Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba na haihuwa se daga bisani,domin kuwa an cire rai kamar daga sama Allah ya kawowa haj nasara cikinta samun hafsat be sauya komai ba na dangane dankaunar dasu momy da daddy kewa shaam ba......duk tabi ta qara yamutsewa batada kiza kiza,har Abba haris ya fahimci haka,kuma yayi juyin duniyarnan amma sam tace ita ba abunda ike damunta,da wannan yayi kiran khairiyya yace lallai tabi yar uwarta taji meke damunta cikin hikima domin ya kula ko wannan dawowan da tayi da dalili. Da dare hafsat ta tashi kukan data sama na rashin yayanta,wayanta ta dauko ta qurawa hotonsa ido a sarari kuwa tana kuka tace

"yaa Allah ina rokonka,ya ubangijin sammai da kassai,ya Allah ka ceceni Allah ka cire mun san yaa shaam a zuciyana,Allah ka rabani da kaunarshi,Allah ka ceci rayuwata karna mutu"" kuka me tsanani ya kwace mata khairiyya da ke kwance tana kallonta tana kuma saurarenta da mamaki tazo ta dafa tace

"Hafsat yaa shaam kuma? So? So naji kina ambata,shine zaki bari san dan uwanki ya hallakaki har haka? Kinga kuwa yanda kika dawo sekace ba poojah kulelen daddy ba? Meyasa zakiyi shiru kibar abu aranki bayan kuma kinada gatan da za'a miki abinda kikeso?" tana kuka ta kasa magana dakyar khairrii ta rarrasheta tayi shiru sannan ta kalleta tace

"Anya khairiyyah yaa shaam ze tab'a sona kuwa? Baze taba sona ba shekaru biyu kenan da yasan i a sanshi amma banda tsana ba abunda yake qara nunamun kullum,ina kyautata zaton a duk fadin duniyarnan a zuciyar yaa shaam wanda ya tsana ni kebin shedan,nikuwa bansan mesaba nayi rashin sa'an zuwana duniya wlhy inaga san yaa shaam ne zeyi ajalina amma dan Allah karki sanarwa kowa kinji?" hannunta ta kama tace

"Wlhy bazan barki cikin azaba bayan inada maganinta,wlhy sena gayawa Abba gobe da safe tayaya poojah?? Tayaya san dan uwanki ze illataki bayan kinada gatanki? Ni gaskiya sena fad'a" kwanciya tayi ajikin khairiyya tama kasa magana......washe gari khairii ko breakfast batayiba taje ta kwashe komai ta sanarwa Abba,aikam ya hau bambami yace

"Amma shine kulelen tayi shiru,shekaru biyu tun lokacin aurenshi fa kenan,lallai wannan yarinyar tasha wahala wlhy bazata sab'uba dole dan ubanshi seya aureta shi kuwa kodan halaccin ubanta akanshi,maza tashi kije anjima zan nemeku" tana barin wurin ya daga waya ya kira yayanshi da shaam akan zezo gidan ya samesu akwai magana,da khairii da Hafsat dakuma umman su khairri aka je.....bayan an gaggaisa ya kalki yayan nashi yace

"Yaya wannan ramar da damuwar da hafsat ke kici duk akan tanasan yayanta ne shaam aurenshi take sanyi ni kuwa na yanke hukuncin ayi auren tunda yanada halin yin hakan" tamkar saukar aradu haka yaa shaam yaji wani maganar da sauri ya d'ago ya kalli abba haris,daddy ne yace

"Haris ai ita kace tana sanshi shifa bamuji ta bakinsa ba,kai shammaz menene ra'ayinka?" k'asa yayi da kanshi kan yace "Daddy ni bawai bana san hafsat bane ba amma dama tun farko ita na fara aura amma sam ni ba tsarin mata biyu a ra'ayina tayi hakuri kawai ta nemi wani" umma ce ta yanka masa wani mari dabesan da zuwansa ba "Kai mara hankalin inane dazaka taramu anan ka gaya mana wani tsari to bari kaji wallahil azeem ko yanzu na mutu indai ba hafsat ce tace bata sankaba bazata aure kaba kaine kaqi wlhy Allah ya isa ban yafe maka ba indai kaine ka kuma cewa bazaka auretaba" se huci take abba haris ma yace "Lallai wannan anyi dan banzan yaro,toka sani ninan na yanke hukunci kuma wlhy koda wasa kakuma furta bakaso na sallamawa duniya kai aure kuma nanda sati biyu masu zuwa zan daura idan muka kaima ita ka dawo mana da gawarta washe gari tsabar rashin san rugura tsari" shidai bece komai ba yayinda hafsat se kuka takeyi daddy yace

