Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bakin ƙofa yana ƙare mata kallo daga inda yake dukda bawai yana ganin fuskan ta ba ne shi kansa da yake namiji yana jin wani iri to bare ita ,da ya ga dai tsayin babu abinda ze yi masa kawai se yayi salla ma ya na ƙarasawa ciki , shiru bata amsa ba ,ajiye ledodin da ke hannun sa yayi ,ya zauna daga gefen gadon ,cikin sanyin murya yace " ya kamata kidena kukan nan dan yanayin sautin sa ya tabbatar min da ba yanzu kika fara ba ,aure ne dai an rigada an ɗaura kuma kuka ko ƙunci be isa yaqq sauya ƙaddara ba ,a iya haka ma ni Nagode wa Allah dan ina da tabbacin ya musanya min ne da mafi alkhari ,ke ce alkairi a rayuwata shiyasa Allah be mallakamin Meerah ba , lokacin da aka ce za'a bani ke nace a'a saboda ina tausayin halin da zaki shiga dan na tabbata baxaki rasa wanda kike so a zuciyar ki ba amma abun mamaki se gashi Ammi tace wai kin amince zaki aurene lallai nayi sa'ar mace me biyayya ,saboda haka nake so ko da bazaki so ni yanzu ba to muyi zaman mutunta juna na tabbata watarana zaki soni ,kuma nayi miki alƙawari baxan taɓa kusan tarki ba se randa zuciyar ki ta amince miki da na zaman abokin rayuwar ki ,ki dena kukan nan da kikeyi ,kishiga ki watsa ruwa ,se ki kwanta nima zan tafi ɗakina ne "

Sosai Rumaisa taji daɗi da jin baze kusan ce ta a yanzu ba ,duk da tayi ƙudurin yi masa biyayya dai dai gwargwado koda ba ta son shi amma tana ganin ƙimar sa domin alfarma yayiwa mahaifiyar ta ,dan haka zata zauna dashi kamar yadda ya buƙata ,share hawayen ta tayi ,cikin Muryar ta da bata fita tace " na gode " murmushi yayi mata yace " nasan kinajin yunwa idan kinyi wankan ga abinci nan na shigo Miki dashi ,ki tabbata kinci kafin ki kwanta " kanta kawai ta ɗaga masa ,tana kallon shi ya fita ɗakin tare da ja mata ƙofa.

Washe gari na tunda tayi sallahr asuba ta koma ta kwanta ,ba ita ta tashi ba se past 9 a gaggauce ta shiga tayi wanka ,bata wani yi kwalliya ba ta saka riga da sket na atamfa motsin da jiyo ne ga kuma kara tanaji kamar ana soya wani abu fito wa tayi tabi hanyar da take jiyo motsin ,sega ta cikin kitchen Muhsin ta gani ya naɗe hannun jalabiyar sa yana zuba ruwan zafi a flask da alama break fast yake shirya wa ,mamaki ne ya kamata ,ya za'ayi ace yana da mata Kuma se ya shigo yayi girki da kansa ,ƙara sawa tayi ,ta ce " ina kwana" da murmushi ɗauke a fuskan sa ya juyo yana kallon ta kasa tayi da kanta dan bazata iya kallon sa ba ,se yanzu yake kallon matar tasa " ita din ma kyakkyawa ce kuma da alama zatayi saukin kai "a bunda yake faɗa kenan a zuciyar sa a fili kuma ya ce " amarya kin tashi lafiya ? Na shigo in dubaki ai na sameki kina bacci ,yanzu ma saurin da nakeyi na kammala miki breakfast dan naga naman da na kawo Miki jiya ma ko buɗe wa bakiyi ba ,kingan shi nan a oven ina warming miki , ga ruwan zafi nan na dafa ,yanzu me kike so ban wani iya girki ba indomie kawai na iya dafawa se kuma idan dankali zan soya miki " girman sa ya daɗa karuwa a idon ta bata san sadda tayi masa murmushi ba a hankali tace " da ka ta sheni ai zan dafa ,ruwan zafin ma ya isa Nagode " hararan wasa yayi mata " a'a ni gidana ba'a zama da yunwa ko kinaso ki rame ne Ammi ta tuhumeni ,tace baxan tafi mata da yarinya ba ,Kinga ki faɗa dai me zaki ci? Shikenan to yanzu katafi ka huta zan kara aikin ko indomie ne se na dafa " yaawwa to yanzu naji batu bara natafi nima in shirya dan zan fita zuwa 2 zan dawo na ɗauke ki muje ayi Miki passport " fita yayi ita kuma tafara tunani ita dai a iya sanin ta idan da mutunci matar sa ne ya kamata ta basu abinci se gashi da kansa cikin kitchen "Allah" ya kyauta ta faɗa tana shiga store din dake cikin kitchen ,ta fara duba abubuwan da ke ciki babu abinda babu na nau'in abinci ,se dai idan tace tayi wani abincin babu wasu vegetables a gidan se kawai ta dafa indomie kamar yadda yace.

