta,kallonsu yayi itada uwarta yace

"Kunyi sakaci dukkannin aikinku ya lalace,kuma mijin yarinyarnan yaji komai ciki kuwa hadda kashe masa gudan jininsa,kunsan cewar wannan abun ba qaramun b'ata ran shi yayi ba,sabida haka wannan aikin dazakuyi bashida wani amfani,idan kuwa kunaso amasa sabon aiki daze rufe masa baki tokuwa ke Haleemah sekin baiwa Aljani kyautar mahaifarki sukutum,tareda sha'awar mijinki ma'ana zamu cire dukkanin wata sha'awa dayake da ita a 'ya mace" zabura haleemah tayi tace "Nashiga uku boka,shikenan ni bazan qara haihuwaba? Kuma shi mijin nawa baze qara samun wata sha'awa akaina ba to meye amfanin auren??" Tsawa ya daka mata

"ke!!!! Karki kawowa mutane raini kinji ko,kune da kanku kuka fada masa kuma yaji,aljani meramo yaso taimakonki ne idan bakyaso kije can,amma kin san na sanar miki asirin ze karye kuma ke zaki haukace,idan kin fisan haukar kije da mahaifar keda hankali sedai ki gani ga wari" zaro ido tayi tace "Kayi hakuri boka ba haka nake nufi,abunda ya kadar dani zancen qwace masa sha'awa" zbura yayi " K'wace masa sha'awa tare yake tafiya da sanya ya manta daduk wani abun da ya faru kuma yana ji yana gani yankasa magana koda be samu mantawar duka ba,shida sha'awar wata mace bama keba har gaban abada,kuma kece da kanki kikace dukiyarsa kadai zaki kwashe kiyi gaba to meye naki da sha'awarsa" haka dai dole suka yarda atake awurin aka hanawa zuciyar shammaz daukar wani mataki yaji a rayuwa baze iya mata koda tsawa ba,mahaifiyar haleemah ta kalli bokan tace "Aiki yayi kyau ya saki kishiyarta sedai yan gidansu nasan zasuce ya dawo da ita bama san hakan shifa ya za'ayi?"

"Dama kin dena wahalar da kanki,sabida wannan yaron basan yarinyar yakeba,bana tunanin ze maidata kudinku da jikinku su huta hakanan" Godiya sukayi sannan suka wuce masaukinsu inda zasu qarashe tambad'ewa Allah ya shiryar damu ya kare muna imaninmu.....

Hafsat Ajikin umma tayi baccinta jirgi,gaba d'aya Dr. Sayyeed duk wani motsi da zatayi idonshi na kanta masifar tausayinta yake ji, gashi yarasa dalilin daya sanya a wuni idan dai har ko kiranta beyiba seyaji wani uban zazzab'i na shirin rufeshi gaba daya,yakuma kasa fahimtar meyake damunshi arayuwa......

*INDIA*

Kwanan su biyu a can agidan su maman Dr.sayyed suka sauka dukansu kasancewar gidan babban gidane ga kuma family d'in sananne ne a mumbai, Abba haris shikad'aine ya sauka a masauki sabida ganin rashin dacewar tarewarsa gidansu alhalin shi namijine....Ranar da aka shiga tiyata da hafsat har Dr.sayyeed dashi aka shiga tunkan amata allurar da za'a shemar dabita take kuka,sosai Dr.sayyeed yaji tausayinta ya kama ta ajikinsa shi dinma sanda yayi kuka da adu'a d'auke a bakinshi aka soma aikin..........

*Bayan kwanaki biyu*

Cikeda fad'uwar gaba ake jiran sakamakon idon hafsat,wanda tsabar fad'uwan gaba ya sany Dr.sayyeed gaba daya ya kasa cin komai ranar,Kasa shiga yayi wurinta sedai a waje ya zauna wurin su Abba haris, sunfi 3 hours zaune zugum zugum kafin fitowar Dr . Din yana zuwa ya miqawa Dr. Say hannu da murmushi d'auke a fuskarsa sannan yace "Congratulations brother, we've succeeded" Miqewa yayi lokaci d'aya " Are you sure my Dr.?" murmushi ya kuma sakar masa

"Sure bros" Rungumeshi yayi sannan yaja hannunshi zuwa d'akin da hafsat take a kwance,takasa banbance tsakanin farin ciki da bak'in ciki wanne takeji,Matsawa yayi kusa da ita yace

