Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Meerah tayi mata tukuna kowa yakama gabansa

Koda Meerah ta koma gida a cikin dakinta ta samu aunty tayi ta gumi da alama tunani takeyi

Wuri tasamu ta zauna,cikin sanyi murya tace " Aunty sannu da gida ,bata amsata ba sema fada da ta fara yimata " yanzu saboda Allah Ameerah abunda kikeyi ya dace kenan,kamarki da kananun shekaru ace kina yawo lungu-lungu kamar marar mafadi ,wai duk da sunan daukar fansa ,yakamata ki natsu kisani ke macece me karancin shekaru sannan kuma bakida kowa se Allah shin taya kike tunanin zaki iya ja da Saudah macen da kowa yabon halinta yakeyi na tabbata bakida karfin da zaki dauki fansa akanta ,murmushi Meerah tayi tace "Aunty yanzu fa kika gama fadar banda kowa se Allah,idan ko hakane kinga ni nakeda babban bango domin duk wanda ya dogara da Allah to ya isar masa ,kedai kimun fatan alkhairi,yanzu ma da wani labari nazo miki

Kwanan nan zanfara aiki a gidan Yusuf Tsoho ,kuma a matsayin me yiwa 'yar Hajia Saudah hidma ,Aunty zatayi magana Meerah ta tareta da fadin " karkice komai Aunty domin bana fatan Allah yakawo ranar da zanyi musu dake ,nasani akwai risky cikin lamarina ,amma nabarwa Allah komai ya shigemin gaba ,bawai kawai saboda fansar yayata bane aa ceton 'yayan yama'ah da yawa ,wayanda Saudah tayi nasarar lalata rayuwarsu ,idan bahaka ba Allah ne kadai yasan wayanda zata 'bata anan gaba ,bayan ita tana nan ta kebe 'yarta da nufin karta lalace Wlh nayi alkawari kamar yanda tayi sanadiyar lalata 'yaran wasu haka nima se na saka yarinyar ta ta lalace wannan alkawarina ne ,iya mamaki Meerah ta baiwa aunty"to kitafi kici abincinki tun safe bakici komaiba tana gama fada tabar 'dakin

Bayan kwana biyu Rufaida tagaji da jiran kiran Fatima gashi bataso ta kirata hakan ze zama kamar raini ne a gareta ,se jujjuya waya takeyi,hakan nan dai ta daure ta danna kira , ringing biyu Fatima ta 'daga shiru Rufaida tayi daga can Fatima tace " hi bab , Rufaida bata amsa ta ba se cewa tayi " I have been waiting for ur call but yuh didn't,are yuh ok? "Yes am ok wlh abubuwane dai suka sha kaina ,sedai nayi iya kokarina naga na kawota gareki but is yet to be possible,but there's only one way ,a wukance Rufaida tace " just go to the point am all ears

murmushi Fatima tayi tace "Sunan yarinyar Ameerah iyayenta miskinai ne ,da baran da takeyine take rufa musu asiri tayi yawon neman aiki har tagaji amma bata dace ba "yuh mean she's educated? Rufaida ta katseta "no sorry I mean aikatau irin na gidaje House maid ,ajiyar zuciya Rufaida tayi tace "to wace hanya ce kike nufin inada "kawai 'daukarta aiki zakiyi kinga ta hakane zaki wulakanta ta yanda kikeso,ki nuna mata banbanci da ke tsakanin me kudi da talaka kaskantacce irinta,cikeda gamsuwa Rufaida tace "tnz alot dear, I will talk to my mom ,nasan dai bazata hana ba amma yakamata na fada mata ,bye,bata jira cewar Fatima ma tayi hang-up ta ajiye wayar....


