Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

_BY_
////////////////////////////////////////////////////
*FIDDAUSI SANI* ( _Damsel Feedorh_ )
///////////////////////////////////////////////////

🅿3️⃣4️⃣


Ana shafa fatiha Dady ya ɗaga waya ya kira Ammi tana ɗagawa yace " Alhamdulillah an ɗaura aure se muyi fatan Allah ya sanya Alkhairi ya kuma sa hakan shine Alkhairi a garesu " cikin mutuwar jiki tace Ameen amma Alh ya maganar ita Rufaida ina fatan dai harda ita aka ɗaura" Kinga Hajia zamuyi wannan maganar daga baya ,dama ita ce ta sameni da kukan ta akan na aura mata shi batare da naji ra'ayin sa ba ba zartar da hukunci yanzu kuma a gaban kowa tace bata son sa saboda haka magana ta ƙare yanzu dai ya jikin Rumaisa ɗin fatan dai da sauƙi dan yau ɗin nan zata tafi ɗakin ta "dogon nunfashi Ammi taja tace " tana nan dai yadda kabarta Alh ,amma doctor ya sake rubuta wasu drugs na aika driver ya siyo mata insha'Allah zata samu sauki kafin anjima ni kaina nafiso akaita gidan ta a yau dinnan kamar ko wace mace "

"Ammi ,Ammi " Amrah keta faman kira tana ratsa mutanen da ke cike da gidan kamar wata gigitacciya ,Ammi da ke faman waya ta jiyo wannan kiran da sauri ta fito dan a tunanin ta wani abunne ya faru da Rumaisa ,karo sukayi da juna ,a rikice Amrah tace " Ammi wai an ɗaura auren Rumaisa? to waye mijin ko shine dalilin wannan ciwon nata nan take? Kama hannun ta Ammi tayi suka shiga daga ciki ,zaunar da ita tayi tace " ki natsu ki kuma fahimta Amrah kisani Allah ya kadddara auren ta a yau ɗin nan kuma babu wanda ya isa ya canja ,ina so ki bata karfin gwiwa ,kece kawa mafi kusanci ga Rumaisa " amma Ammi Rumaisa bata taɓa faɗamin cewar tana da wani saurayi da har sukayi maganar aure da shi ba " Rumaisa ta fansarwa Yayanku mata ne ,kinsan dai Ameerah ko yarinyar da ke aiki ɓangaren Hajia Sauda idan baki manta ba munje gidanku da ita ,ita ce yarinyar da Yayanku ya daɗe yana so kuma babu wanda yasan hakan se ni tun tana ƙaramar ta yake fadin bayada wata mata se ita,na ɗauki abun wasa bansan yana son ta ba se a lokacin da ya nemeta ya rasa ,ya shiga damuwa sosai ,haka nasamu da addu'a da komai Allah ya cire ta a ransa , bayan tsawon lokaci se gashi yazo min da labarin wai yaga Meeran sa ,na ɗauka kawai shirmen sa ne ,da ga nan yaci gaba da bibiyarta har zuwanta gidan nan aiki sedai ni din bansan cewar ita bace se daga baya ,a wannan gaɓar kuma kawunki ya kawo zancen haɗasa da Rumaisa ,yaso yayi bore amma na dakatar dashi tare da nuna masa cewar Meerah har yanzu yarinya ce ya auri Rufaida a yanzu zuwa gaba ni xan goya masa baya akan auren Meerah , kwatsam ya samu labarin zatayi aure shine ya ɗaga hankalin sa har yana kwanciya dan haka banyi sanya ba na tafi can gidan su Meerah na samu Auntyn ta nayi mata bayani a bunda na fahimta ita kanta Auntyn kamar taso ace Mu'aiseen ne ya samu auren Meerah sadai babu yadda za'ayi suce bazasu baiwa shi Muhsin ba ,dukda wai ta fahimci dangin sa kamar basuyi murna da zaɓinsa ba kasancewar su talakawa , na nemi haɗuwa da Yayan Meerah wanda shine ya bada auren ta ,sedai ta nunamin shi mutum ne tsayayye baze taɓa canja magana ba dan haka na nemi sanin waye wanda aka baiwa auren ,har gidansu ta faɗa min da wurin aikin sa , da farko gidansu naso na tafi ,amma se nayi tunanin ba lalae bane iyayen sa su amince ,dan haka kai tsaye na wuce bank nasu ,bansamu matsala wurin ganin sa da seda ma amso numbern sa kafin na tafi ,na same shi na kuma roƙesa akan ya temakeni zan rasa yarona ,amma se ya nunamin cewar shi ma yana son ta hasalima tafiya ce a gabansa nan da wani lokaci ,kuma bazeyi yu yayi tafiyar babu iyali ba dan matar sa tace bazata bisa ba ,ganin na zube a gabansa ina kuka ,se jikinsa yayi sanyi ,yafara bani hakuri tare da amincewa buƙata na ,shi ya ɗauke ni har wurin Babansa ,nayi masa bayani shima ya amince sadai yace yarigada yagama gayyatar jama'a zuwa ɗaurin auren gaskiya baze iya cewa anfasa ba kuma rashin auren Meerah ze iya dakatar da shi Muhsin daga tafiya aikin da zeyi a waje dan shi be yarda magidanci kamar Muhsin yafati cikin turawa babu iyali ba ,bawai saboda be yarda dashi bane sedai yana gudun sheɗanun matan turawa ,ganin wannan dalilin ze kawo min cikas se na nace idan har ya amince zan bashi auren ƴata ,shi dai yace a'a ya haƙura dama beda burin ƙarin aure se akan Meerah tunda ya rasa ya haƙura ,amma se baban sa yace to lallai idan haka ne sadai na basu ƴar tawa don sun san Alh mutumin kirki ne kuma suna jin yadda mutanen gari ke yabon sa da haka dai suka amshi auren Rumaisa kinyi yadda akayi yanzu haka ita da shi basu taɓa ganin junan su ba


