Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

*together* )

*MABARACIYA*

*Story* *and* *writing*

*By*

*FIDDAUSI* *SANI*
(damsel feedorh)

🅿️:2️⃣3️⃣



"Ammi tunanin me kikeyi haka ,kardai saboda wannan haɗin ne kika shiga damuwa?".

Dogon Nunfashi ta ja tana sauke ajiyar zuciya" ko ɗaya Mu'aisam , meyasa zan damu dan Alh yanuna ikon sa akan ka ,karka manta Rufaidah itama yatace ,dan kuwa jinin Alh ce , sedai fin karfin da yanuna ne ya taɓa zuciyata kuma na ta bbata saboda yasan bani ce na haife ka ba shi yasa yayi haka" haba Ammi dan Allah kidena faɗar hakan haihuwa ta ce kawai bakiyi ba ,amma wahalar da kikayi dani na tabbata ko kece kika haifeni iyaka kenan ,akaina menene ba'ayi miki ba a gidan nan kuma duk kika danne ,bantaɓa jin cewar bakece Mahaifiyata ba ,dan kin nuna min soyayyar da baki nunawa waƴanda kika haifa Ammi a lokacin da kika samu Rumaisa nayi tunanin zaki sassauta daga kaunar da kikeyimin amma se ma karuwa yayi ,Ammi kinsan ina sane da lokacin da Hajia saudah tayi makircin ta har ta hana Abba biyamin kudin school ,da kikayi magana lefin ya shafeki har yayi iƙirarin saki akan ki ,ke ce wacce kikaci gaba da ɗaukar dawainiyata da kuɗin ki da kuma ƙarfin ki ,a lokacin na sake tabbatar da kaunarki gareni ,naso nabar gidan nan tun a wancen lokacin dan kuwa har gida natafi amma se Umma tayi min tunin abinda namanta itace ta faɗa min cewar idan har nabar gidan nan to ke nayiwa butulci ba kowa ba ,kuma maƙiyanki zasuji daɗi ,nima na tabbatar da hakan shiyasa na dawo gareki ,Ammi ina zaune a gidan ne saboda ke da ke nayi sabon da banyi shi da wacce ta haifeni ba ,inayi miki so irin na ɗa da uwa ,taya zanjuya wa wacce ta sadaukar da komai nata saboda ni ,Ammi karki manta kece nan kika sakani fara kula Rufaidah ,har nafarajin ta kamar yadda nake jin yayarta Khadijah, wlh ban taɓa jin inayi mata wani so da ban ba kuma bana tunanin zan iya zama da ita a natsayin mata , musamman yanzu da na fahimci cewar ba ita bace zaɓin ki ,shirun da kikaji nayiwa Abba ,kece kika dorani akan hakan kin haneni dayin musu ga manya tun bansan amfanin hakan ba ,yanzu ma naji tsoron namusa masa ne ranki ya ɓaci shiyasa nayi shiru ,dan Allah Ammi karki saka damuwa a ranki ,dan kuwa koda ina son Rufaidah kikace batayi miki ba wlh zan canja ,bare ma bana son ta ,kinsani Ammi ni mutum ne me son ya auri macen da zata darajaki da kuma ni kaina ,kuma matuƙar na aureta hakan baze samu ba ,sam tarbiyyarta beyi min ba Ammi ,naga amfanin auren mace ta gari tun akanki irin yadda kikeyiwa Abba biyaya ,dan haka nima kiyi min addu'a Insha'Allah zaɓin Alkhairi ze zo ,dan Rufaidah ba Alkhairi bace a gareni".