'''''Hajia Saudah da ke zaune tsakiyar wasu mata ,dukannin su babu mai suturar arxiki a jiki,dayar ce tayi mika tare da fadin "nikam wai yau haka zaki barni a gidan nan ,no more enjoy gaskiya da sake tafada tana hararar Hajia Saudah,murmushi tayi mata ta bude baki zatayi magana se ga kiran Rufaida ya shigo wayarta ,ware ido matan sukayi don ganin wata damsel cute tayi appearing a gaban wayar ,da sauri Hajia Saudah ta bar wurin tare da kara wayar a kunnen ta

"Mom Rufaidah ta fada a shagwabe ,ajiyar zuciya Saudah ta sauke ,itama cikin tsan tsar kulawa tace " Auta menene ,sake narkewa Rufaidah tayi tace "Mom gaskiya nide zan biyoki niger I have tired been alone ,babu kowa kusa dani and kince baki yarda nayi kawance ba ,kuma gashi Business dinki baya barinki zama tare da ni ta karashe maganar kamar zatayi kuka "Haba one and only ni kaina ko yaushe tunanin ki nakeyi ,shiyasa nake son na gama harhada komai na dawo da kasuwan cina anan gida ,karki damu Dadyn ki yakusa da wowa ,nasan ze rage miki kewa ok? Ta karashe maganar in a wisfer tone .

Tabe baki Rufaidah tayi tace " to dama so nake asamamin wata 'yar aiki "ina Sharifa ko ta dena zuwa ne Momy ta tambayeta "nop kawai dai ina ra'ayin wata ne tabata amsa a takaice saboda sam batajin dadin nisan da Hajia Saudah takeyi da ita,kuma da tayi korafi ta nuna tana sonta ,katse mata tunani tayi da fadin "shikenan,bari zanyiwa me kawo masu aiki magana ta samomiki " No Momy na rigada na samu wata ma, kawai dai nakira ki ne saboda kisani ,shiru Hajia Saudah tayi kamar me tunani se kuma tace "shikenan bye take care ,da ga haka ta datse kiran

A bangaren kawayen ta kuwa tunda ta fita suka fara musu kowa yana fadin shi za'a mallakawa wannan yarinyar ,dayar ce me suna Hajia Asabe tace ita idan ma ta samu wannan to kawai ciniki zasuyi da Hajia tabata auren ta domin gidan ta zata wuce da ita kai tsaye suna cikin wannan musun ne Hajia Saudah,ta shigo sedai wannan karon fuskarta a hade saboda bata so ma suga damar da zasuyi mata magana

"Hajia nace wannan yarinyar zan mallaka miki ko nawane ,domin ki sadaukar min da ita domin da ganinta ,se tayi dadin makin luv ,kinga yarinyar Masha'Allah kirnjin nan tab da shi ga Dan bakinan wallahi har nafara imagination,yanda zasusha tsutsa gun......"dakata Asabe Hajia Saudah ta katseta cike da fushi taci gaba da magana"me yasa wai ke Sam bakida tunani ko kinsan wacece wannan din to 'yatace Rufaidah wacce kaf itace duniyata ,lalacewa ta bazesa itama ta lalace ba ,saboda haka ,zanmuku alfarma daya ,akwai yaran da nayiwa kaina tanadi ,amma zan barmuku kuji dadinsu banaso wata ta sake yabon surar'yata ,tafada babu alamar wasa a fuskanta

Sage sukayi suna kallon ta cikeda mamaki ,shin ko ta mance a tafiyarsu Babu nuna wariya kuma itama ai lokacin da taga 'yar Hajia Larai haka ta kunace seda ta lalata rayuwar yarinyar wanda shine sanadin yanzu yarinyar ma bata 9ja , domin da ta gwane a harkar tace sedai tayi da Jan fata domin sun fi iya luv ,babu kukan da Hajia Larai batayi ba ,amma tanaji tana gani tayi nesa da 'yarta domin tunda ta fahimci mahaifiyarta ma batada tarbiya se ta dena jin maganar ta baki daya kasancewar dama mahaifinta baya raye

Hajia Asabe zatayi magana ,Larai ta girgiza mata kai alamar kartace komai ,shiru tayi tare da kitsima abubuwa da yawa ta yanda zata mallaki Rufaida, domin tariga ta kwadaita wa kanta ita kuma tayi alkawari ko ta halin ya se ta samota matsalar dayace sam Saudah bata basu damar sanin familin ta ba ,saboda tana da matukar wayo shiyasa ko yaushe sedai ta nuna musu ai business ne yahada su saboda haka no need ace se sun san komai nata ,duk tunaninsu itadin bazawara ce ,domin duk lokacin da mijjnta ze zo wurinta to bata yarda kowa yazo mata gida ,takanyiwa mai gadi warning akan kowa yazo yace bata garin


