Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hure mata kunne da soyayyar su, dan haka ya kira Aunty ta fito yabata kudi masu yawa yace duk abunda za'a bukata ayi dasu idan be isa ba ta kira shi se ya ƙara ,ya kuma she da mata zuwan danginshi kawo akwatin aure ,daganan ya kama gabanshi.

Ɓangaren Ammi

baƙi sun sauka lafiya ,bayan sunci sun sha ta fitar musu da kayan auren a cewar ta dama su ake jira su iso domin a kai kayan sashen Hajia Sauda sosai kam suka yaba kaya musamman Umma har kukan farin ciki tayi da ƙaramci irin na Ammi tabbas ko ita ta haifi Mu'aiseen iyakar ƙoƙarin da zatayi kenan ,a ranta ta ke jin ina ma ace da Rumaisa yayan nata ya haɗa Mu'aiseen ba Rufaida ba ,ko da yake idan ta tuna da abun da Ammi ta faɗa mata akan Mu'aiseen se ta godewa Allah da yasa haɗin yafada akan Rufaida dan idan Rumaisa ce baxa taɓa barin sa yin abun da yayi niyyya ba ko dan saboda halaccin Ammi a garesu

Ƴar' uwar Ammi se yayar Dady ta zumunta aka wakilta domin kai kayan ,duk da a cikin gidan ne amma se da seda suka shiga motor zuwa part din saboda kayan baze dauku a ka ba

Hajia Sauda na zaune itada Laura ,suna tu'ajjabi da mamakin dalilin rashin dawowar Meerah ,to ko ta fahimci wani abunnne "kai babu abinda ma zata fahimta ,tunda basu bata kofar dazata iya zargin su ba hasalima karancin shekarunta baze barta wannan tunanin ba ,jin tsayuwar mota kusa da sashen su yasaka su dakatawa daga tattaunawar da sukeyi ,kan su ankara se shigowar mata ɗauke da kaya suka gani ,haka aka fara jibegesu a falon ,seda aka shigo da komai ,ganin irin kallon da Hajia Sauda keyi musu kamar bata ganesu ba yasaka Yayar Dady fadin Saudah ko baki gane mu ba dai ganin abun arzikin da muka zo dashi Yakamata kibamu wurin zama ,ko da yake lefinmu a gidan ɗan uwanmu be kamata ace mun jiraa anyi mana iso ba Abun arxiƙi ya kawo mu lefen ƴarmu ne muka kawo ,zamu tafi Allah ya sanya Alkhairi" cikin salo Hajia Laura ta washe baki da faɗin " ah Masha'Allah,ashe abun arxiƙi ne ya iso ku kuwa ai da se ku faɗa ko wani abun a shirya muku ko ? Duda dai duk gida ne ,amma bazaku tafi haka ba gaskiya ina zuwa " sama ta haura se gata ta dawo rike da sababin kudi wrappers 2 na 50₦ tace " ga wannan dan Allah babu yawa munfa gode " wani irin kallo sukayi mata kafin sukace " lefe dai ɗanmu yabamu mukawo wa ƴarmu to babu bukatar wani tukuici ,se anjimanku "still ta sake washe baki ta na biyo bayansu tare da sake jaddada godiya ,harseda suka shiga Mota kafin ta dawo.

