Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

๏ปฟ[6:37PM, 2/1/2018] ~Maman_twins๐Ÿ’ž๐Ÿ˜๐ŸŒน: ยฎ *_HASKE WRITERS ASSO_*
( _Home of expert & perfect writers_)


*ALWASHI....!*๐Ÿ’
_(Labarin Hafsat)_


_*NA*_

_*UMMI A'ISHA*_



_Dedicated to MISS XOXO_


_Sakon fatan alkhairi gareki k'anwata Feedohm marubuciyar ZAN RAYU DAKE,ina yimiki fatan alkhairi aduk inda kike, indeed i have no words to thank u, am deeply grateful....! The first page is belong 2 u dear!_



DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN K'AI.



*1*



****Gidane na marayu mai d'auke da tangamemen gate sannan ga katanga babba zagaye da gidan wanda tsawonta ma abin kallone,haka shima cikin gidan yake wawakeken gaske mai dauke da gine gine masu yawa wadanda suka hadar da ofisoshin ma'aikatan gidan da kuma wurin kwanan marayun da kuma duk wani abu na bukatarsu,

Duk inda ka hanga yarane zaune sunyi group group, masu wasa nayi sannan masu hira sunayi yayinda wasu kuma suke yan aikace aikacensu na yau da kullum,

Wasu yanmata ne guda biyu acan gefe su kadai wadanda akalla shekarunsu zasu kai shekaru 23,

Daya daga cikinsu tayi tagumi tana sanye da kodadden hijabi da wata kodaddiyar atamfa ajikinta haka itama dayar kayan jikinta duk sun gajiya,

"Hafsat wai wannan tagumin da kikayi na menene? Yau naga gaba daya yanayin naki sai ahankali tamkar wata marar lafiya..." Daya daga cikin yanmatan tafada bayan ta dafa kawar tata,

"Amina wallahi lafiyata kalau kawai dai ina tunanin makomar rayuwarmu ne acikin gidan nan, ba kasafai mutane suka fiya kulawa damu ba, hatta gwamnati tayi watsi da rayuwarmu sai lokaci zuwa lokaci take tunawa damu..." Wadda aka kira da suna hafsat tayi magana cikin karyewar zuciya,

"Amma dai hafsat wannan ai ba bakon abu bane awajenmu duba da tsawon shekarun da muka diba acikin wannan gida gashi har yau Allah bai kawo wanda zai daukemu ya fitar damu daga cikin gidan nanba ko muma mazamo yaya kamar kowa.."


"Amina kenan tayaya zamu zamo yaya kamar kowa alhalin babu wanda yasan asalinmu, Allah ne kadai yasan tushenmu dan haka kinga maganar amaida mu 'yaya ma bata taso ba.."

"Hmmm babu komai koma dai yayane Allah yana tare damu..."

"Kai yanmatan nan kutaso kuzo muje.." Muryar daya daga cikin ma'aikatan gidan marayun ta ratsa kunnuwansu wanda hakane yayi sanadiyyar katse musu hirar da suke yi,

Mikewa sukayi suka karasa inda take,

"Yawwa kuzo muje, wannan bawan Allahn ne yauma yakawo muku agaji kamar yadda yasaba..."

Batare da sunyi magana ba suka bi bayanta, gaba daya an tattaro yaran gidan antarasu wuri guda gefe kuma wata babbar motace anata sauke kaya daga kanta wadanda suka hadar da buhunhunan kayan abinci da tufafi,

Wuri amina da hafsat suka samu suka tsaya suna kallon irin uba uban kayan da ake saukewa,

Kowacce acikinsu addu'a take acikin zuciyarta kan Allah yasakawa koma wanene wannan mutumin da alkhairi domin yajima yana yi musu hidima,

Kayan da aka sauke daga kan wannan katuwar motar ba dan kadan bane domin bayan kayan abinci da kayan sawa harda barguna da katifu,