Shafa kansa Ammi tayi cikeda alfahari tace " Mu'aisam ko kaɗan banga lefinka ba kuma hakan da kayi ka kyauta ,kuma bawai ina kin ka aureta bane ko ɗaya ,sedai inason nunawa Alh ikona ne akan ka ,kayi haƙuri ka amshi kyautar da yayi maka ,ko mutuwa tana kunyar idon mahaifi Mu'aisam ,taya zakacewa Alh baka son yarshi hakan ma sam be dace ba ,kuma bakasani ba ko akwai alkhairi a tsakanin ku sedai abu ɗaya da zan faɗa maka kar ka tauye kanka ,idan har kasan akwai wacce kake so to kasanar dani nayi maka alƙawarin mallakar ta ,koda rayuka zasu ɓaci ,tashi katafi Allah yayi maka albarka ya tabbatar da alkhairi a tsakanin ku."

Amenn Ameen, Ammi nagode sosai amma dan Allah kicire damuwar nan banason kusamu matsala da Abba saboda wannan abun, Mu'aisam naki ne har abada kece me iko dashi ,Abba ma zanyi masa karane saboda ke ,zan ɗan fita wurin Alƙasim amma bazan daɗe ba zan dawo " adawo lafiya ,Allah ya kiyaye min kai" Amin " ya amsa fuskar shi dauke da murmushi.

Hajiya Sauda#

Suna isa party ɗinsu tayi yarfi da hannun Rufaidah tana aika mata wani mugun kallo , akausashe tace" se kin faɗa min gaskiya ubanki ,kece kika je kika faɗa wa Alh cewar kinason lalataccen yaron ce ko kuwa? jin Muryar da tayi anfani da ita yasaka Rufee fashe wa da kuka dan zata iya cewa tunda take a rayuwar ta Hajia Sauda bata taɓa yi mata tsawa ba bare zagi " ko bakiji me nace ba? tasake katse mata tunani ,cikin rawar murya tace " kiyarda dani Mama ban san komai ba wlh ,tunda kika ce bakison sa na haƙura ban san meyasa Abba ya yanke wannan hukun cin ba" ajiyar zuciya ta sauke se kuma ta sassauta murya tace " Rufaidah a duk duniyar nan babu wacce take sonki fiye dani, nice nasha wahalar haihuwar ki da renon cikin ki ,tunda kika tashi baki taɓa cewa kina son abu banyi miki ba meyasa yanzu ni bazakiyi min wannan Alfarmar ba , Rufaidah da ace auren ki ze yiyu da yaron nan da bari amma taya kike tunanin zan bari ki auri jinin Bilki da Zainabu mutanen da basu taɓa sona a zuciyarsu ba
wanda saboda hassadar da sukeyi min ne yasaka Bilki yin kyautar ɗanta ga Zainabu ,shi kansa yaron ba mutuncina yake gani ba saboda haka nikeso ke da kanki kitafin ki faɗa wa Alh cewar bakison wannan auren akwai wanda kikeso!
Da sauri Rufee ta kalleta ,tana girgiza mata kai " A'a Mama karkiyi haka ,ni kaina ba kaunar Ammi nike ba amma hakan baze hana naso Mu'aisam ba ,kiyimin wannan Alfarmar koda ze zama na ƙarshe a tsakanin mu dan Allah kibarni na aureshi wlh bazan iya auren wani namiji bayan shi ba.

Rufaidah na fahimci bakisan inda ke miki ciwo ba to saboda haka magana ta karshe zaki zaɓa tsakanin nida Mu'aisam dan kuwa matukar kika yarda da auren nan to kisani babu ni babu ke kimanta cewar nice na haifeki kitafi can na barwa Zainabu ku dama kunfi kaunarta dani ,na samu na rabu da Khadijah gaki ke zaki zaman min karfen kafa , shikennan babu komai ,tunda kin zaɓesa akaina " ta karasa tana fashewa da kukan muna funci , wanda yasaka Rufee rarrafawa ta isa gare ta ,itama kukan takeyi amma takasa magana se sharewa Mama hawaye takeyi ,duk da tanajin bazata iya haƙura da auren Mu'aisam ba ,sedai xatayi kokari ta shawo kan Mama ,tunda tana son ta tasan zata barta ta auri wanda take so