Kai da komo ta taras Hajia Sauda tanayi " gaskiya Hajia kinbani mamaki shikenan ke bakida wani mutunci a gidan auren da kike mana taƙama wa'yannan ko ba'a faɗa ba nasan dangin mijin ki ne kiduba yadda suke jefa miki magana" Hajia Sauda dai batace komai ba dan batada bakin magana a yanzu ,Laura ce ta fara buɗe a kwatin ita kanta seda furta Masha'Allah cikin zuciyarta dan ta san duk kushen me kushe baxece kayan nan basu haɗu ba amma a fili se ta taɓe baki tana kallon Saudah " kinsan Allah Hajia Allah ne kawai yasan adadin kudin da matar nan ta yashe Alh ,da sunan hada waƴannan shegun kayan ,amma saboda kirsa da makirci ,se ta nuna kamar da kuɗin ta tayi komai ,kuma fa kinga hakan ba ƙaramin girma ze janyo mata wurin Alh ba ,tabbas tafiki wayo ,ko da yake a banza tayi dan aure se mun lalata shi yanzu dai idan Rufaida tazo ki nuna mata murna da farin ciki akan kayan nan ta yadda zata sake dakankancewa da kin amince kuma ya kamata kisa tafara zuwa gyaran jiki saboda fa komai zamuyi sa ne cikin taku hakan zesa duk abunda muka ce tayi zatayi batare da shakka ba " Daria Sauda tayi tace " shiyasa nake sonki Hajia Laura hakan za'ayi yanzu dai bara Larai tazo ta kwashe min tarkacen nan daga falo kafin ita Rufeen ta dawo.

Meerah

Kamar yadda Muhsin ya faɗa wa Aunty zuwan ƴan'uwansa kawo kaya kuwa se gashi sun zo mata 5 ne duk wacce ka kalla a cikin su kasan tana ji da arxiƙi , shin fiɗa Aunty tayi musu sedai biyu daga cikin su ne kawai suka zauna sauran se wani bin gidan sukeyi da kallo ,haka dai suka gaisa sama sama suka gabatar da kayan har zasu tafi se wata daga cikin su tace wai ina amaryar take da naji ance wai da ƙyar aka bawa Muhsin ita har se da su Alh suka yi magiya yanzu dai na tabbatar da ɗiyar talakawa ce to take dashi har haka da akaso jama na aji" Haba Amina me kike yi haka ina shi dai yaganta kuma yana so ,miye aibun talaka ,kunga kozo mutafi kwana nawa ya rage a kawota har gidanmu a sanda ai zaki ganta ko? Ɗaya daga cikinsu tafaɗa da alama bataji dadin abunda Amina tayi ba,Aunty dai da ido take kallon su da alama jikinta yayi matukar sanyi

Haka dai suka ja tawagar su suka fice.

Juyowar da Aunty zatayi sukayi ido biyu da Meerah , Murmushi tayi tace" yanzu kin fahimta ko Aunty? Abunda nake gujewa kaina kenan ,sufa masu kuɗinnan haka suke sunfison ƙwarya tabi ƙwarya ,sam basa so talaka ya raɓesu ,sedai Yakamata su sani ba ko wane talaka bane wulakantacce zanyi biyayyar aure amma bazan ɗauki wulakancin dangin sa ba ,duk wacce tayimin zan rama wlh" tana gama faɗar haka ta shige ɗakinta ,hannu a kunci tabar Aunty a tsaye.



_Cabdijam_ _anzo wurin fa auren Rufaida da Mu'aiseen ya kankama haka Meerah pageda Muhsin ,ya kuke ganin abun ze kasance ? ma catch next_ 😀


Comments and share pls


#Real@Bazamfaria❤️
*MABARACIYA*


*ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'ى* **ASSɷ📚* ✍
_{Onward Together}_

_STORY AND WRITTEN_
_BY_
////////////////////////////////////////////////////
*FIDDAUSI SANI* ( _Damsel Feedorh_ )
///////////////////////////////////////////////////

🅿3️⃣3️⃣

duk wani shiri da Hajia Laura keyi ,cikin taka tsantsan takeyin sa dan kusan tsun tsu biyu zata jefa da dutse ɗaya na farko dai zata lalata auren Sauda ba tare da ta gane hakan ba na biyu zata cimma burinta akan Rufaida ,shiyasa da Hajia Sauda ta mata maga se ta ce " ta sa ido tayi kallo dai " ita kuma da yake ba dogon nazari ne da ita ba ,ta yarda da cewa temakon ta ne Laura zatayi .