Suna nan zaune sunyi tsuru suna ganin tulin kayan da aka kawo musu har aka kammala sauke kayan nan wakilin wanda yabada kayan akawo ya mike yadanyi jawabi,


_Kamar yadda muka sani kuma muka saba, wannan bawan Allah Wanda mukafi sani da suna baya goya marayu akoda yaushe yana iya kokarinsa wurin ganin ya kyautatawa rayuwar marayu sannan kuma ya sadaukar da dukiyarsa wurin taimakon musulunci, kamar yadda nadade ina fada muku shi wannan bawan Allah matashine ba tsoho ba kawai dai Allah ne ya albarkaceshi da halin manya dan haka muyita yimasa addu'a akan Allah ya albarkaci rayuwarsa da dukiyarsa da kuma iyayensa...._

"Amin..."

Dukkan jama'ar dake wurin suka amsa cikin farin ciki domin wannan bawan Allah ba karamin taimako yake yiba saboda kusan agarin ma shine lamba daya wurin taimakawa rayuwar marayu.

Saida aka gama rabawa marayun kayayyakin da aka kawo musu akan idon wakilin wannan bawan Allahn dake basu gudun mawa wanda suka dade da rada masa suna da baya goya marayu,bayan gama rabon kayan tsaf sannan wakilin baya goya marayu yatafi, sukuma yaran kowa ya kinkimi kayanshi ya nufi wurinda zai adana su, haka suke gudanar da rayuwarsu cikin wannan gida wanda a lokuta mafiya yawa sukan shafe sama da watanni biyu batare da sun samu wani tallafi ba indai ba wannan bawan Allahn ne ya aiko musu ba gashi kuma duk wannan hidimar da yake yi musu basu taba ganinsa ba balle har su gane kamanninsa.


***

Kamar bazai taka k'asa ba haka yake tafiya, sanye yake cikin jar t shirt mai dogon hannu yasha d'amara da jar belt wadda ke d'amare ajikin bakin trouser din dake jikinsa, duk da wai ahakan sauri yake amma baisashi sauya salon tafiyar tashi ba,bak'in face din dake idonshi yadan gyara bayan ya maida hankalinsa kan agogon azurfar dake d'aure a tsintsiyar hannunshi, kamar koda yaushe fuskarshi babu alamun fara'a atare da ita,

K'ofar da zata sadashi da falon mahaifiyarshi ya bude ya shiga fuskar nan kamar zaice wayyo Allah dan tsananin fushi,

Ganin babu kowa aciki yasashi kara yin gaba, awani tsararren falo wanda aka tanada musamman domin hutawa ya isketa, tana zaune saman kujera daga ganinta bazata haura shekaru 45 ba aduniya, farace jajur mai dan jiki, tana sanye da wani leshi mai tsadar gaske, wuyanta da hannuwanta gamida kunnenta duk gwala gwalai ne sai walwali suke, haka yan yatsun hannunta ma duk sunsha zubunan gold,gefenta kuma wata yar matashiyar budurwa ce wacce zata kai shekaru 23 tana kwance tayi matashi da cinyar matar,

Sallama yayi wadda ba lallai su iya jiba domin aciki ciki yayita,

Dukkansu hankalinsu yana ga drama din da suke kallo atashar tauraron dan adam wanda har saida ya zauna sannan suka farga dashi.......



*_Ummi Shatu_*๐Ÿ‘Œ๐Ÿป
[6:37PM, 2/1/2018] ~Maman_twins๐Ÿ’ž๐Ÿ˜๐ŸŒน: ยฎ *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_



*ALWASHI.....!*
๐Ÿ’
_(Labarin Hafsat)_







*_NA_*



*_UMMI A'ISHA_*







_Dedicated to Miss Xoxo_







*2*







***Fuska cikeda annashuwa mahaifiyar tashi ta kalleshi cikin fara,a yayin da shikuma sai faman cijar lebenshi nakasa yake yi fuska babu annuri,



"Yusleem.... Har anshigo?"