Ameerah#

lokacin da ta koma gida ta riske wani batu da ya jirkita tunanin ta ,wai Muhsin yazo tambayar auren ta wurin Yaya Labaran ,kuma ya amince masa ,lokacin da Aunty ta gama labarta mata se kawai taji hawaye yana bin kunci ta ,wanda ta rasa ko na miye, sedai ta alaƙanta hakan da rusa mata plan da wannan auren zeyi "haba Ameerah me kikeyi haka ,se kace za'ayi miki dole shifa yayanki ba yace yabasa bane ,kawai dai ze shiga cikin manema ne ,idan kika ce ga wanda kike so dole shi zamu aura miki" Aunty ta faɗa tana goge mata hawaye " Aunty baxaki gane bane ,nifa wannan Managern yasa nafara jin haushi sa meyasa baze tambayeni ba ,se kawai zeyimin kutse a rayuwa ta ,kinsan dai halin Yaya ai ,ganin sa ze iya cewa aure zanyi nikuma ban shiryawa hakan ba impact ma bana son Muhsin" to wa kekeso? Aunty ta tare nunfashin ta " abinda nake gudu kenan na tabbata shima Yaya idan nace banason Muhsin tambayar da zeyimin kenan ,wanda ke kinsan ba wannan bane a gabana ,hasali ma bazan iya aure da ƙarancin shekarun nan ba gaskiya ,nasan ke zaki fahimceni amma Yaya fa? bazan so na furta wa wani mutum kalmar rashin so ba amma a wannan lokacin dole zan gayawa Manager cewar bana son sa ko hakan zesa ya haƙura dani"

"A'a Meerah baza'ayi haka ba ai ,babu kyau furta kalmar ƙi musamman ga wanda ke son ka ,bakisan me Allah zeyi a gaba ba ,shin idan da rabon aure a tsakanin ku ,kin isa ki tsallake ne? Ni sam banga lefin wannan mutumin ba ,da badan son gaskiya yake yi miki ba na tabbata baze gabatar da kansa garemu ba ,nide shawara ta itace ,kici gaba da kulasa har zuwa lokacin da Allah ze yi miki zaɓi ,idan kuma shine Alkhairi ,se kiga munsha biki.......


Manage pls




Real Bazamfaria ce ❤️
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
( *On* *word* *together* )

*MABARACIYA*

*Story* *and* *writing*

*By*

*FIDDAUSI* *SANI*
(damsel feedorh)

🅿️:2️⃣4️⃣

*This page is* *for My Caring fans @Farida L Nuhu @ Amina Abdullahi@ A* *U* *almarkazy @ Nourrieyyer*
*Nagode sosai da kulawar* *ku Allah yabar* *ƙauna❤️*

Hankali tashe Hajia Sauda ta kira Laura ,sedai kusan ita ma hankalin ta yafi na Sauda tashi ,dan kuwa ta tabbatar da matuƙar Rufee tayi aure to ko ta rasata kenan ,dan haka tace " Hajiya Sauda wannan fa ba ƙaramin al'amari bane ,shiyasa tun farko muke faɗa miki cewar kinyi sake da har kika bari Namiji yake juya ki ,menene a wurinsa me yake baki wanda baki samun finshi ,idan ma kuɗi ne na tabbatar da yanzu ko da baki fishi kuɗi ba to zakuzo daidai ,saboda haka tun wuri kinuna masa cewar kema kinada ƙarfin iko ,ko da hakan ze zamo sanadin rabuwar ku ne"

" Da kata Laura bana kiraki saboda matsalar da ke tsakanina da mijina bane ,kawai mafitar fasa auren nan babu ruwanki da rayuwar aure na idan kuma bakida abun faɗa se na kira wata ko zan samu mafita" ganin kamar ta ɗauki zafi se Hajia Laura tace " to shikennan yanzu dai Hajia zama be kamamu ba gaskiya dole zan shigo Kaduna ,saboda wannan maganar ba na waya bane ,inaso kisaki ranki karki sake nuna cewar bakison wannan auren idan nazo nikuma nayi miki alƙawarin rushe maganar auren nan Alh da kansa zece ya janye " da gaske kikeyi Laura? Haba kina mamaki ne kinsan dai bana faɗar abinda bazan aikata ba ko dan haka kizuba ido kawai kijira zuwa na
"to dan Allah Hajia karki ɓata lokaci kixo dín kamar yadda kikace dan wlh nikaɗai nasan me nakeji kamar zuciyata zata fashe" to ki kwantar da hankalin ki ni ma dan akwai abinda nikeyi ne yanzu kinsan akwai wasu yara da nace miki za'a kawo ,to sun iso ina jiran senator Abba yazo yafara zaɓan wacce yakeso kafin na tallata sauran to shikuma baya kasan amma yace ze dawo jibi ,to yana dawowa zaki ganni " yawwa to Nagode sosai Hajia Laura se kinzo ɗin ina dibon hanyarki".

Muhsin be sake zuwa gidan su Meerah ba kuma be kirata ba ,se bayan kwana biyu ,wannan karon tare da karamar ƴarsa yazo wacce zstakai 4yers ,yarinyar kuwa anyimata gayu tayi kyau sosai cikin riga da wando ta ,zuwan yamma yayi dan haka yasamu unguwar da ɗan mutane babu lefi ,seda ya yi parking tukuna yakira wayarta ,ta na ɗaga wa ,ta gaishe shi " gani a ƙofar gidanku" gidan mu kuma Manager? Be bata amsa ba kawai ya kashe wayar sa, dan ya san halinta ,da musun tsiya ,ya daɗe a wurin zaune yana jiran fitowar ta amma shiru ,itakam Ameerah lokacin da ya kirata dama tana gyaran gida ne dan haka yana kashewa taci gaba da aikin ta ,sam ta ma manta da zuwan shi
Aunty da tafito ne zata shiga duba mara lafiya anan maƙota ta ga motar sa ,koma wa tayi cikin gidan tace " Meerah naga wata mota a bakin gida anya kodai Manager ne yazo ? Hala be samu wanda ze kira masa ke bane" turo baki tayi tace" Aunty sharesa idan ya gaji da zaman ai ze koma inda ya fito ,ni sam bana son takura wlh ina zaman zamana zezo ya dameni" au kinma san da zuwan sa kenan? Shiru tayi batace da Aunty komai ba " Ameerah kidena abinda kike sam babu kyau wulaƙanci bakisan waye mutun ba bakisan darajar da Allah yayi masa ba ,dan haka maza ki ɗauko nayafinki kitafi ,bara ni nabar fitar se zuwa dare "

tana ƙunaƙuni ta shiga ɗaki ta ɗauki haijabin ta ,tazo zata tafi " haba Ameerah yanzu saboda Allah se kije masa a haka ko ɗan powder baxaki shafa ba ,kuma ki sake hijabi dan wannan yayi tsufa da yawa" kamar xatayi kuka haka ta shiga ɗaki ta canzo hijab sedai powdern ne kawai bata shafawa turare ta ɗan fesa kaɗan kafin ta fito " kallon ta Aunty tayi tana girgiza kai " Allah dai ya kyauta miki Ameerah ke sam idan bakiyi niyyar abu ba to babu wanda ya isa ya saki kiyi "narai² tayi da ido kamar xatayi kuka" Kinga jeki ni karkimin kuka bawan Allah nacan kin shanya sa ,dan dai kawai so na so amma taya mutum ze jure duk irin wannan.