"haris ina darai zaka yankewa shaam hukunci? Ina nine ubansa? To baza ai masa auren dole ba indai ina numfashi" ran abba haris ya baci ya kalli yayanshi yace

"yaya iya tsawon zamana dakai ban taba maka musu ba amma wlhy wannan karon bazan lamunta a cutar mun da 'ya ba,wlhy indai har ina numfashi nanda sati biyu zan daura aurensu sannan kuma idan yace yafasa Allah ya isa tsakanina dashi" jikin daddy ne yayi sanyi kuma harga Allah shima yanasan auren,momy ma dadi fal aranta sabida tasani hafsat nasan shaam sosai......bayan sun watse hafsat na d'akinta yayinda kahirri ke toilet shaam ya shigo tamkar wani mayunwacin zaki,tana ganin ta mike a tsorace,Da baya da baya take tafiya har suka isa bango,ya sanya hannunshi ya matse hannunta sosai yace "Kika zab'i aurena bayan kinsan na tsaneki ko? Kika zab'i aurena bayan kinsan zakisha uquba a hannuna? Kika zab'i had'ani da iyayena sabida tsabar san zuciya ko?? Wlhy ki sani se kin gwammace kid'a da karatu indai muddin kika yarda kika shigo hannuna,sekin gwammace da bakizo duniyaba sekin kasa tantance nine kuwa kobani bane,shawara nake baki ki janye inba haka ba ko hmmm wlhy senci qaniyarki da mai da yaji,k'aramar yarinya se iskanci banza tambad'addi'ya....yana kaiwa nan ya saketa ya juya,ita yauma ta kasa koda kukanne sabida bakin ciki,gashi sam bazata fasa aurenshiba koda ze yanakatane gida biyu idan anyi auren......hmmm hafsat kenan anya baki daukowa kanki masifa ba kuwa??....

Mon Nua'iym
[1/21, 7:15 AM] Mmn Sadeeq: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

   Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)
 
*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*

Wannan shafin nakine kyauta Aunty me jiddah musa,Allahu ya wadata ki da hasken rayuwa ya sanyaki a aljannarsa madaukakiya

08
Mamakine ya kama hafsat sanda ta farka taga har qarfe tara ta gota sauqinta daya tana fashin sallah,jiki ba kwari ta tashi ta shige toilet tayi wanka ta sanya rigarta mara nauyi pink color doguwace har qasa ta sanya kula bayan ta tufke kanta a tsakiya sannan ta fito zuwa ktchn indomie da kwai ta dafa ta dawo parlor tad'an tsakura kad'an ita har yanzu ta kasa gane meyene yake damunta wasu lokutan tanaso tayi kuka amma fir se hawayen suqi zuwa tama kasa tunanin komai gaba d'aya,ta kunna uban fankacecen tvn dake cikin parlor din amma takasa fahimtar me akeyi abinda yafi bata mamaki shine batasan tunanin me takeyiba idan za'a yankata batasn me take tunaniba abu daya ta sani shine wani zafi na musamman zuciyarta ke azabtar da ita dashi wanda kuruciyarta ta sanya ta kasa gane dalilin zugin....a haka yaa shaam ya shigo ya sameta bayan yayi amfani da key dinshi yashigo gidan kasancewar yayita faman knocking bata bude ba,kallon tsana ya wurga mata sannan yace " ke hafsat dama tsabar rainin hankaline ya sanya kina jina ina knocking kikamun banza?" gani ko motsi batayiba ya sanya ya matsa kusa da ita ya doddoki kafad'arta firgigit ta dawo daga duniyar tunanin dataje,da sauri ta miqe tsaye tace cikin tsoro "Na'am yaa shaam" harara da kallo me nuna tsananin tsana ya rabita dashi

