Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kalli yaa shaam fuskar nan harta soma kawo ruwa "Yaa shaam kaci kaji wlhy ba taste yanzu fa ko d'an green pepper ta saka man amma haka tayishi,Allah ni bazan ciba kuma" Tsaki hafsat taja bada shirinta,dama fa hafsat gwanar rashin kunya ce kurin tsoron yaa shaam ne ke durqusar da ita,yau kam ta cika fam

"Gaskiya Aunty haleema bansan ya kikeso na miki ba na dafa wancan kince bazakiciba na dafa wannan indomie kince yaji,na kuma dafa wani kince ba yaji ni kije ki dafa da kanki,ko aikin bauta nazo na muku wlhy ko zaku kasheni bazan dafa muku wani ba" kallon mamaki shaam ya mata domin shi har tasoma bashi tausayi ya matso kusa da ita yace "Jeki kitchen ki dafa mata me abunda takeso" tsayuwa tayi a wurin taqi koda motsi,saukar wani kyakyawan mari taji seda ta ga wasu taurari na musamman,yace "ina wasa dakene? Nace kije ki dafa mata wani" kamar yanda batayi magana ba haka bata koda motsa ba da wannan ya shaam ya soma dukanta tamkar wani mahaukaci baji ba gani seda haleemah taga tayi lilis sannan ta saka kukan muna furci tazo tana qwatar hafsat "shaam dan Allah kayi hak'uri,idan ka illatar da qanwarka ni za'aga laifina kuma kaga ai tama gaji ni dama ba ina nufin ta dafa wani bane,nama ji na qoshi tea ma ya isheni,miqewa tayi tsaye ita kuwa tayi hanyar waje har wannan lokacin bakinta be mutuba tana kaiwa kofa tace "kuma wlhy ko zaku kasheni na dena muku girki kenan har abada" bebi ta kanta ba ya dawo wurin haleemh da rarrashi......

Bayan magrib tana d'akinta tana rusar uban kuka abinta shaam ya shigo,zama yayi kusa da ita da yace "Hafsat ni kikewa baqar magana??" bata kulashiba yace "Kinaso na ci gaba da lallasaki kenan?" budar bakinta se cewa tayi

"ka lallasanin ai akwai Allah,kuma wlhy duk wanda yaci zalina Allah ya isa" mamakin kalamanta yakeyi "waye yake koyar dake rashin kunya hafsat?" nurguda bakinta tayi sannan tace

"Wanda suke cin zalina kullum kuma Allah ya isa" miqewa yayi yace "hafsat kin janyowa kanki zaman bakar uquba a gidannan sabida kinga ina miki wasa shine kikemun wulaknci san ranki ko? Wato ke kin isa lallai kuwa zakisha baqar wuya a hannuna" bata kulashiba taci gaba da kukanta yayi ficewarshi yana mejin tsananin tsanar hafsat,tundaga wannan ranar kuwa shaam komai qanqantar laifi idan hafsat ta masa se duka har yakasance daga dazan ya sanyata abu jikinta ze soma rawa,kuma da sauri takeyi,sedai kwanakinnan batada lapiya ko kadan, da wannan ta sameshi tace dashi "Yaa shaam kwanakinnan da zazzab'i sosai nake kwana ko zakaje dani clinic dinka a dubani" kallon ta yayi ya rufe jaridar dake hannunshi " A matsayinki nawa zakijemun clinic? Kinga nawa clinic ma na masu matsalar zuciyane,sabida haka kije wani asibitin kawai" batace masa komai ba taje gun huda daganan suka wuce wurin mijin ta dayake shima likitane,binciken farko ya fito da tambarin heart problem ajiki,sosai sadeeq ya shiga cikin shock,huda ya fara kira a gefe yace

