Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba soyayya bace,k'aunace me zafin gaske,ada nayi tunanin so shine komai se yanzu danake rayuwa dakai na tabbatar wa kaina cewan so shirmene zallah,ada nayi tsammanin cewa akan soyayyar shammaz na shige halin da nashiga na ciwon zuciya se daga baya na fahimci cewar zallar mugunta,cin amana,cin zarafi dakuma wulakantanin dayakene ya sakamun ciwon zuciya,sabida soyayya ruwan shayi ce yana zubewa a qasa kuma sedai kanemi madarar ka rasa shimfidar ruwan banza kawai zaka gani a kasa,kauna kuwa kakkauran kindirmo ce sabida zubewar sa a qasa baze tab'a zama sanadiyar b'acewa kalarsa ba,itace nake maka zallarta,dan Allah uncle say ka k'aunaceni,dukkaninmu muna tsananin buqatar kulawar junanmu" sosai yake kallonta harya kasance ko qiftawa bayayi ya rasa dalilin sa najin komai tamkar a mafarki jikinsa gaba d'aya yayi sanyi,har yanzu hafsat yarinya ce bazata tab'a fahimtar saba idan yace mata kuma bashida hanyar daze bar zuciyarsa ta k'aunace ta sabida wasu manya manyan dalilai,batare dayace mata qala ba ya miqe yabar parlor d'in fuska kici kicin zuciyarnan sam babu dadi a jagule......

*kome hakan yake nufi,da Alama hafsat batada farin jinin masoya a duniya,ba wanda yatab'a cewa yana santa,sannan kuma ita sedai taso wannan taso wancan amma babu wata nasara,Allah ya temaketa dai,muje zuwa kuci gaba da bin alqalamin mom Nu'aiym.....

          
[2/1, 8:32 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)

Wattpadd@ 68billygaladanchi

*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*


18

Dafe kanshi yayi bayan ya kwanta yace cikin kukan dabesan sanda ya kwace masa ba "Meya sanya arayuwa Hafsat take shan wahala har haka,ina tsananin sanki hafsat amma bazanyi ganganci nuna miki hakan ba,kamar yanda bazan tab'a bari soyayya ta tayi tasiri azuciyarki ba,gwaramun haqura dake a matsayin mata akan narasa rayuwarki har abada.." kukan yashigayi kaikace qaramun yarone,ganin wannan bazata fiddashi ba ya sanya ya shirya zuwa gun amininsa kamal khan domin sanar masa matsalarsa......

"Kamal akwai damuwa fa babba wlhy,duk sanda na kwanta senati mugwayen mafarkai akan lallai idan har na kuskura na auri yarinyar nan se an kasheta har lahira,ni bazasu iyamun komai ba sabida riqon addini haka sukace amma wai itad'in alqawarine duk mesan tan daya aureta lallai se sun ga bayanshi babu ita ba tarawa da wani d'a namiji harta bar duniya ni sosai take ban tausayi wlhy,wama yasan ko wancan yayan nata hakance ta faru dashi,ni ina matukar san hafsat son daban taba yiwa wata 'ya mace irin saba a duniya,rashin adalci d'aya zuciyarta tamun na sanya ta qaunaceni,Bansan yanda zatayi da ciwon zuciya ba idan har naguje mata,kuma ni bazan iya cewa da ita ga abunda yake faruwa ba harga Allah" nisawa khan yayi cikin yaren india yace

" Sam karka gjjeta,karkuma ka nuna mata baka santa,wannan ba abinda zeyi illah ya wargaza mata zuciya gaba daya,sanan ni ina abu d'aya ne cikin biyu,kodai iskokaine da ita kokuma asiri aka mata,danni bantab'a jin hakan ba se'a irin harkar iskan nan,nifa a nawa tunanin kabata lokaci,ka kula da ita ka nuna mata soyayyar dakake mata inyaso a hankali kana koyar da ita girman adu'a da tsare azkhar safe rana da dare dakuma yawaita yin azumun litinin da alhamis,kana ana yawaita yin salatin annabi ba adadi,idan ma iskane zasu bayyana kansu idan kuma asirine lallai Allah ze taimaka kaga abun ya karye" murmushi yayi ya daura hannunshi akan kafadar khan

"Inajin dadin shawar warinka abokina,Allah bar zumunci hakan zamuyi ai dole ma".