Mahaifiyar tashi ta tambayeshi da fara,a akan fuskarta,



Saida yasake hade rai idanuwansa na bisa screen din hadaddiyar wayar dake hannunshi sannan ya amsata dakyar,



"Ehh Mami..."



Wata fara,ar tasake yi sannan tayi magana,



"Nima dama tun dazu nake jiranka kazo saboda ina son ka sama mana visa nida surayya zuwa kasar chairo zan kaita medical check up..."



Shiru yayi batare da ya amsa ba yaci gaba da latsa wayarshi, idan da sabo to kowa nagidan ya saba da wannan mummunar dabi'ar tashi tayin shiru idan ana yimasa magana, ko mahaifiyarshi ce tayi masa magana sai yaga dama zai amsa gashi da shegen girman kan tsiya kamar shi yafi kowa,



Saida ya dauki fiyeda mintuna goma sannan ya daga manyan idanuwanshi wadanda suke tamkar kwai domin round eyes gareshi,surayya kanwarshi ya kalla wacce ke kwance akan cinyar mami tana sanye da English wears riga da skirt bakake kanta babu dan kwali,



Baiyi magana ba yasake mayar da kanshi kan screen din wayarshi,



"Mami...am dama ina son infada miki.."



Tattaro hankalinta gaba daya Mami tayi zuwa gareshi,



"To yusleem ina jinka.."



"Mami nasaki khadija yau da safe.."



Zaro idanuwa Mami tayi gamida dafe kirji, surayya kuwa dake kwance akan cinyarta zunbur tayi ta mike zaune, dukkaninsu kallonshi suke cikeda tuhuma gamida zargi iri iri,



"Nashiga uku ni siyama, innalillahi wa inna ilaihir raji'un...." Mami tafada tana tafa hannuwanta,



"Haba yusleem wai kai wanne irin mutum ne? Anya kuwa ba aljana ce ta aureka ba? Karfa ka manta ko watanni uku cikakke ba ayiba da bikinku kaida khadija amma shine yau kazo kake fada min wai ka saketa?



Yusleem mai ka dauki aure ne? Ka daukeshi ne a matsayin wasa, ko kuma abin wasa ko wasan yara?



Yusleem duk fa wannan dukiyar da kake ganin kana da ita bazata taba iya siya maka darajar da aure zai siya maka ba...!"



Dan jan numfashi tayi sannan ta dora,



"Kana yaronka dakai amma acikin shekaru biyar kayi aure sama da guda goma, haba yusleem wannan wacce irin mummunar dabi'a ce, ka mayar da sakin aure ba komaiba,saki da Allah ma baya sonsa amma kai kuma shine ka mayar tamkar sana,arka,



To agaskiya nidai nagama gajiya da wannan halin naka na auri saki, babu damar ka zauna da mace na koda shekara dayane?"



"Gaskiya Yaya bamuji dadin wannan labarin ba, yanzu anty khadijan ma ka saketa?"



Surayya ta fada idonta dauke da kwalla,ko kallonta baiyi ba bare tasa ran zai bata amsa,



Fada mami tasoma balbala masa ta inda take shiga bata nan take fitaba,



"Ni narasa gane kan wannan hali naka yusleem, kwata kwata baka dauki aure da daraja ba, sam baka son zama da mace, wannan wacce irin rayuwa ce,



Kuma bafa kowa kake watsawa kasa a idoba face ni tunda nice nake aura maka matan, yanzu abinda kayi ka kyauta kenan?"



Dan kishingida yayi kadan ya tsurawa wayarshi ido batare da yace komai ba,



"Dakai nake magana kayi min shiru, ka fada min dalilinka na auri saki, akalla ba a kasaru ba yusleem ka auri mata dai dai dai har guda goma sha..., baka da lafiya ne ko yaya?"



Saida ya dan shafi sajen fuskarshi sannan ya kalli mami,



"Mami ni lafiyata kalau sannan dama ai ban taba cewa ga wacce nake so ba, duk matan da nake aure kece kike samo min su ki aura min.."