"Baby wai anya qawarki ba kashe kanta takeso tayi akarin banza ba @kan soyayya kinsan kuwa ciwon zuciyane da ita,fisa bilillah @her age gaskiya bance ba'a samun irin wayannan cases dinba sabida yanzu irin wayannan cutukan sun yi yawa a wurin yarama harda hawan jini,amma ni tausayi take bani gaskiya me take sakawa a zuci har haka,jininta mafa hawa yakeyi" dafe kai huda tayi tace dashi "Hubby kasanme har fa dukanta yakeyi sannan ko kwanciyar aure bayayi da ita,ga school ga problem dinshi girki mafa ita kewa matarshi ko sau daya betaba kwana a bangarentaba,ga hafsat da zurfin ciki tacika barwa kanta abubuwa ni wlhy har naji kaina yana ciwo ma,yanzu meye solution?" dafe kanshi yayi yace "Amma gaskiya shaam ya bani kunya wane irin sakarai ne qanwarka guda daya matar da iyayenta suka nuna maka so tamkar sune suka haifeka shine tsabar mugunta yarinya ko 17 bata hada ba zaka hadata da ciwon zuciya mugun banza" wurin hafsa suka koma dakyar sadiq ya tattaro nutsuwarsa ya shaidawa hafsat komai cikeda rarrashi da nuna mata hanyoyin dazatabi tunda abin beyi nisaba,sosai hafsat tayi kuka sannan ta nuna musu su rufa mata asiri karsu sanar wa kowa,hakan dai aka bata magunguna ta koma gida da damuwa me dinbin yawa wacce ta ninka tada,tundaga wannan lokacin hafsat ta dawo sukuku sam bata walwala gashi batada lapiya a haka har Haleemah ta haifi yaro namiji,wanda bataje wankan gidan ba kuma tanayin 40 days aka maidashi kwana wurin hafsat,komai wahalar khaleefa hafsat keyi baji ba gani, harma ya saba sedai yasha madara wasu lokutan idan ya tashi a bacci da dare ya saka kuka setayi ta rarshinsa idan yaqi itabdinma seta saka mar kuka suyitayi se me aikinta tazo ta karb'eshi.......a haka har khaleefa yayi wata hudu a duniya,san suniya shaam ya dauka ya daura akan yaronnan bama a san ranshi yake barinshi kwana acan ba,danma bayason bacin ran haleema na......

Ranar wata juma'a Cikin dare khaleefa ya tashi da wani irin ciwon da hafsat ta kasa gane na menene,kuka yake tayi tamkar me yana zabure zabure,hankalin hafsat ya tashi ta dauki wayarta tayita kiran shaam baya dagawa,takira haleemah akayi rejectin call din sannan kuma aka kashe ma wayar gaba daya,shaam yaga ta kuma kiranshi yace "Haleemah lafiya kuwa? Kodai in daga inji menene dalilin kiran naga bata taba yin hakan ba?" wani narkewa haleemah tayi tace "Boo me dan Allah manta da ita,nasan kuka khaleefa ke mata shiya sanya kaga ina ce maka akaishi acan kar ya hanamu walawa" biyeta yayi sukayita har kofar gidan tazo ta bubbuga suka mata banza,koda ta koma yaron baya motsi lokacin ma karfe biyar na asuba,da kukanta takira shi again be daga ba,ta aika masa message "Yaa shaam nayita kiranka inaga fa Khaleefa ya rasu" yana fitowa daga gun alwala yaji aran message yaje ya duba a rude ya gayawa haleema da salla be dameta ba tana baccinta aibhar ture juna sukeyi sabida tsabar gidi mewa,banka kofar sukayi suka sameta rungume da gawar tana uban kuka,

"yaa shaam kunga illan rashin daga waya ko? Shine inata kiranku yaron nan se zabura yakeyi amma kuka qi dagawa wlhy kungani ya mutu" ta sake fashewa da kuka,ai shaam na dubawa yaga da gaske ya mutu ya soma jibgar hafsat

"yanzu tsabar bakida mutunci shine kika kashemun yaro,dama wannan qiyayyar taki akanshi ta wuce tunani wlhy kema sena kasheki,jibgarta ya hauyi baji ba gani haleema se kuka takeyi ta dauki gawar se jijigawa takeyi,dakyar yadena dukanta yace dan ubanki kije na sakeki saki d'aya ki barmun gidana........yana kaiwa nan yabar dakin yana me karbar gawar yana kuka,wayanta ta janyo da kyar ta kira Abba haris,yana dagwa dak'yar tace "Abba kazo ka daukeni yaa shammaz ya sakeni kuma so yakeyi ya kasheni da duka,banama iya tashi".............

To jama'a kunjifa yanda ta kasance,anya kuwa shammaz yanada hankali? Anya kuwa wannan halin nashi asirine kawai kodai har da qiyayya da wulaknci? Yaya rayuwa zata juya masa?

Mom Nu'aiym

*Don't forget to vote and comment,ur votes and comments are more important to me than anything plsss do vote for me*

    
[1/21, 7:15 AM] Mmn Sadeeq: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)

*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*


Wattpad@ 68billygaladanchi


11

Sosai ran Abba haris yake a b'ace sanda yazo gidan,kai tsaye part d'in hafsat ya wuce ya tarar sabuwar yar aikinta dasuka saba sarai ta tasata agaba tanata kuka ko motsi batayi,da hancinta da bakinta duk jini,sosai ya tsorata bema wani damu shaam sabida bashida abun ce masa ya sakata a mota itada sarai suka nufi asibiti.....waya yayiwa matarshi da dama ya barota hankali a tashe tana salallami akan driver yazo dasu Uduth suna can,Dr. Sayyeed hamid Ali shine dr d'in da ya duba Hafsat sunkai kusan awanni hud'u akanta kafin ta farfad'o,zuwa yayi ya kira Abba haris a office d'inshi ya kalleshi sosai sannan yace

"Sir wannan yarinyar shekarunta nawa ne?" dubanshi abban yayi yace cikin damuwa "shekarunta sha shida inaga nanda watanni biyar zata cike sha bakwai" jinjina kanshi yayi sannan yace "Amma yallab'ai kuna zaune da qanqanuwar yarinyabhar ciwon zuciyata da hawan jini su mata yawa haka,ni fa a gaskiya nasan is very rare kagan yara masu qananun shekaru irin nata suna fama da wannan cutar,sa'annan wannan uban dukan da kuka ce mijinta ya mata kyautuwa ma yayi ku kaishi gun hukuma sabida kuwa ya tab'a wa yarinyar kai, yanzu haka idan ta farfad'o gaba daya bamusan a wanne halin zata tashiba,sabida jini ya taru mata a k'walwarta,rayuwar yarinyar abar tausayi" dafe kai abba haris yayi tare da zare ido waje cikeda kad'uwa yace "wane irin ciwon zuciya da hawan jini kuma likita? Anya hafsat tamu kake magana kuwa?" nisawa Dr. Sayyeed yayi cikeda tausayawa yace 'Alhj wlhy itan kuwa,kana nufi kenan bakusan tana fama da wayannan cututtukan ba? Bincike ya nunar mana cewa har magungunan take sha" A zuciye ya miqe yace "wannan azzalumin mijin nata ya sani sabida kuwa shikeda asibitin zuciya sukutum wacce itace k'wallin k'wal agarinnan,kuma shine babban likitan zuciya" kallonshi sayyeed yayi cikeda mamaki yace "Alhj Karkace dani Dr. Shammaz kake nufi sabida a iya sanina shikad'aine ya mallaki asibitin zuciya me zaman kanta,bazan amince ba idan har kace dani wai shine da kanshi yayiwa matarshi irin wannan dukan" kallonshi Abba yayi cikeda takaici sannan cikin d'acin zuciya ya furta "Amma zaka iya yadda cewar nine mahaifinsa na asali na haihuwa,yayinda mahaifin wannan yarinyar da yayiwa wannan dukan shine mariqinshi shine ya zamto gata agareshi harya kai wannan matsayin dayake kai a yanzu,amma shine tsabar yana butulu ya aikata wa yarshi wannan mummunan ta'adin" sosai wannan maganar ta girgiza Dr.sayyeed ya zare madubin idonshi ya dawo kujerar dake kusa data Abba ya zauna sannan yayi abba nuni da daya kujerar akan shima ya zauna ya ce