"kina nufin duk wannan knocking dana jima inayi bakijiba,tsabar zamanki sokuwa,kinzo kin tasa tv a gaba kina kallo,Dabadan gidanmu daya ba kuma nasan acikin daula kika taso danace ke dinnan anyi daqiqiyar yar qauye,zuwa nayi inji meyene ya hanaki zuwa ki taya haleemah ku hada breakfast kokuma harkin fara tunanin cewar kishiyar kice kin fara kishi da ita?? Sadda kanta tayi kasa tanaso tayi hawaye koda wannan gululun bakin cikin datakejin ya tasomata ze kwanta amma ina sam ta kasa takuma rasa dalili,abin se yawo yakeyi yana mata sintiri tsakanin maqoshinta zuwa cikin yayan hanjinta dakyar ta iya furta kalmar

"kayi hakuri na makarane" tsaki yaja "ki tabbatar kinje yanzu kun daura girkin rana da ita sabida ba baiwar gidan uban kowa bace dazata girka abinci agidan,kuma ni bazanci abuncin yar aiki ba" Batace komai ba ta juya da siririyar halittarta zuwa ciki domin dauko hijabi,wani tsakin taji yaja a sarari ya furta " Sabida ansan ba wanda ze daukeki da wannan bushashen kunkurun tamkar na marainiyar kaza shine za'a cinnamun,mace se kace allo samb'al haka" sarai ta jiyoshi wani azababben baqin cikine ya dunqule ya sake taso mata mara misaltuwa fatanta daya tasamu tayi hawaye koda ta samu salama amma sam abun yaci tura ta kasa,da wannan ta dauko hijab dinta tafito,bayanshi tabi har sashen haleema ba wani nisa a tsakaninsu kofa kawaice part din kofofinsu suna kallon juna,suna shiga parlor din haleemah ta taso ta rungume shaam,shi kuwa ya manna mata sumba a goshi bayan ya sauke hannayenshi a saman faffad'an kuib'inta ya sauke yana me shafar manya manyan mazaunanta,wani shagwab'ewa tayi tace