Meerah tana fitowa ta ga motarsa ,dan haka ta dawo daga cikin zauren gidan ta tura masa text cewar ya shigo daga ciki ,koma tayi gida ta dauko ta barma tazo ta shimfiɗa masa ,itama se ta zauna daga ƙarshen shimfiɗar zamanta babu wuya se gashi ya shigo hannun sa riƙe da na yarinyar sa zauna wa yayi yana faɗin " anya jan ajinnan beyimun yawa ba Hajia kinsan tsawon lokacin da kika barni a zaune ina jiranki ,ni har nayi tunanin ma baxaki fito ba ,da se dai kiganni cikin gidanku" kawar da zancen tayi da faɗin " ina wuni" lafiya lau yakike nace dai bara naxo tunda na fahimci ko shekara zanyi bankira ki ba to ke baxaki taɓa nemana ba " murmushi kawai tayi tana janyo yarinyar zuwa jikin ta kusan dai yadda Meerah take da son yara ,to hakan ce ma ta faru tsakanin ta da wannan" ya sunan ki? Kallon Muhsin yarinyar tayi ,ya gyaɗa mata kai " ki faɗa mata mana itace fa Auntyn ki ina kece kk ce zakizo kigaishe ta"

gaishe da Meerah tayi ,ta amsata tare da tambayar ina yayunta " Aunty Dadyn mu ne yace baze zo dasu wurin ki ba basajin magana" ayya dadynku be kyauta ba gaskiya idan kika koma kice nace suyi kuka harse yakawosu na gansu kinji? Dariya kawai Hanifa tayi haka tayita yiwa Meerah surutu ita kuma tana biye ta ,ganin haka Muhsin yace " yaudai nazama ɗan rakiya kenan ,naga anmanta dani ma a wurin se biyewa Hanifah kikeyi "dariya Meerah tayi tace " Allah kamar kabarmun ita Momyn ta zatabani? Taɓe baki yayi yace bansani ba sedai ko idan zaki tambayeta ,bara na kira miki ita se kiji daga bakinta "da sauri ta dakatar dashi " a'a Abban Hanifah ,to idan ta tambaya wace ce se na faɗa mata me? Au har an canja mun suna kenan ,aikam dai naji daɗin wnnan,karki damu ai tasan komai akan ki ,dan babu ɓoye ² a tsakanin mu tun ranar da na fara zuwa wurinki se da na sanar da ita ,kuma fatan Alkhairi kawai tayi mana ,Kinga yau ma cewa nayi ta shirya Hanifah zan zo da ita wurin ki, kuma ta shirya ta ɗin na faɗa miki mata ta bata da matsalar komai zakiji dadin zama da ita " taɓe baki Meerah tayi tace" nikam ai banda damuwa da hakan ,yanzu yaushe zaka kawo sauran yaran suma na gansu " uhmm to wani lokacin dai ,zasu zo su wunan miki ma " aikuwa da naji daɗi wlh " wai haka kike da son yara? Kinga kawai ki amince muyi auren mu da wuri Kinga next year i war haka kinsamu naki yaran maybe ma twins" rufe ido tayi tana dariya ,shima dariyar yayi ,dan ze iya cewa yaune rana ta farko da yake ganin dariyar ta irin haka har take bayyana haƙoranta , sedai ko yaushe tayi murmushi.