tana gama dafawa ta zuba kaɗan a plate ,se ta juye sauran a cooler ,ta kai kan dinning ta ajiye ,ita kuma ta shige ɗakin ta ,ba ta wani ci indomien ba saboda cikin ta da takeji a tunkushe , haka ta dauka ta mayar kitchen ta ajiye , koda ta fito kitchen din shima yana shirin shigowa karo suka ci se ya dawo baya " Kinga ma girkin ne? " Ehhh na ka yana kan dinning ma "ohhh ni ai na rigada na sha tea da kin sani ke kaɗai kika girka ,Kinga fita zanyi " ok to a dawo lafiya " Allah yasa ya faɗa yana fita ,ita kuma ta koma ɗakin ta shiga tayi ta wanke toilet ɗin ta sannan ta dawo ta gyara ɗakin ,duk kewa da kaɗaici ya dame ta ,ga bata tunanin ma an zo mata da wayar ta ,hang bag ɗin da Amrah ta haɗo mata kayan amfanin ta ta buɗe cikin Sa'a kuwa wayarta na ciki da sauri ta ɗauko 10 missed call ta samu na Amrah ,se kira ɗaya da Dady yayi mata 10 minutes ago "wasu hawaye taji sun zubo mata ,ganin Ammi bata neme ta ba ,dan haka tafara kiran Daddy , ringing ɗaya ya daga " hello Rumaisa kintashi lafiya? Seda ta share hawayen idon ta tace " lafiya lau Daddy ya gidan ? Gida lafiya lau ya baƙunta "Alhamdulillah " babu dai wata matsala ko? Ehhh Daddy babu komai se kewar ku dan Allah Daddy a kawomin su Mimi su tayani zama " a'a Rumaisa zasu zo dai amma se kin kwa na biyu muma muna cike da kewar ki Allah yayi miki albarka kiyita hakuri kinji " Ameen Ameen Daddy na gode ka gaishe da Ammi " a'a bazamuyi haka da ke ba ki kirata ki gaishe ta mana " turo baki tayi tace " Daddy Ammi ta manta dani ko kirana batayi ba fa ,se kaine ka kirani " Dariya Dady yayi yace " to ayiwa Ammi haƙuri tana kawaici ne babbar ƴa tayi aure ,ki kirata kinji " to shikenan Daddy " kigaishe da mijin naki" wani banbarakwai taji sunan wai mijin ta ,amma dai ta masa da "zeji " da ganan ta maida akalar kiran ga Amrah


Tana ɗagawa tafara mata shaƙiyanci " wato ana can ana shan love anbar waya ina ta faman kira babu reapond ,ke kin manta da wata Amra bayan ni na kasa bacci se tunanin ki nakeyi " hmmm Sis baxaki gane bane bansan kin haɗomin da wayar bane ,se yanzu da na duba " iyye to gist me how was the first night" Kai Amrah Allah ya shiryeki ,ai zaki ji nide yaushe zakizo inata baza ido na zata ko tunda safe na ganki " ke rufamin asiri kinsan halin Hajia Inno ƴar iko itace tace bazamu zo ba sai se kin kwana biyu ,wlh babu yadda banyi da Ammi ba ma ta barni inzo itama tace wai idan nazo zaki iya tada rigima mubarki sekin huta " mtswwww yanzu ke se ki biye su baxaki zo ba ko a ɓoye ,kinganni ni kaɗai a ɗaki kamar mayya matar gidan da alama batada kirki dan Allah dai kizo " to shikenan bara nayi wanka akwai labari ma zan zo wlh ki ajemin kazar amarci ko kin cinye ? Dariya Rumaisa tayi tace " tana nan tana jiranki kedai se kin zo.


#Meerah

Seda ta tabbatar Mu'aiseen ya fita kafin ta fito daga toilet ,zama tayi bakin gado tana tunani "meyasa to ba'a ɗaura auren Rufee da Mu'aiseen? Kuma ta tabbatar da Rufee tana son sa ,lallai dole ta gode ma Allah yanzu ne ta fahimci hikimar Ubangiji na kawo ta cikin a halin gidan ,waya hanya ce me sauƙi da zata kula da duk wani motsi na Hajia Sauda,sedai taya? Dole ne se na fara daƙile harƙallar da takeyi a garin Niger ,domin yin wannan aikin kuma dole se na samu wacce zata shiga cikin gidan domin ganin sirrin su ,tabbas yanzu ne manufata zata fara yanzu ne zan tarwatsa Sauda ,ina so ne hankalin ta ya tashi ta rasa natsuwar ta ta yadda zan samu aikina na Niger ya tafi daidai to me ya kamata nayi?.........





Comments and share pls


#Real@Bazamfaria❤️

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment