Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

muryar me mata magana tana taunar cingam dake bakinta,batace dashi kanzil ba ta wuce taci gaba da tafiya abunta,mamakinta ne ya kama shaam ganin abunda ta masa,se wani yanga takeyi yayinda duk taku d'aya se yalwataccen qugunta yayi magana,ko kallon inda yake bata qara yiba tayi gaba,sosai tabashi mamaki ya had'iye wani yawu me d'aci a rayuwarshi yace "Lallai idan kika zomun da raini sekin gane kuskurenki" ...

A parlor ta tsaya suna gaggai sawa dasu momy da daddy,daddy kallonta yayi "Lallai kulelen daddy girma yazo miki kinga yanda kika dawo kuwa,kuma yanzu naga ba rigima" murmushi kawai tayi batace komai ba, shine ya kuma cewa "Banga jakar kayankiba na zata zakizo gidane ai" sosai kanta tayi tace "Daddy nan gidan ba kowa ni gobe zan koma Allah kuwan"

"Ni bazan takurakiba kulele so karki damu kinji" Miqewa da zummar zuwa kitchen ta hadaw onion samosa da ta zame mata jiki,kullum setaci ko a can dama abuncin suce,kan taje ko ina sega yaa shaam ya shigo ko kallonshi batayi kuma kowa ya kula da hakan shi kuwa ya qurawa yalwataccen gashinta ido harta b'acewa ganinsa,zama yayi kusa da daddy cikeda fusata yace "Daddy kagan kuwa hafsat wulakancin datamun ko gaisawa mafa batayi daniba ko kallona ma batayiba" murmushi daddy yayi yace "kayi hakuri zan mata magana,wataqil fushi takeyi dakai har yanzu" bece kanzil ba harta dawo d'auke da plate dinta na onions samasas ta zauna kusa da momy

"Mommy zakiji samosar albasa zallah,da dad'i wlhy" kallonta momy tayi ta d'an b'ata fuska "Hafsat mesa baki gaida yayan kiba,ko baki ganshi bane?" cikeda rashin kulawa tace "A a momy waye kuma yayan nawa naban gaidaba,nina gaisa da duk wani jinina dama wanda ba jinina ba a gidannan kumafa kina kallo"

"yayanki shammaz nake magana,hafsat" d'an tab'e baki tayi ta yamutsa fuska "Hmmm lallai ma mommy,bakin rijiya fa ba wurin wasan makaho bane,ina nayi matsayin dazan gayarda d'anku,kuma ni wlhy Allah ya kiyaye ya zama yayana" mamakin kalamanta kowa keyi daddy yace cikin fushi "Hafsat kinad hankali kuwa,a gabanmu kike fad'ar wai shammaz ba yayanki bane" turo baki tayi ta soma hawaye sannan ta miqe ta tattare mayafinta ta yane kanta ta wurga wayarta ajaka ta shuri takalminta,wlhy indai kukace zakuna takurani akan gaida wannan wlhy bazan qara zuwa muku ba,ku tambayeshi mana yaya mukayi dashi,ai mun raba duk wata alaqa tsakanina dashi to meye kuwa ruwansa dani" tana kaiwa nan tafito daga main parlor d'n tana kuka, Ganin Uncle say a tsaye jikin motarshi ya sanya ta qara turo baki takuma qara sautin kukan datake har tana doka kafarta a qasa,da sauri yazo kusa da ita

"subhanallah Beaty,.eya sameki kike kuka?" sauke hannunta tayi tace "Bayan su daddy da mommy ne wai sena gayar da shammaz,ni kuwa alqawarin nayi har abada bazan kuma masa magana ba,ni Allah bazanma kwana musu ba" hannunta ya janyo

"Hafsat ur 19 fa,why are u still behaving so childish? Gaskia banaso kuma zamuyi fad'a,meye idan kin gayar da yayanki?" turo baki tayi tace "Uncle say bazaka ganeba banaso ina tunaninshi kuma banso ina ganinshi,tsanar kaina nakeyi kuma wlhy zuciyana yanamun zafi ko tunasa nayi,uncle say plss karkace na gaidashi kaji" tausayinta yaji ya sani sarai har gobe hafsat tanasan shammaz,kuma yasani zuciyarta a cunkushe yake da tsanar abubuwan da ya mata,kan yace wani abin daddy da shammaz sun fito,gaisawa yayi dasu yayinda hafsat tayi kici kicin,bayani daddy ya masa akan fushi zata gida,lokaci daya ya hade fuska yace "Hafsat kinsan shiyasanya na hanaki zuwa hutunnan Allah idan baki nutsuba nida kene,kina girma amma bakya wayau maza ki koma ciki" turo baki tayi tana hawaye "Uncle say bamu mafa gaisa kuma its been long,dama ba wurina kazo ba?"