"Sannu Hafsat,Alhamdulillah komai yayi normal yanzu" kallonshi tayi ta gane muryanshi amma bata taba zata haka kyawunsa yake ba sekace wani haihuwar larabawa,lokacin datake ganinsa bata cikin hankalinta batama iya tuno waye a kanta bare ta tantance fuskoki,ganin batayi magana ba ta qura masa ido ya sanya yayi gyaran tsayuwa yace "Beauty sannu kinji?" murmushi ta sakar masa sannan hawayenta ya silalo da gudunshi tace " Thank you,thank you so very much uncle say,may Allah bless and reward u abundantly" hannunta ya riqe sannan yace yana fad'ad'a fara'arsa " Beauty nafiso inji kina fad'an Alhamdulillah shine ya baki lapiya Allah,soni nawa taimako yazone ta hanyarshi" murmushi tayi amma ta kasa tsaida hawayenta,hannu ya sanya ya share mata hawayen sannan yace "Beauty kiji sauqi gaba d'aya da sauri so nakeyi na kaiki yawo,watannin da kikayi bakya gani duk sekin rama wannan kallon" murmushinta ta fad'ad'a har fararen haqoranta suka bayyana,sannan tace "Uncle say i so much like you,apart from my parents ur d only person nasan yana kulawa dani tamkar blood d'aya yake yawo ajikinmu,bana fatan abunda ze raba zumuncin mu har abada" murmushi kurun yayi haka kawai ya tsinci kanshi da matukar jin dad'in kalamanta "Ameen ya rab" ita kad'ace kalmar daya tsinci harshensa da furtawa,kan wani ya kuma yin magana har su Abba sun afko d'akin.. Da sauri Abba ya rungume hafsat jin ta kira sunan sa,suka yita kukan murna sam barka abinsu.

*Bayan sati biyu*

Hafsat gaba d'aya jikinta yayi saiqi har yawo sun zaga garin ba laifi,sabida har shirin komawa sukeyi,gaba daya qannen say mata suna matukar qaunar hafsat sun shaqu da ita itada khairii ba kadan ba,har roqa sukeyi wai su zauna dasu india suma suyi karatu dayake dukkansu sunajin hausa sabida babansu dabhausar yake musu magana mamansu kadai ke musu yaren india kan tarasu kuma
itama tanajin hausar,koda Hafsat ta roqi Abba haris akan abarta anan tanasan tayi karatun low mmbe hana suba har khairii yace su zauna atake aka nema musu gurbin karatu inda dukkansu suke karatu a jami'a d'aya se dai hafsat low take karatu yayinda kharii ke karantar business admn.....

*NIGERIA*

Zaune ake a babban parlor ana hirar dawowar yan india daddy ba qaramun dad'i yakejiba ganin cewar hafsatunsa harta fara sabon karatu,sabida anan niger tamayi missing semester d'aya kowa se murna yake shi sam yaa shaam hankalinsa baya wurinsu sabida damuwarsa ma ta isheshi sam baya iya tab'uka komai a shinfid'ar matarsa sannnan kumanya kasa gane dalilin daya sanya komai zatayi baze iya yi mata magana ba,tazo tayita karb'ar kudade hannunsa amma baya iya cewa da ita kanzil,daddy ne yace

" Shaammaz kaji qanwarka ta samu gurbin karatu a india,tana can mumbai tana sha'ani abinta banji ka sanya albarka ba" Dan tab'e baki yayi sannan yace "ni anawa tsarin banason banso yarinya taje wani qasar karatu,kawai dai ina mata fatan alkhairi,banza kowa ya masa aka ci gaba da hira,shi dama abba baya amsa koda gaisuwarsa ne......

Kwance hafsat take tana karatu Dr.say ya kirata, "Uncle say ina wuni" kwaikwayar maganarta yayi sannan yace "Duk wannan ladabun baze hanani zazzanekiba,an gayamun bakyashan magani mesa haka?" shagwab'ewa tayi

"Allah ni uncle say ka yarda dani ina shan magani,sameera fa qarya takemun"

"Naji amma mesa bakya shansa akan tsari,Allah idan kukayi hutu punishment dinki shine bazakizo Nigeria ba" kukan shagwaba ta saka masa dakyar ya hakura sannan sukayi sallama....