Tunda hafsat taga yananyin Uncle say se jikinta ya mata sanyi,dak'yar ta iya jan jikinta zuwa bedroom nasu,har akayi magrib da ish bata fito ba,har akazo cin dinner koda aka aika kiranta se cewa khairii tayi ta qoshi tasha fresh milk,ganin haka Uncle say ya gano damuwa tashi ga wannan yasanya ya janyo wayarsa ya rubuta mata txt kamar haka

"My love i swer idan bakizo munci abinci ba bazan ciba nima,kuma na tabbatar bazaki so Uncle say naki ya zauna da yunwa,plss kizo I LOVE YOU". Kasa dauke idanta tayi daga message din tana mamakin kalamansa har ya kuma turo wani jinta shiru

"Baby na dagaske fushi kike sabida namiki shiru dazu,tsabar jin dadin kalamanki ne yake shirin sakani kuka a dazun,kuma inajin kunyar nayi kuka a gabanki amma trust me i love you more than words can tell,plss com and hav dinner together with ur fam" Tana murmushin jin dadi tazo dining d'in ta zauna amma me tarasa dalilin daya sanya matukar kunya ya hanata had'ata ido dashi har abincinma ta gagara ci se wasa takeyi da cokalin hannunta,wayarsa ya dauka ya rubuta mata

"Meye hakan kunyan wa kike kuma? Yauba shagwab'a kenan" karayin k'asa tayi da kanta bayan ta karanta message d'in amma batayi replyin nashi ba,murmushi yankumayi yace cikin message

"u go and get set,we r going for a date" murmushin dake qarawa fuskarta kyau ta d'ago tana masa cikeda qauna sannan a hankali bayan sun had'a ido ta sadda nata idon k'asa lokaci daya taji tana masifar jin nauyinsa kuma ya mata kwarjini,miqewa yayi kakarsa ta kallesa tace

"Bakaci komaiba?" murmushi ya sakar mata

"Nida hafsat zamuje yawo ne,bamasan mu qoshi danyawa a gida,murmushin tayi itama bata tankaba,tun dazu ta kula da yananyinsu ai yau taga sauyi sosai awurin dukkansu musamman Sayyeed dabaya iya d'auke idanshi akanta duk wani zumud'i yake ji......

A hanya yau hafsat gaba d'aya ta kasa sakin jikinta dashi,hannunta ya janyo yace "'Yan matan uncle say yadai niyau tsiwar nakesanji sa shagwab'ar" batayi magana kurun dai ta juyar da kanta d'ayan gefen tana murmushi,hannunta dake had'e da nasa ya matse sosai da sauri tashiga janye hannun ta saka wata qaramar qara,tace cikin shagwab'a "Nashiga uku Uncle say dazafi wlhy" sake hannun yayi yace yana dariya

"gobe ma kya kuma mun banza idan ina miki magana" batace komai ba,shima shirun ya d'anyi,se can taje bayan ya wuce wani samosa joint

"Uncle say onions samosa zanci" kallonta yayi yace "sekin cemun baby tukunna" zaro ido tayi tace "Haba mana Uncle sayyeed" murmushi ya sakar mata yace yana kallon dayan gefen alokacin dayake shan kwanar barin layin "Kinwa kanki sekince Baby say zan siya miki komai ma" Turo baki sannan ta sadda kanta kasa a hankali tace "Baby" dariyar mugunta ya saki sannan yakuma cewa "Cewa zakiyi,Baby say zanci onions samosa" Kara turo baki tayi batai magana na yace "Bazaki fada ba na qara gudu kinwa kanki kenan??" cikin muryan kuka tace

"Baby say zanci onion samosa" parking yayi ya mayarda hankalinshi akanta,sannan yace "kinsan Allah hafsat ba wasa a zancena akan wannan yawan koke koken wlhy semunyi fad'a ke ko wasa aka miki se kinyi kuka,bazan ma qara miki wasa ba" D'agowa tayi tace tana share kwallan