"Gunki nazo amma yanzu ammun waya yayarki tana labor so zanje gunta" matsowa tayi kusa dashi ta soma doddoka k'afa "Allah ni Uncle say sena bika dama tunda nazo banga Aunty ba" girgiza kanshi yayi a gefe d'aya kuma yana jinjina girman da hafsat tayi da kyau,se d'an karen wawta data qaro,kuka kuwa ya saba kullum ne ko a waya se an masashi akan zuwa gida.....

Mom Nu'aiym

*Babu tabbacin cewar gobe zaku samu,se yanda Allah yayi ina busy ne sosai kwanakinnan*
[1/28, 8:22 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

   Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)
 
Wattpadd@ 68billygaladanchi

*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*

  * A shafin daya gabata,munyi kuskuren number,amaimakon 14 se muka saka 15,idan muka ce zamu dawo baya da matsala wasu zasu rikice sabida haka zamu ci gaba da 16 inshaa Allah,nagode.*

                              16
A asibiti kuwa uncle say gaba daya hankalinsa ya tashi jin za'a shiga da suhail cs sabida ta kasa haihuwa,sosai hankalinsa yaqi kwanciya,yakasa zaune ya kasa tsaye shi kuma ba b'angarnsa bane gefen haihuwa,Ganin Dr. Hafiz ya fito daga thereter room ranshi a b'ace ya sanya qirjin say ya doka da k'arfin gaske,yana fatar ba abunda ya faru kenan ba, Gwiwa a sace Dr. Hafiz yazo kusa dashi kallanshi yayi sannan ya d'ora hannunshi a kafad'arshi ya kura masa ido,hannun nashi Dr. Say yabi da kallo sannan a hankali ya mayarda dubansa zuwaga Dr. Hafiz amma beyi magana,cikin dakiya hafiZ yace dashi

"Im so sorry to say we lost both the mother and the child,tunka mufara thereter d'in Allah yayi ikonsa akansu kayi hakuri abokinaHaka Allah ya tsara"Kasa koda motsi yayi idonshi sun qeqeshe sunyi jajir amma ba alamun ruwa acikinsu,ihun da hafsat ta kwallah ne ya dawo dashi duniyar tunanin dayaje,da sauri sukayi kanta se gunjin kuka take wayyo ita Allah Aunty suhaila, bata taba ganinta ba se a hoto kasancewar wancen lokacin dasukayi shiri sosai ita bata gani kuma tunda ta warke bata zoba amma sunyi wata irin shaquwa mara misaltuwa kullum se sunyi waya yafi a irga,ko jiya sanda sukayi waya,yauma da safe haka, sosai hafsat ta gigice dajin zancen Dr.Hafi,say shi yama rasa me zeyi Dr.bafiz ne ya lallashinta azatansa qanwar marigayiyar ce, A haka ya lallaba yayiwa mahaifinshi waya da kuma nata mahaifin kasancewar dama basusan ankawota asibiti ba,mutuwar suhaila ta rikitar da Dr. Say sabida yana matukar qaunar matar tasa,sannan be tab'a kawo mata mutuwa ba ko kan yafita da safe lapiya lau ya barta kuka yake tayi tamkar wani qaramun yaro har akayi sadakar uku,hafsat ma gaba d'aya ji take duniyar ta mata duhu,batajin dad'in komai,haka dai dole kowa ya haqura wanda ya fisu san baiwarsa ya dauke abarsa gaba daya.......