Mom Nu'aiym
[1/25, 8:54 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

   Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)
 
Wattpadd@ 68billygaladanchi

*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*

                                 
*wannan shafin nakine kyauta Ta ma'aiki,inajin dadin comment naki Allah yabar zumunci*

15
Tun bayanda su hafsat sukaji labarin auren uncle say sataji gaba d'aya duniyar ta mata qunci tayaya ma uncle say ze hanata zuwa hutu,ace bikinshi sukutum wai bada ita za'ayi yishiba,gaskia abu beyi ba kam wannan ya sanya taketa fushi dashi,shi kuwa ya kafe akan bazata zoba wanda wannan umarni ne na abba haris,bayaso ya hanata da kanshi amma sam bayaso tazo ta sake tada hankalinta akan shammaz gashi ance su kula sabida matsalar ta na heart,haka akayi bikin tanata qunci batazo ba,gashi su sumayya da suhaila duk sun tafi itada da khairii ne kawai shekara d'aya kenan rabonsu da gidan.......

*Bayan shekara Biyu*

*Takun saqa*

Ba kad'an ba hafsat kejin dad'i zatazo hutu Nigeria bayan shekaru biyu cur datayi harma da yan watanni bata Nigeria,tsakanin itada khairii bazakace wa yafi wani zumud'i ba,koda jirginsu ya sauka hafsat ji takeyi tamkar ta bangaje dukkanin mutanen dake tafiyar yangarnan ta sauko,sabida ba qaramun missing gida tayiba, A yangace yangar dabata san sanda ta koyeshiba take tafiya,ba shakka wanda yasan waccen siririyar hafsat kamar ka busata ta fadi baze yarda cewar wannan data tara mula mulan abun zama da iyayen heeps tare da doka dokan breast cewa itace hafsat d'in daba,sanye take da straight skirt na roba light blue da top red wacce ta d'ameta takuma bayya no ainahin surar da Allah ya mata,ga wani tsukakken flat tommy da bazaka tab'a yadda cewar mamallakiyar wannan booties ne dashiba,tamkar arayuwa ba'a saka masa komai aciki,sanye a idonta dan qareren qaton shade ne me kyau,a saman kanta sirirn fayafine ta yane kanta dashi,tun daga kan goshinta har girar idonta gargasa ne baqae wuluk se sheqi sukeyi,lallai hafsat tayi kyau, takuma qara girma side bag ce me kyau kalar ja rataye a kafad'arta yayinda a k'afarta take sanye da wages blue masu kayu matuqa, khairii ma irin shiga d'aya sukayi kalace kawai ta banbata domin kuwa ita pink and white tayi,sunyi kyau matuka,Abba haris suka fara hangowa inda basuyi qasa a gwiba suka zarce wurinsu suka rungume shi suna murna,

"Abba kai kad'ai kazo ina su momy?" hafsat ta tambaya cikeda k'osawa,murmushi yayi yace "Nine nace kowa ya zauna ba wanda zw biyoni duk suna gidana ku kadai ake jira yau daddy ma na gayyata can sabida yara nema zasu dawo" murmushi tayi sukayi gaba abunsu zuwa mota.......murna sosai akayi domin zuwansu anyi girke girke na masifa masu matukar qayatarwa da dai hafsat nak tayi kasancewar ta jima rabon dataci abuncin gida,su momy suka wuce ita kuwa tace bazata ba se gobe,da dare bayan sun huta wayanta ya soma ya ringing tana dubawa taga sunan uncle say,qin d'agawa tayi gaba d'aya ta turo baki tamkar zatayi kuka kuma kamar yana ganinta,kallonta khaiirii tayi "Uncle say nefa ki d'aga mana" harara ta wurgo mata sannannta tsiyayar da hawayen datake ta faman tarewa "Bazan d'agaba ai cewa yayi dani shine ze dakkomu daga airport shine be zoba kuma na kirasa yama kashe wayan" murmushi kawai khairi tayi indai fad'ane dama tasaba ganin sunayi batanan sanda suke shiryawa abunsu....

Washe gari yamma liqis hafsat tace da driver ya ajiyeta gunsu momynta,haka ta shirya ta wuce yauma kalar dressing na jiya tayi sedai wannan karon lemon green and orange tayi ga alama wannan dressing shine d'abi'ar ta yanzu,a baking katafaren gate d'in gidan tace driver ya ajiyeta yayi tafiyarsa,ba komai a hannunta se wayarta kirar iphone 7 da side bag lemon green dake rataye a kafad'arta,koda ta shigo gate d'in gidan wayarta take dannawa,acikin qatoton madubin idon dake idonta,murmushi takeyi har fararen haqoranta suka bayyana ganin khairii na mata iya shege kan whatssapp akan tafiyanta gida, jitayi ance

"Hafsat ce" D'agowa tayi fuska a had'e jin

Please Login or Register in order to submit comment