" Boo mie banfa karyaba" hannunshi ya kuma saqalawa a kugunta " Bazaki iya girka komai bane da kanki sweetest?" gyad'a masa kanta tayi cikeda shagwab'ar da sam bata karb'eta ba tace " Ni kasanfa jiya baka wani barni bacci ba na gaji kuma chips nake sanci with liver sauce" kallonsa ya maida kan Hafsat "kulele kije ki hada mata breakfast dinnan datakeso sannan bayan kin kammala ki daura lunch kinsan kuma banaso ya wuce 1:00" murmushin yaqe tayi batare datayi magana ba ta wuce su zuwa inda take saaran nanne kitchen din sabida kula da tayi komai na tsarin gidan irine dayane da nata kayane dai ta kula kowannensu da irin nashi,taje ta had'o breakfast din ta kawo dinig ta ajiye sannan ta juya zuwa daura na rana,zuciyarta tana mata suya sosai a daddafe ta kammala girka musu chinese rice da veg pepper chicken and mock champagne drink,a dining ta jere su bayan ta kammala had'a colslow sannan batare data d'ibi komai aciki ba,ta juya zuwa part d'inta,wanka tayi ta sauya kaya sannan tayi kiran umman yaa shaam ta asali akan a aiko mata abinci,da wannan umman ta kira shaam akan yazo ya karb'a wa hafsat abinci,da mamaki yafito parkor din gidanshi ganin kayan abinci a jere ya sanyashi mamaki amma batare da wani dogon nazariba yafita yaje ya karbo ya dawo, da iya karfinsa ya banko kofar gidan ya shigo a parlor ya sameta kwance ta daura wayarta asamn flat tommy d'inta tana tunanin data saba wannan shigowar da yayi a haka be sanya tako motsa ba sabida ta shiryawa kanta tarb'ar duk wani bakin ciki dazezo mata bama yanzu ba har nan gaba,a kanta ya tsaya "Wane munafuncinne ya sanya dakika girka abunci baki ebi naki ba sekika kira sabida ke ba Allah aranki burinki kawai kiga kin had'ani da mahaifiyata,shegiyar yarinya me munafuncin tsiya wlhy kika kuma mun haka sena illata miki fatar jikinki kuma inji zancen nan gidan agidan daddy ko gidan Abba ko hmmm rahbb wlhy nida kene,kuma zanyi baqi da dare kiyi girki a nan part d'in" Harya gama fadan shi ko motsi batayiba a haka ya juya be jima da fitaba sega su huda lokacin kuwa har 3 ta gota ba karamun sanyi tajiba atake huda ta tayata suka hada girki me yawan gaske basu suka zauna ba se 6, wanka hafsat ta sakeyi sukayi sallah sannan suka kule d'akin hafsat kallon ta huda tayi tace "Qawata nasani kina cikin damuwa me tsananin yawa kuma na fahimci hakan tun zuwana,nasani bakyaso ki tattauna matsalolinki da kowa amma ki sani hafsat kin burgeni matuka lallai kinyi hankalin da ban zata kuma inaso naja hankalinki akan abu d'aya,karki kuskura ki sanar wa iyayenki irin zaman da kike acikin gidannan,ke bama suba kowa harni,duk sanda kikeda wani matsala kimun matsal ki gayamun sabida yawan barin abu a zuci yana sanya ciwon zuciya,karki yadda da kowa se kanki,kuma bawai rashin fad'a ba hadda nuna wa dan Allah yar uwata kina daure wa kuma kina jure duk wani wulaknci da shammaz ze miki,kiyi zaman aure me kyau kindaiga ke qaramar yarinyace idan kika biyewa waccen tsohuwar matar wlhy wahala zakiyi sosai sabida nisam ban yarda da ita sabida haka ki kiyaye kinji" se a sannan taji wani kuka ya qwace mata rungume huda tayi ta dinga kuka seda ya isheta sannan ta sake huda ta mata suka yi sallama akan washe gari zasu dawo.......

Mom Nu'aiym
[1/21, 7:15 AM] Mmn Sadeeq: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)

Wattpadd@68billygaladanchi

*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*

09
Da darema haka ta zauna zaman jiran yaa shaam amma shiru kakeji tamkar an aiki bawa garinsu,haka ta kwana ranar kam tana rusar uban kuka,tana idarda sallan asuba wayanta ya soma ringing tana dubawa tagan sunanshi gabanta ya fadi, jiki ba kwari ta d'aga kiran,yace da ita "Karfe 9 zanyi baqi saga abuja zasu sauka a lodge su uku ne ki hada break fast before 8 sabida nafiso su taradda shi suna zuwa" to kawai tace ta ajiye wayan tana sharar kwallah,ga ciwon kai sabida kuka da rashin bacci ga azabar aiki sekace jaka,a daddafe ta hada musu finger sandwitches da sultan chips fried chicken and jello,se 8:15 ta kammala,tana shirin fitowa kitchen d'in ya shigo da sauri taja baya ta durqusa har qasa "yaa shaam barka da kwana" harara ya wurga mata

"ke jakar gidan uban waye wai? Bance dake before 8 ki kammala ba yanzu karfe nawa?" sadda kanta tayi kasa wani qututun bakin ciki ya tasoma mata ta kuma rasa dalilin daya sanya sam bata iya kuka idan yaci zarafinta sedai zuciyarta ta dinga wata suya me azababben rad'ad'i,da k'yar ta lalubo kalmar "kayi hakuri" tsaki yaja "Dama mana kullum kece ayi hakuri,idan kin isa gobema na sakaki aiki na baki lokaci ki wuce time d'in wlhy zaki d'and'ana kud'arki a hannu" batace kanzil ba taje ta dauko warmers d'in data zuba abinci aciki ta sakosu acikin wasu cute baskets guda biyu ta ajiye a gabanshi ta juya zuwa d'akinta cikeda qunci,tana zuwa tayi kiran umma akan zancen yarinyar dasukace zasu kawo mata me tayata aiki,sabida a yanda ta gaji yanzu bataji zata iya girka lunch and dinner kuma taga har haleemah tafara fita aiki tun jiya,bayani umman ta mata akan an kawo yar aikin khairiyya zatazo ta kawota anjima kadan......