duk wani tunani da Yakamata Hajia saudah tayi na neman hanyar rusa auren tayi amma ta kasa samun solution , shiyasa damuwa tayi mata yawa duk da tasan tunda Hajia Laura tace xatayi wani abu akai to xatayin sedai tunanin ta me Hajiya Laura zatayi wanda zesa Alh yace ya janye maganar auren kamar yadda ta faɗa ,tunda wannan abun ya faru ta kauracewa Alh ,sam bata bari ma su haɗu ,gefe ɗaya kuma ga tunanin da takeyi akan Meerah ,ita da tazo Kaduna ta ɗan kwana biyu kafin ta koma ,Sega wannan matsalar ta taso mata yazama dole tayi tabar garin ko dan saboda Ameerah ma da take wani tunani akan yarinyar ,tana cikin wannan tunanin ne sega Binta ta kira wayarta ,ɗagawa tayi jin yanayin Muryar Binta ne yasakata faɗin " lafiya? Hajiya wlh Alh Tanko ne yazo jiya to be sameki ba rabon ayi se na tura ɗaya daga cikin yaran nan takai masa ruwa ,shikennan fa kamar wani tsohon maye ya hakewa yarinyar mutane ,kuma na faɗa masa cewar naki ne kar ya taɓata amma bakiga illar da yayi mata ba seda yaga ta dena mosti daƙyar doctor Ali ya ceto rayuwar ta amma shikansa seda yayi faɗa" dogon nunfashi Hajia Sauda ta sauke tace "wacce daga cikin yaran yar farar ko baƙar? Ehhh Hajia Bakar ce "to yanzu dai ta farfaɗo ko? Ehhh har ma nasamu tasha tea yar uwarta se kuka takeyi " karki damu Binta ,zan kirashi muyi magana ,yasan dole ze biya duk abinda nace ya biya tunda be nemi izini na ba ,ina fatan anyi recording komai? Ehhh komai yana nan Hajia
" To karki damu ,nima nan ɗin akwai yarinyar da nake harar mana duk da nasan bazan sha wahala ba dan na fahimci tanada son kudi ,ki kula da komai Binta ,kuma kitabbatar tana shan magani yadda ya kamata, abata kulawa ta Musamman dan nasan taji jiki ,ko wannan Tumbi na Alh Tanko kawai ai kayane ko ga mu manya bare ma wannan yar cikinsa ,ya gidan komai dai yana tafiya lafiya ko? Ehhh Hajia yawwa to ki kula sosai zan sake kiranki.

tana kashe wayar ta saki murmushi tuna irin kuɗin da zata samu a hannun Alh Tanko ,shigowar Rufee ne yasakata haɗe fuska
Tun kafin tayi magana tace " menene? Um.um Mama dama nazo ne na faɗa miki inaso zan fita ,akwai gidan ƙawata da zan tafi " to Rufaidah kinajin magana ta ne da zaki zo tambaya na ,ina ko cewa nayi bazakije ba ,zakijen tunda yanzu sam banda wani girma a idon ki ,ƙan kanuwa dake wai harkisan kizaɓi namiji akan uwarki " Haba Mama kidena faɗar hakan nifa bawai na zabeshi akanki bane Mama inaso kifahimci wani abu , keda Ammi matsayi daya kuke dashi a wurin Mu'aisam,amma saboda kilibibi irin nata ta kakance komai ,nasa sekace itace uwarsa ,nace ina son sane saboda na tarwatsa burinta ,dan nasan batada wani buri da ya wuce ganin Mu'aisam ya auri Rumaisa ,shiyasa nakeso muyi anfani da damar ,Kinga yanzu idan na auresa dole zan rabashi da ita ai kuma nasan zakiyi farinciki da hakan ,kinsani Mama ina kishin duk wanda be kaunarki ya kike tunanin wai saboda ra'ayin kaina zan aure shi ,duk wannan saboda ke ne " ganin irin kallon da Hajia saudah keyi mata ne yasakata yin shiru " ai bantaɓa sanin ke sakarya bace se yau ,anfaɗami ki ta wannan hanyar zan gurgurta Saudah to dalilin da yasa bazan bari ki auri Mu'aisam ba ni nabarwa kaina sani ,kuma kar kiyi tunanin mallakar sa ,dan wlh bazan bar hakan ta faru ba ,bakisan wanene shi ba baki kuma san abinda ke tsakanina dashi ,ba auren da zakiyi masa ne ze illlata rayuwata Rufaida,baze yiyu na zauna dashi a matsayin suruki ba ,dan Allah ki rarrashe xuciyarki , Rufaida ,ga yaron Hajia Sa'a wlh yafi Mu'aisam komai idan ma baki son shi ,to ki fitar da wanda kikeso mana amma dai ba Mu'aisam ba .

da kyau Rufaidah take kallon ta dan son yiwa kalamanta fashin baƙi shin mene ne to tsakanin ta da Mu'aisam bayan rashin son shi da ta san batayi? "Shikennan Mama ni zan tafi se na dawo " ganin kamar Rufee tafara karyowa ne se Hajia saudah tayi mata murmushin yaƙe tace " kidawo lafiya ,me za'a dafa Miki kafin kidawo? Ko jiyowa batayi ba tace " komai ma".....