Kimanin kwana biyu kenan Mu'aiseen yana fama da rashin lafiya a tsay-tsaye duk ya rame duk da ƙoƙarin ƙarfafa kansa da yakeyi dan baya so Ammi ta gane halin da yake ciki ,sedai yau abun ya gagara dan ko Sallar asuba be fita ba da kyar yasamu yayi Sallah a dakinsa ya koma ya naɗe a bargo ,shiru shirun da Ammi taji ne be shigo ya gaisheta ba bare ya fita aiki saboda haka ta tura Amrah taje ta dubo shi ko ya fita ne maybe yana da uzuri shiyasa be shigo sun gaisa ba ,duk da tasan babu uzurin da ze hana shi zuwa gareta duk saurin da yake se ya fara shigowa sun gaisa kafin yake fita ,sedai ita kanta tana kula da sauyin da ya samu tun satin da ya gabata.

Knocking Amrah ta fara seda ta dauki kusan minti biyar a tsaye ganin ko motsin sa bataji ba se ta tura ƙofar ta shiga ,duhune a falon kasancewar duka windows din a rufe suke ,seda ta laluba ta kunna switch kafin haske ya bayyana ,da ido ta bi falon kulolin abincin da aka kawo masa ,tun jiya suna ajiye da alama ko buɗewa beyi ba ,mamakine ya kamata " to ko dai be kwana a gidan bane ,Ammi ce bata sani ba? ganin batada tabbaci se ta nufi bedroom dinsa , shima babu haske seda ta kunna ,dube²ta fara yi can ta hango shi cikin bargo da sauri ta nufi gadon ta yaye bargon wani irin hucin zafi ne taji ya bugi fuskanta " Subhanallah Yaya bakada lafiya ne? me yake da mun ka kasha magani? duk da halin da yake ciki seda ya ɗan murmusa ,saboda ganin shirmen da Amrah keyi se jera masa tambayoyi takeyi bayan duk wanda ya ganshi yasan cewar beda lafiya amma ita tambaya ba adadi a lokaci ɗaya ,dama Rumaisa ce zata iya te makon sa dan tafi Amrah hankali ,ganin zata sauka daga kan gadon ya saka shi riƙo hannun ta ,cike da ƙarfin hali yace " don't inform Ammi just call me Rumaisa" bata ma gama sauraren shi ba tafincike hannun ta ta fita lokacin har hawaye sun fara bin fuskanta ,tana shiga falon Ammi mutane suka fara binta da ido ,ita ma kallon su takeyi ga hawaye a fuskanta sedai batayi magana ba " ke wane irin iskanci ne zaki shigo mana ido da hawaye kina binmu da kallo kamar wasu baƙin ki lafiya? Hajia Inno ta faɗa (yayar Dady) tana harar Amrah ,kasan cewar ta mace mafaɗa ciya ,turo baki Amrah tayi tace " Goggo ni Ammi nake nema "ai se kishiga ciki kiduba ba ki tsare mu da shegun idonki da kikayi gado ga dangin ubanki ,Duda ya rasu kinja masa zagi" dariya dai mutanen da ke wurin sukayi ,dan kowa yasan jarabar Inno ,ita dai Amrah batabi ta kanta ba ta tafi neman Ammi.

Waya ta sameta ta nayi ,ganin yanayin ta yasaka Ammi sallama da wacce take wayar ta maida hankalinta ga Amrah "Me ya faru keda na tura kidubamin Yayanku kindawo kina kuka har kinsani faduwar gaba me ya faru? "Ammi Yaya beda lafiya sosai kuma shine yace kar na faɗa miki wai na kira Rumaisa ,kuma nasan ita ta wuce school".