*Bayan wata biyu*

Rayuwa a haka taci gaba wa hafsat cikeda qunci da wahala,gashi duk k'wak'war mutum be isa yasan abunda ke damunta sabida dama batada jiki balanta na kace tayi rama,sannan kuma bazaka gane a fuskarta,tana zuwa school yanzu 200l suke kullum huda cikin bata shawarwari na kwarai take akan tayi hakuri kasancewar itace kadai aduniya tasan meyake damun hafsat,kuma har wannan lokacin shammaz baya kwana gidan hafsat indai abubuwan more rayuwane da kudade sedai ta baiwa wani amma sam ba magana me dadi a tsakaninsu wasu lokutan sam ko gayar dashi tayi baya amsawa,yau agajiye ta dawo daga skul tana fitowa wanka wayanta ya soma ringing,d'agawa tayi ganin sunanshi yace " Yanzunnan ki kawomun abinci yunwa nakeji" cikin takaici tamkar zatayi kuka tace

"yaya yau ba abunda naci wlhy yanzunnan na dawo daga skul ko sallah banyiba dan Allah kace Aunty haleemah ta baka mana" wani mirmurshin mugunta yayi da har tana jiyo sautinsa yace " Ita d'inma yunwa takeji kuma yauma agajiye ta dawo ke muke jira ki bamu abinci kuma 1 hour kawai na baki" yana kaiwa nan ya ajiye wayar,cikeda takaici taje kitchen ta dafa musu sphagetty bolognese da orange juice tafita kaimu su haushi tamkar ta had'iye zuciya ta mutu,da sallama tashiga parlor din amma abun mamaki se numfarfashi take jiyowa juyawan dazatayi tagansu akwance suna kissing junansu shaam se shashafa leemah yakeyi yana mamatsa breast dinta kai abubuwan data gani sam bazasu fad'uba,wani takaicine ya taso ya tarnaqeta a wannan lokacin ji hafsat keyi tamkar ga kashe kanta har lahira,da kyar tayi karfin halin zuwa dininga tabajiye kayan ta juya,abunda yafi bqanta ranta shine yanda sukayi tammar basu ganta ba kuma sarai ta sani dukkaninsu ba wanda be sanda zuwanta ba wani abin ma har da gayya suke yinshi,wanda sosai ta kula Aunty haleema wannan surutun datakeyi danta gantane,a wannan ranar kuka hafsat ta kwanayi ko abunci bata iyaci,Allah sarki qaramar yarinya akace ana wata ga wata domin kuwa tun daga sanda hafsat ta gansu a haka se wani azababben sha'awa yake taso mata gashi wannan lokacin ne tashen balagarta seta rasa yanda zatayi a haka take danne zuciyarta tana adu'a Allah ya kawo mata d'auki...

Ranar wata juma'a bayan sallan isha tashiga part din haleemah sabida tanasan ganin yaa shaam akan zancen bikin huda dayake wani satin za'ayi tana zuwa kofar d'kin tajuyosu suna iskancin nasu dasuke ihu sekace wasu maguna,juyowa tayi cikeda takaici anan taci karo da abinda tangamemen tv n dake parlor din ke haskawa wato BF,gabanta ne ya fad'i ganin me akeyi take taja baya se kuma wata zuciyar tace kindaiji ana labari amma yaune ganinki na farko,jeki ki kalla...da wannan ta tsaya ta kurawa tvn idon tana kalon masha'an da ake tafkawa rashin kunya iri iri,dakyar ta dakatar ta juya zuwa part d'inta jikinta har rawa yakeyi wasu abubuwa takeji suna mata yawo kasa haqura tayi da tambayoyin da zuciyar ta ta gaya mata ta zari key na motarta zuwa gidansu huda......kallon huda tayi bayan sun zauna a d'akinta tace bayan ta tattare nutsuwarta zuwaga hudan