"Wacce irin magana kake fada min yusleem? Dan bakai kagansu kana soba shikenan bazaka zauna dasu ba? Wannan dalilinne yasa ka dauki auri saki ba abakin komai ba?



Sau nawa ina baka dama domin ka fito da matar da kake so in aura maka amma sai kayi biris da maganar, kuma ni ai aganina nagama yimaka duk wani gata wanda yadace ace uwa tayiwa danta domin na nemo maka mata yan mutunci, yan asali, masu aji wadanda suka dace dakai amma daga karshe duk dai labarin iri dayane cewa ka sakesu, yanzu kaduba kaga yarinyar nan khadija da ka saketa ka rabu da ita, yarinya ce mai hakuri mai nagarta mai sanin ya kamata, yarinya kyakkyawa yar asali yar mutunci yar kawata hajiya fa'iza,ko wata biyar ba ayiba da bikinku amma kasaketa..."



Dan tsagaitawa mami tayi tana dubanshi cikeda bacin rai, har tsawon mintuna biyar babu wanda yasake magana acikinsu,



"Yusleem wai da me kake takama ne da har kadauki auri saki ba abakin komai ba?



Idan dan kyawun dakake dashi ne yasaka kake yin haka to ya kamata fa kasani akwai wadanda suka zartaka kyau amma basa yin haka,



Idan kuma dan arzikin dakake dashi ne to kasani akwai big millionaires suna nan ba irinkaba young millionaire ba kuma basa aikata wannan wulakancin dakake yi,



Inkuma kuruciyar da kake tare da itane yasaka yin wannan cin mutuncin to wallahi ka gaggauta farkawa daga wannan dogon baccin da kakeyi domin akullum shekarunka sake yawa suke bawai raguwa ba.."



Shiru mami tayi cikeda bacin rai tana huci saboda babatun da tagama yanzu,



Mikewa yayi sannan yayi magana ahankali,kamar mai ciwon baki yace,


"Kiyi hakuri mami.."



Ko amsa masa batayi ba yasaka kai yafice daga cikin falon, nan mami da surayya suka rakashi da idanu....




_*Ummi Shatu*_๐Ÿ‘Œ๐Ÿป
[6:37PM, 2/1/2018] ~Maman_twins๐Ÿ’ž๐Ÿ˜๐ŸŒน: ยฎ *HASKE WRITERS ASSO.*

_(Home of expert & perfect writers)_







*ALWASHI.......!*๐Ÿ’

_(Labarin Hafsat)_







*_NA_*



_*UMMI A'ISHA*_







_Dedicated to Miss Xoxo_




_Fatan alkhairi ga takwarar Nana Hafsat wato Hafsat Rano, this page tukwici ne agareki...!_





*3*







***Dafe goshi mami tayi cikeda damuwa bayan fitar yusleem,nan tayi shiru tana jin wani irin bacin rai yana ziyartar zuciyarta,



Sunfi mintuna biyar itada surayya batare da wani acikinsu ya iya yin koda motsi ba,
Mami ce tayi karfin yin magana cikeda damuwa,


"Narasa gane kan yaron nan, agaskiya abin nasa yawuce tunani, yawuce hankali, gaba daya zagayen jahar nan harma da mak'ota kowa yasanshi awurin auri saki, duk yabi yabatawa kansa suna..."



"Mami wallahi nidai ban yarda yaya yusleem lafiyarsa kalau ba, duk inda akaje aka dawo acikin abubuwa guda uku to abu daya yana damunsa dole,



Kodai aljana ce ta aureshi, ko kuma yana shaye shayen kwayoyi aboye ko kuma kwakwalwarsa ta dan tabu batare da mun saniba..., wallahi mami ki kaishi adubashi" surayya ta kareshi zancen hawaye yana bin kuncinta,



Jinjina kai mami tashiga yi tana kallon surayya amma sai dai kafin takai ga yin magana tuni karar wayarta ta cika musu kunnuwa nan mami ta dauki wayar jikinta asanyaye saboda ganin sunan wanda ke kiran,



Jiki asanyaye mami ta kalli surayya,



"Kinga ni ko? Hajiya fa'iza ce ke kirana mahaifiyar khadija, yanzu ban san me zan fada mataba, ban san irin fushin da take cikiba.."