" Im so sorry Uncle say,bazan kara ba" cikin kuka tayi maganan ko yanzu,shi wlhy dariya ma ta basa,itafa komai qarantar abu kukane,kannewa yayi yace "Oya call me Baby say again" tana kukan tace "Baby say" yace "Noo cewa zakiyi I love u baby say" kallonshi takumayi sannan tace

"I love you Baby say" ta fashe da kuka" jiyayy kamar ya rungumota amma ba hali,ya tabbatar cewar lallai jitai kamar yace ta maresa dayace setace masa baby,yasani tanajin nauyinsa amma wannan ita kadaice damar dazeyi amfani da ita ta saki jikinta dashi mastayin saurayi seya ganar da ita amfanin suturta jiki dakuma yawaita ibadar mahaliccii.... Da wannan yace "kiyi hakuri dear,bazan kuma sakaki kuka ba kinji?" daga masa kai tayi tace "Tokimun matashin murmushi mana,dariya tayi gaba daya hawaye shabe shabe a fuskarta tace " Uncle say a murmushin ma akwai matashine?" dariya ya saki shima "Ea mana bagashi kinyi ba?" suka saka dukkansu......

Mom Nu'aiym
[2/4, 9:26 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)

Wattpadd@ 68billygaladanchi

*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*

                                  19

Shammaz zaune a office d'insa duniyar habaki d'ayanta baqi take masa yarasa yazeyi akan zancen hafsat,sam mahaifinsa yaqi ya basa fuska,gaisuwar sa ma dak'yar yake amsawa,gashi gaba d'aya Haleemah ta gama rainashi zaman auren kawai sukeyi amma sam bajin dad'i har qasar take bari bada izininsa ba,yama rasa tayaya zeyi gashi dai hafsat yanzu kusan shekaru hudu da barinta qasar acewar Mommy ma takusa dawowa domin tace qasarta zata bautawa,amma duk inda yaje da zancenta ba sauqi har wurin hajiyar su wato kakarsa......

    Sosai hafsat ta tara abubuwan burgewa ajikinta,yanzu batada wata damuwa ita da uncle say sambarka,duk da yabar qasar ya koma Niger amma koda wane lokaci suna maqale da juna awaya,sunyi wani sabo mara misaltuwa,kwance take acikin dakinsu tana karatun wani English novel me suna she's with me,khairii ce tashigo ta kalleta taja tsaki

"Allah hafsa kin shiga ukunki kekam,wannan wane irin karatun jarabane kikeyi haka? Kinfasa tafiyarmu nanda kwana ukune, amma meye naki na tsayawa karatun wani banzan novel,kofa kayanki baki had'a ba wannan zumud'in na uncle say duk gulmane abaki kawai ya tsaya bekai zuciba" bata kula taba,kuma sarai tasani bawai kulatan zatayiba wannan ne ya sanya taja wani tsakin ta shiga had'a musu kayan har hafsat,se zumud'in ta takeyi ita kadai tana mitar san banza irin na hafsat....

*NIGERIA*

      Gaba d'aya hafsat gani takeyi tamkar mutanen dake yanga akan jirgin basu san ciwon kansu ba,sakkowa ajirki sekace wanda ya tasa tray na samosa agaba,se yanga sukeyi tamkar basa taka qasa,tun a airport na sultan muhammadu maccido dake garin sokoto ta fahimci sauye sauye da dama da aka samu a garin,idon tane ya sauka akan masoyinta uncle say,shekara d'aya kenan rabon data ganshi,takowa tayi a hankali taje har gabansa ta tsaya ta sakar masa lallau san murmushi,kankace meye wannan kuma idonta ya cicciko ta soma kwallan murnar ganinsa,a hankali ta furta "i so much miss u Baby say" murmushin shima ya sakar mata sannan ya ja hannunta ya riqa cikeda kulawa yace

"Rose kukan kuma na menene,daga had'uwarmu zaki fara ko Baby?" murmushinta ta fad'ad'a batare data dena zubar wahayen ba tace "Uncle say bakada labarin akwai hawayen dadi? sune nake zubarwa tsabar murnar ganinka" Janta yayi suka juya se mota,dama shi kadai yazo tarar su suka shiga suka wuce gidan abba haris kai tsaye,se labarin soyayya sukeyi cikeda qauna da tsananin murnar ganin junansu......