" friend mene ne sha'awa? Yaya kakeji idan kanajin sha'awa?" kallon mamaki hudan ta mata tace "Ban fahimcekiba?" sosa kanta tayi ta labarto mata tun farkon ganinta dasu shaam dakuma abu da ta gani ayau,ta qara da cewar "Huda wasu lokutan sena kasa bacci kinga har kuka nakeyi sena ringajin ina matukar sanjin abinda Aunty leemah keji tana sambatu idan yaa shaam yana mata wannan abun,kuma kinga yau danaga turawannan suna wannan abun sena ringa jin dadi sosai nima inaso kuma naji na rage yawan sha'awa shine nakesan siya nakuma ana yawan cewa haramun ne kallon wayannan abubuwan kuma yana saurin kashe ido?" cikeda tsoro huda tace

"kinga hafsat wlhy ki kama kanki,inake ina kallon wannan abun?? Masu siyarwa ma karuwai kad'ai suka san inda suke masu browsing a waya kuma wlhy duniya tana kallonsu sosai da sosai,sa'annan na kula kinada karfin sha'awa sabida haka wlhy kine ki samu mijinki kice dashi kina buqatarsa inba haka ba wahala tana ganinji,kuma wlhy idan nakuma jin wai zaki siya wayannan mugayen films senaje na fadawa momy,ki barsu yaa shaam matarshi batada maraba da karuwa wlhy ni sunaso su b'atamun ke,wainikam ma tukunna tsaya sanar dani kina yawan adu'a da tsayuwar dare?? Kuma kina azkhar?" dan sosa kanta tayi tace "Gaskia bana,wani yi ina dai adu'a"

"Toki riqayi akan mijinki da duk wata damuwarki kinji huda,adua yana da kyau da kyautata ibadu yawan yin azumin nafila da sallar nafila dakuma azkhar,kina yiwa qananan yara sadaka tunda baki rasa ba kinji,ki cire ranki da wannan mugun kallon indai ba wuta tsundum kikeso kije ba,kuma masu san kalllon wannan ma idan suka saba basa iya denawa,sekiga idan ba namiji a tare dasu suna yiwa kansu abubuwa da hannu kuma wlhy masifa ne Allah ma yayi alkawari. Azabtar da masu irin wannan mugun aikin,seki kiyaye kinji qawata" gyada kanta tayi alamar gamsuwa sannan tamata sallama tabar gidan,huda se tausayinta takeji matuka.......hafsat se tunanin rayuwarta takeyi da abubuwan ban mamaki datake ta faman gani arayuwa,a haka ta isa gidan cikeda damuwa,a harabar ajiye motocin gidan taci karo da yaa shaam tamkar bashiba,bashida niyyan koda kallonta ne balantana yamata magana,da sauri ta qarasa gunshi

"yaa shaam ina wuni?" "Lapiya" ya amsa a taqaice yana shirin shigewa motarsa takuma kallonshi tace " yaa shaam magana nakeso muyi" batare daya kalletaba yace "Enhmm"

"Dama nikam wai yaya banida wani haqqi a gidannan ne koda na kwana a part dinane yanzu kusan watannina biyar agidannan amma koso daya baka taba kwana bangarena ba atare dani" wani kallo ya wurgo mata ya murtuke fuska sannan yace

"Idan tunanin kike kinada wani haqqi a kaina to kuwa kinyi babban kuskure domin nidai,ni shaam wlhy nafi kardinki sam *Bakin rijiya ba wurin wasan makaho bane* bakida wani abu ajikinki ko a fuska daze gayyaceni kwana sashen ki,sa annan kuma bakida wani diri na ya mace dage gayyaceni zuwa shimfidarki,wlhy Hafsat bakida banbanci da namiji awurina,iyayenki sun cuceki domin nidai bazan taba iya furta kalmar saki agarekiba kamar yanda bazan taba iya makwanci dakeba sabida haka idan ma mafarki toki farka samni kam bana san mace sekace tsinken stintsiya se dare kamar wani daren yunwa,kuma me harma kinyi girman dazaki tareni da wani haqqinki wlhy kika kuma mun irin wannan maganar sena tattaki mara kunya fitsararriya haqqin uban wahe dake a hannuna sekace da yunwa take kwana a gidan" batare datace komai ba tayi ciki aranta tace "Nice ma bankai mace ba,nice ma ban isa yasoni ba,nice banida banbanci da tsinken tsintsiya" ko wannan daren hafsat kasa bacci tayi kuma se zazzab'i me zafi ya rufeta Allah ya taimaketa ta kammala exams nata gaba d'aya........washe gari yayi kiranta wai tasan haleemah nada juna biyu bata iyacin abinda ta girka ta kawo mata abunci,tace dashi "yaa shaam nima a kwance nake ko bacci banyiba wlhy banida lapiya" tsaki yaja yace wai mintuna talatin yabata ta kawo kalacin....