Kiranne yakatse wani yasake shigowa,



"Mami ki daga kawai.." Surayya tace da ita bayan ta tsura mata ido,



"Hajiya siyama ina fata dai kinji cin mutuncin da danki yayi mana, koda yake nasanma da saninki zai aikata hakan,yayiwa khadija saki na wulakanci batare da laifin komai ba..." Jin abinda mahaifiyar khadija ke fadi yasa mami saurin katseta domin bata son amintakarsu da kawancensu yabaci ta wannan silar,



"Hajiya fa'iza dan Allah kiyi hakuri kijirani zanzo gidan, dan Allah karki yi fushi akan wannan abun da yafaru, kisani khadija yatace kuma bata da wani banbanci da yayan da nahaifa..."



"Ai hajiya siyama magana tariga da takare Allah yasa haka shine yafi alkhairi kawai kuma dama halin danki ne auri saki tunda ba akan khadija yafara ba, ita khadija kaddara ce kawai ta hauta har takaita ga aurensa..."



K'ittt mami taji hajiya fa'iza takashe wayarta bayan tagama wadannan maganganu,





"Yusleem bai kyauta minba, akansa zumuncinmu da muka dade muna yi da hajiya fa'iza yana neman baci.."



"Ai mami nafada miki wallahi acikin abubuwa guda ukun nan da na zayyano abaya akwai daya aciki wanda ke damunsa"



"Hakane surayya nima nayarda da batunki, indai kuwa hakane to yazama dole inbincike shi sosai har ingano matsalarsa..."



Shuru kowannensu yasake yi har na tsawon wani lokaci, surayya ce tafara mikewa ta nufi bedroom dinta ganin haka yasa mami itama tashi ta shiga nata bedroom din, mintuna kadan tafito cikin sabuwar shiga wacce tafi ta da,



Wani jan swiss lace ta dauro tayafa babban mayafi kalarshi,hannunta rikeda handbag dinta ta leka bedroom din surayya, kwance ta isketa da wayarta ahannu suna yin video call itada Abdul tana fada masa sakin da yusleem yayiwa khadija,



"Yawwa yaya Abdul ga mami..."



Karbar wayar mamin tayi tana kallon Abdul din,



"Mami haka yaya yasake karo wulakanci? Yanzu sury take fada min wai yasaki khadija yau.."



Ajiyar zuciya mami ta sauke,



"Abdul nikaina yanzu haka ban san da wacce kalma zanyi amfani da itaba wurin bawa mahaifiyar khadija hakuri duba da irin wulakancin da yayanku yayi, auren da ko watanni biyar ba ayiba amma wai yau har anyi angama..."



"Ni mami narasa meye matsalar yaya wallahi, ko kadan baya son zama da mace.."



"Abdul koma dai menene matsalarshi yazame min dole intashi atsaye saboda na lura sam shi baisan zuru ba, yanzu haka gidansu khadijan zance inbawa mahaifiyarta hakuri sannan kuma innemi bikonta su taimaka su dawo da ita gidan mijinta.."



"To shikenan mami sai kin dawo.."



"Yawwa abdul sai nadawo, ina khalifa din kuma?"



"Mami shi yashiga school tun dazu yanada lecture ni yau banda class shiyasa nake gida"



"To Allah yabaku sa'a,idan yadawo ka gaidashi itama surayya zuwa nanda 3 weeks zata koma Malaysia hutunta yakare..."



"To shikenan mami Allah yakaimu"



"Amin, babu wata matsala dai ko?"



"Wallahi babu matsalar komai mami domin yaya yana turo mana da kudade akai akai.."