ko gama sauraren ta Ammi batayi ba tace " tashi mu tafi ,ganin fitowar su ne yasaka Umma magana tace wai me ke faruwa ne ta shigo tana kuka ke kuma kinfito hankali a tashe? Batare da Ammi ta tsaya ba tace " ina zuwa Yayansu ne babu lafiya "Umma najin haka ta koma ta zauna dan tasan yanzu haka ba wani ciwo bane kawai rundune irin na Ammi indai abu akan Mu'aiseen ne to fa babu zama ,sauran ƴan'uwanne sukayi masa fatan samun lafiya ,Inno kuwa taɓe baki tayi tace " shi keyiwa amaryar tasa jinya kenan dan ita naga har wa ni rawan ƙafa takeyi jiya na ga shigowar ta gidan nan amma da yake Saude batada mutunci tasan munzo shine takasa turo ƴarta ta gaishe mu ,Allah dai ya kyauta ,ni banso aka haɗa yaron nan da ƴarta ba naso nayi ƙorafi se ga naga ita Zainabu ma tayi murna da hakan shiyasa na kawo ba gani na saka musu dahuwar mutum dai me ƙwassai" babu dai wanda ya tanka ta har ta ƙarashi surutun ta.

Sosai halin da Ammi ta samu Mu'aiseen ya daga mata hankali , toilet ta shiga da kanta ta debo ruwa ta dauko towel ,ta fara goge masa jiki saboda zafin jikin sa yayi yawa ,yanajin duk abunda takeyi masa sedai yama kasa buɗe idon sa ,saboda saran da kansa keyi na azabar ciwo ,tura Amrah tayi ta haɗo mata tea ta kawo mata ,batayi masa magana ba dan ta san halinsa da shegen musun tsiya ,dan haka tafara kiciniyar tada shi ya zauna ,yunƙurawa yayi ya ɗan jingina bayansa da gadon ,bayajin shan tea amma saboda Ammi haka ya daure tama bashi ya ma karba seda yadan sha babu lefi ,kafin ta ajiye cup din ta duba side drower din ta ɗauko magani ta bashi yasha ,gyara masa kwanciya tayi tana rufa masa bedsheet din tace " kayi bacci idan ka tashi zamuyi magana " kai kawai ya iya ɗaga mata ,yana jinsu har suka fita ɗakin ta ja masa ƙofa .

Buɗe idon sa yayi a ransa yana jinjina soyayyar dake tsakanin shi da Ammi be taba jin cewar ba ita bace ta haifesa hasalima shakuwar da ke tsakaninsu babu ita tsakanin sa da Umma ,yanzu da wata uwar ce bazata kula da halin da yake ciki ba kawai tambayoyi zata fara yi masa akan me ya faru amma ita ta barshi har ya samu relief ,haka yayita tunani har bacci yayi nasarar ɗauke shi.

Ammi tana komawa sashen ta ta nemi ganawa da Umma ,su biyu suka keɓe a ɗakin ,ta kora wa Umma bayanin komai ,duk da Umma ta tausaya wa ɗan nata sedai bata goyi bayan shawarar da Ammi ta kawo a matsayin mafita ba " kiyi tunani da kyau Umma nasan Alh ze fahimce ni ,banason wani abu ya samu Mu'aiseen idan na bari hakan ya faru bazan taɓa yafewa kaina ba ,domin tun farko ya bayyana min ra'ayin sa game da ita " a'a Zainabu yin hakan kuma kamar mun so kanmu ne da yawa ita yarinyar tana son sa ne? bamuda wannan tabbacin " shi kansa wanda za'a batan ai ba son sa takeyi ba" duk da haka Zainab haramun ne neman auren cikin aure saboda farincin namu yaran be kamata mu tauye na wasu ba " wlh Umma duk wannan ba kawai saboda Mu'aiseen nakeyi ba har ita kanta yarinyar ,ina son ta kamar yadda nakeso Rumaisa kuma a shirye nake da na fanshe ta da Rumaisa" zare ido Umma tayi cike da mamakin abun da Ammi tace " taya zaki wannan gaskiya abun naki na neman zarta tunani taya zaki ƙuntata Amrah saboda shi ,a rayuwa kowa ya sani akwai nasara akwai faɗuwa saboda haka kibar wannan a matsayin ƙaddarar sa ko ba da haka ba ma bana tunanin ɗanki ze iya riƙe mata biyu kuma hakan kamar wani sabuwar fitinar ne zamu tono tsakanin mu da Saudah ,abar zancen auren nan kawai "