*Bayan sati uku*

Yaa shaam zaune a parlor din gidansa kusa dashi haleema ce take ta faman taunar cingam sekace abun dole, shi kuwa gaba daki daya hankalinsa baya kan kallon dasukeyi yana gun wannan hafsat da gaba d'aya tun zuwanta ta sauya masa tunani,be tab'a zata akwai ranar da tunanin hafsat ze hanashi sakat ba,anya kuwa bazece da abba yayi nadama ze maida itaba,kai idan yaje gun abba baze saurareshiba wataqil gwara ma yaje gun daddy,da wannan tunanin yaje ya kwanta....
Niko nace hmm ubanka zakaci d'anye wlhy..

"Mero ni kuwa wai in tambayeki?" kallon hafsat meron tayi "Ina jinki mana Allah yasa na sani" gyaran zamanta tayi ta tattare nutsuwarta gun mero tace

"meyake damun yaa shaam? Naga duk yabi yayi baqi ya rame,kuma ya rage kiza kiza" kura mata ido mero tayi na yan dak'k'u kan daga nisani bayan ta gama nazarinta ta nisa tace

" kaidin mace ke d'awainiya da shaam hafsat,wlhy haleema tagama da yaa shaam ta shanyeshi tas,danma su momy sun tashi tsaye da adu'a,danma bazaki fahimta bane amma da kunnena naji tana magana da qanwarta harira akan naqasashin dasukayi,ko kad'an fa baya sha'awar mace wai sabida karya tuna abunda suka aikata,in taqaice miki dai kud'ad'e take karba a hannunshi da kadarorinsa baji ba gani nan da kika ganshi yanzu bashi da komai se asibitinsa shi d'inma sabida daddy yana tsaye ne akan asibitinsa da takardun wurin gaba d'aya,sedai tayita yawon banza nabin maza,ni a ranar danaji suna zancen aunmai asiri a ranar na sanarwa momy nanne fa aka d'an samu sauqi domin adu'o i da magungunan tsari sukayita nemar masa,gashi baya kula da ibadunsa da addininsa seda daddy ya tashi tsaye yanzu dai yaji sauqin rashin jin sha'awa duk nice yar rahoto akwai lokuta da dama da idan naje gidan nikan tadfasu suna wasaninsu wasu time ma har kwanciyar aure nake fahimtar sunayi dukda ni ban yarda da matar ba,yanzu abu daya ya gagaremu shine rabashi da matar sabida tsananin santa yakeyi fa,gashi ita kuwa komai ya samo seta qwace shi tatas ni na rasa wane irin kaine sa yaa shaam,gashi kumansu daddy sun saka yana adu'o i kema dai ki tayashi gaskia,yana cikin wahalar mace" nisawa tayi sannan tace "Allah ya kyauta musu,Allah ya shiga tsakaninsa da ita" kallon tausayi mero ta mata ganin tana kwallah tace

" Nasani hafsat har yanzu kina san shaammaz ina rokon Allah ya daidaita tsakaninku" kallonta takumayi tana me sharar kwallan daya zubo mata tace " Mero bana fatan sake zaman aure da shaam,ko a mafatki naganni matsayin matarshi lallai senayi adu'ar tsari daga mugun mafarki had'eda yin sadaka, har kwanan gobe ina san yaa shaam sedai a yanda na fahimta sam wannan bashi bane mafita agareni,so tari zakiga abubuwan damu y'an adam muke so basu suke zamtowa mafakar alkhairi agaremu,yaa shaam ko banda asiri ba sona yakeyiba kuma tsana ta zahiri,nidai wlhy kinji na rantse miki nidashi har gaban abada,ina dai masa fatan alkhairi" jinjina kai mero tayi "To Allah ya kawo miki muji na gari me qaunarki" "Ameen" ta fad'a ataqaice sannan ta kwanta ta runtse idonta......