Sosai Meerah tayi murna dajin Rufaida ta yarda zata dauke ta aiki ,bata damu da komai zata fuskanta ba ,kawai dai burinta ,Hajia Saudah ne ta dauki fansa ,sedai jikinta yayi sanyi tunawa da aunty da tayi ko ya zata dauki al'amarin ,cikeda sanyin jiki ta nufi dakin ta


da sallama ta shiga ,se kuma tasamu wuri ta zauna cikeda mutuwar jiki ,dan dagowa aunty tayi ta dubeta ,cike da kulawa tace "ke kam lafaiyarki ,shiru tayi kamar bazatayi magana ba ,se kuma tace " Aunty a musulunci ma an yarda idan mutum ya cutar dakai ,kuma bazaka iya hakura ba to karama dai dai da abunda yayi maka amma yafiyar ita tafi domin Allah ya tanadi wata kofa a cikin aljannah wanda yayi alkawarinta ga wanda yayi hakuri a inda yakeda ikon ramawa ,sedai duk ba wannan bane dalilin,daukar fansa na ba ,sedan na kubutar da 'wayanda zasu shiga komar Hajia Saudah nan gaba ,wayanda take anfani da 'dayar fuskarta na mutunci,tana keta haddin yaransu ,kimun fatan nasara ,domin cikin kwanan nan zan fara shiga gidan Saudah a matsayin 'yar aiki ,banaso na dauki lokaci a gidan ,ajiyar zuciya aunty tayi tace " Allah ya zama gatanki ya kuma tsare miki mutum cinki daga haka bata sake cewa komai ba .sosai Meerah taji dadin goyon bayan aunty da ta samu cikin sauki ,saboda haka ta turawa Fatima text din zata iya fara zuwa ko yaushe ta tambayi Rufaida......




*Comments nd share pls*




#follow me on wattpad@damselfeedo




#Real@Bazamfaria💘
*INTELLIGENT* *WRITERS* *ASSOCIATION*
(On ward together)

*MABARACIYA*

*Story* *and* *writing*

By

*FIDDAUSI* *SANI*
(damselfeedorh)

🅿️:1️⃣0️⃣


,,,,,,,,Washe gari Rufaida da kanta ta kira Fatima a waya sosai tashiga mamakin ganin kiranta sedai ba ta nuna fa ,daga can Rufaida tace "Fatima ya naji shiru? Murmushi ya subucewa Fatima ba tare da ta shirya wa hakan ba har seda Rufaida taji sautin shi ,cike da mamaki tace" yadai kike dariya ? Dole ne nayi dariya Fatima wai kinsan yarinyar nan taso ta ganeni"wace yarinya ta tambaya ,don ita har ga Allah batasan akan wacce take magana ba

"Mabaraciya ,Fatima tabata amsa a takaice " ok to yanzu ya kukayi da ita " ehhh to kinsan ko cikin talakawan wasu basuda kwadayi da fari yarinyar da mahaifiyar ta kin amincewa sukayi wai ita bazata seda mutunci 'yarta saboda kwadayin abun duniya ba ,shinefa na samu mahaifinta ,na nuna masa irin Alkhairan da zasu samu a cikin aikin nan ,tukuna yayi tsayin daka akan dole se tayi aikatau ,cikeda jin haushi Rufaida tace " wai me suke takama da shi nikaina idan badan saboda na dauki fansa bane me zanyi da aikin ta yanzu ma kawai inaso na koya mata darasine ,idan na fahimta halin uwarta ne ta gado na ganin dede suke da kowanne'dan adam , murmushi tayi mai sauti cikeda jin ita din watace tace " point of correction cox totally akwai distance sosai a tsakanin mu , mabaraciya wacce abunda zataci ma se tayi yawo ta nemo kuma hakan wai iyayenta da ita suka dogara ta zame musu bango ,dole zan nuna mata wacece ni 'yace wacce ko kiran sunan mahaifiyata akayi dole mutum ya natsu domin yasan ta Tara abun duniya despite my father