"Amma nayi mamakin jin wannan maganar,sabida da badan kai bane mahaifinshi wlhy da bazan yarda ace wai Dr. Shaam ne yayi wannan aikin ba,sabida sanin dana masa mutumin Kirkine kuma kamili,Allah yamana tsari da sharri shaidan,yanzu dai bazamu sanar daku komaiba se yanda bincike ya nuna mana,sabida haka ku bamu nanda yamma seka dawo nan muji koma meye" Godiya Abba haris ya masa sannan ya fice kai tsaye gidan Daddy ya wuce ya tarar ana jajen mutuwar khaleefa,a fusace ya kalli jama'ar dake parlor kasancewar duk yan gidane se daddy da shaam,idonshi yayi jajir tamkar gaushin wuta

"waye acikinku ya nemi sanin inda Hafsat take da baku ganta ba" mero ce tayi saurin cewa "Abba mun tambayeta amma yaa shaam ya sanar mana wai tana makaranta" wani kukan kura Abba haris yayi ya shaqi wuyan shaam ya miqar dashi tsaye ya surfafa masa lapiyayyen mari har guda uku a jere a jere,cikin mamaki d'aukacin mutanen dake parlor din suka miqe daddyy ne ya riqeshi "Harisu lapiyan ka kuwa meya faru?,yaro yana cikin zillar rashin yaronshi zakazo kana surfafa masa marika haka,meya maka" cikin huci yace "Sabida yaronshi ya mutu seya nemi kashe yar mutane,wai har shammaz dan bashida imani ba Allah a ranshi ze riqa baiwa hafsat renon yaro cikin dare yashige da tsohuwar matar daya ajiye suna holewa,kuma sabida Allah ya karbi ranshi rana daya ya ce wai hafsat ce ta kasheshi kuma ya mata dan banzan duka harta suma,bayan sakinta dayayi duk wannan be isaba se sanin ya dasa mata ciwon zuciya ba wanda ya sani harma da hawan jini,yanda ga wayannan kuma gashi likita ya tabbatar mun cewar wai hafsat kanta ya tabu sabida dukan daya mata aka,wlhy Yaya Abu bazan tab'a yafewa Shammaz ba,na yafewa duniya shi kuma bazance masa komai ba yaje duniya ce,daga rana me kama da ta yau kar naji kona qara ganin yace nine nan na haifeshi ko mutuwa nayi wlhy banda shammaz a gadona kuma ko'a lahira se an mana hisabi dashi,yaci mutuncina yaci mutuncin dan uwana,yaci mutuncin matarshi yaci mutuncin aure,kuma be ragawa Allah ba,na kuma tabbatar Alkah bazenraga masa ba" Da sauri Daddy ya rufewa Haris baki tare da zaunar dashi dukkuwa danyake yaji maganganun tamkar saukar aradu,wai kan kulelen sa ya tab'u kuma a dalilin dukan da shaam ya mata,sa'annan kuma wai tanada ciwon zuciya adalilin mene wannan? Dakyar ya saisaita kansa ya kalli shaam "shammaz kaji abubuwan da harisu ya fada hakane??" sadda kanshi yayi qasa sannan yace

"Daddy niba abunda nake mata,kuma wlhy bansan da zancen ciwon zuciyaba,da ina mata wani abin aidanta fada tuni,zancen khaleefa kuma itace da kanta taroqi Haleemah akan yana kwana gunta kuma jiyan ma wlhy banso ya kwana candin ba,dukan dana mata kuma ba'a san raina bane harma sakin dana mata duk acikin b'acin raine da gigicewar rasuwa khaleefan" Shiru daddy ya kasa magana kowama yayi shiru se momy dake kuka lokaci lokaci tana jan hanci kasancewar kukan nata bame sauti bane,yafi mintuna biyar kafin yace

" Harisu dan Allah markayiwa d'anka baki,ka janye wayannan kalaman daka masa kuma ka nutsu wannan maganarbta gida ce ba abun tashin hankali bane" miqewa Abba yayi

"wato yaya ba kadan ba ka ke sakarwa shammaz dama yana durun uwarsa san ransa,ni za'a gayawa wai harkar gida wlhy tallahi sena maka wannan yaron kotu senaji dalilin wannan ha'incin kuma koban masa bakiba haqqin yata seya kamashi rasa kunya kawai b'eran tanka,dana sani shine babban amininka koba yanzu sekun kulla babbar abota dashi wlhy" yana kaiwa nan yayi waje,yayinda momy tayi kiran mero suka nufi asibitin uduth daddy ma da shaam din suka bi bayansu kasancewar haleemah tana gidansu.....