   Satinsu daya agarin aka tsayarda ranar auren say da hafsat nanda watanni hudu masu zuwa,dama can tun tana india akayi tambayar auren kowa ma yasan da zancen auren.

*Bayan kwana biyar*

    Tun da hafsat ta dawo basu hadu da yaa shaam ba har yau,gwara ma matarsa sun had'u a gidan daddy,shi kuwa yana sani yake gujewa ganinta sabida gudun karya tayarwa kanshi cutar so da ta jima tana addabar zuciyarsa,yau dai seda ya kira qaninsa da safe ya sanar masa cewa suna gida sannan ya shirya zuwa gidan na daddy,bashida lamarin hafsat ta dauki al'adar waje bata fiya fitaba seda yamma,wannannya sanya ta zuro doguwar rigar jallabiya ja har qasa tasha shape da bakin mayafi da uban qaton madubin ido,lips dinnan sunsha red lipstick,a hankali take taunar cingam dake bakinta tana yamutsa fuska,yau sam setakeji tamkar batada lapiya driver din na parka wa tafito a yangace zuwa cikin gidan daddy cikeda yanga, A hot na gidan ta hango yaa shaam lokaci d'aya qirjin ta ya mugun dokawa,adu'a taci gaba da karantowa ta dauke kanta tamkar bata ganshi ba,murya ya d'aga yace "Hafsa zo zan" qirjin ne yaci gaba da mugun dokawa amma bata ko waigo ba, yi tayi tamkar bata jishiba, shikuwa ganin haka kuma yasan sarai tana jinsa ya sanya yayi saurin tasowa yafara takowa zuwa inda take,ita d'inma sauri ta qara amma ina kan ta isa kofar dazata sadata da cikin gidan ya rigata,tsayawa tayi cak ta runtse idonta ta sauke wata nannauyan ajiyan zuciya,a hankali cikin sanyin murya yace

"Hafsat ya kwana biyu" bud'e idonta tayi a hankali batare da tayi magana ba,tana kallonshi ta cikin gilashin idonta,ya kuma cewa

"Bazak gayarda yayan naki ba?" hannu ta saka ta zare madubin idonta sannan ta lumshe manya manyan ida nuwanta tace "Yaa shaam ina wuni,ya kwana biyu?" murmushi yayi shima hade da daura hannunsa saman qirjinsa yace "Lapiya qalau hafsat yaushe agarin?" murmushin itama tayi tace

"Au baka masan zanzo ba aikuwan na cika tara,seka biya" wani dad'i ne ya xiyar cesa ganin ta sakko,besan kuwa nan umarnin yaa say kawai take bi ba abun beyi wani damuntaba,dak'yar ma take masa murmushin,shikuwa se dadi yake ji ya kalleta sosai

"poojan dady an girma fa sosai yanzu" murmushin takumayi tace

"yaa shaam d'in daddy kuwa ya zama tsoho tunda qanwarsa ta girma" Murmushi yayi ya shafi gefen fuskarsa "Ki shiga ciki yan matan Yaa shaam" wata dariya tayi me cikeda ka raina kanka ta wuce ciki kawai....

Tunda yaa shaam yaga hafsat na sakar masa fuska se kawai ya qudurta aranshi shine ze angwance da ita,da wannan har tunaninsa ya kaishi ga zuwa ya ziyarci Innah wato kakarsu ta wurin iyayensu maza....

Zama yayi ya saka mata uban kuka,akan wai ai asiri aka masa ada,yanzu kowa yasan yana san matarsa Amma abba haris dasu daddy sun hanashi sun baiwa wani har an saka rana nanda watanni hud'u,Innah kuwa tacika fam ta fusata,i da take shiga batanan take fita ba akan za'a hanawa magaji mata,aikam tana da rai basu isaba,da wannan tayi kiran kowa da kowa a gidan ta!!!!