Amrah bawai na yi fafutukar nan kawai saboda Yayanku ya samu wacce yake so bane wlh kinji na rantse miki kaso 70 saboda rayuwar yarinyar ne ina tausayin ta ina kuma ƙaunar ta har cikin raina ,ina da tabbacin zata samu farin ciki a wurin mu ne musamman da Aunty ta sanar dani cin fuskan da dangin Muhsin sukayi musu ,ga yanada mata ,tayi karama da zaman kishi ,burin Rumaisa rayuwar yarinyar ta inganta ta samu ilmi kamar kowa ,nima shine nawa ,saboda haka ina so ki rarrashi Rumaisa ta kwantar da hankalin ta da Allah ,kar ki ƙara mata damuwa "

"Haba Ammi gaskiya bakiyiwa Rumaisa a dalci ba yanzu fa kika gama lissafa irin ƙalubalen da ke tattare da auren shi Muhsin ɗin ,ita Rumaisa zata iya zaman kishi ne ? Kuma bakiyi tunanin ya zasu amshe ta ba hala ma zasufi amsar ita Meerah ɗin akan ta saboda ko babu komai ita ɗan uwansu ya gani ya kuma ce yana so ,kuma shima yana sonta baze bari su wulaƙanta ta ba " Amrah , Rumaisa tafi Meerah shekaru ilmi da wayewar kai ,saboda ita tayi karatu kuma ta tashi a gidan nan taga irin zaman kishin da akeyi ,duk da bana fatan kishiyarta ta kasance irin Sauda amma dai ina faɗa miki duk mugun halinta to fa Rumaisa zata iya zama da ita ,kuna dangin sa matsalar su kuɗine ina da tabbacin sunan Alh kawai da sukaji ya siyawa mata daraja dan kuwa yafi su arziki nesa ba kusa ba shi kuma yaron na san ko be sota ba to baze wulaƙanta ta ba kuma zuwa gaba ze sota matuƙar ta zame masa mace ta gari ,da bayada kirki da a lokacin da yaga hawaye a ido na baze ɗaga hankalin sa har ya sadaukar min da abinda yake so ba , Rumaisa ma tana da kyan da kowa ze iya son ta ,kuma nasan bazata taɓa tabewa ba ko da biyayyar da tayi mana ,ki tayata da addu'a kawai insha'Allah duk zakuyi farinciki da wannan auren."