*Bayan sati biyu*

Shaam durqushe agaban daddy da abba haris dasu momy harma hafsat wacce dominta aka tara zaman,kasancewar wai shaam yace ze aureta kuma ze barta harseta qarasa karatunta a india,kowa yayi shiru yana kallon ta tsuniyar daddy domin kuwa ilahirin jama'ar wurin kallon me bada tatsuniya suke masa harya idar,hafsat dai batace qala ba kazalika bata koda girgiza da zancen ba tunda taga yana mata bata dagawa be dena kiranba ta tabbatar cewar lallai da wata aqasa..... Kallon su Abba yayi yayi wani malalacin murmushi sannan ya kalli hafsat yace "y'ata nasan bazaki tab'a watsan qasa a idoba,ina sauraronki menene naki ra'ayin ni duk abunda kikeso shi zan miki" kallon shi ta dago tayi ido cikin ido suna had'a ido abba ya gano ta shaqa,ta nisa sannan tace idonta a qanqance

" Bazan sake fad'ar abunda zan fad'a a yanzu ba,abu d'aya nake san kusani shine,dukkanin abinda kukaji zan ambata yanzu babu wasa kokuma wani abu makamancin raini aciki,kuskurewa qa'idata d'aya ka iya janyo lalacewar komai musamman idan na aikata abinda zan aikata idan aka kuskuremun qa idar" shiru ta danyi kowama yayi tsit taci gab

"Ni bazawarace ba budurwaba kuma a tsari na addinin musulunci nice dakaina nake da haqqin zab'awa kaina mijin aure a yanzu,bazan lamuncewa zab'in kowa ba tsarin addinina zanbi, kuma wlhy summa tallahi bazan tab'a komawa auren shammaz ba,ko gawata akayi kuskuren daurawa aure da shaam ban yafewa wanda yayi ba koda mahaifinane kuwa, idan aka qarabtayarmun da zancennan wlhy na sanya qafa nashiga duniya nida gida har abada,idan dame tantama kuma ya gwada tada zancen kuga ikon Allah, ku tambayeshi kuji dalilansa naqin zama dani idan dai basankai kuke sanyi ba ai bazaku qara cutar saba kamar yanda kukayi abaya,da bakinsabyace dani ya tsaneni!! An cuceshi da aka had'ashi aure dani,da bakinsa gashinan zaune ya kalli tsabar idona yace dani Babu tabinda ze zauna da mace bushashiya ni menakedashi,mena ajiye ajikina ina fama da qasusuwa,da bakinsa ya kalli tsabar idona yace dani na dena mafarki ze tab'a had'a shimfud'a da banza irina bushashiya,ashe nidin nan icce ce a idonku,ashe bajini a jikina,ashe qarfeceni bansan dadin mijiba,idan har baku sani ba toku sani yau nasha baqar wahala rayuwa da miji fanko,ina da aure an kawar dani sabida gudun wannan yaso ya cillani gayinta banda a litttafan hausa da fina finai ina kuka tab'ajin anyi aure shekara daya amma namiji be taba koda riqe hannun matarsa ba duk sanda kuka ga jikina da nashi ya hadu tofa duka ne,kuma da bakin sa ya sanar mun cewar bakin rijiya ba wurin wasan makaho bane,shine ina makauniya zan dauki kaina inkai daidai bakin rijiya,sabida bana tsoron afkawa aciki,toku sani ina tsoro!! Na rantse da Allah kona rasa mujin aure bazan auri yaa shaam,ninan ni kadaice na san baqar wahalar danash a hannunsa,a ranar dana samu matsala dakaina na roqeshi akan waze aureni idan yasaken ya taimaka ya maidani gidansa,bud'ar bakinsa se cewa yayi dani be soni sanda nake da lapiya ba se yanzu dana dawo nakashashiya,bayan shine silar lalacewar rayuwata da quruciyana kowa namun kallon bazawara!! Kullum zancensa d'aya ya tsananeni yana tunasar dani bakin rijiya ba wurin wasan makaho bane,shine yanzu ze bazamo kome ya gani ajikina oho!!! Ko kuwa dai yanzu zan iya wasa a bakin rijiyar tunda naqasa ta tafi oho!!! D'aukacin mutanen parlor dinnan ku shaideni ranar dazaku qara zuwamun da zancen komawa gidan shaam kun rasani kenan har abada!!!!""

Jikin kowa yayi sanyi yayinda abba haris ya zabgeta da albarka,shaam kuwa ya saka kuka wiwi wai ta taimaka masa....to phaaaa..

Zaune suke idata Uncle say a babban parlor na gidan daddy se shagwab'a takeyi wai bazata koma india ba,shi biyeta yakeyi ya saba haka sukeyi da qannenshi sesu sakashi gaba abu beje yazo ba su saka masa kuka

"Haba dan Allah uncle say,idan kuma na tafi bazan qara ganin kaba fa" murmushi yayi yace "Dan Allah hafsat ki dena rigimarnan,bakya ganin khairi batayi haka ba? Ke komai se kace jin jira,komai rigima komai kuka,na sanar miki akwai wani coirse dazanyi a india na shekara daya kuma nxt montj zanzo,tunda kunfara school seki koma kafin nazo" turo bakinta tayi waje " Ni dai jiranka zanyi bazan iya juran rashin ganin kaba na tsawon wata ni yanzu im used to you over,i just cnt imagine my self with out you around" Murmushi ya sakar mata "Nima haka beauty amma ya zamuyi yanzu idan namiki aure ya zakiyi? Sekice dani zaki tafi" B'ata fuska tayi

"Ni nace dakai zanyi wani aurene,ni bazan taba aureba aje ana dukana,maza basuda kirki wlhy" janyo hannunta yayi shi yarigada ya saba da al'adar indiyawa yace

"Beauty banasan wannan mummunan tunanin dakika sakawa kanki,sam be dace kina cewa bazaki qara aure ba,adu'a zakinayi Allah ya kawo miki muji na gari me qaunarki tsakani da Allah" kallonshi tayi ido cikin ido tace

"Ni koba wannan ba bazanyi aureba,idan nayi aure mijin baze bari ina ganinka kullum ba,nikuwa that will be d worst thing that will happen to me ever,i just cnt imagine my self living a day with out u" murmushi ya sakar mata yana nazarin kalamanta sannan yace

"yanzu dai naji,amma ki daure ki koma school Allah zan siya miki sabon waya da sabon laptop da sabon ipad kuma zan siya miki sabon kaya ma,na zuwa school madam gayu" tana murmushi tace "Thank you for that,buh bana buqatar komai daka lissafa i just need u beside me,idan wannan baze samu ba,zan haqura nace haka Allah ya tsara" sakin hannun mata yayi yace yana miqewa "Thats very good of u gold,zancen waya kuma i already bought one for you, samsung s8 your favorite product,yana mota muje nabaki " miqewa tayi tana ihu tamkar ta rungumeshi,say akwai principles seyaga dama suke riqe babbar waya fa!! A hanyar fita suka had'u da yaa shaam,uncle say ya miqa masa hannu su gaisa,dakyar ya bashi hannu sannan yace " ke hafsat wai an sanar miki kowane mutum kika dakko secikin gida ake kaishi haka akeyi?? Ga guest parlor can kuje amma se ciki,ba wani privacy kuma bare ma" kallon mamaki say ya masa ita kuwa taja hannun say batare data koda kalle shiba domin kuwa ita alqawari tayi idan yayi sallama zata amsa,ita kuma tashigo koda shi kadaine a wuri zata masa sallama amma bazata taba yi masa magana ba,koda ze mata bazata kulashi ba, gabansu yasha sekace wani dolo yace "ke badake nake magana ba?" say ne yace "kayi hakuri Dr. Shammaz inshaa Allah bazan qara zuwa muku gidan bama gaba daya bare kayi fadan bare ya shiga ciki" kawai se hafsa ta saka masa kuka

" look uncle say,lemme just go n pack my things im going back to my Abba's house,im tired of this mesa daga zuwa hutu,Allah bazan kuma dawowa Niger ba sena gama school" hannu ya sanya ya dauko mata mayafin daya fadi ya rufe mata kanta sannan yace " Ina sauri ne gold,muje na baki wayanki" wani kishine ya tasowa shaam yace kai din dan iskan inane dazaka taba ta?? Dama iskancin dakuke kenan ko?" sosai rayuwar say ta baci ya wuce su zuwa mota,ya shige ita kuwa hafsat bakin ciki ya hanata koda motsi daga inda take se kallon say takeyi kunyarsa dukta rufe ta,hannun ta shaam yaja ya mannata da kofar parlor din yace " Ke wlhy ko zaki mutu sekin koma gidana wlhy ki sani wannan kayan dakika tara sena mora,bazan bari banza ta wuce niba" kallonshi kawai takeyi harya gama ya saketa batace dashi ci kanka ba,rayuwarata intayi dubu tota baci,haka ta zauna ta dinga kuka tana kiran uncle say yamma yaqi dagawa gaba daya ta damu da fushin sa,tsinuwa kuwa shaam yashata cikin kwando dubu....