Acikin d'akin kowa yayi zugum zugum an qurawa hafsat dake wance ido, A hankali ta bud'e manya manyan dara daran idonta,sunanan dai a lumshe tamkar mejin bacci a kowane lokaci,d'aya bayan d'aya take bin kowa da kallo,har shaam wanda taqurawa ido bata ko k'iftawa,a hankali kuma ta rufe idon tamkar me bacci can kuma bayan yan mintuna tamkar wacce aka tsira kuma seta fara fizge fizge kan kace me wannan ta soma zabga sambatu

"Dan Allah karka dakeni wlhy ba abunda nawa khaleefa,yaa shaam ka dena dukana zaka kasheni,wayyo Allah daddy kazo ze kasheni,Abba yaa shaam ze kasheni" dak'yar suka rirriqeta shaam yaje yayi kiran nurse dake kusa akan ya akira doctor sannan ya koma kanta, koda dortor yazo seta fara kuka sekuma ta saka dariya kowa a d'akin kuka yakeyi yayinda lokaci d'aya kunya,danasani,nadama da bak'in ciki suka qara taruwa suka lullub'e shaam yama rasa me yake ciki a yanzu,Dr.sayyeed ne yazo dubatan ya kalli shaam ya miqa masa hannu suka gaisa sannan yane kai tsaye wurin hafsat,cewa yayi kowa ya saketa sannan ya sauke mata lallausan murmushi bayan ya riqe hannunta na dama,qura masa ido tayi dukda acikin rashin lapiya take amma setake masa kallon rashin sani yace yana ci gaba da fad'ad'a murmushinsa
"Hafsat sannu kinji meye ne yake damunki? Cikeda wowta tamkar wata yar shekaru biyar tace "Bayan yaa shaam kullum yake dukana na ganeshi so yakeyi ya kasheni,ni ku fita dashi a d'akinnan inba haka duka na zeyi kuma banasan ganinshi" K'ara riqe hannunta yayi yace "Ai indai ni Uncle sayyeed ina nan wancan shaam din baze dakeki ba idan ma yazo dukanki nine zan mar d'an banzan duka yanzu sanar dani ina ne yake miki ciwo?" amaimakon ta bashi amsa se kawai ta matso ta qamqameshi tana kuka da sambatu alamun ba hankali atattare da ita "Uncle sayyeed karka bari yazo kusa dani dan Allah,daddy idan bazakuce ya wuce ba ni bana sanku"k'wallah Abba ya share cikin hikima yayi waje a haka a haka kowa ya watse ya kama gabanshi cikin k'unan rai,Dr.sayyeed be ajiyetaba seda tayi bacci shida kanshi yarinyar ta bashi tausayi over,be tab'a ganin case maka mancin wannan ba awurin yara dai......

Shaam na fitowa yakira Haleemah suka gaisa se kukan munafurci takeyi dak'yar ya rarrasheta ya sanar mata halin da ake ciki,cikeda kirsa tace "Amma ai yaa shaam na sanar maka karka daketa ba laifin ta bane ba inaga kaddara ne kawai" sallama dai ya mata ta ajiye wayar ashe sam shi be ajiyeba yana jiran yaji tace I love you boo me,yanda suka saba se kawai yaji an tafa hannu ana sowa

"Wlhy umma gabad'aya jin wannan labarin senaji gwarama da khaleefa din ya mace,dama kinsan ance seka haifi wanda zeyi silar arziqinka to zuwan khaleefa kenan a duniya,nifa da farko dakikace boka yace rayuwar khaleefa fansa har naji bakya sona,ashe kinfini kaifin hankali tunda ko yanzu nakeso zan iya qara haihuwa,amma fa wannan aikin da tsauri yake umma ji nayi kince bokan yace sena kwana biyar a gidanshi yana saduwa dani kuma kince wai idan har mijina yasan zanje konan dacan aikin bazeyiba sannan kuma idan har yayi koda tunanin muna masa asiri bare ma ya gane to aikin ya karye,ni kuwa ai bazanso hakan ba yanzu ya kenan??"