Ni dama tun ranar da nafara ganin Meerah da yaya nace kamar wasu masoya ,amma yarinyar nan ta Musa yanzu to Ammi ya Meerah zatayi da Sis Rufaida kinsan dai akwai matsala ko me ze hana a raba musu gida idan ba haka ba wlh zata iya cutar da ƴar mutane " karki damu a yanzu dai ba'a ɗaura auren Rufaida da Mu'aiseen ba ,bansan ko nan gaba ba shi yasa ma nayi shawara da Alh be kamata Meerah akaita gidan Mu'aiseen ba ,an gyara ɗayan part din nan da ke ta can baya ,komai akwai a ciki so ana zasu zauna gaskiya kafin nan gaba idan yarinyar ta kara gogewa dan nasan boren da Rufaida tayi ba'a hayyacin ta bane idan ta farfaɗo zata iya zuwa kaiwa ƴar mutane hari to Gara ta zauna nan kusa dani ,kinga nima zata rage min kewar Rumaisa ko,tunda rabuwar mu yazo babu shiri .


Meerah

Daƙyar Aunty ta samu tayi wanka ta saka ɗaya daga cikin kayan lefen da aka kawo mata ,ita madai gidansu babu lefi ya cika da mutanen unguwa da suke abun arxiƙi se dangin Aunty da Yaya suma duk sun zo tum a jiya ma ,ita dai danginta mutum 2 ne suka zo ɗayar yayar Mamanta ne wacce suke uba ɗaya ,se ɗayar kuma matar yayan Mamanta ,babu lefi kuwa sun kawo abun arziƙi duk da babu wani shaƙuwa tsakanin su da Meerah dan tunda tazo ta gaishe su basu sake ganin ta ba ,tana shirya wa ta kwanta bacci me nauyi yayi nasarar sace ta.


Hajia Sauda

Tun da Rufaiy ta fadawa Dady cewar bata son Mu'aiseen shikenan hankalin ta ya yakwnata dan tasan yanzu dole ze janye daga ƙudirin da yayi ,duda haka zuciyarta a ɗardar take ,na hukuncin da ze yanke ,ita dai fatan ta kawai auren ya fasu shine