Ganin dai Umma bazata fahimce ta bane se kawai ta shareta kamar ta bar zancen

Sedai ta yi musu sallama cewar zata fita amma ba jimawa zatayi ba zata dawo ,tabarwa Amrah saƙon cewar tarikayi tana dubo Mu'aiseen idan ya tashi ta kai masa abinci ace yaci inji ta zata dawo masa da albishir din da ze saka shi farinciki

Ba ita ta dawo gidan ba se goshin Magrib ,duk da tana cikin damuwa amma bata bari su Hajia Inno sun gane hakan ba seda tayi sallar isha'i ta gama kafin ta ɗaga waya ta kira Rumaisa tace ta sameta ɗakinta yanzu kuma tazo ita kaɗai ,babu ɓata lokaci kuwa Rumaisa ta xo

Tashin hankalin da ta gani cikin idon Ammi yasaka nata hankalin tashi ita ma " Ammi wai me yake faruwa ne Yaya jikin sa yayi tsanani ko tashi baya iya yi kuma ya hana akaishi hospital ,sedai doctor yazo gida daƙyar ya bari aka saka masa drip"

Na sani Rumaisa ,shine dalilin kiranki da nayi yanzu , Rumaisa bansani ba ko zaki iya yimun wannan temakon ba duk da nasan cewar ke ɗin me biyayya ce kina son farincina idan har haka ne to ki amshi maganar da za faɗa miki ina me tabbatar Miki Allah ze duba sadaukarwar ki da biyayyar da kikayi min ,baxaki taɓa nadama ba ki temakeni Dan girman Allah"Ammi ta kara sa tana haɗa hannun ta ,rawa jikin Rumaisa ya fara ,duk da Ammi bata sanar da ita alfarmar da ta ke so tayi mata ba to ta tabbata al'amarin me girma ne ,fashewa tayi da kuka tana janye hannun Ammi daga rokon da takeyi mata ,cikin kuka tace " Ammi ni ce kike roƙo haka saboda wani buƙata kamar ba ƴar da kika haifa da cikin ki ba ,miye amfanin mu ƴaƴa idan bamu share muku hawaye ba a matsayin iyayenmu da su ka sha wahala akan mu ba , be kamata ki tsaya roƙon kafin ki zarta hukunci a kaina ba ,kamata yayi ki kirani kice ,kin yanke hukunci kaza akaina ,Ni kuma me biyayya ce a gare ki Ammi ,me kike so nayi Miki?


"Allah yayi miki albarka Rumaisa yabaki yaran da za su ji ƙanki kamar yadda kika amince zakiyi min biyayya ba tare da kinsan hukuncin da na zartar ba ,na bada auren ki ba tare da naji ra'ayin ki ba kuma za'a daura auren ne nan da kwana biyu rana ɗaya da na yayanki kenan " matukar girgiza Rumaisa ta girgiza da kalaman Ammi "innalillahi wa'inna ilaihiraji'un"take maimaita cikin ranta "wannann wace irin ƙaddara ce ta kusan to ta to wa Ammi ta baiwa auren ta? Baxaki amince ba ko Rumaisa? Maganar Ammi ta sake shiga kunnen ta ,da sauri ta girgiza kai " na amince Ammi "to baki tambaya waye mijin ba? Na tabbatar da mahaifiya irinki bazata taɓa yiwa ƴarta zaɓin tumin dare ba ,nasan cancantar sa yasa kika amince da zaki bashi ni ,a yanzu banason nasan ko waye Ammi na amince da auren sa ki tayani da addu'a hakan ya zamo Alkhairi a gareni" rungumeta Ammi tayi tana shi yi mata albarka ,nan take zazzaɓi ne zafi ya rufeta ita ma kwantar da ita Ammi tayi kan gado ta tofa mata addu'a tace ,ta yi bacci.