Shiru itadai Fatima tayi tana sauraren ikon Allah ,a ranta take tunanin wane irin girman kai da takama ne ke damun Rufaida,tabbas rayuwar wasu a kwai gyara ,duk da ta ta'allaka hakan da rashin samun rarbiyar uwa da batayi ba ,kowa yasan Hajia Saudah yakuma san irin Alkhairan ta ,da yanda take taimako da son jama'a ko kadan Rufaida bata gaji halinta ba Farar tukunya kenan mai fidda ba'kin tuwo ,Fatima na cikin wannan tunanin ne tani 'kit alamun ta yankee kiran ,bin wayar tayi da kallo tana tunanin shin wace kaddara ce ke kiran Meerah aiki a karkashin wannan da bata gaji mutum ci ba ,tana cikin tunanin ne wayarta ta sake ringing ganin sunan Meerah ya sakata dagawa ,da sauri ,tambayarta Meerah tayi akan yaushe zata fara zuwa " even tomorrow,tabata amsa jiki a sanyaye ,wani irin dadi Meerah taji ,sosai tayiwa Fatima godiya sanann ta yanke kiran

Meerah na zaune dakinta tayi tagumi ,da alama tunani takeyi ,shigowar aunty ne yasakata dawowa daga duniyar tunanin ,kallonta tayi tasakar mata murmushi tare da matsawa daga gefe saboda ta samu wurin zama " kinga ba zama ne ya kawoni ba ,aikenki nakeso nayi kasuwa,sedai naga yamma tayi ina tsoron kitafi kiyi zamanki nasan halinki " kai aunty se kace wata yarinya ,da zan tafi na zauna a titi ,kedai kikawo sakon kawai yanzunnan zan dawo Insha'Allah " yawwa to kishirya se ki sameni a 'dakina aunty tafada tana fita dakin ,tashi Ameerah tayi kayan jikinta kawai ta sauya daga riga da wando zuwa bakar jalabiya sosai tayi kyau ,kamar ba Meerahn da na Sani ba saboda sak ta fito yar gayunya harta yane kanta da dan karamin vail na rigar sekuma ta sauya zuwa hijab red colour Masha'Allah Allah ,tayi kyau sosai abunda ,cikeda na tsuwa ta shiga dakin aunty ,sakin baki aunty tayi tana kallonta har seda tayi kasa da kanta don taji kunyar kallon da aunty ke binta da shi

Cikeda xolaya Aunty tace " Masha'Allah Meerah kinganki kuwa ,idan a hanya na ganki ai bazanxe wannan Meerah ta bace tafada tana dariya ,Dan turo baki Meerah tayi tace" idan da bansan halin aunty na ba da se tafasan kai ,bani sakon nidai natafi ,dariya kawai Aunty tayi ta dauko kudin sakon tabata tare da fada mata abunda zata siyo ,sallama tayimata sannan ta tafi

Adaidaita sahu ta shiga kasancewar akwai dan tazara tsakanin su da kasuwa ,cikin natsuwa tagama siyan duka abunda Aunty tace ,haka ta riko kayan ta nufi titi don samun abun hawa 'a can tsallaken titi ta hango wani mutum yawuce yama tallan a agwalima ,hannu tafara daga mishi alamar yatsaya sedai da alamu sam be kula da itaba ,ganin da tayi kamar babu motorn da ze wuce kusa yasakata saurin tsallakawa ,sedai tun kafin takai tsakiyar titi ta sake duka kayan hannunta sakamakon wani uban horn da yacika kunnen ta duk tabi ta rude ta kasa yin gaba ta kasa yin baya ,sedai tayi tsaye tare da saka duka hannunta biyu ta toshe kunnen ta ,fitowa mutumin da ke cikin motorn yayi ,fuskar shi a hade da alama tabashi haushi sedai kai tsaye bazaka fahimci hakan ba ,tana nan toshe da kunne sedai taji anja hannunta ,anyi gefe da ita cikeda mamaki ta dago dan ganin waye ,sedai har yayi gaba abunshi yana kokarin shiga motorn shi "am sorry ya tsinkayi siririyar muryarta wacce ke nuna har yanzu acikin tsoro take ,dan waigowa yayi sedai karaf idonsu yahade cikin na juna ,bin junan su da kallon sanin suke sedai sun kasa tuna a ina sukasan juna " she damn cute ya furta can kasan makoshi ,saurin janye idonta kanshi Meerah tayi tafara tattara kayan ta da suka watse....