"Kinga hali dubu yar mama,barni da shegen yaronnan maganinsa zamuyi ai,yanzu ki hau bori zaki tsaya anan,kinga gobe seki je,duk ya kira akan zezo ki hanashi harse mungama aikinmu,kuma kinji boka yace daga zaran kin sadu dashi na karshe karki bari awuce awa ashirin da hudu ba tare da kin sadu da mijinki ba,kina yin hakan gaba daya ze kwashe mana dukiyar sa ya bamu,daga nan idan munso mu kasheshi ko kuma mubar masa gidansa inyaso mu koma lalubo wani me kudin,karfa ki manta khaleefa kika bayar akan kinasan yin arziki gudan jininki sabida ki nutsu kar a samu kuskure kuma ki tabbatar yaji wannan ganyen a abinci sabida shine ze gusar mas d hankali yakwashe mana dukiya a arha" dariya tayi suka tafa wanda shaam yaji komai zufa se keto masa takeyi ya kasa sauke wayar a kunnenshi yana saurarensu sunata shirya makirci,shi gaba daya ma ya rikice musamman jinda yayi suna zancen sun dasa masa qiyayyar hafsat,lokaci daya ma yaji ya tsani kansa kuma soyayyar dayake mata ta yaya da kanwa kai tsaye ta dawo da gudun fanfalaqi,amma fa har yau bawai yaji yana santa na soyayyaba.........

Dr. Sayyeed ne ya kalli shaam bayan sun zauna,yace raunin na kanta ya taba mata kwalwa harma yana neman zautar da ita,sannan kuma ga zuciyarta ta tsananta abinda na fuskanta duk sanda kazo wurinta se hawan jininta ya tashi ga bugun zuciyarta dake qaruwa,sabida haka kadan daga mata qafa,zancen gaskiya kuma aikin manta bame wahala bane sedai zeci kudi,abu mafi muhimmanci danakeso ka sani matsayinka na likita shine,lallai wannan jijiyar tata me aika jini me makon saqonnin fahimta akanta aikinta ze janyo wani matsalar,kodai lalacewar ido,kokuma ta kunne sabida haka sekun saka haquri a lamuranku" kuka shaam ya saka tamkar wani qaramun yaro sabida shi gabadaya tunaninsa ya tsaya cak,tayaya ze kalli su abbba da daddy da wannan zancen? Ina courage din? Menene ma mafita agareshi?" A yanda ran Abba haris ya baci idan wani abun ya samu hafsa agarin aikinnan ai tsaf ze tsine masa wlhy kowa ya huta,dak'yar Dr.sayyed ya rarrasheshi yabar asibitin....

*Ur vote is important also ur comment fan's,inasanjin ra'ayoyinku,i hope ur enjoying this story*

Mom Nu'aiym[1/21, 9:43 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)

Wattpadd@ 68billygaladanchi

*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*

12
Dr.sayyed tunda yaje gida yake tunanin yanda zasu b'ullowa lamarin hafsat,haka kawai ya tsinci kansa da tsananin tausayin yarinyar,indai har acikin halin hauka bata manta muguntar da yake mata tokuwa lallai abun ba qaramun abu bane yana cutar da ita over,sam bayaso wani abu ya tab'u a jikinta kuma yasani sarai chancess na rashin samun hakan ba qaramun abu bane, yanaso ayi aikin as soon as possible amma fa sam bayaso ayi garaje a samu matsala.......

Shaam kuwa koda yaje gida masa bacci yayi,bangaren zuciyar sa na masa zafi akan abinda yaji da kunnensa haleemah na fad'a itada uwarta,yayinda dayan bangaren na zuciyarsa ke masa rad'ad'i akan abunda abbansa yace dashi akan hafsat,wani dogon tsaki yaja yace a asarari "Gaba d'aya wannan hafsat d'in ta jamun masifa wlhy,dabadan ta maqale akan seta aureniba wlhy daban shiga wannan mugun yanayinba,ita kuma haleema yaya zatamun haka?? Ina sanki sosai haleema ko baki sani bane" a haka ya dinga sambatu shi kadai harna shirme.......

Dr. Sayyeed da kanshi yayiwa su Abba bayanin rashin lapiyan hafsat da kuma da kuma abinda yake hange idan har aka mata wannan aiki,fatanshi d'aya ayi aikin lapiya kuma adu'arsu itace abun nema" Babu yanda suka iya dole su yarda da akan ayi aikin dukkuwa dayake Abba haris yaso a fita da ita waje daddy ne yace duk inda akayi aikin nasara a wurin Allah take,da wannan aka tsaida ranar aikin nan da sati d'aya......

Hafsat dai tana nan jiya iyau,ba abinda ya ragu har yau ba hankali akanta,yaa shaam tunda suka yaji wannan zancen nasu haleema seya kirata yace ta zauna gidansu se bayan sati biyu zuwa lokacin hankalinta ya kwanta dama kuma hakan takeso ya sanya ta kwantar da hankalinta tayi gidan bokan ta....

Sati ya zago Aka shirya shiga da hafsat tiyata yaa shaam har kuka yayi abubuwa sun taru sun masa yawa yanzu ya tabbatar wa kansa cewar abinda yaji gaskiyane,coz kwana kusan uku baya samun number wayan haleema kuma koyaje gidansu se a ce masa wai batanan sunfita da momy........Aiki dai anyishi cikeda nutsuwa da kuma na sara an samu damar kwashe duk wani jini daya taruwa hafsat a kai, yanzu jira kawai akeyi ta farfad'o, a ga yanda zata tashi......

Umma da momy sunyi jigum jigum suna adu'ar farfado war hafsat lapiya,se suka jiyo maganarta sama sama "Saro kunna mun fitilar d'akin nan kuma ki bani ruwa" kallon juna su umma sukayi sabida su sam basusan da wani zancen wai za'a iya samun matsala ba,da sauri suka miqe atare sukayi kanta,umma ta riqe hannunta tace

"Sannu hafsat ai ranane aikin da'aka mikine akai,inaga lallai alluran nan ne be sakeki ba shiyasanya kike ganin duhu,sannu kinji" Shiru tayi tafara tunano abubuwan da suka faru da ita ita dai bata jin wani jiri gashi ta tabbatar wa kanta cewar idonta abude yake yama za'ayi ace wai allurace,amma seta kama bakinta tayi shiru kawai tana me mamakin har meyake damunta daza'ace wai ammata aiki akai,wasa wasa hafsat haka ta wuni ta kwana bata gani zuwa wannan lokacin har su momy sunsan halinda ake ciki kowa ya sakata agaba har Shaam tana bacci tana farkawa tace

"momy zansha ruwa?" ruwan momy ta bata tasha sannan ta kwantar da ita gyaran kwanciya tayi tace "Momy dan Allah wai se yaushe gari ze waye ne,ni nagaji da ganin duhu idan ma garin be waye ba ku kunna mun fitila" D'aukacin mutanen d'akin suka saka kuka sabida tsabar tausayi daddy ne ya qarasa gunta yace

"Hafsat nasani maganar dazan fad'a miki zaki jita wani iri kuma tabbas zata tayar miki da hankali,amma inaso kiyi hakuri ki yarda da khaddarar Allah ya d'aura miki,khaddarace ta sameki sakamakon dukan da yayanki yayi miki wannan ne ya sanya kanki ya samu matsala na tab'in hankali, to agarin yi miki aikine kuma wata khaddarar ta sake samuwa gashi dai munyi nasara hankalinki ya dawo jikinki amma an tab'a miki wata jijiya aka wacce tayi sana diyar lalacewar idonki yasanya kika dawo makauniya bakya gani" shiru tayi kamar yanda kowa yayi shiru tamkar bataji meyace ba secan hawaye ya fara gangara daga cikin idonta da suke abude bazaka taba cewa basuda lapiyaba ,batayi magana ba wannan ya sanya kowa ya sanya bakinshi ana bata baki seda taji kowa yayi shiru sannan ta sanya daya hannunta dabashida ruwa ta dafe qirjinta tace cikin d'aga murya

"meya sanya a rayuwa nayi rashin sa'an zuwana aduniya? Meya sanya wannan baqar zuciyar tawa takesan mutumin da yafi qaunar mutuwarsa akan ya d'aura idonshi koda akan me ita,meya sanya a rayuwa sam na

Please Login or Register in order to submit comment