Mom Nu'aiym
[1/21, 7:15 AM] Mmn Sadeeq: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

   Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)
 
*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*

    *Wannan shafin nakine maryam Abdullahi gumel,nagode da qaunarki agareni*

10
Tunda hafsat tashiga gida take rusar uban kuka daganan tayi alqawarin ficewa sha'anin yaa shaam koda kuwa soyayyar sa zata hallakar da ita har abada.....da wannan ta mayarda hankalinta akan karatunta matsalar fa d'aya tsananin sha'awar dake damunta kullum ba dare ba rana,ta rasa yanda zatayi da kanta kuma tayi alqawarin koda huda bazata sake sanarwa da duk wata matsala tata ba zata qalubalanci rayuwarta ita daya, amma fa sam bata acikin walwala.....yau dai shirin zuwa gidan momy tayi sabida sunday ne ba school,harta shiga mota yaa shaam ya tsaidata "Kije ki dafa mana abinci sabida Babyn shaam bata da lapiya kin kuma sani sarai tanada juna biyu bata iya cin abinda ta girka" tamkar zata yi kuka haka ta ji amma seta daure batace komai ba tafito zuwa cikin gidan,a bangarenta ta girka komai sannan ta shirya ta dauka takai bangaren haleemah,tana zuwa ta ajiye a dining ta sanar musu,seda haleemah ta kalleta sannan tace,cikeda sigar rarrashi "Dan Allah hafsat kiyi hakuri wlhy bazan iya cin komai ba se indomie,ki daure ki taimaka ki girkamun" kallon mamaki tabita dashi sannan batare datace komai ba ta juya zuwa ktchn din a gurguje gani karfe uku ta gota momy se waya take mata akan bata zoba ta dafa ta kawo mata,har takai kofar barin parlor din tajiyo karar daya bata mamaki "Nashiga ukuna ni haleemah,wlhy boo me baran iya ciba yaji ne aciki sosai ga kuma magi yamun yawa" wani mugun kallo shaam ya wurgawa hafsat

"muguwar yarinya dawo nan ai kinsan muguntar da kika kullah me baqar zuciya,dan ubanki da dakikasan bazaki iyaba meya hanaki kanki tsaye kice bazakiyiba,wato wannan cikin na jikinta shi kikeso ki kashe ko? Muguwar banza muguwar wofi wlhy yau bama inda zaki,kin dinga girka mata indomie kenan se sanda kika girka mata kalan wanda tace ya mata" kan tayi magana kuka ya kwace mata se kuma wayanta ya soma ringing,dagawa tayi tana me hadiye kukan lokaci daya ta qaqalo murmushin daya baiwa shaam mamaki takuma saisaita muryanta

"Momy dan Allah kiyi hakuri,wlhy Aunty Haleema ne batada lapiya inaga kamar bazan samu damar shigowa ba yau,kinga ita kadaice bazan barta haka ba" murmushi momyn tayi tace "Eyyah Allah sarki Allah ya bata lapiya ki gaida ta kinji,yanzu se yaushe??"

"gobe sha biyu nake qare lectures inshaa Allah daga school se gidanki momy karki damu" "To Allah ya kaimu hafsat Allah ya miki albarka kinji" Ameen kawai tace ta ajiye wayan sannan ta juya zuwa kitchn din,dafa wani tayi bata saka yaji ba ta kawo,ai loman farko ta zubar aqasa ta

Please Login or Register in order to submit comment