Misalin ƙarfe 7 na dare dangin Muhsin suka zo tafiya da amarya ,nan fa hankalin Rumaisa ya tashi se yanzu ta tabbatar da gaske ne barin gidansu zatayi ,Umma ta kaita falon Dady dan suyi bankwa na kusa da Dady ta zaunar da ita ,nasiha yayi mata sosai tare da saka mata albarka banda kuka babu abinda takeyi lokacin da ya sallamesu se ta sake fashewa da kuka ta rungume Dady Muryar ta ko fita bayayi tace ''Abba shikenan zan tafi kayafemin idan na taɓa saɓa maka kariƙa sakani a addu'a Allah yabani ikon cin jarabawar nan yabani ikon biyayya ga reshi ,zantafi gidan da bansan kowa ba Abba mijin ma be Sanni ba wataƙila ya soni wataƙila kuma ya tsangwameni , shikenan na rasa komai na rayuwa Abba " be san lokacin dahawayen tausayin ta suka zubo masa ba shi kansa ya yarda ba'ayiwa ƴarsa adalci ba ,ƙur'ani ya ɗauko da Hisnul-muslim ,ya damƙa mata a hannun ta cikin dauriya yace " wanan sune garkuwar ki Rumaisa ,Allah yana tare da ke kiriƙe ibada ki kuma zauna da mijinki da zuciya ɗaya ,Kinga dai yadda Ammin ku ke biyayya kiyi koyi ,Allah yabaku zaman lafiya"ganin idan ya ci gaba da magana ze sautin kukan sa ze iya fitowa ,shikuma baya so ya sare mata gwuiwa dan haka yaɗagawa Umma hannu alamun su tafi ,kamata Umma tayi se aka kaita wurin Ammi kuma , nan kam babu magana da Ammi kuka takeyi bilhaƙƙi ,ta kasa cewa komai ga Rumaisa tsugune a gabanta " ki samata albarka zamu mikata ga mijinta "cewar Umma " lalubo hannun Rumaisa tayi ta haɗa da na Ammi ,dukan su biyu jikinsu rawa yakeyi ,ganin Ammi batace komai ba se Rumaisa tace " Ammi kisakamin albarka dan nasamu ƙarfin zuciyar biyayyar aure dan Allah " rungumeta Ammi tayi tana kuka tana magana " ke me biyayya ce Rumaisa a koda yaushe albarka ta tana biye dake bazan gushe ina yi miki fatan dacewa ba , Allah ya sanya wannan auren ya zama silar farin ciki a gareku ,kiyi biyayya daidai iyawarki ,ki kuma sanya haƙuri a rayuwar ki "ganin kukan nasu na ƙara ƙarfi se Umma ta janye ta ta fita da ita ,ai ko suna fita Amrah ,Mimi da Nawwara suka ƙankame Rumaisa dukansu suka zube kasa ,itama ƙankame su tayi ,tsawa Umma ta daka musu" Wane irin iskanci ne wanan Amrah kinzo kin tara yara kun sakata a gaba da kuka keda zaki ƙarfafa mata gwiwa ,shine saboda iskanci zaki sake ɗaga mata hankali shiyasa nace baxaki je gidan ta ba se bayan kwana biyu " a'a Umma dan Allah kibarta mutafi tare nasan ba lallai bane ma ya shigo yau ba "fincike ta tayi su dai dangin Muhsin da ido kawai suke binsu ,sosai familyn ya burgesu lallai akwai soyayya shaƙuwa a tsakanin su ,wata babbar mace daga cikin su ce tace " Hajia dare yanayi dan Allah kubamu amaryar mu mu zamu tafi" daga Umma se Hajia Inno suka tafi raka Rumaisa ,nan kuma da ƴar'uwar Ammi da ƙawarta ne zasu tafi bikon Meerah.


Tun da akayi sallar Magrib Aunty ke fama da Meerah akan ta sake yin wanka kafin dangin mijinta su iso amma fir taƙi seda Yayar Mamanta tayi mata tsawa ,da su basu da labarin auren ba na soyayya bane ,dole ta shiga tayi wanka da ruwan turaren da Aunty ta haɗa mata ,da ta fito ma Aunty da kanta ta shirya ta cikin atamfarta Mid green se dirty white Vail sosai tayi kyau duk da kumburin da fuskanta tayi na kukan da tasha ,hijab Aunty ta bata tace tayi sallah tukuna ,babu musu tayi sallah ta dade tana kai kukan ta ga Ubangiji akan ya sanya mata son Muhsin ko kaɗan ne Gaishe²da ta fara jiyowa ne ya tabbatar mata da lokacin rabuwa da Auntyn ta ne ya zo ,sedai tayi ƙoƙari wurin ganin batayi kwallah ba sedai kukan zuci ,da Yaya kawai sukayi sallama Aunty cewa tayi bazata iya ganin tafiyar Meerah ba ,sedai letter da ta rubuta ta damƙa mata a hannun ta tun kafin masu bikon su iso ,jikin ta yayi sanyi sosai lokay da yaya ke faɗin " ƙanwata muna fatan sauyin ƙaddararki ya zamo Alkhairi a gareki , bansan ya zaki ɗauke mu ba yayin da kika ga wanda muka aura miki a matsayin miji sedai kisani komai munayi ne domin rayuwar ki ta inganta ,kiyi haƙuri ki kuma yi biyyaya ,Allah ya albarkaci rayuwar auren ki "envelope ya dauko yace " wannan sadaƙin auren ki ne mallakin ki ne "janye hannun ta tayi tace " duk abinda yake mallakina zan iya mallaka wa iyaye na ,kune iyayena waƴa da suka jiɓinci al'amurana ,saboda haka kuriƙe kudin Yaya zakuyi wani hidma dashi ni yanzu addu'ar ku kawai nake nema " sosai suka burge mutanen da ke wurin Kowa se saka mata albarka yake a haka aka fita da ita dan kaita gidan mijinta .