,,,,,,Harhada kayanta tayi batare da ta sake kallon inda yakeba ta tsayarda napep ta shiga, bin Napep din yayi da kallo harse da ta bace wa ganinsa tukuna yatayarda motorn shi ya wuce.

Cikin Napep ma Meerah se tsaki takeyi se yanzu ne takejin haushin rashin siyan agwaluma da batayi ba

Washe gari tunda Meerah tagama sallah takasa komawa barci,saboda ta matsu gari ya waye Fatima ta zo su wuce ,tanan zaune har 8:00am bataga Fatima ba hakan ne yasakata daukar wayarta ta kirata ,cikin bacci Fatima taji karar wayarta ,dan tsaki tayi ganin an katse mata baccinta ,idonta a rufe ta kai wayar a kunne "Hello tafada cikin murya irin na masu baci " kut ,Meerah tafada cike da jin haushi " amma wlh Fatima ke yar wulakanci ce amma dai kinsan jiranki nake ko ,da sauri Fatima ta tashi tana duba agogo ,waro ido tayi tare da Fadin " am sorry our head girl,wlh bansan lokaci yatafi hakan ba ,tsaki Meerah tayi batace komai ba ta kashe wayar

sa sauri Fatima tashiga toilet wanka tayi tukuna ta fito ta shirya ,zuwa tayi ta samu Momynta tayi mata sallama akan zata tafi gidansu Meerah ,fatan dawowa lafiya kawai tayimata ,saboda tasan wacece Meerah da kuma shakuwar da ke tsakanin ta da Fatima ,saboda ma nemanta da Fatima taitayi ne bata sameta ba yasakata hakura ,ranar nan da Meerah tazo kuwa ,har dare labarinta Fatima kebaiwa Momy sedai tace "yanzu Meerah ta sauya ba kamar da ba ,a da Meerah irin yaran nan ne masu kiriniya shiyasa kaf a school dinsu babu wanda be santa ba gashi tanada kokari ,kuma ta iya zama da mutane hakan ne yasa kowa yake kaunarta.

duk da kwatancen da Meerah tayiwa Fatima,amma seda ta sha tambaya kafin tagane gidan su kasancewar a lungu yake ,kuma unguwar ba wurin zuwanta bane ,da sallama dauke a bakinta ta shiga Aunty da ke kitchen ne taji ana sallama lekowa tayi don ganin waye ,kallon rashin Sani tabi Fatima da shi , murmushi tayi tace " ina kwana? Itama anuty amsa ta tayi cikin sakin fuska,zata tambayarta sega Meerah ta fito , da sauri Fatima ta rungumeta tana fadin "on my kneel head girl,dariya sukayi dukansu ,aunty naganin haka ta gane Fatima kawar Meerah ce ,saboda haka takomawarta kitchen dan karasa abunda takeyi.