Kallonsu tayi bayan kowa ga natsa yana saurarenta tace dasu "Dama akan zancen hafsat ne da Magaji,tayaya dukkaninku kunsan airine yayi tasiri akan shi a wancan lokacin yanzu zece yanaso amayar masa da matarsa hankalinsa ya dawo jikinsa amma tsabar bakusan muhimmancin zumunci ba zaku rufe ido ku baiwa wani inada rai banma sani ba,to wlhy kunyi kadan kunji na gaya muku,na baiwa shaam auren hafsat tunda dama saku d'ayane a tsakaninsu,kuma na dawo ma da bikin wata me fita" kallonta Abba haris yayi cikin rudu yace

"Innah dan Allah karki taso da wannan maganar yarinyar nan yanzu ta samu wanda takeso,kuma bazamu zamo qananun mutane ba munyi magana kuma mu dawo muce dasu wai amfasa,dan Allah ki rufa mana asiri maganar nan tunkan ta tashi daga nan mu barta" kanwar haris me binsa ma tasa baki kowa dai yayi magana tana jinsu seda duk suka gama sannan ta kallesu tace

"Dukkaninku nan baku isa kun sauyan ra'ayi ba,sannan idan qaranta kuke gudu ni nan bana gudunta,ku sani wlhy ko yau na mutu duk wanda ya sauya wannan maganar tsakanina dashi Allah ya isa ban yafe ba" zaro ido sukayi dukkansu suka shiga lallami da ban baki,amma qememe tace dasu acikinsu ma wanda ya kuma tada zancen bata yafe ba,indai ba akan zancen bikin bane,kar wanda yazo mata dashi kuma kartaji sun sanar wa Alhj wato mahaifinsu" ai gaba d'aya mamaki ne ya damqe ilahirin su,suka silale d'aya bayan d'aya.....

Mom Nu'aiym ce
[2/6, 9:16 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)

Wattpadd@ 68billygaladanchi

*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*

20
Zirga zirga abba haris keyi tamkar me ynqurin naquda,sam ya kasa gayawa hafsat meke tafiya gata durqushe a gabansa amma se gumi yake had'awa,kar yarunyar nan tayi tunanin cewar san kai yake mata akan d'ansa,ganin yayi shiru beyi magana ba ya sanya takuma cewa

"Abbana gani" jikinsa ne yayi mugun mutuwa jin takirasa da abbanta, yasani hafsat duk gatan da mahaifinta keyi mata gani takeyi tamkar shine ya haifeta kuma yafi santa,hannu ya sanya ya rage zufar data tsatsafo masa a goshi sannan yace,
"jeki ki dakko mayafinki kizo mu je wani wuri" dubanshi tayi haka kurun taji qirjinta na dokawa kuma kanta ya soma sara mata,jiki a mace ta miqe zuwa part nasu ta sako hijab a saman doguwan rigar atamfar dake jikinta tafito......

*A parlor daddy*

Tunda hafsat ta ga kowa zaune har yaa shaam jikinta ya mata sanyi,gaba ki d'aya setaji wani iri,zama tayi yaukam ma akasan carpet ta gayar da kowa,kallonta daddy yayi yace

"Hafsat ina fatan kin san cewar mu iyayenki ne kuma mun isa mu sakaki komai a yanda muke so muke kuma ganin ya dace?" kallon su tayi d'aya bayan d'aya sannan ta sauke idanta akan yaa shaam dayake ta faman murmurshi a hankali hawayenda suka taru mata tun farko suka silalo,ta gyad'a mar kai alamar gamsuwa da jawabinsa sannan yaci gaba

"kuma kinsan cewar dukda muke iyaye a wurinku muma muna da iyayen dasuke sakamu abu adole koda bamaso se munyi shi?" nanma d'aga masa kai kurun tayi wannan lokacin kam tana kuka sosai,ganin yaa shaam na murmushi ta gano da babbar matsala,daddy yaci gaba

"Innah ce da kanta tayi mana umarni akan lallai mu d'aura aurenki da shammaz nanda wata d'aya me zuwa,kuma idan d'ayanmu ya sauya wannan maganar ko bayan ranta bata yafe masa ba" qirjinta ya dad'a dokawa fiye da da,ta d'ago cikeda razani ta kalleshi,idonta ya kada yayi jajir yanzu kam tama kasa kukan se quna da zuciyarta keyi,miqewa tayi ranta a b'ace ta qarewa kowa kallo sannan ta kalli Abba haris tace cikin wata murya me d'aci wacce basu santa da ita ba