Comments and share

Real Bazamfaria ce ❤️
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
( *On* *word* *together* )

*MABARACIYA*

*Story* *and* *writing*

*By*

*FIDDAUSI* *SANI*
(damsel feedorh)

🅿️:2️⃣5️⃣

Bayan kwana biyu
Mu'aisam yana zaune falo yana kallon labarai , sega Rufee ta shigo , cikin takunta irin na yanmata masu ji da kansu, banda tashin kanshi babu abunda jikinta keyi , kujerar da ke kallon tasa ta zauna , cikin muryarta me hade da yanga tace " barka da hutawa Yaya" ta gefen ido ya kalleta kafin ya amsata da " yawwa " duk da yanayin kwalliyarta ya burgeshi musamman kanshin jikinta Wanda tunda ta shigo falon ya sauya , shi mutum ne da yakeson mace me kwalliya da kamshi , kuma duk Rufee ta hada su sedai baya jin ze iya sonta kodan sabotada uwarta , ganin shirun yayi yawa se tace " am Yaya dama cewa nayi ko zaka kaini shopping idan baka komai
" Me ya samu motarki da bazaki fita ke daya ba? Ya tambayeta yana tsareta da ido " haba Yaya yanzu dan Inada mota shine bazaka kaini ba , naga a gidan nan duk wanda ze fita kaine kake kaishi , se nice bazaka kaini ba , wai Yaya me nayi maka kake min haka naga nida su Rumaisa duk dayane koma nace nafisu tunda ni yanzu akwai maganar aure a tsakanin mu me yarage nan da 2 weeks fa shikenan " cikeda kosawa da maganarta yace " wayanda kike ganin ina fita dasu basuda mota ne kekuma yar gata ce ina yaran gidan nan ke kadai ce kikeda mota , kuma kidena tunanin wai zakifi wasu gareni , dukan ku kannena ne babu wani abu bayan wannan "

Suna cikin maganar ne Rumaisa ta shigo da alama dawowar ta kenan daga school, ganin su zaune a falon se batayi kokarin zama ba tana gaishe da Mu'aisam tayi gaba abunta , seda ta shiga dakin ne ta tuna da tambayar da takeso tayiwa Rufee saboda haka ta fito , suna nan zaune kamar yadda ta barsu , sedai wannan karon Mu'aisam yana cewa Rufee " tajira idan anyi sallar la'sar se yakaita , murmushin samun nasara tayi har zatayi magana se kuma tayi shiru ganin Rumaisa tana nufosu

Kusa da ita taje ta zauna tace " nikam sis Rufee na manta kwana biyu na dena ganin Ameerah a gidan nan Allah dai yasa kafiya " ya mutsa fuska tayi tace " waye kuma haka?".

"wata yarinya da takeyi miki aiki ,kamar dai bata daɗe da fara aiki a gidan nan ba ai tanada kirki wlh ,nima ban kula da rashin ganinta ba se jiya ne naga auta tana da kumburi da na tambayeta menene shine tace wai taje part din Mama neman Auntyn ta amma bata ganta ba ,to yau da safe ma ta shiga wai bata ganta ba ,kinsan Auta tuni ta maƙale Aunty Meerah dai "haɗe fuska Rufee tayi taja dogon tsaki,dukansu kallon ta sukayi dan basu san dalilin tsakin ba ,ganin irin kallon da Mu'aisam keyi mata ne yasaka ta wayancewa da faɗin " kedai Rumaisa akwai ki da shirme ,duk akan *Mabaraciya* kike wannan rattafen ,ina zan san inda take ,wataƙil ko sun gama magana da Mama ne dan kamar naji tace wai da ita zata koma ,tunda Kinga m zamana takeyi kuma yanzu aure zanyi so babu kowa a gidan dan haka zata tafi da ita,nifa banma yarda da yarinyar ba " da sauri Mu'aisam ya kalleta har

Please Login or Register in order to submit comment