Koyaya zata kaya a wannan bada qalar,gamu gani dai.....

Mom Nu'aiym ce🔨
[1/30, 8:18 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

   Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)
 
Wattpadd@ 68billygaladanchi

*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*

                                   17

Yaa shaam juyawa yayi zuwa gidansa,ransa a b'ace  yarasa dalilin sha'awar hafsat da Allah ya jarabeshi da ita,gashi sam shi har yanzu beji yana santaba,amma dai tunanin ta kullum dashi yake kwana yake kuma tashi.......hafsat har washe gari idan takira wayar uncle  say baya d'agawa duk hankalinta ya tashi, se messages take sending mai na ban hakuri sekace ita ta masa laifi,ganin dukta damu mero ta kalleta tace

" kulele lapiya dai?? Naga tun jiya kamar kina cikin damuwa?" lumshe idonta tayi sannan tace a wahalce "Uncle say ne yake fushi dani mero,sam yaqi ya saurareni" kallon nutsuwa ta mata take hankalin mero ya tashi,kaddai ace hafsat san wannan sayyeed d'in takeyi? Inko hakane wannan yarinyar taga rayuwa ita gaba daya kullum san maso wani takeyi,kuma a yanda ta kula koda tana san say din batamasan tana yiba,ta yiyu wannan karon da sabon salon daya zo mata

"Menene ya faru yake fushi dake har haka?" dafe kanta tayi sannan ta zayyane mata komai da ya faru ta qara da cewar

"Amma mero kinga ya dace ace wai ya d'auki zafi dani har haka? Bafa nice namar laifi ba,taya ma za'ayi laifin  wani can ya shafan?" nisawa tayi sannan tace "Tooh hafsat kinsan wani be iya fushi ba ta yiyu bawai fushin yake dakeba ranshi ne kurin a b'ace idan ya huce ze kiraki" kan wani yayi magana wayan ta ya soma qara,jikinta har rawa yakeyi ganin uncle say ne,da sauri ta d'aga ta kara a kunne,kasa magana tayi kurin ta sanya masa kuka me tsuma zuciya a hankali yace

"Rose menene kuma na kukan,ke komai bakida wani uzuri,kizo ina parlorn qasa a gidan daddy" zabura tayi ta suri mayafinta ta sauke da sauri,taje kusa dashi ta zauna tace tana sharar kwallah

" Uncle say im so sorry" kallonta yayi yace "meye na bani hakuri kuma me kika mun,naga cols dinki ne,inata fama attending patients jiya goda naje gida it was late i coul'nt col u back,yau kuma tun asuba aka mun waya muna emergency thereter,i had to go there wlhy kina raina,shiyasa da sauri ina gamawa da office nazo na ganki kiyi hakuri"  share k'wallan daya gangaro mata ta saka hannu ta share sannan ta kalleshi tace

"Ni na damu na zata fushi kakeyi dani,rabon danaci abinci tun jiya ma" zaro ido yayi yana kallonta "Wlhy ina ganin mutane masu wawta na dad'e sosai banga irinkiba hafsat,tayaya bakimun laifin komai ba zan soma fushi dake,maza tashi muje na siya miki abun dadi a season 7" murmushi ta masa tace "Karka damu zanyi samosa a gida" B'ata fuska yayi

"Lallai ki tashi mu tafi,banasan shashanci" ahaka taje ta sako hijab tazo suka fita,suna fita yaa shaam na danno kan motarsa acikin gidan,qwafa yayi yace aranshi lallai dani kuke zancen sena qulla maka sharrin dabakasan akwai irinsa a duniya ba !!!!!.....