"Abba na da gaske wai Innanku ne ta fad'a haka ba shiri bane wannan,na tabbatar kai kadaine zaka sanarmun zallar gaskiya" wasu yawu ya had'aya dak'yar masu d'acin gaske sannan yace dak'yar

"Inna ce ta bada umarnin nan jiya hafsat" hijabinta ta gyarawa zama sannan tace " To yayi" Ta juya da gudu zuwa waje batare da tasan me yake damunta ba ko ina zataje ba,daddy da Abba haris ne suka bi bayanta,da gudunta suma haka a haka tafito daga gate d'in gidan tana kawowa kuwa wata motar na dannowa da gudun fanfalaqi atake tayi mata ebar karan mahaukaciya.......dafe kai sukayi dukkansu bame abunyi haka aka cillata acikin drainage dake gefen titin,abbah haris na kuka kamar wani yaro yaje ya fada ya cirota,sam babu alamun numfashi a tattare ita,ta sume mamallakin motar ma daya kasance matashin saurayi dan gayu fitowa yayi ya taya abba haris daukarta suka saka ta mota suka fada atare yaja da karfin gaske sukayi gaba,anan suka bar abba a tsaya ya kasa koda motsi sabida rudu,dakyar ya iya komawa ciki ya kallesu yace

"Bana tunanin hafsat ,
Zata tashi,koda kuwa ta tashin bana tsammanin mata ingantacciyar rayuwa a yanda mota tayi mata wannan eban karan mahaukaciya ta cillata a gota" momy ce ta riga kowa miqewa jin kalamansa ta dage qirji "A ina wannan ya faru Alhj?" kallonta yayi da rinannun idanunsa yace

"A kofar gida yanzu data fita da gudu,ina jiye mata idan ba ajali bane ya fitar da ita" zarewa momy tayi tayi waje da gudu shi kuma ya bita, dak'yar ya samu kanta tazo aka dunguma mota bayan sun kira abba ya sanar musu suna asibitin uduth wurin dr. Say.......

Say yana zaune a office abba haris ya shigo masaa birkice,dakyar ya iya sanar masa mota ta kad'e hafsa tana waje,ai banke abban yayi ya fito da gudu,Trauma suka wuce kai tsaye da ita,babban tashin hankalin say be wuce ganin pause nata yayi qasa ba sosai,sannan gashi bata numfashi daidai abu mafi ban tsoro shine jininta dakeyin qasa sosai amaimakon ya hau,yaukam kasa yin komai yayi ya janyewa wasu likitocin suyi,har yamma suna kanta sedai ba sa'a,Dr. Shuraim ne yafito ya sameshi har iffice shida abba haris da daddy,suna ganin ya shigo suka tashi tsaye,kai tsaye wurin sayyed ya nufa ya dafa kafad'arshi,hannun nashi say yafara kallo sannan ya kalleshi da kyau,yace kafin shuraim yace wani abun

"Dr. Shuraim karkace dani abunda nake tsammani?" kallonshi shuraim yayi cikeda tausaya wa,duk sunsan hafsat itace xe aura kuma yana matukar santa yace

"To zaka ja da ikon Allah ne sayyeed?" kafin wani yace wani abun say ya sulale wurin a sume....

Mom Nua'iym
[2/7, 9:14 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)

Wattpadd@ 68billygaladanchi

*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*

21

Taimakon gaggawa suka bashi atake ya farfad'o,kallonshi Dr. D'in yayi yace "Haba sayyeed da kanka en uwanta kuma suce mana me?" kallon mamaki yake masa sannan yace

