Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tunanin,daukar abincin gidan nan kitafi dashi koda kuwa an rage ne ,idan kika kiyaye wanan shikenan kuskure musu kuwa ,hmmm takarashe tana lumshe ido ,cikeda rashin damuwa Meerah tace " indai zaki kiyaye biyana hakkina ai wanan ba matsala bane ,jin amsarta yasaka Rufee dagowa ta dubeta ,sosai take mamakin jinkai irin na yarinyar ,kiran Larai wacce ke mata aiki tayi ,cikeda ladabi tace " Hajia gani ,kallon mamaki Meerah tabi Larai da shi ,idan aure kauye tayi kusan tahaifi Rufaida,amma gashi tana kankantar da kanta gareta " Rabbi ka kara rufa mana asiri tafada cikin xuciyarta " ki nuna mata dakina ta gyara komai kafin nazo ,tun kafin Larai tayi magana Meerah ta tashi binta tayi ,seda suka fara taka steeps tukuna ta juyo cikin sa'a kuwa sukayi ido biyu da Fatima ,kashe mata ido tayi tare da jinjina mata hannu alamar godiya , murmushi kawai Fatima tayi mata ,daga haka ta dawo kan Rufaida

" Nikam Rufee wai yanzu wane irin horo kike tunanin zakiyiwa yarinyar nan ,saboda da alama tanada jin kai "hararar ta Rufee tayi tace, malama ina da zan dauki matakin kece kika hana " haba taya zan hana baki fahimceni ba kenan ,kinsan dalilin da yasa na sanyayar mata da jiki saboda kar ta tafi? Bata jira amsar Rufee ba tacigaba da magana "to saboda nayi miki alkawarin se kin wulakanta ta kamar dai yanda kikayi alwashi kuma kema nasan kinason haka ,matsalar da aka samu ,saurin fushi dakikayi da wannan nayi anfani na tabbata komai zakiyi mata bazata bar gidannan ba saboda tana kaunar iyayenta kuma tana tausayinsu ,idan tabar gidan nan shikenan duk wani Hop nasu ya lalace,kinga dole zatayi hakuri ko badan saboda itaba ,domin iyayenta

Lumshe ido kawai Rufee tayi "amma yanayin da take magana ne idan kin kula kamar ba na sauran yayan talakawa ba,ni se nake ganin kamar tanada jin kai " karki damu da wannan ,haka wasu yayan talakawa suke idan kika ga suna daukar kai seki zata sudin wasu ne ,ajiyar zuciya Rufaida ta sauke tace " shikenan Teeamah na gode bari na koma bacci nakeji ,kallon mamaki tabita da shi kamar ba daga baccin ta taso ba ,amma a zahiri murmushi tayi tare da fadin " shikenan nima bara na wuce Mamana tana jirana ,dan ya mutsa fuska Rufaida tayi kamar bataji dadin furucin Teema ba bata dai ce komai ba ta tashi sukayi sallama.


Cikin ƙanƙanin lokaci Meerah ta gayara duka rooms ɗin ,bakin wani da yake a rufe ta dawo ,tsaye tayi tana ƙare wa ɗakin kallo cikin zuciyarta take ayyana cewar shine ɗakin Hajia Saudah ,ɗan zagayawa tayi inda taga window,sedai a rufe windown take ,motsin da tajine kamar ana taka steps yasakata barin wurin da sauri ,kallon tuhuma Rufee tabita dashi ƙasa tayi da kanta tace " na kammala ,tsaki kawai tayi mata ta taɓa ta tayi shigewarta ,da kallo Meerah tabita ,tana nemamata shiriya ga Allah,dan Allah yayi ka mai kuɗi bayana nufin kafi kowa bane .

Rufaida na shiga ɗakinta taji wani sanyi da ƙanshi ya bugeta babu shiri tafaɗa kan gado tana lumshe ido a zuciyarta mamaki take ya'akayi wannan villager ta iya gyaran ɗaki har haka gashi bata wani ɓata lokaci ba tayi mata aikin da ko Larai da take babba bazata iya irinshi ba ,taɓa baki tayi tace " ko da yake dagani tasaba aikatau .