*Bayan wata d'aya*

Tun bayan da su poojah suka koma school yaa shaan yake cikin damuwa,da kanshi ya fahimci cewar lallai ko bayan sha'awa san poojah ya masa mummunan kamu ba kad'an ba, gaba d'aya mantawa ma yakeyi da wata haleemah a rayuwar sa kuma sam yadena bata kud'i hasalima baya kwanciya wuri d'aya da ita sun raba jaha ita kuwa dama ba sanshi takeba wannan ya sanya bata damu ba neman mazan datake kawai tasaka agaba tana samun kudad'e dama abu d'aya ya tsayar da ita shine asibitinsa daya saura ta k'wace masa,ganin kuma baya zuwa wurinta azatonta aikin da boka yace ze koma yine na ganin sun kwace asibitin daya kuma cewa lallai ne seya hanashi jin sha'awarta,wannan ya sanya hankalinta yake a kwance,yau shiri na musamman yayiwa zuwa gidan daddy akan maganar auren sa da hafsat wanda yake wannan kadaice mafita agareshi,koda yaje ga mamakinsa daddy haquri ya bashi akan lallai se idan hafsat dince da kanta ta amincewa komawa gidan sa amma muddin ba ita kesan koma masa ba toko lallai ya zame masa dole ya haqura,da wannan b'acin ran ya koma gidan sa.

*INDIA*

Tun bayan rasuwar matar Dr. Say yake cikin tsananin damuwa,shidai sosai ba kadan ba yake santa over,yaji zafin mutuwar ta fiyeda tunanin me hankali,zaune yake a babban parlor ya rufe fuskarsa da littafin dayake nazari,tunani ne fal a ranshi na suhaila wanda sam bemasan cewar hawaye sun fara gangaro masa ba,poojah kuwa tajima tsaye akanshi tana nazarinsa wanda shigowarta gidan kenan daga makaranta,a hankalibta sanya hannu ta janye littafin dake saman fuskar tasa ganin hawaye ya sanya ta danja baya a d'an tsorace,k'ura mata ido yayi itama din shi take kallo,zama tayi kusa dashi ta kalleshi cikin kulawa tace cinkin mutuwar jiki

"Uncle me kuka kuma? Meya sameka haka?" d'an juyar da kanshi yayi yace "Hafsat suhaila na,suhaila na nake tunawa,yaushe zan samu macen da zata mayemun gurbinta arayuwa?? Wlhy ina matukar kewarta" tausayin sa ne ya kamata tace jikinta a mace "Uncle say dan Allah ka rage damuwar nan,idan kana wannan kukan mu kuma muce me? Batun yauba na kula dakai sosai kake damuwa da rashin ta koka manta cewar Allah wanda yafi kowa santa mahaliccin ta shine ya karb'e abarsa,kuma arayuwa ba'a tab'a barin wani dan wani kuma Allah shi yasan dalilinsa na dauke rayuwarta alokacin daka fi buqatarta,dan Allah kayi hakuri" kallon ta yayi yace "Na sani hafsat wlhy na sani narasa dalilin daya sanya na kasa cireta araina,kuma kullum tunanina a duniya waye zata mayemun gurbin suhaila? Waye ze soni kamar yanda suhaila take sona,wa zata kula dani kamar yanda suhaila take kula dani?" riqo hannunsa tayi sannan tace tana zubar kwalla

"Nice nan zan maka dukkanin abubuwan nan daka rasa uncle say,meyasa bakasan kawa kanka adalci ne,had'uwana dakai had'in Allah ne sabida haka tun farkon had'uwa na dakai nakeji ajikina i meant for u and u alone,Ban tab'aji araina ina sanka ba ko kadan bantaba jin soyayyarka araina ba,amma kullum ina tambayar kaina menene k'auna? Banida mutumin danike matukar kewa sama dakai aduk fad'in duniyar nan,banida mutumin danike matukar tausayi aduk fadin duniyar nan sama dakai,banida wanda nakejin damuwar sa tawace har raina se kai kad'ai uncle say,banida wanda arayuwa nakejin tamkar zan rasa farin cikina idan yana fushi dani sama dakai,banida wanda arayuwa banida burin daya wuce naganni kusa dashi sama dakai,banida wanda nakejin zan iya sadaukar da dukkanin farin cikina akansa se kai kad'ai uncle say,banida burin daya wuce farin cikinka arayuwa,babu abinda yake qayatar dani se inganka cikin walwala,babu abu mafi soyuwa agareni se ganin farin cikinka inga kana dariya yafi komai saukarmun da nishad'i,a iya tunani wayannan abubuwan

Please Login or Register in order to submit comment