"Allah yasanya mafarki nakeyi" murmushi Dr. d'in yayi yace

"Ya zakayi da ikon Allah akanta to? Arziqinmu d'aya ma karayar iya hannu ne,se buguwa datayi aka,wanda wannan shine yake san bamu matsala sabida dama akwai wannan matsalar damuwa na d'aya idanta" sauke ajiyar zuciya yayi sannan yace "Indai da ranta komai yazo mana da sauqi ai,indai inada rai da yardar Allah da izininsa seta samu lapiya" ahaka suka dunguma dunkansu dakin da take.......tunda hafsat taji likita awa su daddy bayanin cewar idantane suke tunani adawo baya kuma idan ya samu matsala lallai wannan karon gyaruwanshi se Allah,amma dai bazasukai karshen maganar ba seta farfad'o idan har bata gani da matsala idan kuma tana ganin komai to wannan daidaine,hankalinta ne ya tashi amna bata nuna ta farka ba hasalima ko motsin kirki batayi ba daga kwanciyar datake,har suka fita aka barta ita kadai,da sauri ta bud'e idon nata tana ganin hasken fitila da komai sannan ta sauke ajiyar zuciya had'e da tunano abinda ya faru,dukda tanajin azabar d'aurin da aka yiwa hannunta seta samu kanta da murmushi,ita kadai tasan ma'anar sa kuwa........

Washe gari hafsa ta farka amma qememe tanuna bata gani,wannan abun ya tashi hankalin sayyeed musamman dayake ya sani yanzu kam da matsala tunda shine na biyu,agaban su daddy sanda yayi kuka sosai yana me mata adu'a,shaam kuwa koda Dr. Shuraim yamasa bayani kasa cewa komai yayi gaba ki daya jikinsa ya masa sanyi,dana sanin abubuwa da dama ya farayi ciki kuwa hadda zuwa ya ziyarci Innah,yana ganin dayabi abun a hankali da duk haka bata zo ta faru ba,jan jikinsa yayi zuwa kofar dakin da hafsa take ciki,a hankali ya tura ya shiga ganin ba kowa ita kuma tamkar me bacci ya sanya ya matsa kusa da ita ya kurawa fuskarta ido dayake da tabbacin lallai dabeyi yunkurin tarwatsa farin cikinta ba da duk hakan bata faru ba,da fuskarta bata kumbura har haka ba,da yanzu tana gani yanda kowa ke gani da yanzu hannunta be karye ba lapiyanshi qalau,da yanzu bata kwance a wannan asibitin, dafe kanshi yayi ya furta a sarati cikin muryar kuka

"Mesa arayuwa ni shammaz na cika san kaina da yawa? Mesa zan wulaqanta jinina kuma yarinyar data zab'i zama dani ta sadaukar da farin cikinta akaina? Mesa zan sakaki a had'ari hafsat? Mesa tunda kika fara girma kika san meye so kika fara dani nake kuma kan wulaqanta miki rayuwa? Tunda kikace kina sona nake qasaki ta hanyoyi daban daban,Allah kuwan Allah ze barni kuwa? Zan iya jin dadin rayuwa bayan haqqinki na saman kaina?" fashewa yayi da kuka awurin cikeda ban tausayi sam sam bayasan abunda ze tashi hankalin hafsat yanzu,ita kuwa duk wani abinda yaje fada a kunnenta yake fad'a sedai tana d'aukar kalamanshi cikeda yaudara mara misaltuwa,sam bata yarda dashi musamman a wannan gab'ar data nemi san datake msa ta rasa gaba d'aya........

Uncle sayyeed ne yazo dakinta da dare ba kowa se ita kad'ai,ta rufe idonta ruf tamkar me bacci zama yayi a kusa da ita ya kura mata ido ba tare da yayi magana ba,taji kamshin turarensa wannan ya sanya ta bud'e idanta a hankali,tabbatarwa kanta tayi da cewar shi kadaine ya sanya ta sauke masa su,cikeda tsoro yankalleta dakyau murmushi ta sakar masa tace

"Uncle baby,wannan ita kad'aice hanyar dazanbi in raba kaina da shammaz,na tabbatar a yanda nake nakasasshiya baze aureni ba,nakuma sn bakada labarin cewar Innah ta sokoto ta rantse sena auri shammaz kota tsinewa sundaddy, banje mota ya kadeni da gangan ba,amma jin cewar idona

Please Login or Register in order to submit comment