Meerah kam tana saukowa ,ta samu wuri a falon ta zauna ganin shiru shiru bata fitoba yasakata sha'awar zuwa haraban gidan ,tana tafe tana ƙare wa gidan kallo ,batayi aune ba taji tayi karo da mutum,cikeda tsoro ta ɗago don gudun kar kowaye yayi mata rashin mutumci tunda ta kula kamar halayyar ƴan gidan ne "ke? taji yafaɗa yana nuna ta ,itama zare ido tayi saboda ta ganeshi mutumin nan ne da tataɓa yaɗuwa dashi kasuwa " me kikeyi a gidanmu ? Tambayar da yayi mata kenan,murguɗa masa baki tayi zata taɓa shi ta wuce ,fixgota yayi yace " bakiji me nace ba ? Cike da jin haushi tace " aikatau ,shiru yayi yana kallonta ,bece komaiba ya saketa ,raɓashi tayi ta wuce fasa zuwa balcony ɗin tayi tadawo falon ta zauna da kallo yabita ,tabbas yasaka wasi-wasi akan yarinyar ,da fari tazo gidan amatsayin Mabaraciya ahaka yaganta ,se kuma ya ganta a hanya a matsayin cikakkiyar me gata ,a yau kuma ta dawo gidansu amatsayin ƴar aiki,anya kuwa yarinyar nan Mabaraciya ce kodai anturo ta ne leƙen asiri" i will find it out ,yafaɗa yana shiga falon shima

a falon ya ganta raɓe gefen kujera ,bece da ita komai ba ,Larai da yaga tafito ya kalla yace " ke kiramin Rufaida , kusan a tare suka sauko itada Rufaida ,tunda ta hangoshi ta washe baki,cikeda jin daɗin ganinsa tace " Welcome MM ,shima Murmushi ya mayar mata yace " tnz ,haka kike zaune a ɗaki ke kaɗai instead of ko ƴan aikinnan kizauna kuyi hira ai sa ragemiki kaɗaici ko? Wane irin kallo tabi Meerah da sam tanuna hankalin ta baya kansu " yanzu Yaya saboda banda hankali se na zauna cikin ƴan aikin da sukecin abinci a ƙarƙashina na sakasu aikin da duk na gadama ,kuma zan iya marinsu idan suka kuskurewa umurni na ,amma duk da haka kake cewa wai nayi hira dasu? God forbid,never dead my body ,girgiza kai kawai Mu'aiseen yayi cikin zuciyarshi yake faɗar " yuh won't ever change ,a zahiri kuma tashi yayi tsaye yace " to ni zantafi dama fita zanyi nace bara na leƙoƙi tunda ke kinfi ƙarfin zuwa inda mutane suke "afuwan yaya ,harzaka tafi ko lemu bakasha ba ,laluba cikinsa yayi yace " don't worry am ok " ok to mutafi na rakaka,haka suka jero suna tafe suna hira ,itadai Meerah mamaki yakasheta ashe dama tana dariya lallai tafaɗa tana ci gaba da kallon tv,tana nan har Rufee tazo ta wuce ta,kallon agogon falon tayi taga har lokacin sallah yayi,inda taga Larai ta shiga tun ɗazu nan tabi Sega ta cikin kithen,sannu da aiki tayiwa Larai kafin ta tambayeta inda zata samu ruwan alolah,da sakin fuska Larai ta nuna mata wani coridor tace " akwai bayima acan idan zaki zagaya,Murmushi itama tayi tace " Nagode tare da bin hanyar seda tashiga toilet tayi fitsari tukuna tayi alwala ,a ɗan gefen wurin ta shinfiɗa kallabinta ta tayarda Sallah,tana idarwa ta dawo ciki zaman jiran tsammani ,ganin har kusan ƙarfe 4 Rufaida bata sauko ba ga kuma yunwa da takeji se kawai ta yanke shawar tafiya gida tunda dai ta kammala ayyukan ta to bataga dalilin zamanta ba kuma,wurin Larai taje tayi mata sallama ,kafin ta fito ta kama hanya ,koda ta shiga gida ana kiraye-kirayen sallar la'asar,a matuƙar gajiye tashiga gidan Aunty da ke zaune tana jiran dawo warta ta tareta da sauri tanayi mata sannu Ruwa tafara kawo mata girgiza kai tayi tace " Aunty ai se cikina ya ƙulle me kika dafa mana yau? Narasa me zan dafa shine kawai na yimana ɗan wake ,washe baki Meerah tayi tace," kin kyau ta min kamar kinsan nayi marmarin sa bani naci cikina har kukan yunwa yakeyi ,tashi aunty tayi ta kawo mata ɗan waken aikuwa ta hau ci kamar Mayun waciya ,seda tazo ƙarshe Aunty tace " gaskiya Ameerah ki canja wata shawarar dan bazaki sake komawa aikin nan ba ,a firgice ta saki sauran ɗan waken da yake hannunta tace " haba Aunty kenan duk wahalata tatafi a banza kenan seda nafarajin ƙanshin nasara shine zakice na dena ,koda a ce Rufaida zata riƙa yanka nama na ne zan jure matuƙar zan haɗu da muguwar matar nan Hajia Saudah.......















#Real@Bazamfaria
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
( *On* *word* *together* )

*MABARACIYA*

*Story* *and* *writing*

*By*

*FIDDAUSI* *SANI*
(damsel feedorh)

🅿️:1️⃣2️⃣

dafa kafaɗarta Aunty tayi cikin sanyin murya tace "Meerah bawai ina so na hanaki ɗaukar fansan abinda akayi Miki bane ,saboda addini ma yabamu wannan damar idan har aka cuceka kuma kaga bazaka iya yafewa ba to ka rama daidai da yadda akayi maka ,sedai kituna irin tanadin da Allah yayiwa masu yafiya musamman a inda sukeda halin ramawa, Meerah inajin tsoron faruwar wani abu gareki Hajia saudah da kike gani ba ƙaramar mace ba kuma mijinta ma babban mutum ne na tabbata koda za'a kamata da lefin fasa kauri da yara mata tofa babu wani hukunci da zata fuskanta ,domin su sukeda doka , Allah ne kawai xe iya hukunta su bawai dan'adam ba musamman ke mace karama me rauni ,karkiyi wasa da rayuwar ki bamuda kowa se Allah.

Shiru Meerah tayi tana sauraren Aunty har seda tayi shiru ,alamun ta gama maganarta,murmushi tayi harseda fararen haƙoranta suka bayyana ,cikin salon maganarta tace " Aunty naji daɗi da kika ce Allah ne ce iya hukunta ,ki fahimceni bawai inason yaƙar ta bane ko kuma burin fansa ne kawai a gabana ba , a'a inaso ne na nuɓutar da sauran yaran da take ƙoƙarin halakarwa na kuma bayyanar da ɓoyayyiyar fuskanta wacce take cin amanar addini ,mutane da yawa suna yabonta akan kirkin ta har takan ɗauke wasu daga cikin yaran marasa ƙarfi da sunan zata tallafi rayuwar su wanda babu wanda yasan me take sakasu sunayi ,kasuwanci takeyi dasu

Saboda haka temako ɗaya nikeso kiyimin Aunty shine kitayani da addu'a Allah yabani ikon cin nasara akanta"

tana gama faɗar haka bata jira cewar Aunty ba ,tayi shigewar ta ɗaki, girgiza kai kawai tayi saboda tasan halin Meerah da naci akan bu tunda har tayi niyya to babu wanda ya isa ya dakar da ita.

Washe gari tunda tayi Sallahr asuba bata koma bacci ba dan haka tafita tayi share² sannan tayi wanke² seda ta gama tukuna ta shiga wanka ,bata ɓata lokaci ba saboda saurin da takeyi kar ta haɗu da rashin mutuncin Rufaidah ,yau kam doguwar rigar atamfa ta saka babu lefi da ɗan haske ta duk da ta koɗe amma tafi kayan jiya haske ,ko mai bata shafawa jikinta ba ta ɗauki hijabinta tsoho shima ta saka ,a bakin ƙofa ta haɗu da aunty tana shirin shigowa ɗakin ,ɗan matsawa tayi daga gefe tana murmushi ta gaisheta " bade har zaki tafi ba gashi na makara daga na gishingiɗa bacci ya ɗaukeni" murmushi ta sake yi tace " karki damu Aunty ,ai dama za'a riƙa bani abinci a can yanzu idan nace na tsaya zanbata lokaci ,ga yarinyar batada kirki"to shikenan kide kula dan Allah ,kikama mutuncin ki kuma Allah ya kiyaye se kin dawo "Insha'Allah Aunty Nagode" daga haka ta fita gidan , cikin natsuwa take tafiyar ta kamar yadda ta saba seda tayi nisa sosai kafin ta samu a caɓa ,ka san cewar safiyace sosai,unguwar da xe kaita ta faɗa masa ,babu ɓata lokaci tahau suka tafi.

Koda ta kai sa sashen su Rufaidah a rufe yake alamar bata tashi ba kenan ,tasan ko tayi knocking ba ji xatayi ba saboda haka ta samu wuri daga gefe ta zauna ,takai kusan 30 minutes,kafin taji maganar Larai a kanta ,ɗagowa tayi tana kallonta " Fatima me kikeyi anan baki shiga kin fara aikinki ba?"instead ta amsa mata se tayi murmushi tare da gaisheta, amsawa tayi tana sake maimaita tambayar " wlh Aunty Nazo naga kofar a rufe shine na tsaya nan kafin a buɗe"

Kama hannunta Larai tayi tace " to ai tanan baya zaki shigo ,mutafi kina ɓata lokaci ,bakisan halin me gidan bane"Meerah batace komai ba tabi Larai suka shiga ,tsaye tayi tana tunanin inda zata fara gyarawa ,can dai tayanke shawarar fara gyaran falo kafin fitinanniyar can ta tashi ,se ta shiga ta gyara mata ,sunan da ta sakawa Rufee kenan.

Seda ta tabbatar da ta gyara ko ina a downstairs,tukuna ta kai dubanta ga agogon da ke manne a bangon falon karfe 8:30 ya nuna mata ,a fili ta furta " ko ma tayi sallah? sedai tunanin batada me amsa matane ya sakata nufar kitchen wurin Larai " sannu da aiki Aunty" murnushi Larai tayi mata " harkin kammala gyaran kenan " ehhh iya kasanne da ɗakunan da ke ciki ,ina tsoron na haura sama ne bansani ba ko bata tashi bacci ba" cab!ai se 10 zata tashi " taɓe baki Meerah tayi tace " to bara na tayaki aiki kafin ta tashi" a'a wlh da kin barshi ai ma na kusa kammalawa,kunun gyaɗarnan ne kawai yayi saura "ehhh ai ko wanke² ne se nayi Miki ,naga kinyi abincin kashi²,hala duka gidan ke kike musu a binci? " Hmmm ko ɗaya Meerah kinsan musu kuɗin nan sam basu san tattali ba duk wannan da kikaga nayi na Hajia Rufaidah ne ,yanzu ma idan ta gadama zata iya cewa duk babu abinda yayi mata ,sedai na canja wani" cike da mamaki Meerah ta kalli Larai tace " kuma se kin sake ɗin? "to yarnan zamanta nikeyi a gidan nan fa dole na canja idan tace beyi mata ba" can!amma wallahi....bata karasa ba sakamakon tsawar da sukayi from no where,cikeda rashin mutunci Rufaidah tace...

"Larai badai abincin da zanci bane kika bari wannan me suffar aljanu ta taɓa?" A'a ranki ya daɗe yanzun nan ta shigo ma har na kammala komai" itadai Ameerah tsaye tayi tana binsu da ido musamman Larai da jikinta har shecking yake tsabar tsoron Rufaidah,wani dogon tsaki taja tana maida idonta kan Meerah a wulaƙance tace " shishigin ki babu abinda ze ƙara Miki se tsana a xuciyata,idan ma ba kinraina ni bane har yaushe zakizo baki jira na tashi bacci kin gyara min ɗaki ba ,kishigo nan kina abinda ba'a saka ki ba ,ok nasan saboda kwaɗayi kikayi wannan ko wato agama ki kwasa kikaiwa cima kwance iyayenki ko,su sun zauna sun turoki aikatau wayasani ma ko da shegen kyan nan naki zasuyi anfani kun zata ko akwai maza a gidan nan ,to ahir ɗinku ko munada maza sunfi ƙarfin matsiyata irinku"ta ƙarashe tare da kafe Meerah da ido dan ganin duk wannan maganar da ta faɗa mata murmushi ne kwance a fuskanta kamar ma bata fahimci zagin da takeyi mata ba ,ganin tayi shiru ne Meerah ta raɓa zata wuce ta batare da ta furta komai ba , da sauri Rufee ta fizgota ta dawo baya

" Who dere you ina magana zaki wuce ,wato kam ga Mahaukaciya ko?nan ma shiru Meerah tayi tana kallon ta kamar bazatayi magana ba se kuma tace " Ai bansan amsar abinda kika faɗa kike nema ba shi yasa nayi shiru ,amma tunda har kin buƙaci haka inaso kisani ,duk yadda iyaye suke sunan su iyaye, Bara na tambayeki menene ma'anar iyaye? nasan baki sani ba saboda bakisan daɗin su ba ,abinda kika sani kawai ,kinada buƙata abaki kuɗi kiyi ,anfaɗa Miki komai ne kuɗi keyi akwai farin cikin da kuɗi bazasu baki ba ,amma kulawar iyayenki kawai ya wadatar dashi ,kamar yadda kika ce iyayena matsiyata ne to ina so ki gyara kalaminki ,domin mu arziƙin imani kawai da Allah yayi musu ya ishemu alfahari ,kyau da kike magana kuma ,naji daɗi tunda duk rashin sonki gareni ,idonki be rufe ba har seda ya tabbatar miki da Ni ɗin me kyau ce ,Kinga akwai yiyuwar idan gidan da Nazo babu maza to matan ciki su taya ko? Cikin zafin rai Rufee ta ɗaga hannu zata mari Meerah da sauri ta kauce ,tana dariya ta fita daga kitchen ɗin

Ba Larai da tayi mutuwar tsaye ba hatta Rufee ta kasa motsi ,babban baƙin cikinta a gaban Larai Meerah tayi mata wannan iskancin , lalai dole ne ta ɗauki mataki akan ta ,amma zata fara kiran Fatima ta sheda mata kafin suyi shawarar irin tozarcin da zasuyi mata ,dan tayi alƙawarin se tayi nadamar zuwanta duniya.

Meerah kam xuciyarta wasai taketa gyaran ɗakin duk da wani ɓangare na xuciyarta na cikeda tsoron kar Rufee ta koreta, tun kafin ta fara abun da ya kawota ,gashi ma ko maganar Hajia saudah bataji anayi ba bare ta saka ran ganinta ,haka dai ta samu ta kammala komai har toilet ta wanke mata se kanshi ke tashi a ɗakin ta janyo mata ƙofa ta rufe ,har zata sauka se takai dubanta ga ɗayar ƙofar dake rufe ,tanason ta shiga ɗakin duk da zuciyarta na faɗa mata cewar ɗakin Hajia saudah ne ,jin kamar za'a hauro sama ya sakata saukowa da sauri ,sedai a mamakinta Rufee bata falon.

More comments more typing

Idan har comments ɗin ku ya burgeni to zakuci gaba da samun Mabaraciya ko yaushe Insha'Allah

Vote and follow me Dan Allah

Real Bazamfaria❤️
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
( *On* *word* *together* )

*MABARACIYA*

*Story* *and* *writing*

*By*

*FIDDAUSI* *SANI*
(damsel feedorh)

🅿️:1️⃣3️⃣


Fitowa tayi waje dan tsoron ta zauna falon kuma tayi lefi ,wurin wasu flowers ta samu ta zauna ,tunanin halayyar Rufee kawai takeyi ,wai dama haka wasu masu kuɗi ke rayuwa sam basu ɗauki talaka a bakin komai ba ,to me ke sa suna haka gata ko rashin tarbiyya? Kai gaskiya dai rashin tarbiyya ne meyasa mu lokacin ko masu yi mana aiki Ammi bata yiwa tsawa bare har mu muyi musu ,koda haline kowa da irin nasa"tayi nisa sosai a duniyar tunani har batasan da tsayuwar mutum akan ta ba,Mu'aiseen da tun da ta zauna yake wurin yake kallonta ganin kamar tayi nisa a tunani shine ya ƙaraso ,amma duk da haka bata san da tsuyuwarsa,ƙura mata ido yayi yana nazarin ta,be san me yasa zuciyarsa ke zargin yarinyar ba sam be yarda da ita ba ,gyaran murya yayi ,da sauri ta ɗago kanta ta dubeshi ,a jiyar zuciya ta sauke kuma se ta haɗe fuska ta raɓashi zata koma ciki "me kike tunani haka har Nazo baki sani ba? "Batare da ta waigo ba tace masa " Babu kawai taci gaba da tafiyarta,shima tafiyarsa yayi dama fita zeyi se ya hango ya ta fito shine yazo wurin


ɗakin Larai ta tafi ,dan bata so ta sake haɗuwa da Rufee har ta bar gidan ,a zaune ta sameta tana ninkin kaya da alama daga shanya ta kwaso su ,ganin yadda Larai ke binta da ido ne yasa tayi murmushi,tana yiwa kanta mazauni tare da faɗin " Aunty har kingama aikin kema? Ganin Larai batace komai bane yasaka ta faɗin " lafiya dai? Ajiyar zuciya ta sauke tace " Kinkuwa san ganganci da kika yiwa kanki bana tunanin zaki ci gaba da aiki gidan nan ,dan wlh kinci Sa'a Hajia bata nan da se ta saka an wulaƙantaki tukuna ta koreki ,saboda tana matuƙar son Hajia Rufaidah,Sam batason ɓacin ranta amma naga kin dage kina mayar mata da magana yau ba ke ba harni nasan se ɓacin rai ya shefeni dan a fusace tafita gidan nan " ayya Aunty to miye lefina itace fa ta buƙaci na bata amsa ,shine ni kuma ba bata " cab! amma dai bakisan wacece ita ba ko? gyara zama Meerah tayi cike da rashin damuwa tace " yawwa faɗa min ko ita ɗin wacece Kinga se na kiyaye gaba"

Rufaidah da kike gani su biyu ne a wurin Hajia saudah yayarta tayi aure shekara biyu kenan da suka wuce ,kaf a duniyar nan bana tunanin akwai abinda Hajia saudah keso fiye da Rufaidah, duk kuɗin da kikejin ana faɗar me gidan nan yana dasu to Hajia ta fishi saboda ita ɗin irin matan nan ne da basu dogara da dukiyar miji ba sosai take neman nata gashi tana te mako sosai shiyasa takeda jama'a don kuwa idan taxo garin nan zakiga ko yaushe gidan cike da jama'a sedai tanada isa ita ma kamar yadda kika ga Rufaidah banbanci shine ita bata wulaƙanta talaka amma kuma a gabanta Rufee xatayi wulaƙancin bata cewa komai bansani ba ko saboda son da takeyi mata ne

Da ido kawai Meerah take bin Larai ganin yadda take yabon kirkin Sauda , murmushi tayi tace " Allah sarki kice ita tana da kirki ni har najima da tana nan kila da zamu ɗan fi samun alkhairi ko" sosai kuwa gaskiya tana da Alkhairi base kuɗin aikin ka take baka ba kuma idan zata koma haka zata baka kuɗi da yawa tace kayi mata addu'a" cike da jin daɗin labarin Larai Meerah tace " to wai ita wane irin business takeyi haka?shiru Larai tayi kamar me tunani zuwa can tace "to gaskiya dai ban sani ba ,amma dai ko wane irin business ne nasan babbane kam shiyasa bata iya zama anan ,mijinta yayi har ya gaji mafi yawancin lokaci ma idan Kinga tazo to tana neman masu tayata raba kayanne dan tana ƙorafin ma'aikata sunyi mata kaɗan ,saboda hidimar raba kaya wai idan sun iso ,shiyasa ma kike ganin bata aje masu aiki anan da yawa da tazo taga me aiki se tace zata tafi da ita can wai acan tafi bukatar su ,saboda jigila"kiran da Rufaidah ta ƙwallowa Larai ne yasakata tashi da sauri dan amsa kiran.ajiyar zuciya Meerah ta sauke "kenan idan ina zama da Larai zan ƙara fahimtar wasu abubuwan ,lalai Hajia saudah ta cika shu'umar mace ,wato ta killace ta ta yar a gida tana kai ƴaƴan wasu.......

Akwana a tashi babu wuya ,yau ga shi Meerah ta kai tsawon sati biyu da fara aiki a ƙarƙashin Rufaidah,babu abinda yake bata mamaki kamar ganin yadda Rufee ta fita harkarta ,sam bata shiga sha'anin ta ,duk da hakan yayi mata daɗi ,amma kuma wani ɓangare na xuciyarta yanaso ko da rashin mutuncin ne yariƙa shiga tsakanin su ,domin tana kallon illa da yawa a rayuwar Rufaidah ,ace teenager like Rufaidah amma Sam bata damu da ibada ba ,koda harda rashin zuwa makaranta da kuma hulɗa da batayi da jama'a,dan ko a ɗan zuwan da takeyi ta fahimci cewar ,rayuwar kaɗai ci Rufaidah keyi dan bata taɓa shiga sashen su Mu'aiseen ba ,haka idan ba shine yazo nan sashen su to babu wanda yataɓa zuwa daga can sashen.

tana cikin wannan tunanin ne xuciyarta ta kwaɗaitar da ita son shiga bangaren su Haisam ,san ko tunda take zuwa gidan ,iya kacinta shiga sabgar aikinta babu ruwan ta da kowa ,ɗakin Larai ta leƙa se ta sameta kan dadduma da alama bata idar da addu'a ba ,saboda haka kawai ta nufi sashen su Mu'aiseen kanta tsaye batare da tunanin komai ba

Tun daga nesa take jiyo hayaniyar mutanen gidan ,lokacin da ta karasa bakin kofar da ze sadata da main falon su ,se taja ta tsaya tanabin takalman da ke zube a kofar ,se hayaniya suke da alama musu sukeyi akan wani abun ,ɗaya bayan ɗaya takebin takalmin da ido kamar me son gano wani abu ,ganin idan ma ta shiga batasan abinda zata ce dasu ba ,se kawo ta jiyo ta fito ɓangaren.

Sedai abinda Meerah bata sani ba shine tun shigowar ta Mu'aiseen ya ganta ,tsaye yayi yana tunanin yarinyar ,tabbas yana zarginta sam bai yarda da itaba, zuciyar sa na bashi cewar wasu suka turota gidansu ,dan su cutar dasu ,idan ko hakane yazama dole yasaka ido sosai a kanta kuma zejawa Rufaidah kunne ,duk da yasan ba kula masu aiki takeyi ba ,xeyi bincike sosai akanta.

Seda taje tayiwa Larai sallama ,kafin ta wuce gida.

Niger state

Hajiya Sauda ce zaune a tsakiyar aminan ta ,magana sukeyi amma sam baka jin me suke faɗa da alama suna tattaunawa ne akan abinda ya shafe rayuwar su wanda basa so kowa yaji ,sun daɗe a haka kafin kira ya shigo a wayar ɗaya daga cikin su ,kallon juna sukayi ,se ta saki muemushi tace "Alh Tanko ne kisan sa sarkin naci tunda yaga hoton wata baby a wayana shikennan ya ɗaga hankalinsa kuma na faɗa masa cewar tawa ce bazan bashi ba amma ya dage ,akan ze bani ko nawa ne wai yarinyar irin wacce yakeso ne"ta karashe faɗa tana yamutsa fuska " haba ke ko Hajia mene ne idan har ze bada abinda kikeso aikawai kibar masa ,ga matan nan da yawa kuma kwanan nan Hajia saudah zata yi tafiya na tabbata zata samo mana wasu hot babies kinsan dai Hajia bata tafiyar banza" dukan su kallon Hajia saudah sukayi,cikin son tabbatar da Abinda Hajia Laura ta faɗa ,gyaɗa musu kai tayi cikin tabbatar wa tace " kema kinsan hana wa Alh Tanko yarinyar ze iya janyo mana matsala ,sune masu ɗaure mana gindi da yanzu zaman Niger yafi karfin mu kuna

Please Login or Register in order to submit comment