daganan ta wuce ɗakin Mu'aiseen,ba ta sameshi a ɗakin ba sedai motsin ruwa da taji a toilet haka ya tabbatar mata da wanka yakeyi ,ajiyar zuciya ta sauke don hakan yana nufin ya samu sauƙi kenan ,bata daɗe da zama ba ya fito daga wankan " Ammi na bakiyi bacci ba? Murmushi tayi masa " ina zanyi bacci banzo na duba ka ba Mu'aiseen , Alhamdulillah dai da alama jikin da sauƙi" ehhh naji sauki Ammi duk nacin ciwo idan uwar mutum tazo ai dole ya gudu "ya faɗa yana zura jalabiya ,dawo wa yayi inda take ya zauna " Ammi ke kanki hidimar bikin nan duk yasa kinyi wani iri ko da yake rabuwa da ɗa ba wasa ba"dariya tayi tace " ai shiyasa naga shi ɗan har da jinya saboda ze rabu da uwar sa "hmmmm Ammi kenan ni fa dama na dakatar da gyaran gidana , ina tunanin ana zamu zauna gaskiya ,saboda Ni dai bazan ɗauki masu aiki a gida na ba idan ma na ɗauka befi shara da morphing ba to dole ne yarinya indai har zata zauna a ƙarƙashina ta shiga kitchen ta girka min abinci ,dan haka Ammi na ta sabamin ban saba cin abinci masu aiki ba ,kinga idan muka zauna a nan zata koyi aiki a wurinki " kallon sa kawai Ammi keyi har yagama maganar sa kafin tace " to wacce daga cikin su zata zauna anan? Uwar gidan ko amaryar? "Haba Ammi kinfi kowa sanin ita kam na rasa ta rashi na har abada renon banza nayi a zuciyata shiyasa akace arashin tayi akan bar arha ,da tun lokacin da na samo ta na bayyana manufa ta da hakan be faru ba ,shiyasa ma na haƙura da Rufaida wataƙil ita ce Alkhairin da Ubangiji ya zaɓamin" sosai ya baiwa Ammi tausayi lallae ta yarda ba ƙaramin so yakeyiwa yarinyar ba ,murmushi tayi cikin ranta take kitsima irin farincikin da zeyi idan ya san fafutukar da tayi dan tabbatar masa da samun wacce ya daɗe da soyayyar ta ,amma a fili se tace " karka sare haka ,bakasan hukuncin Allah ba ze iya sauya ƙaddara a ko wane lokaci kaidai ka ƙarfafa wa kanka ,kuma ka cire damuwar nan insha'Allah zakayi farin ciki ,jibi iwar haka kana cikin iyalin ka yarona ya girma" rufe ido yayi yana daria ,kamar ba shine mara lafiyar da ke kwance a ɗazu ba ,haka kawai yakejin farin ciki na lulluɓe zuciyar sa ,bayan yasan kamata yayi ace yana cikin damuwa ze rasa abar ƙaunarsa nan da 44hours ,amma yarasa dalilin hakan.

Washe gari da zazzabi me zafi Rumaisa ta tashi ,Amrah tayi² ta sanar mata abunda ke damunta ganin yadda take ta faman kuka ,amma taƙi ma tayi magana ,ganin haka se ta ƙyaleta .