Kama hannun Fatima Meerah tayi ,suka shiga daki ,sedai sosai take ganin mamaki hadi da ayar tambaya a idon Fatima ,sharewa tayi tace " ko so kike tace tafasa son ' yar aikin ,dariya Fatima tayi tace " a yanda xuciyarta take cikeda son wulakanta ki ,banajin zata hakura ,amma nikam Meerah meyasa kika zabi to zarta kanki a matsayin yar aiki? Wai ina ya Maryam wai? Dan danan yanayin Meerah ya sauya ,idon ta na kawo kwallah " am sorry Meerah bansan zakiji haushin tambayar ba ,girgiza mata kai Meerah tayi tace" Fatima shin ganin yanda rayuwa ta mayar dani ma bazaki gane cewa komai ya sauya ba ,banda kowa a duniyar nan yanzu ,se wannan matar itace ta mayemin gurbin dangina ,Fatima idan kana duba rayuwa zaka gane kaidin ba kowa bane ,yanzu dai gani Ameerah Farook Head girl da ake alfahari da ita a school 'yargatar da kowa ke burin sakata farinciki Ummina ,Abbanah, yayata mafi soyuwa ,amma gashi yau na wayi gari banda kowa ,burin yayata ya rushe na son ganin nazama cikakkiyar Birrester,ta karashe tana zubar da kwallah ,sosai tausayinta yakama Fatima , hakuri kawai ta bata ,duk da tanason tambayarta dalilin mutuwar Maryam sedai bata so tasake sakata kuka ,kiran aunty ne yasakata,tashi ta fita , kallo daya aunty tayi mata ta gane kuka tayi " ki dauki breakfast dinki ,tafada tana daukar nata tayi ficewa ,cikin mutuwar jiki taaniye jug din kunun agaban Fatima sake fita tayi segata ta dawo da plate din alale,tunkafin ta karasa ajiyewa Fatima ,ta janyo cup ta zuba kunu cikin jin dadi tace " kamar kinsan wlh banci komai ba ,ashe da rabon nazo nasha favorite dina kunun tsamiya ,sosai kuwa tasha kunun hakan ba karamin dadi yayiwa Meerah ba ,don batayi tunanin zatasha ba ,seda suka koshi ,tukuna Meerah ta tashi ,tube kayan jikinta tayi ,ta fiddo wata kodaddiyar atamfa ,duk ta cimuimuye da alama ta dade cikin tsomakara

Kallon mamaki Fatima kebinta da shi ,cikin lokaci takoma kamar irin mutanen nan ,da talauci yayiwa kanta 'bata sha mamaki ba seda taga ta yafa wani gyale kodadde irin pashminar dinnan da akayi yayi can da " mutafi tacewa Fatima " Haba Meerah me kikeyi haka kinkuwa sam wane irin gida zamu tafi ,ai seki saka Rufaida korarmu " kar ki manta ,fa Mabaraciya ce ke gabanki,zamu tafi ne amatsayin yar aiki bawai kawarta ba ,kuma kora bana tunanin haka daga wurinta domin bawai saboda nayimata aiki ta daukeni ba ,sedan ta wulakantani,so na fison taganni a wulakancen ,jinjina kai Fatima tayi alamar gamsuwa .

Seda ta shiga dakin aunty tace" aunty kimun fatan nasara zamutafi " to Ameerah rabbi ya dafa miki ,da amen ta amsa tana jin dadi har cikin ranta ,sun dade sosai abakin titi kafin suka samu Napep din da zata kaisu unguwar


Knocking sukayi me gadi ya leko ,binsu da kallo yake ,yagane Fatima ,itace wacce ke zuwa wurin Rufaida, sedai mamakin ganin ta yake tare da wannan da batada banbanci da mahaukaciya ,gaisheda Fatima yayi yana bude mata kofa ,shiga tayi Meerah nabinta da a baya " ikon Allah yafada cikin xuciyar shi ,ga yarinya kyakkyawa ,ta bugu da jarida,amma da ganinta ta hadu da jarabtar ciwon haka ,ga kuma talauci domin da gani wannan tana cikin ciwon rashi


Tunda suka shiga gidan Meerah takebin harabar gidan da kallo yananan yanda ta sanshi,sedai sabon fenti da akayi " dallah malama zaki fara kauyanci tun bamu shiga ciki ba ,Fatima tafada cikin sigar xolaya ,murmushi kawai tayi wanda da alama na yake ne ,cigaba da tafiya sukayi se gasu sun bayyana a cikin wani falo na alfarma ,fadin kyau da tsarinshi bata lokacine ,zama Fatima tayi akan daya daga cikin kujerun falon ,itama Meerah ta samu daya ta zauna " sannu da zuwa Hajia me aiki ta gaisheta ,cikin sakim fuska Fatima ta amsa ,kifadawa Rufaida ina jiranta,da "to ta amsa,bata dade da tafiya ba segata tadawo tace " tana zuwa ,andauki tsawon 10 minutes,se alamun saukowar Rufaida daga stairs sukayi " tun kafin ta karaso suka tsinkayi muryarta tanafadin .........