Jijjiga kai mami tayi, "yanada wannan kokarin kam,zama da mace ne bai iyaba"



Dariya abdul yafara nan ta mikawa surayya wayar tamike tana gyara mayafinta, jin surayya da abdul sun cigaba da hira yasata fadin,



"Surayya bazaki rakani bane intafi?"



"Mami kije kawai sai kin dawo.."



"Haba surayya da ina cewa sai ki kaimu kawai.."



"Mami bazan iya driving ba wallahi kin san cikina ciwo yake.."



"To bani key din motar taki inje Mamman driver yakaini.."



Hannunta ta mika kan drewar tadauko key din tabata takoma ta kwanta taci gaba da yin video call dinta itada Abdul yayinda ita kuma mami tafita,



Shu'aibu kuku ta iske acikin kitchen yana yin yan aikace aikacensa kamar yadda yasaba nan tabar mishi abinda take son yadafa mata kafin tadawo,sannan tadora da cewar ya leka bedroom din sury itama ya tambayeta abinda take sha'awar ci da daddare sai ya dafa mata,



Tunda tafito driver dinta wanda aka tanada musamman domin kaita unguwa yazo ya tareta tareda karbar key din motar dake hannunta, bude mata yayi tashiga owners corner ta zauna yaja suka tafi.





Kai tsaye gidansu khadija suka nufa koda sukaje mahaifiyar khadija wato hajiya fa'iza babu yabo babu fallasa ta karbi mami,gyaran murya Mami tayi sannan tace,


"Hajiya fa'iza mu taru muyi hakuri mu daidata yaran nan mu mayar da khadija dakinta dan Allah.."



Tagumin da tayi tagyara, "hajiya siyama ba ki nayiba amma kisani wallahi macen da zata iya zama da yusleem sai antona, kinga tunda khadija ta shigo gidan nan tana can ta kunshe adaki tana kuka, taki ci taki sha..."



"Ikon Allah, to me yayi mata?" Mami tafada cikeda damuwa,



"Waya sani, sai dai muje tare ko zatayi magana..."

Mahaifiyar khadija tafada fuskarta adaure.






*_Ummi Shatu_*๐Ÿ‘Œ๐Ÿป
[6:37PM, 2/1/2018] ~Maman_twins๐Ÿ’ž๐Ÿ˜๐ŸŒน: ยฎ *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert & perfect writers)_




*ALWASHI...!*๐Ÿ’
_(Labarin Hafsat)_




*_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*



_Dedicated to MISS XOXO_



*4*

aishaummi.blogspot.com




***Tashi mami tayi tabi bayan hajiya fa'iza zuwa dakin da khadija ke kwance tagama cin kuka ta koshi dan tsabar kuka yanzu ko hawayen ma bata iyayi,

Zama mami tayi agefen gadon da khadijan ke zaune ta dafata jikinta asanyaye,

"Khadija kiyi hakuri kinji, insha Allah komai zai daidaita sannan zaki koma gidan mijinki"

D'aga jajayen idanuwanta wadanda suka rine tayi ta kalli mami,

"Mami bazan iya komawa gidansa ba, nahakura da aurenshi, bazan sake iya zaman aure dashi ba wallahi"

Gaban mami ne yashiga dukan tara tara saboda jin abinda khadija tafada,

"Khadija wani abu yayi miki?"

"Mami ni babu abinda yayi min kawai wulakancinshi ne bazan iya cigaba da jurewa ba"

Dafata mami tasake yi,cikin sigar lallashi tace,

"Nasani khadija, kuma nasan kinada hakuri amma daurewa zakiyi kisake yin wani hakurin ki koma dakinki..."

"Mami bazan iya komawa ba wallahi nidai nahakura"

"To kuma khadija idan Allah ya kaddaro da rabo a tsakaninku fa? Bana son ayi gaggawar yanke hukunci daga baya kuma azo ana dana sani"

Sai a lokacin hajiya fa'iza mahaifiyar khadija tayi magana,

"Ai hajiya siyama maganar rabo a tsakaninsu ma babu shi saboda tunda akayi auren bai taba shiga dakinta ba, ko kallo bata isheshi ba bare har ya kulata"

Tagumi mami ta rafka taci gaba da sauraron bayanin da hajiya fa'iza take yimata na irin zaman da yusleem yayi da khadija ta rufe maganar da cewa,

"Kawai dai muyi addu'a Allah yasa hakane mafi alkhairi, nanda sati biyu kuma zamuzo mu kwashe kayanta ki fada masa"

Ita dai mami jiki babu kwari ta mike bayan tagama bawa khadija da mahaifiyarta hakuri, jakarta ta dauka ta fita ranta babu dadi zuciyarta cike da bacin rai, wannan karon kam yazama dole ta nunawa yusleem fushinta akan abinda yajima yana aikatawa na sakin mata babu gaira bare dalili, babu laifin tsaye babu na zaune.

Har kofar gida hajiya fa'iza ta rakata suna cigaba da bawa juna hakuri musamman ma mami da take ganin laifin na yusleem ne domin shine yake nema yaja mata lalacewar zumuncinsu da matar da suka dade atare,

Mota Mamman driver ya bude mata tashiga ta zauna ya rufe suka tafi domin tuni hajiya fa'iza tajima da shigewa cikin gida.

Da tunani kala kala acikin zuciyarta suka karasa gida, cikeda damuwa take zayyanewa surayya abinda yafaru, suna tsaka da yin maganar sukaji shigowar yusleem,

Bai karaso cikin falon ba yatsaya a dining area, sanye yake da jar t shirt mai gajeren hannu sai black trouser, kamshin turaren lailatul abyad da na real oud ne yake tashi daga jikinsa, fuskarshi tayi fes sai annurin kyaune yake fita daga gareta,

D'aga murya Mami tayi tayadda tasan zai iya jiyota,

"Kai..."

"Na'am ma..." Ya amsa yana kokarin bude jeren flasks din dake ajiye asaman table din,

"Zo nan.." Mami tafada bayan ta daure fuskarta, fasa diban abincin yayi ya tasamma cikin falon inda su Mami suke.


***

Rayuwar Hafsat haka taci gaba da tafiya agidan marayu, yanzu haka ta maida hankali sosai wurin koyon sana'o'in hannu domin ana zuwa akoya musu, musamman aka ajiye musu wadanda zasu rinka koyar dasu,

Cikin lokutan da babu yawa ta kwarance wurin sak'a sannan tafara iya dinkin keke,haka kawarta Amina itama tana yi daidai gwargwado,

Kullum cikin yin sak'a suke itada Amina suna warwarewa sai su sake saka wani abun nadaban kamar hula, safa, ko riga,

Yau ma kamar kullum suna zaune a inda suka saba zama suna yar hirarsu kowaccensu tana rikeda koreshi tana yin saka,

Hirarsu ce ta katse saboda gano wasu manya manyan motoci da sukayi suna kokarin shigowa cikin harabar gidan,

Amina ce ta zunguri Hafsat da hannunta,

"Hafsat yauma da alama munyi baki, watakila mai girma governor ne yakawo mana ziyarar bazata.."

"Nima dai abinda nake tunani kenan Amina, koma dai menene kinga tashi muje ayi damu kin san bahaushe yace wai gani ya kori ji..."

Mikewa sukayi atare kowaccensu ta tukunkune zaren kulunta da koreshi suka nufi inda suka hango mutanen gidan suna tafiya....




*_Ummi Shatu_*๐Ÿ‘Œ๐Ÿป
[6:37PM, 2/1/2018] ~Maman_twins๐Ÿ’ž๐Ÿ˜๐ŸŒน: ยฎ *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert & perfect writers)_




*ALWASHI...!*๐Ÿ’


2 Comments On ALWASHI
avatar
aliyu-1-5-2

12 months ago

Reply

I appreciate it

avatar
aliyu-1-5-2

12 months ago

Reply

I appreciate it

Please Login or Register in order to submit comment