Rana bata ƙarya ,a yau 31/5 Yakama ranar daurin auren mutane shida ,tun safe Dady baya gida yana can wurin hidimar sauke bakin sa duk da tun a daren jiya wasu suka riga suka sauka ,idan kazo layin gidan lallai zaka sheda ana babbar hidma ne duk da ba'a nan ne za'a ɗaura auren ba amma talakawa sun cika layin gidan to sun sani sadaka ne dai se sun zamu a banza ma akayi bare ze aurar da yara har guda biyu dan ba su san da zancen auren Rumaisa ba ,musamman da sukaji ance macen ƴar Hajia Sauda ce me ruwan kudi wacce ta saba jiƙa su da kuɗi a duk lokacin da tazo gari to bare yanzu da zata aurar da ƴarta ,dan haka kowa be bari anbarshi a baya ba ,ƙarfe biyu aka saka ɗaurin auren ,wanda bayan daurin auren ya kammala akwai walima da Alh Abdullahi tsoho ya shirya ta zallar maza kawai ,ƙarfe ɗaya da rabi Dady ya shigo gidan don duba jikin Rumaisa da Umma tayi mishi waya cewa yayi tsanani ,ita dai tana ganin gara a fasa yi mata wannan auren dama ita can bata amince da wannan shawarar ta Ammi ba ,shi kansa hankalin sa ya tashi ganin yadda ƴar tasa ta koma cikin kwana biyu ,sedai da yace za'a fasa auren Rumaisa ta dage akan a ɗaura ita lafiyarta lau kawai dai batada ƙarfin jiki ne ,wannan karon Ammi ɓoyewa tayi tana kuka ,se yanzu take ganin rashin kyautatawar ta ga babbar ƴar ta ,gashi ita tana ƙoƙarin sanya ta farinci ki meyasa batayi tunanin hakan ba ,seda ta sha kukan ta me isa ta wanke fuska ta fito ,kiran da akyiwa Dady ne yasaka shi tashi dan yasan shi ake jira lokaci na ƙurewa za'a ɗaura auren har ya buɗe mota ze fita Sega Rufaida da gudu tana kwala masa kira tundaga nesa ta rugo da gudu se faman ihu take tana fadin "Dady karku ɗaura auren nan wlh na fasa bana son shi idan ka aura min shi wlh se na kashe shi ,ihun da takeyi ne ya janyo hankalin mutane da yawa da suka fara cika gidan bangaren Ammi ,Riketa Umma tayi dan gani tayi kamar ba'a hayyacin ta take ba ,cikin tsawa tace " ke natsu Rufaida waye bakiso? Cikin rawar Murya tace " Mu'aiseen ,idan aka aura min shi kashe shi zanyi in kashe kaina kowa ya huta "innalillahi wa'inna ilaihiraji'un mutanen wurin suka fara maimaita wa "ke kuwa kinsan baki son sa kika bari har se yanzu da babu mafita se ta ɗaura auren zakice kin fasa ? Dady daskarewa yayi yama kasa magana ,ga se kiran wayarsa akeyi ,dan haka be ce komai ba ya bude motar sa sedai tashin motar suka gani ,.

Kama Rufaida Umma tayi zata kaita can sashen su saboda ta fahimci ba'a hayyacin ta take ba ,cikin tsawa Hajia Inno tace " sake ta ta koma ai da kanta ta zo ,turo ta akayi ta isar da saƙon kuma ta isar , Alhamdulillah mu ba'a isa a kunyatamu ,kuwuce muci gaba da sha'anin mu babu fashi ,jikin kowa a sanyaye a koma ciki ,

Karfe biyu daidai ,Alkawarin Ubangiji ya tabbata wani baya auren matar wani ,kamar yadda rabon wani ke kashe wani ,to wannan karon dai Alhamdulillah don kuwa rabon beyi kisa ba sedai ya canja ƙaddarar mutane da yawa ,a lokacin da Mu'aiseen ke tunanin ya rasa a lokacin Allah ya dubi zuciyarsa ya dawo masa da abar son sa cikin sauƙi

An ɗaura auren Mu'aiseen da Ameerah
Mushin da Rumaisa

Auren da ya samu albarkar manyan malamai masu kudi da talakawa


Duk da shi Mu'aiseen be samu halartar daurin auren ba koda ya zo har anshafa fatiha ,kuma kaikaitar idon jama'a yayi ya sulalewar sa ,saboda haka yasan dai an ɗaura masa aure amma be san cewar bada Rufaida bane



Haka Meerah bata san cewar ba Muhsin bane angonta

To se muyi fatan dai samun zaman lafiya a tsakaninsu



Comment and share pls


08039228702

#Real@Bazamfari❤️
*MABARACIYA*


*ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'ى* *ASSɷ* 📚✍*
_{Onward Together}_

_STORY AND WRITTEN_


Please Login or Register in order to submit comment