"Masha'Allah" shine abinda masu kawo amarya Meerah suke ta furta wa yayin da suka saka ƙafarsu a luntsumemen falon da aka kira da mallakin ta wani lafiyayayyen sanyi da ƙamshine ya ratsa su ,duk tunda suka ga motocin da aka zo ɗaukar ta suka fara tunanin me kuɗine mijin ,basu tabbatar ba to seda suka shigo cikin gidan Alhannar duniya kenan ,babu abinda ba'a zuba mata ba na more rayuwa ,dan haka suka ƙara yi mata nasiha ,duk da sun san ita yarinya ce me biyayya amma shi zaman aure seda haƙuri ,suna cikin zagayen gidan Aiken Ammi ya riskesu manyan kuloli ne dauke da abinci farfesun kaji se drinks ,aikam zama sukayi suka cika tumbin su ,daga ƙarshe sukayiwa Meerah sallama suka kama gabansu

Ai suna fita se ta samu nasarar fashewa da kuka ,ta daɗe tana kuka ganin wannan baze zaman mata mafita ba ga ko sallar isha'i batayi ba dan haka ta shiga toilet ta ɗora alwala ta fara gabatar da Sallah

da ta idar ta koma kan gado tayi zaune tana jiran ganin ta inda ango ze ɓullo shiru² har ƙarfe 11 be shigo ba ,aiko se ta kara tabbatar wa kanta zaman wulaƙanci zatayi ,ace kusan 4 hours da kawo ta amma bezo ya duba ta ba hala ma matar sa ce ta hanashi zuwa gare ta ,s
Kifewa tayi taci gaba da risgar kukan ta ,dan zuciyarta tayi mata nauyi

Ɓangaren Muhsin kam ,yana ɗakinsa ya kulle yana baccin hankali kwance ,babu wanda yaga shigowar sa gidan ,tun bayan ɗaurin aure bashi ya tashi ba se after 5 a gaggauce yayi wanka yayi sallah sannan ya dauko wayarsa da ke silent kusa missed call 35 ya gani a wayar kira 5 na Ammi ne se 2 na Dady ,Umma ma dai kan wannan karon ta kira shi har kira biyu sauran kiran kuma na abokanan sa ne ,dafe kai yayi ,dan yasan tunda yaga kira Umma to abu me muhimmanci ne ,zama yayi da niyyar bin kiran nasu sega wai kiran abokin nasa ya shigo , yana ɗagawa,ya rufe shi da masifa akan wulakanci da yayi musu ,haƙuri yafara basu sukace ya fito gasu a harabar gidansu ,dole yamaida wayar aljihu ,ya samu ya fita ta kofar baya dan mutane sunyi yawa a gidan , ɗaukar sa sukayi suka wuce hotel a can suka bashi kayan da ze canja wai ashe sun haɗa masa walima ne na iya maza kawai ,aiko abun ba ƙaramin ƙayatar da shi yayi ba dan sun kashe kudi iya kudi ,ga har wanda be sa ran sun san da maganar auren ba ma sun halarci walimar ,wanann hidimar ita ta ɗauke hankalin sa har dare yayi ,se kusan ƙarfe 10:30 suka kamo hanyar gida ,a parking lot yayi musu sallama akan ya gode base sun shiga ba daya daga cikin su ne me suna Awwal yace " wlh baka isa ba se munga amarya ka sani ko a cikin ƙawayenta mu ma mu samu " aiko bazakayi aure ba kenan ,na faɗa maka babu wanda ze shiga yanzu kwa dawo daga baya ganin ta "ganin dai da gaske yakeyi ,dole suka juya bayan sun gama zaginsa ,shidai da dariya ya rakasu