**Magana ta gaskiya mutanen Group ɗina zan Dena yi muku posting,se nake ganin kamar labarin be karɓu* a *wurinku ba ace bb wacce zata iya yin comment,ku gyara idan kunaso ko na* *komawats* *Wattpad dama asalin labarin nasu ne*


Comments nd share

#Vote and follow me@ damselfeedo




#Real#Bazamfaria
*INTELLIGENT* *WRITERS* *ASSOCIATION*
(On ward together)

*MABARACIYA*

*Story* *and* *writing*

By

*FIDDAUSI* *SANI*
(damselfeedorh)

🅿️:1️⃣1️⃣

,,,,,,,Kuskure mafi girma shine na riski kaskantacciyar yarinya zaune a inda nake zama ,tunda Rufaida tayi wannan maganar Meerah ta fahimci da ita take ,cikin sanyi jiki ta zube kasa,cikeda da isa Rufaida ta karaso cikin falon ,seda ta samu wuri ta zauna tukuna ta kalli Fatima tana wani yamutsa fuska tace " ke kam Teemah kincika jajume jajume ina kuma yau kika samo Mahaukaciya? Tayi maganar cikeda wulakanci ,sosai kalmar ta shigi Meerah wanda hakan yasakata dago ido da sauri ta kalli Rufaida,sedai saurin mayar da kanta tayi akasa ,saboda bataso ta fahimci komai.

Murmushi Fatima tayi tace " she's the one, blinking ido Meerah tayi mata alamar bataso ta nuna taganeta ,saboda kar yarinyar ta canja ra'ayi ,shiru Meerah tayi tana saurarensu

Fatima kamar yanda naji kince kina neman 'yar aiki to gata na samo miki ,cikeda hargowa tace "me kike nufi badai wannan me kala da mahaukatan ce zan dauka aiki ba ,wannan ko ruwa ta taba ai bazan iya shan suba kidubeta fa " aa Rufee bazamuyi haka ba ,ko ba komai yarinyar ,iyayenta ne abun tausayi ba ita ba ,suna fama da ciwon talauci

" And so? Ko nice na saka musu talaucin ,daga ganin iyayenta ,basu san me sukeyi ba tunda har zasu iya turota aiki a irin wanann yanayin,cikin tsawa Meerah tace " karki kuskura 'yarnan zan iya daukar komai amma banda cin fuska ga sanyi idaniya ta ,iyaye da kike gani sunfi karfin to zarci ,tana gama fadar hakan ta tashi da niyar fita ,sedai a cikin xuciyarta addu'ah take Allah yasa Fatima ta tsaidata ,domin batasan da wannan plan dinba ,har tafara taka kafarta ta tsinkayi muryar Fatima tana fadin " fitar da zakiyi shine sakaci na karshe da zakiyi da damarki ,idan har da gaske kike iyayenki sanyin idaniyarki ne to kuwa tafiya bata kamakiba domin kinsan yanda suka kwallafa rai a wannan aikin naki ,suna ganin kamar wata mafita ce Allah ya kawo musu na fita daga kangi yunwar da kuke fama dashi ,kinada kanne kanana ,dukansu yanzu ,burinsu akanki yake be kamata mai nema yarika xuciya ba .

Shiru Rufaida tayi tana saurarensu,ita sam hankalinta be kam maganar Fatima kawai tunanin irin xuciyar yarinyar takeyi ,tayi zaton ,komai zatayi mata bazata tanka ba saboda ,zafin talauci kwafa tayi tana ayyana irin tozarcin da zatayi mata ,jiki a sabule Meerah ta dawo ta zauna ,tana sauke ajiyar zuciya domin batayi tunanin Fatima zata iya yin wanan tunanin ba , seda Rufee tayi wani irin murmushi wanda itakadai ta barwa kanta sani manufar sa tukuna tace " Temah ,idan zata iya kiyaye duka sharuddan da zan gindaya mata ,kallon Meerah Fatima tayi tace to kinji ,cikeda dakewa tace" ina saurare

Na farko dai ni banda 'dakin da zan ajiyeki , bawai kuma saboda babu dakin a gidan bane sam sedai baki can canci ki zauna ba ,na biyu dole 7:00 yayi miki a cikin gidannan ,saboda 8 Nake tashi nayi sallah to kafin nashiga bayi ina bukatar ki tsaftace shi, se abu na karshe ,gada kiyarda yunwar iyayenki yasaki

Please Login or Register in order to submit comment