Shiru ya samu falon se sheshekar kukan da yake jiyowa a cikin bedroom hakan ne yabashi tabbacin tana ciki mamaki ne ya kamashi me ze saka Rufaida kuka bayan burinta ya cika na ganin ta aure shi idan ma kuka ne ai shi Yakamata yayi ba ita ba ,haɗe fuska yayi yana nufar ɗakin ,a kife ya sameta kan gado batamaji motsin shigowar sa ba ,cikin faɗa²yace " wannan wane irin muna funcine ina ke kika ce kina sona kuma aka baki to kukan uban me kike yi bana son gulma" kamar a mafalki Meerah take jin Muryar Mu'aiseen ,hakan ya sakata yaye nayafinta da sauri ,karaf suka haɗa ido wani irin zabura sukayi dukan su ,ita bata san lokacin da ta diro daga kan gadon ba suka fara nuna juna da yatsa kowa yakasa magana ,shine ma yayi ƙoƙarin haɗa kalmomi cikin rawar baki yace ...........






Comments and share pls


#Real@Bazamfaria❤️
*MABARACIYA*


*ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'ى* *ASSɷ* 📚✍*
_{Onward Together}_

_STORY AND WRITTEN_
_BY_
////////////////////////////////////////////////////
*FIDDAUSI SANI* ( _Damsel Feedorh_ )
///////////////////////////////////////////////////

🅿3️⃣5️⃣


_Baki_ _baze iya furta irin jindadin da kuke sakani rabbi yabar ƙauna_ _one_ 💞


Yace" ke me kike yi a nan? Hararan sa tayi ,tana koma kan gado taci gaba da kukan ta " ke banason rashin kunyar nan naki ina kika kai matata ke kuma me ya kawo ki nan? " Kai zan tambaya ina ka kaimin Mijina kuma me ya kawo ka gidana? Wayar da ke aljihun sa ne yayi ringing dubuwa yayi yaga Ammi ce da sauri ya ɗaga wayar " kufito kai da Meerah ina falon ku"tana gama faɗar haka ta kashe wayar ,bin wayar yayi da ido me hakan ke nufi Ammi ta san da zuwan yarinyar kenan cikin gidan nan " kifito Ammi tana jiranmu a falo yana gama faɗa mata bejirata ba ya fice ,haɗiye kukan ta tayi tafa ra tambayar kanta " shin me hakan ke nufi wace Ammin ke ne man mu? Tashi tayi ta bi bayan sa don son cirewa zuciyarta ko konto ,tana fitowa Ammi ta taso da sauri ta rungumota jikin ta kusa da inda Mu'aiseen ya zauna ta zaunar da ita ,da sauri ta ɗaga kai ta kalleta.

Komawa Ammi tayi ta zauna ,kafin ta fara magana " A rayuwar nan duk abinda bawa zeyi ana so ya barwa Allah zaɓin sa da yawa zamu so abu wanda ba Alkhairi bane a garemu idan muka barwa Allah zaɓi de ya zaɓa mana mafi Alkhairi ,tun kafin a haife mutum ƙaddararsa take rubuce a littafin sa ,shiyasa ake son mu yawaita addu'a ,don neman yardar Allah a cikin lamurran mu Ameerah da ke zan fara ,dan idan har akwai cutarwa a cikin abun da na aikata to ke na cutar ,nayi karambani a cikin rayuwar ki ,duk da Ni nayi hakan ne a matsayin uwa a gareki ,don tunda na fara ganin ki sonki da tausayin ki ya lulluɓe zuciyata , kyawawan dabi'un ku yasaka ni jin bazan iya barinki ki fita daga cikin a halina ba

Na nemawa ɗana auren ki tare da roƙon iyayenki kar su sanar dake dan inajin tsoron irin boren da zakiyi, ban san hakan xe iya zama matsala ba ,ina roƙon ki da Allah ki amshi auren nan da hannu bibbiyu na tabba ta ze zamo Alkhairi a gareki , Meerah saboda kwaɗayin samun ki ga ɗana na fansar da Rumaisa ga Muhsin yanzu haka tana gidan sa " da sauri suka kalli Ammi

" Ƙwarai kuwa ,zan faɗa muku yadda akayi auren nan naku ya yiyu bayan ko wanne daga cikin ku yana da wanda ze aura"
"Maida hankalinsu sukayi gare ta ,seda ta sanar dasu komai sadai bata bayyanar da irin son da Mu'aiseen yakeyiwa Meerah ba ,kuma kai tsaye bata faɗa musu dalilin rashin ɗaura auren sa da Rufaida ba ,se cewa tayi dai auren sa da Rufaida ba yanzu ba saboda wani dalili da ya taso , sosai kuwa wannan dalilin yayiwa Mu'aiseen daɗi a ransa yake addu'ar Allah yasa dalilin ya zama silar rashin auren su da ita har abada.

" Yanzu Ammi kina nufin Rumaisa tayi aure kuma zasu bar ƙasar nan to karatun ta fa? Mu'aiseen kaidai ga amanar ƴaƴa nan na baka ,idan kacutar da ita Allah ya na kallon ka ,kayi hakuri da duk wani saɓani da zaku fuskanta ita yarinya ce bata san menene aure ba zata tarbiyyantu ne da tarbiyyar da kayi mata ,Ameerah " ɗago kai tayi ta kalli Ammi sedai kwarjinin da tayi mata yasakata saurin duƙar da kanta " kiyi biyayya ga mijin ki idan yayi Miki ba daidai ba kizo ki sanar dani ki ɗauke ni tamkar mahaifiyarki bazan taɓa barin Mu'aiseen ya cutar da ke ba ,inayi muku fatan Alkhairi ,Allah ya albarkaci rayuwar aure ku" tana gama faɗar hakan ta mike " ni zan tafi in kwanta bacci nikeji"

" Mungode sosai Ammi Allah ya saka da alkhari muje na raka ki "Mu'aiseen ya faɗa yana yunƙurawa dan rakata.
Hararan wasa tayi masa " bana son gulma tun yanzu zaka fara nuna rashin kulawa ga ƴar tawa ,idan katafi rakani ita ta zauna da wa? Kaga zo ka rufe ƙofa kawai se Allah ya tashemu lfy "Meerah kam da tunanin ta yabar jikin ta bata masan wainar da suke toyawa ba se jin maganar sa tayi tsakiyar kanta " wane tunani zakiyi bayan nasan cike kike da farin cikin samun miji me kyau kamata ,nide an cuceni da aka haɗa ni da farar kura " ni bazan ce an cuce ni ba dan nasan iyaye bazasu taɓa cutar da ƴarsu ba ,Amma ka sani auren Alfarma nayi maka wlh badan Ammi ba da a yau dinnan bazan kwana gidan ka ba kuma koda kaga ina tunani ni tunanin masoyi na nakeyi ba kai ba, to karkayi tunanin kana da matsayin da har zanyi tunanin ka ,kajira har baƙar matar ka tazo wata ƙila ita da batasan ciwon kanta ba zata iya ɓata lokaci da tunanin ka " ba zato ba tsammani taji ya murɗe mata baki ,kuma yaƙi sakar mata " daga yanzu kika sake maganar wani banza a gidana wlh se nabaki mamaki ,ni faɗa miki akayi nayi murna da liƙamin ke da kayi ko miye? Kema kinsani ba dan Ammi ce tayi wannan ba da babu abinda ze hanaki kwana gidanku a yau dinnan sakarya kuma ki wuce mutafi muyi sallah"

Wani irin kallo tayi masa " kayi sallah kai da wa? Kajira har wacce ba liƙa maka akayi ba ta shigo , ni banda wannan lokacin naka " tana gama faɗa tayi hanyar ɗaki ,daskarewa yayi saboda mamakin yarinya to me hakan ke nufi bata son sa ko me?

Lallai zan jure duk wani iskan ta amma baxan lamunci ta

Please Login or Register in order to submit comment